An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [18/08, 4:20 pm] Bilkisu H MUHD: _*GABA DA SO*_              _BY_ *BILKISU H MUHD* Phone 08031307884 Page 1 *MARUBUCIYAR* ILLAR SABO RASHIN RABO YA YI SAKE ZAFIN HAWAYE NA BAKIN KAZAFI WAYA FI SONTA GORO DA SANKARA JINI BIYU DACEWA KAUNA CE BAYAN KUSKURE MATSALAR KAUNA TARAIRAYA DAKE NA DACE AKWAI BANBANCI BAKIN KAZAFI MULKIN MALLAKA IZZATU BAYAN KUSKURE KA AURE NI KYAUTAR ZUCIYA *sannan yanzu ta zauna ta kure basirarta gun rubuta muku littafin da bata taba fitar dashi a takadda ba littafine Wanda a online tafara rubutashi , littafin yazo da sabon salo tare da sarkakiya hadi da soyayya mai taba zuciya kowa yaji sunan littafin GABA  DA SO  zai sojin menene agaba da so daman da akwai abinda yake GABA DA SO,to karanta wannan littafin dan sanin menene ke GABA DA SO.* makaranta kundai san yadda alkalaminta🖊️yake.  Wanda ya santa ya santa Wanda bai santaba yakamata ya gwada karanta books dinta lalle bazata baku kunya ba. Sannan zaku samu dukkanin littattafai na ta hanyar 👇🏻👇🏻👇🏻 Wattpad:👇🏻 @bilkishmuhd Arewa Book:👇🏻 bilkisuhmuhd WHATSAPP GROUP NA BILKISU H. MUHD👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/Fp8jRB4MGGqB1I6J9gc0NE?mode=ac_t WHATSAPP CHANNEL NA BILKISU H. MUHD👇🏻 https://whatsapp.com/channel/0029VarKaWtBfxnxJ2STpI1o FACEBOOK GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻 https://www.facebook.com/groups/1845344956261189/?ref=share&mibextid=NSMWBT BUSINESS GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/IOFJMOHiTTMJ9cNLRroppc?mode=ac_t ------------------💥 Ɗakine madaidaici  babu wasu tarkace a ciki,daga ɗan ƙaramin gado medium size sai set ɗin akwatuna masu ɗan karan kyau sai ɗaukar ido suke da alamu basu ji jikiba, daga can gefe  guda wani tebur ne mai ɗan girma da tulun wasu manya-manyan littattafai akai, daga jikin bangon ɗakin katon hoton tane wanda suka ɗauka da gwamna da mahaifinta ALHAJI IBRAHIM sun sanyata a tsakiya, kusa da hoton agogon bangone  wanda akayi mishi ado da ruwan gwal. Kwance take akan ɗan madedecin gadonta tayi ruf da ciki da littafi agabanta tana karantawa, yanayin yanda tayi kwanciyar hakan ne yabawa bajajjen Hips dinta damar buɗewa wanda a shekarun ta goma sha takwas tsaf zaka rantse ƙugun babbar mace ne, sanye take da riga mara nauyi iya gwiwa mai dauke da hannun shimi, rigar tabada kyakykyawan haɗin kai wajan bayyana farar fatarta, iPhone dinta ta hanga yana fidda haske alamun kira yashigo, dam! taji gabanta ya buga, cikin sauri ta mike ta nufi ƙofa ta kulle tare da murɗa key ta koma ta rufe window ta saki labule ta koma gado ta ɗauki wayar ta janyo lallausar bargonta ta rufa dashi sannan ta ɗauki kiran tareda sanya wayar a kunne. ''Assalamu Alaikum" taji ya faɗa cikin tattausar muryar da ako yaushe bata gajiya da jinshi. "Ameen" ta amsa  cikin muryar raɗa a takaice, duk da cikin yanayin raɗa tayi maganar hakan bai hana zazzaqar muryarta bayyanaba, cikin nutsuwa taci gaba da fadin "maiyasa ka kirani yanzu?, kamance nace da kai ABU baya fita da wannan lokacin,? dan Allah kada ka sake, inajin tsoro, inajin tsoro idan ya gane kasheni zaiyi..... " "Oh God, tom shikenan ayi mini afuwa mancewa nayi".  shuru sukayi zuwa wani lokaci sannan ya numfasa yace"Baby kina kan layi?" shiru tayi, batare da tace komai ba. " ko kinajin tsoron magana ne?" Duk da tana cikin blanket saida tadan leƙo da kanta waje tasake kallon dakin zuciyar ta cikeda tsoron mahaifin nata, duk da cewa ta kulle koi'na, sannan tamaida kanta cikin blanket din ta sassauta murya tace"eh haka ne, dan Allah kayi hakuri muyi magana anjima, ka kirani adaidai lokacin da kake kirana" Motsin tahowa taji da sauri ta katse wayar ta koma da sauri ta murɗa key ta buɗe ƙofar sabida gudun zargi ta komo da gudu ta kwanta tanajin lokacin da Abu ya turo ƙofar ya shigo ya dade tsaye akanta zuciyar ta sai bugawa takeyi da karfi tamkar zata faso ƙirjinta tanajin tsoro kada ZARUK ya sake kira, fuskarta ta hada wani uban gumi wanda yasa lallausar sumar kanta kwanciya akan goshinta, maimakon ya fita sai ya koma ya zauna a gefen gadon, mufici ya dauka yanayi mata firfita. "Oh Allah" tace azuciyar ta, dole ta dan motsa a hankali ta bude manyan idanuwanta sukayi ido biyu dashi, wani tausayinshi ya kamata, bata taɓa ganin ubanda keson ɗansa kamar Abu ba, anya kuwa tayi wa Abu adalci da take aikata abinda a kullum yake gargadinta da aikatashi?. ya katse mata tunani yayi tareda fadin" lu'u lu'u na harkinyi bacci haka da wuri?" murmushi tasaki wanda yayi nasarar loɓawar kumatunta duka biyun, mikewa tayi ta zauna "Abu kainane naji yanayi mini ciwo amman yanzu natashi bara na ɗanyi karatu" yayi murmushi cike da tsananin soyayya irinta ɗa da uba, cikin kulawa yace" tom shikenan bara na kawo miki shayin kisha ko" "Abu kabarshi kawai cikina ya cika" "A'a kin mance shiyake taimaka miki gun karatu?" bai jira ta sake magana ba yayi waje. Cikin zafin nama ta ɗauki wayar ta switching dinshi baki ɗaya. -------------------💥 Rantsatstsiyar motar daya gani tsaye a ƙofar gidan sa ƙirar Range rover  ne yasa sai da gaban sa yayi wata irin bugawa, to amman kuma mai ya kawo su gunshi?. sanin cewar baici bashin kowa bane ya bashi ƙwarin gwiwar ƙarasawa gareshi. Kafin ma ya ƙarasa bakin motar wani haɗaɗɗen Alhajin birni ya ɓallo murfin motar yafuto, nan take gaba ɗaya wajan ya gwaure da wani irin ƙamshi kai da ganin mutumin zaka tabbatar da acikin masu kuɗin ma shiɗin yaci ya tada kai. Cikin takun isa da ƙasaita irinna masu dashi ya nufo Alhaji Ibrahim fuska a sake tare da miƙa masa hannu, sai da Alhaji Ibrahim ya danyi jim kafin ya miƙa nasa hannun. Cikin fara'ah baƙon yace" ya kamata mushiga daga cikin mota ko kuma mu ɗan keɓe dan naga kamar muna a kan hanya ne" "Haba malam ya daga ganinka zakace mu shiga motarka,? ai kagaya mini abinda ke tafe da kai tukunnan, nufar kama danayi ba ƙaramin shahada nayiba domin zai iya yuwuwa zuwa kayi dan ka cutar damu nida ɗiyata". Murmushi Alhajin yayi kawai sannan yace" Kada ka damu bazan cutar da kaiba alkhairi ne ke tafe dani, yanzu tunda baka amince da shiga motata ba ka saukeni a inda yayi maka" "Yauwa yanzu naji magana, jirani na fito" ya faɗi hakan tareda shiga gida, bakon na binshi da kallo shi dariya ma yake bashi yaga alamar kwata-kwata bashi da yadda, amman yasan zai saki jiki in har yaji abinda ke tafe dashi. Hango shi yayi tafe da kujeru guda biyu irin ta roba. Bayan sun zauna baƙon ya kalli Alhaji Ibrahim yace" Idan bazaka mance ba Alhaji haruna wanda akeyiwa laƙabi da mass gyaɗi-gyaɗi hardashi a halartar taron da aka yi na daliban da suka wakilci ƙasa da ƙasa a can Abuja inda ƴarka IKHLAS ta lashe gasar har kusan zan'iya cewa a wannan karon shi yabaku kujerun makka kafin hon zubairu balannaji ya fara baku" Abu Ya jinjina kansa alamun gamsuwa, saide acan ƙasan zuciyar sa gaba daya ya gama ƙosawa, yana son jin mai ke tafe da shi. hakane yasa shi katse shi cikin rashin iya maganar sa kamar yadda kowa ya sani babu ruwan sa da kai waye yakan furta duk abinda ya zo bakin shi. " da Allah malam ka gaya mini abinda ke tafe da kai ni na gaji kana wahalar dani ina da abin yi"  furucinsa yayiwa baƙon zafi, amman babu yadda ya iya, shiyasa ko kaɗan bayason mu'amala da talaka. " ok ai yanzu zantafi, kamar yadda nayi maka bayani shi mass yaya nane kuma....." "Ashsha ai kaji irin ta, ni bana son wannan kewaye-kewayen, ba sai ka faɗi dangantaka ba kawai gaya mini mai ya kawo ka?" Tofa Alhaji nazifi ya fara harzuƙa, sai dai ya shiga lallashin zuciyar sa gudun samun matsala. " to na fahimta, ɗan sa ne yaga Ikhlas yana so abinda ya kawo ni kenan" wata iriyar zabura Alhaji Ibrahim yayi tamkar wanda aka aikowa da sakon mutuwa. " yarinya ta ko secondiri bata gamaba kuma koda ta gama sai tayi karatu mai zurfin-zurfi sai ta kai ƙololuwa kamar inda na tsara" "Ikon Allah" Alhaji nazifi yafurta a zuciyar sa, nan kuma Allah ya kawomu, tabbas bahaushe yayi gaskiya da yace ɗan kuka mai jawa uwarsa jifa, jibifa ko sacondry bai iya faɗi ba amma shi yake cin irin wannan buri. " ranka ya daɗe na fahimce ka wato ƴarka karatu zata yi sosai ko? "Yis fadi ka ƙara" Alhaji nazifi ya ƙara danne dariyar dake son kwace masa, Allah sarki yana son yin turanci sai dai bakin ya kasa. " muma gidan mu gidan ƴan bokone kamar yadda kake ɗin nan ɗan boko, da ikon Allah zamu cika maka dukkan burinka a kanta, kawai ka amince da mu. " kamar yaya?" cewar Alhaji Ibrahim. " Ina nufin zatayi karatu a gidan mu, inma likita ta karanta zamu gina mata asibiti nata na kanta muna da tarin dukiyar da bazai taba karewa ba zamu....." "Kaga Malam dakata Dan Allah!!, kada ka batawa kanka lokaci, yarinyata zata samu duk abinda take sone akan kanta bata dalilin mijin taba, ninasan wahalar da nasha Kuɗi ba asiri bane! Kuɗi ruwa ne — yau yana nan, gobe ya zube. Ina son 'yata ta dogara da kai, ba ta zauna tana jiran sadakar aure daga dansa ba. Na raini Ikhalas da gumi, da addu'a, da halacci. Ba zan miƙa ta hannun kuɗi ba!dan haka bana son taci arzikin mijin ta ballantana yayi mata gori, idan har son ta yake da gaske, yana iya jiran wannan lokacin" Yana faɗin haka ya mike tsaye alamar ya gama magana, hakane yasa shi ma Alhaji nazifi ya mike ya soma tattaki zai nufi mota. Alhaji Ibrahim yabi bayan Alhaji Nazifi da kallo sannan cikin daga murya yace"wallahi ko da ɗan Ƙaruna ne zai zo sai na cika burina, kowa daga yaga ɗiyata ta sami daukaka sai yace zai lallaba ya raɓeta duk sai nayi maganinku, dan kuna ganinku da kuɗi, to ina sa rai duka nan gaba sai kundawo ƙarƙashin ta tun yanzuma ga ishara kun fara gani" Alhaji Nazifi ya juyo ya kalle shi tareda faɗin" shikenan babu damuwa hakan yayi kyau" Ya shige motar sa ya figa da ƙarfi. Da gudu ta miƙe jiki na rawa sabida yadda ya buɗe dukkan muryarsa cikin ƙwala mata kira sai da ta kume da ƙyaure. Ta yo waje da sauri jikin ta har rawa yake, a setting room ta ganshi tsaye yana faman kai komo zaman ma ta ga gareshi, tana kokarin tsugunawa cikin masifa ya juyo ya kalleta. " kigaya mini wanene zubairu ballannaji? wani shaiɗanin ɗan nasa kika turo ya zo neman auren ki!!?" ya kalli ƙofar daki tareda daga murya yace"ke! kina ina?" Ammi ta fito daga ɗaki a sukwane, babbar mace mai cikar kamala da kuma haiba a fuska. kallonta yayi yace"maza ɗauko mini wayar ta a ɗakin nata" ya faɗi hakan yana mata nuni da ikhalas wadda tayi tsamo-tsamo kamar anjiƙa ɓera. Jinjina kai kawai Ammi tayi ta nufi hanyar ɗakin. kallonsa ya maido kan Ikhalas yace"zaki buɗe baki kifaɗamin gaskiya ko sai nayi miki illah?" A nitse ta soma magana. " Allah shine shaidata Abu ban taɓa jin irin wannan sunan ba" Adaidai lokacin Ammi tadawo, ta rissina tareda mika mishi wayar. Wayar ya kunna ya shiga bincike lungu da sako na ciki. Gaban Ikhalas ne ya fara faɗuwa, tarasa gane a ina take, jinta take ita ba'a sama ba, kuma ba'a ƙasa ba, tsoron ta ɗaya kada a samu akasi ZARUK ya kirata adede wannan lokacin, ƙirjinta kamar zai fashe saboda tsoro. "karɓi wayar" ta ji yana cewa. Tayi wani firgigit da sauri tasa hannu ta karɓa. yana huci kamar wanda yayi dambe ya kalleta. "kada ki kuskura na kamaki  kina mu'amala da wani namiji, kibari idan lokaci yayi da kaina zanyi miki zaɓin mutumin da ya dace dake, muddin kika tsaya kika dage zamu sami irin mijin da yayi mana, yanzu karatu zakiyi, yanzu kika soma sa ƙafa ba kiyi komai bama a karatu, nasarorin da kike ta samu ya tabbatar mana da cewar keta dabance, ke zaɓaɓɓiya ce cikin al'umma, Ubangiji ya nuna mana hakan, dan haka dole ne muyi amfani da damarmu, ada anayi mini gorin ɗa, ban haihuba, haka kuma da Allah ya tashi bani haihuwa sai ya soma da bani mace a lokacin dangina da abokai suka dinga zinɗena, lokaci ɗaya sai ubangiji yayi musu ishara da baiwarki, Ikhlass sai na nunawa mutane cewar mace zata yi fiye da abinda na miji zaiyi, idan mace na iya zama shugabar ƙasa to a ƙasarnan a kanki za'a fara" Ya dubeta tare da dafa kafaɗarta, ya cigaba da magana cikin cizon leɓe kamar wani mai cin alwashi. " wahalar da nasha sai na fanshe, nima sai anzo ana kwatance dani in taka duk wanda naga dama, bazan yi alfahari dan kin auri wani shahararre ba zanyi alfahari ne kawai idan ke kika zama wata" Ammi tana tsaye tana kallonsa, mamaki ya gama kashe ta a tsaye, kallonsa take kamar wani taɓaɓɓe. Ajiyar zuciya ta sauke tare da faɗin "Allah ya tabbatar mana da alkhairi" Ƙuro mata ido yayi yana son fahimtar wani abu. Cikin halin ko'in kula yace" gashi nan yana kan tabbatar wa tunda mun fara cin arzikin ta tunkan taje ko ina, ji nakeyi da yawon haya muke yi bani da komai ba wani wanda ke ganinmu da mutunci, yanzu fa munsami jari mun sauke farari, saiki duba ki gani nan gaba ya zamu dawo" Ya dawo da kallonsa ga Ikhlas. "Maza jeki, Allah ya haska rayuwar ki" Tunda ta komo daki komai ya kunce mata, kanta taji ya sara tsabar ciwo, hakan yasa cikin sauri ta cire ribon ɗin dake kanta tasaki lallausan dogon gashin ta ya bazu a kan doron bayan ta ko za taji sauƙin ciwon kan, hannun ta tasa akan goshin ta tare da lumshe ido, idan abban ta yana wasu maganganun takan ga tamkar yana da matsala a ƙwaƙwalwarsa, a kullum yana yin wasu abubuwa tamkar bai yadda da Allah ba, ya mance cewar a kwai mutuwa zai iya dauke ta ko Kuma ya dauke shi  gashi gaba  ɗaya, yaƙi kyautata ma'amala tsakanin shi da dangin shi, bashi da burin da ya wuce ya dasa tsanan su a zuciyar ta, shi kam mai suka yi masa haka har yake cin alwashi a kansu? ko kaɗan baya son su raɓeta, duk kuwa da cewar duk lokacin da ta shiga cikin su kamar zasu cinye ta, ƙauna suke nuna mata muraran... Shigowar Ammi ya katse mata tunani, zama tayi a bakin gado tana fuskantar ta. "Yar gata, matso ki zauna kusa da ni. Kafin duniya ta koya miki wacece ke, ki bari na fada miki. Na haife ki da bege, na raina ki da addu’a. Allah ya azurtaki da baiwa da basira, kuma na gode masa. Amma ki sani, baiwa ba hujja bace ta raina wasu. Girma na gaskiya ba yana cikin jin kai bane, yana cikin saukin kai. Na lura da yadda mahaifinki ke kokarin nuna miki cewa ke daban ce – wato ‘gifted’. Hakika, Allah ya baki abin da ya bambanta ki, amma kada ki bari hakan ya zamar miki abin daukaka har ki fara ganin kanki fiye da sauran mutane. Wanda ke sonki da gaskiya zai koya miki kauna, ba kyama ba. Zai kara miki tausayi, ba tsana ba. Zai kara miki son zumunci, ba yanke shi ba. Amma idan yana koya miki cewa dangi basa da amfani, ko cewa ke kin fi kowa – to yana cire miki darajar zuciyar da zata tsira da mutunci. Ki saurare ni da zuciyarki, ba kunnuwanki kadai ba. Mutum mai kirki ba ya nuna hasken shi da gurbata wasu ba. Idan haskenki na gaskiya ne, zai haskaka kowa a kusa da ke, ba ya kona su. Ki yi alfahari da kanki, amma kada ki raina wani. Ki san darajarki, amma kada ki manta da jinin da kika fito daga cikinsa. Akwai mutunci cikin girmamawa, kuma akwai daukaka cikin saukin kai. Duniya tana iya fada miki ki zama wadda ke sama da kowa, amma zuciyar uwa tana rokonki ki zama wadda ke kusa da kowa. Wannan shine girman da Allah ke so." " daga karshe bazan gaji da sanar dake cewar zaɓin Allah zaki nema ba, domin zaɓinsa yafi zaɓin kowa, ko kaɗan kada ki bari ya rikita miki tunani, yadda danginsa ke tafi dake kaɗai zai sa ki yanke hukunci a kan yadda yake aibata su a gurinki" Bata sake cewa komi ba ta miƙe tayi waje. Kalaman Ammi sunfi tasiri a gareta fiye dana Abu, yadda Ammi ke gaya mata haka Rahma ke gaya mata. wanne yaƙi ne zai faru idan Abu yasan cewa Ikhalas tana waya da Zaruk? Www 10 w shin burinsa zai cika a kanta ko kuma zaiyi rashin nasara? Wwwwwe Bilkisu H. Muhd ✍🏻1w²w [18/08, 4:20 pm] Bilkisu H MUHD: _*GABA DA SO*_              _BY_ *BILKISU H MUHD* Phone 08031307884 Page 2 *MARUBUCIYAR* ILLAR SABO RASHIN RABO YA YI SAKE ZAFIN HAWAYE NA BAKIN KAZAFI WAYA FI SONTA GORO DA SANKARA JINI BIYU DACEWA KAUNA CE BAYAN KUSKURE MATSALAR KAUNA TARAIRAYA DAKE NA DACE AKWAI BANBANCI BAKIN KAZAFI MULKIN MALLAKA IZZATU BAYAN KUSKURE KA AURE NI KYAUTAR ZUCIYA *sannan yanzu ta zauna ta kure basirarta gun rubuta muku littafin da bata taba fitar dashi a takadda ba littafine Wanda a online tafara rubutashi , littafin yazo da sabon salo tare da sarkakiya hadi da soyayya mai taba zuciya kowa yaji sunan littafin GABA  DA SO  zai sojin menene agaba da so daman da akwai abinda yake GABA DA SO,to karanta wannan littafin dan sanin menene ke GABA DA SO.* makaranta kundai san yadda alkalaminta🖊️yake.  Wanda ya santa ya santa Wanda bai santaba yakamata ya gwada karanta books dinta lalle bazata baku kunya ba. Sannan zaku samu dukkanin littattafai na ta hanyar 👇🏻👇🏻👇🏻 Wattpad:👇🏻 @bilkishmuhd Arewa Book:👇🏻 bilkisuhmuhd WHATSAPP GROUP NA BILKISU H. MUHD👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/Fp8jRB4MGGqB1I6J9gc0NE?mode=ac_t WHATSAPP CHANNEL NA BILKISU H. MUHD👇🏻 https://whatsapp.com/channel/0029VarKaWtBfxnxJ2STpI1o FACEBOOK GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻 https://www.facebook.com/groups/1845344956261189/?ref=share&mibextid=NSMWBT BUSINESS GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/IOFJMOHiTTMJ9cNLRroppc?mode=ac_t ------------------💥 Tunda sanyin safiya ƙofar gidan ke cike a nata faman fita da buhunhunan kayan masarufi kama kan buhunhunan shinkafa, fulawa, katan-katan din taliya da sauran ababen ci, wani abin birgewa shine jama'a sun jeru babu wata hayaniya. Alhaji Ashir wanda ake yiwa laƙabi da baban sukari da kanshi yake rabon waɗannan kaya duk wanda ya miƙawa zai fara rangaɗo addu'oi har kakan kakansa sai an yiwa addu'a, wani tsoho da aka zo kansa jikin shi na rawa yana sharar ƙwallah ya shiga jero mishi addu'a "ubangiji ya bayyana fatima yasa tana hannun nagari, Allah ya baka haihuwa ubangiji ya rabaka da duniya lfy" "Ameen, Ameen" Abin da Alhaji Ashir kawai yake cewa kenan, inda yake jin wani miki na tasowa a can ƙarƙashin zuciyar sa.       ***                ***               ***            *** Tafe suke su biyu itada ƙawar ta Rahma, gaba ɗayan su sanye suke cikin kayan makaranta sai dai kayan yayi bala'in yiwa Ikhalas kyau kamar ba uniform ba, duk wanda ya kalleta a cikin kayan sai ya sake juyawa saboda yanda kayan ya karɓeta kamar dan ita aka yi, daf da zasu gilma ta gun Ikhalas ta dubi Rahama sannan tace"ban taɓa ganin mutum irin shi ba, idan aka ce dani waye gwanina cewa zanyi baban sukari, ina ƙaunar bawan Allannan" Rahama ta dube ta"Kinga ance bai taɓa haihuwa ba yana baƙin cikin ya mutu ya barwa matarshi gado, dan haka yake ɓarnatar da dukiyar sa, saboda abin nasa yayi yawa" "Mtssss" Ikhlas taja tsaki sannan tace"kawai sai yayi ta rabar da dukiyar sa ba dan Allah ba sai dan mugunta ko? da Allah Rahma kada ki sake faɗin haka in ba haka ba sai a ɗauke ki a matsayin jahila" daga karshe abin ya nemi ya zame musu rigima hakan ne yasa Ikhlas ta tsuke baki. -------------------💥 "Bilkisu duba min wani jarababben ne ke ta faman buga mani ƙofa haka kamar wanda naci ban biya ba?" Bilkisu dake ƙoƙarin fitowa daga toilet ta amsa da " toh" da sauri ta ƙarasa ta buɗe, wani matashi ta gani da kurar turi ɗauke da buhun shinkafa da buhun fulawa sai ƙaramin buhun suga irin mai cin kwano biyar matashin yace "baban sukari ne yace a kawo nan gidan" "masha Allah mungode sosai Allah ya saka" godiyar da yaji tayi yawa ne yasa shi saurin miƙewa ya buɗe dukkan muryarsa "meke faruwa ne a nan?" ya ƙarasa wajan tare da kallon matashin. "Kai malam wannan kuma daga ina?" Matashin ya gaya masa kamar yadda ya gaya wa Bilkisu, suna ƙoƙarin saukewa Alhaji Ibrahim yace" dakata kai zan saɓa maka muddin ka sauke waɗan nan kayan a gidan nan, an faɗa maka mu mayunwata ne irin ku?, to ku koma kuce dashi lalacewar mu bata kai a kawo mana sadaka ba, ya kaiwa mabuƙata mu kam munfi ƙarfin a bamu, maza ku kwashe tarkacen ku" Bilkisu kam saboda tsabar mamaki bakin ta ya ƙi rufuwa ga wani nauyi da kunya daya lulluɓeta ji take yi kamar zata haɗiyi zuciya, juyawa tayi ta koma ciki. ......................... 💥 A hanyar dawowar su Ikhlas daga makaranta tun daga nesa suka ga ana nuno su, gaban ta ne ya faɗi ta rasa dalilin nunawar, duk sai taji ta tsargu, har suka iso gun idon matasan na kanta. Wani ya ɗaga murya yana faɗin" nasan shi sosai fa, da talaka ne futuk sai dai a kawo musu ragowar jagwalgwalon yara suci shi da matarshi, kullum ka gan shi cikin tsumma yake abin tausayi, ban san yadda aka yi ya waye haka ba" Wata murya taji kamar tasan mai shi yana cewa"wannan ƴar tasa da ita suke takama, gidan da suke ciki ma nata ne, da fa a gidan ƙasa yake haya, ɗakin su ko rufin kirki babu" Sai hahaha suka sa dariya. "Ɗan shegiya sai faɗin rai" da sauri suka ɗaga ƙafa Rahma tace"ikhalas kamar na hango wannan ɗan yayan baban naku a gun kodai da ku suke? ni naga gaba ɗaya mu suke kallo musamman ma ke" "Su suka sani" cewar Ikhalas. ....................... 💥 Ammi ce ta bata labarin abin da ya faru a inda itama ta gaya mata maganar da ta jiyo ana yi a waje " Amman Ammi mai yasa Abu ya ke haka ne baya tsoron bakin mutane, idan baya so sai ya karɓa ko su Baffa hamza sai ya baiwa" Bilkisu ta sauke ajiyar zuciya," ni na ce ke kanki kin fi kowa sanin halinsa? sai nuna isa gashi bai isa ɗinba" Ikhalas taji kalamen Ammi sunyi mata tsauri sai ta dingajin babu dadi aganinta bai kamata ta fito da irin wannan maganar agabanta ba kawai ta barshi aranta tunda ita din y'ace. motsin shigowar da suka ji ne yasa su yin shiru. --------------------------------------- "Ai in Allah ya yadda sai Ikhlas ta mutu inyaso muga ta ƙarya" Salisu ya fada. baffa Hamza ne ya dakatar da shi gun tsinkeshi da wani azababben mari ya dafe kunci yana huci baffa Hamza yace"dan uban ka ƙanwar taka ka ke yiwa fatan mutuwa? ita ɗin mai tayi maka kawai sabida halin ubanta?" Cikin ƙunci yace"Amman Abba abin nasa ne akwai ban haushi, ya sani mu ba unguwar mu ɗaya da baban sukari ba, yasani mu ba, bamu za'ayi ba, ya san kuma da hakan amman tsabar baƙin hali da son nuna fariya ya....." "Ba zaka yi mani shiru ba ko? ko kai baka taɓa cin abinci bane?" " Toh amman Abba ko yanzu babu wanda ya karya a cikin mu" "Ba zaka yi mani shuru ba ko!!?" gyaɗa kansa yayi, Fuuuu yayi waje yana faman ƙunƙuni. "An faɗa in Allah ya yadda ƙwaƙwalwar ta sai ta zama ta jakai" "Abban su Salisu dole fa yaji babu daɗi, kai ban san me yasa baka ganin laifin su ba" "Banda ke da abun ki Dija kowa fa arziƙin shi yake ci, muma fa mun haifa wataran zamu ci albarkacin yaran mu, baki sani ba ƙila ma a kwai shugaban ƙasa a cikin yaran naki" ya faɗa yana murmushi. Banza tayi masa ta shige ciki ita bata taɓa ganin marar zuciya irin baban Salisu ba. ........................ 💥 Haj Hauwa ce durƙushe a gaban malam tana faman kuka"yanzu malam babu yadda za'a yi in samu haihuwa?" Malam ya maida hankali a kan ƙasar da ke gaban sa ya ɗanyi zane zanen sa ya ɗago kai ya dube ta" gaskiya mijin ki ba mai haihuwa bane" Ta jinjina kai cikin tashin hankali " to malam menene abin yi?" ya ɗanyi shuru yana shafar ƙasar dake gaban sa, sannan ya ɗago yace"kawai dai a sake sabon ta soyayyar  yaron ki a zuciyar sa" "Toh malam kodai a kashe shi?" Da sauri malamin ya ɗago yana duban ta" ai mutuwa sai lokaci yayi, kuma mu babu kisa a tsarin aikin mu idan lalle sai kisan kike so sai dai ki nemi wani" Jikin ta ne yayi sanyi duk sai taji ta muzanta " to shikenan a sabunta soyayyar yaron nawa a zuciyarsa in yaso ya zamto sai yadda mukayi da shi" bundle din ƴan dubu dubu ta ajiye masa suka yi sallama.   ---------------------------------------                 Alhaji Ashir (Baban sikari) shahararren attajiri ne wanda bashi da burin da ya wuce ya farantawa mabuƙata, kullum yana jin cewar an bashi arziƙin ne kawai domin ya taimakawa marasa ƙarfi, har matasa ne dashi waɗan da ya wakilta a kan duk wanda yake cikin unguwar tasu idan bashi da shi a gaya masa, ya sayi motoci irin bus bus ɗin nan dan kai  yara makaranta, waɗanda ya ɗauki nauyin karatun su ba zasu lissafu ba, Alhaji Ashir ɗan kwangila ne sannan yana da manyan kantina a kasuwar kwari, ana juya masa kuɗaɗen shi. Dattijo ne shi ɗan kimanin shekara sittin, yana da mata guda ɗaya, a halin yanzu matarsa ta fari Allah yayi mata rasuwa, sai hauwa wadda i tace ke zaune da shi da yaron ta ƙwaya ɗaya wanda ta haifa a wani gidan wato Nazir, tun yana ɗan shekara goma sha huɗu ta kawo shi gidan, yanzu haka shekarunsa ashirin da takwas, taƙadari ne na gasken gaske, sai dai a gaban baban sukari babu mutumin kirki irin shi, baban sukari ya riƙi Nazir tamkar ɗan cikin sa ƙaton shago ya mallaka masa a  kasuwar kwari, sai dai Nazir da haj hauwa basu da buri illa ya danƙa ragamar dukkan harkokin shi a hannun sa, sun bi malamai sun bi bokaye har sun gaji, duk lokacin da baban sukari ke fidda zakka ji suke yi tamkar za suyi hauka, yanzu burin hauwa ta yaya zata sami haihuwa da shi ko dan taci gadon shi, wannan kenan. Cikin mamaki ta kalli ƙawar tata sannan tace"Lalle haj hauwa yau na tabbatar da baki da hankali, yo idan kika saka aka kashe shi dame zaki ƙaru? ai gwara kisaka ayi masa asirin da zai zamo shi ba'a mace ba, shi ba'a raye ba, yanzu fa da zaran ya mutu waɗanda ma baki taɓa gani ba zasu yunƙura suce ɗan'uwan su ne, kuma dole ne a raba gadon dasu" Hajiya hauwa ta saki ajiyar zuciya, cikin damuwa tace"haka ne aminiya, yanzu meye abin yi?" " Abin yi kawai mubi a hankali zamu sami wanda zaiyi mana aiki a kansa, kudi zaki bani naje India kinsan ance sheɗanun bokaye sunfi yawa a can" Wata uwar shewa suka saka tare da tafawa wannan kenan. -----------------------------------💥      America Babban birnin Amurka shine Washington, D.C. Shi ne cibiyar gwamnati ta Tarayyar Amurka, inda Aso Villa na Amurka wato White House, Majalisa (Capitol Hill), da Kotun Koli (Supreme Court) suke. Georgetown Wannan tsohuwar unguwa ce mai tarihi da kudi. Tana cike da gidaje masu tsada, shaguna masu kyau, manyan restaurants, da manyan mutanen kasa. Akwai celebrities da diplomats da manyan ‘yan kasuwa da ke zaune a nan. The Four Seasons Hotel Washington, D.C. Yana cikin Georgetown. Wannan hotel din yana da matakin duniya, yana karbar shugabanni, celebrities, da ‘yan kasuwa. Farashin ɗakin dare ɗaya yana iya haura $1000 . A hotel  din wani katon Holl ne wanda ya gama kayatuwa da kayan alatu da wasu irin kujeru na alfarma ga yadda holl din yayi shuru zaka tabbatar da cewar abinda ake tattauna akai yana da matukar mahinmanci. Wani matashi wanda bazai wuce shekaru ashirin da takwas ba sanye da white shirt da Black jeans yayi aski low cut mai tsafta sanye yake da Rolex agogo a sandar hannunsa da kuma tabarau rayban sai dan karamin zoben gold a yatsan sa takalmin kafarsa Fendi shoes sai Hermes belt dake daure a kugunshi. Zaruk kenan yong billions wanda ake ji dashi a wannan zamanin manyan kusoshi ke neman hada hannu dashi ayanzu haka iya da hannun jari a campanunuwa irinsu Apple Inc. (AAPL) Kamfani mafi girma a duniya bisa kasuwar daraja (market capitalization). Yana kera iPhone, iPad, Mac, da sauran kayayyakin zamani. Saka hannun jari a Apple yana da daraja saboda yana da ƙarfi sosai a kasuwa. Microsoft (MSFT) Shahararren kamfani na fasahar zamani. Yana da software irin su Windows da Microsoft Office, da kuma Azure (cloud computing). Amazon (AMZN) Babban kamfani na e-commerce (sayayya ta yanar gizo). Hakanan yana da Amazon Web Services (AWS) – babban kamfani na girgijen ajiya. Wanda ke kawo riba sosai. Nvidia (NVDA) Kamfani mai ƙera kwakwalwan kwamfuta da ake amfani da su wajen AI, da wasanni (gaming). Hannun jarinsa ya haɓaka sosai a cikin shekarun baya-bayan nan saboda tasirin AI. Inda Zaruk ke zaune da wasu irin speakers jere agabansa yana magana kadai zai tabbatar da cewa shidin wani babban kusane da ake ji dashi Ya dade yana jawabi cikin muryarsa mai ƙarfi da kwarjini, lokacin daya gama jawabin gaba daya aka dauki tafi . Wadanda suke baki agun kasan cewar yaune ganinsu da shi na farko yayi mutukar birgesu tambaye suke wai waye shi sabida gaba daya shi din bai kaisu haske ba amman fatarshi tafi tasu kwanciya da kyau gashi da tsayi wanda bai wuce misali ba siffa mai kyau  alamar kulawa da lafiya. Tafiya da tsayuwa irin ta jarumi Gaskiya da aminci: baya yaudara, kuma abin dogara ne. yana da hangen nesa da sanin me yake nema. yana da Sauƙin kai ba mai girman kai ko wulaƙanci ga mutane ba. yana da Kiyaye magana da alkawari: idan ya ce zai yi, to sai ya yi. yana nuna damuwa da jinƙai ga na kusa da shi. Kyakkyawa ne na gaske . bayan kowa ya gama jawabinsa  taro ya watse sai dai shi kasan cewarsa musulmi sai da shi da tsitarin musulmen dake gun sukayi addu,o'insu kafin su watse. gashi dai ba'a ƙasar musulunci ya taso ba amman yana ibada tamkar yau zai bar duniya, haka kuma mutum  ne mai  son ibada, abin da zai baka mamakin a kan Zaruk kaf gidan shine kaɗai musulmi, sunyi iya yinsu akan ya koma Christian amman fir yaƙi, kasancewar su a turai kowa na bin ra'ayin sa ne, kafin mahaifinsa John ya mutu ya gargaɗi dangin sa cewar kada wanda ya kuskura ya tilasta shi a barshi a musuluncin sa, dan haka kowa ya sa masa ido, wannan banbancin addinin baisa sun ƙyamace shi ba, suna mutuƙar ƙaunar sa, za kayi mamakin idan kaga Zaruk na yin hausa tamkar ya girma cikin garin Kano, hakan ta samo asali ne ta dalilin gidansu amininsa wanda ya kasance kaf ya kare rayuwarsa a cikin gidansu, kwanciyar bacci ne kawai ke raba su da gidan sai dai yanzu gaba ɗaya sun koma Nigeria, lokacin da uban gidan su ya mutu wato John mahaifin Zaruk a dalilin yadda suka riƙe Zaruk ya sanya John ya mallaka  masa dukiya mai tarin yawa  har kawo yanzu Alhaji Auwal, Zaruk dinne ya zamo mai gidan sa, arzikin da Zaruk ya gada a wajen John bashi da iyaka, abun birgewar shine baka taɓa sanin waye shi  ko a suturar da yake sawa  inba sanin ta kansu kayi ba sai ka zaci mai saukin kudi ne sabida rashin hayaniyar kayan wani fannin ya kan saka na matsakaicin kuɗi. --------------------------------------------- Babban Gida Gini mai hawa   da launuka masu natsuwa (fari, grey, da duhu-blue).kewaye da babban haraba Gidaje Na Cikin Gida (Guest Villas) Domin ma aikata da baki da kuma abokai. Swimming Pool mai kyan gani da haske da tsakar dare. Ga Private Garden: Lambu da shuke-shuke masu tsada, kamar orchids da bonsai trees. Garage na Supercars: Ferrari, Lamborghini, da Mercedes Maybach suna a tsare. Cikin Gida (Interior) Babban Falo (Living Room): Mai fadi, design na zamani (minimalist + luxury), da LED lights masu canza launi. Glass Walls: Ganuwar gilashi da ke nuna lambu ko pool. Library + Office: Wurin da yake karatu da gudanar da business. Kitchen na zamani: Inda shi kansa zai iya dafa wani abu idan yana so Home Cinema:  ta kallo fim. Idan ya gayyaci abokai Fitness Room / Gym: Don ya nuna jikinsa yana aiki, lafiyayye ne. Balcony mai View: Wurin da zai dinga kallon taurari idan yana jin damuwa tayi masa yawa. Sanye yake da White Shirt + Dark Jeans Yana tsaye a gaban gilas din falo yana kallon ruwan sama da tunanin mushinta. Ikhalas na waya da Zaruk a ɓoye, ta gefe guda kuma tace baban sikari yana birgeta, Iklhas yane😅 Yaya zata kaya tsakanin Baban sikari da kuma matarsa Hajiya hauwa? shin tana yin nasara a kansa domin su samu gadon dukiyar sa? Tafiyar tamu me tsawo ce kawai ku antayo mu tafi tare💃🏻💃🏻💃🏻 Bilkisu H Muhd✍🏻 [18/08, 4:20 pm] Bilkisu H MUHD: _*GABA DA SO*_              _BY_ *BILKISU H MUHD* Phone 08031307884 Page 4 *MARUBUCIYAR* ILLAR SABO RASHIN RABO YA YI SAKE ZAFIN HAWAYE NA BAKIN KAZAFI WAYA FI SONTA GORO DA SANKARA JINI BIYU DACEWA KAUNA CE BAYAN KUSKURE MATSALAR KAUNA TARAIRAYA DAKE NA DACE AKWAI BANBANCI BAKIN KAZAFI MULKIN MALLAKA IZZATU BAYAN KUSKURE KA AURE NI KYAUTAR ZUCIYA *sannan yanzu ta zauna ta kure basirarta gun rubuta muku littafin da bata taba fitar dashi a takadda ba littafine Wanda a online tafara rubutashi , littafin yazo da sabon salo tare da sarkakiya hadi da soyayya mai taba zuciya kowa yaji sunan littafin GABA  DA SO  zai sojin menene agaba da so daman da akwai abinda yake GABA DA SO,to karanta wannan littafin dan sanin menene ke GABA DA SO.* makaranta kundai san yadda alkalaminta🖊️yake.  Wanda ya santa ya santa Wanda bai santaba yakamata ya gwada karanta books dinta lalle bazata baku kunya ba. Sannan zaku samu dukkanin littattafai na ta hanyar 👇🏻👇🏻👇🏻 Wattpad:👇🏻 @bilkishmuhd Arewa Book:👇🏻 bilkisuhmuhd WHATSAPP GROUP NA BILKISU H. MUHD👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/Fp8jRB4MGGqB1I6J9gc0NE?mode=ac_t WHATSAPP CHANNEL NA BILKISU H. MUHD👇🏻 https://whatsapp.com/channel/0029VarKaWtBfxnxJ2STpI1o FACEBOOK GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻 https://www.facebook.com/groups/1845344956261189/?ref=share&mibextid=NSMWBT BUSINESS GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/IOFJMOHiTTMJ9cNLRroppc?mode=ac_t ------------------💥 Haba mommy wannan ta,adin yayi yawa ai bashine ƙaruna ba wanda yafi kowa kudi da a kullim shi bashi da magana sai na ya taimaki jama'a ,wai kinji makudan kudin da yabayar wai wasu malamai zasu tafi can Kan dutse da'awa,amman mu idan mukace muna son kudi sai an tambayi abinda zamuyi dasu kodan ni bashi ya haife niba ai inda ace ni dansa ne komai zai sakar mini shago fa daya ya bani mai naci aciki Mai na bawa mutane na ga jamila na dauke da ciki ni dai gaskiya nagaji kawai ki sama mana mafita"haba Nazir kadinga kasa da murya mana kofa yaushe zai iya shigowa,ni nafison mubishi a sannu mutun ne shi mai wayo idan na nuna ina son abinsa bazai sake gaya mini sirrin shiba kaga yana yawan gaya mini inda kadarorinshi suke idan mukace zamuyi wani yunkuri zamu rasa abubuwa da dama idan muka dan jinkir ta dazaran ya gama gaya mini inda dukkan kadarorinshi suke komeye sai muyi mishi sallama suka jiwo daga harabar gidan " yanake jin murya kamar ta rakiya ta dan leka ta taga aikuwa da gudu ta kwasa kamar wata karamar yarinya suka rungume juna har suna huwaɗuwa haj Hauwa ta ruko hannun rakiya cancan kuryar daki take shirin kaita zasu wuce kawai Nazir ya bisu da kallo babu sannu ballan tana gaisuwa shifa duk wata kawa ta mahaifiyar ta to tazo ne ta yagi rabonta.    acan cikin daki atsakiyar gado tana zaune dafi'an gabanta kayan ciye-ciye ne kala kala,kai kana kallon rakiya zaka tabbatar da tsohuwar kilakice babu digon kunya a idanunta. Kaf haj Hauwa ta gama shaida mata abinda ke faruwa da kuma wanda take shirinyi. "Tabdijan lalle bakima da hankali to duk abinda kika tsara beyiba hajiyata kawai harka zamu bude haj Hauwa ta gyara zama " banfahimta ba " badai baya haihuwa ba to zamu samo mishi yaro awaje dole ki dana bariki bama sai na koya miki ba tunda an taba danawa,kawai sake lale zakiyi ki koma ruwa zabura tayi cike da mamaki" haba rakiya tsofai tsofai dani,kuma fa karki mance ina da saurayin ɗa  bandama ban haihu da wuri ba da yanzu ina da guda uku kafinshi"tsaya tukunnan saratu badai kina jinin al'ada ba" inayi amman wani fannin nakanyi wata biyu zuwa uku kafin nayi" kinga koma kin daina zamu dawo dashi ki samo yaro a manna mishi" a,a rakiya ina ganin wannan hanyar bamai bullewa bace mutuminan yafasan baya haihuwa"to ba yana da sani ba, yasani idan Allah yaga dama zai iya juya lamarinsa ke kodama ya gane dole ya yadda nasani kodan tsira da mutuncinsa, haj Hauwa ta dinga jinjina kai alamar zancen ya shigeta,ammanfa sai kin bude bakin aljihu idan da kuruciya ke za'ake biya idan kuma kin zama iya ke zaki biya,kuma biya mai kyau dazaran komai ya kankama yanzu zaki ga kin zama yarinya,amman kuma sai fa kina hadawa da gyara naga yanzu duk kin sukurkuce kamar bakeba dan yaro bazai baki hadin kai kina tsaminnan ba jibeki kin sanya kaya mai kyau harda su janbaki sai dai gashi sai wani bashi'bashi kikeyi ga tsami nasan awannan hamamin danake ji kin kai sati bakiyi wankaba,"a,a ke Kuma banson cin fuska" kinsanni tin da bana barin abu aciki batare da na amayar ba nasani yadda kike wannan warin na tabbata pant din dake jikinki ba karamin doyi yake ba Kuma--tayi saurin katseta "waike rakiya kin mance wacece ni " yo koma wacece kedai kinsan ba,a bakin komai nake ganinki ba sabida tun muna fita da dan bantai muke tare kinsan ke ba komai bace face matsiya ciya wadda bata da cin yau mune ma muke taimakawa gidan ku da guntattakin abincin da yaran gidan mu sukaci suka rage"haba rakiya wannan cin fuskar yayi yawa,ko kin mance ni mamanku take rikewa nake rakata gun kwaraten ta yawan ma danakeyi ada ai ita ta sanyani a hanya" Kinga to mubar zance haka muyi abinda ke gabanmu haj Hauwa sai cika da batsewa take" haba tawan saki rai mana muyi shawarar yadda zamu ci arziki mubarshi amazaunin sa" hehehe mubarshi fa kika ce ai shi wannan arzikin sai mun cinyeshi tas ko kale bazamu bariba suka kwashe da dariya tare da tafawa" shegiyas ashe har yanzu bakin halin nanan. ------------------------------------ Karfe goma Sha daya da rabi na dare ikhlas ce keta faman Kai komo idanunta a rintse rike da littafi a hannu da alama tana son tabbatar da cewar haddar da take kokarin yi ya zauna mata akanta  sai dai ga mamaki ta wannan karon haddar taki zama innillahi wa'inna ilaihim raju'un wannan shine karo na farko da hakan ta faru da ita wayyo Allah wai meke shirin faruwa da ita ne? ta koma ta zauna gaba daya tunanin zaruk ya hanata sukuni.    kwance da ammi agado  yadan bude ido ahankali sabida sautin karatun ikhlas da yaji da sauri ya diro daga gado ya kinkimi flast din shayi sai yajishi babu nauyi alamar Babu komi aciki ya ja tsaki.     Ammi tadan dago Kai.     "Indai shayi ne na shanye". "amman dai kinsan ikhlas zata bukata ko" yafada cike da takaici. "shikenan sai naki Sha sabida bukatar ikhlas. Ta koma ta kwanta taja bargo ta rufe kai. Mikewa yayi ya dauki flast din ya shiga kitchen ya kunna gas ya dora wani tea din baibar gunba sai da shayi ya kammalu ya juye cikin flast sannan ya nufi dakinta. Ita kam ikhlass tasake mikewa tana zagawa cikin karatu tare da sake rintse i cikin rashin sani ta bangaji abban nata har sai da flast din ya kusa faduwa da sauri ta bude idanunta. " Sannu Abu bansan ka shigoba. Yayi murmushi Mai tattare da  kulawa. " Sannu da himma ikhlas,mamanki ta ce ta kawo miki nescafe din naki ko? " Eh. Ya ajiye flast din dake rike a hannunsa " kifa dinga amfani da nescefe shi zai taimaka miki wajen karatun ki baza kiji bacci ba. Ta dan jinjina kai alamar to. " Zanje na wanke uniform Inna gama sai na Sha tea din. Yayi murmushi . "Sai dai kijira nefa kuma sukawo wuta kiyi gugan ,na wankesu tun dazu. Ya juya ya fita ta koma ta zauna agefen gado kaunar Abu na kara ratsa zuciyar ta,duk yadda yake takure ta amman yadda yake nuna mata kulawa tanaji babu Wanda ya kaita sa,an samun uba. Acan karkashin zuciyar ta tausayawa kanta takeyi da ta yadda ta sake soyayyar wanda bata sani ba ya hudata, ta yadda koda mai abban ta zayyi bata jin zata iya rayuwa batare da shi ba. Wannan kenan. Ahankali ta ware idanunta yayin da hasken rana ya dallare mata idanu abu biyu ne ya fado mata makarar yin sallar asuba sai gugan uniform . "Subhanallahi, Tayi saurin dirowa daga gado zata fita ta hangi uniform din nata a kan dirowa. Ta kada Kai cikin murmushi tasan wannan aikin Abu ne,ta fada bathroom tayi wanka tare da dauro alwala ta haukan dadduma tayi sallah bayan ta idar ta zauna ta rasa addu, ar da za tayi kamar yadda Ammi tace a duk lokacin da tayi sallah ta dinga rokawa kanta samun miji na gari, jitakeyi aranta Zaruk din miji ne na gari tsintar kanta tayi da fadin Allah ka sassauta zuciyar Abu ya amince mini zaruk ya zamo abokin rayuwa ta,ta yaya, wani bangare daga cikin zuciyar ta tayi mata wannan tambayar ras taji gabata ya buga da sauri ta kwautar da wannan tunanin muryar Ammi taji tana kwala mata kira da sauri ta mike.   Alhaji Ibrahim zaune a darning table suna karyawa ikhlas ta fito cikin Shirin makaranta ta durkusa har kasa ta gaidasu ta koma ta zauna agaggwuce ta fara cin abincin  Wanda taci baikai ya kawoba ta sunkuci Jakarta zata fice. "Abu sai na dawo,ammi natafi. da sauri Ammi ta dauko raguwar break din nata ta juye mata cikin wata yar karamar roba Mai murfi ta zuge jakar ta  Wanda ke goye abayanta ta zira aciki. Gudu gudu sauri sauri ikhlas ta fice a gidan. Alhaji Ibrahim yana kokarin yiwa Ammi magana Handset din Sa ya shiga ruri yayi saurin dauka yadade suna musayar magana daganan ya aje wayar cike da farin ciki. Tunda ya fara wayar ammi ta kafeshi da ido ta sauke ajiyar zuciya lokacin da ya aje wayar tana kallonsa. "Yarki fa likafa nata ci gaba,yanzu haka ansanya sunanta agasar da za,ayi acan  abuja  sannan idan har ikhlass tazo koda ta biyar ne  za,a  a fita kasar London kafinma mu je candin sai munje mun sauke farali anyi mana alkawarim zamu sake komawa mu sauke farali lalle lu'ulu'una kyauta ce daga Allah. "Amman baka ganin idan wannan abin yayi yawa za,a dinga jin tsoron dosanta da sunan aure. Wani irin zabura yayi. "Ke kina da hankali kuwa,tabbas na yadda baki San ciwon kanki ba,aini kiga nayiwa lu'ulu'una aure sai naga ta taka kololuwar matsayi a ilimi. Ammi ta katseshi da fadin " Kana son kace koda mijii yazo bazatayi aure ba? "Kinga jinan, wallahi ko dan gidan dangwatai ne ya zo neman aurenta sai na cika burina kan na aurar da ita gareshi in bazai jira ba ya kara gaba,ni nafison ta Sami arziki na kashin kanta ba na mijin ta Wanda ko yaushe zai dingayi mata gori ba ita kadai fa na mallaka sai na baiwa kowa kunya akanta bazata yi irin rayuwar danayi ba muddin ina raye sai ta zama a bar kwatance. Ammi kawai jinjina Kai takeyi cike da takaici. "Amman yakamata ka sani tuni ubangiji ya gama tsara mata rayuwar ta. Kafin ya yi magana ta mike tabar gun dan ta tabbatar ta baro rigima muddin bata dan kwaice daga gun ba.   Bayan an tashi a makaranta ta dade tsaye tana Jiran napep duk Wanda ta tsare sai yace ba nan zaiyi ba Iphone dinta ya soma ringing ta dubi fuskar wayar. "Wayyo Allah Abu ne.. Ta ratsa Kore tare da kafe wayar a kunne. "Ina kika tsaya kusan awa guda da tashi?. "Abu mota nake jira har yanzu bansamo ba Amman insha Allah yanzu zan karaso. "To shikenan sai kin dawo. Ta maida wayar cikin jaka ta soma tafiya cikin hanzari wani dattijo Mai napep ya hangeta har ya wuce ya fahimci akwai damuwa a tattare da ita ya dawo da baya yayi parking hadi da dan leko da Kai . "Ina zakije? Kamar zatayi kuka. "Sharada. "Bisimillah,shigo muje. Tunda ta shiga napep take ta faman sake sake. "Munzo sharadan. Tayi firgigita tana kokarin dauko masa kudi dari biyar ta mika masa ta sauka zata tafi. "Tsaya ki karbi canjinki. "Kaje kawai . "Nagode sosai. Sai da yaja babur din ta gane bai kaiga inda takeson tsayawa ba duk taji ba dadi tabbas yau zatasha tafiyar ƙafa gashi tabashi dukkan kudin ballantana ta sake shiga wani,kwanar mai kwaikwa zuwa masallacin juma,a na sharada akwai tazara yazatayi? Wata tsohuwa ta hanga rike da uban kullin kaya har rankwafawa ta danyi tafe take dakyar tausayi ya kamata tuni ta mance da tata matsalar. BILKISU H MUHD,✍️ [18/08, 4:20 pm] Bilkisu H MUHD: _*GABA DA SO*_              _BY_ *BILKISU H MUHD* Phone 08031307884 Page 3 *MARUBUCIYAR* ILLAR SABO RASHIN RABO YA YI SAKE ZAFIN HAWAYE NA BAKIN KAZAFI WAYA FI SONTA GORO DA SANKARA JINI BIYU DACEWA KAUNA CE BAYAN KUSKURE MATSALAR KAUNA TARAIRAYA DAKE NA DACE AKWAI BANBANCI BAKIN KAZAFI MULKIN MALLAKA IZZATU BAYAN KUSKURE KA AURE NI KYAUTAR ZUCIYA *sannan yanzu ta zauna ta kure basirarta gun rubuta muku littafin da bata taba fitar dashi a takadda ba littafine Wanda a online tafara rubutashi , littafin yazo da sabon salo tare da sarkakiya hadi da soyayya mai taba zuciya kowa yaji sunan littafin GABA  DA SO  zai sojin menene agaba da so daman da akwai abinda yake GABA DA SO,to karanta wannan littafin dan sanin menene ke GABA DA SO.* makaranta kundai san yadda alkalaminta🖊️yake.  Wanda ya santa ya santa Wanda bai santaba yakamata ya gwada karanta books dinta lalle bazata baku kunya ba. Sannan zaku samu dukkanin littattafai na ta hanyar 👇🏻👇🏻👇🏻 Wattpad:👇🏻 @bilkishmuhd Arewa Book:👇🏻 bilkisuhmuhd WHATSAPP GROUP NA BILKISU H. MUHD👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/Fp8jRB4MGGqB1I6J9gc0NE?mode=ac_t WHATSAPP CHANNEL NA BILKISU H. MUHD👇🏻 https://whatsapp.com/channel/0029VarKaWtBfxnxJ2STpI1o FACEBOOK GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻 https://www.facebook.com/groups/1845344956261189/?ref=share&mibextid=NSMWBT BUSINESS GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/IOFJMOHiTTMJ9cNLRroppc?mode=ac_t ------------------💥 Tunda ya rasa mahaifi sa yake ji shi tamkar wanda aka dauke shi daga cikin inuwa aka maida shi tsakiyar kwalleriyar rana, Amman bai san mai yasa ba haduwarsa da Aisha ya sauya komi, itace wacca ruhinsa da zuciyar sa ke mutukar so, tabbas yanzu ya soma jin rayuwa nayi mishi dadi, yanzu yasomajin yana son rayuwa. Aisha ta zama rayuwar sa farin cikin sa, hakannan ta zama burinsa.     Sai dai wani fannin ya kan ji tamkar kirjinshi zai fashe idan ya tuna yana soyayya ne da babu yakan tsinci kan shi cikin wani irin tashin hankali, eh babu zai ce mana tun da bashi da tabbaci akanta sai dai yakanji sanyi da rangwame idan ya tuna cewar Allah na karbar addu, ar wanda ya roke shi da izinin Allah koda tana karshen duniya wata ran zai mallake ta kamar yadda yake ji ajikinsa, ya soma sonta da wasa ya maida ta tamkar nishadinsa idan yana jin nishadi yakan kirata kawai musamman idan yana son yin yaran hausa duk da ba Mai son magana bace cikin hikima da dabara yake Mata wayo har ta saki jiki dashi batare da ta sani ba ahakan yayi mutakar sabawa da ita ahankali soyayyarta ta dinga hudashi musamman da ya fahimci tana da kananun shekaru sai yayi amfani da hakan  ya koya mata sonsa yadda bazata iya ba idan babushi sai dai akaf shakuwarsu ya fahimci cewar akwai matsala ita din kuma matsoraciya ce ya kuma fahimci tana mutukar kaunar mahaifinta kuma tana kokarin bin umarninsa dan haka yake fuskantar kalu bale a kaunar su. Yana zaune a hadadden office dinshi wanda tsananin haduwarsa tamkar fadar wani basaraken ma aikata ake so ya tantance sabobbin da za'a diba a kamfani mutum shida kawai ya iya gani acikin darurruwar muta ne karshen sai wasu ya wakilta rashin daga wayarsa da Aisha batayi ba duk shi ke damunsa yanajin ajikinshi tamkar bashi da lafiya komawa yayi gida. bayan yakoma gidama yaci gaba da kira nan ma bata dagaba yanzu ne ya kara tabbatar da shakuwar su ya kasa zaune ya kasa tsaye komi yayi masa baki kallon komi da kowa yake a haka su kansu ma aikatan gidan sun lura da haka, duk da ba mutun ne mai son magana ba gaba daya jisukeyi babu dadi musamman  Jafar da Ayan wadan da ayanzu sune mafi kusanci dashi sabida kasan cewar su musulmai Kuma suma hafcase ne sai dai Ayan balarabane shi Kuma Jafar dan Iran ne amman asalin mahaifiyar su hausawa ne haka kuma Inka gansu hausawa ne sak sai dai hasken fatar da suke dashi shima din ba sosai ba dan Zaruk yafisu haske nesa ba kusaba. Jafar ne da Ayan suke tattaunawa" kwana biyu kenan bashi da walwala bantaba ganin boss cikin wannan yanayi ba,Ayan yace" to ko Kuma bashi da lfy"kai banace ba ,rabona dai da ganinsa cikin wannan yanayi tin lokacin da aka kama dan uwansa osi,duk cikin harshen turanci suke wadannan maganganun" mai yasa bazamu gwada kiran osi ba? " wallahi zurfin ciki bayyi ba yau da ace boss zai gaya mini matsalar shi ko ace zan san matsalar zan iya yin komi akai, bashi da magana, amman yanayin sa ya nuna yana cikin matukar damuwa. " ina kasani boss bazai so haka ba kawai muyi mishi addu, a. "dai dai da minti daya bana son ganin shi cikin damuwa wallahi boss ya fiye mini komi, bantaba ganin mutum irin saba mai mayar da matsalar wani tashi. Daga can garden suka hango  yana ta faman danne dannen waya yana kuma kai komo. Daga inda Jafar yake hangenshi kamar zai saka kuka. " Ya Allah ka kawo mana mafita. Zaruk ya koma ya zauna akan wata doguwar kujera irin ta turawa wanda a kayiwa gun rumfa da wata yar'bukka abar sha, awa ya  zube wayoyin nashi akan table cikin yanayin damuwa daya daga cikin wayoyin ya soma ringing da sauri ya dubi wayar bro ya gani rubuce a fiskar wayar ya saki ajiyar zuciya a sanyaye ya dauka hadi da karawa a kunne. "Assalamu alaikum. " hi bos yau banji kaba. " ina cikin koshin lfy. Jin muryar sa ya tabbatar masa cewar akwai damuwa sai  yaji kamar ya shigo ta cikin wayar dan ya sani in zai kwana yana lallashi  bazai taba jin komi daga bakin saba idan kuwa suna tare kwakkwafin sa zai sanya ya gano komai. "my boss please, and please kada ka ce dani babu damuwa ina rokon alfarma ka gaya mini inba hakaba na rantse zan toho. ras gaban Zaruk  ya fadi yasa ni zai aikata, zuwan sa kuma zai haifar da babbar mosifa, zuwan shi zai iya kawo sanadin rasa shi, yana kaunar sa matuka bazai iya jure rasa shiba a duniyar nan yana yi masa kauna irin wanda zai iya yiwa wanda suka fito ciki daya da sauri ya kwarara kansa yasaki rai. " brother kana jin zan iya samun matsala maina rasa a wannan duniyar, na sani mutuwa dolece nima zan mutu kamar yadda iyayena suka mutu dole zan sawa kaina hak'urin wannan, to amman bacin rashin su bani da wata matsala duk wata daula da hamshakai suke tutiya dashi ina da, sannan ina da dan, uwa wanda yake mutukar kaunata to kagani bani da wata damuwa, kawai dai ka kirani a daidai lokacin da na farka daga bacci Wata doguwar ajiyar zuciya osi ya saki tare da duba agogon dake daure a tsintsiyar hannun shi. " bro bacci a irin wannan lokacin? " mun dan zazzaga camfany shi yasa "Naji dadi, yanzu bani labari, haka suka cigaba da hirar abinda ya danganci kamfanin sa dake Nigeria.  ---------------------💥 Kwance take tayi ruf da ciki da littafi ajiye agabanta karatu takeyi Amman Tama rasa Mai zata karanta komai ya kunce mata tadaina daga wayar sane don ta gwada ta yadda zata rabu dashi tanajin babu dadi ta yadda take cin amanar Abu  sai dai hakan yasa ta jigata sosai meyasa ta bari hakan tafaru da ita batasan lokacin da sonsa ya hudata hakaba tana kuma ji ajikinta kamar yana cikin damuwa Ta sauke ajiyar zuciya game da tsurawa handset dinta ido kamar tana sauraron kira ta ture littafin dake gabanta gefe ta mike zaune kanta ne ya dinga Wani irin sarawa bazata iya jurewa ba daukar wayar tayi ta shiga loda number sa ciki kira ta shigayi sai dai har ta katse ba,a daga ba sai da ta maimaita Hakan kusan sau uku babu alamar za,a daga tilas ta hakura ta koma kasa kan tayis ta kwanta tana jan wasu ayoyi azuciyar ta ko taji sanyi tana karatun tana kissima kammanninshi . Bata sanshiba Amman tanajin ajikinta zata soshi ko ya yake da wannan tunane tunanen bacci yayi awon gaba da ita ,bacci Mai tattare da mafarkai iri'iri. Washe gari wunin ranar haka tayishi cikin rashin kuzari zo kaga tashin hankali gun Alhaji Ibrahim gaba daya ya wuni yanayi mata hayaki da rubutu wai kila ana son taba mata tauraron tane wani turare daya gumbuda mata sai da ta kusan barin duniya dan tsabar tarin wahala bai iya fita ko kofar gida ba cike yake fal da zullumi ita kuwa Allah, Allah ta dingayi ya fice ta sake kiran sa ko zai daga kiran haka ne yasa ta kwarara jikinta hadda debo su wanki tanayi . A sitting room tana jiyo su yana magana da Ammi. " Mai nace dake ,so ake a tabata yanzu dataji hayaki bagashi ta mike ba. Ammi kawai binshi takeyi da kallon ta kaici ita kuwa can cikin zuciyarta tana tausayin Abu tana Kuma tausayawa kanta aranar ko masallachi baije ba agida yayi sallolinsa. Tun karfe tara ta tattara ta koma dakinta. Karfe dayan Handset dinta ta hanga yana fidda haske alamar kira ya shigo, kamar yadda ta saba ko yaushe wayar tata a silent yake  koda yar uwa mace  Abu beyadda ta kira taba wai kada su juyar mata da tunani Rahman ce kadai ya amince suyi mu'amala da ita sabida tare suka taso sannan gidan su yan bokone sannan ko yaushe intazo zai ga karatu suke yi. Abinda besani ba ita din ce ke kokarin rusa masa ginin daya dade yana ginawa. Har wayar ta katse wani kiran ya sake shigowa bata iya daukaba tunanin Abu takeyi da kwalla taf idanunta. Ya zabi ya hana kan shi komi ya gyara ta duk wani abun daya danganci kayan gayu sutura mai tsada turarurruka maya mayen gashi  kafin ta zama haka har dako yashayi sukanyi kwanaki basu dora tukunya ba muddin zai biya mata bukatar makarantar boko Yakanyi alfahari kansa ya fasu a duk lokacin da ya kalleta baya son kowa ya rabeta musamman ma da baiwar da Allah yayi mata ya bayyana kwakwalwar ta tamkar bata mutane ba duk abinda kwakwalwarta ta gani sai ta dauka tamkar wanda ake bude mata kwakwalwarta ajuye mata Yana mutukar kaunar ta fiye da yadda yake kaunar kansa haka ne yasa ya saka mata tsaro sosai tare da takunkumi ya kuma takure ta, yana sakar mata fuska sosai amman idan aka zo batun karatu baya sassauta mata yana jin duk wanda ya rabeta yana sa rai da cutar da ita zai yi dan haka koda wadanda suke jini daya bai yadda su rabe taba. Wayar na sake cigaba da ringin akaro na biyar da sauri ta mike tayi tattaki zuwa bakin kofa kamar yadda ta saba a duk sa'adda zatayi waya ta kulle tare da murda key ta koma ta rufe windows duk sabida wai kada iska ya debi maganar ta ya kai waje ta komo ta zauna ta janyo bargo ta rufa bayan ta dauki waya "Ishahh Ta yadda ya furta sai da yasanya ta saki wani dogon ajiyar zuciya.,bazai nuna mata ya damu da rashin daga wayarsa da batayi ba, tasanshi ba lalle yayi mata maganar  ba mutunne shi mara son dawo da magana baya idan abu ya wuce bai fiya maimai tashi ba. '' bakiyi bacci ba? Jinjina kai kawai tayi tamkar tana gabansa. "Ina son ki hadani da Abu gaba daya idanunta sukayo waje jikinta ya hau rawa jitake yi ma kamar ya gama gaya Masa  cewar suna soyayya har ta soma tunani hukuncin da zai yanke mata ya katse mata tunani. ''ina rokonki da ki amince, ina ji ajikina kece wacca Allah ya zaba mini, tunkan nasanki kike zuwan mini amafarki bansan kiba amman nasan muryarki, ki amince mini nayi alkawari, baza kiyi dana sani ba. "ba yanzuba ina jin tsoro papa zai dauki mataki a kaina baya son na kula kowa kumama dan baka ganni bane nifa karama ce ban.... " kullum haka kike cewa amman ai dolene ya aurar dake ko tunda kina ganin lokacin baiyi ba ,kawai kiyi mini alkawari baki da mijin da ya wuce ni ni kuma in Zaki kai shekaru dari nayi alkawari zan jiraki- - - "Kayi hakuri. Akufule yace " Nacinye shi... " Shiwa Ta tambaya. Hakurin mana Batasan sa adda ta dinga dariya ba har yanajin sautin dariyar cikin wayar sa. "Wallahi, idan zan rasa ki, zan haukace. Ban san yadda zan iya cigaba da numfashi ba, Ina sonki baby ina mutukar sonki Kada ki barni. Kada ki gushe daga zuciyata. Kada ki sa ni rayuwa ba ke ba. Zai fi sauki a cire zuciyata gaba ɗaya. Yagama kashe mata zuciya wani irin sonsa ne ke tasowa daga can cikin ranta. " Bansan kiba ban taba ganin kiba kawai sonki  Allah ya halitta min bansan mai hakan ke nufiba naji kawai ina tsananin sonki haka nayi Alkawari tsakanina da Ubangiji bazan taba aure ba muddin kina raye duk kuma yadda zaki boye mini nayi alkawari sai na zakuloki domin Allah ya halicce kine dominni haka nake ji ajikina sai kin zamo tawa,tawa ni, ni kadai. Takasa ce masa komai tasani duk yadda yakeji tanajin fiye da hakan "Allah ya hada fuskokin mu ,shine kawai Mai wahala agare ni duk Wani tsaro na Abu zan iya ji dashi nasan yadda zan bi dashi. Hmmmm kawai tace yayinda ya shiga yi mata hirar da dole ta saki jiki dashi sosai  hirar tasa mai tattare da bugun ciki yana son sanin a inda take sai dai duk yadda hirar ta kaiga yi mata dadi bata sake ta sanar dashi a Wani state take a Nigeria ba hakan ya tabbatar masa da cewar tabbas tana da mutukar wayo Kuma tana bin dokokin abbanta Hakan na Kara daga darajarta a idanunsa. " ina zuwa. Tace dashi yauma bata jira maizai ceba ta katse wayar. Zubewa tayi agodo ta shiga rusa kuka kukan da takejin shine kadai zai sanyaya mata rai. To mutane na ya abin yake ne ,ga  Ikhlass na ganin cewar duk yadda Zaruk ke sonta bai kamo kafar taba ankya kuwa, kunfasan shi so makahone inda ace abinda take ikirari hakane ai da bata boye masa halinda zuciyar ta ke ciki ba,amman dai muje zuwa Bilkisu H MUHD -----✍🏻 [18/08, 4:20 pm] Bilkisu H MUHD: _*GABA DA SO*_              _BY_ *BILKISU H MUHD* Phone 08031307884 Page 5 *MARUBUCIYAR* ILLAR SABO RASHIN RABO YA YI SAKE ZAFIN HAWAYE NA BAKIN KAZAFI WAYA FI SONTA GORO DA SANKARA JINI BIYU DACEWA KAUNA CE BAYAN KUSKURE MATSALAR KAUNA TARAIRAYA DAKE NA DACE AKWAI BANBANCI BAKIN KAZAFI MULKIN MALLAKA IZZATU BAYAN KUSKURE KA AURE NI KYAUTAR ZUCIYA *sannan yanzu ta zauna ta kure basirarta gun rubuta muku littafin da bata taba fitar dashi a takadda ba littafine Wanda a online tafara rubutashi , littafin yazo da sabon salo tare da sarkakiya hadi da soyayya mai taba zuciya kowa yaji sunan littafin GABA  DA SO  zai sojin menene agaba da so daman da akwai abinda yake GABA DA SO,to karanta wannan littafin dan sanin menene ke GABA DA SO.* makaranta kundai san yadda alkalaminta🖊️yake.  Wanda ya santa ya santa Wanda bai santaba yakamata ya gwada karanta books dinta lalle bazata baku kunya ba. Sannan zaku samu dukkanin littattafai na ta hanyar 👇🏻👇🏻👇🏻 Wattpad:👇🏻 @bilkishmuhd Arewa Book:👇🏻 bilkisuhmuhd WHATSAPP GROUP NA BILKISU H. MUHD👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/Fp8jRB4MGGqB1I6J9gc0NE?mode=ac_t WHATSAPP CHANNEL NA BILKISU H. MUHD👇🏻 https://whatsapp.com/channel/0029VarKaWtBfxnxJ2STpI1o FACEBOOK GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻 https://www.facebook.com/groups/1845344956261189/?ref=share&mibextid=NSMWBT BUSINESS GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/IOFJMOHiTTMJ9cNLRroppc?mode=ac_t ------------------💥 ta tunkari tsohuwar. da sauri ta karbe kayan hannunta "Sannu kaka,Ina zakije? "Yauwa jikata yar albarka,zanje gida ne, "Amman Ina ne gidan,wacca unguwa? "badawa nake,can zani. "bara natsarar miki abun hawa ya kai ki ko. "da kin barni sannu a hankali zan iya karasawa,kune yaran yanzu bakwa jurewa tafita. wannan kalmarce ta sanya ta karewa tsohuwar kallo babu alamar wahala atare da ita asalima atamfar dake jikinta ta supar holland ce babba takalmin kafarta da gyalen da ta cukyikuyeshi a wuya su kadai kayan kudine abin kallo wanda ba jikin kowaba ta jinjina kai kawai kila rikici ne kawai ta tsufa "a,a kaka badawa fa ba nan bace,kibari kawai. Kan kaka ta sake magana tini  ta tsayar da napep. " badawa zaka kaita dan Allah ka tabbatar da ka ajiye ta a kofar gidansu kaji. "naji Amman abani dubu daya. " Haba malam kana ganin dai tsohuwa ce ka rage mata. " Shikenan naji kawo dari Tara, wallahi dagashi babu ragi. Ikhlas ta juya ta kalli tsohuwar. "Kaka kinji abinda yace. " shiyasa nace aƙafa zani,kuma kinganni nan ko naira biyar ban fito da itaba ki kyaleni kurum. Ai bata gama rufe baki ba mai adaidaita ya kama gabansa,ita dai batajin zata iya barin tsohuwa agun ga hadari na faman ganga mowa Haka tasake tsare wani wai tana tunanin za,a dubi tsufanta akaita fir kowa yaki wata dabarace ta fado mata Iphone  dinta ta da karamar wayar ta dauko daga cikin jaka ta nufi Mai siyar da man dake gaf da inda suke tsaye ta riga ta tabbatar da nan ne gun zamansa har gidan su tasani makocin su Kawar Rahama ce dan haka batayi shakkar dosar saba "Malam ni yar nan unguwar ce dan Allah ga wayata kabani aron dubu biyu zan kawo maka kudin anjima sai kabani wayar tawa. "Tab lallema yarinyar nan ance da ke ni soko ne kawai dan kin maidani shashasha ki kawo mini wayar sata kice na baki dubu biyu lalle kinci Kai, ki bar gunnan ko na kira yansanda nace dasu ga barauniyar waya nan. ta koma gefe ta tsaya cikin tunanin mafita Faisal wanda tauraron shi ke haskawa mutum ne mai ji da kansa ga izza tamkar wani basarake kai daganinsa zaka fahimci irin mutane nan ne "yan takife marasa tsoro kwayar idon sa kadai zaka kalla ka tabbatar bashi da kunya ba kuma shi da tsoro baya shakkar taka kowa kuma bashi da kunyar firta magana a lokacin da ya so duk girmanka zai iya yagaka a ɗabi'unsa kaf babu abin birgewa kamar kyautar sa yana da kyauta na ban mamaki haka kuma shi din yana da mutukar kyau, kyakkyawa ne na gasken gaske sai dai shi  wankan tarwada ne wato chocolate colour tunda ta fara wannan hada hadan yake kallonta birgeshi takeyi ayadda take actin dinta kyakkyawar ce ita ga kananan shekaru babu abinda yafi Jan hankalinsa da ita irin dimple dinta Wanda ko magana takeyi lobawa yake ga dan karamin zagayayyen bakin ta wanda da gani zayyi dadin kiss take ya shiga ayyana gashinan sun kebe da ita. Shifa Faisal idan yaga mace ko asuturce take zai kalle ta ne a tsirara, ya kware sosai gun iskanci koda matar aure ce ta kawo kanta indai mai kyauce zai amshi gayyatar ta in kuma budurwa ce muddin tana mu,amala da maza barkatai to zai yaga ta ya kyamaceta shifa tsabar kwarewar sa yana ganin mace mai bin maza zai ramfota,duk da tantirancin sa Amman ya tsani mace mara kamun kai. dirowa yayi daga kan motar ya nufeta. " Ko zan iya taimaka miki,? Yafada yana watso mata wani mayen kallo. Kallo daya tayi masa tayi saurin kawas da kai sabida yadda taga yana wani ƙare mata kallo. " atakyace tayi masa bayani. Ya kunshe wata dariyar mugunta aciki. "zan baki sama da dubu daya kibata har tasami dan canji amman da sharadi. Tadago da idanu luuu tana kallonsa " Zan baki duk abinda kike bukata sabida naga kina son taimako,ki bani lambar wayar ki. bata iya ha'inci ba ba kuma tayin karya sai dai a yanzu zata iyayin duka biyun domin taimakon tsohuwar nan. Batasan sa adda ta shiga lissafo masa wasu lambobin karya ba. Tunda ta fara karanto mishi ya dora idanunshi akan kirjinta ko kiftawa baya yi tsabar kwarewa babu yadda za'ayi ta iya fahimtar yadda ya ke kallon nata jiyakeyi kamar zai ruƙumƙumeta. cikin dashasshiyar muryar ta mai fusgar duk wani mai sauraro tace " kudin sunyi yewa. Ta danyi mishi nuni da tsohuwar dake dan nesa dasu. " ita ce nake son biyawa kudin mota, nasan dubu daya zai isheta inya so sai ka bata dubu biyu tarike canji a hannunta yana kare mata wani mayen kallo. "oh no, Ai kyautar manya zaki yi ta yadda zata ji dadi kawai bata dubu biyar sai Allah ya hada mu cikin ladan. da sauri ta kada kai. " nagode, amman kabata dubu biyu. " ke fa, bakya bukatar komi? " hakan ma na gode. Ya mika mata dubu biyu ta karɓa ta yi masa godiya hadi da saurin barin gun. Wata doguwar ajiyar zuciya ya sauke cike da tsananin bukata zai bar gun ya hangi iphone a aƙsa ƙasa ta lulluɓeta ya ɗan durkusa ya dauka fuskar wayar yaga hoton ta  zai bita ya bata wani tunani ya zo mishi komawa yayi cikin motar sa. ----------------------------------------- Alhaji Ibrahim na ta Kai komo yakasa samun nutsuwa lokaci lokaci yakan Kai duba ga agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa ammi tafito daga kitchen "Haba Alhaji ikhlas fa ba yarinkya bace ballantana ta bata tana kuma da kamun kanta balle kace tatafi gantali Ina tunanin wani muhinmin abunne ya tsayar da ita. "Kinsani kinsan yadda nake da tarin makiya da Y'an bakin ciki zasu iya yin komi akanta zasu iya lalata mata rayuwa zasu iya yi mata asiri zasu- Cike da takaici ta katseshi. " haba Alhaji yakamata ka sani koda duk duniya zasu taru akanta don su cutar da ita muddin Allah bai amintaba babu abinda zai sameta. Yaja tsaki. Mtss. "Kinga rufamin baki,bazaki taba gane waba,waima shin kin bata rubutun tsarin jikinta jiya tasha,ko,ko dai yauma kin mance? Yakafe ta da ido. "nikam na sha,afa da zaka yadda da shawarata kawai ka mikawa Allah lamuran yarinyar nan,inko ka cika yin shishshigi sai ya barka da iyawar ka. Tini idanunsa suka juye zuwa jajaye. "Nace da ke,ke na barwa lamarinta ko Yaya wallahi idan baki fita daga idanuna ba zan saba miki Sumsum ta bar masa gu cikin faɗin Allah ya kyauta. Atsorace ta shigo gidan tana tafe kamar wacca kwai yafashewa aciki tuni yayi kanta da bugu da gudu ammi tafito daga daki ta shiga tsakaninsu. Yana huci. " Ki matsa yau sai ta gaya mini gidan ubanda ta tsaya,Inba haka ba sai na lahira yafita jin daɗi. Cikin kuka ta zayya ne musu abinda ya faru Cikin daga murya. "Ashe baki ajiye wannan banzan halayyar takiba,idan kikayi wasa da wannan raunannan zuciyar taki za,a dinga cutar dake, ke dai da abin da ya Kai na tausayi da Wanda bai kaiba duka tausayi yake baki. "Abu matar tsohuwa ce shiyasa na taimaketa---- "dallacan yi min shuru,ita din na tabbatar tana da jikoki da dangi,kina son kice kin fisu damuwa da ita ne,ko kuwa kin fisu tausayinta. "Kayi hakuri bazan sake ba. Kofin dake kusa dashi ya dauka ya cillo mata ji kake kum a goshinta ta dafe gun cikin  tsananin azaba. Yaci gaba da banbamin fada. "Aisu jikokin nata ko "yayan nata sunsan tsohuwa ce suka bari tafita,sabida sunga zata iya ne,kuma daga yau Ina son ki cire wannan shegen tausayin daga zuciyarki in ba hakaba zamuyi ta samun matsala da ke,ke inma takaice miki muddin kika cigaba da tafi da zuciyarki ahaka bazan yafe mikiba,tashi kiban guri. Ammi zaune akan tabarma,yayin da ikhlas ke zaune akan kujera ɗan tsuguno tana wanke wanke gaba daya tunanin inda ta yadda wayar ta take kafin ta fito daga daki ta duba jakar ta bataji wayar ta aciki ba. Ammi ta numfasa." ba,a biyayya ga sabawa umarnin ubangiji ko da kuwa umarnin iyaye ne. Ikhlas tadan dakatar da wanke,wanken tana kallon Ammi. " Ina nufin kada ki Soma hawa layin da Abu ke son ɗoraki dan shi tausayi yanki ne na imani,kada ki fasa taimakawa Wanda ke buƙatar taimako muddin kina da yadda zakiyi, Wasu hawaye suka silalo kan kuncin ta sani Abu ba zai taba daga mata kafaba tabbas akwa kura. Ammi ta kafe ta da ido tana nazarinta  ta sani akwa abinda ke damun ta. "Ikhlas ai anwuce gurin ya kamata a ce kin kwantar da hankalinki indai ba kuma akwai wata matsalar ba. Kokarin ɓoye damuwarta tayi. "Ammi naji tsoro naga ran Abu ya baci sosai, Ƙokarin kwantar mata da hankali take. "Kada mu biye mashi shi wani irin baudadden mutum ne.   A dakin ta gaba daya tagama zazzage ko ina tare da juye dukkan kayan dake cikin jakar har yanzu gani take zata iya ganin wayar  ko ina na dakinta ta hautsina babu alamar wayar ta. Zama tayi dirshan a kasa kuka take yi sosai komi nata na cikin wayar yanzu mai zata cewa Abu Rahama ce ta shigo dakin baki bude take duban aminiyar tata wadda ta koma tamkar wata taɓaɓɓiya. "ke ikhalas lafiya kuwa, mai kike nema haka? Cikin muryar tashin hankali. "wayata na duba ko'ina bangani ba. Azabure tace "kina nufin iphone? Ikhlass ta jinjina kai. ' tab babbar magana, ke kin tabbatar da kin shigo da ita cikin gidannan? Shiru ikhalas tayi tana tunani. " ina tunanin agun da na saka wannan tsohuwa a mota na yadda wayar. " wacce tsohuwa kuma. Labari tabawa Rahama yadda komi ya faru. "Ai kinji garin neman gira kin rasa ido, tasowa zaki yi mubi hanya. " to amman mai zancewa Ammi? " zan roketa cewa zanyi zaki rakani gidan kitso. ----------------------------------------- Tamgamemen gida ne wanda kana gani ka san ma mallakin gidan yaci ya tada kai gidan na dauke da wasu mahaukatan get guda uku kafin ma ka nutsa cikin gidan gaba daya intaluck ne tun daga get din farko har kawo na karshe inda zai sadaka da cikin gidan akwai bangaren ma aikatan gidan sai bangaren karen sa wanda ya ke kira da champion yana ji da karen mutuka  kamar yadda shima karen ke ji dashi,  sai can gaba shine shashin masu gida Zakuyi mamaki idan nace duk girman gidannan tsohuwa ce aciki sai ɗan ji kanta da kuma masuyi musu hidima girki shara, wanki da guga sai masu bawa furannin gidan ruwa. Setting room ne Wanda yagama gajiya da kayan alatu ga wani sassanyar kamshi dake faman tashi hoton  faisal ne kato window size tare da wani handsome kyakkyawa fari kwal kamar balarabe sai wani hoton wanda handsome dinne kadai ajiki yana faman murmushi sanye da kayan mu irin ta Hausawa an Rubuta Ahmad a jikin hoton da manyan baki sai wani hoton nashi wanda yake sanye da wando 3cotter da riga mai yankakken hannu yana amsa waya da alama baimasan an dauka ba, tabbas ko waye wannan,namusammanne agun Faisal . [18/08, 4:20 pm] Bilkisu H MUHD: _*GABA DA SO*_              _BY_ *BILKISU H MUHD* Phone 08031307884 Page 7 *MARUBUCIYAR* ILLAR SABO RASHIN RABO YA YI SAKE ZAFIN HAWAYE NA BAKIN KAZAFI WAYA FI SONTA GORO DA SANKARA JINI BIYU DACEWA KAUNA CE BAYAN KUSKURE MATSALAR KAUNA TARAIRAYA DAKE NA DACE AKWAI BANBANCI BAKIN KAZAFI MULKIN MALLAKA IZZATU BAYAN KUSKURE KA AURE NI KYAUTAR ZUCIYA *sannan yanzu ta zauna ta kure basirarta gun rubuta muku littafin da bata taba fitar dashi a takadda ba littafine Wanda a online tafara rubutashi , littafin yazo da sabon salo tare da sarkakiya hadi da soyayya mai taba zuciya kowa yaji sunan littafin GABA  DA SO  zai sojin menene agaba da so daman da akwai abinda yake GABA DA SO,to karanta wannan littafin dan sanin menene ke GABA DA SO.* makaranta kundai san yadda alkalaminta🖊️yake.  Wanda ya santa ya santa Wanda bai santaba yakamata ya gwada karanta books dinta lalle bazata baku kunya ba. Sannan zaku samu dukkanin littattafai na ta hanyar 👇🏻👇🏻👇🏻 Wattpad:👇🏻 @bilkishmuhd Arewa Book:👇🏻 bilkisuhmuhd WHATSAPP GROUP NA BILKISU H. MUHD👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/Fp8jRB4MGGqB1I6J9gc0NE?mode=ac_t WHATSAPP CHANNEL NA BILKISU H. MUHD👇🏻 https://whatsapp.com/channel/0029VarKaWtBfxnxJ2STpI1o FACEBOOK GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻 https://www.facebook.com/groups/1845344956261189/?ref=share&mibextid=NSMWBT BUSINESS GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/IOFJMOHiTTMJ9cNLRroppc?mode=ac_t ------------------💥 Fada doctor yakeyi sosai kamar zai rufe iyayen da duka . Duk inda wannan Mara imanin yake yakamata ayi Shari,a dashi,kin kuma dauki hakkin yarinkya wadda bataji ba bata gani ba asali ma babu alamar cewar tataba sanin wani inda hakan ta faru baza,ta Sami wannan matsalar ba gashinan ya lallata muku rayuwar yarinkya inhar ba,a dace ba da yuwuwar ta hadu da ciwon yoyon fitsari. Cike da kulawa likita ya mayar da kallon sa ga zainab wadda saboda tsabar wahala ta kode tayi wani irin rama. ",ya sunanki? Ya tambaya gaba daya idanun su duka a kanta, Tashiga hauhawa kamar mai jin tsoro. "Kugaya mini ina ne nan aina nake,mai nakeyi anan?ina tambaya kunyi mun shuru kowa na kallona kamar ba mutum ba. Kakarta ta toshe baki da hijabi tana kuka shi ko malam idanunshi sunyi jawar yanajin abinda yafi kuka zuciyarshi na faman tafarfasa. Likitan ya maida kai kasa yana cigaba da rubuce rubucensa.tsahon mintina biyar ya dago . "Yanzu kafin muyi komai zamu fara baku gado sannan za a yi mata taimakon gaggawa  kafin komai ya biyo baya "sannu zainab. Kawai binshi tayi da ido daga bisani tayi murmushi mai hade da kuka. Bayanin likita ya gama gigita su da dubun danasani musamman ma kakar ta. Zainab ta dubi kakar ta wadda ke faman kuka ta dauko hannu tana shafa fuskar kakar. " kema fyade yayi miki, yaji miki ciwo sannu kaka, mugune, Amman Ina sonsa. Dukkan wadanda ke dakin kallon kallo suka koma yi. " likita mai ke shirin faruwa? "cikin kunan rai ya dubesu. " tsahon wani lokaci takai cikin wannan sumbatun. Sai ga kwalla wani na bin wani a fuskar baban zainab "ka tambayi babarmu ita ta hana kowa zuwa inda take a wani daki ta ajiye ta kusa da bandaki ko fitila babu, abincima ba, a bata sai ta kama babu mai shiga gunta kawaicina ya hana na bibiyeta gashi na cutar da ita. babarmu kuwa kuka take yi sosai idanunta duk sun tattasa ita kuwa zainab daga ta kalli wancan sai ta kalli wannan sai tayi murmushi wani lokacin tayi kuka bara na barku anan Wanda zamu Dora nan gaba. --------------------------------------   Rakiya kina ganin wannan yaron zai saurare ni kuwa jibeshi fa tamkar shiyayi kansa, kai banajin zai Soni, "aikinji ki , kina abu kamar karamar yarinya waya gaya miki batun so akeyi, in batun so ake daman mai zaiyi dake mtss, magana ce kawai na kisaki data masu karfi dan wannan sai kin dire mishi sama da milyan guda ,dan haka idan yayi miki sai kiyi bayani ta sauke wani ajiyar zuciya " rakiya wannan ya cancanta,wannan dan shilan Aiko Nazir dina be kaiba , rakiya atura mishi milyan biyu banason murabu ina son mu kulla alaka mai karfi,ina sonsa"  ke Kam dadina dake kenan ,in kika kuskura kikayi mishi zancen soyayya zaki kwabawa garin ki ruwa kawai kedai kibi abinda na gaya miki. -----------------------------------------    Ya caba kwalliya har ya gaji ya fito sai kamshi yake Akan darduma ya ga kaka tana jan carbi ya kalleta yana murmushi ya matsa daf da ita ya ɗan rankwafa. "Kakata zan fita a nema min sa, a zan je gun mutuniyar. bata iya magana ba sabida addu, a take yi cikin daga hannu ya kama hanya zai fita daidai lokacin ta shafa " da izinin Allah daga kanta zaka ga darasu, daga kanta zaka kiyayi duniya sai ta wahalar da kai kuma har a bada tafi karfin ka, ko a zaman aure bazaka taba samun taba Ta sake daga hannu. " Allah na rokeka akan wannan baiwa taka ka nuna mishi iya karsa idan ka tsara cewar matar sace ka juya lamarin kada ya taba samu ta ka kuma azabtar dashi da soyayyar ta mai zafi kila hakan ya zamo sanadin shiriyar sa ta--- " haba kaka!! Irin wannan mugun jafa,i haka kamar ba jinin kiba. " wallahi kaima sai kayi kuka kamar yadda kasa iyayen yara kuka ko jikakeyi bansan abinda kake shukawa ba, wallahi kar nake kallon ka da idanuna biyu. tafice tabarshi tana nemawa ikhalas tsari ga fadawa tarkon azzalumi irinsa.   Rahama ce tayi kudin mota suka koma  sunyi iya duban su basu ga wayar ba suka dau hanya suna dubawa nanma shuru dole  babu alamar wayar komawa suka yi gida ajigace Allah ya taimaka Abu bai dawo ba. Sallama suka yi da Rahama ta koma gida ita kuma ta koma dakin ta cike da tunanin abinda zata gayawa Abu. Har karfe dayan dare bata iya rintsawa ba ta mike ta shiga bathroom ta dauro Alwala ta fito ta shinfida darduma ta dauko alkur'ani mai girma ta shinfida ta hau ta fara jero sallar nafila sai da taji kafafunta na neman gagararta tsayawa sannan tayi sallama ta janyo Alkur'ani ta soma tilawa. Karamar wayar ta ta hanga yana haske alamar kiranta ake da sauri ta mike cikin goge kwallar fuskar ta ta ratsa kore Assalamualaikum  ya ce kafin ta amsa ya fara magana,kada ki boye mini gaya mini maike damunki tayi murmushi yayin da kuka ke neman kwace mata" maiyasa kace   haka?" Baby nayi mafarki mara dadi yau akanki tin daga lokacin na kasa samun nutsuwa ta danyi dum cikin kokarin daidaita kanta" babu komai kaji," please baby kada ki juya mini baya in kikayi haka zan haukace Ina mutukar sonki  Ina sonki dayawa dan Allah kibani magani yau," magani wanna iri," ina son ganinki yau Ina son hotonki hakanne zai rage mini radadin danakeji , "Zuciyata ta samu natsuwa tun daga lokacin da kika shigo rayuwata." "Ki ce min 'Ina sonka' sau ɗaya, zan rayu da wannan jin daɗin har abada."shuru yayi yana son ji daga gareta,bata da niyar magana" baby zaki toro min picture ɗin yanzu? " kayi hakuri idan ka ganni bazaka soni ba " saboda me?"bani da kyau ni mummuna ce duk abinda yake mai kyau ajikin mace bani da---stop it,I say stop ya isheni haka ni nace kibani hotonki Ina sonki aduk yadda kike dan haka ki bar wannan shirmen" tsintar kanta tayi da fadin bani dashi,"ok to yayi kyau nagode duf ya katse wayar Wani irin son sa taji yana kara ruruwa acikin zuciyar ta, tanajin tausayin shi  kwanciya tayi akan darduma yazatayi ne tayaya zata iya cireshi arayuwar ta. Abu ne ya turo kofa daidai lokacin ta maida hankalinta kan alkur,anin dake gabanta . " ashe idon ki biyu " nakasa bacci. "ki dauko littafi ki dan taba karatu, karatu yafi zama da irin wannan lokacin. Wani kallon shakku ta koma yi masa, ta fahimci Abu ya dauki karatunta da muhinmanci fiye da ibadar ta  in banda haka Alkur'ni fa yagani ajiye a inda take fa bata ce komi ba banda binshi da ido da tayi tana son sanar dashi batan wayar ta amman takaici ya hana ta magana. Ya kamata mu waiwaya baya dan jin wanene Mahaifin Ikhlas wato Alhaji Ibrahim.       Tuna baya    Bai taba shiga aji dan koyon karatun boko ba,na muhammadiyya ma ba sosai yayi ba,in da ya lakanta hakan da rashinjin da ya shuka, alokacin baya shine bin kucakan matan lungu shine tare hanya yana dumbularwa "yan mata kirji shine tsokana shine gantali idan yafita tun safe baidawowa sai zai kwanta bacci yau iyayensa bazasu taba cewa sun moreshi koda ta hanyar tayasu aikin gida ba, sai d'aga murya akan tasu ko cewa sukayi mikon ruwa insha sai da kunkuni da buga kafa yake zuwa wani sa'inma ko kallonsu bayayi wadannan halayya nasa su suka saka iyayen suka sallamashi Hakan bai sa ya nutsu yagane cewa gajiya sukayi suka barshi da halinsa ba ko kadan befito daga dangin da suke da abin hannu ba kaf dinsu babu Wanda za,a nuna ace yana da dan abin hannu duk Wanda ka duba acikinsu beki a tallafa masa ba  dangin bawani yawa ne dasu ba har kawo lokacin da yarasa iyayen nasa bai sauya halayya ba tabbas hausawa na cewa idon iyaye mashine bai tashi gane kuren saba sai da ya rasa iyayensa anan ya gane cewar duk wani daga masa kafa da akeyi sabida mahaifansa ne yayyensa wa anda suke uba daya ma burus sukayi dashi haka ne yasa yatashi tamkar wani shashasha kowa kyamarsa yake bashida wani suturar kirki na sakawa idan kaga yaci abinci to dako yaje yayo a kasuwa sannan ya Sami kudin da zaici abinci yana dan shekara ashirin da bakwai yaɗan soma mallakar hankalinsa inda wani bawan Allah Mai suna malam isa ya jashi jikinsa ,malam isa kayan gwari yake saidawa idan aka siya Ibrahim ne ke kaiwa masu siye cikin mota sannan a sallameshi.  [18/08, 4:20 pm] Bilkisu H MUHD: _*GABA DA SO*_              _BY_ *BILKISU H MUHD* Phone 08031307884 Page 6 *MARUBUCIYAR* ILLAR SABO RASHIN RABO YA YI SAKE ZAFIN HAWAYE NA BAKIN KAZAFI WAYA FI SONTA GORO DA SANKARA JINI BIYU DACEWA KAUNA CE BAYAN KUSKURE MATSALAR KAUNA TARAIRAYA DAKE NA DACE AKWAI BANBANCI BAKIN KAZAFI MULKIN MALLAKA IZZATU BAYAN KUSKURE KA AURE NI KYAUTAR ZUCIYA *sannan yanzu ta zauna ta kure basirarta gun rubuta muku littafin da bata taba fitar dashi a takadda ba littafine Wanda a online tafara rubutashi , littafin yazo da sabon salo tare da sarkakiya hadi da soyayya mai taba zuciya kowa yaji sunan littafin GABA  DA SO  zai sojin menene agaba da so daman da akwai abinda yake GABA DA SO,to karanta wannan littafin dan sanin menene ke GABA DA SO.* makaranta kundai san yadda alkalaminta🖊️yake.  Wanda ya santa ya santa Wanda bai santaba yakamata ya gwada karanta books dinta lalle bazata baku kunya ba. Sannan zaku samu dukkanin littattafai na ta hanyar 👇🏻👇🏻👇🏻 Wattpad:👇🏻 @bilkishmuhd Arewa Book:👇🏻 bilkisuhmuhd WHATSAPP GROUP NA BILKISU H. MUHD👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/Fp8jRB4MGGqB1I6J9gc0NE?mode=ac_t WHATSAPP CHANNEL NA BILKISU H. MUHD👇🏻 https://whatsapp.com/channel/0029VarKaWtBfxnxJ2STpI1o FACEBOOK GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻 https://www.facebook.com/groups/1845344956261189/?ref=share&mibextid=NSMWBT BUSINESS GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/IOFJMOHiTTMJ9cNLRroppc?mode=ac_t ------------------💥 Faisal kwance akan wata doguwar kujera sanye da gajeren wando sai singlet kan kafet lemone ajiye sassanya kofin har wani raba yake daya daga cikin wayarsa ta dauki ruri ya kalli wayar ya basar har ta katse wani kiran ya sake shigowa yaja tsaki in bai daga kirannan ba bazata bari ya hutaba Ya ratsa kore ya kafa a kunne. "Hy, hot milk where are you? Muryar wata mata ta tambaya " Ina jin ki, kifadi abinda kike son fadi ko in katse wayar. Daga daya bangaren tace "oh my god, what wrong? "please malama bana son damu, nace kidaina kira, kawai ki turo test. " kayi hakuri ranka ya dade, daman ina son ganin kane, gaba daya na kasa samun nutsuwa. "ke mahaukaciya, agurina yanzu kingama bandaro, nagaji da tuwo ina son sauyi, Ta soma magana cikin damuwa. " kada kayi mini haka, yanzu haka na kama mana daki. "kinga inkin amince akwai wannan kanwar taki yar lukutannan ita kawai nake muradi, kiyi mata waya sai ta canjeki. Wata uwar ashar ta danna ya katse wayar. Ko ajikinsa ya gyara zamansa ya mika hannu ya janyo wata drowa wata yar karamar roba ya dauko ya bude wasu irin kwayoyi ne a ciki ya dauki guda shida ya watsa a baki ya kora da ruwa ya koma ya kwanta lamo tuni ya mance inda kansa yake. Bayan wasu awanni ya dawo hayyacinsa ya tashi ya shiga bathroom ya ware shaya a kansa ya dade ruwan na zuba akan nasa a hankali wani nutsuwa ya fara saukar masa sannan ya dauki soso da sabulu ya cuɗa jiki bayan ya gama ya dauraye jiki ya dauki tawul ya tsane jiki ya janyo daya tawul din ya daura.    Handset din ikhalas ne rike a hannunsa ya na faman shige da fice a ciki yayi murmushi abubuwan ta gwanin burgewa itace mace ta farko da ta soma birgeshi tana da kyau ta gama hada komi ga hotunanta da familyn ta da malaman makarantar su daya bangaren kuma hutunan tane data dauka lokacin saukar ta ya tsayar da idanunsa akan wani hoto data dauka babu hijabi sai dan siririn bakin mayafi data yane kanta dashi wasu daddeku daga cikin kwayoyin gashinta sun rufu akan fuskarta wasu abubuwa yaketa aiyanawa aransa,. Gaskiya yarinyar nan mai kyauce acan karkashin zuciyarsa ya dinga jin tanayi mishi wani irin kwar jini ya Kai yatsa yana zagaye saitin bakinta dashi tamkar tana gabansa wani irin azababban Sha,awarta ya dinga fusgarsa idan bai idar da nufinsa akantaba zai iya haukacewa. Tadade tsaye akansa bazata taba mance wannan kyakkyawar fuskar ba tsaf ta fahimci "yar aljanna  ce,sunan da talakaba ma ikhalas kenan tun lokacin da ta Kira ɗanta da surukar ta awaya tana basu labarin irin jahadin datayi akanta da suka tambayi sunan ta tarasa Mai zatace sai cewa tayi yar aljanna ita din haka take komi kankantar alheri kambamashi takeyi takasa mance fuskar ikhlas, tana jin ta a ranta ta rasa mai yasa To amman mai ya hada lalataccen jikan nata da wannan salihar. "mai sunan baba aina kasan wannan yar karamar yarinyar? Yayi murmushi. " kaka, kema kin yaba kenan, ko? Ya fada yana kallon ta. "nace aina kasan ta, ka bani amsa ba. " kakahh, manene naki na daga hankali nifa namiji ne, namiji wanda yasan abu mai kyau,dan haka na yaba. "Allah bazai baka ikon cutar da itaba,mutumin banza. Tana huci tana komi taciga da banbami. "Wallahi wannan tafi karfinka albarka na tattare da ita dan haka kayi ahankali in ba hakaba sai ka tafka dana sani. Ya dinga kyalkyala dariya. " Haba yar tsohuwa ni akwai matar da zata fi karfina a wannan duniyar tun daga larabawa indiyawa ballantana bakar fata yar mutsiyata,ai kawai Kisha kuruminki Ina tabbatar Miki da kyar ne in baza a kawo miki ɗan da zaki goyaba. Yana magana yana dariyar ƙeta. Carbin dake rike a hannun ta, ta daddage ta tsula masa tsakanin ta da Allah ta kai mishi dukan ya gantsare sabida ta shige shi har tsakar kansa. "ah kajimu da tsohuwa da Carbin zaki dakeni, sabida kawai ina son kawo miki tattaba kunne. Ta tsorata sosai kaf halinsa babu Wanda bata saniba Inya kwallafa rai akan mace duk ustazan cinta sai ya lalata ta yasan salo salo na yaudara idan yana narkar da kudi sai ka dauka injin kudi ne dashi yake bugawa mace daya ce ta gagareshi awannan duniyar itace zainab      Ya hadu da ita Kamar yadda ya hadu da ikhalas , zainab yarinyace "yar kimanin shekara ashirin da daya nitsattsiya ce yar malamai tana da kyau daidai nata haduwarsu da ita ya gama haukacewa kota halin kaka yana son kasan cewa da ita amman ko kallo bai ishetaba duk hanyar da yabi taki bari ta ce masa koda sannu haka ne yasa yadinga bin sahunta har ya yi bincike akanta yagama sanin komi akanta sai dai ya lura cewa iyayenta irin iyayennan ne masu gudun duniya hakane yasa ya sauya taku inda yaje ga mahaifinta ya nuna cewar yanason auren zainab abashi dama su dan fahimci juna,wannan dalilin ne yasa zainab ta fara tsayawa dashi da ike shidin maye ne ko ince shidin na da banne  yasan duk yadda zayyi ya mallaki zuciyar mace komi tsaurin ta iya kalamensa sun taka rawar gani gun mallakar zuciyar ta kallo daya yayi mata ta kamu da wani mugun sonsa sai dai hakan bai sa ta saki jiki da shi ba sabida wani mugun kunkyace da ita ko ido bata bari su hada dole ya boye maitarsa  ya kudurce a ransa dole ya biya bukatarsa koda sama da kasa zasu hade. Kafin mahaifinta yabashi dama da kansa ya tura mutane neman aurenta ya kuma ce a cikin wata daya yakeson agama komi,mahaifanta sun nuna sai dai asaka wata shida don sugama kintsawa,take ya nuna cewar baya bukatar komi shi yagama komi yana da komi duk da haka sunki amincewa haka yasa ya dinga bin danginsu har aka shawo kan mahaifinta ya amince zo kaga inda yadinga yi musu barin kudi akwatuna kawai sat hudu aka kawo basu sallama ba sai da sukaga gidan da za,a kaita da kayan dakin daya zuba Mata, duk anyi wannan sha, ani batare da sanin kowa nasa ba. Awata dayan aka gama biki ankai zainab gidan ta kowa ya watse inda yashigo tana zaune a kan sallaya ta kudundune Kai kuka takeyi sosai hannu ya Kai ya dagata cak ya zaunar da ita ajikinsa ya fara aiwatar da abinda ta kasa ganewa ganin yana neman zakewa yasa ta fara magana cikin raunannaniyar murya. "Jinakeyi sai munyi sallah ko. Cikin wata shakekkiyar murya. Jinakeyi sai da na biya sadaki na kuma cika duk wasu sharadai ko cewa akayi idan bamuyi sallah ba aure mu ya haramta? daman shi mutunne wanda bai iya rarrashi ba,jin maganar tasa tayi banbarakwai ahankali ta kada Kai hadi da tsuke baki akan gado ya direta yana kokarin sauke alkawarinsa duk yadda tayi ihu tayi kuka baisa ya sauraraba yadda yayi Mata Babu kyawun gani bai kyaletaba sai dai yaga bata iya motsin arziki ya Suri pillow ya koma sitingroom . koda asuba tayi da kyar ta mike tana tafiya cikin rintse ido da cije lebe ga wasu zafafan hawaye  na faman bin kuncinta wani irin zazzabine ya rufeta jitakeyi kamar mutuwa zatayi wanka tayi kamar yadda musulunci ya tanadar Mana azaune tayi sallah akan dardumar bacci ya kara dauketa . bugun kofa ne ya tasheta  batayi yunkurin tashiba tana tunanin Faisal zaije ya bude Amman sai taji shuru ta mike dakyar tana daddafa banga ta karasa ga kofar babu alamarsa kamar ma ya fita haka ta murda key babbar yayar ta tagani da kishiyar babarta fuskarsu Babu walwala jitayi jikinta ya kama rawa tana son jin da mai suka zo bata ankara ba sai jitayi yayarta ta dauketa da wani mugun mari har sai da ya haddasa Mata ganin kyallin wuta zata zube kasa kishiyar mamansu ta rikota itama ta wanketa da nata Marin kan kace maye gaba daya sun rufar Mata wani irin jiri ne ya debeta wani duhu ya ziyarci idanunta bata sake sanin inda kanta yake ba. ------------------------------------------- "baba kibari mu kaita asibiti bai kamata ace mun ajeta agida ba. "Idan ka Kara cewa sai mun kaita asibiti sai na tsine maka Kai baka ganin irin abin kunkyar data jawo mana. Ta rushe da kuka. Ta dubi dukkan mutan gidan ta soma magana. Duk Wanda ya sanar da cewar zainab na gidannan ba,a gidan mijin taba sai na tsine masa,a nan gida na zata ci gaba da zama a wannan dakin kuma ko tsakar gida baza ta dinga fitaba. Maganganun da ta dingaji kenan sama,sama akanta . Takara yin lamo kwakkwarar motsi takiyi. Allahumma ajirni fi masibati ta dinga maimaitawa,shin mai duk wadannan maganganun ke nufi mai ke faruwa da ita Ina shi Faisal din. baba nakasa yadda da abinda yaronnan ya fada,ni na yadda da tarbiyar da nayiwa yarinkyata. Tsawa baba ta daka masa Kai da Allah rufa Mana baki!!,ka  goda Allah ma da baice a biyashi abinda ya kasheba ta Yaya yaro zai kashe Mata uban makudan kudi haka sannan yace zai yi mata sharri wacece ita wayasan da ita, Ta rushe da kuka, Amman kanta tayiwa . "baba kiyi hakuri mu kaita asibiti komeye sai a dauki mataki daga baya dan girman Allah. Kanin babanta ya fada. Kaga kafita a idanuna,kowa kuma yatashi ya bar mini gida kada na kara ganin kafar kowa agidannan. Sumsum suka mike yayar zainab ta soke wata farar takarda agefen zainab " Sai da ta dainajin motsin kowa sannan ta mike zaune da kyar nan taci karo da takarda hannu na rawa ta dauka ta bude ga abinda tagani aciki. Ni faisal na saki zainab saki daya adalilin cin amanata da tayi atinanina na auri yar gidan malamai ashe abinda ban Sani ba zaben tumun dare nayi a takyai ce ko kadan bata kawo mini budurcin taba yanayin yadda na sameta tamkar wadda ta hayayyafa   tagama zubar da dukkan mutuncin ta a titi  amman a dalilin dattakon iyayenta na bar mata duk abinda na yi Mata bana  sonta a cikin rayuwata koda a mafar ki na. Takaddar ta zamo daga hannunta ta sake rushewa da kuka,sai dai kokadan ba kukan kazafin da yayi mata takeyi ba sai kukan ta Yaya zata iya rayuwa babushi bata wani dade dashiba Amman soyayyarsa ta game dukkan jinin jikinta Wannan kenan. Sati biyu kenan tana acikin wannan hali haka take jin wani irin ciwo na tasowa acan kasanta wanda koda fitsari zatayi sai da kuka yau kam abin harda su jini sai dai takasa fada ma kakan tata sai da ta fito daga toilet da baba tashiga taga jini kwance akasa tsoro yakamata da kanta ta shiga dakin zainab inda ta taddata tana ta faman numfarfashi Kamar wadda ake Shirin zare ma rai.  da gudu takira baban Zainab inda suka garzaya hospital da ita. [18/08, 4:20 pm] Bilkisu H MUHD: _*GABA DA SO*_              _BY_ *BILKISU H MUHD* Phone 08031307884 Page 8 *MARUBUCIYAR* ILLAR SABO RASHIN RABO YA YI SAKE ZAFIN HAWAYE NA BAKIN KAZAFI WAYA FI SONTA GORO DA SANKARA JINI BIYU DACEWA KAUNA CE BAYAN KUSKURE MATSALAR KAUNA TARAIRAYA DAKE NA DACE AKWAI BANBANCI BAKIN KAZAFI MULKIN MALLAKA IZZATU BAYAN KUSKURE KA AURE NI KYAUTAR ZUCIYA *sannan yanzu ta zauna ta kure basirarta gun rubuta muku littafin da bata taba fitar dashi a takadda ba littafine Wanda a online tafara rubutashi , littafin yazo da sabon salo tare da sarkakiya hadi da soyayya mai taba zuciya kowa yaji sunan littafin GABA  DA SO  zai sojin menene agaba da so daman da akwai abinda yake GABA DA SO,to karanta wannan littafin dan sanin menene ke GABA DA SO.* makaranta kundai san yadda alkalaminta🖊️yake.  Wanda ya santa ya santa Wanda bai santaba yakamata ya gwada karanta books dinta lalle bazata baku kunya ba. Sannan zaku samu dukkanin littattafai na ta hanyar 👇🏻👇🏻👇🏻 Wattpad:👇🏻 @bilkishmuhd Arewa Book:👇🏻 bilkisuhmuhd WHATSAPP GROUP NA BILKISU H. MUHD👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/Fp8jRB4MGGqB1I6J9gc0NE?mode=ac_t WHATSAPP CHANNEL NA BILKISU H. MUHD👇🏻 https://whatsapp.com/channel/0029VarKaWtBfxnxJ2STpI1o FACEBOOK GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻 https://www.facebook.com/groups/1845344956261189/?ref=share&mibextid=NSMWBT BUSINESS GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/IOFJMOHiTTMJ9cNLRroppc?mode=ac_t ------------------💥 Malam Isa shi ke zaunar da Ibrahim, yana yi masa karatun zaman duniya. Tausayin sa da shakuwarsu ya sa bai kyama masa ba, har ya ba shi auren ‘yarinyarsa. Bayan shekaru sun ɗan fara ja, anan ya fara jin ciwon rashin tsayuwarsa wajen neman ilimi — sakamakon banbance-banbancen da yake gani. Gaba ɗaya ba a damawa da shi; kullum kallon ɗan kauye marar wayewa ake yi masa. Sau da dama idan ya je kasuwa wajen siyayya, rashin iya lissafinsa ya kan sa costoma su fasa siyayya a gunsa idan ya tafka wani shirme. Sai ayita tsokanarsa anayi masa dariya, shi kuwa malam Isakarfinsa ya ƙare ya daina zuwa kasuwa. Dole dansa ya gaje shi, wanda kuma tasu bata zo ɗaya da Ibrahim ba haka ne yasa shi ya daina zuwa kasuwar. sai ya cigaba da bige-bigen nasa da shiga rigima. Gaba ɗaya ya kara birkicewa. A nan ne ya soma gane babban kuskuren da ya tafka — musamman idan yaga ‘yan uwansa suna buga bugansu duk da basu da karfi, amma duk abinda zasu ci baya gagarar su. Duk fitsarar sa sai da ya dawo yayi laushi. Haka yake binsu agindi-agindi ya boye duk wani tsiwarsa. Babban yayansu Malam Musa da Yaya Hamza su ke bashi abincin safe da zai ci da iyalinsa, sai dayan Malam Yusuf shi ke bashi na rana. Sai kuma gidan kanwarsa Binta wadda ta dauki nauyin na dare. Duk suna yin hakan ba don halin saba ba, sai don mutuncin matarsa. Yau da gobe sai Allah ,shine kadai baya gajiyawa da bayinsa domin yanzu kam ya soma fuskantar wulakanci inda suke bashi abinci a agantale yayinda yaran su suka gama raina shi. Har kananan yaran su, idan sun tattare ragowa abinci sai su hada masa haka zasu dinga cin karo da gashi majina duk aciki babu yadda suka iya haka zasuci. Wata rana ya fahimci matarsa na da ciki. Wannan labari ya cika shi da farin ciki. Ya yi alwashin iri-iri akan dan da za a haifa. Duk kasalancinsa a ibada, wannan karon ya dage da tashin dare, salloli akan lokaci, addu’ar Allah ya bashi ɗa wanda zai haskaka a dangi da duniya. Matarsa ta fahimci wannan nacinsa ba don yana da ilimi ba, sai don zuciya. Ta yi amfani da iliminta da salon kissa, inda ta dinga koya masa yadda zai bautawa Allah tare da bashi shawarar ya shiga makarantar yaƙi da jahilci. Cikin ikon Allah, ashe shi ma mutum ne na musamman — kwakwalwarsa tamkar ta computer. Duk kuwa da ya manyanta, yanzu kam yana iya karatu da rubutu, sannan bangaren Arabic ya kan iya hada baki da biya wasu surori. Matarsa ta kan taimaka masa wajen addu’ar cikar burinsa. A ƙarshe Allah ya sauketa lafiya, sai dai mace ta haifa. Wannan ya sa ta ji burin mijinta bai cika ba. Amma ga mamakinta sai taga farin ciki yake sosai. Ya zauna kusa da ita yana dubanta da kallon tsanaki. “Baiwar Allah, me ke faruwa ne?” Ta danyi murmushi. “Naso na cika maka burinka wajen haihuwar namiji, sai gashi na haifa maka mace. Naga kuma baka damu ba, farin ciki kawai kakeyi.” Ya ce: “Hakika ina da burin samun ɗa namiji, amma nasani duk abinda namiji zai iya yi, mace ma zata iya. Kalli fa yarinyata — ban taɓa ganin jaririya mai kyawunta ba. Jinake ajikina, itace komai nawa. Jinake kowa zai yi alfahari da ita. Wannan ita ce tamkar da goma. Na shayin mafarkin wata yarinya mai kama da yar Larabawa tana zaune cikin dubban jama’a, kowa na tafa mata yana yi mata kirari. Kina haihuwar mace, na tabbatar wannan ta cikin mafarkin itace.” Kawai sai jaririya ta fara murmushi kamar ta ji me ake cewa. “Kingani tana murmushi. Kalli ruwan kyawu. Na sani wannan ba zata yi irin yacca nayi ba — zaki bata tarbiya irin taki, ko?” Ta ce: “Mijina, da izinin Allah wannan yarinya kowa zai yi alfahari da ita. Rayuwarta zata haskaka, ko da kuwa bayan raina ne. Insha Allah baza ta taɓe ba.” Ya ce: “To yanzu gaya min, wata yo?” Ta kalli jaririyar. “Bakinta irin nawa, idanunta mankya-mankya kamar naka, farace tas kamar kai, halayenta iri—” Ya ce da sauri: “Irin taki.” Suka sa dariya gaba ɗaya. Daga nan ya raɗa mata suna Nana Aisha, amma za,a dinga kiranta Ikhalas. Tunda aka haifeta suke samun albarka. Wasu ma saboda kyawunta suke kawo musu kyauta. A takaice sai da aka yanka raguna uku. Ikhalas tana shekara biyu da rabi aka saka ta makaranta. Idan aka tashi, ana yi mata lesson na musamman. Makaranta ce mai tsada, makocinsu ne ya dauki nauyin ta. Duk wani buri Ibrahim ya dora akan ta. Tana ƙarama iyayenta suka tabbatar da addu’arsu ta karbu. Tana da kokari, nutsuwa, turanci a bakinta tamkar a England aka haifeta. Ta zama abar alfahari a makarantar Abul Anwar Computable School. Yanayinta ya saje da yaran masu kudi saboda makocinsu duk abinda ya siya ma ‘ya’yansa sai ya siya mata. Ta gama primary tana shekara takwas, yar karama ce amma magana bata dame ta, ba ta da surutun yara. Ga takura da Ibrahim ya yi mata da karatu — baya taba barinta ta huta. Kwakwalwarta ta gama horuwa, mamanta har ta kan tausaya mata. Suna shirin shiga secondary school sai Allah yayi wa makocinsu rasuwa. Ibrahim yayi kuka kamar zai mutu. Wannan ne yasa Ikhalas ta koma makarantar gwamnati. A wannan lokacin suka hadu da Rahama suka shaku. Ita ce kadai da Ibrahim ya amince da alakarta da Ikhalas — amma bai sani ba Rahama ce ke kokarin rusa masa burinsa, ta hanyar karfafa Ikhalas akan wanda basu san waye ba — wato Zaruk. Zaruk ne Ikhalas ke mutuwar kauna tamkar ranta. Har yanzu ta kasa bayyana wa iyayenta abin da ya faru da wayarta. Tunda ya kyalla ido kan hotunanta, bai da tunanin da ya wuce ta. Ya shiga laluben lambobin wayarsa, har ya hango My Number a contact dinta. Ya mike a dokance, ya shiga kiran ta. Suna zaune ita da Rahama cike da alhini, sai karamar handset dinta ta soma ringing. Ta duba fuskar wayar, taga lambarta. Ta dubi Rahama cike da mugun farin ciki, rudewar farin ciki ya hana ta furta sunan Rahman. Muryarta na rawa har da kwalla: “Kingani? Ana kirana da layina… Allah na gode maka.” Rahama ta ce: “Bangane ba, kamar yaya?” “A layina ake kirana.” “To kiyi sauri ki amsa.” Ikhalas ta dauki wayar, ta kara kunne. “Hi mai kyau, shin baki damu da wayarki bane? Koda bashi da tsada, abubuwan dake ciki zasu zama masu tsada — musamman hotunan tauraruwar ilimi kamar ki.” Ta dubi Rahama, amma ta kasa cewa komai. Rahama ta karbi wayar. “Kina jina ko? Idan kina bukatar wayarki, gobe da misalin karfe goma na safe mu hadu a Tahir Hotel sai ki karba.” Idanun Rahman suka fito — hakan yasa Ikhalas ta tsorata. Ta girgiza kai alamar baza ta je ba. “Kayi hakuri, ba’a barina fita ko ina.” Ta cire wayar a kunne tana tambayar Rahama: “Ina ne Tahir Hotel?” Kalmar hotel ta zame mata kamar harshen wuta a kunne. Zuciyarta na harbawa. Rahama ta lallashe ta, amma muryar mutumin daga can ta kara tsananta mata tsoro: “Zan maishe ki mujiyar jama’a. Zan karya miki mutuncinki idan kika ki zuwa — musamman idan na yi amfani da kyawawan hotunanki dake cikin wayar.” Hawaye suka zubo mata. Ta kasa jurewa. “To… zan zo. Amma me yasa sai a can zan karɓa?” Wayar ta katse. Ta rage numfashi tana kallon Rahama, idonta cike da tambayoyi da tsoro. Rahama ta ce: “Ki kwantar da hankalinki, Ikhalas. Allah ba zai tozarta ki ba. Amma ki ji tsoron mutum idan zuciyarsa ta mutu — irin wannan zai iya yin duk abin da zai bata miki suna. Na san kina jin haushin jin cewa ki tafi hotel, amma ki fahimci ba duk wanda yake cikin hotel yake aikata mugunta ba. Amma a gaskiya, wannan zamanin mutane sun fi daukar hotel a matsayin ramin zunubi. Idan aka ji an ganki a can, koda babu komai, za a yi miki hukunci ba tare da sauraronki ba. Sau nawa kika ji labarin an dauki hoton mace tsirara? Sau nawa kika ga an baza video ana yi mata dariya? Wani lokacin ma hakan don kazantar da suna ake yi, ba don wani abu ba. Idan hakan ya same ki babu mafita — kimarki zata zube gaba daya. Iyaye ma zasu iya cewa, ‘Ashe wannan ce asalin halinta.’ Wannan shi ne abin da zuciyata ke tsoron ki fada ciki. Ba wai lalata jiki kawai ake yi ba — suna ma ana lalawa har ya kasa gyaruwa.” [18/08, 4:20 pm] Bilkisu H MUHD: _*GABA DA SO*_              _BY_ *BILKISU H MUHD* Phone 08031307884 Page 9 *MARUBUCIYAR* ILLAR SABO RASHIN RABO YA YI SAKE ZAFIN HAWAYE NA BAKIN KAZAFI WAYA FI SONTA GORO DA SANKARA JINI BIYU DACEWA KAUNA CE BAYAN KUSKURE MATSALAR KAUNA TARAIRAYA DAKE NA DACE AKWAI BANBANCI BAKIN KAZAFI MULKIN MALLAKA IZZATU BAYAN KUSKURE KA AURE NI KYAUTAR ZUCIYA *sannan yanzu ta zauna ta kure basirarta gun rubuta muku littafin da bata taba fitar dashi a takadda ba littafine Wanda a online tafara rubutashi , littafin yazo da sabon salo tare da sarkakiya hadi da soyayya mai taba zuciya kowa yaji sunan littafin GABA  DA SO  zai sojin menene agaba da so daman da akwai abinda yake GABA DA SO,to karanta wannan littafin dan sanin menene ke GABA DA SO.* makaranta kundai san yadda alkalaminta🖊️yake.  Wanda ya santa ya santa Wanda bai santaba yakamata ya gwada karanta books dinta lalle bazata baku kunya ba. Sannan zaku samu dukkanin littattafai na ta hanyar 👇🏻👇🏻👇🏻 Wattpad:👇🏻 @bilkishmuhd Arewa Book:👇🏻 bilkisuhmuhd WHATSAPP GROUP NA BILKISU H. MUHD👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/Fp8jRB4MGGqB1I6J9gc0NE?mode=ac_t WHATSAPP CHANNEL NA BILKISU H. MUHD👇🏻 https://whatsapp.com/channel/0029VarKaWtBfxnxJ2STpI1o FACEBOOK GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻 https://www.facebook.com/groups/1845344956261189/?ref=share&mibextid=NSMWBT BUSINESS GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/IOFJMOHiTTMJ9cNLRroppc?mode=ac_t ------------------💥 Ikhlass na fitowa, amma ƙafafunta tamkar an ɗaura musu sarƙa. Zuciyarta tana bugawa kamar ana dukan ganga a cikin ƙirjinta. Hawaye sun gaji da saukowa, amma ba su gajiya da yin zafi a idanuwanta. Kunnenta yana maimaita kalaman da ta ji daga mutumin nan, kalaman da idan suka tabbata — Abu zai ɗaure rai, fushin da ba zai gushe ba har abada ba. Wannan abin ba ƙaramin kunya zai bata a idon mutane ba. Kafin ta gama tunanin yadda zata iya tserewa daga wannan jarrabawar, saƙon nan ya shigo. Hannunta na rawa, ta duba — address. Saƙon ya ɗauke da umarni mai sanyi amma mai tsini: "nan da awa ɗaya kacal. Idan baki zo ba, ki kashe waya ki saurari abin da zai biyo baya." Wata gagarumar damuwa ta kulle mata ƙwaƙwalwa. Ta san yau Asabar ce, babu makaranta. Wace ƙarya zata yi? Ta shiga kai-koma a ɗaki, zuciyarta ta rikice kamar wutar lantarki da aka saki a tsakar ruwa. Daga can sitting room, ta ji muryar Abu da Ammi na hira. Hanyar tsira ta fado mata. Ta yi wanka, ta fito, ta shafa mai kaɗan, babu hoda. Ta ɗauko uniform ɗinta, wanda tun jiya ta goge, ta saka. Gabanta na harbawa, ta fito. --- "Lu’ulu’u, yau Asabar ne fa," Abu ya ce da mamaki. "Nasani, Abu… amma an ce muzo saboda mun kusa fara jarrabawa," ta amsa tana boye rawar murya. Abu ya ciro kuɗi daga aljihunsa, ya miƙa mata. Ammi ta haɗe fuska. "Me ya sa baki sanar da ni ba?" "Na manta ne…" ta ce da sanyin murya. "A irin wannan lokaci kuma? makaranta?" Ammi ta sake tambaya, idonta na neman zurfafawa cikin sirrinta. Kafafunta suka yi sanyi, ta san idan Ammi ta matsa tambaya, zata iya gano gaskiya. Ta yi shiru kawai. "Allah ya bada sa’a," Ammi ta ce, bata ji daɗi ba. Ta fice da sauri kamar wadda mai shirin tashi sama. --- Adai-daita ya tsaya gabanta, fiye da biyar in suka tambaye ta inda za ta,sai ta kasa furtawa. Sai wani sabon saƙo ya shigo: "Lokacinki na ƙarewa." Nan ta tilasta kanta ta faɗin address. Tunda ta shiga napep, hawaye suka fara gudu. Direban yana kallonta ta gefe, kamar yana tambayar kansa, "Ina yarinyar nan ke nufa haka?" "Mun iso. Ki bani hakkina kafin wani ya zo ya ce na ɗauke masa ‘ya ," direban ya faɗa yana murmushin ɓoyayyen damuwa. Zuciyarta ta ce kawai: Allahumma ajirni fi musibati… --- Ta tsaya a bakin hotel, jikinta na rawa. Idanunta sun cika da hawaye, zuciya na bugun bala’i. Da sassarfa ta shiga ciki, ta yi karo da wani mutum tsaye gabanta. "Kece mai amsar waya?" Ta ɗaga kai, amma ta kasa magana. "Kije daki mai lamba goma sha ɗaya. Oga na can yana jiranki." Numfashinta ya kulle, jikinta na rawa. "Kiyi sauri kafin ki jawo wa kanki matsala," ya ƙara faɗa yana nuna hanya. Ta tafi a hankali, tana waiwaye. Ta isa kofar ɗakin 11, ta rintse idanu, hannunta na rawa. --- Sai kawai aka murɗa key, ƙofar ta buɗe. Wani kallo mai nauyi ya sauka kanta. "Shigo," muryarsa ta fito mai sanyi amma mai ɗauke da guba. Ya zauna yana kallonta, yana jin duk jikinsa na tsigar sha’awa da mamaki. Singlet ce a jikinsa da gajeren wando, Ta kame idonta, ta shiga maimaita addu’a a ranta. "Kinga, shige ciki ki bani wayata, sai ki karɓi taki," ya faɗa. Ta shige sum-sum. Ya nuna mata kujerar zama, amma ta ki. Sai kawai ya daka mata tsawa, ta tsinci kanta da zama. Gumi ya gangaro daga gashinta zuwa fuskarta. "Naga kina gumi kamar wadda ta gudu daga fanfalaki. Sha ruwa." Ta girgiza kai. Sai kawai ya ɗaga muryarsa, ta tsorata ta da sauri ta karɓi robar ruwan. Bai tsaya nan ba ya ɗauki lemon, ya buɗe ya mika mata. Cikin firgici ta karɓa, ta sha har sai da kwalin ya ƙare. Yana ta kallonta, idanunsa sun sauya launi. Ya fara tambayarta: "Sunan ki?" "Ikhlas." "Wace makaranta kike zuwa? Ajin ki nawa?" Tana amsa masa a fusge, zuciyarta na juyawa. Murmushin mugunta ya bayyana a fuskarsa. A hankali ya cire hijab da dankwali, ya fara laluben rigarta. Amma a tsakar wannan sha’awa, wata zuciya ta shige masa — ina ma ace ita matata ce… Ya tsaya cak, zuciyarsa na bugawa. Amma kalaman kakarsa suka katse masa nufin da zai aikata. Wani kira ya shigo wayarsa Grany yagani a rubuce. "Oh, kakahhh… me zan yi miki kuma?" Wayar ta katse ba tare da ya daga ba. Sai can ta sake ruri, afusace ya ratsa ya kara a kunne. "Ina bin sahunka ban ganka ba, na tsorata da abin da ka fada dazu. Na kasa samun nutsuwa saboda na san halinka. To ka ji, wallahi ka keta mutuncin yarinyar nan, ba zan taba yafe maka ba — kai da iyayen da suka yi sanadin zuwanka duniya. Sai la’anar Allah ta tabbata a gare ka, azzalumi! Daga kanta zaka ga aya. Kuma ma, ko yatsanta ka taba, ina rokon Ubangiji ya yi gaggawar saka mata ta inda zaka kasa fita har abada. Sai Allah ya jarrabe ka akan wannan!” "Ya isa haka!!" "Haba, irin wannan jafai haka, kamar ba jinin kiba?" Ta ja tsaki, ta kashe wayar. Duk tantirancinsa, yana tsoron bakin kakarsa. Tun kafin ya taso, ya riga ya canfata da cewa tana da kambun baka — duk ikirarin da ta yi, yawanci yana tabbata. Muguwa ce shiyasa kullum zaka ganta a kan buzu, gaba daya bata da lokacin bacci, hannunta kullum rike da carbi. Ya koma falon cikin dakin yana ta zarya. Kalaman kaka ne suka dinga yi masa yawo a kwakwalwa, yayin da idanunsa ke haska masa halittar Ikhlas. Ya sauke ajiyar zuciya. Yadda yake jin ta a ransa ya kasa tantancewa — tsananin sha’awa ne, ko kuma takaicin sumbatun kaka? Ya fara sumbatu kamar wani tababbe, yana maimaita kalmomi da ba shi da tabbacin ma’anarsu, kamar zuciyarsa na rikici tsakanin son wani abu da tsoron la’anar da aka jefa masa. A’a, ban taɓa jin mace ta shiga zuciyata ta ratsa kowace jijiyata irin haka ba. Na gode wa Allah da ban keta mata haddi ba… amma inajin kamar an ajiye ni a hannunta ta hanyar da ba zan iya guduwa ba. Daga can ƙasan zuciyata, akwai wani ƙauna mai zurfi da dole sai na kare rayuwata da ita dole sai ita ce matata. Sai dai gaba ɗaya na tsani kaina. Me yasa na bi wannan hanyar? Da wane ido zan sake dubanta? Yaya zan haɗa ido da ita? Zuciyata na ƙuna kamar wuta, zuciyata na harbawa da ciwo, amma har yanzu ina jin wani irin ƙarfin sha’awar ta a cikina. Wannan ji mai haɗa tsoro da farin ciki ya mamaye ni, har numfashina ya fara nauyi. --- A gefe guda, Ikhlass ta motsa a hankali. Idanunta suka buɗe cikin kasala, amma ciwon kai ya daki ƙwaƙwalwarta kamar guduma. Tana yunƙurin tashi, sai ta ga hijabinta da dankwalinta a gefe, uniform ɗinta a cunkushe. Wani irin ƙara mai haɗe da kuka ya kuɓce mata. Da gudu ta fice, ba tare da ta ɗauki hijabi ko takalmi ba. Tafiyarta cike take da girgiza ƙasa da bugun ƙafa, kowa na kallonta da mamaki. Ita wacce kullum ake gani cikin mutunci da kunya, yau tana gudu a haka. Shi kuma daga nesa ya hange ta. Zuciyarsa ta doki ƙirji da ƙarfin da bai taɓa ji ba. Ya kira mai tsaron ƙofar da gaggawa, hannunsa na rawa. “Dakatar da ita… don Allah, ka dakatar da wannan yarinyar!” Kafin ya fito, mai gadin ya riga ya nufo shi. “Tana ina?!” ya tambaya da muryar da ke girgiza zuciya. “Sorry oga… mota ce ta bugeta,” mai gadin ya faɗa da lalatacciyar Hausan sa, ya wuce. “What…!” Kalmomin suka makale a makogwaro. Idonsa ya fara juyawa da tsoro, zuciyarsa na bugawa da ƙarfi. Ya gangaro daga bene da gudu, kowa na kallonsa amma ba wanda ya iya tambayarsa. A waje, ya tarar da taron mutane. Jini yana kwance a titi. Zuciyarsa ta yi nauyi kamar an ɗora dutse a kai. “Ina yarinyar da ta yi hatsari?” ya tare wani saurayi. “‘Yan sanda sun ɗauke ta. Na tabbata asibiti za su kai ta Allah dai yasa bata mutuba ,dan wannan sai wani ikon Allah,” saurayin ya ce, ya wuce. Wannan shine last free page mai son cigaba ya tuntuɓe ni a wannan numbar -08031307884 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels