UMMAH KO SALMA Book 1 Complete Hausa Novel Document by UMMAH KO SALMA Book 1
UMMAH KO SALMA Book 1
Reading Time: 0 Hours
Added On: 06, Feb 2025
Author: Aisha Hamza Muaysh Graphics ,
Ebook Compiler : Admin
Author Group : Unknown group
Author Phone : 09131096058
Book License : Free
Category: Love Novels
File Size: 14.8 kb
File Type: txt
Views: 282+
Download: 76+
Last download: 7 hours ago
_NA A'ISHA HAMZA_ (MUAYSH GRAPHICS)
11/OCTOBER/2004
Bismillah
Godiya ta tabbata ga Allah (S,W,A) Wanda yabani ikon fara rubuta wannan littafi lafiya ina fatan yanda nafara lafiya Allah yabani ikon gamawa lafiya
Labarin Ummah ko Salma labarine kirkirarre ba rayuwar wani aka kwaikwayo ba koda kuwa tayi kamanceceniya data wani zai iya kasancewa domin duk abinda muka hasashe a rayuwa zai iya yiwuwa wani shi hakan ya faru dashi
Ina fatan masu karatu za'a min uzuri kusan dan Adam ajizi ne dole zai iya kasancewa nayi kuskure a wani wajen a cikin rubutu na ina fatan za'a fahinceni kuma aiman uzuri
Nagode sosai da wanda zamu fara karatu dasu da kuma waɗanda zasu karanta nan gaba kuma ina neman addu'ar ku akoda yaushe
Allah ya jikan iyayen mu da gafara Ameen 😭🙏
Umma umma umma sunan da taketa faman kira kenan tunda ta farka kwance take saman tafkeken gadonta wanda taketa faman juyi ita kaɗai sai kiran sunan ummah take idanuwanta gam suke domin ko buɗe su batayi ba
A firgice ta shigo dakin hannun ta rike da uniform da kuma school bag hada da sandal duka a ƙasa ta zube takalman ta juya ta ajiye jakar saman bedside drawer uniform din kuma ta ajiye su daga gefen gadon
A dabarbarce take furta kalmar kiyi hakuri bansan kin farka ba ina sauri ne nahaɗa miki breakfast nakawo maki da naga sun gama
Sai a lokacin ta fara ƙoƙarin bude lumsassun idanuwanta masu kama da wanda bacci bai ishe shi ba ta ɗora su akan yarinyar da taketa faman kwalawa kira
Kin kyauta shine kawai abinda ta iya furtawa kafin ta yunqura ta mike zaune tana ƙara lumshe idanuwanta hadi da hamma
Kasa kasa ta furta saina tuna maki abinda ya kamata ne tanajan tsoki kamar bata son furta kalma da sauri wadda aka yiwa magana ta haye saman gadon tareda zagayawa bayanta tana daga mata rigar jikinta sama
Saida ta cire mata rigar kafin taqarasa yin cilli da'ita qasa ta mike tsaye saman gadon kamar yadda ta cire mata rigar haka taja dogon wandon nata arsh silk ne yadin wandon daga gani kayan bacci ne masu tsada da ɗaukar ido wajen kyallin yadin
Ƙasa tay mata i dashi ya rage daga ita sai short da bazai wuce gwuiwowinta ba da suka fito santala santala sai havebest
Saida tagama taimaka mata tacire kayan kafin ta sauko ƙasa tareda miƙa mata hannu ta kamo ta itama ta ziro kafafunta kamar wadda batasan taka ƙasa haka ta mike
Sakin hannunta tayi a hankali take tafiya ta nufi toilet domin tayi wanka Saida ta rike handle kafin ta juyo ta dubeta tsaye ƙekam daga ƙasa har sama taqare mata kallo kafin tace karki bari yau nayi let a school saboda shiriritarki
Ikon Allah wai na cikin masai ke cewa na waje ka taka kashi kai tunda ga farko zaka fara gane wanene mashiriricin a cikin su amma ta haɗe rai ala dole kar aja mata let a makaranta oh to muje dai zuwa muga ya zata qare kunsan bani gani na kyalene ah to😆😆😆
Sunkuyar da kanta tayi ƙasa tace inshaa Allah bazakiyi let ba Saida ta shige kafin ta sauke ajiyar zuciya tayi waje kafin ta fito tadawo hannunta rike da faffadan tray wanda yake cike da kayan abinci kala kala iya dai abinda nake iya tantancewa a ciki akwai soyayyar kaza a banƙarenta sai kuma tea cup guda ɗaya yaji kayan hadi sai slice bread a cikin ledarsa sai kuma wainar ƙwai da aka soya a cikin plate sai noodles da wasu hadaddun warmers da bangane sukuma suwaye aka zubo a ciki ba
Dan madaidaicin table ta jawo ta ɗora kayan abincin a sama kafin ta koma gefe ta tsaya ba tareda ta fita waje ba
Fitowa tayi jikinta sanye da ɗan qaramin towel wanda ya bayyana santala Santalan cinyoyinta da wani qarami a hannun ta tana ta faman goge jikinta
Saida ta gama kafin tanufi mirror ta zauna batare da tace komai ba Umma tawuce daga bayanta tajawo hand dryer tajona jikin socket ɗin dakin Saida ta tabbatar ta busar mata da kanta bayan ta gama ta shafe mata shi da mai kafin ta bi illahirin jikinta tana shafa mata man a jikinta
Saida tagama tsaf tana zaune anan aka jawo dan madaidaicin table din dakin da aka jere shi da abinci a baki umma ta shiga bata shi tana ci kamar bata son taunawa tsaf tagama tace ta koshi uniform Umma ta dauko ta fara mika mata inner wears ita kuma ta juya baya Saida ta kammala sakawa tayi gyaran murya
A hankali ta taimaka mata ta saka uniform ɗin wanda ko arzikin scarp babu a cikin su sai riga da mini skirt wanda iya gwuiwa ya tsaya sai doguwar safa fara wadda zata kai inda skirt din ya tsaya daƙyar ta tattara mata gashin kanta da ribbom ta daure shi
Saida tagama shiryawa tsaf Umma ta dauko mata school bag dinta sukayo waje parlour suka fito tsaf yake a gyare sai masu aiki da suke ta shirya breakfast a wani dining table mai mazaunin mutum shida uku na facing uku
Tana gama umma na bayanta har suka fito wajen gidan parking space suka nufa kafin su isa saiga wani babban mutum ya fito daga motar ya buɗe bayan motar
Kafin ta shiga Saida yafara gaisheta Barka da safiya Sweety yauwa baba ta bashi amsa a taqaice Saida ta zauna kafin umma ta mika mata jakar daga ciki har zata juya
Muryar ta ta tsaida ita tana faɗin ina zakije waye zai ɗauka school bag din idan mun isa school din
Ƙasa ta kalla tana wasa da yatsun hannunta baba ne yayi saurin faɗin haba umma ke sai kace wata qaramar yarinya idan ta manta saiki dinga tuna mata yau Alhamis zakije tahfeez Koh
Bata dago ba har ya gama magana kafin yace karki damu sweety ni zan rakaki har aji inshaa Allah
Bata qara cewa komai ba tagyara zamanta kafin ya rufe mata motar ya koma mazaunin driver ya zauna
Saida suka fice daga gidan kafin umma tajuya da sauri takoma cikin gidan kamar yanda suka bar parlour bakowa a ciki haka tadawo ta same shi
Wucewa tayi dakin Sweety ta gyara mata shi tsaf duk da dama ba datti gareshi ba ta wanke toilet da inner wears din data cire bayan ta gama ta kwashe kayan da taci abinci tayi waje dasu ta kulle mata kofar
Sauri sauri take tafito tanufi hanyar fita daga parlour ɗin kamar daga sama taji ya ambaci sunanta ke umma kiran da tasan dole sai ya ɓata mata lokacin zuwa gida yanzu
Matashi ne da bazai wuce 19 years ba daga gani jikinsa yaji hutu fari ne sosai yanada dan saje kaɗan saboda an dan fara girma kuma jiki na shan hutu
Na'am ta amsa ƙasa ƙasa su biyu ne a saman dining ɗin suna cin abinci daga gani basu jin yunwa sai wani cakalkalashi suke kamar an musu dole
Meyasa ke bakijin magana umma dole ke sai ana tuna maki ba nace kidinga gyaramin dakina ba eye
Dayan da kamar baisan tana wajen ba wanda bazai wuce 17 years ba suna kama da Babban daga gani yaya da qanine su biyun yace ai kasan ta baiwar Sweety ce kamar don ita aka halitta ta baka isa ka sanya ta abu tayi maka ba indai Sweety na nan
Tsaki yaja yace to yau ko Daddy bazai iya tseratar dake ba bare wata Sweety maza ki wuce ki gyaramin daki na
Shegiya munafuka ana mata magana tana wani sumsum dakai qaramin ya faɗa yana ƙoƙarin mikewa
Juyawa tayi zuciyar ta babu daɗi kullum addu'a take batason haduwa da mutanen nan a cikin gidan nan yau gashi batayi tsammani ba sai suka haɗe
Karki kuskura Inga kin shiga dakin nan Saida ta sauke ajiyar zuciya kafin tace Alhmdllh a zuciyarta
ta juyo Nawwara ce tsaye hannunta rike da tea cup kayan bacci ne ma a jikinta daga kitchen ta fito taganta zata shiga dakin su Safwan
Budurwa ce amma zata kai irin 24 years dinnan tanada dirin jiki itama farace sosai amma ba kamar mazan ba tanada manyan idanuwa da dan hancinta qarami da yasha nose ring
Ba aikin Sweety kaɗai kike a gidan nan ba me zakije yi dakin su Safwan ko so kike kija mana zagi eyyee
Ah ah Anty Nawwara Saheeb ne yace lallai sai na gyara masa dakin sa taqarasa da in,ina… don tasan dole ne saiya hukuntata indai yasamu dama
Ido ya raina fata daga Saheeb har Safwan qarasowa tayi parlour tana ajiye tea cup ɗin hannunta saman stool
Wai kai Meyasa saheeb bazaka girma ba eyee dole kai saika nema mana magana a gidan nan koh to wallahi kufita daga idona daga kai har Safwan Meyasa bakujin magana ne
Wallahi
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.
Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku
ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.
Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi
NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
Read / Download UMMAH KO SALMA Book 1
You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
OR
Login RegisterReleted Novels
- BAKINA YA JAMIN - Dr Maryama Ibraheem
- KAMAR DA WASA - Ummi Aisha
- MAJOR SALMAN - Maman Hanan
- KYAUTAR KODA - NoorEman
- MATAR SOJAA - Aisha Muhammad Maman Shakur
- BAYI MA 'YA'YANE' BOOK ONE - Jameela Jameey ƴar mutan Kankia
- YATSUNMU - Sadnaf
- SIRRIN DAUKAKA - Aisha JB
- KUFAN WUTA - Safiyya Abdullahi Huguma
- SHIGAR SAURI - Maman Shalele
- SANADIN KADDARATA - Mhiz Innocent
- BABANA DA MIJINA - fertymerh xarah