Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 3
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels NAMIJIN GASKE Littafi na daya Complet Na Shuraih Usman Namijin gaske Part 1A (c) shuraih Usman @shuraih 99% NAMIJIN GASKE Littafina daya 1 Marubuci:- Shuraih Usman Typing:- Shuraih Usman Tel. 08133209890 Part A . Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa wannan labari ta ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan za'a kiyaye Copyright Shuraih Usman . Saurayi ne kyakkyawa ma'aboci kyawun fuska, wacce duk ya macen da yai arba da ita sai kware masa. Babu komai ajikinsa face wata falmara ta fatan zaki, falmarar ba'a rufe madannin ta ba, hakan tasa dukkan ilahirin kirjinsa a bayyane yake a fili, Gaba daya kirjinsa waje yake, hakan ce ta bayyana surar kirar jikinsa, ko ina ajikinsa a murmurde suke, a yayin da wasu guruna suka bayyana bisa tumbinsa kai kace baya cin abinci ne. A kasansa kuwa wata gajeriyar wando ce iya guiwa , ya sanya ,rike yake da gabjejiyar itace a hannunsa . Yana tafe yana waige waige koda zaici karo da abinda ya fito nema, kai da gani kasan wannan kyakkyawan saurayin farauta ya fito yi, . Yana tafiya yana gunaguni a cikin zuciyarsa kuwa tunani yake "wai yayane anya wannan karon da sa'a kuwa, Ni dana ke fitowa farauta na kamo manyan namun daji masu ababen al'ajabi, Kuma cikin kwanaki biyu rak nake kamosu sannan na tasamma gida,amma wannan karon gashi har na tasamma kwanaki hudu amma ko tsuntsu banyi arba da shi, Maganar tasa ta katse a dalilin wani gurnani daya ji, Ai koda yaji wannan gurnanin sai ya cika da farin ciki ainun bisa ganin wahalarsa tazo karshe, . Gurnanin yaci gaba da kusanto shi, ta cikin wata duhuwar sarkakiya ne gurnanin ke fitowa. Nan ya tasamma wannan sarkakiyar, koda ya rage baifi saura kadan ya karisa ba, kawai gani yayi wata murgujejiyar damisa ta fito daga cikin sarkakiyar ta bayyana a gabansa, . Ya dubi wannan damisar sai ya ganta lafceciya, sai yayi murmushi sannan a fili yace da alamu dai yau zan koma izuwa gida da karamin nama. Itako damisar sai dalalar da yawu take bisa kasa, Yau kwanakinta kusan goma kenan bata dandani Nama ba , kullum sai ciyayi take ci Toh yau ga tsuntsu daga sama gasasshe, . Mayunwaciyar Damisar tayi ruri sannan ta fada kan jarumin saurayin , Nan suka zube kasa gaba dayansu Damisar tana bisansa sai kokarin farke wuyansa take da hakoranta, a yayin da shi kuma saurayin ya rike habarta da hannunsa, sannan yasa kafa ya taka ta , take damisar tayi sama yadda kasan an dauketa da majaujawa , koda damisar ta fado bisa kasa sai tayi wata irin kara sakamakon jin zafin takun da saurayin yamata . . Saurayin ya mike tsaye sannan yayi wata irin tsayuwa irin na Mazan kwarai, . Damisar na ganin haka sai ta kara dumfaro shi da nufin tai tsalle ta diram mai a wuya, Koda tai tsallen da nufin ta fada akan wuyansa sai kyakkyawar saurayin ya sanya hannunsa guda . Ya rike mata makoshi, sai gashi murgujejiya kuma lafceciyar damisar na wutsil wutsil a hannunsa kai kace, masunci ne ya kama kifi. . Take saurayin ya daga damisar sama sannan yai jifa da ita , koda yai jifa da ita sai taje ta gwaru da wani babban bishiya , take bishiyan ya fadi rikica, Wannan damisar ko shurawa batai ba, Kyakkyawan saurayin yazo gaban gawar damisar , ya tsugunna da nufin ya sabata a kafadarsa yayi gida, . Ba zato babu tsammani kawai sai ya fara jin Dirdir gowan wasu abubuwa a bayansa, Koda ya juya don yaga mene wannan. Anan ne yayi arba da su, Wasu gabza gabzan Arnan daji ne, Su wayannan arnan dajin suna sanyene warki na fatun mesa,dukkanninsu kamanninsu da fasalin surar jikinsu dayane , Lafta lafta ne ma'abota tarin damatsa babu kaya a jikinsu face wannan warkin na fatan mesa, . Daya daga cikinsu yazo gab da wannan kyakkyawan saurayin yace " yakai wannan kyakkyawan saurayin kayi sani cewa ka aikata babban kuskure a garemu wanda hukuncinka shine kisa mafi muni" . Cikin gadara saurayin ya dubi arnan dajin nan wayanda adadinsu yakai dari yace "Ku sani ni bansan mai na aikata a gareku ba da har zaku yanke wannan hukuncin akaina " . Shugaban arnan dajin ya daka masa tsawa sannan yai nuni da dan yatsansa izuwa ga gawar damisar nan yace "shi wannan damisar daka hallaka , shine mafi kusanci ga abin bautarmu, duk wata bukata da muke da ita ga abin bautarmu muddin muka kama kafa da wannan damisar toh take abin bautarmu yake biya mana buka tunmu. . Kasani yakai wannan gafallallen saurayi, ako wacce rana mun kasance muna farauto ma wannan damisar mutun daya don tayi kalaci da shi, Haka muka kasance muna yi har tsawon wasu shekaru, Kwatsam sai gashi an wayi gari mun fita nemo wa damisar abin kalacinta, har muka debi tsawon lokaci bamu dawo ba, Hakan yasa yunwa ya addebeta ta fito neman wanda tsautsayi ya kasa dashi, sai gashi ka kashe mana ita, Abisa wannan mummunan zunubin daka aikata mana ne shugabanmu Boka Abulzulmu ya turo mu damu yimaka kisa irin ta wulakanci , Don haka ina umartarka daka bani kanka cikin maslaha nai maka kisan sauki, " Koda jin haka sai kyakkyawan sauyarin ya tuntsire da dariya, sai da yayi mai isarsa sannan yace "Ashe ma mugun iri na rage A doron kasa kunga yanzu babu wata rai dazata kara salwanta a dalilin wannan Damisar" Yana rufe bakinsa sai shugaban arnan dajin yayi kukan kura sannan nufo kan saurayin, hannunsa rike da sharbebiyar takobi, Koda yazo daf da saurayin sai ya kai mai sara da nufin ya cisge mai kai, cikin zafin nama saurayin ya sunkuya saran tabi iska, . Kafin shugaban arnan dajin ya sake kaimai wani saran . Sai kyakkyawan saurayin yayi wuf cikin zafin nama ya kirba ma shugaban arnan dajin dundu a baya, Nan take shugaban arnan dajin ya kwalla kara sannan yayi taga taga tamkar zai fadi amma sai ya tirje, take ya furzar da jini daga bakinsa. Saurayin baiyi kasa a guiwa ba ya kama kan shugaban arnan dajin ya murde, karan karyewan kashi ta bayyana, duk wata gaba ta daina motsi ajikin shugaban arnan dajin, . Kyakkyawan saurayin yai jifa da gawar izuwa ga sansanin da arnan dajin ke tsaitsaiye, . Wasu arnan daji biyu suka cafe gawan amma sabida karfin jifan da saurayin yayi da gawan sai da suka zube kasa gaba dayansu. . Koda arnan dajin suka ga abinda saurayin ya aikata ga shugabansu sai dukkaninsu suka yi kururuwa sannan suka zare makamansu, nan suka rugo da gudu da nufin su isa wajen da saurayin yake su gididdibashi gida gida. Shi ko saurayin koda yaga sun nufoshi sai yayi murmushi sannnan ya gyara tsayuwansa. Koda arnan dajin suka kariso wajenda saurayin yake sai sukai mai rubdugu. Shi ko saurayin koda yaga haka sai ya sanya dukkan karfinsa ya tarwatsasu, hohoho!! Da mutum yana wajen yanaganin yanda mutun daya ya gagari daruruwan mutane lallai daya tabbatar da cewa wannan kyakkyawan saurayin ya cika NAMIJIN GASKE mai tarwatsa maza. . Arnan dajin sai kai masa sara da suka suke , shi ko ya wanzu yana mai zullewa da gociya, Babu abin da zaibaka mamaki da saurayin face ganin ko makami babu a hannunsa. A duk lokacin daya samu arnen daji ya kirba mai naushi ko dundu. Nan take zakaga mutun ya fadi wanwar akasa ko shurawa bazai yiba . Sai da aka dauki tsawon lokaci ana wannan fafatawan inda saurayin yai ta ragargazar arnan dajin , Har ya samu nasarar karkashesu gaba daya. Sannan ya dauki gawan damisar ya azata bisa kafadansa, yayi tafiyarsa . Tafiya yake har ya kawo bakin wata bukka , sannan yayarda gawar damisar a kasa, . Ya nufi wani turki ya zauna , Zamansa keda wuya sai waya kyakkyawan mace ta fito daga cikin wannan bukkan . Wannan matar zata kai shekaru hamsin da doriya amma in kaganta kace yar shekara talatin da wani abune. Matar ta dubi saurayin tace dashi "MUHAISIN sai yau kadawo" Jarumin saurayin da aka kira da muhaisin ya dubi wannan matar yace "Ummi na kenan kisani dadewar danayi ta samo asaline daga rashin samun dabbar danake nema" . Wannan matar sunan ta hamasiya sun kasance suna rayuwa acikin wannan kungurmin dajin shekara da shekaru ita da danta muhaisin Tun muhaisin bai mallaki hankalin kansa ba Ya taso ya tsinci kansa acikin wannan daji, Tun baifi shekaru tara a duniya ba mahaifiyanshi hamasiya take ganin ababen al'ajabi a tattare da shi. Don alokacin baifi shekara tara a duniya ba amma sai taga ya fita da nufin zai je farauta, in ya fita kuwa baya da wowa sai bayan kwanaki biyu . Nan zai dawo da manyan namun daji wayanda ko rikakken mafarauci ma sai yayi da gaske kafin ya kama irinsu . Tun hamasiya tana al'ajabi har tazo ta daina ,bangaren jarumta kuwa duk yawan abokan gaba tarwatsasu yake, kuma shi baya fada da makami don ko dabbobi ma wuyanzu yake murdewa. Tun da yake a rayuwarsa bai taba yin yaki ko fada da makami ba da zallan karfin damtse yake yakan ayari guda na yan fashi, da kuma gungun yan harin sumame. Haryanzu da kwai wasu yanfashi dake tarkonsa Su yan fashin sun riga da sunsan yafi karfinsu shi yasa da sun hadu sai kaga yan fashin sun ruga a guje . Ace warsu wai lokacin haduwarsu baiyiba tukun idan lokaci yayi su da kansu zasu nemeshi, . Alokacin da muhaisin ya mallaki hankalin kansa sai ya fara tambayar hamasiya mahaifinshi Hamasiya takance da shi mahaifinsa ya rasu. . Alokacin da hamasiya tazo gaban muhaisin don taga alamun gajiya ajikinsa sai taga gefen damtsensa na zubar da jini , nan da nan hankalinta ya tashi ta yagi wani kyalle dake rataye bisa wannan turkin , sannan ta kama hannun muhaisin tana daure mai wannan raunin . Nan ta tambayeshi meya ji mai wannan rauni, Bai boye mata komai ba , ya labarta mata artabonsa da arnan daji . Koda hamasiya ta saurari labarinsa sai nan da nan kwalla ya cika mata idanu, koda muhaisin ya lura da yanayin da mahaifiyarsa ta shiga sai ya ce" yake ummina shin ina dalilin zubar da hawayenkinnan , " Hamasiya tayi sauri ta share kwallan tace" yakai dana kayisani bako maine ya sanya ni zubda hawaye ba face tuno da mahaifinka da nayi, Lallai ka gaji mahaifinka dana." . Muhaisin najin haka sai ya durkusa bisa guiwowinsa yace" Na rokeki ummina daki sanar dani labarin mahaifina da kuma dalilin dayasa muke rayuwa a cikin wannan kungurmin dajin" . Koda jin wannan tambayan sai Hamasiya ta mike tsaye sannan ta nufi wannan bukkar koda tazo gab da bukkan sai ta tsaya ta dafa bukkan da hannu daya sannan ta juyo ta dubi muhaisin tace " yakai dana hakika yau kayi mani babban tambaya , hakika bawai banason sanar dakai labarin mahaifinka bane sai dai, bana son tuna baya, bana son tuna babban masoyina abin kauna na" koda tazo nan a zancenta sai wasu kwalla na bakin ciki suka gangaro bisa kuncinta. . Muhaisin ya kariso wajenda take sannan yace "Ya ummina hakika kece kadai nake gani nakejin farin ciki a cikin zuciyana, bana son ganin zubowan kwallanki, bana son jin labarin muddin hakan zai tsaida zuban kwallanki" . Hamasiya najin haka sai ta tausaya ma muhaisin ainun ta sanya hannu ta tallafo habarsa tace "Yakai dana kasani Mahaifinka Gawurtaaccen Sarki ne Adali mai jinkan talakawa, Mahaifinka shike mulkin birnin Tehran . Kamanninka dana mahaifinka sak babu banbamci, Sunansa Sarki HINZUR IBN HUMAS" . Namijin gaske 1 Part 1B (c)shuraih usman @shuraih 99% NAMIJIN GASKE Littafina daya 1 Marubuci:- Shuraih Usman Typing:- Shuraih Usman Tel. 08133209890 Part B . Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa wannan labari ta ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan za'a kiyaye Copyright Shuraih Usman . Kimanin shekaru ashirin da suka gabata a birnin tehran , birnin tehran babban birnine wanda mutanen cikinsa yawancin sana'arsu itace Noman kayan Abinci iri iri, Kasuwar garin nacine a duk mako. Kuma daga wasu garuruwan sukan ziyarci wannan kasuwa a duk makon da zaici, . Al'umman birnin tehran ma'abota son zaman lafiya ne, A yayin da adalin sarkinsu hinzur bin humas, ya tsaya tsayin daka wajen yada zaman lafiya a duk sassan birnin . Sarki hinzur babban sadaulkine wanda duk ilahirin nahiyar babu sadauki kamarsa. Ya kasance yana da wani dan uwa mai Suna Humaiz bin Humas . Shi Humaiz yan uba suke da hinzur wannnan tasa ya kullaci hinzur sosai a cikin zuciyarsa, Wacce har takai ta komo So yake yaga bayan sarki hinzur sannan ya kwaci mulkinsa. Duk da kuwa alokacin matsayin wazirin tehran yake. Duk wani bakin ciki da hassada gami da kyashi da yake wa sarki hinzur bai taba Nuna wa a gabansa ba, hasalima irin biyayya da so da kauna da yake nuna wa hinzur kai kace tamkar da gaskece amma na ciki na ciki . Waziri humaiz yasan bazai iya tarar sarki hinzur gaba da gaba ba, don kuwa linzami tafi karfin bakin kaza. Hakan tasa yaje ya samu wasu yanfashi a wajen gari cikin wani kungurmin daji , nan take ya zayyane masu bukatarsa na son su taimakeshi su hada karfi da karfe, don su kawar da sarki hinzur a ban kasa. . Shugaban yan fashin mai suna kallabu ya dubi waziri humaiz bayan sun gama sauraron bayaninsa yace da shi , "Yakai wazirin birnin tehran hakika kazo mana da abinda muka dade muna jira tsawon wasu watanni, lallai kasani wannan taimako daka nema daga wajenmu tamkar mune muka nemi taimako daga gareka" Waziri najin haka sai ya cika da tsananin mamaki sannan ya dubi kallabu yace "shin kai kuwa wannan shugaba ta yanfashi meye dalilin ka na fadin hakan" Nan take Kallabu ya bushe da dariya saida yayi mai isarsa sannan ya dubi Waziri humaiz yace da shi "yakai humaiz kai sani cewa mun dade muna son ganin bayan sarki hinzur bisa takura mana da yayi, lallai zamu taimakeke ba tareda mun karbi ko kwandalarka ba, Abin dana ke jimana shakka iyace ta yaya zamu ratsa har mu shiga gidan sarki hinzur . Humaiz najin wannan tambayar sai yayi murmushi sannan yace" indai maganan shiga gidan sarkine toh lallai ina tabbatar maku shan ruwa ma ya fishi sauki a wajena, domin kuwa akwai wani hadimina da zansa ya jagoranceku har zuwa turakar sarki" ." Koda yamma tayi sai shugaban yanfashi da yaransa kimanin su dari biyar, sukayi shiri irin ta fatake sannan suka tasamma birnin tehran . Koda suka iso bakin kofan birnin tehran sai masu tsaron kofa suka tsaida su, Wani badakare wanda da alamu shine babba acikin dakaru masu tsaron kofan garin ya kusanto gaban wayannan yanfashi wayanda suka yi shirin fatake ya tambayesu "Yaku wayannan ayari su waye ku , sannan Me ke tafe da ku izuwa wannan kasa tamu mai tarin daraja" . Koda jin haka sai kallabu wanda yabadda kamanninsa ta hanyar nade wata katuwar rawani a kansa ya dubi wannan dakare yace "Yakai wannan mai tsaron kofan kasani mu fatakene sannan bada niyyar komai muka iso wannan birnin ba face don kasuwanci" Shugaban masu tsaron kofan yace "Wacce irin haja kuka dauko" Kallabu yai nuni da hannunsa ga bayansa wasu rakumane a kalla sunkai hamsin dauke da manyan sundukai a bayansu, Sarkin kofa ya iso gaban rakumi daya sannan ya bude sunduki daya daga cikin sundukannan , Babu komai aciki face kayan masarufi kama daga dangin zinare har zuwa kan su murjani da yakutu. Nan take shugaban masu tsaron kofa ya bada umarni da a bude musu kofa su wuce . Koda suka shigo birnin tehran basu zame ko ina ba sai cikin kasuwan garin , inda suna isa suka tarar da wani hadimin waziri humaiz . Wannan hadimi yai masu jagora izuwa wata babban gida ta sirri wacce ta kasance mallakin waziri humaiz ne. **** ***** Can cikin talaitainin dare kuwa dukkan wayannan yan fashin sunyi mugun shirin yaki. Kai kace yakin duniya zasuje Gama kimtsawarsu keda wuya sai hadimin waziri humaiz daya jagoranci su kallabu izuwa wannan gida ta sirri ya shigo garesu . Sunan hadimin KAMSAS kuma shine amintaccen hadimin waziri humaiz Kamsas ba karamin hatsabibi ba ne don kuwa duk cikin hadiman waziri babu wanda yake matukar ji dashi tamkar kamsas . Nan kamsas ya dubi kallabu yace " ya shugabana Muna iya tafiya yanzu" . Ta bayan gari suka bi gudun kar wani yaji takun sawaye ya yawaita ya farka daga barci. Ba a dadeba suka fara hango kofan gidan sarki, masu gadi na nan sai zagaye suke ta ko ina Koda kallabu yaga haka sai ya dubi kamsas "Shin ta ya ya kake ganin zamu ratsa wayannan da karu masu tsananin yawa wayanda na tabbata ko munyi nasarar gamawa da toh sai nayi asarar dakaru masu yawan gaske .daga karshe kuma in muka shiga gidan sarki ragowan sauran dakarunsa su karisamu. Kamsas na jin haka sai yayi murmushi sannan yace "ya shugabana kai dai ka tsaya zakaga ta yadda zamu samu nasarar shiga gidan kuma batare da mun raunata badakare ko guda daya ba" . Kamsas na gama fadin haka sai ya rike hannun shugaban yafashi kallabu sannan yace mai yai ma yaransa umarni da kowa ya rike hannun juna, Cikin dan kankanin lokaci sai gaba daya yan fashinnan suka rirrike hannuwan yan uwansu. Nan take kamsas ya fara fadin wasu kalmomi daga cikin yaren girkawa, Take sai wata guguwa bayyana , koda bayyanar guguwar saita nufosu tana zuwa wajenda suke sai ta suresu tai sama da su ****** ***** Marubuci:- Shuraih Usman Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman Company:- Shuraih 99% (c) shuraih Usman 2017 Typing:- shuraih 99% Namijin gaske 1 Part 1C (c)Shuraih Usman @shuraih 99% NAMIJIN GASKE Littafina daya 1 Marubuci:- Shuraih Usman Typing:- Shuraih Usman Tel. 08133209890 Part C . A cikin farfajiyar gidan sarki hinzur dakaru sai kai kawo suke duk da yake cikin darene amma farfajiyar gidan a haskake take yadda ko Allurace ta fadi sai anganta, . Ba zato ba tsammani sai gani akayi wata iriyar guguwa ta bayyana Gaba daya dakarun gidan suka mai da hankalinsu ga wannan guguwa, cikin kankanin lokaci guguwan ya lafa , koda bacewan guguwan sai su kallabu suka bayyana suna masu rike hannuwan junansu. Dakarun sarki hinzur na ganin bayyanarsu sannan sukaga dukkansu suna dauke da muggan makamai, Take sukayi kukan kura sannan suka zare makamansu daga cikin kufe, Sannan suka afka ma su kallabu, Su kuwa su kallabu koda ganin haka sai suma sukai kukan kura sannan suka falfala da gudu don su tarbi dakarun sarki hinzur, Nan aka rincabe da azababben yaki Farfajiyar gidan bakajin komai sai karafkiyar takubba da karajin Dakaru, jini sai malala yake tamkar an yanka wani babban dabba, Aikoda aka fara wannan yaki sai dakarun sarki hinzur suka raina kansu , domin yan fashin wani irin salon yaki suke ,sannan gasu da juriya dacin rai da naci, don sai kaga badakare ya zabga masu sara a jikinsu jini yayi fallatsi, amma sabida tsabar naci haka zasu cigaba da yakin . A yayin da dakarun sarki suka fahimci muddin akaci gaba da wannan gumurzu toh yan fashin na iya karar da su gaba daya, hakan tasa wani badakare mai matukar girman jiki ya falfala da gudu izuwa wani bangare na gidan, Koda ya je wajenda yake son zuwa . Wata irin dogon ginice mai tsayi wacce a samarta akayi mata rumfa, Irin wannan ginin ana amfani da sune ta hanyar ganin wanda yake wajen gidan sarki ko ta hanyar sada wani sako, ajikin ginin da kwaita iriyar matattakala ta katako, da isan wannan badakare sai ya kama wannan matattakala ta katako, ya fara hayewa izuwa saman birnin ko da yakai ga karshen ginin sai, ya dauki wata makekiyar mabushi, yana dauka ya kafata abakinsa sannan ya ringa busawa har tsawon wasu dakiku sannan ya saurara. . A yayin da ake tsaka da gumurzu lokacinda su kallabu suka fara cin karfin dakarun sarki hinzur Suna kara kusantar asalin babban kofan da zata sada mutum izuwa cikin falon gidan sarautar, , Alokacinne suka ji wata irin busa na tashi,koda kallabu ya saurari wannan busa sai zuciyarsa ta bashi lallai ba lafiya ba, hakan tasa ya ayyana aransa ya kamata suyi sauri su aikata abinda zasu aikata su wuce abinsu, Rashin sani tafi dare duhu, lallai da yanfashinnan sun san abin da zai biyo baya toh da sun gaggauta barin wannan gidan sarautar don ceton rayukansu, . Wannan busar bana komai bani illa busan Yaki, kuma sanar da mutane cewa gari babu lafiya. . Kwance yake bisa shimfidarsa daga shi sai gajeran wando, duba daya zakai mai kagane cewa yana jin dadin wannan baccin da yake Gabjejen katone baki amma bakinsa bawai irin baki kirin nan bane, , Ba kyakkyawa bane amma kuma ba a kirashi da mummuna ba, Yana da tarin damatsa, jikinsa a cure take a waje daya , Kamar acikin mafarki sai yaji wannan busa , zumbur ya mike sannan ya natsu don kara sauraron busar tabbas wannan busace dake tabbatarda cewa birnin nan na cikin tashin hankali, nan da nan ya sanya kaya ajinkinsa, sannan ya sanya sulken yakinsa, Ya daoki takobin sa ya rataya , sannan ya fito farfajiyar gidan Nan da nan ya nufi turkin dawakansa da zuwa ya haye kan wata bakar doki Take dokin tai rimi sannan ta fice daga cikin gidan. Wannan gabjejen mayaki ba kowa bane face sarkin yakin birnin Tehran mai suna ZABBAGI bin SHARMIL . Abin da su kallabu basu sani ba shine A lokacinda suka isa gidan sarki hinzur Dakarun da suke fada dasu dakarune masu kare lafiyan sarki su dubu daya, . Su wayannan dakaru basa rabuwa da wannan gidan sarautar sai sati yadda za'a canja da wasu su wayannan suje su huta . Acikin gari kuwa koda Mayaka da dakaru suka ji wannan busa , Nan da nan duk wani mayaki kuma dakare na wannan birni yayi shirin yaki sannan aka tasamma gidan sarki, Sabida karan busar daga cikin gidan take fitowa, Sarki hinzur na turakansa sai sharbar barci yake kwatsam sai yaji karar wannan busar acikin kunnuwansa Nan take ya mike daga kwancen daya ke , Koda ya fahimci busar na fitowa daga cikin gidansa ne sai ransa ya baci, Cikin kankanin lokaci gagarumin shigar yaki irin ta sarakai, ya dora takobin sa akan kafadarsa Cikin hasala da zafin rai ya bangaje kofan turakanshi take kofan ta fadi kasa shirim, Kofar na faduwa ya fito ya fara tafiya cikin izza koda yaga yayi tafiya mai dan tsayi amma bai hadu da dakarunsa ba, sabanin da, sai ya kara fusata nan da nan ya falfala da azabaBben gudu Cikin kankanin lokaci ya iso bakin babban kofan da zata sadashi da farfajiyar gidan, Cikin kunan rai ya daki kofan da kafansa take kofan ta fadi rikica , Kofan na budewa sarki hinzur yai arba da wayannan yan fashin sai ratattakan dakarunsa suke. Nan take ya kwala wata irin kara wacce tasa gabadaya mayakan suka tsaida yakin sannan sukai dubi izuwa wajen da yake tsaye . Yanfashin naganin haka sai suka falfalo da gudun tsiya don su afka ma sarki hinzur Sarki hinzur na ganin haka sai shima ya ruga da gudu don ya tarbesu, Koda ya rage baifi saura taku kadan ba tsakaninsa da yanfashin sai ya daka tsalle yai sama , a saman ne cikin zafin nama ya shafttare, Makogwaron yanfashinnan da sukai kansa su biyar. . Nan fa sarki hinzur ya cigaba da sara da suka baji ba gani duk inda ya nufa sai de kaga sassan jikin mutun na yawo bisa sararin samaniya, yadda kasan ana sassabe a gona, tabbas masifa ba' a samata rana lallai da mutum yana wajen yana ganin irin yanda sarki hinzur ke yiwa wayannan yanfashi kisan gilla toh daya tabbata lallai sarki hinzur ya cika NAMIJIN GASKE duk girman kato sai dai kaga yayi tsalle ya saka takobinsa ya farke masa ciki take zakaga jini yayi tsartuwa, cikin kankanin lokaci sarki hinzur ya kashe kasu biyu cikin kaso uku na yanfashin . Koda yan fashin suka fuskanci muddin aka cigaba da wannan yakin a haka toh tabbas nan da wasu yan dakiku za'a karar da su Ai nan take yanfashinnan suka fara neman hanyar tsira, cikin masifaffen gudu suka tasamma kofan fita daga gidan da nufin su fice daga gidan sarautar, Bazato sai gani sukai kofan gidan ta bude da kanta Budewar kofan keda wuya sai ga sarkin yaki zabbagu ibn sharmil da mayaka abayansa kimanin milyan daya , Nan fa sarkin yaki ya cigaba da fille kawunan yanfashinnan shi kallabu koda ganin haka sai ya hankalinsa yayi matukar dugunzuma take ya sadakar cewa ya rigaya ya mutu, Tsulum sai ganin Kamsas yayi ya bayyana agabansa yana baiyana ya kama hannun kallabu yana shirin furta kalmomin dazu kenan kawai sai gani sukai sarki hinzur ya baiyana a gabansu Cikin matukar hassala sarki hinzur ya daga takobinsa sama da nufin ya fille kan shugaban yan fashi kallabu da kuma kamsas , Koda Takobin tazo daidai saitin wuyan kallabu Sai........ . SAI ME SHIN AGANINKU KALLABU ZAI TSIRA DAGA KAIFIN TAKOBIN SARKI HINZUR KUWA . Namijin gaske 1 Part 1D (c)shuraih Usman @shuraih 99% NAMIJIN GASKE Littafina daya 1 Marubuci:- Shuraih Usman Typing:- Shuraih Usman Tel. 08133209890 Part D . Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa wannan labari ta ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan za'a kiyaye Copyright Shuraih Usman . Koda Takobin tazo daidai saitin wuyan kallabu Sai wata iriyar guguwa mai karfin tsiya ta bayyana cikin kankanin lokaci guguwar ta zuke kallabu da kamsas. . Koda ganin haka sai ran sarki hinzur yai matukar baci nan da nan ya auka wa sauran yanfashin da suka rage, Cikin kankanin lokaci aka karkashe dukkan yan fashinnan, A

Chapter 1 of 3