An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
[10/8, 7:31 PM] Sarauniya: 💉💊💉GWAJI KAFIN AURE💉💊💉
(TEST)
GAJEREN LABARI
LABARI DA RUBUTAWA
ZAINAB SALIHU YAREEMA
(SARAUNIYAR KANAWA)
*AREWA WRITTERS ASSOCIATION*
*SADAUKARWA*
Na sadaukar da wannan Novel ga duk wani mai fama da cutar Sikila Mace ko Namiji, Allah ya albarkaci Rayuwar ku ya sa ku rabauta da gidajen Aljanna, ya yaye muku damuwar ku, ya sassauta muku ciwon ku😥😥. wannan Novel ɗin naku ne kuyi yadda kuke so.
*YABO DA JINJINAR BAN GIRMA GAREKA*
ALIYU UMAR GUMEL
Ina matuƙar godiya Allah ya biyaka da gidan Aljanna.🙏
*JINJINA DA FATAN ALHERI.*
HUSSAINI M YERO
Yaya na Abun alfahari na kai ɗin mutum ne na gari, nagode da ƙwarin gwiwar da ka bani gurin Rbuta wannan labari
*Soyayya babu haɗi a ciki*
My rigimammiyar masoyiya
*Xayyeesherthul-humaerath*
Son so nake miki.
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
SHAFI NA FARKO
"Wayyo Allah na ku ciremun kafar nan Umma, Hannuna kamar ana dandatsamun shi kai na kamar zai cire, wai yaushe zan dai na jin ciwon nan,? ya Allah ka ɗauki rai na in huta."
"Haba Zainaba mai yasa kike faɗin haka ne Cuta ba Mutuwa bace fa, Addu'a ya kamata ki dinga yi ba kuka."
Cewar Mahaifiyar da take zaune a gefen ta ta riƙe mata Hannu tana tofa mata addu'a, Hawaye na tsiyaya a Idanuwar ta.
"ya Allah kaga Halin da wannan Baiwar taka take ciki, Allah ka sassauta mata, Allah ya kawo mana iyakan wannan Cuta, Allah ka yafemun tabbas ni na biye ma son Zuciya na ja ma ƴa ta faɗawa cikin wannan halin."
Yanda suka ga Rana haka suka ga dare ranar basuyi barci ba, Safe nayi Mahaifiyar ta ta shirya ƴarinyar suka nufi Asibiti.
*************************
Wacece Zainab.?
Asalin su yan garin Kaduna ne, Sunan Mahaifin ta Lawal, Sunan Mahaifiyar ta Halima.
Sunyi Aure ne irin Auren Soyayya, in da gaba ɗaya Idon su ya rufe sun kasa gane Illar da iyayen su da dangi suke ta hango musu, lokacin da sukaje sukayi Test domin tantance lafiyar su Likitocin sun tabbatar musu da cewa ba zasu iya Auren Junan su ba kasancewar Genotype nasu yazo ɗaya, (Insha Allah bayanin hakan zai zo a shafi na gaba) Amma suka rufe ido suka kulle kunnin su sukace sai sunyi Aure bazasu taba iya rabuwa da juna ba, haka iyayen suka samusu ido sukayi Aure a haka.
Bayan Auren su da wata ɗaya Halima ta samu ciki mai shegen laulayi, sosai take shan Wahala, bayan cikin ya kai Wata tara ta fara Naƙuda, haka Lawal ya ɗauke ta sai Asibiti, sai da ta kwana ta yini ta haihu ta haifi sankacecen yaron ta sak mahaifin shi, Murna a gurin Lawal da Halima baya misiltuwa, nan da nan dangin suka cika Asibiti ana taya su Murna, bayan kwana ɗaya aka sallamo mai jego da ɗan ta, iya kulawa Halima na samu a gurin uwar mijin ta da iyayen ta da Mijin ta, da ranar Suna yazo yaro ya ci Suna Munir, anyi suna na gani na faɗa, haka har suka gama wanka suka fara zagaya ƴan Uwa da abokan Arziki.
Bayan Wata uku da Haihuwar Munir ya fara wani ciwo, nan da nan sai idon shi ya kakkafe, ga hannuwar shi sun kunbura da kafafuwa in ya fara kuka tun dare har safe basuyi Barci ba, gari na wayewa suka nufi Asibiti hankali tashe, suna zuwa suka ga likita ya tabbatar musu da yaron su yana ɗauke da ciwon Sikila, hankalin su yayi matuƙar tashi likita ya ƙara da cewa kuma yaron nasu na buƙatar ƙarin jini.
Bayan sati biyu Munir yace ga garin ku ne, Sosai mutuwar ya girgizasu.
Sai da Halima ta haihu sau biyar suna Rasuwa, har Lawal ya fara juya ma Halima baya ya fara mata Wulaƙanci, ko magana bai cika shiga tsakanin su ba, in tayi magana ya hau ta da Masifa, kwatsam sai gashi ta samu wani cikin, nan Lawal yayi tsalle ya dire yace sai an zubar da cikin, don shi ya gaji da wahala da ƴaƴan da ba zama suke yi ba, ita kuma tace wallahi ba zata zubar da cikin ta ba tana son abun ta, shine yace ba Abun da ya shafeshi da Abun da zata haifa tace eh taji ta Amince.
Shine aka Haifi Zainab tunda aka Haifeta Mahaifinta bai taɓa ɗaukan ta ba, ko kallan inda take ma bai yi ko ciwon ta ya tashi ta fara kuka cikin dare tashi yake ya koma falo ya barsu, gashi yau shekarar ta goma Sha uku Amma dai dai da rana ɗaya bai taɓa kula yarinyar ba, Asali ma yanzu shirin Aure yakeyi.
Sai yanzu Halima take dana sanin biye ma son zuciya da tayi gashi taga abun da ƴan uwan ta suke faɗa mata, sosai Lawal ke wulaƙan ta ta tayi kuka yafi a ƙirga.✍️✍️✍️✍️
SARAUNIYAR KANAWA👸
DON ALLAH KUYI SHARE SABODA AKWAI DARASIN DA NAKE SON ISARWA🙏🙏🙏
COMMENT🥰🥰🥰
[10/8, 7:31 PM] Sarauniya: 💉💊💉GWAJI KAFIN AURE💉💊💉
(TEST)
GAJEREN LABARI
LABARI DA RUBUTAWA
ZAINAB SALIHU YAREEMA
(SARAUNIYAR KANAWA)
*AREWA WRITTERS ASSOCIATION*
*SADAUKARWA*
Na sadaukar da wannan Novel ga duk wani mai fama da cutar Sikila Mace ko Namiji, Allah ya albarkaci Rayuwar ku ya sa ku rabauta da gidajen Aljanna, ya yaye muku damuwar ku, ya sassauta muku ciwon ku😥😥. wannan Novel ɗin naku ne kuyi yadda kuke so.
*YABO DA JINJINAR BAN GIRMA GAREKA*
_ALIYU UMAR GUMEL_
_Ina matuƙar godiya Allah ya biyaka da gidan Aljanna.🙏_
*JINJINA DA FATAN ALHERI*
_HUSSAINI M YERO_
_Yaya na Abun alfahari na kai ɗin mutum ne na gari, nagode da gwarin_ _gwiwar da ka bani gurin Rbuta wannan labari._
Soyayya babu haɗi a ciki
My rigimammiyar masoyiya
*Xayyeesherthul-humaerath*
Son so nake miki.
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
SHAFI NA BIYU
KUMA NA ƘARSHE
"Tabbas Hajiya kunyi kuskure babba, saboda kunyi Test ɗin nan kunga cewa kwayar hallitar ku iri ɗaya ne tana ɗauke da kwayar cutar Sikila sannan kuka biye ma son Zuciya ku ka cutar da ƴar ku gashinan tana wahala, ko shin likitar bai muku bayanin mecece cutar Sikila ba,? to bari in miki bayani dalla-dallah yan da zaki gane."
*CUTAR SIKILA*
Cuta ce ta gado wanda yake shafar jini. Kafun mu fahimce ta yadda ya kamata muna buƙatar musan menene Jini da abubuwan da ke cikin sa da anfanin sa a jiki.
*JINI*
Akwai kwayoyin hallita kala-kala da ke cikin jini, irin su jar-kwayar jini(erythrocytes), sai kwayoyin sojojin jini wato(lymphocyte), sai kwayoyin dakon sinadarai(plasma), sai kwayoyin daskararwa wato (platelets), sai kwayar bayar da umarni wato (hormones), sai ruwa da sauransu. kowanne a cikin ababen da na lissafo akwai irin aikin da yake yiwa jiki.
*jajayen kwayoyin jini*:- wasu jajayen kwayoyin jini ne zagayayyu masu ɗan faɗi kamar faifai sai dai suna da ɗan tudu kamar taya sun ɗan lotsa daga tsakiya. Suna da yawa matuƙa a jini, linkin ba linkin ɗin sauran kwayoyin dake cikin jinin shiyasa jini yake da launin *Ja* kamar Zoɓo. jar-kwayar jini cike take da wani ruwan sinadari ana ce masa (haemoglobin) shi da iska kamar mayen karfe suke.
*ƁARGO*:- Shine yake samar da duk wata jar-kwayar jini a jiki.
Anfanin jar-kwayar jini shine ɗaukar iskar da muke shaƙa daga Hunhunmu ya rarrabata zuwa ga kwayoyin Hallitu jiki, da kuma ɗaukar wanda kwayoyin jiki suka gama Anfani da ita su maidota Hunhu, shi kuma Hunhu ya furzar da ita waje.
Karku manta kwayoyin halittar jiki suna buƙatar iska fiye da komai domin su rayu.
Don haka akwai matsala gagaruma a yayin da aka samu yankewar iska, domin waɗan nan kwayoyi zasu gagara sauke nauyin dake kansu.
*Sickle cells*:- Sune Nakasassun kwayoyin jan jini, suffarsu ta banbamta da yadda lafiyayyun suke, su zaka gansu kamar lauje ko *'C*' irin waɗan nan bazasu iya anfanin komai ba, wasu kuma sukanyi kaɗan mafi yawansu in suka shiga Hunhu bazasu iya ɗauko komai ba sai dai su shiga su fito.
Kamar fasasshiyar guga ce ka tsomata a rijiya haka zaka fito da ita bata janyo komai ba, to haka misalin nakasassun kwayoyin halittar masu fama da sikila take.
Sannan nakasassun kwayoyin suna mutuwa da wuri fiye da lafiyayyun, shiyasa masu sikila suke da yawan matsalar karancin Jini.
Mai sikila da yawa kwayoyin jinin su Nakasassu ne basa iya aikin komai, hakan yasa kwayoyin Halittar su jikin su suke matuƙar galabaita saboda karancin iska, kasancewar waɗanda yake da su da yawa basu da anfani, basa aiki yadda ya kamata.
*Sickle cells crisis*:- A yayin da waɗan nan nakasassun kwayoyin jini suka sarkafu da juna kasancewar su kamar lauje, da sunyi yawa sun cushe guri ɗaya har ta kai ga sunyi dunkulewar da zasu toshe jijiyar da suke cikin ta hakan yakan haddasawa mare lafiyar jin tsananin ciwo a dai dai in da aka samu toshewar a jikinsa, wani karan abun yakanyi tsananin da da har ya kai mare lafiyar ya fita hayyacin sa, har wani sashi na jikin sa zakiga yana kumbura, ko wata gaba ta maƙale taki motsi, wannan shine matsala mafi wahalarwa ga mai sikila, sai dai ciwon mataki-mataki ne akwai mai tsanani akwai mai sauki.
*Alamomin Sikila*
Yawan ciwon jiki, yawan jin raɗaɗi cikin Ƙasusuwa zaiji kamar an sa mai zarto ana dandaƙa ƙashin, wani karon riƙewar gaɓoɓi, rashin girman yaro, zakaga yaro ya ƙanƙance baya girma kwata-kwata, yawan kunburin ciki, akwai wata Hallita a cikin mutum ana ce mata Saifa wato (spleen), takan kumbura, shine zaka ga dunga yawan ganin masu sikila da katon ciki, kamar an kifa mai kwarya a cikin, kumburin jiki musamman hannaye da ƙafafuwa zasu dunga kunbura ga tsananin raɗaɗi da zafi, yawan ƙarancin jini lokaci-lokaci, riƙewar ƙirji, da dai sauransu.
*Taya ake magance ta*?
Cutar sikila bata da wani magani da zaka sha ka warke har ya zuwa yanzu, ana iya magance ta ne kawai ta hanyar dashen ɓargo wanda sai mai hali zai iya domin har yanzu ina tunanin ba'a farayi a ƙasar nan ba sai dai ƙasashen waje, sai ana buƙatar a yawaita samai jini lokaci-lokaci domin magance mai rashin ƙarancin jini da yake fuskanta wato (Anemia).
*Taya zan ba yara na kariya daga kamuwa da cutar*.?
Kuna iya ƙare ƴaƴan ku daga kamuwa da cutar sikila ce ta hanyar yin gwaji wato (Genotype Test), gwajin kwayoyin Halittar gado kafin Aure.
Kuma ita cutar sikila bata yaɗuwa, sai dai a haifeka da ita, don haka wani bai shafa ma wani.
*Taya ake gadon ta*.?
Idan har Mahaifinka da mahaifiyar ka suna ɗauke da gene na sikila sai kowannensu ya bada gene nasa na sikila a wajen ɗaukar cikin ka to tabbas za'a haifeka ɗauke da cutar sikila.
Idan ɗaya kuma ya bada lafiyayyen gene ɗaya ya bada mai ɗauke da cutar za'a haifi yaro bai dashi Amma yana ɗauke da kwayar cutar a jikin sa, sai dai bazaiyi tasiri ba.
Ƴar ka ko Ɗan ka zasu iya kamuwa da sikila ce matuƙar in kai Carier ne kuma ka Auri Carier ma'ana ma AS ya Auri mai AS, to tabbas zasu haifi mai sikila, sai dai yana da kyau mai AA ya Auri ma AS, KO SS ma'ana mai AA dai shine ainihin lafiyayye wanda bai ɗauke da kwayar cutar ko kaɗan a jikin sa.
Numfasawa Umma tayi tace "yanzu Doctor haka Zainab zata rayu cikin halin ciwo, ba wani taimako da zaku iya ba ta."?
"Umma ni musulma ce na yarda da kaddara ta, kuma nasan ciwo, rayuwa, Mutuwa, duk daga Allah ne Amma ina ji a jikina Umma bazanyi tsawon rai ba, kuma ina da burin zama likita domin in taimaki masu irin lalura ta."
Ta ƙarasa maganar tana kuka tana mai rungume mahaifiyar ta.
"Zainaba ki yafemun ni nabi son zuciya na biye ma Soyayya, gashi yau ina da na sani domin tun bayan haihuwar ki Zainaba Mahaifin ki ya haɗa baki da likitoci aka juyamun mahaifa, ke kaɗai nake gani in ji daɗi, in kika mutu ina zan sa rayuwa ta."
Ta ƙarasa maganar tana mai ƙara rungume ƴar tata gaba ɗaya mutanen dake gurin sai da suka zubar musu da hawaye.
Haka suka baro Asibiti bayan likita ya mata wannan dogon bayanin, ya kuma rubuta musu ƴan magungunar da yasan zai sauƙaƙa ma Zainab ciwo ya kuma yi mata Allura.
*Bayan shekara Goma*.
Kuka takeyi sosai har tana neman shuɗewa.
Da sauri dattijiwar matar ta ƙarisa shigowa ɗakin tana mai faɗin, "Zainaba lafiya mai ke damunki ko jikin ne ya motsa."?
Ta faɗa tana mai riƙo ƴar tata.
"Umma Hasssan shi ma ya guje ni, wai bazai taɓa iya Aure na ba saboda lalura ta, Umma meye laifi na,? ni na ɗora ma kai na wannan cutar, meyasa mutane basu da Imani meyasa basu da tausayi ne." ?
Ta ƙarasa maganar tana ƙara fashewa da wani kukar. Sosai mahaifiyar tata take jin tausayin ƴar tata har cikin ran ta, da sauri ta goge hawayen da yake nemon sauko mata saboda kar ƴar ta gani sai dai ta makara, don Zainaba ta gan ta.
"Umma yau shekara ta talatin da biyar ina fama da wannan lalurar, kuma Umma ni ma mutum ce kamar kowa Ina buƙatar in yi Aure kar in je in faɗa hanyar saɓon Allah, ina iyaka ƙoƙari na don gani na kare kai na, Umma ta ko dai bani da rabon Aure ne a duniya,? Umma ina son Aure."
Ta ƙarasa maganar cikin kuka, gaba ɗaya Tausayin ta ya lulluɓe Mahaifiyar ta don wannan shine karo na biyar da ake yaudarar yarinyar da sunji tana fama da sikila sai suce bazasu iya ba. Tunanin ta ne ya katse lokacin da taji ihun Zainab.
"Na shiga uku ƴa ta don Allah karki mutu ki barni.!"
Ta faɗa cikin tashin hankali tana fita tsakar gidan su don neman agaji, nan da nan suka nufi Asibiti da Zainaba tana ta Aman jini.
Suna isa Asibiti likitoci suka karɓe ta akayi Emergency da ita, da kyar aka samu numfashin ta ya dai daita kuma jinin ya tsaya.
Bayan likita ya fito ya buƙaci ganin Umma a offishin shi, bayan sun zauna ya fara magana da cewa, "Hajiya mai yasa kuke da sakaci ne bayan kun san condition ɗin yarinyar nan, Amma har kukayi sakaci ta ƙara kamuwa da wasu cutar har biyu, kuma dukkan su manyar cututtuka masu saurin kashe mutum, Ciwon zuciya, da Hawan jini, kuma a koda yaushe zata iya rasa ran ta."
"Na shiga uku na ni Halima, wallahi doctor ba yadda zanyi ne."
"Sir maralafiyar nan fa ta farfaɗo ta cigaba da Aman jini, ga kuka da takeyi tana ƙafarta kuma a kira mata mahaifiyar ta."
Ai aguje da Umma da Doctor suka fita suka nufa wurin ta, Suna isa ta ce, "Umma ta ki yafemin duk abun da nayi miki tabbas ni mutuwa zanyi yau ɗin nan." tari ne ya sarƙafe ta nan ta fara buga kafarta da jikin gado tana a cire ƙafar wayyo ita zata mutu, gaba ɗaya likitoci sun kasa bata wani taimako ma, a ranar Zainaba tace ga garin ku nan, da misalin karfe sha biyun dare, a take a gurin Umma ta yanke jiki ta faɗi.
Washe gari Lawal ya zo Asibitin yana kuka yana ba Umma Haƙuri, yayi nadama sosai duk da bai ƙaunar Zainaba bai sa ta gajiya da yi mai biyayya ba a matsayin shi na Mahaifin ta duk cikin ƴaƴan shi ta fisu ladabi da biyayya ga ƙoƙari don a dalilin ta mahaifin nata yaje saudiya lokacin da ta ci gasar karatun alkur'ani mai girma, duk da haka bai sa mahaifin nata ya so ta ko ya jawo ta a jiki ba sai hantara da kyara tsakanin su, a gurin Mahaifiyar ta ce kawai take samun gata.
Ranar Lawal yayi kuka har ya gode Allah.
*Bayan sati ɗaya*
Gaba ɗaya Umma ta rame kullum ta shiga ɗaki sai taga kamar zata ga Zainaba akan katifar ta ne, haka rayuwa ta cigaba ma Umma cikin kunci da dana sani.
*TAMMAT BIHAMDULILLAH A NAN NA KAWO ƘARSHEN WANNAN ƊAN GAJEREN LABARIN NAWA DA FATA KUNJI DAƊIN SA.*
*DON ALLAH DUK WANDA YA KARANTA YAYI SHARING ƊIN SA DOMIN ƳAN UWA NA SAMARI DA ƳAN MATA*
*SARAUNIYAR KANAWA CE*👸
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 1