Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 1
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels SADAUKI SAIFUL MAUT MAI TAKOBIN GASKIYA: Part 1: A wani zamani ne wanda ya shude a cikin birnin kisra an yi wani azzalumin sarki mai suna Jawat ibn Kafir shi dai wannan sarki Allah ya bashi karfin damtse da karfin tsafi da mayaka na ban tsoro dan kuwa kumin girman gari idan ya tura mayakan sa to fa yan garin sun shiga balai da kuma son mata ko yar wacece in dai ya hada ido da ita to fa sai ya hada kwanciya da ita a haka sai da ya tara mata wajen tamanin da biyar kuma duk basu taba haihuwa ba saboda kafin ya kwanta da mece sai yayi anfani da tsafin sa yayi toshe mahaifarta toh a kusada garin akwai wani karamin kauye mai suna Birnin Islama toh yan garin kuwa musulmai ne fatake ne masu tafiye tafiye toh su kuwa suna tafiyane da aladar Musulunci suna da wani adalin sarki mai suna Maut ibn Salim shi dai sarki salim Allah yayi masa albarka da yaya biyu mace da namiji, masu harshashe kuwa sun ce a wannan zamani ba wanda yakai su kyau ballatana ita macen mai suna Lasmina, shi kuwa namijin Allah ya bashi jarumtaka da sa a don kuwa ba abin da yasa a gaba idan yace sai yayi to kuwa ba wanda ya isa ya tsai dashi don kuwa tun yana yaro yake yin abubuwan alajabi don da akwai lokacin da ya tafi dajin da akeyiwa lakabi da kauful jat a tarihin dajin nan ba wanda yake shiga dajin nan ya fito lafiya amma shi kadai ya shiga da zuwa kuwa sai ya fara ganin abubuwan ban tsoro amma ko gezau baiyi ba ya cikin dajin wajen dakika ashirin sannan yaga wani babban zaki ya durfafo wajensa maimakon ya gudu amma sai ya fara shirin fada shi kanshi zakin yasan cewa ya gamu da gomonsa ai kuwa sai zakin ya tahu a guje kamar mayun waci yana zuwa kusa da shi sai ya daka tsalle shi ko Saiful maut bai ko matsa ba zakin na zuwa suka fara kokawa da yakushi har wajen dakika talatin sai gashi saiful maut ya kashe zakin da karfin damtse kawai sannan yakai cikin gari totun daga ranar mutane suka fara jinjina masa zamu cigaba idan munga likes da comments dinku to muna jira SADAUKI SAIFUL MAUT MAI TAKOBIN GASKIYA PART: TWO A kasar sarki Jawat kuwa yana zaune a dakin tsafinsa a gaban madubin tsafinsa inda yake binciko kyawawon mata na duniya wanda zai tura mayakansa su dauko ta koda da karfin yaki ne ko tsafi yana nan dai a zaune akan wani turmin tsagi wanda aka rufe da wani jan yadi a tarihi ance ba wanda y taba shiga cikin dakin tsafin ya fito da rai saboda irin hatsatsubin da suke cikin sa shi ko sarki jawat yana ta kallon hotunan yan matan kawai sai ya hango wani hoton wata kyakkyawar mace wanda tunda yake duniya bai taba ganin kyakkyawa kamar ta ba sai yayi binciken wacece budurwar da kuma garin da take ai kuwa yana dubawa yaga ai yar sarkin garin Islama ne kawai sai ya fara dariyar mugunta dan kuwa shaawarta yake tun bai ganta ba kawai sai ya tura wani aljanun sa ya kira wazirinsa mai suna kafaru a lokacin da wazirin yazo sai ya rusuna ya kwashi gaisuwa yace a mai duniya naga ka turo a kira ni lafiya kuwa sai sarki ya numfasa yanuna masa hoto gimbiya Lasmina aikuwa da waziri yaga hoto gimbiya lasmina sai da ya kusa zautuwa amma sai kawai ya share yace ya mai duniya yanzu kana son inje garin Islam in tambayo ma hannun gimbiya lasmina ka aure ta sai kuwa sarki jawat ya dinka dariya kamar bazai daina ba amma sai kawai ya tsuke baki yace ina son yanzu ka dauki dukiya mai yawa ka kai wa sarki maut kuma ka gabatar da bukata ta agareshi waziri yace angama ya mai duniya sannan ya tashi ya tafi baitul mali don a hada dukiyar da sarki yace. Acan garin islama kuwa ana ta fadanci sai kawai aka ga su waziri kafaru sun shigo da kayyayaki akan rakuma sai suka shigo cikin fada zasu rusuna amma sai sarki maut ya dakatar dasu yace ai ba wanda ake rusunawa sai Allahu wanda ya halicci sammai da kassai shi kuwa waziri ko damuwa baiyi ba sai yace yakai sarki maut kasani cewa sarkin mune ya aiko mu dan mu fada maka cewa yana son yarka gimbiya lasmina da aure tun kafin ya gama maganarsa Sadauki Saiful ya tari numfashi sa yace ai bazai taba yiyuwa ba dan ruwa da wuta basa zama waje daya ku fada wa sarkin ku haka mu bamu da lokaci da zamu bata akan ku dan zamu je mu bautawa ubangijin mune idan kun gadama ku tafi idan kuma kun gadama ku tsaya sai sarki maut yace ga sakona ga sarkin ku kuce masa bazai yu ba GASKIYA PART: 3 Alokacin da waziri kafaru yaga irin wulakancin da sarki maut yayi musu shi da dansa sai ya ji wani mugun haushi sannan ya cewa dakarun da yazo dasu cewa su tafi a lokacin da ya isa birnin kisra sai ya huce fada wajen sarki domin ya isar da sakon da ya karbo daga garin islama alokacin da ya isa wajen sarki sai ya kwashi gaisuwa yace ya mai duniya ai tun danake a duniyar nan bantaba ganin wulakanci irin wannan ba sai ya kwashi labarin abunda yafaru ya fada ma sarki, kawai sai sarki ya takarkare ya ringa dariyu wanda ya bawa waziri matukar mamaki sai kuwa ya tsuke baki yace yanzu anan duniyar da akwai garin da zan tura ince ina son abu amma maimakon abani sai a wulakanta ni toh kuwa garin islama sun shiga bala in da basu taba koda tunanin sa ba yakai waziri yanzu ka tura a kira min sarkin yaki don a gobe nake son in gama da garin islama alokacin da sarkin yaki yazo sai ya kwashi gaisuwa sarki jawat yace ina son ka tara min dakaru kamar dubu daya gobe da safe don ina son kashe duk wani abu mai rai kuma in baje garin islama sai sarkin yaki yace angama ya mai duniya sannan ya tafi ya bar sarki da waziri suka cigaba da tattauna yanda zasu bullo wa alamarin gobe. Da gari ya waye sai ga dakaru nan a cikin sulken yaki na ban tsoro don idan ka dansu kuwa to dole ne kasan cewa wannan su ake kira da bala i sai ga sarki nan ya fito daga cikin fadarsa da shigar yaki wanda baitaba yi ba kai idan wani raggon yaga wannan shiga ta sarki jawat to gaskiya zai iya mutuwa yana zaune ne akan tabarmar tsafi wanda yake yawo akan iska yace yaku dakarun masifa da bala i to yau ina son ku sani cewa wannan yakin ba zamu tausayawa kowa ba kisa ne kawai amma ina son akama mun gimbiya lasmina a raye don itace makasudin wannan yaki sai dakarun su kace an gama ya mai duniya sannan suka fuskanci kofar fita daga birnin suka nausa hanyar birnin islama. Acan birnin islama kuwa sadauki saiful da ya dawo daga masallaci sai ya tafi turakar mahaifansa yayi gaishe dasu sannan yace wa abbansa wato sarki maut cewa shi zai tafi farauta suka sa masa albarka da kuma adduar sa a sannan ya tafi dakin kanwarsa wato gimbiya lasmina suka gaisa take cewa ya samo mata inibi nunanne yace toh sannan yafi to cikin bargar dawakin ya hau dokinsa sannan ya nausa cikin daji abinda bai sani ba kuwa shine bazai kara ganin garin ba alamarin su sarki jawat kuwa sai gudu suke har dai suka karasa garin wajen sallar azahar suna zuwa suka afka su fara # sara da # suka suna kona gidaje suka kashe kuwa abirnin har cikin fadar sarki maut suka shiga suka kama shi da matar sa da gimbiya anan take sarki ya fille kan sarki maut sannan ya fille na mahaifiyar su sadauki saiful aka saka gimbiya akan doki sannan suka tafi suka bar birnin wanda aka baje shi. Shi kuwa saduaki saiful yana ta farauta har ya fara shirya taho wa gida sannan yatuna da inibin da kanwarsa wato gimbiya tace ya samo mata yana tafiyane ya hango bishiyar aiko bai bata lokaci ba ya tsinko mai yawa ya taho dashi gida tundaga nesa ya fara hango wani irin hayaki ya turnike a sararin samaniya sai ya kara gudun dokinsa domin yaga mai ya faru. zamu cigaba SADAUKI SAIFUL MAUT MAI TAKOBIN GASKIYA PART: FOUR Alokacin da sadauki saiful ya iso cikin garin su yaga irin barnar da aka musu da kisa sai kawai ya nufi fadar abban sa ai kuwa yana zuwa yaga gawarwaki a ko ina burjuk yana shiga kawai sai ya yi arba da gawar mahaifinsa da na mahaifiyarsa amma kuma babu kawuna atare da gangar jikin su kawai sai ya tsuguna ya fara zubar da wasu zafafan hawaye wanda tun lokacin da aka haife shi bai taba zubarda hawaye ba sai yau sai ya nemu ruwa mai tsarki yayi musu wanka yanda musulunci ya koyar damu ya sallace su sannan ya binne su yana mai yin kuka da bakin cikin abubuwan da suka faru alokacin da bayanan ya dau lokuta kamar sa a daya asannan ne kanwarsa ta fado mai a rai yayi ta duba wa bai ganta ba yana cikin duba wa sai yaga wani farin haske wanda tun da aka haife shi baitaba ganin haske kamar sa ba hasken ya tunkare shi kamar zai bankade shi sai ya sare takobinsa daga cikin gidan ta yana dube duben ta inda abin zai kawo masa farmaki amma maimakon a kawo masa hari sai yaji wani murya mai zaki tayi masa salama ya amsa sai wata farar aljana ce ta baiyana a gaban sa tana mai wani irin murmushi tace yakai saiful dan marigayi maut kasani cewa ni aljana ce kuma musulma mahaifina ya kasance sarkin garin mu mahaifina yana da adalci amma yana da wani waziri wanda yake zalunci don kuwa a duk cikin aljanun garin mu suna jin tsoron sa in bada mahaifina toh shi dai wazirin mahaifina kuwa ya kasance yana musulunci ne a fuska amma wani gagarumin boka ne toh wata rana muna zaune ni da mahaifiyata sai muka ga mahaifina ya shigo a guje yace mu hada yan kayyayakin mu mu gudu wai wazirinsa ya hada mayaka don su karbe sarautar sa kuma su mayar da garin mahaifina garin bautar gumakai muna cikin hada kayan mu ne sai muka ji an bankado kofar turakar mahaifina in taikaice maka labari yakai saiful maut agabana wazirin mahaifina ya kashe mahaifana a gabana wanda har yanzu na kanji bakin cikin rasuwar iyayena amma ba abinda zan iya yi don sau wajen goma ina zuwa gidan wazirin maihaifina don in dau fansa amma na kasa daukar fansa ba dan komai ba don duk kayan yakin da za amfani dashi bazai taba tasiri a jikinsa ba to shi to alamarin iyayenka kuwa ba kuwa bane ya kashe su in b sai sarki jawat na birnin kisra don kawai ya nemi hannun kanwarka wato gimbiya lasmina don ya aura amma kuka ki amsa masa to shine ya taso da kansa don ya hukunta ku toh abinda yasa na kawo maka dauki don kuwa yanzu wazirin mahaifina da sarki jawat sun hada karfi da karfe don su mai da kuwa da kuwa bautar gumakai a yanzu dai acan birnin kisra kuwa ana ta shirye shiryen bikin sarki jawat da kanwarka lasmina Toh acan birnin kisra kuwa sarki jawat yana isa cikin fada yasa aka soke kawunan iyayen sadauki saiful a kofar shiga gari ta yanda idai zaka shiga sai ka gani sannan kuma yasa akayi shela cewa za a daura masa aure da gimbiya lasmina a kwanaki goma masu zuwa SADAUKI SAIFUL MAUT MAI TAKOBIN GASKIYA PART:5 A bangaren saiful kuwa shi da bakuwar aljana kuwa sun na ta daukar gawarwakin wadanda aka kashe suna binnewa da suka gama ne sannan ta gabatar da kanta cewa ya kai sadauki saiful ni dai sunana jazwariya yanzu ina son kayi sani cewa akwai wani takobi wanda zai iya tasiri akan kowani tsafi sai sadauki saiful ua dube ta yace yake jazwariya shin kina cewa da akwai takobin da zai yi tarihi a jikin sarki jawat da wazirin mahaifinki aljana jazwariya tace kwarai kuwa don kuwa takobin yana nan a wani tsibiri mai suna liswar wanda daga nan zuwa can tafiyar kwana goma ne anan sadauki saiful yace to yanzu ya zamu yi don kuwa a kwana goman za a daura auren kanwata da sarki jawat ai kuwa in dai haka ne ba mu samu ta zama ba don akwai babban aiki a gaba mu yanzu kuwa zamu kama hanya ko jazwariya tace kwarai kuma anan suka kama hanya zuwa tsibirin liswar wanda yan tarihi sun ce ba wanda ya ke shiga dajin da tsibirin yake ya fito lafiya ballatana ka kai ga hawa tsibirin komin tsafin ka ko kuma juriyarka da kuma karfin damtsenka sai ka gaji ko aljanu ma suna shakkar wannan tsibirin don kuwa idan sun kusanto wannan tsibirin sai kaga sun fara kururuwa badon komai ba sai don fatar jikinsu ne zai dinga zangwayewa yana narkewa kamar yanda karfe yake narkuwa acikin gagarumin wuta ahaka su sadauki suka kama hanya wanda shi sadauki ya kama dokinsa ya hau ita kuwa aljana jazwariya ta kada fukafukanta sai kace tsuntsuwa ahaka suka rinka tafiya hankalin su a kwance abinda basu sani ba kuwa shi ne boka zamir yana kollonsu ta cikin madubin tsafinsa sai ya wani kece da wata mahaukaciyar dariya wanda yasa duk cikin kogon tsafisa ya fara girgiza kamar zai rugurguje sannan ya tsuke bakin sa ya daina dariya sannan ya bace daga kogon tsafinsa wanda yake cikin wani tsafafen daji wanda ba kowa yake samun ganin wajen ba sai dai fa indai boka zamir yace kazo to shine zaka samu damar ganin wajen alamarin sarki jawat kuwa birnin kisra ya fara cika da mutane da kuwanne bangare na duniya duk inda ka duba mutane ne burjik duk wani masauki ya cika har tantuna ake kafa wa domin mutane su samu wurin kwana mawaka da maroka kuwa ba a bar su a baya ba kuwa don ko barci basa yi amma fa sun samu kyaututtuka da dama don wani sarki ma idan wani mawaki ko maroki ya yi masa kirari sai kaga kawai ya bada umarni a bashi dukiya wanda daga shi har tataba kunnansa basu isa su karar da dukiyarnan ba shi kuwa sarki jawat gaba dayan hankalinsa yana wajen tunanin daurin auren sa da za a yi nan da yan kwanaki shi dai gani yake kwanaki goman da yace yayi yawa yana zaune a cikin turakarsa sai ya tuna cewa fa bai ko ga gimbiya lasmina ba aranar ya mike ya nufi dakin da yasa aka kulle ta aciki yana zuwa ya bude ya shiga ya tarar da gimbiya lasmina a zaune tana ta faman zubarda hawayen bakin cikin rashin iyayenta da tayi kuma gashi bata ko kara jin duriyar yayanta ba sarki jawat ya kusanto ta yana mai cewa yake masoyiyata kiyi sani cewa kin riga da kin zama tawa ba wanda ya isa ya shigo cikin fadar nan da nufin ya kubutar dake yana cikin yin magana yaji an kwankwasa kofar dakin sai ya juya ya fita yana fita kuwa ya ga boka zamir suka gaisa anan fa boka zamir ya fada masa abubuwan da suka gudana tsakanin sadauki saiful maut da kuma aljana jazwairya sai sarki jawat yace bari in turo mayakana kamar dabu daya su kashe min wannan yaron Shin su sadauki saiful maut da aljana jazwariya zasu samu damar dauko takobin gaskiya? Sarki jawat zai samu damar kusantar gimbiya lasmina kuwa? To domin sanin amsar tambayoyin nan to zamu cigiba insha Allah sadauki saiful Maut mai Takobin Gaskiya PART: 6 Alamarin su sadauki saiful maut shida aljana jazwariya kuwa tun lokacin da suka fara tafiya basa ko tsayawa sai dai in lokacin sallah yayi sai su dan tsaya su yada zango sannan su gabatar da sallah idan sun gama shi sadauki saiful sai ya mike ya je ya farauto abinda zai sa a bakinsa don ita aljana jazwariya bata cin komai sai dai ta rinka salati da addu oi a haka suka rinka tafiya na wajen kwana biyu a cikin kwana goma kafin a daura aure sarki jazat da gimbiya lasmina a bangaren su sarki jawat kuwa gashi saura kwana takwas washe garin ranar da sarki da boka jazwir suka gana kuwa da dukudukun safiya sarki jawat yasa aka kira masa sarkin yakinsa yana zuwa ya kwashi gaisuwa yace ya mai duniya gani nan nazo daga jin sakon ka sarki jawat yace ina son ka hadu rundunar mayaka guda dari wadanda suke ji da kansu a jarumtaka ina sun kabi bayan wannan yaron nan mai suna sadauki saiful da sarki maut wanda kanwarsa take wajen ina ku riskesa kafin ya isa kan tsibirin lazmir domin yana son dauko takobin gaskiya domin ya kawatar dani da babban abokina boka jazwir sarkin yaki yace toh mai duniya ina so ka kwantar da hankalinka domin zan kawo maka kan sadauki saiful ibn maut sarki yace kwarai kuwa na gamsu da bayaninka yakai sarkin yakina amma ina son karka kashe shi ina son ka kamo minshi a raye domin yaga yanda za a daura min aure da kanwarsa kwana takwas masu zuwa da yarda ubangiji na zalzulu ko bata lokaci baiyi ba ya fita ya fara hada jarumai wadanda idan suka tunkare kowanne gari toh kuwa garin yasha bala i kai harta tsofafin harda yara kashewa suke alokacin da sarkin yaki ya gama tarasu sai yace sarki yace mu tunkari tsibirin lasmir domin mu kamo sadaki saiful maut a raye ko a macce sai suka amsa da toh sannan kowa ya kama dokinsa suka fara tafiya wanda idan kagansu sai ka tsorata da shigarsu Alamarin su sadauki saiful kuwa suna cigaba da tafiya basu hadu da kowa ba har a lokacin sannan suka cigaba da tafiya da lokacin sallah yayi sai suka yada zango domin suyi sallah sun gama sallah kenan sai sadauki saiful ya dan kinshigida domin yandan huta sun da zauna bai kai ko rabin sa a ba suka fara jin sahun dokuna masu yawa sun tunkaru inda suke kawai sai sadauki saiful ya mike a guje domin ya tsaya cikin shiri bakowa bane suka tunjaro wajen nan in banda su sarkin yaki garin kisra ita kuwa aljana jazwariya tana zaune akan bushiya don bata da karfin damtse ballatana ta taimaki sadauki saiful maut suna karasowa su ka sauko daga kan dawakansu domin su yi wa sadauki saiful kwab daya abinda basu sani ba cewa shi kuwa sadauki ya riga da yayi lissafin yanda zai girbi rayukansu aikuwa ko wani bata lokaci basu yi ba jarumai masu ji da kansu guda goma suka zabura suka ruga a guje suka yo kansa SHIN SU SARKIN YAKI ZASU SAMU GALABA AKAN SADAUKI SAIFUL domin sanin wannan amsa sai a biyo ni sai anjima An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 1 of 1