Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 2
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng HIKAHIKAYAR LAILA DA MAJNUN maimaici ne√ Hikayar Laila da Majnun an ba da ita kimanin shekaru dubu da suka wuce, kuma an bayar da ita ta fuskoki da dama, to amma dukkan fuskokin sun hadu akan ginshiki daya, watau tsarkakkiyar soyayya ce tsakaninsu. Ga irin hikayar da muka rairayo: Wani saurayi mai suna Qays ibn Mulawwah dan kabilar Banu Amar. Qays ya kasance mai fasahaf da basira a makarantarsu, sai dai ya kamu da soyayyar Laila bint Mahdi Ibn Sa’ad an fi kiran ta da Laila Amiriya, a hankali ya rika nuna mata soyayya ta hanyar kulawa da sauran alamu. Duk lokacin da ta makara zuwa makaranta sai hankalinsa ya tashi ya rasa sukuni, gaba daya sai ya zuba wa kofa ido ba ya mayar da hankali ga karatunsa. Wata rana da zuciyarsa ta cika da bege, ya ji kirjinsa kamar ya fashe, bai san lokacin da ya rika rubuta sunan Laila a takardar rubutunsa ba maimakon abin da ake koya musu. Dalibai da suka ga haka sai suka hakikance lallai ya yi nisa wajen kaunar ta. Da haka ita ma Laila ta soma kaunarsa ya zamana duk makarantar an san su a matsayin masoya. Shi Qays kamar tun yana yaro k’arami masu ilmin taurari suka bayyanawa mahaifinsa cewa zai kasance wanda rayuwarsa za ta fada cikin wahala da musiba. Suka kara da cewa idan ba a yi da gaske ba ma zai iya haukacewa. Tun daga wannan lokacin mahaifinsa ke samo masa lak’ani da magunguna da addu’oi. Yayin da ya data sai mahaifinsa ya dauke shi ya kai shi Dimashka karatu inda anan ne ya hadu da Laila. Ita Laila ta kasance ‘yar shugaban kabilar Sharwaris, wadda a da zamanin Jahiliyya ba sa ga maciji da kabilar su Qays. Laila da Qays suka zama tamkar jini daya tsoka daya idan bai ga daya sai ya kama rashin lafiya, amma Qays abin na sa ya fi tsanani, domin kuwa har wakoki yake rubutawa masoyiyarsa yana karanta su a ko’ina. Daya daga wakokin da yayi mata ita ce: Na so ki ya mai kyau dan gaske Wane wata ko tauraro mai haske Kin shiga ruhina kin mammallake In babu ke to ni kuwa na hakkake Ba za ni rayu a duniyar nan ba A makaranta aka rinka gulmar su ana nuna Majnun duk inda ya wuce, sai ya kasance idan ka yi masa abu ka ce masa ya yi hakuri don Laila, shikenan zancen ya wuce. Da dalibai suka gano lagonsa, suka rika dauke masa kayan rubutu suna cewa ya basu domin darajar Laila. Ba musu sai ya ba su. Maubin (malamin) makarantar ya damu kwarai da irin wannan al’amari. Musamman da ya ga Qaysa wanda yanzu sunan ya bace ya koma Majnun Laila (Mahaukacin Laila) ya rubutawa iyayensu takarda yana fadakar da su halin da ‘ya’yansu ke ciki. Iyayen Laila suka cire ta daga makarantar aka kirawo wani kwararren malami yana koya mata karatu a gida. Ciwon so ba shi da magani! Maimakon hakan hakan ya yi magani sai ya dada rikita al’amari. Majnun ya daina karanta komai kullum sai kuka sai waka, duk abin da ya gani sai ya ga yana masa gizo da kamannin Laila. Nan da nan sai ya soma rera wakar so gare ta. Mahaifin Majnun ya zo takanas ya dauke shi zuwa wajen likitoci da ‘yan tsibbu da bokaye da sauran masu da’awar magani duk abin ya zama tamkar wutar kara ana yayyafa mata fetur. Abokai da ‘yan uwa na kusa da na nesa suka zo domin tausasa zuciyar Majnun ya daina tunanin Laila amma duk a banza. Wani daga baffaninsa ya ce masa, “wai kai Qays me ka gani a jikin Laila da ka nace mata haka? Ka zo mu je na nuna maka mata dubu wadanda suka fit a kyau da kyan fasali da asali da mulki da dukiya da sarauta ka zabi wadda ta yi maka.” Majnun ya dube shi ya girgiza kai ya ce, “idanun Majnun Qays ba wanda suke so da gani tamkar Laila.” Ya daga hannu sama ya ce, “Ya Allah! Na san ba ka yi kyakkyawa a duniyar tamkar Laila ba. Na tabbata ita tana daga asalin Hurul Aini da suka zo duniya shan iska. Ya Allah alk’awarinka bay a tashi, na tabbata daga kan Laila ba zaka sake wata kyakkyawa ba. Ya Allah ka ba ni Laila!” Wani daga kabilarsu ya ba shi shawarar ya dauki Majnun zuwa Makka ya yi roko a ka’aba kan Allah ya dauke masa son Laila a zuciyarsa. Amma saboda tsananin soyayya a yayin da suka je dakin ka’aba sai mahaifinsa yace masa: kama tufafin ka’aba ka roki Allah ya cire maka son Laila sai Majnun ya kama yace: “Allah na tuba gareka daga dukkan laifi, amma bazan tuba daga son da nake yiwa Laila ba . . . Ya k’ara da cewa, “Ko Luqman, babban malami masani na tabbata ba shi da maganin ciwon so…Idan ma yana da shi ina fata babu wanda ke tsakanina da Laila. Ya waka wadannan baitoci: A Makka na ce da shehin malami, Wai shin wace ke cutar da ni? Shin laifi ta ke yi to a sanar da ni, Shehi ya ce “d’ana bi a hankali, Azaba na nan zuwa can gare ta Na yi farat na ce masa “a’a na yafe, Da azaba ta samu Laila ko a gefe, Ba ni kauna gara ta same ni a lafe, Da na daina sonta a barci ko fake, Gara na mutu da ciwon kaunar ta Sannan ya ce da murya mai raurawa, “Allah ka ba ni Laila!” GO BE ZÀMU DAURAHIKAYAR LAILA MAJNUN...2 Yayin da iyayen Majnun suka ga haka kullum lamarin nasa k’ara lalacewa ya ke yi, sai suka ga babu mafita face su je su nemi auren Laila wurin iyayenta. Wannan shine mataki na k’arshe da suke ganin zai magance matsalar d’ansu. Suka tashi jakadu na musamman zuwa garin su Laila suka bayyana musu irin halin da d’ansu yake ciki game da soyayyar Laila. Sannan jakadun suka nemi aurenta dominsa. Iyayen Laila suka amsa da cewa, “mu a wajenmu abin da Majnun yake yi domin ‘yar mu wulak’anci ne mai girma. Kuma duk da yake mun san cewa Laila tana da ra’ayinsa amma ba zamu iya aurar da ita gare shi ba. A dalilinsa mun cire ta daga makaranta, mu a wajenmu, mahaukaci ne kad’ai zai rik’a irin abinda Majnun ke yi.” Da haka iyayen Majnun suka ji dad'i tunda su a tsammaninsu idan har ya daina shiririta za su amince su aura masa ita. Saboda haka suka shiga tausasarsa suna ba shi shawarar ya nutsu ya daina abubuwan da yake. Majnun ya amince da haka, amma da sharadin za a kaishi ya ga abar k'aunarsa Laila. Suka shirya suka tafi tare da wakilansa zuwa garin su Laila. Aka sauke su a wani babban gida sannan aka kawo musu abinci da abinsha. An kawata wajen da fitilu masu launi iri dabam - dabam. Sannan a kunna turaren wuta ko'ina sai kamshi ke tashi. An jera kasake masu yawa cike da abinci da fulawoyi masu k'ayatarwa. Zuciyar Majnun kuwa ta kasa nutsuwa, ji yake kamar yayi tsuntsuwa ya tafi ga masoyiyarsa. Bai iya jurewa ba sai ya mik'e a gaban waliyan Laila ya rika safa da marwa yana rera wadannan baitoci: Na yi nisan zango don na gane ki, Ga shi na zo nan ina ta bid'ar ki, Ina kike ina kika shiga ne in ganki, Zuciyata tana ta jidali domin nemanki Ya ki taho abar begena don Allah nunan kanki Jimawa kad'an sai ga karen da Laila ke zuwa da shi makaranta ya shigo gidan. Majnun sai ya ji ya kasa jurewa, ya zabura wajen karen nan ya rungume shi yana sumbatarsa yana cewa, "Na ga rabin Laila saura rabin. Ya karen nan mai baiwa maza je ka ingizo min Laila." Garin wutsulniyar da kare yake yi da k'afafu ya ture farantan abincin, suka bata gaban rigar wani dattijo mai fada aji a dangin Laila. Shi kuwa gogan naka sai ya d'auki wani tsiron fulawa ya mak'alawa karen a wuya yana ce masa, "maza je ka kaiwa Laila ka mik'a min gaisuwata gare ta." Duk jama'ar wurin suka yi tsit suna kallon ikon Allah. Wakilan da suka rako shi suka rasa inda zasu sa kansu domin kunya. Wakilan Laila kuwa suka cika da fushi iyakar fushi. Wani daga cikinsu ya fusata ya ce wa Majnun, "Shin bautar kare ka zo ko kuwa maganar aure?" Kai tsaye Majnun ya kalli mutumin ya ce, "wannan karen a wurina ya fi mutum dubu daraja, domin a jikinsa ina ganin surar masoyiyata wadda k'aunarta ke d'amfare a zuciyata dare da rana." Duk wuri aka d'auki salati. Jama'a suka rik'a zundensa suna cewa ya haukace. Dattijon nan da aka b'atawa riga da abinci ya mik'e a fusace ya fice daga gidan. Duk jama'a ma suka watse. Da wannan jama'a suka rika rantsewa cewa haukan nan dai bai rabu da shi ba, sai ma abin da ya yi gaba. Daga nan iyayen Laila suka fito kai tsaye suka ce ba zasu aurar da 'yar su ga Majnun ba. To daga nan sai duk wani fatan samun nutsuwarsa ya zama sharon gayya, suka hakikance ba za su iya magance masa matsalar ba, don haka suka sa masa albarka suka kyale shi bisa halinsa. Shi kuwa duk inda ya shiga lungu da sak'o sai ya rik'a cigiyar Laila ko sun san inda take da yadda zai sadu da ita. A haka har ya yi kicibis da wani jakada mai aikin raba takardu. Ya tambaye shi labarin Laila. Jakada ya ce masa Laila da iyayenta sun tashi daga garinsu sun koma wani gari mai nisa, daga nan garin zuwa can tafiyar mil dari da ashirin ne. Majnun ya shiga yi masa magiyar yana ba shi sako zuwa gare. Jakada ya amince zai karb'I sak'on takarda kurum babu wani abu. Majnun ya zauna yayi ta rubutun shafuka da yawa, har jakada ya gaji ya ce masa, "wacce irin wasika ce haka?" Majnun ya ce, "wasikar soyayya ce bata da k'arshe." Jakada ya yi dariya da haka sannan ya ce, "to samu waje ka d'iga aya ka bani na tafi." Majnun ya nad'e takardar ya ba shi. Sannan ya nemi ya yi masa rakiya kad'an. Suna tafe Majnun na ba wa jakada labarin abar k'aunarsa Laila shi kuma yana ta mamaki. Sai da suka shafe mil goma Majnun na tafiya a k'asa Jakada na bisa rak'umi. Jakada ya ce masa, "to ka koma haka, ka yi nisa kwarai da gidanku." Majnun ya juyo ya soma tafiya sannan ya juya ya ce da Jakada da babbar murya, "ya kai k'aunataccen abokina! Wallahi na yi mantuwar wani muhimmin sak'o da nake so na rubuta mata!" Jakada ya ce, "to gaskiya ba zan tsaya ba, sai dai ka fad'a min da baki na fad'a mata. Majnun ya kowa ya same shi suka rankaya. Suna tafe yana fad'a masa sak'on har suka share wasu mil goman. Jakada ya ce, "ka koma haka kada a neme ka a gidanku." Ya juyo ya soma tafiya sannan ya waigo ya ce, "wallahi ba domin kada ka ce na matsa maka ba da na k'ara maka wani sak'on. Muhimmi ne kwarai na mance da shi. Jakada ya ce, "to matso ka fad'a min!" Suka sake rankayawa yana ta fad'a masa sak'o. Haka suka yi ta yi har kafin su ankara sai ga shi sun isa garin da Laila take. Jakada yayi mamakin irin wannan soyayya, sannan ya ce da Majnun, "Babu buk'atar kai wa Laila sak'o gare ni domin kuwa ga shi mun zo garin da take." Da jin haka Majnun ya cika da farin ciki da murna. Ya fad'i sumamme don tsananin farin ciki. ZAMUCI GABA INSHA ALLAHU GOBE" Whatsapp only 08071051138^ LAILA MAJNUN...3 ^•^ Bayan ya farfad’o jakada ya ce masa, “ba na so a ganka, domin jama’a na iya kama ka su yi maka wulak’anci kafin ka ga Laila. Ga wani kango can ka shiga ka zauna a ciki ka huta domin ka yi tafiya mai yawa. Zan isar da sak’onka ga Laila yanzun nan.” Majnun ya yarda da shawarar jakada ya shiga kangon nan ya zauna zuciyarsa na harbawa kamar ta tsage. Sakamakon tafiyar da ya sha duk yayi futu – futu. Tufafinsa sun yi jawur da k’ura, gashin kansa duk ya kukkulle, ga kafafunsa sun yi fato – fato da kura da faso da kaushi. Ga shi nan dai yarbajila da shi. Duk da haka, da ya tuna cewar yana garin da Laila ta ke gaba d’aya sai ya ji ransa ya yi fari fat. Ya cika da murna da farin ciki, zuciyarsa ta cika da bege ya rik’a rera wak’a yana cewa: Na aika sako na wajen masoyiya, Zuciyata da rayukana gaba daya, Na mika su dukansu wajenki gimbiya, Ke ce tawa hakika na fadi gaskiya. Na sallama miki kaina lahira da duniya. Daga nan sai gajiya ta kama shi, ya ji yana so ya kwanta. To amma sai ya rika tunanin shin a wanne bangare Laila take? Domin baya so ya kwanta inda k'afarsa zata rika kallon jihar da take domin a wajensa hakan cin amanar kauna ne. Zai iya shurinta bai sani ba. Ya tsaya yana tunani, shin tana gabas ne ko yamma ko kudu ko kuwa arewa? Duk inda ya sa kansa sai ya tuna kila a wannan bangaren take, sai yayi maza ya sake waje. Daga baya dai sai ya samo igiya ya daura a kafarsa ya samu gini ya daura kafar, yana zamana yana reto kamar jemage. A wannan yanayi kuma bai fasa rera mata wak'a ba yana cewa: Hajjina da Umarata na wajenki, Makka ta da Madina sune ganinki, Baitil Mukdis wurina murmushinki, Arzikina duk ni dai in ga dariyarki, Na sallama kaina gaba wurinki Kishin ruwa na damunsa amma babu ruwa a kurkusa, haka ya hakura wutar bege na hura shi, tana kone masa sassan jiki da zuciya. Jakada ya yi sallama k'ofar gidansu Laila ta fito, ya ce mata, "na yi kokari da gaske domin na yi miki magana, game da masoyinki Majnun wanda ban taba ganin tamkarsa ba a fagen so." Ya kwashe labarin duk yadda suka yi ya fad'a mata. Sannan ya kara da cewa, "yanzu haka na bar shi a bayan gari domin gudun kada a wulak'anta shi idan jama'a suka ganshi." Da Laila ta ji haka sai tausayinsa ya kama ta. Ta tafi wajen uwar goyonta ta ce mata, "me yake faruwa ga mutumin da ya yi tafiyar mil dari da ashirin a kasa ba tare da ya huta ba?" Tsohuwa ta ce, "wannan mutumin ba zai rayu ba mutuwa zai yi." Laila na jin haka sai ta ji ta shiga damuwa, ta sake ce mata, "babu wani magani?" "Magani daya ne a sanina. Dole ya sha ruwan saman da aka ajiye shi akalla shekara d'aya, kuma dole ruwan ya zamana maciji ya sha daga gare shi. Sannan ya daura igiya a kafarsa ya zamana kansa na kallon kasa zuwa wani lokaci. Idan ya aikata hakan watakila zai tsira da ransa." Da ta ji haka sai ta yi tagumi tana cewa, "wannan magani akwai wahalar samu, kai ba ma zai yiwu ba." Ta d'aga hannu sama tana rok'on Allah ta ce, "Ya Allah mai kulla soyayya, mai bayarwa mai hanawa ka taimaki Qays Majnun ya samu wannan magani." Ta shafa sannan ta yi ajiyar zuciya ta ce, "soyayya bata da magani sai ita kanta." Allah da ikonsa, Majnun na rataye da kafarsa a sama ga kishirwa na addabarsa sai ya kwance igiyar ya tafi neman ruwa. Bai samu ruwa ba sai wani tsohon kasko a wani lungu. Ya tarar wani zabgegen maciji na shan ruwan. Ya kore shi sannan ya kafa kai ya shanye ruwan gaba daya. Ya samu waje ya zauna yana wake - wakensa. Da gari ya waye Laila ta shirya abinci mai rai da lafiya ta kirawo kuyanga a boye ta fada mata komai sannan ta nemi ta kai wa Majnun inda yake a bayan gari. Kuma ta bata sakon a fada masa cewar ita ma tana nan tana kaunarsa kuma tana son ganinsa, amma da zarar ta samu dama zata zo ta ganshi. Yayin da kuyanga ta je wajen sai ta tarar da mutane biyu. Daya ya hada kai da gwiwa kuma duk ya rame ga kansa nan duguzunzum, dayan kuma mai kiba jawur da shi, sai dai ya manyanta. Kuyangar ta dube su duka biyun ta ga babu wanda ya cancanci Laila ta so shi. Ita kanta ma ta ji duk basu kwanta mata a rai ba, balle kuma Laila. Duk da haka domin cika umarni sai ta ce, "a cikinku waye Majnun?" Mai kibar ne kadai ya ji sai ya taso wajenta ya ce, "me ya faru?" Sai ta nuna kwandon abinci ta ce, "cewa aka yi na kawo masa wannan daga Laila." Nan da nan ya karbe abincin yana cewa "ni ne Majnun." Ta fada masa sakon Laila ya yi mata dan wasa haka sannan ya sa abinci a gaba ya cinye. Ya ragewa Majnun dan kadan. Daga wannan rana kullum sai ta kawo masa abinci da sakon baka, shi kuma sai ya cinye ya rage kadan domin Majnun. Kullum Laila kan tambayi kuyanga, "me ya ce ki fada min?" Sai kuyanga ta ce, "wai ya gode madalla da abinci." Laila ta shiga kokwanto anya kuwa Majnun dinta ne? Bayan kwana uku dai da ta gaji sai ta ce da kuyanga, "yaya kika ga kamannin Majnun din?" Kuyanga ta ce, "wani mai kiba yana da saje da kasumba...ya manyanta..." Farat Laila ta ce, "wallahi ba shi ba ne, wannan jakada ne wanda ya kawo min sakonsa. Majnun ba tsoho ba ne kuma ba shi da kiba." Ta dubi kuyanga ta ce, "su nawa ne a wurin?" Kuyanga ta ce, "su biyu ne." Laila ta yi ajiyar zuciya ta ce, "to yau ba za a kai abinci ba, amma zan sa ki musu wata jarrabawa domin mu gane Majnun na gaskiya." Ta bata wuka ta fad'a mata abin da zata yi da ita. Kuyanga ta tafi wajensu Majnun, ta tarar da jakada na tsaye yana jiranta. Tana zuwa ya soma yi mata sannu da zuwa. Ya mika hannu da nufin ya karbi gara, maimako haka sai ya ga ta fito da wata sharbebiyar wuka. Ta ce, "Laila bata da lafiya, ana bukatar jinin masoyinta kwalba daya wanda da shi za a hada maganin. Shi yasa na zo wajenka na diba." Yana ganin haka sai jikinsa ya kama rawa ya ce, "to ni dai ba masoyinta ba ne, kuma ba ni ne Majnun ba, gashi can a zaune." Ta wuce zuwa wajen Majnun ta fada masa kamar yadda ta fada wa Jakada. Yana jin haka ya karbi wukar da hanzari, ya sumbace ta sannan ya ce, "na gode wa Allah da ya kaddara cewa jinina ne zai warkar da ciwon masoyiyata." Ya darzaza wukar a hannunsa. ZAMU GABA INSHA ALLAHU^•^LAILA MAJNUN...4^•^ Maimakon jini ya zubo sai wajen kurum ya yai farat fat, alamar babu jini. Ya sake keta wani wajen, nan ma babu jinin saboda bai ci abinci ba ballantana a samu abin da ake buk'ata. Da ya ga haka sai ya soka wukar a hamatarsa inda babbar jijiyar jini take, nan jinin ya rika kwarara. Ya tara ya mik'awa kuyangar wadda tuni tsoro da mamaki sun hana ta motsi. Yayin da ta koma gida ta shaida wa Laila irin abin mamakin da ta gani wajen Majnun, sai Laila ta yi ta kuka tana tausaya masa. A cikin gari kuwa, labarin Majnun ya cika gari, sai aka samu wasu shakiyan matasa suka dauko kulake suka nufi inda yake. Tun daga nesa da Jakada ya hango su sai ya hau taguwarsa ya sulale ya bar Majnun yana wake - wakensa yadda ya saba. Matasan na zuwa suka hau bugunsa suna shuri da naushi da yakushi. Suka daure shi da igiya sannan suka tsaya daga nesa suna jifarsa. Da Laila ta ji labari sai ta sheko da gudu ta zo ta kare shi daga bugun mutane, ta rika zaginsu tana korarsu. Shi kuwa duk da yana daure ga bugu da ya sha amma sai ya ji ransa ya yi fari fat da ganin abar begensa ya rika ambaton sunanta yana cewa: Laila, Laila, Laila tawa ce, Domin akanki ne na haukace, Wasu na kallona wai na karkace, To amma fa yau na samu dace, Da ganin haskenki ya masoyiya Iyayen Laila suka turo aka tafi da ita gida tana kuka. Da suka ga lamarin ya wuce saninsu sai suka yi shirin yin balaguro na wani lokacin. Domin a tsammaninsu idan suka tafo suka jima Majnun zai gaji da nemanta har ya saduda ya hakura. Suka shirya kaya suka tafi wani gari da basu ambata ba, gudun kada ya ji ya bi su can. To amma kafin su tashi Laila ta rubuta takarda a boye ta ba wa kuyangarta ta kaiwa Majnun. Ya bude ya karanta cewar Masoyina, bulaguro za mu yi wani gari mai nisa, haduwar mu zata yi wuya anan. Idan zaka iya mu hadu a zangon farko cikin sahara. Yana gama karantawa ya ce da kuyangar, "ki gaishe ta da kyau da kyau, kuma ki fada mata cewar ina nan tafe." Lokacin da su Laila suka sauka a zangon farko ta tafi ita da kuyangarta zuwa inda ta ce masa ya je zata same shi. A tsammaninta bai isa ya zo wurin ba a wannan lokacin, domin su a abin hawa suke, shi kuwa a kasa yake. Tana zuwa ta same shi ya hada kai da gwiwa yana ta kiran sunanta, "Laila! Ya Laila!! Ya Laila!!!" Ta karaso wurinsa tana mai cewa, "Ya Majnunun Soyayya ga Lailarka ta iso!!l duwatsun kusa da na nesa suka dauki muryarta tana amo. Nan da nan ya zabura zuwa gare ta, yana mai cewa, "shin da gaske ne Laila ke ce anan?" Ta amsa "ni ce!" Ya mika mata hannu ta rike sai suka ji kururuwar mahaifanta suna nemanta domin a cigaba da tafiya. Ta juya da hanzari, ya ce, "Haba Laila kada ki tafi ki bar ni da begenki!" Ta ce, "kar ka damu, idan na dawo za mu hadu anan." "Yaushe za ki dawo?" Ya tambaye ta. Ta ce, "ban san lokacin ba, amma da zarar mun taho zan aika maka." Da haka ta tafi ta bar shi anan. Majnun ya ce a ransa, "idan ta dawo wa zata aika ya fada min? A ina dan sakon zai same ni? Kawai bari na zauna anan din har sai ta dawo." Ya share wuri ya zauna ba shi da wani abinci sai ganyen bishiyar da ke wajen yana shan ruwa dake bubbugowa karkashin dutse. A kullum zancensa shine kiran sunan Laila da addu'ar ta dawo ta same shi. A haka har tsiron bishiya ya fito daga 'ya'yan itacen da yake jefarwa, ganyenta ya nannade masa jiki ya zama tamkar bishiyar a jikinsa ta tsiro. A can garin da su iyayen Laila suka je da ita kuwa, sai wani attajiri ya fito yana sonta da aure. Nan take ya bawa iyayen rakumma dari gami da wasu kyautuka masu yawa. Da Laila ta ga alamar laila za a aurar da ita gare shi sai ciwo ya kama ta. Ta yi ta fama, iyayen suka yi nufin komawa gida domin magani alabarshi idan ta warware sai a yi auren. A hanyar su ta dawowa suka sauka a wannan zangon. Duk da tana fama da jinya Laila ta taso zuwa wurin da suka yi alkawari da Majnun. Ta kusa isa kenan ta gamu da wani mutum ya ce mata, "yarinya kada ki je wurin nan da kika nufa. Akwai wata fatalwa mai kamar bishiya da ta bayyana. Kullum tana kiran sunan Laila, Laila." Da ta ji haka sai ta tabbatar Majnun ne bai tafi ba. Ta karasa wurin da gudu. Yana ganinta yayi zumbur ya mike tsaye yana mai farin ciki, yana cewa "Laila kin cika alkawari? Laila ke ce kuwa? Laila za ki aure ni??" Kasancewar ya jima sosai a zaune baya mikewa sai jiri ya debe shi, a lokaci guda kuma zuciyarsa ta buga saboda tsanannin farin

Chapter 1 of 2