Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 2
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels SAI NA GA RAHMA SADAU Marubuci Imam abdullahi usman Publish by:-http://fb.com/hausaebOoks SAI NA GA RAHMA SADAU Na IMAM ABDULLAHI USMAN Gajeren labari Dedicated to Sulaiman Ibrahim Azlan Posts by SHURAIH 99% Part 1 FARKON LABARIN . zaune nake a kofar gida, bisa kan benchi. Yammaci ne misalin karfe 4 da 'yan mintuna. Nazari nake gami da tunanin lbrn da zan soma wallafa. "assalamu alaikum" muryar wani matashi ta katseni, "wa'alai kassalam" nace gami da dagowa na kalleshi. "yauwa wlh dama ni bakon kane, nasha wahala kafin in samu gidanku, wuni nai ina yawo. Yace dani na sake dubansa, tabbas duk inda aka je, aka zo bakauyene, kuma ba bafulatani bane. "gashi kuma bangane kaba, anya kuwa ni imam din kake nema ? Na ce dashi. Ya gyara tsayuwa gami da cewa "tabbas kaidin dai, wannan me rubuta lbr a yanar gizo, koba nan ne unguwar matsango ba ? Ya fada gami da jefamin tambaya. "maraba da zuwa, tabbas nine, na fada gami da mikewa, nace muje daga ciki. Daki na na kaishi, gami da dauko masa ruwa da guntun abincin rana. Na bashi waje, sai da ya gama sannan na dawo. "da farko ina maka barka da zuwa, sannan zanso sanin kai waye da dalilin zuwanka" nace dashi, dai dai lokacin da zauna bakin katifa. Bakon yai ajiyar zuciya gami da cewa " sunana rabi'u amma anfi sani na da rabe, nazo ne daga kauyen dalli nan karamar hukumar shira, akwai wani abokina dan makaranta, da muke kwana daki guda da shi, shi ke karanta mana lbrn ka, gaskiya muna jin dadi. Yanzu haka takaici nake da ban iya karatu da rubutu ba, tabbas da ace na iya, da saina kwace maka dukkan magoya bayanka, da zarar na rubuta lbr daya. Nai murmushin rainin wayo gami da cewa "ina maka barka da zuwa, kuma nayi farin ciki, ashe kaima kana da ra'ayin rubu2 ? Ya gyara zama "ai kai dai kawai ka bari, allah ne ya ragewa aya zaki, yanzu dai ka karkada kunnuwanka, kasha lbrn soyayyata da rahama sadau. "comedy kenan, na fada araina, yanzu wannan ba kauyen har ya isa ya tsara wani lbr ? Jifa tsabar shirme wai shi da rahama sadau. Amma a zahiri sai nace "inajinka" {ko ba komai ai zansha nishadi dan lokacin completly ali artwork na dauke shi} rabe ko ince rabi'u ya soma da cewa.... ¤¤ malam barau da gwoggo tani sune mahaifana, babana bai da wata sana'a face noma, ita kuwa gwoggo tani dinkin tabarmar kaba take. Ni ka daine dansu, dagani ba kowa, hakan yasa suka shagwa6ani, bana kallon kowa da mutumci duk girmanka yanzu zan maka tijara, in takaicema lbr ko su iyayen nawa ma ban ganinsu da daraja. Na dago idanuna na kalle shi cikin mamaki. "karkai mamaki na bawan allah, su suka raine ni da hakan, kuma na dau course. Ya cigaba "shekara ta 18, amma bansan ko bihim ba, abarma maganar boko kam, dan ko A ban saniba. Wayar da babana ya siyamin ban cika ta da komai ba, face fina finai da wakoki gami da fotunan rahama sadau. Dan haka na taso mai kaunar wannan baiwar allah, awancan lokacin inason rahama sadau fiye da kowa a duniya....! Bari in takaita haka, in soma fada maka, musabbabin lamarin. Karfe 8 da 'yan mintuna, na fito daga dakina rike da wata tsohuwar jakata, ba komai ciki face 'yan tsummo kara na. Mahaifiyata dake fama da wutar dumame ta dago ta dubeni, "dan baba ina zaka da tarin kaya haka ? Sai da na gama garkame dakin, na dubeta nace "neman rahama sadau" a zabure ta dubeni, tuni idanun ta sun kawo ruwa, "dan baba ka rufa mana asiri, dan allah karka fada uwa duniya. "wannan kuma ya rage naki gwoggo, amma yau kwana sai kano. Nace gami da rarumar 'yar jakata na aza a ka. "wayyo allah malam na shiga uku. Tafada da karfi babana ya fito daga daki. a rikice taimar bayani, ya ruga da gudu da nufin ya taroni. "kai dan baba" naji yana kwadamin kira a sa'ilin har nayi nisa, na kusa cimma tasha, na tsaya gami da jiransa. "wlh baba saina tafi nemanta, ai yanzu da hankali na niba yaro bane. Nace dashi ina huci. Mahaifina yana kuka, yana roko na, gami da rikemin jakata. Akan na hakura da tafiyar nan, amma haka na fizge jakata har sai da ya fadi, naje tasha na hau motar azare, daganan na shiga ta zuwa kano, da zumar haduwa da rahama sadau. Direban motarmu, ya kure totir, gami da jan motar aguje.......! ¤¤ port 2 na loading ¤ www.facebook.com/hausaebooks SAI NA GA RAHMA SADAU Na IMAM ABDULLAHI USMAN Gajeren labari Dedicated to Kingboy Isa Posts by SHURAIH 99% Part 2 . motarmu ta shalla kan titi, zakai mutukar razana idan kaga yadda direban mu yake, jan motar da gudu, kai kace ba rayukan al'uma bane aciki. An saukemu a wata tasha, da na mance sunanta, passingers kowa ya soma sanin inda dare yai masa. Nima jakata na dauka, gami da mikewa nai gabas, sai da dai 'yar ubansun tafiya sannan na yanke shawarar yin tambaya, tunda hausawa sunce matambayi bashi 6ata. Wani mutumi na hango, akallah zaikai shekaru 28 yazo gilmawa ta gabana. "malam dan allah tambaya nake" nace dashi yaimin kallon banza , gami da cewa "ina jinka" na gyara tsayuwa na ce "dan allah inane gidan "yan film din hausa ? Ya dubeni a wulakance gami da cewa "ka gamu da aiki ai shasha, anan zakai ta gararamba" yana gama fadin hakan yai tafiyarsa. Na bishi da idanu gami da jijjiga kai, lokaci guda naji hajijiya na damuna, sakamakon cikina dake min korafin yunwa. Sannu ahankali na bude baki gami da kiran wata yarinya mai sai da gurasa da ruwansha. Haka na ci gura sar nan, tana shakata ina korawa da ruwa. Nakoma jikin wata inuwa na dan huta. Daga bisani na kuma daukan jakata, lokacin rana ta take. "malam dan allah ni bakone, tambaya nake. Na ce da wani mutumi da nake kyautata zaton zai kai 30. Ya dubeni cikin sakin fuska " yauwa inajin ka" cikin kwarin gwiywa nace "wlh ni bako ne, daga jihar bauchi nazo wajen "yan film ne, ina son ganin RAHAMA SADAU. Mutumin yazaro idanu gami da yin murmushi cikin farin ciki yace "alhamdullah, ka godewa allah, tazo gidan sauki, allah ya takai tama, sunana YASEEN AUWAL". Cikin zumudi na dubeshi, kana nufin daraktan film din RARIYA..? Ya jinjina kai gami da yin murmushi, yace tabbas kuwa "yanzu haka na kai mota ta gareji ne. "dan allah malam ka taimakeni, dan allah kaimin hanyar ganinta, wlh dan ita nazo. Nace dashi cikin sigar rarrashi. Ya dubeni gami da dafa kafadata yace "zan tai ma keka, kasa aranka kaga PRIANKHA, ni dai kawai bukatata kayar da dani. "malam na yarda dakai wlh, nace dashi cikin zumudi. Nan ya tara mana adai dai ta. muka shiga, aka kaimu wata unguwa. Kasan me yaban mamaki imam ? Na jijjiga kaina. yace " gidan da ya kaini amatsayin gidansa, bawani gd ne na kuzo, mu gani ba, dan gidan kansilan kauyenmu ma ya fishi. Daki dayane ciki da falo, balaifi akwai tv da "yan kujeru a falon, dakin kuma katifa dayane. Bandaki ya soma nunamin yace naje nai wanka, yana zuwa. Na dade ina wankan, daga bisani na fito. Na tarar da shi zaune, a bakin katifar ga wata kodaddiyar kula a gabansa. Da kyar na iya sanya kaya, duk ya kureni da wasu idanuwansa, niko ba sabawa nai ba. Ya sani agaba sai da naci abincin. Daga nan hira muka dingayi, yana bani lbrn wuyar da suka sha a shooting din RARIYA, nayi mamaki da wani abokinsa ya kawo masa ziyara, naji yana kiransa NURA AJI DADI, amma banda halin tambaya. Da daddare an kawo wuta, tun kusan 8 ya kunna mana kallo, anan yake sanar dani cewa RAHAMA SADAU taje daukar wani film za suy kwana 6 su dawo. Ni kuma na yarda. Da daddare muna kwance....! Rabe yana zuwa nan ya fashe da kuka, na dago gami da kallonsa cikin kaduwa nace meya faru? Ya jijjiga kai gami da share kwalla yace..... Ashe....! ¤¤¤ page na loarding ¤ ¤ SAI NA GA RAHMA SADAU Na IMAM ABDULLAHI USMAN Gajeren labari Dedicated to Jidda Abdullahi Usman Posts by SHURAIH 99% Part 3 . rabe ya tsai da hawayen dake gudana a idanuwan sa, yace ashe..! Mutumin nan yaudarata yai, mutumin banza ne, fasiki, macuci, ji nai ya sanya hannun sa a al'aurata...! "Innalillahi shine abinda na fada cikin tashin hankali, nace ya aka kare ? Rabe ya jijjiga kayi gami da share wasu hawaye, lokaci guda wasu suka biyo baya. Muryarsa adashe yaci gaba, "haka inaji, ina gani, ba barci nake ba, ya karishi wasan sa dani...! Rabe na zuwa nan ya kuma fashewa da kuka, na matso kusa dashi gami da dafashi, ina mai bashi hakuri. Ya cigaba da bani lbr, "imam bani da mafita a wannan lokaci, sabida a wannan lokaci idan nai wani yunkuri, komai zai iya faruwa. Da gari yawaye har kusan 7 bai tashi daga bacci ba, cikin sanda na hada na dau jakata, gami da ficewa daga gidan, wani kuka ne, ya su6ucemin lokacin da na tuna abinda wannan tsinannen bawan allah yaimin. Na dubi rabe gami da cewa "ba yaseen auwal din bane ba kenan? Ya dubeni cikin takaici, "haba imam yakake tambayar abinda ka sani ? Kaima kasan kawai ya yaudareni ne ya cuceni. Nai tsam, dani dama tunda ya soma bani lbrn na gano wannan mutumin 6atagari ne, baida nasaba da'yan wasan hausa. Inajin ka malam rabi'u nace dashi. Ya cigaba "jiki na yana rawa, na gaggauta barin layin, sai da na danyi nisa, na sami waje na zauna gami da soma risgar kuka, hawaye nata kwarara a idanuwa na. "malam tun dazu nazo wucewa, na tarar da kai kana ta kuka lafiya ? Wani matashi da nake zaton zai kai 20 yaimin wannan tambaya. Na dago da jajayen idanuwana, na kalleshi, koba komai ina bukatar taima ko. "dan allah ka fadamin damuwarka, musulmi dan uwan musulmi ne, kuma daga gani kai bakone" yace dani cikin sigar lallashi. Nan take na juye masa lbr na, da duk wani abu da yafaru dani. Ya tausayamin sosai, sannan ya dora da cewar " wancan gidan ba gidan mutanen arziki bane, an dade dama ana zarginsu da naiman juna, allah ya kyauta. Idan bazaka damu ba, kabiyoni muje wajen uwargijiyata, wata matace mai saida abinci, nasan bazaka samu matsala ba, inyaso kadan zauna na wani lokaci kafin ka ta samma komawa gida, tunda kaga ga yanayin da ake ciki. Nan nabi wannan bawan allah, ya tara mana adaidaita muka nufi kasuwa, domin dama siyayya zaiyowa ogarsa. Nikam duk da wannan bala'i da nagani, ina nan da kudiri na na SAI NAGA RAHAMA SADAU. A hanyarmu ta zuwa wurin abincin nasu, yake shaidamin sunansa ali, asali shi almajiri ne, tun yana yaro ya 6ige da yiwa wannan mata aiki. Acewarsa yunwa ce tasa shi guduwa da makaranta, kuma an kawo shi tun yana kankani ne, zuwa yanzu malamin nasu ya mace, shekaru 12 da suka gabata, kuma bai san garinsu ba, dan haka uwani mai abinci itace uwarsa da ubansa, dan tai masa abinda iyayen nasa basu masa ba. Acewar sa kenan. "rabe zakaji dadin gurin mu, dan akwai wata kawata a wajen, itama mayyar rahama sadauce, zuwa yanzu sunanta ya tashi daga hanne ya koma SADAU, dan haka zaka samu bayanai da dama awajenta. Alin keta koromin wannan bayani, dai dai lokacin da adai daitan keta tsala gudu, gaskiya wajen nasu da nisa na fada araina. " alokuta da dama nakanji haushin, HANNE SADAU idan naji ta fiye maganar wannan fitsararrar yarinya rahama. Nai murmushi cikin zolaya nace, "ba'a zagin sadau a wajena" yaduben cikin raha yace "SAI KAGA RAHAMA SADAU" murmushi kawai nayi. Wurin abincin nasu wajen garine, rumface sai dakuna langa langa, guda uku. Mai adai dai ta ya sauke mu, gami da dire kayan har harabar wajen, gayyar doyace da shinkafa gami da sauran tarkace. Wata siririyar matashiya na gani, wanda ko kadan bata more mayin bilicin ba, domin ita da taima 6ata mata fuska yai, ta zama 2 kala. Tana zaune tana tsintar wake. Ga iyayen tukwane guda uku a murhu. Wata gajeriya mummuna, mai mici mici idanu, tafi to daga cikin rumfar ta nufomu. "shegen sama ka dawo ne? take fada dai lokacin da ta karaso garemu. "Eh wlh hajiya" aliyu ya bata amsa "ina ka samo wannan dan shilan kuma ? Ko shima ya fito ne ? Matar ta kuma tambayarsa. wannan siririyar matashiyar dubo yadda muke aka ron farko gami da watsamin harara....! ¤¤ page 4 is loading ¤ ¤ journalist din kune. SAI NA GA RAHMA SADAU Na IMAM ABDULLAHI USMAN Gajeren labari Posts by SHURAIH 99% Part 4 . ali ya dubi uwani mai abinci gami da cewa "hajja rahama sadau ya fito nema. Hajja tai wata shu'umar dariya irin tasu, ta gogaggun 'yan duniya tace "da haka muka soma, wai kuturu yaga mai kyasbi. Ta dubeni na dan lokaci tace da aliyu "shegen kai shi da kinka, in mun gama aiki, sai inzo in dora masa karatu" ali ya dubeni gami da cewa "muje ciki" na bishi a baya. Har yanzu wannan siririya mai kama da kilaki tana watsamin harara. Wata macacciyar katifa ce a ya she, cikin dakin sai tabarma guda daya gami da dan tarkace da ba'a rasaba. "nan ne dakina, anan zamu zauna, har zuwa lokacin da zakai gaba" shegen sama ko ince ali ke koromin wannan bayani, bayan mun shige dakin langa langar madaidaici. Na ajiye jakata gefe gami da tsayuwa ina karewa tsohon langa langan idanu. "Ka zauna mana, muryar ali ta katseni, zamanai a kan tabarmar dake yashe. Da karfi aka banko kofar cikin fusata, hajja ce tana huci, ta malmalo ashariya "banason shirme shege, kazo kai aiki, ka wani kule dakin dan uwarka, musamu mu kammala, bayan kasan kwanan zancen. tafada tana zare mici micin idanuwanta, bakinta har kumfa yake tsabar masifa. Shikam shegen sama, tun lokacin da ta soma sirfa masifa jikinsa ke ta rawa. A gaggauce ya fice tabi bayansa. Nai ajiyar zuciya gami da kwantawa kan katifar, sai alokacin na tuna mahaifiyata gwoggo tani, alkah sarki mace mai sanyi maras hayaniya, baki na ta6e gami da runtse idanuwa, bacci yai awon gaba dani. Bansan iya lokacin da na dauka ina bacci ba, na dai farka naga wata madaidaiciyar kula a gabana da ruwan sha a kofi. Wata matashi wanda itama nake kyautata zaton ma'aikaciyar hajjace, ta shiga ba tare da sallama ba. Sai dai ga dukkan alamu tasan yadda ake bilicin tunda ita kam yo kodar da ita, kamar yadda take bida, duk da kasancewar ta kakkaura. "hajja tace kaci abinci, ga ruwansha, zata zo kuy magana. Tana gama fadin hakan ta nufi kofar ficewa, "dan allah ina aliyu ? Na jefe ta da wannan tambayar "wai shegen sama kake tambaya ? Ai ya tafi naiman arziki" matashiyar tace dani, dai dai lokacin da ta isa bakin kofa ? "naiman arziki ? Na tambayeta cikin mamaki ta kalleni gami da yin wani shu'umin murmushi tace "kar ka damu, zaka gane da zarar hajja tazo, ta dora maka karatu" tana gama fadin hakan tai ficewarta. Zulumi tare da juyayi suka ziyarci kwanyata, daga bisani na bude abincin domin ina fada da "yar gusau {tofa katsinawa} shinkafa jalofiya harda namanta tana kamshi. Banyi wasa da abincin nan ba, haka na ringa sanya shi acikina, sai da na koshi. Na kora da ruwa. Na koma na kwanta, inajin hayaniyar mutane a wajen, daga bisani hayaniyar ta dan ragu wajejen mangariba. Hajjo ta shigo dakin wannan karon wani leshine ajikinta, harda "yar kwalliyarta, sai dai abinda na fahimta ga hajjo shine, ita muninta na musamman ne domin da tai kwalliyar maimakon tai kyan gani, a'a sai kwalliyar ta fito mata da asirin siririn kan da ke gareta. Ta karaso ta zauna gefen katifar da nake daf dani, har munajin numfashin juna. Tai ajiyar zuciya gami da cewa, "ka saki jikin ka dan shila, dama irin ku nake nema, kana da kyau ka godewa allah tun daga nan ya baka jari. Abinci muke sai dawa kamar yadda ka gani anan, a kallah munkai mu 13, duk a karkashina suke, ciki kuwa harda mai mana gadin wajen nan, sakamakon da daddare mukam fita naiman abin rufawa juna asiri, kasan dai wannan abincin da muke bazai kwashe mana duk bukatun mu ba, kasan rai da buri muna son tara arziki. Yanzu haka shegen sama {ali} hajiyarsa tazo ta daukeshi, taimin balance idan ya kare kwanaki biyun zatai masa nasa balance din, kayar da ka zauna damu, ka tara arziki, ita da kanta RAHAMA SADAU zata nemeka. Yadda kake da kyan nan, bazan saka a kasuwa ba, zan barwa kaina kai ni zannayima ka balance din, a duk lokacin da kaimin aiki. Hajja ju ta kworo wannan uban bayani gami da mikewa, tai hanyar fita gami da cewa, zumu fita naiman arziki, sai gobe zamu dawo sassafe, kafin nan kai shawara da zuciyarka, duk da nasan bawanda yaki kudi. Tana gama fadin hakan tai ficewarta ta barni a daskare...! ¤ ¤ ¤ part 5 is loading ¤ ¤ina da group a facebook IMAM ABDULLAHI USMAN HAUSA NOVELS GROUP za ku iya yin searching kuy joying, domin kasan cewa da littafaina kala la. Bugu da kari ina da page IMAM ABDULLAHI USMAN tanan zaku iya kasancewa dani kai tsaye duk dai a facebook. Ngd ¤ journalist din kune. SAI NA GA RAHMA SADAU Na IMAM ABDULLAHI USMAN Gajeren labari Posts by SHURAIH 99% Part 5 . nadade azaune ina daskare, duk abin duniya yabi ya sheni, tabbas yau ina ganin ta kaina ya 6arawo a hannun mata. A haka har dare ya tsala, ina nan zaune, daga bisani na mike tseye gami da ficewa daga dakin. Babu kowa a harabar wajen, duk hayanir nan ta shude. Ga uban duhu daya dabai baye wajen. Kukan karnuka na tashi daga wani waje da bansan ko ina ne ba. "Bako ka fito kenan" aka ce dani da wata iriyar murya. Na waiga kusurwar da najiyo muryar, zaune akan benci yana rike da sigari yana karawa sama hazo. Duk da duhun daren bai hanani ganin saba. "haba dai kar dai tsoro kaji ? Nine megadin wajen nan. Yace dani, dai dai lokacinda na nuna alamar tsoro. Na karasa wajensa gami da zama akan bencin. Sai da yagama zuke sigarin ya kashe wutar gami da cewa,"Bawan allah, kai kuma wacce kaddarar ce ta jefoka karkashin Hajjaju mai abun dadi ? Kalaman nasa suka doki zuciyata na gyara zama, gami da fuskantar sa nace "banda amsar tambayarka! Yayi jim daga bisani yace "ga dai alamun ka kamar ba ficacceba, bawan allah idan kasan kai ba tayar gaban keke bane ka gaggauta nisantar wajen nan" na jingina da jikin langa langa gami da cewa "meye kuma tayar gaban keke ? Mutumin da nake kyautata zaton zai kai shekaru 30 ya sheke da dariya, gami da cewa, "kana nufin bakasan wannan jaririn yaren ba ? Na dirice na nuna masa kauyan cina a fili. Shiko ya karkace yake ta shekamin jawabi, ban boye masa maganganun da hajjaju ta fadamin ba, anan ya warwaremin zare da abawa. Ashe alin da ya kawoni nan din shima gogeggen dan duniyane, fasikanci ba irin wanda ba yayi da sunan naima arziki. Ita kuwa hajjo karamin aikin ta shine karuwanci, acewar sa takan dauko yara 'yan sha 17,18 zuwa 20 tana lalata dasu, abar batun sauran matan dake gabanta wadanda sukan idan kaso musu adalci shine ka kirasu da karuwai. "kaga bawan allah idan dai kasan kai ba na banza bane, yan zun nan ka dauko jakar ka, in nuna maka hanya, wlh banda yau hajiya tayi kamu ba, da i yanzu kuna chan tana fadama mecece duniyar." mai gadin ya karkare surutansa da bani wannan shawarar. Cikin mintuna 2 naje na dauko jakata, naiwa dakin kallon karshe, na nufo wajensa. Mikewa yai gami da haska fitilar da ke hannunsa yace muje zuwa. Yai min rakiya mai nisa, daga bisani muka soma hangowa hasken gari, yaja tun ga ya tsaya, ya sanya hannu a aljihu gami mikomin kudi yace "gashi dubu biyu ce, nasan zata isheka komawa garinku, bawan allah ka koma ga iyayenka ka naimi gafararsu karabu da batun wata 'yar wasan hausa." na kar6a gami da yi masa godiya, mukai bankwana, na kutsa kai birnin kano. Abakin titi na kwana, washe gari na shiga tambayar ina zanga RAHAMA SADAU ?, kai gaskiya ranar naga wulakanci da yawa, wasu mahaukaci suka daukeni. Sai daga karshe wani yake sanar dani cewa rahaman 'yar kuduna ce, dan haka kadunan zan nufu, a cewarsa ba abun da ke kawota kano face aiki. Nai masa godiya gami da daura aniyar tafiya kaduna. Tuni na samu mota, duk da dare ya soma yi, motarmu ta wulwula hanyar kaduna. Naga saurin isarmu, direba ya watsar da mu a tasha nasoma naiman hawajen kwana domin na kudurta araina cewar gobe SAI NAGA RAHAMA SADAU. Tunda gani a kd arumfar wani maishayi naji wasu matasa suna maganar shahararre wajen kwalliyar mata da rahama sadau ta 6ude. Faduwa tazo dai dai da zama kenan, tabbas idan naje shagonta nasan samunta abune mai sauki. Nai murmushin nasara gami da ajiyar zuciya.........! ¤¤ *¤ . . Last page is loading .¤ . ¤ journalist din kune. SAI NA GA RAHMA SADAU Na IMAM ABDULLAHI USMAN Gajeren labari Posts by SHURAIH 99% Part 6 KARSHE . A bakin titi na kwana, aranar, washe gari kuwa, naci gaba da sana'ata. Wato tambaya, sai dai tambayar ta yau ta bambamta da wacce nake a baya. Tunda da tambaya nake ina zanga RAHAMA SADAU ? Yan zu kuwa kai tsaye, nake tambayar jama'a dan allah inane SADAU BEAUTY ? Hakan ma na jima ina tambaya bansamu kwakkwarar amsa ba, kai kace ba'a kadunan nake ba. Cikin tambaye tambayen nawa ne, na tambayi wata matashi "yar kwalisa. Kai da ganinta kaga "yar swag. Gaskiya imam nayi mamakin saukin kanta, dan cewa tai dani "gaskiya shagon ba'a unguwar nan yake ba, sai dai kuma yanzu hakama chan zani. Idan ba damuwa muje in sau keka sai na nu na maka wajen. Cikin azar6a6i na amince, sai dai nayi mamakin nisan wajen, sai da mukaje kusa da wajen wurin sannan ta nunamin shagon gami da ajiyeni. Gadiya nai. Ta karamin jawabi da cewar kaga yau asabat tana nan ma, insha allahu zaka sameta. Bakina cike da azar6a6i na nufi hanya domin tsallakawa nai arba da rahama sadau. Imam naga kaddara ko ince alhakin iyayena dana taho na baro. Na dubi rabe gami da cewa mai yafaru ? Rabe ya gyara zama gami da cewa "ai mota ce taimin diban karan mahaukaciya daga nan bansan inda nake ba" sai budan idanu nai na ganni a garin mu, cikin gidanmu. Na dubi rabe cikin rashin yarda nace kamar yaya ? Yace "cikin hikimar ubangiji ashe lokacin da lamarin ya faru akwai idon sani wato dan garinmu, shi yaiwa na allah jagora suka dawo dani har gida. Na roki gafarar iyayena. Nai zaman jinyar karayar da nai a hannu da kafa. Bayan nasamu saukine na soma daukar karatun addini awajen wani malami. Imam a yanzu nayiwa kaina karatun ta nutsu, ina zaune zaman mutumci da iyaye. Kaji lbrn da nake dauke dashi. Rabe yace dani. Nai jigum ina nazarin wannan labari. ** Alhamdullah ** karshe ** ngd fans ** Imam Abdullahi Usman An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin

Chapter 1 of 2