Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

musu da abuntabawa , daga bisani kuma munada bukatar ahadamana kayataccen dinner in the night saboda farinciki wannan ranar , "

Insha allah yanzu kuwa Ammi tafadi cikin farinciki tareda mikewa tafice , sundan taba hira sosai yayinda Kamal yaciga ba dabasu labarin yanda wasansu ta kwallon kafa takasance, seguraran azahar tagabato kai suka suma watsewa domin gabatar da bautan ubangiji, koda suka fadeelah suka shigo bedroom dinsu Reeda ne kadai tashiga toilet tagabato alwalanta sukuwa Nisha da Fadeelah suna fashin sallah ya bakon nasu kusan atare yaziyarcesu,

cikin Nisha da yamurda matane nayunwa yasa tatuna tunsafe ba abunda tasawa cikinta , hakan yasa tamike tafice tabar fadeelah dake kwance saman bed tana latsa wayarta , Nisha direct kitchen tanufa ta tadda barka tana tsaka da aikin da ammi tasata , barka naganin nisha tasaki murmushi,

"yar nan yau koma ina kika shiga kolekoni ba kiba inata cikiyarki "murmushi nisha itama tayi tana fadin

"kinsan yanzu papan Aheel yace nadaina kawo masa breakfast daga nan sede naje can part dinsa nayimasa girki dana dawo kuma bacci nakomayi shiyasa yau bakijiniba ai "
.
" Kai amma yayankun nan yana wahalar mana dake amma ko bakomai zaki samu lada ai, amma koya kikeji da wannan masifaffiyan matar tashi mai bala'in kishin tsaya duk ita take kore masu mata aiki saboda rashin hankali irin nata , Barka tafad'i gamida jimami"

"Uhm baba barka taimakeni da a binda zansawa acikina because yunwa nakeji sosai tunsafe namance banci komai ba Nisha tafad'i gamida kaiwar da zancen barka,"

"laa ai ammi tafadamin bake a breakfast din dazu sabida bacci kike baki tashiba shiyasama nakillace miki naki breakfast din amma inda wani abunda kikeso kifadi yanzu sena miki shi,"

"aa basekin wahalar da kankiba iya wannan dinma yayi ,"

"To shikenan kede jekizauna a dining table yanzunan zanfito" Barka tafad'i, bamusu Nisha tayi abunda Barka tace ba dadewa Barka tafito daga kitchen tajerawa Nisha plate agabanta plate din Irish and chicken dawani hadin salad agefe se dan madaidaicin kyakykyawan bowl mai daukeda fruit salad wanda yaji madara Yakuma sha sanyi ,bawani tsayawa jira Nisha tasoma ci seda taci takoshi takauda yunwar dake tareda ita daga nan tadauki plates din tanufi kitchen, tana shiga ta ajiyesu daga bisani tashiga taya Barka da aikace aikacen da take ,sannu ahankali sunayi suna fira hatsuka kammala daga nan suka shiga jera kayan lunch bisa dining table daga nan Barka takoma kitchen tadauko try din abincin data tanadarwa kamal da matarsa masu lunch din tasuma kokarin ficewa,

"Baba Barka ina kuma zaki bayan gani ? nasan lunch din su ya kamal ne da Aunty Nabilah please bani nakaimusu na hutar dake ,"

"Aa yar nan baza ayi hakaba, tunsafe kika gama bautan yayansu yanzu kuma nabarki kikare Dana kaninsa gaskiya baza ayi haka daniba kibarshi kawai yanzu zanje nadawo "

"Please baba Barka kibari nakai mana " nanfa Nisha taita mata magiya tareda dagewa Barka wanda yasa dole Barka tahakura tabata try din abincin nisha ta amsa tareda sa kai tafice , Nisha nakarisowa door din Kamal tashiyin knocking bugu daya zuwa biyu aka bude, koda budewa kuwa Nabilah takagani tsaye cikin shirin kananun kaya t shirt da wando skintight wanda yawuce gwiwar kafarta kadan tasakalo sumarta har baya yakwanta lub tayi kyau da ita, murmushi Nabilah tasakarwa Nisha cikin sanyin murya tace ,

" Please come in! ahankali nisha tasakalo kafarta takariso cikin parlour yayinda Nabilah tamaida door tarufe ta dawo kusa da Neesha ta tsaya tana cigaba da murmushi, itama nisha murmushi take daga bisani tashiga fadin, "

" Am..dam.ma lunch dinku nakawo muku ,"

"Ayya thanks you so much" Nabilah tafad'i gamida karban try din abincin takarisa dashi saman table ta ajiye ganin haka yasa cikin hanzari nisha tace,"

" se anjima daga haka tajuya tafice tabar nabilah tsaye tana binta daga kallo hartafice , Neesha nafita tundaga nisa ta hangi ajmal hanunsa dauke da na Aheel se kamal da Daddy wanda yanzu dawowarsu daga masallaci sunjero suna tafiya gwanin sha'awa da burgewa Kamal daga nesa ya hangi nisha tafito daga part dinshi amma kafin su iso harta shige bangaransu cikin sauri, direct Ajmal yanufi side dinshi shida dansa hakama Daddy yanufi nashi sashin , daga nan Kamal shima yakarisa nashi part din,
Da dare guraren karfe 9:pm gabaki daya ahalin abubakar modibbo bature sun hade guri guda suna gudanar da kayataccen dinner, dining table medauke da gurin zaman mutum 12 kowanne acikinsu yakasance daga daya daga ciki wasu suna facing din wasu gwanin burgewa da ban sha'awa harda Heelah wacce Ajmal ya gayyatota badan komai because Daddy yace yana bukatan kowa yakasance gurin dinner, Heelah batasan da dawowarsu kamal ba kwata kwata seyanzu da tashigo ta ganewa idonta wanda hakan ba karamin mamaki tayiba ,

Nisha kuwa tayi tsayuwar daka wajan taya Barka kawo abinci anajerewa wanda komai tare suka gudanar dashi seda suka kammala jera komai Barka tajuya takoma ciki nisha kuma tasamu daman zama kamar yadda kowa yazauna ,daga nanfa kowannensu yashiga serving din kanshi da abunda yakeso yana zubawa a plate, banda ajmal dako motsi baiyiba bayida kuma niyar motsawaa

"yade kowa yadibi abunda yakeso yana ci kaikuwa kasa phone agaba kana dannawa?" Daddy ke tambayan ajmal dayayi sunkuye da kayi yana latsa phone dinsa, dan dago kai yayi ba tareda yace komai ba ya ajiye phone din gefe daga bisani yagyara zama ya kallo nisha wacce idonta ke kanshi because kujerunsu yana facing najuna, yanda yakora mata ido tasan serving dinshi yakeso tayi amma ita kuma nisha setashiga kallon heelah wacce takecin abinci tana yamutsa fiska kamar wacce akasa dole ko kallon inda sukema batayi, nan kuma taimada kallonta ga ajmal wanda ya hade rai yabata fiska wani kallon da yakuma watsa matane yasa nisha mikewa tsulum wanda hakan yayi sanadin dawowada hankalim ahalin guresu,

daga Hajia Daddy suwa Ammi suka shiga murmusawa ganin yanda Nisha ke serving din ajmal gwanin shaawa da burgewa duk da dama sunsan ajmal inde tawannan fanninne to komai se amsa abincin ma inda zaisamu adinga bashi abaki ajiye spoon zaiyi , Goggo rabi bakinta kamar zai taba kumatu tsabar murmushin jin dadi, kamal kuwa da mamaki yake kallon nisha ganin bani na iya irin na yarinyar dayin abunda ba asataba gaba daya yarinyar tanasun bawa kanta wahala , taban garan heelah nunawa tayi ko ajikinta amma cikin zuciya allah kadai tasan kunar zunda take gaba daya nisha Rana shigar mata hanci amma ba dadewa zata facuta,

Nisha harta gama serving din ajmal takoma tazauna kamal kebinta da kallo , nabilah kuwa duk motsin mijinta idonta nakansa , abincin dake gabanta bawani ci sosai takeba kawai tsakura take tana juya spoon ajmal kuwa nisha nagama serving dinshi yashiga gunar da nashi cin abincin, Jim kadan ta bangaran nabilah tafarajin kanta na bala'in sarawa, jitayi duniyar najuya mata ahankali ta ajiye spoon din hanunta adan dafe tamike daniyar tashi ,

"Bade harkin kammalaba" Ammi ta tsareta da tambaya , nabilah bude baki tayi daniyar magana sekuma takasa because wani yunkurin amai dayataso mata aiko cikin hanzari ta toshe bakinta tawatsa aguje tafice daga parlourn,
gabaki dayansu se bin bayanta da kallo suka shigayi harta fice banda kamal dayayi yunkurin tashi yabita,

"mekatsaya jira da ka kasa bin bayan matarka kamata yayi kabita idan da wani abunda yaci karfinku sekazo kayi magana" Hajia tafad'i tana kallon Kamal wanda keta zare ido shibai zaunaba baikuma tsayaba but jin abunda hajia tafad'i yasashi jin karfin gwaiwar bin bayan matarshi dan haka cikin hanzari yabi bayanta, "

" Masha allah , ikon allah kai allah abin godiya, tsarabar Canada har gida kai alhamdulillahi" Goggo rabi tafadi tana daga hannuwa sama, hajia da Ammi farinciki harsun kasa cewa komai , Daddy kuwa kai kasa se murmushi yake heelah se hararo Goggo rabi take wacce keta kwararo godiya ga ubangiji",

" dama kinbar wannan godiyar dakike dan abunda kuke tunani insha allahu zubewa zaiyi bade tahaifeshi cikin gidan nanba heelah ke maganar zuci , gefe kuwasu reeda ne ke magana kasa kasa tsakaninsu,

"Awwwn nabilah fa kamar cikine gareta ko" fadeelah tafad'i ahankali,

" bakamar bane cikinema" reeda tabata amsa yayinda sukacigaba da cin abincinsu kamar basu suka gama kuskus yanzuba, duk abunda suka gama tattaunawa tsakaninsu nisha najinsu se murmushi take gefe gefe aheel zaisamu kani zasu samu little baby, shikuwa gogan ko ajikinshi tamkar baisan me akecikiba abincinsa yakeci cikin kwanciyar hankali,

Kamal nakarisawa part dinsu koda yashigo parlour ba nabilah aciki hakan yabashi daman karisawa cikin bedroom nan yaci karo da sautin nabilah cikin toilet tanata faman zabga amai cikin hanzari yakarisa baking toilet din ya tsaya harseda ta gamayin aman tawanke bakinta tafito ta tararda kamal bakin door yana jiranta,

"sannu! meyake damunkine" Kamal ya tambaya gamida tallafota suka karisa bakin bed suka zauna, "

"Please tell me what's wrong ? "Kamal yakuma tambaya, "

" bakomai nabilah tafadi gamida sunnar dakai kasa ,cikin hanzari kamal yadauki phone dinshi yasuma lalubar wata number,

"Wait! what are you doing?" Nabilah ta tambaya gamida rike hanunshi,

" doctor fu'ad zankira yanzo ya dubaki yafadamin meke damunki" Kamal yabata amsa cikin damuwa Nabilah karban wayar tayi ta ajiye gefe daga bisani takalleshi yana fad'in,

" bakasan me yake damunaba? gyada mata kai kawai kamal yayi daga nan nabilah tadauki hand din shi tadaura saman cikinta tacigaba da fad'in,

"Babynmune yake zuwa very soon zan koma mummy kaikuma zaka dawo Daddy

🌴🌴 *IG AJEEMAL*🌴🌴

* _STORY AND WRITING_*
By
*_OUM AMREESH_*❤
_khaleeseart Raeeys_

........ *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
(J.W.A)
_masu aiki da zallan fikira da fusaha tareda jajircewa wajan sarrafa alkhalamin wajan ilmantarwa fadakarwa tareda nishad'a tarda al'umma_

بسم ا لله الر حمن الر حيم

.................*_Free book_*😍
.....page51

Cikin murna da farinciki gamida d'auki kamal ke kallon nabilah, "

Oh god waiyanzu ciki gareki ? d'an g'yad'a kai nabilah tayi tasunnar dakai tana murmushi, "

Oh Allah nagode maka zanzama Daddy yanzu nakara girma nima kamal yafad'i tareda rungumo nabilah yana cigaba da fad'in, "

Nagode Allah yamiki albarka ya kareki keda babyna , daga nan nabilah tarungumishi cikin tsatsan so da kauna tana fad'in "

Ameen sannu ahankali suka suma lulawa duniyar maaurata cikin shauki da begen juna , ....

Abangaransu Daddy koda sukajira suga dowowar kamal sukaji shiru hakan ya tabbar musu lapiar kenan da haka suka cigaba da gudanar da dinner d insu , koda suka kammala daga nan kowa yashiga watsewa don yau ba tsayawa dugun hira kasancewa dare yayi sosai , dama ajmal baitsaya wani dugun cin abinciba yatashi yafice, matarshima tarufa masa baya tareda aheel daketa rigima shi bazai mom dinsaba gurin auntynsa zai kasance , daker heelah tasamu tayakiceshi daga jikin nisha suka fice ,

sude hajia har kullum suna mamakin sabonda aheel yayi da nisha , dan haka suma suna gama kammala cin abincin suka suma watsewa kowa yanufi turakarsa , zuciyoyinsu cike da farin ciki da nishad'i, washe gari guraren karfe 8:am bayan ammi tayi breakfast di'nta yanda tasaba tayi shirinta nazuwa office, nan tafito daga part dinsu direct tanufi part din kamal , seda tazo daidai door d'in tashigayin knocking, bugu daya zuwa biyu aka bude kamal ne yafad'e door d'in yanda sanye cikin black jallabiya ganin ammi tsaye bakin door yasan yashiga sakin murmushi yana fad'in,

"Please Ammi yakika tsaya shigo mana" ,murmushi itama ammi keyi batareda wani musuba takarisa shiga cikin parlourn, can doguwar sofa ta hangi nabilah takishingida wanda ganin ammi yasa tamike zaune tana yar murmushi gamida sun kuyar dakai

"Ai dama kinyi kwanciyarki karna takuraki , ammi tafad'i gamida karisawa kusa da nabilah tazauna,"
Ammi ina kwana antashi lapia,

"Lapia qlu yajikin nakikuma dafatan ba abunda yake damunki yanzu, d'an gy'ada kai nabilah tayi tana fad'in

"Bakomai !"

", that's good dama yanzu nake shirin tafiya office shine nace bari nazo naga jikin naki , kuma natambaya Inda akwai wani abunda kikeda shaawa nasa akawo miki because karkicigaba da wahalar da kanki, "

"Yauwa Ammi tambayeta de yanzunan nakita tambayanta tafad'i min metakesu taci naje nayi mata order but taki wai bata shaawar komai, kinga wadannan kayan fruit din sune kadai tasamu tadan tabasu Kamal yatare maganar yana nunawa Ammi plate
d'in kayan fruit dake ajiye saman table,
Yana kuma kallon Nabilah dayi sunkuye da kai ,

"sudinma babu laifi suna da amfani amma fruit kad'ai bazai wadaceki keda bari naje zansa barka takawomiki abun tabawa wanda zaki'iyaci , karkidinga barin cikin ki dayunwa, d'an g'yad'a kai nabilah tayi taga haka ammi tamike tana kallon kamal tana fad'in"
Nizan wuce kakula da kyau , "

To ammi kamal yace daga haka yarako ammi harbakin door daga bisani sukayi sallama kamal ya maida door yarufe tareda komawa kosa da nabilah yazauna yamata matashi da cinyarsa kamar yanda suke dazu kafin shigowar ammi , ahankali yakeshafa sumar kanta yana fad'in, "

allah yasa kihaifamin baby mai kama dake kamal yafadi yana kallon nabilah da face dinsu ke fiskantar najuna, dan wani cool smile nabilah tasake tana fad'in, "

Nikuma nafison nahaifi baby sak irinka , because of what? Kamal ya tambaya "

Because kafini kyau da komai nabilah tafad'i cike da murmushi, shima murmushin yake yaname jan dugun hancinta yana fad'in, "

And you ba fatanmu de allah yasauke ki lpy "

Ameen nabilah ta amsa cikin sanyin murya ,Jim kadan suna tsaka da yar firan tasu sukajiyo knocking din door, "

come in! kamal yafadi ba tareda ya motsa daga inda yakeba gaba kidayansu suka tsirawa kofar ido dan ganin maishigowa ganin Barka dauke da try din abinci yasa kamal yasake jingina da jikin sofa yana murmushi, ita kuwa Nabilah kokarin tashi daga cinyarshi tashigayi amma kamal ya hanata dan haka yasa tahakura da tashin , "

Megida Barka da safiya fatan antashi lpy baba bakar tafadi tana yar dariya because kamal mutumintane sosai , tasu tazo daya kasancewanshi mai barkwanci da sun wasa wani lokacin bakamar yayansuba shikadai yafita zaka cikin gidan bayida wasa kuma bayidason magana sosai wani lokacin kuma inyajuye kamar bashiba,"

Yauwa barkade uwar daki ya aikin kamal yabata amsa yana yar murmushi, dama Ammi tace nakawowa madam wannan Barka tafadi gamida ajiye try din abincin saman table dinda ke gabansu tashiga kallon nabilah dake kwance saman cinyarshi tayi lamo takamar mai bacci wanda ganin shigowar barka yasa takulle ido because yanzu gaba daya kunyar kowa take ko hada ido dakowa batasonyi, amma daga kaga yanda eye lashes dinta kerawa zaka fahimci ba baccin takeba rufe ido kawai tayi dan murmushi Barka tasaki gamida kada kai tana fad'in, "

Megida bari naje nakarisa aiyukana se anjima allah ya inganta , kamal cikin farinciki ya amsa da "

amin mungode

daga haka Barka takama hanyar fita still de murmushi bai gushe daga face dintaba harta karisa ficewa tajanyu musu door din tarufe, kamal kallonsa yamayar kan nabilah yayinda yakuma jan dugun hancinta yanda fad'in, "
To yanzu kam semi samudaman bude idon iyayen kunya , waima kunyar mekikejine haka shigowar ammi dazu kigabi kika takura kanki sewani nuke nuke kikefa , bude ido tayi tana kallonshi daga bisani tatura baki tana fad'in"

Ni wallahi kunyar kowa nakeji yanzu ko hada ido dakowa banasonyi ,"

meye dalili ko saboda kintaho musu da tsaraban Canada kamal yafadi yana yar dariya, dan bugu takaiwa shouldern kamal tana fad'in, "

Kaikam bakajin komai ko ? "

To maizanji kuwa bayan nasan kokarin danayi tashi muyi breakfast dan yunwan nakeji kamal yafadi gamida tada nabilah zauna yashiga bude food flats din abincin, pepper soup din kifine da soyayyiyar irish tareda wani hadin salad nakayan itatuwa masu kara lafiya da kuzari se wani dan madaidaicin bowl wanda ke rufe da Yugo fruit salad ancika madara acikinsa, bawani tsayawa bata time kamal yashiga serving din su ,

yana gama zuba abincin a plate yashiga bawa nabilah abaki kamar karaman baby shima yanaci ba laifi komai tadan tabashi taji kuma jidadin abinci sosai especially hadin salad din tafi bashi ma himmanci dadin dadawa yanda kamal yayi tsayuwar kaida fata wajan ganin taci takoshi bakaramin dadi hakan tajiba koba komai yana kula da ita sosai but hankalita yaki kwanci ganin kamal da nisha Inuwa daya suke zaune suna haduwa dajuna wanda hakan baya mata dadi kokadan ,


*_IG AJEEMAL*_

Story and writing by
Oum amreesh

Nisha hanunta har rawa yake gurin kunna light din bedroom din aiko tana kunnawa haske maikyau da inganci yabaiyana cikin dakin , ahanzarce tajiyu tamaida hankalinta ga saman carpet , kwance yake ya dunk'ule guri guda kamar mejin sanyi still yana rungume da pillow tsam a chest dinshi yana sanye cikin kyakykyawan milk jallabiya gashin kansa duk sun hargitso face dinsa sun manne saboda zufanda suka tsatstsafo masa ,

idonsa arufe jin motsin mutum da kuma kuna light da akayi yasashi kokarin bude ido ahankali yasaukesu kan Nisha dake kokarin karisowa inda yake lips dinta se bari yake, idonsa yamayar yarintse wanda sukayi jawur dasu because haske yayiwa idonsa karfe "

Ya ilahi Nisha tafurta ahankali yayinda tagama karisawa gareshi gefe ta sunkuya kasa tana kallonshi"

meyasa sameka? are you okay? Nisha tashiga jera masa tambayoyi cikin rawar murya, jin shiru bai amsa mataba yasa takuma tambayan shi still shirun yakumayi ba amsa hakan yasa tayi tunanin tashi tabashiguri domin atunaninta maybe hanlin nasane na miskilanci yamotsa , amma ayanda taganshi yanzu kamar Wanda bashida cikakkiyar lapia saboda yanayinsa gaba kidaya yanuna hakan gashi yayi shiru baya magana balle tasan abinda ke damunshi, can gefe takalla inda wayansa keta faman ruri saman bed sekuma ta maida kallonta gareshi shiru bai motsa ba baikuma sake bude idoba se ajiyar zuciya dataji yana saukewa , gaba kidaya tagama tsorita anya papan aheel kalau yake kuwa ? gashi haryanzu kiran phone dinshi aketayi ba adenaba da alamar mekiran ya k'agu ,

Ahankali Nisha ta isa ga bed din tasa hanu ta dauki wayar daga fiskar wayan taga maikiran sunan doctor fu'ad ya baiyana jikin screen phone din , nan Nisha ta fahimci yau ana duba file din ajmal that means bashida lapia kenan Nisha karisawa tayi tareda wayar inda ajmal take kwance taduka kusa dashi tana fadi'n,"

ga phone dinka anata kira , halwayude bai kumace mata kalaba idonsa arintse se red lip dinsa daketa faman bari yana motsi, "

Allah sarki maybe yanajin jiki sosaine da hartayi tunanin daga masa wayar tafadawa doctor fu'ad halinda ta iske ajmal aciki to amma wayakaita wannan karan banin dan haka seta ajiye wayar agefensa tana fadi'n,"

sannu bari naje nafadawa su hajia azo akaika asibiti Nisha na gama fadi'n haka tamike cikin hanzari, charab taji yariko kasan riganta cikin sauri Nisha tajuyo takalleshi still idonsa arufe se bakinsa dayaketa kokarin motsawa yanaso yace wani abin , Nisha dawowa tayi kusa dashi tasunkuyu tana kallonshi,tana kuma kallon lips dinsa meyakeson fadi"

Help me! abunda taji yace kenan slowly araunace Nisha tashiga tambayanshi,"

wani abun kakesone kafin takomacewa wani abu sejitayi yace ,"

d'agani ! dan tsaro ido Nisha tayi tana kallonshi kafintace ,"

indagaka zuwa ina ? "

Bed kawai taji yakuma fadi yana mai sake rungume pillow jikinsa da alamar sanyi yakeji sosai , kallonshi Nisha tashigayi sama da kasa yanzu inba neman magana irin na papan aheel ba ina ita ina iya dagashi , gaba kidayanta in aka hadata guri guda bata wuce lumansa dayaba ga tsayi gajiki tasan ba karamin nauyi zaiyiba to amma yazatayi tunda ya nemi taimakonta dole ta taimaka mishi yaka karfinta , dab dashi taje takuma tsugunawa ta dan janye pillow dinda yarungume ita kanta pillow seda tayi dumi saboda zafin jikin ajmal, dan koda ta matso dab dashi numfashinda yake fitarwa shima dumine jikinsa yayi zafi sosai,

da ganan Nisha shiga taimaka mishi wajan tashin takamo hand dinshi tadaura saman shoulder dinta dakyar da sidin goshi tareda taimakonsa cikin karfin hali suka samu daman mikewa , sede koda suka tashi taku daya zuwa biyu suka shigayin tangal tangal da juna ajmal karfenshi ya gaza because jikinsa ba kwari sosai bayajin karfi ajikinsa jikinsa duk amace yake haka Nisha taji yasake mata ragaman jikinsa gaba daya duk yanda Nisha tayi kokarin tallafoshi amma se jikake luuu ajmal na kokarin faduwa aiko cikin sauri da fargaban faduwar tasa Nisha taja hanusa da karfi suka fada saman bed tare kamar kifan mazar k'waila haka suka kife ruf ajmal yarufe Nisha da faffadan k'irjinsa ko burbud'inta ba agani, wani dugun numfashi ajmal yashiga saukewa jinshi saman lallausan bed din shi zamu iyacewa gaba daya ajmal baya cikin sense dinshi Sam yamance yana kwance kan halittan da adam ,

itakuwa Nisha tunda suka kife takasa motsi se zazzare ido tashigayi face dintama ba agani balle hancinta yashaki numfashi taririn zafin jikin ajmal sebugunta yake gashi bayida niyar dagata hala ko suma yayi taji shiru bai dagataba bugun heart dinshi da yanayin yanda yake sauke ajiyar zuciya duk tana iyaji , shikuwa mutumin jin dumin jikin Nisha yabashi wani yanayi mai dadi da kozari ajikinsa yasa yashiga sake tattarota jikinsa yarungume kamar yanda yasaba rungume pillownsa jinwani wawan runguma da ajmal yamatane yasa idanunta suka fito waje tsabar tsoro dakidima Nisha tasaki wani kara tana fadi'n,"

Wayyo Allah wayyo ummana zaikashenii.., tar ajmal yabude ido jin muryan Nisha datake sumbatu, cikin zafin nama dakarfin hali ajmal ya kauce gefe cikin sauri yasa hand yadafe goshinsa face dinsa yana kallon sama yarintsa idonshi, Nisha najin kaucewan ajmal tayi hanzarin zamowa daga bed din tana sauke ajiyar zuciya tareda tattaro numfashin ta dake kokarin tsayawa hanu takai tadauki mayafinta dake saman bed din Wanda yafice daga kanta tamaidashi mazauninsa , sidi sidi tasuma kokarin barin bedroom din kanta asunkuye hartazo bakin door tajiyu takai kallonta gareshi, lokacin harya yasan gyara kwanciyarshi yakai hannu yaja blanket yarufo jikinshi , Nisha juyawa tayi tafice daga bedroom din ajmal yabi bayanta da kallo akunyace yarasa wani irin zazzabine yarufeshi haka da har yakasa control kanshi har seda yanemi taimako,

rintse ido yakumayi gashide yarufe jikinsa da blanket but baisamu irin relief dinda yasamu dazu da yarungume Nisha ba amatsayin pillow shine mai wannan dumi me dadinba dan mintunan daya samu yayi ajikinta har yafara jin saukin abunda ke damunshi, gaba daya ji yayi ransa yadagule masa yarasa meke masa dadi , Nisha kuwa tana fitowa daga bedroom din tanufo downstairs gudu gudu sauri sauri haka take sakkowa idonta duk sun fito waje tsabar o, tana gama sakkowa taja ta tsaya ganin doctor fu'ad zaune bisa kujeran parlourn yanata faman Kiran line din ajmal,

ganin sakkowan Nisha arikece yasa hankalin doctor fu'ad dawowaa gareta wanda yasashi mikewa yashiga yimata murmushi, itama murmushin tashiga kirkirowa tana shafa gefen wuyanta daga nan tashiga dagawa doctor fu'ad gaisuwa, cikin fara'a ya amsa da mamakin yanda yariyar ta canza kyanta yagara baiyana dan da ace baisan tabama ba lallai yace yataba ganin taba ,"

mutuminfa nakirashi bai daukaba doctor fu'ad ya tambaya,"

yana bedroom din shi Nisha ta bashi amsa asanyaye,"

Alright barinaje naduashi doctor fu'ad na gama fadi'n

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment