Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

ALIYU HAYDAR Complete Hausa Novel Document by ALIYU HAYDAR


ALIYU HAYDAR

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 40198



ALIYU HAYDAR

Reading Time: 3 Hours

Added On: 27, Apr 2025

Author: Khausar M Hassan ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : +2347067465637

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 226.76 kb

File Type: txt

Views: 181+

Download: 219+

Last download: 5 hours ago

Description/Story: [11/15, 4:56 PM] Kausar~Luv: [7/29, 11:50 AM] Kausar Luv💞: *ALIYU_HAYDAR*
Page ((1))

©Kausar M Hassan

Bismillahi Rahmani Raheem!

"Alhaji dan darajar Allah kayi hak'uri ni bansan laifin da nai maka ba, mai ya kawo maganari saki"???
Cewar yar matashiyar matan dake tsaye a gaban wannan dattijon, wadda ta kasance ita ba fara ba ita kuma ba baq'a ba, shekarunta bazasu wuce 30 ba.
"Hajiya na fad'amaki cewan na' sakeki saki daya saboda hka idan Allah y baki miji kiyi aure"
Yana gama fad'in yaja rigarsa fuuu y wuce.
Kai kawea ta girgizah saboda tasan tabbas mutum baya tab'a wuce kaddararsa, hakan yasa ta koma d'akinta ta tattara kayanta a cikin jaka ta had'a ta dau mayafinta ta fito, zuciyanta cike da k'una da bakin ciki, tana kawowa tsakiyan gidan d'anta na dawowa dga makaranta, jakar makarantar shi ya yarda akasa, da gudu ya isa gareta.
"Mame tafiya zamuyi ne naganki da jaka a hannu"?
Rage tsayenta tai dea2 nashi tasa hannunta ta dafa kanshi
"Aliyu ba tafiya zamuyi ba, nidea zan tafie, kuma a nan zan barka, ina mai maka nasiha da kazama namiji, kazama mai hakuri da juirya akan duk abunda zai biyo bayanka"
"Mame dan Allah kada ki tafie ki barni, wallahi zan rik'a jin magana, bazan k'ara fasa kwano ko d'aya a gidan nan ba, zan rik'a share ko ina, mame dan Allah".
Rungumeshi tai tana zubar da hawayen rabuwa da d'anta, wanda yake shine sanyin idaniyanta.
"Aliyu ni wnnn duk baya damuna, ko wanne yaro haka yake, hasali ma ni kullum addu'ah nake maka akan Allah ya shiryaka, nasan kuwa Allah zai amshe addu'ahta"
Gyaran muryan da tajine ya katsie mata zancen da takeyi
"Kai zubairu amso min yaron chan" ya fad'a murya a fusace.
Zubairu dake kusa dasu, yasa hannu yana raba uwa da d'anta.
Zubairu ya amsheshi, hajiya ta juya ta nupie kopan dake fita gidan.
"Mame dan Allah ki dawo kada ki tafie, mame!!!".
Haka ta fice ta barshi a gidan zuciyoyinsu cike da tarin bakin ciki mara misaltuwa...
[7/29, 11:50 AM] Kausar Luv💞: *ALIYU_HAYDAR*
Page ((2))

©Kausar M Hassan

Ganin baida mafita sea ta Allah, yasa ya cigaba da huci kaman wani sabo zakin daya fito neman abunci, hannun zubairu ya garzawa cizo, wnda hakn yay sanadiyar sakinshi da zubairu da yay, da gudu y haura gidan saman, ya bud'e wani d'aki wnda da alama wannan shine d'akinshi, banka kopar yay ya maida y kulle da padlock ya hau kan d'an karamin gadonshi ya kwanta ya cigaba da kuka.
Alhj baiji dad'in kasantuwar hakan ba, shi kanshi baisan maisa yay hkn ba.
Cike da tak'aicin abunda ya aikata y kama hanyar shiga d'akinshi. Wata mata na hango fara tas da itah, iya inda akeso mace takai to ta kai, sanye cikin dogowan riga bak'a tasa dan k'aramin hijab, da baqaqen takalmi, chewing gum ne a bakinta tana tauna Karas_karas.
Ganin Alhj da tai yasa taja ta tsaya chack kaman gunkin da aka ajiye.
"Alhj ina hajiya salma"?
Shiru yay jim kad'an tukkuna ya nisa
"Na saketa hajjah rabi, kuma nace idan ta samu miji to tayi aure.
Kirji ta daka cike da nuna rashin jin dad'i fal a fuskanta
"Haba Alhj dan Allah, kayi hkuri ka dawo da ita mana mai yay zafi haka shi ba wuta ba"?
A fusace ya bata amsa
"Kinga na gama magana, kuma bana so a k'ara dawomin da ita farko"
Zatayi wata magana ya ra6ata ya wuce, kai ta girgizah tukunna ta qaraso tsakar gidan, ganin jakar Aliyu da tai yasa ta tabbatar da cewan ya dawo dga makaranta.
"Zubairu!!!" Hajjah ta hau kiran sunanshi
Jiki na rawa ya amsa kiran da take masa
"Na'am hajiya gani" ya karaso kusa da ita cikin ladabi.
"Aliyu y dawo dga makaranta ne"?
"Eh hajjjah ya dawo"
"Yana inane"?
"Yana d'akinshi hajiya"
Alama tai masa da hannu wadda ke nuna cewan ya wuce, da sauri y kama hanya y bar falon.
Hajjah rai a 6ace ta hau gidan saman, dai_dai d'akin aliyu taja ta tsaya, a hnkli ta fara kwan_kwasa kopar.
Aliyu daya riga ya hasala ya fara magana
"Wanene"?
"Aliyu nice mamanka ka bud'e kopan nan"
"Nifa ummi bazan bud'e ba sea abbi ya dawo min da mame"
Shiru tai tukkuna ta qara cewan
"Ka bud'e d'ana zan maka komai kake so kana so kasa mamanka kuka ne, kasan idan bana ganinka bana jin dad'i'
Cikin muryar shagwa6a ya bud'e baki
"Ummi zaki hana anty nana ta daken"
"Na maka alkawari bazata kara dukanka a gabana ba kaji aliyuna jan gwarzo zakin fama, ka bud'e dakin".
Tasowa yay ya bud'e dakin, da gudu ya fad'a jikin ummi, ummi ta rungumeshi sosai, a jikinta ya matuqar bata tausayi har a cikin zuciyanta"
"Yi shiru d'ana ka deana kuka, ga umminka nan tare dakai, zan baka dukkan gatan da mame dinka ke baka kaji ko"?
Kai ya d'aga tare da cewan
"To ummina"
Murmushi tai masa taja hannunshi zuwa d'akinta.
Tana isa ta tarar da nana zaune a d'akin, cike da hasala ta taso akanshi
"Ummi ya zaki shigo mana da yaron nan a d'aki sarai kinsan bayajin magana ynxn nan zai fara fasa mana kaya"
"Ke"! Ummi ta daka mata tsawa
"Bana son iskanci da d'iban albarka, ke kinsan da ya nai renonki ne, kowanne yaro haka yake, kurciya ce idan yay ta kuma zata wuce, komai lokacine"
Nana ta dubie aliyu ta dubie ummi
"Naji ummi amma gskya nifa...
"Kefa mi? Bazaki zauna da d'an uwanki lpy bane? Tsaya kiji wallahi nai maki iyaka da yaron nan, fice ki bani guri'

Baki ta tunzure ta kama hanyar fitah dga d'akin, yayinda ummi ta juya ta dubie Aliyu
"Kada ka damu kaji d'ana mamanka na nan tare dakai"
Mujie in baka chocolate"
Murmushi yay ya saki ranshi, suka wuce chan kuryar dakinta
Yayinda Nana tai d'akinta ta maida ta kulle, zuciyanta nai mata k'una sbd ita a duniya ta tsani aliyu, bata sonshi ko kad'an a cikin rayuwanta...
Meye dalilil"?...
®Kausar Luv💞
[11/15, 5:18 PM] Kausar~Luv: *ALIYU_HAYDAR*
Page ((3))


©Kausar M Hassan

A chan bangaren hajiya salma kuwa tana fitah dga gidan kai tsaye taxi ta tsayar tasa jakarta a ciki.
"Malam mai taxi unguwar shanu zaka kaini"
"To hajiya"
Suka kama hanya sea unguwar shanu, suna isa dea2 kopan gidan da zata shiga ta tsayar da mai taxi di'n ta ciro kudi'nshi naira d'ari ta bashi, ta dauki jakarta, dea2 kopan ta tsaya tana kallonshi, rabonta da gidan tun ranar da aka sata lallen aurenta sea kuma yau datazo, kuma zuwan bana wuni ba na zama gabad'aya, hawayenta ta share tasa kafanta a gidan daya kasance matsakaici tare dayin sallamanta.
Yar dattijowan dake zaune akan kujera ta d'ago idanunta, ganin "yarta da tai yasa ta d'ago ta dubeta
"Salma ina Aliyu"?
Wannan shine tambyan da tafara yimatah
Kuka ta fashe dashi tai zaune dirshan akasa
"Mama alhj ya sakeni, kuma yace "idan nasamu miji inyi aure".
Dattijowan ta girgizah kai
"Bkomai salma Allah yasa haka shine mafi alkhairi, dauki jakarki ki shiga da ita dga ciki"
Hakan ko akayi ta dauki jakarta ta shiga dakin da rabonta dashi shekara goma shaa biyu. Rayuwa kenan.

Karfe takwas na daren wannan rana ta alhamis.
Aliyu ne kwance akan kafafun ummi, yana wasa da d'an super man d'in roba, anty nana ce ta shigo a d'akin ta zauna kusa da ummi.
"Ummi abbi na kira"
Ummi ta tashi zaune ta dubie aliyu duba na soyayya
"Aliyu ka jirani ynxn nan zan dawo, bance kai fad'a da kowa ba, kaji ko?
Kai y girgizah ya cigaba da magana dashi da super man dinshi kaman ynda yake daukan yanayi.
Ummi ta kama hanyar fita d'akin yayinda ya rage dga anty nana sea aliyu.
Kallonshi tai tun daga sama har k'asa ta watsar tasa hannu ta rik'e masa kunne
"Kai dan ubanka waye yace ka shigo d'akin nan"?
Shiru yay, yaja jinin jikinshi sbd tsabar tsoron nana dayakeyi.
"kana jina kayi shiru kasan cewa bana son ina magana ana kyaleni ko"?
Cikin rawar murya ya fara magana
"Anty nana mai nai maiki dan Allah? ynxn fa zaune nake banyi komai ba"
"Taras"! Kaji saukan mari a fuskan aliyu , wnda hakan yay sanadiyyan sakin mutum butumin super man din dake hannunshi ya kwallah k'ara saboda zafin marin dayaji.
Tashi tai ta kalleshi
"Dan ubanka ka sake
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download ALIYU HAYDAR

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album