An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@Sanazdeeyah_ #FITATTUHUƊU2025 _*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*_ _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_ _Dukkan godiya da yabo su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa mai komai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta annabi Muhammad(SAW)._ _Wannan littafin mallakata ne, ban yarda wani ko wata ya yi amfani da shi ta wata siga ba, yin haka saɓawa doka ne kuma ba zan lamunta ba, a kiyaye!_ 🆓Page 1 *_SHIMFIƊA_* Tun daga ƙofar get na fara jiyo guɗa da shewa ta mata, na kai dubana ga ƙofar da mata ke ta tururuwar shigowa cikin gidanmu wasu daga cikin su suna ɗauke da akwatunan lefe. Ina kallo ana nuno inda nake da Yazid na tabbatar gulmata suke, ina kallo suka wuce da akwatuna set biyu ma'ana guda sha biyu cur. Murmushin yaƙe kawai na yi sannan na kai duba na ga Yazid dake zaune gabana, kan sa na gani a ƙasa, tuni ya lula wata duniyar tunani. "Yazid!" Na kira sunan sa a hankali, ya ɗago yana kallo na, "Tunanin me kake?" "Wannan lefen Saddiqa ne?" Murmushi na sake faɗaɗawa tare da cewa "E nata ne, ni sam ba a sanar dani cewa yau za a kawo lefen ba, na dai san ance mini cikin satin nan ne." "Kiyi haƙuri Sadiya, sai na ga sam ban yi ƙoƙari ba." "Ni kuma na ga ƙoƙarin ka Yazid, ka daina damuwa da abinda wani ya kawo, ka yi alfahari da naka, akwati biyar da ka kawo min duk wanda bai gode maka ba, ba zai zage ka ba, sannan ni ina alfahari da hakan. Yazid yatsun hannu ma ba ɗaya bane, samunka dana wani ba zai taɓa zama ɗaya ba." "Nagode 'yar aljanna" Ya faɗa yana murmushi. "Haka nake son ganin fuskar ka a ko da yaushe." Hirar su suka cigaba da kuma tsara yadda abubuwan bikinsu zai kasance. Kafin daga bisani ya yi mata sallama ya hau machine ɗin sa ya bar gidan. Tana shiga tana ana ɗaga kayan lefe ana ta yabawa, ta gaida su tana ƙoƙarin wucewa Umma Habiba ta kirata, dawowa tayi tare da tsayawa gabanta, "Baki ga lefen Saddiqa ba" "Na gani Umma, so nake ku gama gani sai inzo in kalla, amma yanzu ga manya ai bana zauna ba." "Yazid ɗin ya tafi ne?" Kallon mamaki ta yi mata sannan ta ce "E, ya tafi!" "To shi kenan, za ki iya tafiya." Tana zama akan gado ta ji hawaye masu zafi sun sauka a kuncinta. _In dai Yazid za ki aura wallahi ba zan kai wannan kayan ɗakin gidan matsiyaci ba, gara na ajiye wa Auta._ Hannu ta saka ta goge hawayen da suke sunturi saman fuskarta, kafin ta miƙe ta cire gyalenta ta ninke ta saka a drawer. Tana juyowa Umma Habiba ta faɗo ɗakin. "Ko aiki kike?" "A'a Umma, babu abinda nake yi." "Yawwa to zauna magana za mu yi." Tana zama Umma Habiba ta riƙo hannayenta tare da faɗin, "Sadiya! Kar ki yarda ki ɓata ƙuruciyarki, a yanzu ba a auren soyayya auren mafita ake yi" "Auren mafita kuma Umma?" "E, ina nufin ko wace mace tana kallon inda za taje ta huta ne, har yaran talakawa bare ke da kike da gata." Shiru Sadiya ta yi, dan ta fara fahimtar inda maganar ta dosa. "Sadiya ki farka daga nannauyan baccin da kike yi, ki amince da zaɓin mahaifiyarki" "Umma gaskiya ni bana son Alhaji Sani, kuma hankali na bai kwanta da shi ba, sannan bana son shiga ramin da ba nice na haƙa ba" "Dalla shashasha, matar sa ɗaya ce, sai kuma yara biyu, ke kina tunanin idan Yazid ɗin ne ya samu dama ba zai ƙara aure ba, akwai wanda ya fi talaka rashin mutunci a lokacin da Allah ya ara masa lokaci" "Umma ni dai Yazid nake so, kuma shi ne zaɓina, ko Abba kafin ya rasu ya sanarwa da Mameey cewa ta aura mana wanda muke so matuƙar baya da aibu." "To aibun Yazid talauci, ba lallai ya iya riƙe ki ba." Murmushi ta sake yi tare sa janye hannayenta. "Ni dai Yazid ne zaɓina, kuma baya zaman banza yana da abin yi" Tana faɗa ta sauke kai ƙasa, Mameey ta shigo ɗakin hakan ya saka ta sake sauke kai ƙasa. "Habiba! Ta ga lefen da aka kawo wa Yayarta?" "E ta gani, amma hakan bai saka ta saduda ba" Kallon Sadiya tayi, sai kuma ta juya ta fice. Umma Habiba ta kalli Sadiya ta ce "Ki dai zauna kiyi tunani" Ita dai Sadiya bata ce komai ba har Umma ta fita. Ranar a ɗaki ta yini har zuwa bayan magriba lokacin Saddiqa da Surayya suka dawo gidan. "Ya naga kin yi lamo kamar mara lafiya" Tashi ta yi ta zauna lokacin kuma Surayya ta fara ƙoƙarin cire kaya ita kuma Saddiqa ta zauna gefenta. "Mene ya faru?" "Akan lefen ki da aka kawo ne" "Bai masu ba?" Kai Sadiya ta girgiza sannan ta ce "Kawo lefen ki da aka yi ne ya jawo aka cigaba da rura wutar tsanar Yazid a gidan nan" "Wai mene aibun Yazid?" "Babu kawai dan dai ba shi ne zaɓin Mameey ba" "Ki kwantar da hankalinki Sadiya, tunda dai kina son shi shima yana sonki insha Allah komai zai wuce da zarar an gama hidimar biki" "Ni ma fa har ga Allah bana goyon bayan ta auri Yazid" Cewar Surayya Kallon Surayya ta yi kafin ta yi magana Saddiqa ta ce "Sannu mara kunya, waye ya saka bakin ki a maganar mu?" "Allah ya baku haƙuri" Ta faɗa tana shiga toilet, ajiyar Zuciya Sadiya ta sauke tare da dafe fuska. Mameey kuwa sai da ta bambanta auren Sadiya da Saddiqa, domin sai da ta ƙara sati ɗaya a bikin Saddiqa saboda kawai Yazid ya ce baya da kuɗin da zai yi kamu da dinner sai dai walima, ƙarshe ma sai kiranshi tayi ta ce ba ta son walimar za a ɗaura aure a yi yinin biki a kai amarya. Hakan kuwa aka yi dan da ƙyar ma ta yarda ta bayar da kayan ɗakin aka kai Sadiya dasu, dan cewa tayi ba zata bari akai kayan ɗaki masu tsada gidan da bai dace ba, kuma ahalin da ba su san darajar kaya masu tsada ba. A haka dai 'yan uwa suka saka baki, haka Saddiqa ma tayi kuka ta kuma ce muddin ba a kaiwa Sadiya kayan ta ba, to itama bata so. Sati ɗaya da kai Sadiya aka fara bikin Saddiqa wanda biki ne kamar shi ne auren fari a gida, party ma kala biyar ne, tun daga ranar talata har zuwa asabar, taso zuwa amma Yazid ya hana ya ce ta bari ranar yinin biki sai ta je, abinda ya guda kuwa sai da hakan ta faru domin ranar yinin da taje kallon wulaƙanci suka yi mata suna ganin sun raina leshin dake jikinta, duk da a cikin leshin shi ne mai tsada a cikin kayan lefenta. A gidan Saddiqa ce kawai ke goyon bayan auren Sadiya da Yazid. ************** Ruwan da ta ji yana zuba a jikinta ya saka ta yi firgigit ta buɗe ido tare da miƙewa zaune, saboda yadda sanyin ruwan ya ratsata. Najma da Ihsan suka farka, tuni Ihsan ta fara kuka dan ita ce ƙarama, sanyin ruwa ya farkar da ita daga baccin da ba su daɗe da farawa ba. Cikin hanzari suka sauka daga katifar, Sadiya ta ɗauke katifar ta jingine a gefen da ruwa baya zuba, sannan ta ɗauki bargonsu ta zura a leda ta ƙulle ta fita da sauri, a lokacin ta ga Yazid ya hasko fitila ya fito daga na shi ɗakin, wanda ta tabbatar shima ruwan ne ya farkar da shi dan gidan babu inda baya zuba, shiyasa duk albarkar ruwan sama amma su gudun shi suke. Ledar ta kai zaure dan nan ne mafakar su idan ana ruwan dare, ta ƙarasa can gefen da babu feshin ruwan kasancewar zauren yana da ɗan girma, dan murhunanta ma da take girki anan suke tun lokacin da damuna ta shigo. Yazid ya ƙaraso zauren da Ihsan a kafaɗarsa hannunsa na riƙe da Najma. "Kin ga bari na ɗauko kayan namu kar su jiƙe sai a canja masu saboda kar danshi ya masu illa." Kai kawai ta gyaɗa tana janyo yaran, ya dawo da sauri da bakkon kayansu, ta sumu ta shimfiɗa tabarma tana ganin yaran suna ta rawar ɗari, ta saka zannuwa akai sannan ta kwantar dasu ta ruɓanya bargo ta yafa masu har kansu, sai lokacin ta fara jin hawaye kwance saman kuncinta, ta dafa tsohon cikinta da ta ji yana motsawa. "Sadiya ki tashi ki canja kaya" Kallon shi ta yi sai kuma ta fashe da kuka a fili, da sauri ya ƙarasa gabanta ya jata jikinsa duk da a jiƙe take "Kiyi haƙuri na san bana sauke haƙƙin da Allah ya ɗora min naku." "Ka daina faɗar haka abban Najma" Ta furta tana ɗagowa. "Na san kana iya ƙoƙarinka, kuma Allah yana sane damu." Tana gama faɗa ta miƙe ta buɗe bakko ta ɗauki kaya ta canja sannan ta kalleshi. "Ka samu ka kwanta, ka ga da wuri kake fita aiki." "Ba zan iya kwanciya na yi bacci ba, ko da na kwanta ma na san ba zan iya komawa bacci ba." Ji tayi wasu hawayen sun ƙara cika kwarmin idanunta, ta koma kusa da shi ta zauna, ya janyota ya ɗora kanta bisa cinyarsa tare da faɗin ki samu kiyi bacci. Idanuwanta kawai ta rufe amma sam bata samu tayi bacci ba, sai ma rawar ɗari da ta fara kasancewar tana da pneumonia, da sauri ya cire rigar sanyin dake jikinsa ya yafa mata, ta haɗe ƙafafunta sosai, ranar ba ƙaramin ruwa aka tafka ba, sai gab da asuba ya tsagaita. Da fitila yake haskawa ya ga tsakar gidan nasu ya cika maƙil da ruwa, banɗaki kuwa ya rufta, dama na ƙasa ne. "Ya Allah mun gode maka" Ya furta sannan ya ɗauki buta ya yi alwallah, yana idarwa ya ga Sadiya ta shigo. "Abban Najma banɗakin mu ya rufta" "Wallahi nima yanzu na gani" Ajiyar zuciya kawai ta sauke babu wanda ya ƙara magana a cikinsu. Koda ta yi sallah miƙewa ta yi ta shiga ɗakin, ta fara ta ɗakin kwanansu, nan ta fara yiwa aiki, tana ta tsane ruwa bayan ta gama fito da kayan ɗakin, har gari ya fara haske sannan ta gama ta koma ɗayan ɗakin da kujerunta ke ciki nan ma ta hau aiki sai dai har ta gama Yazid bai dawo ba lokacin kuma yara sun tashi daga bacci. " 'Yan matana an tashi?" Ta faɗa lokacin da Ihsan ta rungumeta itama Najma ta ƙaraso gabanta "Mommy sanyi muke ji" "Akwai sanyi fa, amma karku damu yanzu da Daddy yazo mun yi breakfast sai muje gidan Mameey kuna son zuwa?" Kai suka gyaɗa suna dariya, inda ya ɗan bushe a taɓen gidan nan ta shimfiɗa masu tabarma, sannan taje zaure ta ɗebe shimfiɗar ta dawo da ita ciki, ta ajiye sannan ta sake komawa ta hura wuta a murhu ta ɗora ruwan zafi yaran ta ce su dawo zauren su sha ɗumin wuta. "Najma karku yi wasan wuta kin ji ko?" "To Mommy" "Yawwa Najmata bari na ƙarasa aiki kafin Daddy ya dawo ya kawo abin kari ko?" "Mommy yau ba zan je school ba?" "E yau mun makara sai dai gobe" Bata ce komai ba, ita kuma Sadiya ta shiga ciki. Ƙarfe takwas da kusan rabi taji yaran suna "Oyoyo Daddy" Ta kai dubanta ga zauren sannan ta ajiye tsintsiyar hannunta ta ƙarasa. "Sannu da zuwa Abban Najma" Ta faɗa tana karɓar ledar hannunsa. "Kamar na sani na sayo bread da lipton da sugar, sai a haɗa saboda yaran, akwai pasta da ɗan kayan miya sai ayi da rana ko?" Masha Allah, kace yau mun dace" "Ai yau ina fita naga ana sauke kaya, shi ne nima na shiga cikinsu, to bayan mun gama sai aka bamu dubu biyu kawai na yi cefane da ita" "Allah sarki Yazid, Allah ya maka buɗi na alkhairi" "Amin mar'atussaliha" Murmushi tayi sannan ta ce "Na ga kayi ƙura, bari na sauke ruwan idan na ɗebi na tea sauran sai kayi wanka" "Kin manta banɗaki ya rufta? Yanzu fa dole sai an gyara" Ya furta yana shigewa ciki da damuwa. Kallon shi tayi itama jikinta gabaɗaya ya yi sanyi. Har za ta bishi sai kuma ta kalli yaran ta ga duk suna tare da yunwa, tunda jiya ba wani ƙoshin kirki suka yi ba. Da sauri ta koma ciki bata ga Yazid ba, ta tabbatar ya shiga ɗaki ne, ta ɗauki flask da cups ta koma zauren, rufe gidan ta yi ta saka sakata sannan ta haɗawa yaran shayi ta gutsura masu bread ɗin, akan tabarmar ta saka suka zauna ta surka masu sannan ta miƙe ta shiga gidan. Ɗakinta ta shiga ta ganshi zaune ya haɗa kai da gwiwa "Habibi!" Ɗago kai ya yi yana kallonta, ta ƙarasa gabansa tare da miƙa masa hannu, hannun ya riƙe sannan a hankali ya miƙe tsaye, rungumarshi kawai ya ji tayi dan bai yi expecting hakan ba "Haba Babyna idan kana damuwa ni ina kake so na kai tawa rayuwar, ka san fa kaine farin cikina" Ɗago ta ya yi yana kallonta, ta ɗan sakar masa murmushi "Jiya kuka kika yi sosai, yau kuma kina murmushi, Sadiya na san ni ɗin ba miji nagari bane a garek...." Da sauri ta saka hannu ta rufe masa baki. "Dan Allah ka daina faɗar haka, kar ka saka ƙwarin gwiwata ya sace, Yazid kai miji nagari ne, wanda ko wace mace ke fatan samu." "Sadiya! Ki duba daga gidan dana ɗauko ki, amma kalli gidan da muke rayuwa a yanzu, ba kece macen daya dace na aura ba, saboda cimar da nake baki a gidanku a guba suke kallonta" "Yazid meyasa kake faɗar haka? Lokacin da muka yi aure babu abinda na nema na rasa a gidanka, a yanzu ma da karayar arziƙi ta same ka ba zan zama mai butulci a gareka ba." "Ko lokacin dana aure ki ai ni mai ƙaramin ƙarfi ne, abinda kike so kin samu ne a lokacin muna daga ni sai ke, amma tunda aka haifi Najma buƙatu suka ƙaru sai abubuwa suka taɓarɓare a ciki kuwa har da rasa aiki na" "Kar ka yi yaƙi da ƙaddara, ka bi komai a sannu Allah zai warware mana, kuma yara da kake magana rahama ne a gare mu, wasu da kuɗinsu neman haihuwa suke amma ba su samu ba, mu kuma ka ga ko a haka alhamdulillah mun samu albarkar aure, ga Najma ga Ihsan kuma ga unborn a cikina." "Hannu ya saka ya shafa cikin nata, sannan ya ce "Kullum na kalli cikin nan sai na godewa Allah da ya bani ke a matsayin mata, yanzu fa tun cikin nan yana ƙarami kika bani shawara na sayi wannan ƙaramar tunkiyar na kai gurin Iya Mama, gashi yanzu da Iya Mama ta haɗata cikin dabbobinta har ta haifi 'yan biyu." "Ai dama shiyasa na ce ka saya tunda har aka ce tana da ciki sai ka ga an dace." "Wallahi kuwa gashi dai an dace ɗin, Iya Mama ta ce suma har sun fara tasawa." "Ma sha Allah" "Yanzu fa kuɗin rago ya kai dubu ɗari, kuma shima na dubu ɗarin ba wani bane" "Wai dagaske?" "Wallahi fa, ai ba ƙaramar dabara bace da muka sayi tunkiya kuma ta haifi mace da namiji, yanzu idan Allah ya sauke ki lafiya sai kawai na sayar da ita a sayi ragon suna, su kuma sauran sai a barsu har zuwa su girma mu gani" "Hakane, to Allah ya inganta" "Amin" "Muje mu karya, ina so muje gida da yara sai mu samu mu yi wanka acan tunda banɗakin mu ya rufta, kuma ka ga kayan nan dole sai ɗakin ya bushe kafin na mayar" "Nima zanje gidan Umma sai na yi wanka, dama ina so na miki magana, kin san dai tsohon ciki ne dake amma shi ne kika yi aikin nan, meyasa baki bari nazo na kama miki ba" "To ba gashi har na gama ba" "A'a Sadiya dan Allah ki riƙa hutawa" "Hutu ai ba na mace mai yara bane" "Ni dai na faɗa miki" "To ka fito dai mu karya, kuma ka daina zama a danshi in ba so kake sanyi ya kama min kai ba" Murmushi kawai ya yi, sannan ya ce "Kin san tsabar damuwa ban ma san nan na shigo ba" "Ka rage damuwar nan dan Allah" "Insha Allahu. Ki je ki karya ku kaɗai na sayawa" "Ai ya mana yawa, dan Allah karka ƙi karyawa" "To shi kenan muje" "Yawwa Babyna" Murmushi kawai ya yi, yana lumshe ido. Suna shiga zauren ta kalli yaran ta ce "Najma bari na gama haɗawa Daddy breakfast sai na yi muku wanka ko?" Kai Najma ta gyaɗa, ita kuma ta janyo cups ta haɗa masu, suna sha suna ɗan taɓa hira har suka gama. Yana ƙoƙarin fita ta ɗan dakatar da shi ya tsaya yana kallonta "Dama na ce kodai kujeruna za a sayar a gyara mana rufi?" "A'a Sadiya wannan karon ba zan ɗauki shawarar ki ba, haka kika sayar da gado abu bai yi ba, sannan gadonki ma...." "Ya isa dan Allah Yazid, bana son ka riƙa faɗar haka, ni da kai duk ɗaya ne meyasa kake wannan maganar, duk wani abu dana mallaka ai naka ne" "Na yarda amma kujerunki ba za a sayar ba, yanzu haka fitar da zan yi insha Allah akwai aikin da zanyi na samu kuɗi, na san Basiru zai min gyaran nan koda bashi ne insha Allah." "Bana so ka yi ta wahalar da kanka" "Abinda ya zama dole ne Sadiya" Ya saka hannu a aljihu ya fito da naira ɗari biyar ya miƙa mata, "Wannan fa?" "Ku yi kuɗin napep zuwa gida." "Kai fa? Kana da wasu a hannunka?" "Kar ki damu, ke dai ki karɓa kawai" "To mungode Allah ya ƙara maka buɗi Abban Najma" "Amin Maman Najma" Murmushi ta yi tana rufe fuska. ***** ***** Tun da Napep ya sauke su take jin gabanta yana faɗuwa ‘lahaula wala ƙuwata illa billah’ Shi ne abinda take nanatawa a ranta, mai napep ya bata canjin ɗari biyu ta juya ta shiga gidan. "Ya na ji gidan shiru" Ta faɗa lokacin da ta kutsa kai cikin parlourn. "Wa nake gani kamar Aunty Sady?" Jin haka ya saka ta kai dubanta gare shi. "Kai! Yaro yaushe ka diro garin?" "Ban daɗe ba Aunty ina ta son zuwa gidanki sai ga ki kinzo" "Faɗi gaskiya dai, borin kunya kawai kake dan ka ganni anan" Najma gaishe sa ta yi, ya janyota ita da Ihsan ɗin "Ga su duk sun yi wayo" "Aikam dai kana ubansu amma basu sanka ba, rabonka da gidana an fi shekaru biyu ka gyara hali Faruq" Kai ya sosa yana dariya. Umar Faruq ɗa ne ga ƙanen mahaifinsu, kuma mahaifiyarsa 'yar asalin maiduguri ce babanshi ya aurota zuwa kano, sai dai tun Faruq na da shekaru 4 a duniya Allah ya yiwa mahaifinsa rasuwa, bayan mahaifiyarsa ta gama takaba ta koma can maiduguri da shi sai dai yana ɗan shekara 6 a duniya ta dawo da shi Kano wurin mahaifin su Sadiya anan ya girma yanzu haka shekarunsa 22 a duniya, Saddiqa ta ba shi shekaru 7 a haihuwa, Sadiya ta ba shi 4 yayinda suke sa'anni da Auta. "Ina Mameey da Auta ne na ji gidan shiru?" "Mameey tana ɗaki ta je ɗauko min saƙo zan kai wa Aunty Saddiqa, ita kuma Surayya tana school bata dawo ba" "Nima ka san ina son zuwa gidan Saddiqa" "To kizo muje tare" "Gaskiya ba zamu tafi tare ba dan sai na gama hutawa a gida sannan zan je" Ta ƙarasa maganar tana miƙewa "Bari na je gurin Mameey" "To sai kin dawo." Tana tura ƙofar Mameey ta ɗago ta kalleta, "Wa nake gani a gidan nan kamar Sadiya." "Mameey ni ce, ina kwana" "Lafiya lau, mene ya kawo ki da safiya haka?" "Yanzu 11 ta wuce fa" "Ba time na tambaya ba, abinda ya kawo ki na tambaya." Ji ta yi jikinta ya yi sanyi. "Na zo ne kawai na yini anan." "To ki koma gidan ki" Furucin ya daketa, ta kalli Mameey dan ta tabbatar da maganar da take faɗa. "Ki koma gidanki na ce kafin ranki ya ɓaci" "Mameey naz..." "Ki rufa min baki Sadiya, ba zan taɓa lamuntar zuwanki gidan nan ba muddin ba da takardar saki na ganki ba" Zaro idanuwa ta yi tana kallon mahaifiyarta. "Dube ki da Allah, shekaru ashirin da biyar ne ko shidda kike dasu amma 'ya'ya biyu har da cikin na uku, kin zama kamar tsohuwa, wani ya kalle ki zai yi tunanin kin haura arba'in a duniya" Ɗan lumshe ido ta yi tana jin raɗaɗin furucin, lokacin kuma ta tsinkayi muryar Mameey tana faɗin "Sai a rantse kin girmi Saddiqa, ga ta nan har yanzu kamar budurwa, amma ke kin liƙewa talaka kuma kince kina ta haihuwa saboda rashin sanin ciwon kai" Kallon Mameey ta yi lokacin wasu siraran hawaye suka fito daga fuskarta zuwa kuncinta. "Kiyi haƙuri Mameey" "Haƙuri ɗaya zan yi kije ki karɓo takardar saki a gurin wancan matsayacin, ni kuma zan riƙe ki domin ni dolenki ce, amma muddin kina tare da Yazid to wallahi mun ta samun matsala dake, haba Sadiya so hauka ne? Kin sayar da gado kin bashi ya lalata kuɗin, sannan kika matsa min kan lallai sai na baki gadonki, na baki nan ma kika ba shi kuɗin suka nutse" "Amma Mameey kowa ya san duk manoman da sukayi noman shinkafa a shekarar da ta wuce babu wanda bai yi asararta ba, ruwa ne ya shanyeta, Mameey na faɗa miki ya fi a ƙirga." "Dalla rufa min baki, me kika ce min lokacin da za ki karɓa? Kin ce min sana'a za kiyi ashe ƙarya kike mijinki ne ya zugo ki kika karɓa kika danƙa masa" "Wallahi Mameey ba shi ya ce na karɓa ba, ra'ayi na ne kawai" "Wallahi idan na sake faɗa kika faɗa sai na tsinka miki mari." Kan ta kawai ta sauke ƙasa hawaye na ta sintiri a fuskarta. "Kafin na fito parlour ki tabbatar kin ɗebi yaranki kin bar min gida, in ba haka ba wallahi ranki sai ya ɓaci." Juyawa kawai ta yi kafin ta fita ta ji Mameey na faɗin, "Idan kina son zuwa gidan nan to ki kashe aurenki dan bana ƙaunar wancan matsiyacin." Fita kawai ta yi, a corridor ta tsaya ta goge hawaye sannan ta ƙarasa parlourn, ta tarar sun haye kan Faruq suna ta wasa. "Wato duk kun haye Uncle kuna neman karya shi" Ta faɗa cikin ƙarfin hali tana dariyar yaƙe. Kallonta ya yi, ya ga yanayinta ya canja, kuma da mamakinsa sai ya ga ta sauke Ihsan daga kan shi tana ƙoƙarin sauke Najma. "Ya za ki sauke su muna wasanmu?" "Zamu tafi ne" "Tafiya?" Kai ta gyaɗa. "Amma ke kika ce min zaku yini a nan" "A'a dama na faɗa ne kawai" Sai kuma ta yi saurin goge hawayen daya zubo mata. "Aunty Sady lafiya kuwa?" "Ba komai Yaro abu ne ya faɗa min a ido" Kallon side ɗin Mameey ya yi sannan ya kalleta "Idan ina ƙarami kun min wayo yanzu ni ɗin fa ba Yaro bane, kawai suna ne daya zama linzami" "Kawai zamu tafi ne" Ta furta tana riƙe yaranta, shima miƙewa ya yi "Dan Allah Aunty Sady ki zauna." "Ka barta ta tafi, ba ta zaɓi aure sama da uwar da ta kawota duniya ba." Dukkansu kallon Mameey sukayi data fito daga side ɗinta, ta ƙaraso parlour sannan ta ajiye ƙatuwar ledar dake hannunta "Gasu nan ka kaiwa Saddiqa, kace mata lace ɗin ɗaya aka samu shiyasa na ɗaukar mata atampopi guda uku." "Mameey dan Allah kiyi haƙuri, shekaru nawa da auren nan amma har yanzu..." "Yaro kai ɗa nagari ne, kana jin maganata karka yarda ka fusata ni" "Mameey dan Allah karki min baki, ina da dalilina na zama da Yazid kamar yadda kema kike da naki dalilin, Mameey mijina yana ƙaunata yana kuma ƙoƙarin kyautata min, dan me zan rabu da shi? Talauci? Mameey a duniya babu wanda yake ma wani arziƙi, sannan ko waye zan aura Allah zai iya masa jarabawa irin wadda yawa Yazid idan yaso" Mameey a fusace tayo kanta, Faruq ya yi saurin shiga tsakaninsu. "Haba Mameey dan Allah kiyi haƙuri" "Kana jin abinda take faɗa fa?" "Dan Allah kiyi haƙuri Mameey" "Sadiya idan na ƙara ganinki a gidan nan wallahi sai ranki ya ɓaci" Da sauri Sadiya ta fita, shi kuma ya kalli Mameey sannan ya bi bayansu. A farfajiyar gidan ya tsayar dasu. "Dan Allah Aunty Sady kiyi haƙuri, in dai Mameey ce kin ri ga kin saba da halinta." Bata ce komai ba ya ce "Bari na ɗauko kayan sai muje gidan Aunty Saddiqa tare" "A'a Yaro, ba zan iya zuwa yanzu ba, gida zamu wuce" "Meyasa? Haba Aunty Sady a gidan nan na san kin fi kowa haƙuri" "Yaro ba zan iya zuwa ba, kuma kada ka faɗawa Saddiqa abinda ya faru." "It's okay bari na ɗauko kayan sai na miƙa ku gida kafin na wuce" "Gaskiya a'a, ni ba zan ƙara jawa kaina wani faɗan ba, so kake ta sake zagina in na shiga motarta" "Mahaifiya ce, ba yadda muka iya" "E, amma gaskiya ba zan shiga ba" Tana gama maganar ta juya, shi kuma ya zaro dubu ɗaya a aljihu ya bawa Najma "Ga shi ko, ku sayi sweet." Kallon Faruq ta yi lokacin Najma na faɗin angode. Wuce wa kawai ta yi, yana nan tsaye har suka bar gidan sannan ya koma ciki, bai tarar da Mameey a parlour ba, dan haka zama kawai ya yi, dan baya so ya fita ya ga Sadiya na tafiya zuwa titi shi kuma ya wuce a mota. ****** ****** ******* Shiru ta yi na wani lokaci kafin ta ce "To ɗaki na zuba, bayi kuma ya rufta ga damuna yanzu a tsakiyarta muke, kana ganin yadda gari yake a yanzu ma hadari ne gashi nan, ya zakuyi?" "Umma tun farkon damuna haka muke ta fama wallahi, indai ana ruwa to a tsaye muke har a gama, idan da dare ne kuwa sai dai mu tsaya a soro, wallahi ni na fi tausayin yaran da kuma Sadiya da take da tsohon ciki" "Amma baka tausayin kanka ko? Yarinyar nan na tsaneta, saboda kana aurenta komai naka ya lalace" "Umma dan Allah ki daina faɗar haka, ni na yi imani cewar duk abinda ya faru dani yana cikin ƙaddarata ne" "Har da auren mai baƙinjini? Wadda tayi sanadin rugujewar lamuranka" "Umma..." "Yazid zan iya baka umarni ka ɗauka?" "Umma ai ba zan taɓa iya tsallake umarninki ba" "To ka saki Sadiya" Zaro idanuwansa ya yi yana kallonta, dan bai taɓa tunanin zata faɗi haka ba. _Littafin WUTAR ƘAIƘAYI ba free book bane, amma ina muku albishir da cewa book1 gabaɗaya zai kasance free, sannan akwai yuwuwar zaɓar mutum biyu da suka fi kowa yin sharhi akai su karanta kyauta._ _Sannan littafin tafe yake da tagwayensa. *TAZARAR SO, WA'ATI* da kuma *A CIKIN IDO* za ku samu littattafan a farashi kamar haka. Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* _Domin neman ƙarin bayani sai a tuntuɓemu a WhatsApp ta wannan number 07035111671._ ```Sai kunzo!``` #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah [6/16, 8:47 AM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@sanazdeeyah_ _Facebook@SaNaz Talkshow_ Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ _Book 1_ ```🆓Page 2``` "Wannan zazzare idanuwan da kake ya tabbatar min da ba zaka iya ba." "Umma dan Allah kiyi haƙuri, amma Sadiya bata min laifin da zan saketa ba, tana kyautata min, sannan kuma uwar 'ya'yana ce" "Gayyar 'ya'ya matan, sam babu magaji, wannan cikin ma bana fidda ɗayan biyu ko dai ya zube ko kuma shima a haifi mace." Umma! Haba Umma, ciki wata takwas ai ba za ai fatan haka ba" "Bayan waccan yarinyar Lihisan take ko wa, sau biyu tana ɓari fa, ga kuma talauci sai ƙara binku yake" "Umma idan ba Sadiya ba, na san babu macen da zata iya zama dani a haka, da wata ce da tuni ta gudu, amma Sadiya ta zauna dani, kuma a hakan tana kyautata min daidai gwargwado" "To tunda haka ne ai sai ka tashi ka tafi ku ƙarata ko." Jiki babu ƙwari ya miƙe. "Allah ya huci zuciyarki Umma" Baki kawai ta taɓe tana binsa da ido. ******** ******** Kitchen ɗin ya leƙa "Oh wai kina nan nake ta kwaɗa sallama" "Faruq kaine a gidan nawa?" "Ni ne fa" Kallon 'yan aikin ta yi sannan ta ce "Ku ƙarasa ina zuwa, amma ku kula karku bari ya sayu da yawa" Tana gama faɗa ta fita. Kayan ta karɓa tana fito dasu "Kenan dai zuwan ba nawa bane, gaskiya Faruq baka da zumunci" "Haka dai ake ta faɗa" "Allah ya shiryeka, ai ba dan Sadiya ta faɗa min zata zo ba da daga nan gidanta zaka wuce dan wannan kayan nata ne." "Wai dama ita kika sayawa?" "Eh amma ban faɗawa kowa ba, har Mameey" "Ai gara da baki faɗa ba, dan yanzu ta gama ciwa Aunty Sady mutunci" "Ai dama Sadiya bata da farin jini tunda ta auri Yazid" "To wai mene laifin Uncle Yazid ɗin?" "Kawai ba shi ne zaɓin Mameey ba, ita burinta Sadiya ta auri wani ɗan siyasa ita kuma Sadiya ta dage sai Yazid" "To tana son mijinta, ni wallahi ban ga aibunsa ba, ga fara'a da wuya ka ga fushinsa" "Itama tana shanyewa fa, duk abubuwan da Mameey ke mata" "Amma duk da haka yau da kuka ta bar gida" "Gaskiya Mameey bata kyautawa wallahi" "Hmm! Ai ni rasa bakin magana na yi, kuma na ce mata ta zo mu taho nan tare ta dage gida zata wuce" "Kenan dai ba zata zo ba?" "Gaskiya ko za ta zo ba yau ba, dan yanzu haka rai ɓace ta bar gidan" "Auta na nan kuwa?" "A'a gaskiya bata nan, tana school bata koma ba" "Okay yanzu dai haƙuri za kayi idan mun gama hira ka tafi gidan Sadiya tunda a mota ne sai ka kai mata, kuma ga awarar da nayi mata sai dai ka haɗa duk ka kai mata" "Aunty Saddiqa ni fa ba wai na zama ɗan aike bane" "To idan bamu aike ka ba waye zamu aika?" "Ya na iya!" Ya furta yana gyara zama. ******* ******* ******* Suna zaune a tsakar gidan bisa tabarma, Sadiyar na ɗan matsar hawaye jefi-jefi, sallama ta ji daga waje dan haka da sauri ta miƙe tare da zura hijab, ta fita dan ta duba. "Sannunku" "Yawwa sannu dai, maigidan yana nan kuwa?" "Baya nan" "Dama 'yan nepa ne mun zo karɓar kuɗin wuta." Sai lokacin ta kai dubanta ga kurangar da suka jingine jikin tumbar wuta. "Dan Allah ku yi haƙuri idan ya dawo zan sanar masa sai ya kai kuɗin har ofishin ku." "Idan ya kai kuɗin sai a dawo a mayar masa amma yanzu gaskiya yankewa zamuyi dan tun jiya muka sanar da shi cewa indai bai kawo kuɗi ba zamu zo mu yanke, kuɗaɗen da ake binku suna da yawa" "Mun sani amma wallahi iya haske kaɗai muke gani ko fanka bamu da ita" "To Hajiya wannan kuma ai ba laifun mu bane, kune kuka ga zaku iya, ka ga Bala, maza hau ka yanke, idan sun biya sai a gyara." Tun da motar ta shawo kwana Sadiya ta kafeta da ido, gabanta ba ƙaramin faɗuwa ya yi ba, dan in dai Mameey ce ta tabbatar sai an samu matsala. Faruq ne ya fito daga motar, ya ƙarasa gabanta "Aunty Sady ba dai wutar ku za a yanke ba" "Sun ce sai sun yanke" "Ai ba munce bane, ke kanki kin san mun ɗaga muku ƙafa" Ajiyar zuciya kawai ta sauke bata sake magana ba. "Har nawa ne kuɗin?" Faruq ya tambayi ogan nasu. "21,000. Duk wata dubu uku kaɗai muke karɓa a gidan nan na su, amma wannan shi ne wata na bakwai basu bayar da kuɗi ba, tunda suka dawo gidan nan sau ɗaya suka bayar." "Zan bayar, ya sauka kar a yanke musu wuta" "A'a Yaro kar ma ka fara, ina ka ga wannan kuɗin" "Amma dai Aunty kin san idan bani dasu ai ba zan ce a sauka ba" "Ka bari su yanke, idan Yazid yazo sai ya biya a gyara" "Hmmm! Oga bari na maka transfer." Sadiya komawa cikin gidan ta yi dan ta lura Faruq ma ba zai ji maganarta ba. Tana nan zaune ya shigo da ledar a hannunsa, Ihsan da Najma da gudu suka je suka rungume shi. "Uncle ka dawo" "E babies" Ya fara ƙarewa gidan kallo yana sake shiga tsananin mamaki. "Aunty Sadiya anan kuke rayuwa?" "Faruq karka ce komai dan Allah" "Kiyi haƙuri amma dole na faɗa, duk yadda nake ganin munin wancan gidan naku sai naga ya fi wannan daraja." "Ka zauna Yaro" Kan tabarmar ya ƙarasa ya zauna. "Can daya rushe ina ne?" "Banɗakinmu ne, shiyasa ma na tafi gida dan nayi wanka acan tunda na samu dai na yiwa yara, amma kuma ka ga abinda Mameey ta yi" "Aunty Sady kuma a haka kuke haƙuri da rayuwa, naga kin fito da kaya da alamun ma ɗakin zuba yake" Murmushin yaƙe ta yi kawai. "Zan yi wa Aunty Saddiqa magana sai mu haɗa a gyara banɗakin da rufin ma, ni ba zan iya ni kaɗai ba, musamman ma banɗaki at anytime za a iya buƙata." "A'a ni ban ce ku yi hakan ba, ba alhakinku bane gyara muhalli na, kuma shi kansa Yazid ɗin ya fita samo mai aiki ne." Murmushin yaƙe Faruq ya yi sannan ya ce "Ga wannan ashe ma naki ne aka saka ni wahala biyu, wannan awarar ma takice ta ce tunda baki je ba, sai na kawo miki" Sadiya ta buɗe ledar da mamaki take ɗaga leshi da atampopin "Wai Saddiqa bata gajiya ne?" "Ta ya zata gaji, ai ba'a gajiya da kyautatawa ɗan uwa" "Hakane, amma gaskiya sun yi kyau sosai, nagode Allah ya saka da alheri kace zan zo har gida na kuma yin godiya." "Insha Allah" Ya faɗa yana miƙewa. "Ya kake ƙoƙarin tashi?" "E, zan tafi" "Tun yanzu?" "Akwai abinda nake son yi" "Kai dai baka son ka zauna saboda ka ga gidan nawa duk sai a hankali" "Aunty Sady kenan!" "Anyway, ka gaida min Auta, ita ce bamu haɗu ba" "Za taji insha Allahu" **** **** **** Yana shiga Mameey da Auta suka ɗago suna kallonsa. "Lafiya kuwa? Na ga ka shigo kamar wanda aka jefo" Zama ya yi a ɗaya daga cikin kujerun, ya ɗan dafe kansa kaɗan sannan ya ɗago. "Mameey dan Allah ki ɗan ragawa Aunty Sady, wallahi tana buƙatar mu, tana da damuwa" "Yaro kana ganin irin abinda take yi, ni wallahi bana tausayin Sadiya domin ita ta jefa kan ta a halin da take ciki" "Ƙaddararta ce a haka Mameey" "Yaro! Batun fa Aunty Sadiya da laifin ta, ko dangin mijinta ma kallon mai farar ƙafa suke mata amma ta nacewa Yazid" "Baki da kunya Auta, yanzu kin taɓa kiran sunan mijin Saddiqa babu kara?" "Ni fa dama tun can bai min ba, kuma a yanzu ma wallahi gani nake shi ne ya saka ta a baƙar rayuwar nan" "To dama waye, tun lokacin daya fara son ta, nake ƙoƙarin rabasu amma Sadiya taƙi ganewa, gani take kamar zan rabata da rayuwarta, tun lokacin daya sanar min shi malamin makaranta ne kuma albashinsa naira dubu talatin ne na san tabbas irin wannan ranar zata zo" "Mameey yanzu duk ba wannan ba, tunda aure dai ta riga tayi, kuma dole sai ta aure shi saboda Ihsan da Najma, amma dan Allah a duba lamarin ta" "Yaro me kake so a duba? Ta karɓi gadonta ta bashi yayi noma suka salwanta, 'yar uwarta ta bata kuɗi dan ta ja jari nan ma ta ba shi ya lalata su a banza, yanzu har gadonta ta sayar fa kuma still babu kuɗin, so me kuma zamu yi da ya wuce mu zuba masu ido" "A'a Mameey hannun ka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka zubar" "Faruq kenan, wallahi idan ya isheka da azabar ciwo tuni zaka yanke shi" "Dan Allah Mameey ki taimaka, wallahi yanzu haka daga gidan nake, banɗakinsu ya rufta, sannan duka ɗakunansu zuba suke, ta ce min jiya ma sai a zaure suka kwana" "Anty Sadyn?" Cewar Auta "E ita fa" "Mameey..." "Surayya dan Allah ka da ki saka na yi abinda ban yi niyya ba" Tana gama faɗa ta miƙe ta bar parlorn. Surayya kallon Faruq ta yi ta ce "Yaro wai da gaske kake?" "Kin san ba zan yi ƙarya ba, kaɗan ya hana na yi wa Aunty Sady kuka" "Nawa ne zai isa a yi aikin gabaɗaya" "Zai ci kuɗi da yawa kin san rufi yana da tsada" "Banɗaki daya rufta shima fa zai ci kuɗi" "Wallahi kuwa" "Zan bayar da 20k sai a yiwa Aunty Saddiqa magana ma" "Amma a ina kika samu?" "Ka san Mameey tana bani 10k duk ƙarshen month, na transport da abinci, so dama ina da 15k a ajiye idan ta bani na this month gobe zuwa jibi sai na haɗa na bayar" "Amma kina ganin ke ba za ki takura ba?" "Yaro muddin muka bar Aunty Sady a haka mu za a zaga, muna gari ɗaya amma tana fama da rayuwa, ni da za a bani gado na da zan raba biyu ne na bata rabi" Murmushi ya yi, tare da faɗin "Lallai Auta kin fara hankali." Harara ta watsa masa tare da faɗin "Kai ma kayi hankali bare ni" Murmushi ya yi, dan baya da energyn yin faɗa a wannan lokaci. ****** ****** ****** Kyakkyawar mace, doguwa fara sol ta fito daga toilet, dogayen hannayenta suna kan doguwar fuskarta tana goge ruwan dake kan girarta, ta ƙarasa jikin drawer ta buɗe tare da ɗauko hijab, tana ƙoƙarin zurawa ta ji anyi knocking ƙofar, da sauri ta kai dubanta ga ƙofar sannan ta saka hannu a hankali tana laluben glass ɗinta, tana ɗauka ta saka sannan ta ƙarasa jikin ƙofar ta buɗe. "Ya dai?" "Mommy ta ce na sanar miki Yaya Affan ya farka" "What?" "Ehen! Ya farka kuma sunanki ya fara kira" "Muje na gan shi" Ta faɗa tana yin gaba, har ma ta wuce Lawisa da tazo kiranta, a parlour suka ci karo da Mommy. "Badriyya dama idanunki biyu amma kika zauna a ɗaki, bayan kin san Dr ya ce ki daina zama ke kaɗai" "Ance min Affan ya farka?" "E, amma ba za ki samu ganin shi a yanzu ba?" "Amma Mo...." "Ki bi umarnina kawai Badriyya" Ɗan lumshe idanunta ta yi, sannan ta buɗe ta diresu akan Mommy wadda taga ɓacin rai kwance saman fuskarta. "Har yanzu Affan bai dawo dai-dai, kuma daya farka sunan Nashwa ya kira, kuma ya buƙaci ya ganta, dan haka kafin ki ga Affan da buƙatar Dr ya fara ganinsa." "Nashwa!" Badriyya ta maimaita sannan ta samu kujera a daddafe ta zauna jin kanta yana sara mata, sai kuma tayi zubur ta miƙe tsaye tare da nufar gaban ƙatuwar plasma dake ajiye kan tv stand ta rage volume sannan ta tayar da sallah. Tana idarwa ta ɗaga hannayenta hawaye masu zafi suka kwanta saman fuskarta ta fara addu'o'in neman mafita a rayuwarsu, sannan ta shafa ta lalubi glass ɗinta ta mayar da shi fuska sannan ta miƙe tsaye, bata ga Mommy a parlour ba sai Lawisa da ta zabga uban tagumi a bisa rug dake shimfiɗe tsakiyar parlourn. "Aunty Badriyya" Lawisa ta furta tana kallonta, ita kuma bata ce komi ba, sai ido da ta bi Lawisa da shi. "Tabbas ya farka kuma da kunnena na ji ya ambaci sunanki ba Nashwa ba" "Lawisa baki ji daidai ba, amma ni na san idan sunana Affan ya kira, babu abinda zai hana Mommy ƙin bari na ganinsa" "To ko dai kunne na ne bai faɗa min daidai ba" Murmushin yaƙe Badriyya tayi lokacin kuma taji wasu siraran hawaye sun ƙara zubo mata. Zama tayi ɗaya daga cikin kujerun sannan ta ce "Tsayin watanni shidda kenan, ban fita ko ina sannan kuma ina gida ɗaya da Affan amma an hana na ganshi, Lawisa ya Affan ya koma?" "Aunty Badriyya Affan ya rame sosai, ya yi duhu, sannan kuma ya tara suma da yawa" "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Badriyya ta furta tana dafe fuska da hannu. "Yanzu duk gayu irin na Affan haka ya koma" "Ƙwarai Aunty, sai dai kuma...." Shigowar Mommy ne ya saka Lawisa ƙin ƙarasa maganar da take ƙoƙarin yi. "Badriyya!" "Na'am Mommy" Ta furta tana tasowa. "Zauna ma ba sai kin tashi ba" Mommy ta furta daga inda take tsaye kafin ta ƙaraso ta zauna kan kujera. "Tsawon watanni shidda kenan sai yau Allah ya tashi Affan, kuma Nashwa ya ce yana son gani bake ba, duk da kece a tare da shi a lokacin da wannan iftila'in ya same ku, amma meyasa ya nemi Nashwa?" Kallonta Badriyya ke yi sai dai ta rasa amsar da zata bata. "Badriyya anya babu haɗin bakin ki wurin kai Affan ƙasa?" Da sauri ta ɗago ta kalli Mommy hawaye tuni sun wanke mata fuska. "Mommy ko da zan kai kowa ƙasa ban da Affan" "Ta ya zan gaskata haka? Meyasa ya ambaci Nashwa bake ba?" "Ban sani ba" Ta furta tana sakin kukanta a fili. Sai lokacin Lawisa ta ce "Amma Mommy da bakina na ji ya ambaci sunan Aunty Ba...." "Dilla rufa min baki, ki bini a hankali Lawisa. Kin ci sa'a sosai dana barki kike ganin Affan" Tana gama faɗa ta tashi ta wuce ta barsu anan parlour. "Sai yaushe zan bar gidan nan? Sai yaushe zan ga ko da hasken rana ne Lawisa? Meyasa ba a kashe ni ba? Gabaɗaya an garƙame rayuwata a wannan sashe an kuma rufe ko ina, ko haske bana gani sai na lantarki" Dafe goshi ta yi tana sakin wani sabon kukan. Lawisa da sauri ta taso ta ƙaraso gabanta ta ce "Aunty Badriyya kiyi haƙuri, insha Allahu komai ya zo ƙarshe tunda Yaya Affan ya tashi" Riƙota Badriyya tayi tare da faɗin "Lawisa kin tabbatar Affan ne ba musaya aka yi ba?" "Aunty babu wanda ya yi musaya, kin san Affan tun fil'azal ɗan lelen Mommy ne, kuma ko bayan rasuwar Daddy Mommy tafi tausayawa Affan. Aunty na san Mommy ba za ta taɓa cutar da Affan ba, sai dai...." "Sai dai me?" "Babu komai" "Ki faɗa min gaskiya Lawisa, na san in har Affan ya rasu to tabbas ba za a barni a raye ba" "Rayuwarki ba a hannun kowa take ba" "Idan har haka ne a barni naje ga iyayena da kuma dangina meyasa aka ajiye ni anan?" Ajiyar zuciya Lawisa ta sauke sannan ta ce "Maganar gaskiya fitarki anan abu ne da zai matuƙar wahala muddin ba Affan bane ya tashi" "Meyasa?" "Saboda daga ke har Affan a idon duniya matattu ne tun ranar da kuka samu haɗari..." Ko maganar bata ƙarasa ba Badriyya ta sume a gurin. ***** ***** ***** Kallon shi take tun daya fara shan ruwan bai ajiye ba sai daya shanye tas, ta kalli kofin sannan ta ce "Gaskiya kasha rana Abban Najwa" "Sosai ma, kin ga dai jiya an kwana ana ruwa amma kin ga yanda rana ta ƙwalla har zuwa yanzu da yamma tayi." "Bara na kawo abinci, idan ka ci sai ka huta, sannan mu mayar da kayan ɗaki" Bata jira me zai faɗa ba kawai ta miƙe ta ɗauko masa abincin, ta dire masa a gabansa. "Yau dai Saddiqa ta aiko mana da awara mai yawa" "Yanzu nake shirin cewa ina kika samo awara" "Ita ta aiko Faruq ya kawo." "Yawwa Sadiya, kin ga dai bana nan kika fito da kayan nan kika yi aiki, dan haka yanzu haƙuri za kiyi ni na mayar ba tare da kin yi aiki ba, ki daina dan Allah kinji" "Yazid abu ne daya zama dole sai anyi" "To kin yi naki yanzu ki bari nayi nawa" "Wani aikin kayi fa, kuma sai na bari ka sake kama wani" "Ni na ce zan iya ai" Murmushi tayi sannan ta ce "Yanzu ya ake ciki game da gyaran banɗaki?" Shiru ya yi kafin ya ce "Sadiya ni kaina abin nan yana damuna wallahi, gaskiya sana'ar buga-buga ba ta mai iyali bace, kin ga dai yanda rayuwar ta zama a yanzu, sai muyi dakon ma ko mu sauke kaya amma sai a bamu dubu biyu, dubu uku" "To ko dai a faɗawa mai gidan? Sai nake ganin ai shi ne da alhakin gyarawa ba kai ba" "Wallahi ba zai yi ba, baki san zaluncin su ba, akan gyaran nan zai iya cewa mu bar masa gida, kuma in muka bari gyarawa zai yi ya saka wasu" Miƙewa tayi, ya yi tunanin ko ranta ne ya ɓaci, sai ya ga ta ɗauko wata leda ta dawo ta zauna. "Saddiqa ce ta aiko min da kaya wai na yi fitar suna, to ni ina naga kuɗin da zan ɗinka kayan ma, shi ne na ce bari na kawo maka kawai a sayar a saka rufi ko a ɗaki ɗaya ne, sai kuma a gyara banɗaki in za su isa, dan kayan gaskiya masu tsada ne sosai." "Sadiya ba zai yuwu ba, ki ɗinka kayanki ta gani ta ji daɗi" "Gaskiya ni nafi buƙatar gyaran nan fiye da ɗinka wannan kaya." "Duk da haka ki bari a samu wata mafitar dai, yanzu dai za a shigo a kwashe ƙasar kafin mu ga abinda Allah zai yi." Ba dan taso ba haka ta haƙura ta riƙe kayan. _Washe Gari_ Tana cikin shirya Najma ya fito, suka sakarwa juna murmushi. "Daddyn Najma ina kwana" "Lafiya lau Momyn Najma" "Har ta karya?" "E, da yake akwai sauran bread sai na ɗumama awara na haɗa mata ruwan lipton tasha" "Sugar a ina kika samu?" "Na bayar ta sayo ne, ai ka san jiya Faruq ya basu kuɗi so dasu nayi amfani" "To bari nazo na kaita ko" "To!" Ta faɗa tana goya mata school bag sannan ta ce Najma ban da wasa" Ta miƙa mata lunchbox ɗinta. Yana ƙoƙarin fita Umma ta doka sallama, abin ya basu mamaki sosai ganinta da sassafe ko ƙarfe takwas bata yi ba. "Umma lafiya kuwa?" Yazid ya tambaya yana kallonta da mamaki. "Oh sai babu lafiya za ka ganni a gidanka?" Murmushi ya yi, kafin ya sake magana Sadiya ta duƙa har ƙasa ta gaisheta, sai dai bata ko kalleta ba bare ta amsa gaisuwarta. Sai ma cewa Yazid ta yi "Ga kuɗi a samu a gyara banɗaki ayau, domin shi ba kamar ɗaki bane da zaku yi ta faman raɓe-raɓe in ana ruwan sama" Kallon kuɗin yake kafin ya ce "Umma a ina kika samo kuɗi masu yawa haka?" "Ka dai riƙe sai nayi maka bayani" Karɓar kuɗin ya yi yana kuma kallonta har a lokacin. "Tinkiyar ka dake ƙauye ita naje na sayar dan a samu a gyara inda ya ɓaci" Zaro idanuwa ya yi, ya kalleta sannan ya kalli Sadiya da har lokacin tana nan a ƙasa. *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting. Sannan ina maraba da duk wanda suke so a tallata musu hajarsu, a cikin littafin, ko kuma a facebook da tiktok ku tuntuɓi wannan lambar 07035111671_* *_Har yanzu na yi VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_* Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah🦋✍️ [6/16, 8:47 AM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@sanasdeeyah_ _Facebook@SaNaz Talkshow_ Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ _Book 1_ ```🆓Page 3``` "Umma dan Allah idan ma wasa kike ki daina, wallahi zuciyata bugawa take" "Ni sa'ar wasanka ce da zan maka wasa? Ai ko tsokana tun ranar dana baka umarni ka rabu da wannan annobar mai farar ƙafa ka kafe ka ƙeƙashe kace ka ji ka gani na fita sabgarka, yanzu ma dan ka kawo min kukan ka shiyasa na ga ya dace na yi abinda zan iya" "Umma....!" Sai kuma ya dafe kai, sannan ya sake juya kuɗin "Umma wannan tinkiyar fa na ajiyeta ne saboda haihuwa idan Sadiya tayi in musaya da rago a yanka, amma...." "Dalla dakata Yazid" Ta katse shi cikin ɓacin rai. "Haihuwar da ba a san ranarta ba shi ne zaka kasa gyara banɗaki, idan ta haihu yanzu a nan tsakar gida za ta riƙa wankan jego? To gasu nan dai na fita haƙƙinka, in ka ga dama kar ka gyara banɗakin ruwanka ne wannan." Tana gama magana ta juya ta fice, sai lokacin Sadiya ta sauke ajiyar zuciya gami da miƙewa ta shiga ɗaki. Gefen katifa ta zauna sai kuma ta fashe da kuka mara sauti, yana shigowa ta fara ƙoƙarin goge hawayen duk da a lokacin wani bai bar zuba ba. Kusa da ita ya zauna tare da faɗin "Dan Allah kiyi haƙuri da abinda Umma ta miki" Ba ta ce komai ba, sai ma kanta data sauke ƙasa. "Wannan kuɗin ba za taɓa ba, zanje na sayo rago komin ƙanƙantarsa, ko kuma na je ƙauye sai na haɗa yaran data haifa a sayar sai a sayi rago." "A'a Yazid! Umma ta fimu gaskiya, ka yi amfani da kuɗin a gyara bayin da kum...." Bata ƙarasa ba ta ji cikinta ya karta, ta ɗan cije leɓe "Ya dai?" Ya tambaya yana kallonta. "Cikina!" Ta furta sai ƙuma ta sauka ƙasa lokacin da taji bayanta ya riƙe. Hannun Yazid ta riƙo ta kalleshi cikin tashin hankali "Cikina da bayana Yazid" Sai kuma ta fashe da kuka. Ganin dai ta ruɗe ta ce nan ta ce can ya saka da sauri ya tashi ya tafi neman mota zuwa asibiti. ****** ****** ****** A hankali ta ajiye ledar sannan ta juya zata fita taji ya kira sunanta. Juyowa tayi ta kalleshi, sai kuma ta ƙarasa gaban gadon. "Dama za a iya haɗa baki dake aci amanata?" Kai ta girgiza lokacin da hawaye masu zafi suka fito daga idanuwanta. "Ina Nashwa take?" Kallonshi take, kafin tayi magana aka turo ƙofa, juyawa tayi tana kallon Mommy da ta shigo. "Lawisa! Me kika faɗa masa?" "Babu komai Mommy" "To fita, tun da kin kawo abinda na saka ki" "Mommy...!" Ya furta a sanyaye lokacin kuma Lawisa ta juya zata fita. "Dan Allah ki bani dama na yi magana da Badriyya" "Affan har yanzu baka da lafiya, ka bari ka warware sai kayi magana da duk wanda kake so" "Kun hanani ganin kowa Mommy ko dai Nashwa ta haƙura dani? Ta tsaneni bata son ganina ko?" "Nashwa ba zata tsane ka ba" "Idan har Nashwa na ƙaunata ita ya kamata na fara gani a lokacin dana buɗe idanuwana, Mommy ki bani damar magana da Badriyya please" "Badriyya bata tare damu, daga ni sai kai sai Lawisa a gidan nan" "Mommy na san tana gidan nan Lawisa ta faɗa min please Mom" Ya furta yana haɗe hannaye ita kuma ta dafe goshi. "Affan ya tambayeni?" Badriyya ta faɗa lokacin tana zura glasses ɗinta bayan ta gama goge hawayen daya wanke fuskarta. "Aunty Badriyya kiyi haƙuri amma har yanzu Nashwa yake son gani duk da na sanar masa muna tare dake a cikin gidan nan" Riƙo hannun Lawisa ta yi cikin kuka ta ce "Meyasa ban mutu ba? Meyasa na rayu? Nashwa ce ya kamata ta rayu amma bani ba" "Saboda Affan bai nemeki ba shiyasa kike wannan fatan? Aunty Badriyya ko da Affan baya son ki bai kamata kiyi wa kanki fatan mutuwa ba" "To mene ya rage Lawisa?" Ta furta tana miƙewa tsaye "Na rasa komai Lawisa, rayuwa nake kamar gawa a gidan nan, an hanani fita, an hanani waya, hatta iyayen da suka kawo ni duniya a tunaninsu ina ƙarƙashin ƙasa, mene yafi wannan ciwo, me ake nufi dani ne?" "Na san rayuwarki ba zata taɓa ƙarewa a haka ba, Mommy tana so komai ya lafa sai mu tattara mu bar garin nan." "To ni mene nawa a ciki? Meyasa ke ake bari ki fita kije office ni kuma aka kulleni anan, karatu da kuma yarona babu Lawisa" Ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka. "Karatunki yana nan insha Allah, bambanci kuma ke matar Affan ce, zasu iya bibiyarki" "Idan har basu bibiyi ƙanwar Affan ba, ba zasu bibiyi matarsa ba" "Aunty Badriyya, nima iya asibiti ne kaɗai nake zuwa, kuma kullum bana cire nose mask da glass ɗin idona, daga asibiti sai gida, amma akwai wani ƙoƙari da zan miki" "Wane iri kenan?" "Zan miki hanyar ganin Affan ba tare da Mommy ta sani ba, sai dai akwai abu ɗaya da nake so na roƙeki" "Ina jinki" "Karki ɗaga hankalinki idan kin ga yadda ya koma, idan kika ɗaga hankalinki to Mommy zata iya ganewa" "Insha Allah ba zan ɗaga hankalina ba Lawisa, amma kina ganin Affan zai so ganina?" "E me zai hana, kefa matarsa ce" Hannu ta saka ta goge hawaye sannan ta ce "Allah yasa ya yi farin ciki da hakan" "Amin ya rabbi" Hannu ta saka tana goge mata hawaye fuskarta ɗauke da murmushi. ****** ****** ****** Yana tsaye a ƙofar labour room shi kaɗai yake ta zagaye, ya kira wayar Siddiqa yafi a ƙirga amma a kashe, Auta da Mameey kuwa gabaɗaya sun jefashi a blacklist. "Kaine mijin Sadiya?" Jin an yi maganar ya saka shi saurin kallon matar. "Ni ne" "Ok. Ka biyoni office na maka ƙarin bayani" Tana wucewa ya kalli labour room ɗin sannan ya bi bayanta da sauri. Takarta ta miƙa masa lokacin tana zare glass ɗin fuskarta "Gaskiya dole sai dai a yi mata c.s saboda ɗan a gicciye yake ba zata iya haihuwa da kanta ba." "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ya furta da jimami sannan ya ce "Allah yasa ayi aikin lafiya" "Amin. Zaka biya kuɗin aiki dubu ɗari da hamsin, sai kuma jini da muke buƙata leda biyu, idan ka biya zamu bayar da takarda kayi signing" "Oh...oh..ok" Ya faɗa sannan ya miƙe, maimakon ya fita sai ya fara yin hanyar toilet" "Waccan ce ƙofar fita" Ta furta tana kallonsa. Yana fita kai tsaye gida ya koma ya ɗauko kuɗin da Umma ta kawo da wanda ya ɗan samu ya haɗa ya ƙirga gabaɗaya dubu casa'in da ɗaya da ɗari biyar ne. Tunani ya fara yi, ta ina zai nemo cikon, ganin babu sarki sai Allah ya saka ya ɗauki napep zuwa gidansu. Da Fatima ya fara cin karo a tsakar gida tana tsintar wake "Ina Umma" Shi ne abinda ya furta bayan sallama. "Yaya ina wuni" "Ina Umma na ce?" "Gani, lafiya kake mata masifa, kaje waccan mai farar ƙafar ta haɗo maka zafi shi ne zaka huce kan ƙanwarka" "Umma akwai matsala" "Allah ya rabamu da ita, mene ya faru?" "Sadiya ce babu lafiya, tana can haihuwa tazo kuma ance dole sai an mata c.s Umma wallahi bani da wasu kuɗi face wanda kika kawo ɗazu, kuma ba za su isa ba" "To me kake nufi kenan?" "Umma dan Allah ko ranta min ne kiyi" "Rance? Ni in ranta maka kuɗi ka kai ayi wa waccan yarinyar da bata ganin mutuncina aiki" "Bata gani kam, ga son nuna ita ta Allah...." "Ki rufa min baki Fatima ko na mangareki" Maryam da ta fito tana hamma kallon shi tayi sannan ta ce "Yaya ina wuni" Bai amsa ba, Umma ta ce "Ai ba zai amsa miki ba tunda an taɓa 'yarso gayyar 'ya'ya mata, na tabbatar yanzun ma mace za a fiddo. Mtsww" "Umma ki sani wannan ba zaɓin Sadiya bane yin Allah ne" "To na ce zaɓinta ne? Ai uwarsu ma haka ta diresu babu namiji a cikinsu shiyasa gidan babu tarbiyya babu ƙwaɓa, ka ga Yazid ka tashi ka bar min gida kafin ka gama ɓata min rai." "Maryam" Ya faɗa yana kallonta. "Dan Allah ko zan samu rancen dubu hamsin a wurinki" "Wooo! Yaya ni da ita waye ya ajiye wani" "Amma naga business kike kuma baki rasa kuɗi" "Oh ni Rahane, kenan har ka fara zargin 'yan uwanka suna da shi suka hana ka" Miƙewa ya yi, suna kallon shi har ya bar gidan. "Dan Allah dubesa yana tafiya sumi-sumi duk ya bi ya lalace ya mayar da kanshi talakan ƙarfi da yaji" "Ni wallahi haushi ma take bani na tsaneta shiyasa ma ko gidan bana zuwa" Cewar Fatima, Maryam ta ɗora da faɗin "In kinje ma da takaici za ki dawo, ko kuma ki dawo da baƙar yunwa. _*5 hours later*_ Kallon nurse ya yi ya ce "Please ko zan iya shiga na ganta?" "E ai tana ward zaka iya shiga" Har ya wuce ta ce "Amma bawan Allah ɗan ji mana" Juyowa ya yi sannan ya dawo gabanta. "Ka tausayawa baiwar Allahn nan kar ta rasa rayuwarta ko kuma mahaifarta ta samu matsala dan Allah" "Wallahi tunda na fita ban zauna ba, fafutukar haɗa kuɗi kawai nake" "Kuma har yanzu basu haɗa ba?" "90k ne kawai a hannuna." "To ina ganin ka je kayiwa Doctor magana, zai iya yi mata aikin in yaso daga baya sai ka biya sauran kuɗin kafin a sallameta" "To shikenan, bari na dubata tukun." Halin daya same ta kuwa sai daya ji kamar ya zubda mata hawaye. "Abban Najma ka samo kuɗin?" Ta faɗa da ƙyar, hawaye na fita a idanunta. "Su nake fafutukar nema insha Allah za a samu" "Dan Allah ka nemo, ni kaɗai na san irin azabar ciwon da nake ji, ko kuma ka je ka sanarwa da Mameey" "Haƙƙina ne ba haƙƙinsu ba, bana so ya zama takura" "Ka taimaka min kar in mutu dan Allah" Ta faɗa tana sakin kuka, shi kuma cikin tashin hankali ya miƙe tsaye" "Bari na je na ga yadda za ai" Har ya wuce ta riƙo hannunsa, ya kalleta "Koda na mutu dan Allah ka kular min da yarana, kar ka bari su yi kukan maraici" "Ki daina wannan maganar, insha Allahu zamu rayu tare mu kuma gina rayuwar 'ya'yanmu tare." Yana gama faɗa ya wuce da sauri. Ajiyar zuciya Doctor ya sauke kafin ya ce "A baya muna yin haka, amma sai wasu patients suke samu su sulale daga zarar an masu alfarma, wannan dalilin ne ya saka muka daina" "Wallahi ba zan taɓa guduwa ba, zan iya baku adireshi na" "Ka yi haƙuri yallaɓai, matsalar ba daga mu bane daga sama ne aka aiko cewar mu daina wannan alfarmar" Shiru ya yi kafin ya miƙe ya fita kawai. Kai tsaye makarantar su Najma ya wuce lokacin ma daya je har ɗalibai sun gama tafiya sai kaɗan da aka makara wurin ɗaukarsu. Ya ɗauketa suka koma gida baya da wani kuzarin yi masu wanka kawai ya ɗauki kayansu a leda ya saka sannan ya shiga maƙota ya karɓo Ihsan, har zai tafi Fiddausi ta biyo shi "Lafiya kuwa har yanzu Sadiyar bata sauka ba?" "Wallahi har yanzu dai tana can tana fama, yanzu haka ma sun ce aiki za su yi mata" "Aiki kuma?" "Wallahi kuwa" "Oh! Shi fa ciki haka yake da wuyar sha'ani ko wanne da kalar nasa naƙudar, ga Najma da Ihsan lafiya ta haifesu amma wannan sai anyi aiki." "To ya za ayi" "Tana labour? Dan na gama abinci yanzu nake ƙoƙarin zuwa, dan ma ka dage sai kun tafi ai da har kai ka tsaya ka ci tunda bata nan, Ihsan ce kaɗai ta ci ga kuma Najma ma na san tana jin yunwa." "Ai ina sauri ne zan kaisu gida" "Nan ma ai gida ne da ka barsu na yi mata wanka, ka ga sai na tafi dasu asibiti amma babu daɗi mene amfanin maƙotaka ace ka tafi ka kai su har can unguwar dan Allah ka bar su anan" "To shi kenan nagode, amma dan Allah in za ki tafi ki barsu a gida kar ki tafi dasu kin san yara kar su je can su yi ta ƙiriniya ga kuma mararsa lafiya" "To shi kenan ba damuwa" Godiya ya yi mata sannan ya bar su Najma anan, dama suna wasa da yaran gidan shiyasa ma daya ce su zauna ya je ya dawo ba su wani damu ba. ****** ******* ****** A hankali suke tafiya gabanta bayan faɗuwa babu abinda yake, a haka har suka ƙarasa ɗakin da Affan ke jinya. Lawisa ta kalli Badriyya murya ƙasa ta ce "Dan Allah karki daɗe, kuma duk yanayin da za ki ganshi ka da ki tsorata." Kai Badriyya ta gyaɗa sannan ta murɗa handle ɗin ɗakin ta shiga. Yana kwance a gado amma tsabar ramarsa bata gane da mutum a gadon ba, tana tsaye tana ƙarewa ɗakin kallo kawai taga ya ɗan motsa, da mamaki take kallon gadon kafin kai tsaye ta ƙarasa gabansa. "What!? Affan kaine a haka?" Ta furta da ƙarfi lokaci guda kuma ta runtse ido tare da rufe bakinta da hannu. Tuni hawaye sun fara mata sintiri a fuska duk da idanunta a rufe suke. "Tunda kin gansa hankalinki ya kwanta ai" Ta ji muryar Mommy kamar daga sama, da sauri ta buɗe idanuwanta ta kalli Mommy sannan ta ƙara kallon Affan, ya koma kamar ƙwaringwal idanuwansa sun zama ƙwala-ƙwala yayinda fatarsa gabaɗaya ta wani bushe, kanshi am masa aski ral. "Ban yarda wannan Affan bane Mommy ina Affan kuma me kuke nufi dani?" "Ai dama na san ba za ki yarda ba shiyasa tun farko ban bari kin ganshi ba, fita." Ta ƙarasa magana cikin tsawa. "Mommy wannan zalunci ne, ya kamata akai Affan asibiti yana buƙatar kulawa ta musamman" Kusa da ita Mommy ta ƙarasa sannan ta ce "Me kike faɗa Badriyya?" "Mommy idan ɗan da kika haifa ne a haka wallahi na tabbatar sai kin nemo mafita, ba za ki bar shi a haka ya kom...." Mari taji lafiyayye a kuncinta, wanda har yayi sanadiyyar faɗuwar glass ɗinsa, cikin ɓacin rai Mommy ta saka ƙafa ta take glass ɗin. "Daga yanzu a haka za ki cigaba da zama a cikin gidan nan naga da wane idon za ki kalleni kina faɗar maganganu har haka, ke kin isa ki faɗa min yadda zan so Affan, kin san yadda nake ƙaunar Affan a raina, da yaushe kika san Affan ɗin? A ƙarƙashin kulawa ta ya rayu har ya zama mutum kika same shi har kike faɗa min wannan maganar banza" Hawaye kawai take, dusu-dusu take ganin Mommy dan ganinta kawai take amma bata iya gane ita take kallo ko kuma ta juya mata baya. "Badriyya!" Ta ji muryar Affan ta doki dodon kunnenta. Da sauri ta juya tana kallonsa sai dai a yanzu bata iya gane komai saboda babu gilashi, tana iya gane akwai mutum a gadon amma bata iya gane komai nasa. "Ki je gurin mijinki, tunda baƙin naci ya kawo ki" Hannu ta saka tana tafiya tana lalube har ta ƙarasa jikin side drawer ta zauna "Kuma ki faɗa masa wani abu da zai ɗaga hankalinsa ki ga yadda zan saɓa kamanninki" "Affan..!" Ta furta lokacin da wasu siraran hawaye suka zubo mata. "Affan kana jina? Kuma kana iya gane komai?" "Ina Nashwa take?" Shi ne abinda ya faɗa, ta sake jin hawaye a fuskarta. "Affan ka kwantar da hankalinka, Nashwa tana nan kuma na san za ta zo gareka" "Yaushe?" "Soon insha Allah" "Badriyya mene ya same ki naga kamar bakya gani?" Bata iya ba shi amsa ba sai hawaye daya mamaye mata fuska. "Kukan da kike yi ya tabbatar min ba dake aka haɗa baki wajen ajiye ni anan ba, ina fatan daga wajen Nashwa ma ya kasance haka" "Nashwa ba za ta taɓa cutar da kai ba Affan" "To amma meyasa ta gujeni?" "Ba tafiya ta yi ba, ina mai tabbatar maka da zata dawo gareka, aiki ne ya ɗan riƙeta a Abuja" "To nan ina ne?" "Nan muna Ibadan ka kwantar da hankalinka" "Nashwa nake son gani ko ta halin ƙaƙa" "Kin ga Badriyya tashi ki fita ya isa kuma, dan ance ba a so ya fiya surutu" Tana ƙoƙarin miƙewa tana dafa bango, Mommy ta ƙaraso tare da fuzgar hannunta hakan ba ƙaramin tsorata ta yayi ba. Sai data jata har parlour sannan ta hankaɗata ta faɗi ƙasa. "Wannan ya zama shi ne farko shi ne kuma na ƙarshe da za kije gurin Affan musamman ba tare da sanina ba. Lawisa da tun shigowarsu ta miƙe sai lokacin tayi saurin sauke ƙwayar idanunta ƙasa. "Ke kuma kin kyauta" Tana gama maganar ta juya ta barsu anan. Ranar kwana Badriyya tayi tana kuka, Allah yaso ba gilashi ɗaya ne da ita ba. ***** ***** ****** An ɗebi kusan awowi shidda Yazid na ta fafutukar neman cikon kuɗin aiki, amma bai samu ba, gashi nurse ɗin sai kira take, ya rasa ina zai tsoma gudan ransa. Kai tsaye gidan su Sadiya ya nufa dan nan ne last hope ɗinsa. Yana tsaye a farfajiyar gidan sai ga maigadi daya tafi yi masa iso ya fito tare da Faruq. "Oh ashe ma ɗan gida ne, Uncle Yazid ai da ka ƙaraso ciki" Ya faɗa yana miƙa masa hannu suka yi musabaha. "Ai bama wani abu bane dama Sadiya ce naƙuda ta kama, to tun safe ma tana asibiti" Sai kuma ya yi shiru wanda hakan ne ya tabbatarwa da Farouq akwai matsala. "Aunty Sadiya'n ta haihu ne?" "A'a dole C.S za ayi saboda yaron a gicciye yake to sai dai kuɗin dake hannuna basu da yawa tun safe nake ta fafutukar neman ciko, dana ga yamma naVyi sai na ce gara dai na sanar daku" "Subhanallahi! Bari na sanarwa Mameey in yaso sai mu wuce tare" "To babu damuwa" Ya faɗa yana gyara tsayuwa. "Hmmm! Ba ga irinta nan ba, kuɗin da za a yiwa matarka aiki baka da shi, wallahi ban taɓa ganin faƙirin mutum irin mijin Sadiya ba, ni ban ga abinda ta gani a jikinsa ta nace masa ba." "Mameey a fara ceton ran Yaya Sadiya first, in ya so duk maganar da za ayi ta biyo baya" Surayya tayi magana tana yana gyalenta. "Shi kenan ku je, duk abinda ake ciki ku riƙa kirana kuna sanar min, Faruq ka kira Saddiqa kuwa?" "Na kira har 3 times bata ɗaga ba, na san idan ta gani za ta kira" "Ok. Allah ya raba lafiya" "Amin Mameey" Suna zuwa suka tarar babu kowa a wajen Sadiya face wannan maƙociyar ta su, lokacin Sadiya ta galabaita ko magana aka yi mata sai dai ta bi mutum da ido, kuma shima kallon da gani bata san waye akanta ba. Yazid da Faruq sune suka biya kuɗaɗen da aka buƙata sannan aka basu receipt suka kaiwa likita, cikin mintuna talatin aka gama shiryata zuwa theater room. Suna nan zaune, amma Yazid ya kasa zama yana tsaye yana addu'ar Allah ya sauketa lafiya, Faruq da wayarsa ta fara ringing ya kalla. "Mameey" Ya furta lokacin daya kara a kunne. "Ya ake ciki ne Faruq?" "An dai shigar da ita theater sai fatan a yi aiki lafiya" "Dan Allah ana ciro Baby ku kira ku sanar min, sannan kuma ku tabbatar Sadiya ta tashi please" Murmushi ya yi kafin ya ce "Mameey ki tayata da addua, insha Allah da ƙafafuwanta za ta fito" "Allah yasa" "Amin ya rabbi." Tana kashewa ya kalli Yazid ya ce "Uncle ka zauna tun ɗazu kake a tsaye" "Kar ka damu Faruq zan zauna" Ya furta a sanyaye sannan ya mayar da kallon sa theater room. _Bayan wasu awoyi_ Mameey ta kira ya fi a ƙirga ana faɗa mata Sadiya har lokacin ba a san komai game da ita ba, domin wanda aka shigar da ita tare an fito da matar kuma ma tagwaye ta haifa, amma Sadiya shiru, suna dai ta addu'a tare da fatan samun nasara. Likita daya fito da sauri suka miƙe, Yazid kuwa dama a tsayen yake. "Kune kuka kawo Sadiya Mustapha?" Ya tambaya tun kafin su yi tasu tambayar. "E mune" Shiru ya ɗan yi kafin ya ƙara kallonsu, Faruq kasa haƙuri ya yi ya ce "Doctor dan Allah ka faɗa mana shin ya 'yar uwarmu take, wannan kallon da kake mana wallahi ba ƙaramin furgita muke ba" "Am sorry to say...." "Doctor dan zatin Allah kar ka ce Aunty Sady ta mutu" Surayya ta faɗa tare da fashewa da kuka, ta kuma kai gwiwoyinta ƙasa, dan ta ji gabaɗaya sun kasa ɗaukarta. *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting. Sannan ina maraba da duk wanda suke so a tallata musu hajarsu, a cikin littafin, ko kuma a facebook da tiktok ku tuntuɓi wannan lambar 07035111671_* *_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_* Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah🦋✍️ [6/16, 8:47 AM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ Arewabooks@sanazdeeyah Facebook@SaNaz Talkshow Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ _Book 1_ ```🆓Page 4``` "Karku ɗaga hankalinku, 'yar uwarku ba rasuwa tayi ba tana nan da ran ta, sai dai ɗiyar da aka cire mata ta rasu sannan itama mun saka mata oxygen dan haka a yanzu ba zamu baku ita ba sai zuwa dare" "To Doctor babu matsala, a bamu yarinyar sai muje mu yi mata sutura" Cewar Faruq, dan Yazid ya kasa magana. "Za a fito da ita yanzu tare da uwa" Doctor na wucewa Faruq ya kalli Surayya ya ce "Auta ki tashi tunda dai tana nan da ranta ai da sauƙi ma." Miƙewa ta yi tana goge guntun hawayenta. Yazid ma ajiyar zuciya ya sauke, duk da an rasa jaririyar amma dai da sauƙi. Shi ya karɓi jaririyar tare da uwa ya tafi da ita, su kuma suka zauna jiran a fito da ita duk da ance masu za a ɗauki lokaci kafin a fito da ita. ***** ***** ***** Kallon gawar ta yi sannan ta ce "Astagfirullah, kar dai ace min mara mutunci amma ai can gidan ya kamata a kai gawar ko?" "Umma da nan da can ɗin duk ɗaya ne, kuma ni tunanin in kai can bai zo min ba, har ma na kira liman na sanar masa, tunda dai jaririya ce" "Shi kenan, Allah ubangiji ya sa mai ceto ce" "Amin ya rabbi." Fatima da take tsaye sai lokacin ta ce "Da alama dai Sadiya uwar mata ce, da wannan ta rayu mata uku reras fa" "To ke ɗin ba mace bace, bana son rashin kunya Fatima" "Allah ya baka haƙuri Yaya" Ta faɗa tana wucewa. Har sai da aka gama sutura sannan ya samu ya sake dawowa gurin Umma. "Wallahi duk ka fita hayyacin ka Yazid." Murmushi ya yi sannan ya ce "Umma dan Allah ku shirya ku dubo Sadiya" Shiru ta yi kamar tana karantarsa sannan ta ce "Kai dai komai Sadiya, to idan bamu dubo ta ba za a doke mu ne?" "Umma ba maganar duka ba ne, maganar dacewa ce" "To tunda bana yin abinda ya dace ba zanje ba, 'yan uwanta su zo su rufeni da duka" Shiru ya yi, ya ɗan lumshe ido sannan ya buɗe, ya kuma miƙe tsaye "Umma ni zan wuce" Bata kula shi ba har sai daya fita ta ce, "Mace ta bi ta shanye ka" Maryam a zaure ta ci karo da shi, ta gaida shi ya amsa sannan ya fita ita kuma ta shiga gidan. "Umma! Umma!!" Kallonta ta yi sannan ta ce, "To makauniya gani anan, ke baki da aiki sai kwaɗawa mutum kira kamar kin bani bashi" "Yi haƙuri Umma, naga Yaya ya fita da ɓacin rai, hala kuɗi ne suka sake yanke masa" "A'a, ke dai kawai ki saka ɗan uwan nan naki a addu'a Allah ya haɗa shi da mayya, matarsa ce ta haihu ɗan babu rai" "Umma 'ya dai" Cewar Fatima" "Au wai macen aka kuma?" "E, amma dai babu rai" "Lallai wannan mata ta zame mana alaƙaƙai" "Hmm! Ai wannan akan ta zai iya saɓawa kowa" "Na ga alama kam!" Ta furta tana cire gyale kafin ta ce "Gaskiya test ɗin yau tayi masifar wahala, ni Allah yasa ma na ci" "Amin, ya kike yiwa kanki mugun baki, ni yanzu ai kece hope ɗina, tunda wancan sakaran na haifawa mace." "Umma insha Allahu ba zan baki kunya ba" "Allah ya sa." ***** ***** Kallon banza ta sake watsa masa kafin ta ce "Amma ai da buƙatar kanka ce da har gida za kazo, ni kam baka kyauta min ba, yanzu idan da Sadiya ta farka ban zo ba ai babu yadda za ai na wanke laifi na" "Aunty Saddiqa dan Allah a huce haka, wallahi ki tambayi Auta, daga ni har ita mun miki kira yafi a ƙirga, kuma bani da nutsuwar zuwa na faɗa miki" Ya ƙarasa yana ɗan murmushi wanda har sai da lips ɗinsa ya loɓa. "Za kayi dariya mana, tunda ka san abinda ka aikata." Surayya zama tayi gefen gadon da Sadiya take tare da faɗin "Kema Aunty Saddiqa da laifin ki, sai ayi ta kiranki ki ƙi ɗaga waya" "Amma dai kin san ina sane ba zan ƙi ɗagawa ba, ina can kitchen mun fito da komai na ce yau general cleaning zan yi, saboda azumi yana ta ƙaratowa, gara na gama kintsa komai" "Kin ga kenan bamu da laifi, kin bar waya a sama kin sakko parlorn ƙasa kuma cikin kitchen" Za ta sake magana suka ga Sadiya ta motsa, da sauri Faruq ya miƙe ya ƙarasa jikin gadon nata. A hankali ta fara motsa baki suna kallo, sai data gama salati sannan a hankali ta fara buɗe idanuwanta, sai da ta kallesu ɗaya bayan ɗaya sannan ta kai hannunta saman cikinta taji wayam, da sauri ta miƙe zaune, har sai da ta ɗanji zafi Saddiqa ta riƙeta, "Auta maza kirawo Doctor" Surayya da sauri ta fita kiran Doctor. "Saddiqa na haihu kenan? Me na haifa? Yana ina?" Rasa amsar da za su bata sukayi, ta kalli Faruq shima ita yake kallo. "Kin ga ki kwantar da hankalinki tukun, kin ga dai C.S ne aka yi miki, akwai ɗinki a cikin ki kar ki fama" "Ina Babyn?" Ta sake tambaya a kuma daidai lokacin Dr ya shigo. Jikin gadon ya tsaya ya gama duba ta, sannan ya ƙara da cewa "Mun rasa babyn, amma ke kuma mun yi nasarar ceto rayuwarki, ki godewa Allah kuma kiyi tawakkali da shi, insha Allahu za ki samu wasu rabon a gaba" Har ya gama magana bata ce komai ba, sai daya fita sannan ta fashe da kuka. "Kiyi haƙuri Aunty Sady..." Auta ta faɗa a lokacin kuma Saddiqa ta yi saurin yi mata alama ta yi shiru. Sai da Sadiya ta yi kuka sosai sannan ta share hawaye ta kallesu. "Mene na haifa kuma ina Yazid da yara?" "Ba mu ga yaran ba, wataƙila suna gidan kakarsu, amma shi Yazid bai daɗe da fita ba kika tashi." "Saddiqa mene na haifa?" "Mace ce" Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa "Allah ya sa mai ceto ce" "Amin ya rabbi" Satin ta ɗaya aka sallameta sai dai gida aka wuce da ita saboda ɗinkinta sai ya ƙarasa warkewa a cewar Mameey. Tana kwance a kan kujera yaran suka shigo, Ihsan tana ƙoƙarin hawa jikinta Surayya ta janyeta "Sarakan san jiki ni ai naso an miki ƙanwa ko kin bari Yayata ta huta" Murmushi Sadiya ta yi sannan ta kalli Surayya sai kuma ta ɗan tashi zaune. "Autah" "Na'am" "Wai ko dai kun daidaita da Faruq ne?" "Wane Faruq" "Har guda nawa ne damu?" "Aunty wai wannan ɗan yaron? Taɓ! Allah ya kiyaye" "Kin dai san mace ba ta fin ƙarfin namiji ko?" "Ai wallahi ni kam ba dai Faruq ba haba ki daina faɗa ma kar ya raina ni" Murmushi ta sake yi tare da faɗin "Na ɗauka 'yar gida za a yi" "Aunty Sady kenan." Fitowar Mameey ce ta dakatar da su. Ta samu kujera ta zauna sannan ta kalli Surayya. "Auta kama yaran ku tafi ina son yin magana da Sadiya." Ji tayi gabanta ya yanke ya faɗi, a kuma lokacin Autah ta kama hannun yaran suka wuce. "Sadiya!" Shiru tayi kanta a ƙasa, zuciyarta na harbawa da sauri. "Kin san babu abinda mijinki ya kawo sannan danginsa babu wanda ya zo?" Kallonta tayi sannan ta ce "Mameey naman da aka kawo daga gidan Aunty Saddiqa shi ne ya kai mata ya ce ta sarrafa sai ta kawo mi..." "Dalla rufa min baki. Ni za ku rainawa hankali?" Kai Sadiya ta girgiza lokacin kuma hawaye masu zafi suka subo mata. "To na san cewa ba Yazid bane ya kai, kuma C.S aka yi miki kina buƙatar ki ci nama sosai ko da shi ne ya kai wannan yana nufin sau ɗaya za ki ci naman ƙan-baki? To ni duk ba wannan ba, a rasa wanda zai zo ya duba ki bare ya miki jaje, wai dole ne aure a wannan ahalin matsiyatan, to ki kirawo min shi yanzun nan" "Mameey dan Allah kiyi haƙuri" "Za ki kirawo min shi ko kuma ni in tashi in tafi gidansu" "A'a Mameey" Sadiya ta faɗa da sauri sannan ta ɗauki wayarta ta kirashi. "Ki duba wayar da kike amfani da ita, ko an baki ma sai kin ba shi ya sayar kamar wadda aka yi wa asiri, so ai ba hauka bane" Ita dai bata ce komai ba ta miƙewa Mameey waya lokacin da Yazid ya ɗaga. Jin muryar Mameey ya saka ya gaisheta "Ba gaisuwarka nake buƙata ba ka riƙe kayanka. A daidai lokacin Faruq ya yi sallama ya ji Mameey na faɗar haka. Kallon Sadiya ya yi sannan ya kalli Mameey. "Sadiya nake so ka saka, dan ko yanzu ka saketa ba zata rasa miji ba, amma ni har yau ban ga wata ribar aurenka ba, bayan rama da lalacewa da tayi, sannan ta haihu amma a rasa wanda zai zo ya mata jaje a gidanku, to Yazid na baka nan da anjima ka turowa Sadiya takardarta, bata jira me zai faɗa ba ta kashe. "Mameey dan Allah kar ki rabani da Yazid, wallahi ba zan iya rayuwa ba sai da shi." "Sadiya!" Mameey ta furta da mamaki tana kallonta. "Ni kike kallo kina cewa kar na rabaki da ɗa namiji?" Shiru tayi hawaye na tsiyaya daga idanunta. Faruq ya samu guri ya zauna "Mameey tunda tana son mijinta please let it be!" "Faruq idan ina magana da Sadiya akan miji kana saka baki wallahi sai ranka ya yi mummunan ɓaci" "Am sorry Mameey" Kallon Sadiya ta sake yi sannan ta ce "Sai ki zaɓa ko Yazid ko mahaifiyar ki, tunda ke baki san annabi ya faku ba." "Mameey...." Sai kuma ta tsaya lokacin da taji komai yana juya mata. A take a gurin ta suma. ********** Tana kwance akan gado ta ji anyi knocking ta san ko bata bayar da umarni ba dole a shigo domin mutum biyu ne kaɗai take iya gani, daga Mommy sai Lawisa. Shigowar Lawisa ta saka Badriyya saurin tashi zaune. "Meyasa yau baki fito ba" "Bana jindaɗi ne" Miƙewa Lawisa tayi ta ƙarasa gaban kwanukan abincin, babu abinda ta taɓa, kallonta ta yi sannan ta ce "Tun safe babu abinda kika ci, ko dai akwai wani abu?" "Lawisa so nake na fita daga gidan nan" Kallonta sosai take kafin ta ce "Zamanki a gidan nan yafi fitarki alheri" "Meyasa?" "Saboda dake da Affan gabaɗaya wanted ne" "Shin wai me muka aikata ne? Affan bai yi kisan kai ba, haka ni kuma ban san mene ake ba ina cikin gida fa lokacin da ya yi aikin, shi da Nashwa suka yi amma bani ba" "Dalilin daya saka suka kashe Nashwa kenan" "What?" Ta furta tana miƙewa tsaye. "Abinda ya kamata ace kin sani ne tuntuni, Nashwa ta rasu, kuma a dalilin ƙoƙarin bankaɗo abinda bai shafeta ba, har gara Affan ma aikinsa ne duk da shima bai zama wajibi a garesa sai ya kutsa inda yafi ƙarfinsa, amma ki sani tun daga ranar suke neman Affan, shi ne dalilin daya saka suka buga motarku a tunaninsu kun mutu mune kaɗai muka san kuna raye" "Amma......" Sai kuma ta yi shiru. "Ki faɗi duk abinda ke ranki." "A lokacin da abin ya faru Nashwa bata garin, ta tafi Kano tunda ita tun satin bikin ma ta tafi, mu kuma a hanyar zuwa dinner ne accident ɗin ya faru" "To kina tunanin idonsu baya kanta bayan ta bi Affan sun ganowa kansu abinda yafi ƙarfinsu." "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Badriyya ta furta tana dafe kai. "Abinda ya kamata ace kin daɗe da sani ne na sanar dake a yanzu. Kun yi hatsari a kuma wannan hatsarin yaronku ya rasu, ku kuma aka ɗauke ku ranga-ranga zuwa asibiti, bayan an tabbatar da kuna raye shugabansa ne ya bayar da shawarar a bayyana rasuwarku ga duniya hakan kaɗai zai saka masu nemanku su haƙura, domin yadda kukayi hatsari ana gani an san shiryayye ne, muna tsaka da wannan tashin hankalin aka kiramu aka sanar mana da an harbi Nashwa, ita a take aka ce ta rasu dan ba a kaita asibiti da rai ba." Shiru Lawisa tayi kafin ta cigaba da cewa "Yadda kika riƙa ɗagawa Affan hankali akan auren, da yadda kika riƙa faɗar maganganu da ace babu ke hatsarin nan da ya afku da kuma ace bamu san da case ɗin nan ba, to babu yadda zai ai mu kasa ɗaura laifin mutuwar a kanki" Kuka sosai Badriyya take, "Aunty Badriyya na san duk abinda kika yi a wancan lokacin kinyi ne saboda son da kike yiwa Affan, to a yanzu Affan naki ne ke kaɗai, Nashwa bata raye" "Affan ba zai taɓa zama nata ba" Da sauri suka kalli ƙofa. Mommy ta shigo ɗakin sannan ta tsaya tana kallonsu. "Affan ba zai taɓa kasancewa tare da ita ba, domin ni ban yarda babu hannunta a kisan ba, tunda dai ga shi har yanzu Affan bai damu ya ganta ba" "Mommy wallahi ba zan taɓa iya kisa ba, ko in saka hannu a kisa" "Bincike ne kaɗai zai tabbatar da haka, kuma daga zarar Affan ya miƙe zai iya tona miki asiri, wannan dalilin ne ya saka kika zama matatta har a gurin iyayenki" Kai ta riƙe tana jin wani irin zugi, ita bata taɓa sanin son da takewa Affan zai zama matsala har haka ba. "Mommy gaskiya bata da hannu, idan da hannunta, ba zata yarda su tafi mota ɗaya da Affan ba" "Lawisa a yanzu ba zai shaideta ba, zamu jira har lokacin da Affan zai samu lafiya" "Ajiyar zuciya kawai ta sauke. Yayinda Badriyya ta cigaba da rera kuka. ****** ****** Shiru Lawisa ta yi na ɗan lokaci kafin ta ce "Amma kina ganin babu matsala idan mun koma Kano Mommy?" "E, in sha Allahu babu komai, tunda kin ga duk abinda ya faru da shi a Yola ne, babu haɗi gwamnatin Kano da Yola" "Amma kuma ai Nashwa 'yar Kano ce, kuma har can suka bi ta suka kashe" "Ita sun bita Kano saboda dama bibiyarta suke, Lawisa idan muka bar Affan a haka zai iya haukacewa gabaɗaya saboda a yanzu haka in kika kalli Affan kin san ba daidai yake ba" "Hakane Umma" "Ana so ya fara ɗan fita, kuma kin ga nan Abuja masu kuɗi anan suke lafewa, duk inda zai kai Affan zai iya haɗuwa da wasu daga cikinsu" "Amma Mommy meyasa sai Kano?" "Saboda ina da 'yan uwa sosai acan yanzu haka na bayar da cigiyar gida, daga zarar an samu to zamu koma can, sai kuma mu sama masa personal consultant da zai riƙa duba shi" "Badriyya fa?" "Na kira iyayenta, na sanar masu tana raye, yanzu haka suna hanyar zuwa nan Abuja" "Mommy ba matsala?" "Insha Allah babu" "To Allah yasa" "Amin ya Allah. Ki kirawo min Badriyya ta sameni a bedroom ɗina" "Okay." Ta furta tana da miƙewa ta bar parlourn. Tana shiga ta ga badriyya ta fito daga toilet tana laluba hanya tana tafiya, murmushi Lawisa ta yi sannan ta ƙarasa jikin side drawer ta ɗauki glass ɗinta ta ƙarasa gami da saka mata a fuska. "Aunty Badriyya ki riƙa shiga toilet da glass ɗinki idan ba haka ba wata rana za ki iya rasa inda yake kuma babu wani a kusa da zai kawo miki" Murmushi ta yi tare da zama sannan ta kalli Lawisa "So nake na koyi yawo babu shi saboda hakan zai min amfani wata rana" "Wane ya faɗa miki ba zaki samu lafiya ba?" "Bar wannan maganar Lawisa ai ni na san ganina ya tafi" "A'a Aunty tunda har kike gani da glass ina mai tabbatar miki nan gaba kaɗan za ki riƙa gani ba tare da shi ba, tunda ba da shi aka haife ki ba." "Ai ɗan adam ba a gama masa halitta har sai ya koma ga mahaliccinsa" "Hakane amma insha Allah za ki cigaba da gani" "Allah ya sa" "Amin Aunty. Wani albishir nazo miki da shi." "Na me?" "Abbu da Ammi ɗinki suna hanya" Ƙirji ta dafe tare da faɗin "Dan Allah dagaske kike?" "Sosai, yanzu ma Mommy ce ta ce na kiraki" Cikin farin ciki Badriyya ta juya, Lawisa ta yi saurin cewa "Ɗan ji mana" Tsayawa tayi tana kallonta. "A bedroom ɗinta za ki same ta" Kai ta gyaɗa sannan ta wuce, ita kuma Lawisa ta yi murmushi. Da sallama ta shiga ɗakin, Mommy ta kafe ta da idanuwanta. "Mommy barka da gida" "Yawwa Badriyya ki samu waje ki zauna" "To Mommy" Ta faɗa sannan ta zauna a gabanta amma akan carpet ta zauna. "Badriyya" "Na'am" "Iyayenki za su ƙaraso yau, kuma sai sun iso ne za su gane cewa kina raye, sai dai zuwansu ba zai sa su ɗauke ki ba, dole ne ki zauna tare damu har zuwa lokacin da Affan zai tashi" Ba ta iya cewa komai ba, har sai da Mommy ta ba ta umarnin tafiya sannan ta miƙe a sanyaye ta bar ɗakin. ****** ****** Tana buɗe idanuwanta akan Faruq ta fara sauke su, kafin ta kai dubanta ga Mameey sai kuma ta lumshe ido. "Tun da ta farka alhamdillah". Mameey ta furta tare da wucewa, Faruq a gefen gadon ya zauna yana kallonta cike da tausayawa. "Aunty Sady" Ya furta a hankali, ido ta buɗe ta kalleshi. "Please ki kwantar da hankalinki, Uncle Yazid naki ne har abada" Idanuwanta ta ɗan lumshe sannan ta buɗe tana kallon Farouq. "Dan Allah ki daina damuwa, domin idan kina damuwa mu ma ba zamu taɓa samun kwanciyar hankali ba. Ƙoƙarin tashi take, dan haka ya taimaka mata ta zauna tare da jingina bayanta da fuskar gado. Kallon Farouq ta yi sannan ta ce "Farouq mene laifin Yazid? Saboda Allah bai mi shi arziqi ba? Idan kowa ke zaɓawa kansa rayuwa na tabbatar Yazid ba zai zaɓi talauci ba" "Aunty Sady dan Allah ki kwantar da hankalinki, kin dai san halin Mameey ya kamata ace kiyi haƙuri da irin abubuwan da take miki" Haka Faruq ya yi ta kwantar mata da hankali duk da shi ƙane ne a gare ta amma shawarwari da kuma nasihohinsa sun kwantar mata da zuciya sosai, a lokacin ta ƙara tabbatar da lallai Faruq ya yi hankali. Da yamma tana kwance a gado Surayya ta shigo ɗakin. "Kowa yana parlour amma kina nan abin ki" Ta faɗa tana zama kan gadon, ita kuma ta tashi zaune. "Hmmm kin san tunanin me nake yi?" "A'a sai kin faɗa" "Surayya wallahi gani nake kin dace da Faruq" "Kai Aunty!" Ta dafe kai sannan ta ce "Kodai zamu bari Najma ta girma sai a bawa Faruq" "Ai ba za ki yiwa Faruq fatan ya jira Najma ba" "To ni kuma ta ya ya kike tunanin zan jira shi?" "Oh za kiyi aure ne yanzu?" "Sai na gama school amma ni kam Faruq ya min yaro" Dariya Sadiya ta yi tare da faɗin lallai ma yarinyar nan to yaushe kika fara soyayya da har Faruq zai miki yaro?" "Aunty ni dai ki rufa min asiri ki daina maganar nan ka da ma ya ji ya raina ni" "Sannu babba to an daina, amma ni ina hango miki dacewa ne" "Kin san Allah dan ba ki ganin Faruq kullum shiyasa kike masa kallon salihi" "To ai shi kenan, Allah ya zaɓa mafi alheri" "Amin." A*Dare* Tana zaune a ƙasan rug ɗin dake ɗakin tana bawa Ihsan abinci ta jiwo hayaniya daga parlour, gabanta ya faɗi ta miƙe tare da cewa Ihsan "Baby cigaba da cin abinci ina zuwa" Da sauri ta fita jikinta a sanyaye. Ganin Yazid abin ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba. "Yawwa dama yanzu nake shirin kiranki sai ga ki kin kawo kanki" A ƙasa ta zauna tare da sauke kai ƙasa lokaci guda ta ji bugun zuciyarta na ƙaruwa. "Na fara tunanin wannan mutumin asiri ya yi miki Sadiya" Kai ta ɗaga ta kalli Mameey hawaye na zuba a idanuwanta. "Zan baki zaɓi biyu ne ki zaɓi ɗaya, ko dai ki zauna anan wannan gaulan mijin naki ya baki takardarki ko kuma ki bi mijinki ni kuma bana buƙatar ganinki a gidana har abada" "Mameey..." "Babu abinda zan ji Sadiya zaɓi ya rage naki" Tana gama faɗa ta wuce abinta ta bar Yazid da Sadiya a parlour cikin furgici. *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting. Sannan ina maraba da duk wanda suke so a tallata musu hajarsu, a cikin littafin, ko kuma a facebook da tiktok ku tuntuɓi wannan lambar 07035111671_* *_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_* Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* lLITTAFAN SUNE: 1-WUTAR ƘAIƘAYI 2-WA'ADI. 3-A CIKIN IDO.. 4-TAZARAR SO #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah🦋✍️ [6/16, 8:47 AM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@sanazty Faceboo@SaNaz Deeyah Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ _Book 1_ ```🆓Page 5``` Sun fi mintuna biyu zaune babu wanda ya tankawa wani, sai dai Sadiya hawaye kawai ke zuba a fuskarta. "Sadiya" Ta ji ya kira sunanta a sanyaye, ta ɗago ta kalleshi idanuwanta har sun fara canja launi. "Dan Allah ka da ki rabu dani wallahi ba zan iya rayuwa babu ke a ciki" Ba ta ba shi amsa ba haka zalika ba ta bar kuka ba. "Na yi miki alƙawarin ba zan taɓa bari ki wulaƙanta ba, kuma na san Mameey tana fushi ne amma za ta sauko saboda tana sonku" "Ina tsoro Yazid" "Kar ki zaɓi rabuwarmu saboda ba zan iya rabuwa da ke ba, dan Allah ki tausaya min" Ya furta yana haɗe hannayensa. Haka ya yi ta roƙonta har ta ji cewa za ta iya bin sa, duk da tana cikin fargabar furucin Mameey, amma rayuwa da mijinta da kuma yaranta ya fi mata komai. Tana cikin haɗa kayansu Mameey ta shigo. "Sadiya haɗa kaya kike za ki bi miji?" Ɗagowa ta yi da rinannun idanuwanta ta kalli Mameey. "Kiyi haƙuri Mameey bana so na raba kan yarana dan Allah Mameey ki fahimc...." "Dakata, tunda dai haka kika zaɓa ya miki kyau, Allah ya barku tare ke da shi." Tana gama faɗa ta juya. ********** Ko da ta shiga gidan ta yi mamaki sosai da ta gan shi a tsaftace, kuma an gyara bayin sannan an sake musu rufi. Sai bayan sun huta ne take tambayarsa inda ya samu kuɗin da ya yi wannan aikin, anan yake sanar da ita sauran kuɗin aikin da aka mata ne ya haɗa ya yi gyaran gida. Shiru ta yi idanuwanta cike da ruwan hawaye dan ƙiris suke jira su zuba. "Sadiya kiyi haƙuri, ki ɗauki dangana Allah ya sa mai ceto ce, ke kuma Allah ya baki lafiya me ɗorewa" "Ban taɓa yin wahalar labor kamar na wannan cikin ba, ashe bama zamu rayu tare ba" Ta saka yatsa tana goge hawaye. "Haba Babyna, dan Allah ki bar kuka, insha Allah zamu samu wasu" Jin haka ya saka ta lumshe ido cikin jindaɗi, duk da suna da yara kuma suna cikin matsi na rayuwa amma hakan baya hanasu shan soyayya. Ranar cikin farin ciki da annashuwa suka kwana, duk da ɗinkin ta bai gama warkewa ba amma dai sai daya daɗaɗa mata ya kuma mantar da ita damuwar da ta taho da ita daga gida. *08:00am* Tana gaban murhu tana dafa ruwan shayi sai ga shi ya fito ya ƙarasa inda take. "Maman Najma ni zan tafi kasuwa." "Haba Abban Najma ya za ka fita baka karya ba" Murmushi ya yi sannan ya ce "Kar ki damu nima zan samu abu a waje na ci, amma kin ga na yi rana yanzu" Miƙewa ta yi tana kallonsa. "Dama akwai abinda nake son baka, amma tunda yanzu ka yi rana sai mu bari sai gobe idan Allah ya kaimu." "Allah ya kaimu" "Amin Abban Yara Allah ya tsare hanya" "Amin Babyn Baby" ****** ****** "Saddiqa a haka kike tunanun zan cigaba da haƙuri da Sadiya bayan ba ta jin magana ta kuma ba ta san kima da darajata ba" Mameey ta yi maganar cikin ɓacin rai. "Mameey dan Allah kiyi wa Sadiya uzuri, ni na san tana yin haka ne saboda yaranta ba ta so ta fito kuma ace za a ƙwace mata yara" "Haba Saddiqa ai ban san meyasa da ke da Faruq sam baku ganin laifin Sadiya sai kuce wai na yi mata uzuri, wane uzuri ne ban mata ba, dole sai ta tura kan ta inda ba a yi da ita." Faruq zama ya gyara sannan ya ce, "Mameey dan Allah kiyi haƙuri" "Ni fa ina ganin mijin nan nata asiri ya mata, haba wannan wane irin so ne?" Cewar Surayya. "Babu asirin da ya yi mata, kema idan kika yi aure kika haihu za ki gane irin yanda ɗa yake a zuciyar mahaifiya" Saddiqa ta faɗa tana kallon Surayya. "Amma dai kin san ko yaran Sadiya sun kai dubu zan iya riƙewa ko?" "Mameey za ki iya amma kina da tabbacin 'yan uwansa za su yarda su bar mata yaran? Musamman ma mahaifiyar shi da ba ƙaunarta take ba" "To sai ta bar musu dama ai ba dasu taje gidan ba." "Mameey kema fa kina jin zafin yadda Sadiya ke shan wahala a gidan Yazid duk da cewar Yazid yana ƙaunar Sadiya, to ya kike tunanin Sadiya za taji idan aka ƙwace yaranta aka damƙa a hannun da babu kulawa?" "Shi kenan tunda kun zaɓi Sadiya sama dani, taje ga miji nan ai dama itama miji ta zaɓa sama da mahaifiya" Tana gama faɗa ta tashi rai ɓace ta bar parlourn. Faruq ya sauke ajiyar zuciya tare da faɗin "Aunty Sady dai ƙaddararta ce a haka, kuma naga da ita da Uncle Yazid gabaɗaya suna son junansu ya kamata both family ɗin su bar su su yi rayuwarsu mu bisu da addua" "Ai ƙiyayyar Yazid a gurin Mameey fa ta daɗe Faruq" "Na sani Aunty Saddiqa amma tunda har da yara ya kamata Mameey ta haƙura." Sai lokaci Surayya ta ƙara soma baki a maganar ta ce, "Ni fa bana son Yazid ɗin nan, dama tun farko ba su dace da Aunty Sadiya ba, ni wlh ban san me ta gani ba" "Ki rufa mana baki mara kunya kawai" "Daga faɗar gaskiya" "Ke har wata gaskiya ne da ke" "Kai kuma Faruq ka kiyayeni wallahi" "Oh ni dai kike so kice na kiyaye ki" "Kin san dai ba zan taɓa faɗa miki haka ba Aunty Saddiqa." Tana gama maganar itama ta miƙe ta wuce. Saddiqa ta girgiza kai tare da cewa "Allah ya kyauta." ****** ******* Kuka sosai suke yi ita da Ammi sai da suka yi mai isarsu sannan suka tsagaita. "Amma gaskiya baku kyauta mana ba da kuka kasa faɗa mana gaskiya" "Yanzu ai ga shi kun sani, kuma a baya da mun faɗa muku gaskiya ai ba zaku iya protecting ɗin ta ba." "Haba Malama, ita ɗin fa 'yar mu ce jininmu" Ammi ta furta rai a matuƙar ɓace. Abbu ya yi saurin cewa "Mariya kiyi shiru ba abin faɗa bane, tunda dai tana raye mu godewa Allah, da fa har mun fitar da rai da ita." "Wannan ai mugunta ce, kalli yadda Badriyya ta koma, wata takwas kana ɗaki, kawai dai so sukayi su kwantar da ita kamar yadda shima Affan yake a kwance" "Wace irin magana kike faɗa haka Mariya?" "Komai ma, taya za ki ɗauko mutum ki ajiye wata takwas a ɗaki kuma ba wani ciwo yake ba, to wallahi sai na ɗauki matakin shari'a dake." Murmushi Mommy ta yi sannan ta ce, "Wannan shi ne babban kuskuren da za ki tafka a rayuwarki, muddin kika bayyana cewar Badriyya da Affan suna raye" Lawisa dai bata ce komai ba, sai ma faɗuwar gaba da taji ya risketa. "Badriyya tashi mu tafi, wallahi Affan ko ɗan gwal ne kin gama aurensa, kuma Allah ya isa bamu yafe ba" Sai a lokacin Badriyya ta saki wani sabon kuka, duk yadda taso ta bar gidan amma a yanzu sai taji bata so, duk da a gidan ma ba wani haɗuwa suke da Affan ba, amma a yanzu ta san in ta tafi za ta ƙara yin nesa da shi ne. Sai dai duk yadda taso amma iyayenta suka turje har sai da suka tafi da ita ba tare da Affan ya san wainar da ake toyawa ba. _Dare_ Tana ajiye masa abinci ta kalleshi taga idanuwansa a kanta suke, zama tayi tare da faɗin "Ko dai kana buƙatar wani abu?" "Ina Nashwa?" Ji ta yi gabanta ya faɗi, dan maganar Nashwa kawai ake mata ta ji ranta ya sosu, saboda ta san ba za su taɓa dawo masa da Nashwa ba. "Yaya bata nan, Nashwa tana Kano mu kuma muna nan Abuja, amma insha Allah next week zamu koma Kano" "Meyasa Nashwa bata zo tayi jinyata ba, ko ba a sanar da ita dalilinta na samu haɗari ba, ita ta takura sai anyi dinner kuma a hanyar zuwa muka samu accident, shin ba a ɗaura auren ba?" "Yaya baka da wata cikakkiyar lafiya, ba a so ka riƙa doguwar maganar so dan Allah ka yi haƙuri a hankali za ka san komai" "Yaushe? Ina so ku sanar dani gaskiya na ga sai ɓoye-ɓoye ake min" "Yaya calm down ka dai warke sosai sai ka gaji da ganin duk wanda kake so gani" Murmushi kawai ya yi, ita kuma ta miƙe ta fita. Kai tsaye bedroom ɗinta ta wuce, tana shiga ta faɗa gado tare da fashewa da kuka, sai kuma ta miƙe tana share hawaye ta janyo waya. "Ai na ɗauka ɓatan hanya kika yi Lawisa" "Haba dai" "E mana, na sanki ba ki da zumunci baki neman mutane, ke ko a group ma baki yin magana." "Wallahi abubuwa ne suka kwaɓe anan Rayyana, amma dai in komai ya lafa zan dawo normal" "It's ok. Ya kike ya gida da kuma Mommy?" "Lafiya lau. Dama na kirana ne na tambayeki" "Ke nan dai ba zumunci kika kira a yi ba" "Har da zumuncin ma" "Faɗi gaskiya dai" Murmushi ta yi sannan ta ce "Gaskiyar kenan" "To ina sauraronki" Zama Lawisa ta gyara sannan ta ce "Ina wannan wadda kika ce tana kama da matar da Yayana zai aura lokacin da na saka pre wedding pictures ɗinsu?" "Oh na gane, ai an ɗan kwana biyu ƙila ma har ta kusa haihuwa ko?" "Ina fa, kin san ko bikin ma ba ayi ba ta rasu sai shi kuma Yayana ya haɗu da cutar paralysis" "Subhanallahi! Amma baki taɓa faɗa ba Lawisa" "Rayyana abubuwa sun caɓe mana wallahi bani ma da wannan nutsuwar social media ma ai ɗauke mata ƙafa na yi" "Allah sarki, Allah yajiƙanta da rahama, ya jikin nasa?" "Da sauƙi sosai" "Allah ya ƙara masa lafiya" "Amin ya Allah. Dama cewa na yi idan babu damuwa ko za ki haɗani da mai kama da Nashwa, kuma ki turo min hoton ta " "Kin san mene matsalar?" "A'a sai kin faɗa" "Matar aure ce yaranta har biyu, na ukun ma dan baizo da rai ba C.S aka mata a gida tayi jinya dan munje mun dubata, kin san a time ɗin na ce miki dan dai taku siririya ce kuma tana da ɓular hanci da fashin goshi da sai na ce Sadiya ce, to itama Sadiyar yanzu ta zama siririya" "To amma ba kin ce min ƙawarki ba ce?" "E, ƙawata ce auren wuri ta yi" "Oh Allah sarki" "But duk da haka ina son contact da kuma hotonta in babu damuwa" "Gaskiya bani da ko ɗaya amma anjima insha Allah zan leƙa gidan nasu sai na karɓar miki number, hoton ne dai ban san ya za ai ba" "Ko da dabara ne a lokacin a ɗauka please" "Shi kenan zan jarraba" "Nagode sosai Rayyana" "Haba karki damu." *5 Months Later* Jin knocking ya saka ya yi saurin ɗaukar hoton ya mayar ƙasan pillow, a daidai lokacin Mameey ta kunno kai cikin ɗakin, sai da ta ƙarewa ɗakin kallo sannan ta zauna gefen gadon. "Mene yake damunka Faruq?" "Babu komai" Ya faɗa kansa a ƙasa. "Faruq ka san kai baka isa kayi min wayo ba ko? Dududu nawa kake?" "Mameey idan akwai ba zan ɓoye ba" "Amma Dr ya faɗa min damuwa ce ta yi maka yawa shiyasa jininka yake hawa, ya kuma sanar min in akwai abin da ake maka to a daina, ka faɗa min ko dai wani yana maka abin da baka so?" Kai ya girgiza sannan ya ce "Mameey kawai stress ɗin karatu ne" "Karatu?" Ya gyaɗa kai. "To ai friend ɗinka ya ce min tsawon wata guda baka je school ba, ko kaje baka shiga lecture, wani lokacin kuma baka shiga school ma, anan kuma ka ɗauki mota ka fita, shin canjin nan na mene? Me ke faruwa?" "Mameey ƙarya yake min" Ya furta yana ƙoƙarin dira daga gadon. "To ina kuma zaka je?" "Ina son zuwa gidan Aunty Saddiqa ne" "To ai shi kenan, ita ƙila ka faɗa mata gaskiya" Ta faɗa sannan ta miƙe ta bar masa ɗakin. Hoton ya janyo ya ƙura masa ido, sannan ya rungume hoton ya lumshe ido yana jin kansa na ƙara zafi da tafarfasa, da sauri ya miƙe ya mayar da hoton inda yake ɓoyonsa sannan ya faɗa toilet. A gurguje ya yi wanka ya shirya sannan ya fita. Mameey ta yi mamaki da taga bai karɓi key ɗin mota ba ya fice haka abinsa, anan ta fahimci lallai damuwarsa mai yawa ce. Waya ta ɗauko ta kira Saddiqa. "Mameey da yanzu nake shirin zuwa, ina wuni" "Lafiya lau, ya kike?" "Alhamdulillah" "Yanzu nake shirin zuwa na duba jikin Yaro, na ji Surayya ta ce har yanzu jikin nasa babu daɗi" "Ni ai lamarin Yaro har tsoro yake bani, yanzu yake ce min ya tafi gidanki shiyasa na ce bari na kirawo ki" "Nan ya taho kenan" "E haka dai ya ce min" "To shi kenan bari na jira shi" "Yawwa idan yazo dan Allah ki riƙeshi ya sanar miki abinda ke damun shi" "To shi kenan." ****** ****** A zaure ya tsaya yana sallama, tana daga ɗaki ta ji sallamar Faruq ta fito tsakar gida tare da amsa masa sallama. "Yaro shigo mana sai kace wani baƙo" Ta faɗa tana tsaye daga ƙofar ɗakin. "Ashe za ki ɗauki murya." "Haba to ni ko a mafarki ai ba zan kasa shaida muryarka ba Yaro" "Gaskiya Aunty Sady ki daina ce min Yaro, ni fa na isa aure, kin ga yarinya nan" Ya faɗa yana nuna Ihsan da ta fito, sannan ya ƙarasa gami da miƙa mata ledar da yayi masu tsarabar chocolates da fancy biscuits." "Ka san dai ba zata iya riƙewa ba ko, duk mene ka siyo haka mai uban yawa?" "Babu ruwanki, yarana na yiwa tsaraba" Ya faɗa yana fito da chocolate ya bawa Ihsan sannan ya kama hannunta suka shiga parlourn. "Thank Allah kuna da nepa" "E basu daɗe da dawo da ita ba, ga zafi ana yi, ai mukam muna nan muna shan OX ɗin daka saya mana, da yanzu muna ta fama da mafici" Murmushi ya yi tare da faɗin "Najma tana school?" "Ana can sun kusa tashi ma." "E, 12 ta kusa" "Za ka ci dambu?" "Aunty Sady ni kome kika bani ai ci zan yi" "Ok. Bari na zuba maka, dama akwai magana a baki na" "Kema har an faɗa miki kenan" "Kuma baka so na sani ko?" "Faɗa ne ni bana so" "Ai dole mu yi maka tunda mun girmeka" "Kai Aunty" "E mana." Sai daya gama ci ya sha ruwa sannan ta kalleshi a nutse ta ce "Yaro wallahi ka rame, kuma kallo ɗaya za a yi maka a gane kana da damuwa, ni na yi mamaki ma daka zauna ka ci abinci sosai anan dan cewa aka yi baka cin abinci ma" Shiru ya yi kafin ya ce "Aunty Sady ni sunana Faruq" "To na ji, faɗa min mece ce matsalar?" "Ko da na faɗa miki baki da maganinta" "Ina da shi dan ko shawara na baka na san na yi maganin wani ciwon" "Hmmm!" "Dan Allah ka faɗa min Faruq" "Aunty Sady akwai wacce nake so, kuma wallahi lokaci ɗaya na ji kawai sonta ya shige ni ba tare da na yi aune ba, Aunty na san kin san so tunda naga irin son da kike wa Uncle Yazid, to ni kuma wadda nake so na san ba zata taɓa sona ba, shiyasa nake son yaƙi da zuciyata na ga na cire son amma abin ya gagara" Sai ganin hawaye tayi a kuncinsa, abin ya bata mamaki sosai. "Faruq kuka akan mace?" "Ni kaɗai na san yadda nake ji." "To wace ce?" "Mene amfanin faɗar, bayan ba za ki iya convincing ɗinta ta so ni ba? Kawai a barni a haka" "Ka faɗa min, na maka alqawarin ko ɗiyar waye zan jarraba" "Za ki iya?" "Sosai ma" Shiru ya yi yana kallon gefe guda na tsawon second 30 kafin ya juyo ya kalleta. *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting. Sannan ina maraba da duk wanda suke so a tallata musu hajarsu, a cikin littafin, ko kuma a facebook da tiktok ku tuntuɓi wannan lambar 07035111671_* *_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_* Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* lLITTAFAN SUNE: 1-WUTAR ƘAIƘAYI 2-WA'ADI. 3-A CIKIN IDO.. 4-TAZARAR SO #FITATTUHUDU2025 #WUTARKAIKAYI #SaNaz_deeyah [6/16, 8:47 AM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@sanazty_ _Facebook@SaNaz Deeyah_ Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ _Book 1_ ```🆓Page 6``` "Aunty Sady indai ba korata kike daga gidanki ba to dan Allah kar ki takura kan lallai sai na faɗa miki ko wace ce, ni dai kawai ki tayani addu'a Allah ya sa na manta da ita." "Shi kenan, Allah ya zaɓa mafi alkhairi" "Amin ya rabbi." Ya ɗan taɓa hira da ita kafin daga bisani bacci ya ɗauke sa, dan haka ta ƙara matsar masa da fanka sannan suka fita ita da Ihsan. ***** ***** "Gaskiya bai zo ba tun ɗazu ƙila dai ya yi amfani da sunana ya yi tafiyarsa wani wurin" "To amma ina zai je bayan fama nake ya daina zaman kaɗaici amma yaƙi" "To bara na kirawo Sadiya mu ji" "Kina ganin zai je can kuwa?" "Ba tabbas amma bari na tambaya." Tana katsewa ta kira Sadiya. "Yar halak yanzun nan Najma ta gama ce min wai yaushe zan kawo ta gidanki na ce mata ta bari sai weekend" "Allah sarki, dan Allah ki kawo su tun friday" "In sha Allah, ya kike ya gida" "Lafiya lau, cewa na yi ko Faruq yazo gidan ki ɗazu?" "Ai yana nan tun safe, yanzu haka ma bacci yake" "A gidan na ki?" "Wallahi kuwa, da alama yana da damuwa kuma baya samun isasshen bacci sai anan ne yanzu ya samu ya runtsa" "Gaskiya na yi mamaki sosai, gidana ya ce zai taho fa" "Aikam dai yana nan" "To ba damuwa tunda mun san inda yake ai da sauƙi" "Hakane" "Bari na barki haka, zamuyi magana daga baya." "To shi kenan." Tana katsewa ta kira Mameey ta sanar da ita, sai a sannan hankalinta ya ɗan kwanta tunda an san inda yake. _*Bayan wata ɗaya*_ Ta daɗe a gaban gadon da yake kwance kafin daga bisani ta samu ta zauna akan carpet dake shimfiɗe a ƙasa. "Ni fa abin har ya fara bani tsoro, ciwo sai gaba yake kuma baya jin magani" "To ina zai ji magani tunda babbar matsalar shi ne damuwa kuma yaƙi ya fitar da ita a ransa." "Allah ya ba shi lafiya, Yazid ma ya ce idan ya taso daga kasuwa zai zo ya duba shi" Saddiqa ta ce "Sadiya ni kin san me nake tunani?" "A'a sai kin faɗa" "Kamar damuwar Faruq akan so ne" "So?" "Ƙwarai kuwa, saboda idan kin lura sai ya zauna ya ƙurawa guri ɗaya ido, sannan Mameey da Surayya sun sha kama shi da hoto amma daya gansu sai ya ɓoye baya bari su gani" "To a bincike ɗakin idan baya nan sai mu ga wace yarinya ce." "Surry da Mameey ba irin laluben da basu yi idan baya nan amma basu gani, na 'yan gida kawai suke gani" "Ya ilahi, to amma..." Wayar Saddiqa da ta fara ya saka Sadiya gintse sauran maganar. "Hello Dee!" "Har yanzu Mameeyn bata dawo ba" "Ok. To ba damuwa bari na fito tunda Sadiya ma tana nan" Tana gama faɗa ta kalleta. "Sadiya tunda Mameey har yanzu bata dawo ba bari na tashi na tafi gida na ɗora girki." "To shi kenan sai kin dawo" "Ok" Tana fita Sadiya ta miƙe ta koma jikin gadon da Faruq ke kwance ta zauna gefen gadon ta ƙura masa ido. "Allah ya baka wannan wadda kake so ɗin, wadda ka kasa faɗa mana ko da sunanta." Tana miƙewa taji ya riƙo hannunta, sai da ta ɗan tsorata dan batayi tunanin idanuwanshi biyu ba. "Ki zauna a kusa dani kar ki tashi" Zama tayi tana sake kallonsa, har a lokacin idanuwansa a rufe suke. "Aunty Sady ai na faɗa miki ba za ta taɓa so na ba" "Ka faɗa min ko wace ce ni na jarraba" "Ba za ki iya convincing ɗinta ta so ni ba" "Saboda me?" "Saboda ta yi nisa a son wani, har ma an saka ranar aurenta" "Duk da haka ka bani dama na jarraba..." Bai bata amsa ba aka turo ƙofa, Mameey da Surayya ne. "Aunty Sady kin ƙaraso kenan, ina wuni" Cewar Surayya. "Lafiya lau Surry" Ta kalli Mameey da ta ɗaga hankalinta ta ce "Ina wuni Mameey" Wani kallon banza ta watsa mata duk sai ta yi sanyi. "Mene ya kawo ki nan?" Furucin ya bala'in bata mamaki, ta ƙara jin ta yi sanyi dan ta yi tunanin Mameey ta huce. "Magana fa nake miki" Ta daka mata tsawar da ba ita ba, hatta Surayya sai da ta tsorata, shi kuma Faruq a lokacin ya buɗe idanunsa. "Mameey nazo duba Faruq ne" "Tunda kin duba shi ai sai ki kama hanya ko" "Mameey kiyi haƙuri" "Ki riƙe haƙurinki ki tattara ki koma inda kika fito tunda kin yi dubiya. Ba taji daɗi ba, kuma sam babu ƙwari haka ta ɗauki pause ɗinta ta fita daga asibitin. Napep ɗin da ta tara kai tsaye gida ta ce ya kaita. Tun daga nesa ta hango wata baƙar Benz sai sheƙi take. Mamaki sosai take dan ta san akaf 'yan uwan Yazid na kusa dai babu mai kalar motar nan da har zai kawo masa ziyara, bata dai sani ba ko 'yan uwa na nesa. Tana shiga Yazid ya ɗago ya kalleta tare da cewa "Yawwa ga ta ma ta dawo" Kallon mata biyu dake zaune kan tabarma ta yi, gabaɗaya babu wadda ta sani a cikinsu, sai dai yadda taga ɗaya ta ƙura mata ido har sai da ta tsargu sosai. "Mommyn Najma ki zauna mana, bari na samo masu lemo da ruwa, yanzu dama nake shirin kiranki domin sun ce min baƙin ki ne." Mamaki da kuma damuwarta ta yi ƙoƙarin kawarwa wajen ƙirƙiro murmushin dole sannan ta zauna. "Sannunku da zuwa" "Yawwa sannu" Yana ƙoƙarin fita ɗayar ta yi saurin cewa kar ka damu wallahi ba sai ka sayo mana komai ba, daga gida muke a ƙoshe muke" "Ai ruwa da lemo ba dan yunwa ake shansu ba, kuma ku baƙin madam ne, so dole na girmama ku." Daga haka ya fice, ita kuma ɗayar ta kalleta. "Sunana Lawisa, na san baki sanni ba, wannan kuma abokiyar aikina ce sunanta Mansurah. "Allah sarki sannunku da zuwa" "Yawwa sannu" Shiru ya ɗan biyo baya kafin daga bisani Lawisa ta ce "Dama nazo neman wata alfarma ne a gurinki" "Alfarma kuma? Tame?" Zama Lawisa ta gyara sannan ta fara da faɗin "Yayana ɗan jarida ne yana aiki da wani gidan radio acan garinmu Yola, mutum ne mai hazaƙa da kuma jajircewa, sai dai a shekara ta uku da fara aikinsa wata gagarumar matsala ta kunne kai, lokacin anyi zaɓe so gaskiya an ɗan rasa rayuka da dama, shi kuma sai ya nemi ya bankaɗo sirrikan wasu 'yan jarida wanda bai kai ga cimmasu ba suka ganoshi kuma suka haddasa masa hatsarin da har sai da ɗansa kwaya ɗaya tilo ya rasa rayuwarsa. Lokacin ana gab da aurensa dan a hanyarsu ta zuwa wajen bikin hatsarin ya faru, ita kuma wadda zai aura ɗin suka bita har garin nasu suka kasheta da bindiga suka harbeta" "Subhanallahi" Sadiya ta furta tana ɗan dafe goshi. "Amma idan na fahimta aure na biyu zai yi a lokacin?" "E, saboda ai na faɗa miki yana da ɗa" "Hakane! To Allah yajiƙansu da rahama ya sa can tafi musu nan" "Amin ya rabbi." Shigowar Yazid ne ya saka bata yi magana ba sai amsa sallamar da tayi tare da miƙewa ta karɓi ledar hannunsa, shi kuma ya shiga ɗaki. Kitchen ta shiga ta saka ruwa da lemo a plate sannan ta ɗauki cups ta fita, a gabansu ta ajiye tare da zama. "Ina jinku, mene alaqata da labarin da kika bayar?" "Alaqarki da labarin shi ne kamar da kuke yi da Nashwa" "Nashwa!" Ta maimaita sunan. "E, itace wadda aka kashe" Zaro ido Sadiya tayi, ita kuma Lawisa ta janyo waya ta buɗe hotunan Nashwa tare da nunawa Sadiya. Karɓa ta yi tana kalla ɗaya bayan ɗaya, "Tabbas muna kama sosai, sai dai ni bani da ɓular hanci ai, kuma bani da fashin goshi" Murmushi Lawisa ta yi sannan ta ce "Nima ba wai na ce kece Nashwa ba, na san Nashawa ta rasu, amma kamar da kike da ita yasa nazo gareki" Miƙewa Sadiya ta yi cikin tashin hankali ta haɗe hannayenta. "Dan Allah ku rufa min asiri idan dan muna kama da ita ne wallahi bani da alaqa da ita, ban san Yola ba ban taɓa zuwa ba, ban san komai daga siyasar Yola ba, dan Allah karku kashe ni ina da yara ƙanana" Cikin tashin hankali Yazid ya fito daga ɗaki jin abinda take faɗa, da sauri ta ƙarasa gabansa tare da riƙesa "Abban yara turo su aka yi, suna da alaqa da 'yan siyasar kuma ni ban san komai ba." Lawisa da Mansura gabaɗaya suka miƙe tsaye. "Ki fahimce mu, wallahi nazo ne onbehalf of my brother, he is in critical condition dan Allah ki saurareni, ni Likita ce bani da haɗi da siyasa, ta faɗa tana fito da ID card ɗin ta. A sanyaye suka zauna, Lawisa ta sake maimaita buƙatarta, sai a sannan Yazid ya ce "To yanzu mene abin yi? Sadiya matar aure ce, kuma kin tabbatar ba ita ce wadda kuke nema ba" "Hakane kuma na san hoton Sadiya tun kafin Nashwa ta rasu, lokacin na saka hotonta a story na whatsapp sai wata ta ce min tana kama da ƙawarta har ta turo min hotonki" "Wace ce?" "Gaskiya ba zan faɗa miki ba, saboda na mata alkawarin ba zan yi haka" Leɓe Sadiya ta cije sannan ta ce "Hmmm!" "Sadiya dan Allah kiyi min taimakon nan, har yanzu Yaya ba sai Nashwa ta rasu ba" "Ya kamata ku gaggauta faɗa masa saboda bani da alaqa da Yayanki kuma ni matar aure ce babu abin da zai sa naje ga Yayanki a matsayin wata wadda bani bace, dan Allah kiyi haƙuri " Tana gama faɗa ta miƙe da sauri ta shige ɗaki. "Buƙatarku ba mai yuwuwa bace, ku yi haƙuri" Yazid ya faɗa yana miƙewa. ******* ******* Tana kwashe tuwo ya shigo gidan. "Yau tuwo ake mana kenan" "E, amma fa saboda Faruq na yi dan na san yana son tuwo miyar egusi shi ne favorite ɗinsa." Kujera ya ja ya zauna gabanta, tana zubawa yana ƙulle ledar. "Sadiya nifa ina ji a jikina daga wannan shekarar wahalarmu ta ƙare" "Allah yasa" "Amin, amma shawararki ta noman attarahu da kuma gudunmawar kuɗi da kika bayar ina ji a jikina bana tarhu zai yi kyau kuma zamu samu alheri" "Allah yasa" "Amin Sadiya, gaskiya zai yi wuya a samu mace kamarki" Murmushi ta yi sannan ta ce "Ai kai ma samun jajirtaccen namiji kamarka sai an tona" "Sadiya" "Na'am" "Kina ganin idan naje duba Faruq ba za a samu matsala ba?" "Ina fatan haka insha Allah" "To Allah yasa" "Amin" _*Asibiti*_ Koda suka shiga ana ta yi masa faɗa baya son cin abinci. Sadiya ta gaida Mameey sannan ta ajiye ledar abinci, Yazid ma ya gaishe ta, sai dai yau anci sa'a ta amsa gaisuwar babu yabo babu fallasa. Saddiqa ta gaida shi sannan ya ƙarasa gaban gadon ya duba Faruq, bai ko zauna ba ya tafi, dama ba su taho da yara ba. "Aunty Sady me kika kawo min?" Faruq ya tambaya yana kallonta. "Tuwo ne, ko za ka ci yanzu na zuba maka? Dan Allah Faruq ka riƙa cin abinci, jinya ba zata yuwu babu abinci ba." "Kema kya faɗa masa, kowa mitar da yake masa kenan amma ya yi kunnen uwar shegu damu." "Zan ci!" Ya furta a sanyaye, murmushi Sadiya ta yi sannan ta miƙe ta zuba masa. "Da kaina ma zan baka" Ta faɗa tana zama gefen gadon. Babu wanda baiyi mamakin yadda Sadiya ta lallaɓa shi ya ci tuwo da yawa, sannan aka ba shi yoghurt ya sha kaɗan. "Dada ma tana tafe ai, bata ƙasar kuma wai ticket ya mata wahalar samu amma insha Allah zuwa next week za ta shigo Nigeria" "Allah ya kaimu, ƙila ita zai faɗa mata abinda ke damunsa" "Taɓ! To Allah ya sa" "Amin." ***** ****** Cikin tashin hankali yake kallonsu. "Mommy amma meyasa baku faɗa min ba" "Saboda baka cikin hayyacinka Affan" "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, amma ita Nashwa mene lafinta da za su rabata da duniya" "Tare kuka ga sirrinsu ka ga kuwa dole itama su yi tunanin za ta iya tona asirinsu" "Mommy ni ina so na koma Yola ina so na fallasa wani sirri da zai girgiza al'umma" "Kayi haƙuri Affan amma koda ka koma Yola babu wanda zai karɓeka, saboda zasuyi tunanin fatalwa ce" Bai yi magana ba, sai dai yanayin fuskarsa kaɗai zai tabbatar maka da yana buƙatar ƙarin bayani amma bai samu ba sai ma cewa ta yi. "Anan zamu cigaba da rayuwa kuma za ka nemi aiki amma ba jarida ba domin ka gama aikin jarida." Tana gama maganar ta miƙe ta bar ɗakin. Lawisa ta taso daga kan sofa ta koma gadon ta zauna a gefe. "Yaya sai haƙuri amma abubuwa da yawa marassa daɗi sun faru, sannan kuma ina da wani albishir da zai saka ka farin ciki" "Lawisa shi ke nan na rasa Nashwa?" "Addu'a za mu cigaba da yi mata Allah ya gafarta mata ya san can tafi mata nan" Idanuwansa tuni sun kaɗa sun yi jajir. "Babu Nashwa sannan babu ɗana" "Yaya ka yi haƙuri" "Itama Badriyya an raba ni da ita" "Na san ita kanta a duk inda take hankalinta yana gareka, kuma dole su neme mu su dawo maka da matarka tunda ba sakinta ka yi ba. Kuma ka san mene?" "A'a sai kin faɗa" "Na haɗu da mai kama da Nashwa sosai" "Da gaske?" "Wallahi da gaske nake kuma abin daɗi ma a garin nan take" Miƙewa tsaye ya yi sai kuma ya koma ya zauna saboda jiri da ya ji. "Lawisa tashi muje gareta babu mamaki Nashwa ta ce ta yi ɓadda kama." "Yaya ba ita bace" "Karki manta Nashwa marainiya ce, a gidan marayuwa ta girma kafin daga bisani wata mata ta ɗauketa, baki tunanin dama 'yan biyu ne?" "Gaskiya ba twins bane, saboda ita wannan tana da dangi da kowa da marainiya ce ba za a ƙi faɗa mata ba." "Lawisa akwai wanda suke riƙe yara kuma har yaran su koma ga Allah basu san cewa ba waɗannan ne asalin iyayensu ba" Shiru ta yi sannan ta ce "Haka ne amma...." "A'a Lawisa, koma dai mene ina son ganinta" "Shi kenan" "Ayau nake son na ganta" "Yaya kayi haƙuri za ka ganta amma mu bi komai a sannu" "Ban gane ba, ganinta wani big deal ne?" "Sosai ma" "Yi min bayani" "Yaya just be calm please" "Lawisa so kike ki sosa min rai?" "Ba haka bane Yaya, amma ka san idan a haka ka je ba zata karɓeka ba, dole zamuje ka yi aski and kana buƙatar waya ma" "Wannan duk zamu iya ayau kafin muje" "Yamma tayi so dole mu bi komai step by step kuma Mommy ma bata sani ba har yanzu sannan kuma ba za ta taɓa yarda mu fita at this hour ba, ni kaina idan ba night duty nake ba bata yarda fa" "It's ok Allah ya kaimu gobe" "Amin ya rabbi." ****** ****** A bakin ƙofar ta gansu sun yi cirko-cirko, lokacin Surayya ta shigo dan har da ita ta gani. Gaban Saddiqa ta ƙarasa da ledar magunguna da ta tafi karɓowa ta kalleta "Lafiya kuwa?" "Wai daga ɗan surutun da mukayi har jininsa ya hau, shi ne aka saka muka fito yanzu haka Likitoci biyu ne a ciki" "Subhanallahi. To ai naga ba wata magana ya yi da yawa ba" "Ke da kika san dama ba lafiya ne da shi ba, kuma fa abin har ya fara taɓa zuciyar shi" "Gaskiya Faruq baya kyautawa, ya faɗa mana amma yaƙi faɗa mana ko wace ce bare mu san abin yi" "Mun yi magana da shi jiya, yake ce min faɗar ma bata da amfani na takura masa shi ne yake cewa ai tayi aure" "Matar aure?" Sadiya ta faɗa da mamaki. "Yi ƙasa da murya kar Mameey ta ji, ya ce dan Allah kar na sanar mata" "Tashin hankali" Ta furta tare da dafe goshi. Fitowar likita ya saka suka yi shiru. "Dr Allah ya sa dai jikin na shi da sauƙi" "E, da sauƙi alhamdulillah, ina magungunan?" Da sauri Sadiya ta miƙe ta ba shi sannan ta koma ta zauna. Ya shiga ya ɗan juma a ciki sannan ya sake fitowa. "Wace ce Sadiya?" "Ni ce" Ta furta tana miƙewa. "To zo mana" Ya furta yana komawa ciki. A sanyaye ta turo ƙofar yana zaune ma ya jingina bayanshi da bangon gadon. "Wannan ce?" Dr ya tambaya yana nuna Sadiya, shi kuma Faruq ya gyaɗa kai. "Sadiya bismilla zauna mana" Zama ta yi sannan ta ce "Jikin na shi da sauƙi?" "E, ku san haka" Ɗayan Dr ya faɗa tare da jan kujera ya zauna gabanta. "Sadiya ko?" "E, ni ce" Shiru ya yi sannan ya ce "Kin san kece sanadin ciwon ɗan uwanki?" "Ni kuma? Meyasa na zama sanadi?" "Saboda kece wadda yake so kuma ya kasa furta mata" Cikin tsananin tashin hankali ta miƙe tsaye, ta kai dubanta ga Faruq ta ga ya sauke kai ƙasa. *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._* *_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_* Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* lLITTAFAN SUNE: 1-WUTAR ƘAIƘAYI 2-WA'ADI. 3-A CIKIN IDO.. 4-TAZARAR SO #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah [6/16, 8:51 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@sanazty_ Facebook@SaNaz Deeyah Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ _Book 1_ ```🆓Page 7``` Murmushi ta yi sannan ta kalli Dr ta ce "Ba gaskiya ya faɗa ba, ya ɓoye ne kawai dan baya so kowa ya sani" "Ba mu kiraki nan dan mu yi drama ba Sadiya, tabbas ya shaida mana kece sai dai kuma ya ce ba zai iya faɗa miki ba saboda kina da aure" "Dagaske ne Faruq?" Ta furta tana kallonsa, sai dai har lokacin kanshi yana ƙasa. "Faruq ka faɗa min cewar ƙarya ne abin da kunnuwana ke ji" Hawaye ta ga sun zubo daga fuskarsa, itama sai lokacin ta ji hawaye masu zafi a kuncinta "Faruq ni?" Sai kuma ta dafe kai tare da zama a kujerar da ta tashi. Dr ya kalleta ya sake cewa "Bama so ya yi surutu da yawa, mun saka shi ya amayar da abin da ke ransa ne ko zai samu sukuni saboda ciwon yana ƙoƙarin taɓa heart ɗinsa." Miƙewa Sadiya tayi ta koma gaban Faruq "Ɗago ka kalleni Yaro" Ta furta da muryar kuka, sai dai bai ɗago ba. "Yaushe hakan ta faru? Yaro ka san ko bani da aure ko ace ni budurwa ce ai nafi ƙarfinka saboda ni yayarka ce, shekaru har uku na baka a duniya, kana yaro ni ce nake maka wanka da tsarki sannan na goyaka babu adadi a bayana, dan baka da kunya ni za ka kalla da yarana har biyu kace ni kake so?" "Namiji baya taɓa fin ƙarfin mace Aunty Sady" Sai lokacin ya yi maganar a sanyaye. "Oh haka kace, to ka sani in zaka warke daga ciwon nan ka cigaba da rayuwa ka warke in kuma son za ka cigaba to ga fili ga mai doki, ni bama zaka ƙara ganina a asibitin nan insha Allah, tunda na lura baka da hankali" Tana gama magana ta juya a fusace ta fita. Gabaɗaya juyowa sukayi kan ta suna tambayar lafiya. Ta saka hannu ta goge hawaye sannan ta kallesu "Jikin da sauƙi" "Amma shi ne kika fito kina kuka?" "Maneey ya ƙi faɗa min wadda ya...." Sai kuma tayi shiru. "Ya kuma kika yi shiru" "Ba komai Mameey, zan tafi gida" Kallonta Saddiqa tayi sannan ta ce "Haba gaskiya ba lafiya ba, kuma kin san ba zamu taɓa bari ki tafi gida a haka ba." A daddafe ta kama kujera ta zauna sai kuma ta fashe da kuka, hakan ya saka dole Mameey ta nufi ɗakin hankali a tashe. Tana shiga lokacin Doctors ɗin suna ƙoƙarin fitowa. "Yawwa Hajiya mun samu ya yi bacci, dan Allah kar a yi hayaniya da yawa" "Dr dan Allah ka faɗa min gaskiya mene ke faruwa mene ya sa kuka kira Sadiya kuma me aka faɗa mata wanda ya ɗaga hankalinta har haka" "Babu komai kawai ya buƙaci ganinta ne, ita kuma tana shigowa ta fara kuka" Bata gamsu da abin da suka faɗa ba amma ba ta so ta yi musu dasu shiyasa kawai ta ƙyale. Ko da suka shigo Sadiya bata fi mintuna ashirin ba ta tafi gida. A gida ma kukan tasha ta godewa Allah, Yazid ya yi juyin duniya amma taƙi faɗa masa abin da ke faruwa, ta yi alqawarin barin abin a ranta har abada. _Bayan Sati Ɗaya_ Tana zaune da yamma a tsakar gida tana gyarawa Ihsan gashi sai ga kiran Saddiqa. "Yanzu nake maganarki a raina" "Hmm! Baki da kirki Sadiya" "Me kuma na yi?" "Ai kin fi kowa sani, yanzu Sadiya na faɗa miki yau jirgin su Faruq zai tashi amma Sadiya tun lokacin nan baki sake dawowa asibiti ba, kuma ai kin zo ma kuyi sallama ko" "Wai yau ne?" "Ban sani ba, kar ki raina min hankali mana, ko jiya na faɗa miki kuma tun ana processing ai na faɗa miki" "Afuwan Saddiqa ni kam sai ana mini uzuri" "Kin kyauta ai" Ƙit ta kashe, Sadiya da sauri ta bita sai dai bata ɗaga ba, ta sake kiranta sai taga ta yanke kiran, har ta ji ba daɗi sai kuma ga Saddiqa ta biyota. "Dan Allah kuyi min afuwa ba zan samu damar zuwa ba, Allah ya sawwaqe ya ba shi lafiya" "Amin amma dama ai kin makara dan sai da jirginsu ya tashi sannan muka juyo yanzu haka zan mayar da su Mameey gida ne kuma kafin na wuce zan biyo ta gidan naki" "To sai kin zo" Tana kashewa ta sauke ajiyar zuciya. "Faruq kenan! Allah ya baka lafiya amma ka ɗauko dala ba gammo." Ɗan maƙotansu ne ya shigo sai daya gaishe ta sannan ya ce "Sallama ake a waje" "Kace musu baya nan" "Ance dake ake sallama" "Ni kuma? Su waye?" Sai kuma ta sake kallon yaron "Kace ina zuwa" Tana gama faɗa ta miƙe. "Ihsan ɗina ki zauna ina zuwa kinji" Yarinyar ta gyaɗa kai ita kuma ta ja hijab a igiya ta zura sannan ta fita. Tun da Affan ya ƙyalla ido ya ga fitowarta gabansa ke faɗuwa, domin har yanayin tafiyarta sai ya ga kamar Nashwa ce. Ita kuwa mamaki kawai take tana tunanin ko wani ne a dangin Mameey ko Abba yazo ganinta, dan ta san sune masu ƙunbar susa. Sai dai tana ƙarasawa ta ga Lawisa sai taji gabanta ya yanke ya faɗi, ta ji kamar ta juya amma kawai ta dake. "Assalamu alaikum" "Wa alaikumussalam" Ya amsa ita kuma Lawisa ta ce "Kiyi haƙuri amma Yayana ya matsa sai na kawo shi gare ki" "Amma...." "Ya sani na faɗa masa ke matar aure ce kuma ba Nashwa bace" "Ina wuni" Sadiya ta furta tana kallon Affan. Yayinda shi kuma ya juya yana kallon Lawisa da mamaki, dan bata faɗa masa Sadiya na da aure ba. "Ta ce min shekara guda da faruwar abin ko?" Kai ya ɗaga dan ya kasa cewa komai. "Allah sarki, ni kum ka ga shekarata 6 da aure ina da yara biyu. Ina maka jaje Allah yajiƙanta da rahama ya baka madadinta." "Amma kamarku ta ɓaci, sai dai ita Nashwa tana da fashin goshi kuma tana da ƙullar hanci, da ace bata dasu kece mai su da sai na ce kece Nashwa, kin yi ɓula da fashin goshi ne dan kiyi ɓadda kama" "Allah sarki, ai da sisternka ta nuna min naga muna yanayi sai dai ta fini kyau" Murmushi ya yi wanda sai a lokacin ne ya yi. "Amma ni har yanzu tunani nake ko dai kuna da alaqa ko kuma 'yan biyu ne" Dariya tayi ta saka hannu ta rufe baki. "Sai dai alaqa amma ni kam ni ɗaya ce" "Yaya ina zuwa bari na amsa waya" Lawisa ta faɗa gami da barin wurin. Shi kuma ya mayar da kallonsa ga Sadiya "Komai naku iri ɗaya har murmushin ku" "Dan dai muna kama shiyasa kake ganin kamar haka" "Kin san Allah lokacin da kika fito sai dana ji faɗuwar gaba na kuma shagala da kallonki astagfirulla ke matar aure ce amma fitowarki idanuwana Nashwa kawai suke nuna min." "Lallai kana ji da Nashwa zan so na ji labarinta" "Idan har mijinki ya amince zan sake dawowa har gida ko kuma ki bani numberki zan baki labarin tun daga haɗuwarmu har zuwa rasuwarta" "Allah sarki, to bari na karɓi numberka, idan yaso in ya bani dama sai na kiraka" "To shi kenan" Miƙa masa waya tayi sai dai ɗaga idon da za tayi taga Umma da yaranta sun fito daga napep. Ji tayi gabanta ya faɗi saboda irin kallon da taga suna yi mata, yana bata wayar daidai lokacin Fatima da Maryam suka ƙaraso. "Allah ya toni asirinki dai" Fatima ta faɗa tana watsa mata kallon banza. "Da mijinki amma kina bin wasu mazan to wallahi kamar kinyi a gaban Yaya" Maryam ta faɗa, shi kuma ya kalli Maryam ɗin rai a ɓace ya ce "Ke ki iya bakinki" "Idan taƙi fa?" Cewar Fatima. "Duka zan mata kuma in saka a rufe min ita" Shiru Fatima tayi, ita kuma Maryam tayi ƙwafa sannan ta ce "Za ki gane kurenki" Tana gama maganar ta juya Fatima ta rufa mata baya, dama mai napep ɗin bai tafi ba, ganin har Umma ta shiga ya saka Sadiya saurin juyawa ta ƙarasa da sauri. "Umma ina wuni" "Ka da ki sake kirana da Umma dan ni babu karuwa a 'ya'yana" Ji tayi hawaye ya zubo mata, ta ce "Umma wallahi yadda kike tunani ba haka bane" "Kaga mai adaidaita mayar damu inda ka ɗauko mu" "Umma dan Allah..." Ganin mai adaidaita ya tayar yana neman kassarata saboda ta riƙe ƙarfen machine ɗin ya saka ta saki, suka ja suka wuce, hannu ta saka tana goge hawaye a daidai lokacin Affan ya ƙaraso gabanta. "Dan Allah ku tafi kar ku ja min matsala" Ta furta lokacin wasu hawayen suks ƙara cika kwarmin idanuwanta. "Su waye wannan?" "Surukata ce da ƙannen mijina" Ta faɗa a lokacin ta ji wasu sabbin hawaye. "Yaya lafiya?" Lawisa ta faɗa tana ƙarasowa wurin, ta kalli Sadiya ta ce "Mene yake faruwa ya naga tana kuka?" "Mother Inlaw ɗin ta ne tazo suka mana tijara" "To akan me?" "I don't know" Murmushin ƙarfin hali Sadiya ta yi kafin ta ce "Kin ga Sister nagode sosai amma dan Allah ku tafi, nima yanzu na bar yarinya ita kaɗai a gida" "Ai ba zamu barki a wannan yanayin ba" "Idan baku barni ba, zai iya jawo min matsala dan Allah" Ta ƙarasa tana haɗe hannayenta . "Yaya muje" Lawisa ta furta tana kallonsa, shi kuma yayiwa Sadiya ƙyar. "Mu tafi mu barta in this situation?" "Kar ka damu Yaya muje kawai" Sadiya dai da sauri ta juya ta shiga gida Affan kuma ya sauke ajiyar zuciya. Tana shiga ta zauna tare da dafe goshi, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya tare da kafe guri ɗaya da ido. ***** ***** "Amma kina ganin hakan ba zai ja mata matsala ba?" "To ban dai sani ba amma bana fatan haka" "Dole zan ƙara bibiya daga baya inji, Lawisa nagode kin bani madadin Nashwa duk da ta kasance matar aure amma zan yi ƙoƙarin kyautatawa yaranta ko dan Nashwa" "Yaya kana son Nashwa da yawa, Allah dai ya gafarta mata" "Amin ya rabbi, me sunan yaran kuma shekara nawa?" "E to! Ƙaramar dai bata wuce 3yrs ba babbar kuma ban taɓa ganinta ba." "It's ok. Amma dai kamar suna fama da matsin rayuwa" "Kuma fa a hakan gidansu ba laifi suna da hali amma ta auri talaka, a yadda aka bani labari ma ance mamanta har yau bata son auren" "To ke ina ruwanki da jin gulma, tunda dai tana son mijinta kuma suna zaune lafiya ki barsu abin su." Murmushi ta yi bata ƙara cewa komai ba har suka isa gida. "Ya naga kun dawo cikin fara'a Affan kayi kyau sosai ka warware" Ɗan sosa kai ya yi sanan ya zauna kujera. "Mommy albishirinki" "Goro" "Mommy naga mai kama da Nashwa sosai Mommy kamar ta ɓaci" "Mai kama da Nashwa fa kace?" "Mommy dagaske bari ki ga hotonta" Lawisa ta faɗa tana buɗe wayarta. Shi kuma Affan murmushi kawai yake. Lawisa ta miƙawa Mommy wayar, ta kalla sannan ta ce "Lallai suna fuzgen kama sai dai wannan ta ɗan fi Nashwa duhu" "Ni kaina dana ganta nayi tunanin Nashwa ce Mommy" "Allah sarki, ita mene sunanta kuma ɗiyar waye?" Lawisa ta kalli Affan shi kuma ya ɗan gyara murya sannan ya ce "Sunanta Sadiya amma bamu gama sanin komai a kanta ba" "Allah ya sa tagari ce" Da ƙyar suka iya furta amin. Miƙewa Affan ya yi ya wuce bedroom ɗinsa, da sauri Lawisa ta bi shi. "No matter what karki yarda Mommy ta san yarinyar nan tana da aure" "Meyasa?" "Saboda za ta fara nasiha kuma zata haramta min taimakon da nake son yi" Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce "To shikenan" Sai kuma ta juya ta bar ɗakin. ***** ***** "What!? To ke wane tsautsayi ne ya saka kika fita" "Wallahi Aunty Saddiqa kawai ni ban ma sani ba" "Yanzu mararsa mutuncin Allah kaɗai ya san yadda za su ƙara rura abin dan ma shi Yazid ɗin ya yarda dake" "Wallahi na yi dana sanin fita, nifa har yanzu jikina tsuma yake." "Ki kwantar da hankalinki insha Allah ba abinda zai faru" "Allah yasa, hala shi ne abinda ya hanaki zuwa airport?" Ganin ta samu mafaka ta ce "E shi ne, tun ɗazu ina zaune na kasa sukuni" "Aikuwa Faruq yana ta maganarki kamar ma kece favorite sister'n Faruq, har jirginsu zai tashi sai ya ce min in kula dake tausayi kike ba shi" Iska ta furzar sannan ta kalli Saddiqa ta ce "Allah ya ba shi lafiya" "Amin, and ya bani letter ya ce dan Allah kar na karanta, da Auta za ta karɓa tun a asibiti sai ya ce a'a shi ya san idan ya bawa Auta sai ta buɗa" Murmushi Sadiya ta yi tare da faɗin "Auta anji jiki" "Wai ina Najma ne sai Ihsan na gani tana wasa" "Sai 6 za ta dawo daga islamiyya" Sadiya ta faɗa tana karɓar letter da Saddiqa ta fito daga jaka. Saddiqa ta ɗan taɓe baki ta ce "Wai Yazid ƙiri-ƙiri yaƙi yarda na riƙe Ihsan fisabilillahi ya yi adalci kenan?" "Kin san Yazid akwai ƙwalafacin 'ya'ya kiyi masa uzuri" "Uhmmm "Kiyi haƙuri Aunty Saddiqa zan ƙoƙarin fahimtar da shi ko Ihsan ɗin ya baki" "Allah ya sa, kin ga bari na tashi na tafi" "Tun yanzu?" "To yaushe kike so na tafi" "Bayan isha'i in mun gama hira" "Ai ban tambaya ba da nayi miki zaman" Murmushi kawai tayi. *_09:30pm_* Har ta fara bacci dan tuni ta yi wa yara shimfiɗa itama ta yi, jin alamun shigowarsa ya saka ta buɗe ido tare da kunna hasken fitilar wayarta. A hankali ta miƙe sannan ta fita tsakar gidan, lokacin shi kuma yana ƙoƙarin shiga ɗayan ɗakin. "Abban yara ka shigo" "E" Ya amsa a gajarce sannan ya shige, ita kuma da sauri ta mara masa baya, yana ƙoƙarin cire kaya ta shiga. "Yau ka yi nisan kiwo" Bai tanka ta ba ta ƙara da cewa "Kodai na ɗora ruwan zafi kayi wankan dan naga kamar ana ɗan sanyi" "Ban saka ki ba" Sai a lokacin ta fahimci ransa a ɓace yake. Tana zaune har ya yi wanka ya fito, ya fara shiryawa ta tashi da nufin ta taimaka masa kamar yadda suka saba amma sai ya dakatar da ita. "Abban yara lafiya kuwa?" "Babu komai" Shiru ta ɗan yi tana daga tsaye ya zira jallabiya yana ƙoƙarin kwanciya ta ce "Abinci fa?" "Na ƙoshi" "Amma me ka ci da har zai ƙosar da kai?" "Sadiya dan Allah ki bar ni na huta a gajiye nake, ki tashi ki fita a ɗakin nan" "Abban yara yau ni kake kora?" Zaune ya miƙe sannan ya ce "I need privacy! Stay away from me please" Ɗan zaro ido ta yi har sai da ta gigice ta rasa ina ce ƙofar fita, kafin daga bisani ta gano ta, ta tsaya jikin ƙofar ɗakin tana sake kallon shi kafin ta fice. Ranar bata iya bacci ba, duk da ta dawo ɗakin ta tarar da shi ya yi bacci abinsa kuma baccin ma ya yi nisa, ta san halinsa sarai damuwa hana shi bacci take, wannan dalilin ne ya saka ta san lallai ƙila ya huce, sai dai tonowa da zuwan su Lawisa ya saka ta faɗa sabuwar damuwa domin tunaninta gabaɗaya ya karkata akan Umma ta kirashi ta sanar da shi. Daren ranar dai haka ta ɓata shi ta saƙa wannan ta kunce wancan. Tunda aka fara kiran asuba take ta son ta ji motsinsa amma bata ji ba, dan haka ta miƙe ta fita ta yi brush ta yi alwallah sannan ta je ɗakinsa. A zaune ta tarar da shi yana miƙa da alamu lokacin ya tashi daga bacci. "Ka tashi kenan, nazo na tashe ka ne dama dan ban ji motsinka ba" Da ido ya bita, ita kuma a sanyaye ta juya ta fita. Kwana uku ya jera yana wannan sabuwar ɗabi'a ta rasa gane kan gadonsa, idan ya fita da safe baya dawowa gidan sai sun fara bacci. Yau dai ta saka a ranta za ta masa magana ta ji laifin da tayi masa, ta zauna batayi bacci ba har ya dawo duk da ko da tayi bacci idan taji shigowarsa sai ta farka. Tana jin shigowarsa amma batayi yunƙurin tashi ba, tana ji ya fito ya ɗiba ruwa ya yi wanka ya gama shiri tsab sannan ta tashi ta nufi ɗakin nasa. Ko da ta shiga waya ta tarar yana yi duk da wayar tasa ta ga yana yi ne da ɓacin rai, tana shiga ya kashe. Ta ajiye flask da plate a gabansa. "Abban yara sannu da zuwa" Ta furta tana ƙoƙarin buɗe flask ɗin. "Bana buƙatar abinci." Cak ta tsaya, sai kuma daga baya ta janye flask ɗin a sanyaye. "Dama ina son magana da kai ne" "Sadiya na dawo a gajiye ina buƙatar na huta" "Dan Allah Abban yara kayi haƙuri ka faɗa min laifina, wannan hukuncin ya yi min tsauri da yawa" "Laifin me?" "Abban yara wallahi na tuba ka rufa min asiri da wanne zanji? Ka ƙaurace min, ka kuma ƙauracewa yaranka idan laifi na yi ya kamata ka faɗa min sai na gyara amma wannan hukunci ya yi min tsauri na kasa jurewa." Ta furta tana share hawayen da suka zuba mata. "Sadiya" Ya furta a tausashe, kallonshi ta yi sai kuma tayi ƙasa da kai. Hannu ya saka cikin aljihunsa ya fito da takarsar ya ce "Waye ya baki wannan?" Gabanta ya faɗi ta ƙurawa takardar ido. *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._* *_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_* Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* lLITTAFAN SUNE: 1-WUTAR ƘAIƘAYI 2-WA'ADI. 3-A CIKIN IDO.. 4-TAZARAR SO #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah [6/18, 1:56 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@sanazty _Facebook@SaNaz Deeyah_ Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ _Book 1_ ```🆓Page 8``` "Tambayarki nake?" Ya ƙara maimaitawa. Jikinta a sanyaye laɓɓanta sun yi nauyi ta kasa ɗaga su bare har ta faɗa masa. "Umma ta kirani tayi faɗa sosai akan ta ganki a ƙofar gidan nan da wani namiji da bata san shi a danginki ba, kuna hira sai dariya kike; ta ce min tana kallo kika ba shi wayarki ya saka miki numbersa, Sadiya lokacin da aka faɗa min na rasa wane tunani zan yi, na san ba za ki ci amanata ba kuma Umma ba zata min ƙarya ba, to waye zan yarda da shi, da wannan tunanin na dawo gida, na kwanta kenan na ji kamar takarda a ƙasan fulo ina ɗagowa naga ita ce, na kuma duba naga kalaman soyayya ne kuma har yana cewa har abada ba zai daina sonki ba kuma zai jiraki tsawon rayuwarsa, idan kuma ance ya mutu to soyayyarki ce ta yi ajalinsa, Sadiya na san kin ajiye a ɗakin nan ne dan na gani kuma na gani na ɗauka, kullum sai na karanta kuma a halin yanzu na gama haddaceta, hatta inda aka saka comma da fullstop ina iya gane gurin komai yana cikin ƙwaƙwalwata, Sadiya dama bakya sona?" A hankali ta ɗago idanuwanta, hawaye sun mata sharkaf a fuska ta kalleshi, shima ita yake kallo. "Ban taɓa haɗa soyayyarki da wata 'ya mace ba, na jure baƙin ciki da takaici dominki, na ji a raina iya wuya zan zauna dake, Sadiya babu abinda ba a faɗa min ba a kanki har a gabanki ana faɗa cewa ke mai farar ƙafa ce, Umma da 'yan uwana tunani suke aurenki shi ne ya ruguza ni amma duk abin da ake faɗa shanyewa nake, sai gashi kin min sakayya da wannan." "Wallahi yadda kake tunani ba haka bane Abban yara" "To ya ya ne?" Hannu ta saka tana goge hawaye duk da bai bar zuba ba sannan ta ce "Ina zaune ina gyarawa Ihsan kai kawai sai aka yi sallama a waje, har ma na ce a shigo sai yaron da aka aiko ya ce maza ne shi ne na fita, sai kuma naga wannan Lawisar ce wadda tazo gidan nan har ta ce ina kama da matar wan ta, tare da shi suka zo, wallahi ba dan ina so ba na tsaya ka san wulaƙanci ba halayya ta bane, ba zan ƙaryata Umma ba amma har na gama magana dasu ban wani saki jiki ba, ita kuma number roƙota ya yi akan na ba shi tawa saboda yana so yaja yarana a jiki sai na ce masa ba zai yuwu ba saboda ni matar aure ce amma zan karɓi tashi idan ka bani izni sai na kirawo shi duk da na san ba mai wuyuwa bane tunda babu wani alaqa ta jini, zan ɗauko maka wayata ma ka duba, wallahi ka tambayi su Shamsu mai wanki sun ganmu a tsaya dani da shi da ƙanwarsa ne, sai dai a lokacin da Umma tazo ƙanwar ta tafi amsa waya." Ta saka hannu tana share hawayen da ya mata sharkaf a fuska sannan ta dube shi. "Ita kuma takardar bata da alaqa da su, ranar da Faruq ya bar ƙasar ranar ne suka zo kuma a ranar ne Aunty Saddiqa ta kawo min takardar kuma wallahi ko ita bata san mene a ciki ba, sannan babu wanda ya san abin da ke faruwa, ada na yi niyyar na ɓoyewa na barwa zuciyata amma a yanzu zan sanar maka komai." Ta numfasa sannan ta ce "Ciwon da Faruq yake fama da shi to so ne ya jawo masa, ni da Saddiqa har da Surayya mun yi ƙoƙarin ya sanar mana ko wace ce amma yaƙi faɗa, dama dai Faruq yana da zurfin ciki kuma yana da kafiya, tun abin bai yi ƙarfi ba har ya yi yazo ya fara taɓa zuciyarshi, wata rana naje asibiti sai aka fito da kowa waje dan a duba shi amma ni kuma sai Dr ya kirani, Likita da kansa ya sanar min cewa ni ce na jefa Faruq a wannan halin, ya kamu da sona kuma gashi na masa nisa saboda ina da aure" Jin haka ya saka Yazid miƙewa tsaye, ita kuma ta ja numfashi sannan ta cigaba da cewa "Ban bar ɗakin ba sai dana masa gargaɗi idan ma ya haukace ya dawo daidai, bayan yara biyu da nake dasu na bawa Faruq shekara uku har da watanni a duniya, ko Surayya cewa tayi ya mata yaro da aure bare ni, na faɗa masa cewar ko bani da aure ai nafi ƙarfinsa, na sanar da shi cewa muddin bai janye ba to zai kashe kansa a banza. Tun daga ranar ban sake komawa asibiti ba, ko kai nan kasha ƙwawar naje amma sai na goce, ciwon nasa ya yi tsanani shi ne aka tafi da shi Germany to ranar a airport ya bawa Saddiqa wannan ta kawo min, idan baka yarda ba ka tambayeta, wallahi Yazid ko da wasa ban taɓa tunanin cin amanarka ba, amma sai ga shi kana zargina har da ƙaurace min." Miƙewa tayi wannan karon bata yi yunƙurin goge hawayen ba ta fice da sauri. Tana shiga ɗaki ta fashe da kuka a fili, Najma da Ihsan duk suka farka, aikuwa Najma ta hau kukan itama, ya shigo ɗakin a sanyaye ya hau kan katifar. "Haba Sadiya ya za ki ɗagawa yara hankali a daren nan?" Bata tanka masa ba sai dai ta daina kukan a fili sai shashsheƙa, ya janye Najma a jikinta ya ce "To yi shiru mana mene na kuka, itama Mommy ta daina, kwanta kiyi bacci abinki" Janyewa tayi ta sake komawa jikin Sadiya ta kwanta, haka Ihsan ma, shi kuma a hankali yake ɗan shafa bayan Najma har ya samu tayi bacci, dan Najma ta fi Ihsan rigima da ƙwalafacin uwa. Yana ganin sun yi bacci ya dubeta, ya ga fuskarta har ya ɗan kumbura saboda kuka. "Sadyna ki kwanta kiyi bacci" "Ba na ji" Ta furta da muryarta wadda da ƙyar ta fita saboda ta dashe. "Dan Allah kiyi haƙuri na san ban kyauta ba dana kasa tsayawa na bincika amma ki bari da safe mu yi maganar." "Abban yara wallahi bana jin bacci kawai kaje ka kwanta" "Ba zan iya kwanciya na barki a damuwa ba, please Babyna" Ya faɗa yana komawa gabanta sannan ya miƙar da ita, ya ja ta ɗakinshi. Suna shiga ta fashe da sabon kuka, a hankali ya rungumeta yana rarrashin abarsa da ƙyar ya shawo kanta ta samu tayi bacci, shi kuma ya ƙura mata idanu cike da tausayawa. "Tabbas na miki bahaguwar fahimta, ki gafarce ni hubbyna" Ya daɗe a zaune kafin daga bisani bacci ya ɗauke shi. ****** ****** Sai da ta gama duba kayan sannan ta kalleshi da murmushi. "Sun yi kyau amma fa Yaya ina tsoron mijinta kar ya mana tijara" "Kina ganin har sai ya yi haka duk da yaransa na kyautatawa?" "Talaka fa faɗin rai ne da shi, kuma ka ga wannan atampopin da wannan lace ɗin zai ga a wane dalili zaka sayawa matarsa" "A dalilin Nashwa, na taɓa saya mata kuma ta ɗinka na ganta dasu" "Yaya wannan ba Nashwa bace kuma...." "Stop it da Allah!" Ya dakatar da ita da tsawa. A tsorace take kallonsa kafin ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. "Lawisa kiyi abin da na saka ki" "Allah ya huci zuciyarka Yaya" "Amin" Ya furta tare da barin ɗakin ita kuma da ido kawai ta bi shi. Yana fita parlour ya tarar da Mommy zaune tana waya, ya samu ɗaya daga kujerun ɗakin ya zauna sannan ya kalli Mommy, yana jin yadda take wayar ya san maganarsa ake, har sai da suka gama sannan ta kalleshi. "Affan ya dai? Na ga baka cikin walwala" "Mommy akwai abin da ke damuna" "Wane abu ne?" "Mommy wannan mai kama da Nashwa dana faɗa miki" "E, me tayi?" "Ba komai kawai dai har yanzu ina ji a jikina kamar Nashwa ce Allah ya dawo min da ita." "Na yi tunanin har kun daidaita ai, yanzu muke waya da Hajiya Bilkisu ta ce min kaje ka ga 'yarta ko zaku daidaita, to kuma sai na ce mata akwai wadda kake so amma ban san ya ake ciki ba zan yi magana da kai." "Mommy ni gaskiya babu wurin wadda zan je, kawai dai ace ta yi haƙuri" "Ta faɗa min yarinyar za ta zo nan gobe, so ina so in san idan kun daidaita da ita wadda kake cewa tana kama da Nashwa" "Ba mu daidaita ba, sai kin bani lokaci Mommy" "To Affan Allah ubangiji ya tabbatar mana da alkhairi" "Amin Mommy." ****** ****** "Ki ajiye wanki nan Sadiya kin ga dai kin yi da yawa ki bari na ƙarasa sauran sai kiyi shanya" Murmushi ta yi sannan ta ce "Abban yara kenan, tunda dai ka dage bari na je na ɗora girki" "To ai dama wanki na namiji ne kuma kin san ko ba wanki ba ai sunnah ne miji ya taya matarsa aiki." "Ga matar da ta shanye miji ba!" Da kakkausar murya suka ji maganar wanda maganar ita ce sallamarta. "Yakumbo Bahijja sannu da zuwa" "Kai dalla rufa min baki lusarin namiji kawai" Ta faɗa tana ƙara shigowa cikin tsakar gidan. "Yakumbo ina yini" "Idan ban yini ba za ki ganni ne? Munafukar mace" Wani yawu mai ɗaci Sadiya ta haɗiya sannan ta sauke kai ƙasa. "Ka zo ka saki baki kana washe wa mace baki kana mata aikin gida. Wai ba a faɗa maka abin da wannan matar tayi ba, ta tsaya da kwarto a ƙofar gidanka amma ban ga alamun ka ɗauki wani mataki ba." "Yakumbo wallahi yadda kuke tunani ba haka bane" "Oh baka yarda kwartuwa bace fasiƙa?" Ɗago ido Sadiya ta yi har sun kaɗa sun yi jajir ta kalleta. "Kika ƙura min ido kamar mayya ko za ki dake ni ne?" Da sauri ta miƙe ta shige ɗaki tana gunjin kuka. "Ga mahauƙaciya tana magana ko, shi ne ta wuce ta barni anan tsaye." "Yakum....." "Ka rufa min baki Yazid wallahi ka bani mamaki, zuwa na yi yanzu a gabana ka danƙarawa matar nan saki kafin ranka ya yi mummunan ɓaci" Kallon ƙofar ɗakin ya yi sannan ya juyo ya kalli Yakumbo Bahijja. "Sadiya baiwar Allah ce, duk yadda kuke tunani ba haka bane." Sallamar yaro ne ya dakatar dasu duk suka kalli ƙofar. "Ana sallama da Sadiya" Yaron ya faɗa. "Inji wa?" Cewar Yakumbo. "Wani ne a mota" "Ka gani ko? Kwarton ya ƙaraso kenan" Ta kalli yaron ta ce "Kace tana zuwa" Yakumbo Bahijja ta faɗa. Sai da yaron ya fita sannan ta kalleshi ta ce "Sai ka kirata muje mu ƙure ƙaryarta ko" Shiru ya yi bai ce komai ba. "Magana nake maka ko baka ji na ne" Jiki a sanyaye ya juya ya shiga ɗakin. "Sadiya" Ya ambaci sunan tare da zama gefen gadon. Bata amsa masa ba sai dai hannu da ta saka tana goge hawaye wasu na sake zubowa. "Sadiya kin yi da wani ne zai zo a gidan nan ko a family ɗinku?" Kai ta girgiza alamar a'a. "To waye kike tunanin ya zo gurinki?" Bata ba shi amsa ba dan bakinta ya mata nauyi ba zata iya furta ko kalma ɗaya ba. "Yakumbo ta ce ki fito muje, amma ina so na san waye kafin muje" Kawai gani suka yi ta ɗaga labule. "Malamai jiranku nake, ke ki tashi ki ɗauki hijab ɗinki." Sam bata basu damar magana ba har Sadiya ta ɗauki hijab ta zura suka fita. Tana fita gabanta ya yi mummunan faɗuwa ganin Affan tsaye jikin mota. "Ka gani ko?" Yakumbo ta faɗa da ɓacin rai sannan ta fuzgi hannun Sadiya da ƙarfi ta ƙarasa gaban Affan. "Kai ne ka zo nemanta?" "E, amma nazo gurin yar...." "Dakata Malam, kai baka kunyar kwartanci da rana tsaka?" Buɗe baki ya yi yana kallonta. "Ko bata faɗa maka ita ɗin matar aure bace, ko dan irinku masu hannu da shuni kun fi son bin matan aure saboda shi iskancin gaba kuka ba shi." "Kin ga malama ka da ki ƙara kirana da wannan sunan domin da mutuncina da kuma kimata" "Ai ni ban gansu ba, tunda ga shi nan kana bin matar aure" "Sadiya kamar ƙanwa take a gurina, kece dai kike so ki mayar da abin wata kala" "Ƙarya kake a danginsu waye kai? Saboda ka ga mun kamaka red handed shi ne zaka fake da ƙanwa" Ta juya a fasace ta kalli Yazid. "Kai kuma me kake jira kana gani ƙaton banza da matarka sannan yana faɗa min magana son ransa amma kayi shiru ka zuba ido, ka kira a maka shege cell ya ji in fasiƙanci da matar aure abin yi ne, kuma wallahi ko baka so sai ka rabu da wannan matsiyaciyar ayau ɗin nan" Cikin ɓacin rai Affan ya fito da waya ya kira sannan ya ce yana so azo ayi arresting ɗin Yakumbo a bisa cin zarafin da tayi masa. "Ni zaka yi wa barazana, to ina nan zan ga uban da zai ɗaukeni anan" Gaba ɗaya ta tara musu 'yan unguwa, ita kuwa Sadiya ta ja hijab ɗinta tana ta kuka. Yazid ba irin haƙurin da bai bawa Yakumbo kan su koma gida amma taƙi sai ma ƙara zage-zage take tana faɗin yau ta kama kwarto kuma kowa sai ya sani, yana tsaya jikin motar ya kafeta da ido, kuma gurin kowa ya kasa tunkararsa ganin yadda yake da kuma motar daya zo da ita sun san babban mutum ne. Taku biyu ya yi ya ƙarasa gaban Sadiya, anan ran Yazid ya ɓaci sosai. "Sadiya ki koma gida saboda ke matar aure ce kina da daraja, ki barni da matar nan" "Kai Malam ya haka? Ina ruwanka? Ni ne mijinta ba kai ba" "Oh kai ne amma kuma ban ga alama ba, domin ban ga ka ɗauki hakan da daraja ba matarka a waje ana wannan hayaniyar amma ka kasa suturta ta" "Kai har ka isa ka faɗa min yadda zan yi da matata, kana da hankali kuwa?" Cikin ɓacin rai Yakumbo ta ce "Ka gani ba, matarka amma yana maka iko da ita, wannan ai shirmen banza ne." Affan bai ƙara cewa komai ba kawai ya koma jikin motarsa ya tsaya. Suna nan tsaye sai ga motar 'yan sanda, suna isowa suka ƙarasa gaban Affan. "Ga ta nan ku yi arresting ɗinta" Ya faɗa yana nuna Yakumbo, sai kuma a lokacin ido ya raina fata. "Ki shiga mota ko na shigar dake" "Idan baka san darajar mace ba sai ka shigar dani, Yazid kana gani ana ci min mutunci ko?" "Yakumbo kije kawai zan biyo bayanki" Kallon Sadiya tayi sannan ta ce "Wallahi tsanarki yanzu na fara, kuma kin gama aure a ahalinmu ni zaki saka a nuna wa arziƙi ko?" Cikin ɓacin rai ta shiga bayan motar suka ja. A fusace Yazid ya juyo ya kalli Sadiya ita kuma gabanta ya sake faɗuwa taji ƙirjinta ya yi wani irin duka. "Ki wuce gida mana me kika jira" A furgice da juya ta wuce, Affan kuma da ido kawai yake bin ta yana jin da yana da iko sai ya hukunta Yazid kan tsawar da ya yiwa Sadiya. "Kai kuma kana ganin kayi amfani da kuɗi ka tozarta mu, to ka sani ni kuma wallahi sai na rama" "Ba zaka taɓa iyawa ba, baka da ƙarfin nan, sannan ni ban maka abin da zaka iya ramawa ba, kwarto ta kirani bayan ni ko ƙofar gidanka ban tsaya ba bare na shiga ciki, to ta ina na yi kwartancin kenan? Wallahi sai na ɗauki ƙwaƙwƙwaran mataki akan wannan ƙazafin" Yana gama faɗa ya shige mota ya ja rai a ɓace. Da sauri Yazid ya shiga gida. Tun daga zaure yake kwaɗawa Sadiya kira har ya shiga ciki. A tsakar gidan ya tsaya yana huci, ita kuma tana zaune kan daɓe ta haɗa kai da gwiwa. "Sadiya ki ɗago ki faɗa min alaqarki da shi da har yake zuwa gidanki kai tsaye" Miƙewa tayi hawaye sharkaf a fuskarta ta ce "Yanzu Yazid har ka fara zargina?" "Zargi ko gaskiya, kina ganin tijarar da ya yi sannan kai tsaye ya turo a kiraki fa, Sadiya mene tsakaninku?" Wannan karon cikin tsaya ya yi maganar. Kuka ta ƙara saki da ƙarfi, Ihsan ta fito daga ɗaki ta ƙarasa gabanta. "Mommy wane ya dokeki?" Rungume Ihsan ta yi ta ƙara durƙushewa a wajen tana kuka. *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._* *_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_* Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* lLITTAFAN SUNE: 1-WUTAR ƘAIƘAYI 2-WA'ADI. 3-A CIKIN IDO.. 4-TAZARAR SO #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah [6/18, 1:56 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@sanazty _Facebook@SaNaz Deeyah_ Tiktok Handle: Habibtyn Habibi👸💍🦋 Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe Facebook page: https://www.facebook.com/share/16d2wDeqer/ *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ _Book 1_ ```🆓Page 9``` Rai a ɓace ya wuce ɗaki, bai daɗe ba sai gashi ya fito haka ya saka kai ya fita ya bar ta cikin tashin hankali. Tana durƙushe a ƙasa har ta yi kuka ta gama sai hawaye kawai dake fitowa jefi-jefi, maƙotanta biyu suka doka sallama. Baki kawai ta motsa dan muryarta taƙi fitowa; su ma jikinsu a sanyaye suka shigo suka zauna. "Sadiya dan Allah kiyi haƙuri" Hannu ta saka ta goge hawaye sannan ta ɗan yi murmushi wanda iyakarsa leɓe. "Sannunku da zuwa." "Yawwa, kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki." Sun mata kara sosai domin sun zauna har bayan magriba sannan suka tafi, Sadiya hankalinta a tashe yake sosai ta kasa sukuni ta kasa sakin jiki haka har aka yi isha'i tana zaune tana zulumin abinda zai je ya dawo. "Ina take algungumar" Shi ne abinda ta ji lokacin ta gama yi wa yara shimfiɗa. Fatima da Maryam ne suka shigo sai wata ƙanwar Umma mai suna Aunty Adawiyya. Sadiya na fitowa tsakar gida kawai taji an rufeta da duka ta ko ina, tun tana ƙoƙarin kare kai har ta kasa jikinta gabaɗaya sun mata lilis bakinta kuwa har ya fashe haka suka barta a kwance tana numfarfashi. Najma na gabanta tana jijjigata ita kuma Ihsan tuni ta yi bacci, tun tana iya gane abu har ta daina saboda dukan da suka yi mata. *********** "Hajiya sai dai fa ku yi haƙuri amma ba zamu iya ba da beli ba sai dai ku dawo zuwa gobe idan wanda ya shigar da ƙara ya yafe, amma ba a ba mu damar beli ba" "Officer dan Allah ku taimaka wallahi tana da larurar hawan jini" "Amma ta san da haka take rashin kunya?" "Haƙuri za kuyi dan Allah" "Gaskiya ba zai yuwu ba" Har zai ƙara magana Umma ta ce "Rabu da su Yazid, mu je kawai" Kallon Umma ya yi sannan ya ce "Yakumbo Bahijja bata da lafiya" "Yazid zama anan ƙarin cin mutunci da ƙasƙanci zai ja mana, saboda talaka ba su ɗauke shi a bakin komai ba" Kallon ɗan sanda ya yi sannan ya juya kawai ya fita rai a ɓace Umma ta mara masa baya. "Yazid!" Ya ji ta kira sunansa dan haka ya tsagaita saurin da yake, ita kuma ta ƙaraso gabansa ta kalle shi sannan ta ɗan kauda kai. "Ka haƙura da wannan yarinyar indai ba da gwal aka ƙerata ba, kai ko gwal ce ita ai babu amfanin tarayya da abin da zai cutar da kai." "Umma ba laifin Sadiya bane, saboda ni ban ga alamun ta san shi ba." "Yazid na tabbatar da ta san shi dan ni na ga hakan da idona ba labari aka bani ba." "Umma maganar ba ta nan ba ce, mu samu mu fitar da Yakumbo dai tukun." ****** ****** Yawo yake a tsakar ɗakin kafin ya juyo ya kalli Lawisa dake zaune kan sofa. "Shiyasa na ce miki muje tare saboda bana so a samu matsala amma sai kika kawo min wani banzan uzurinki." "Yaya ka yi haƙuri dan Allah wallahi ni da na san haka za ta faru da da kaina zan karɓa na kai." "Hmmm! Ban taɓa ganin saunan miji kamar nata ba, wallahi darajar aure kaɗai ya saka ban wanka mishi mari ba, saboda idan na mare shi abin kan ta zai koma." Ɗan zaro ido tayi sannan ta ce "To alhamdulillah tunda baka yi marin ba, amma fa wallahi da mun shiga uku, so kake ya fassaraka?" "Na nawa kuma, ai sun yi kuma sai na shiga kotu da ita" "Yaya Affan abi abin nan a hankali wallahi idan Mommy ta gane abin da muka aikata za a iya samun matsala" Shiru ya yi tare da zama gefen gado ya saka hannu a fuska rai ɓace. "Yaya!" Lawisa ta furta a sanyaye. Ɗago ido ya yi ya kalleta. "Ka yi haƙuri ka ba da damar a sallameta" "Ba zan iya ba, sai na ɗauki mataki, domin da kwarto ta kirani bayan ko ina saurayi ban yi ba bare yanzu" "To ni dai na gama shiri yanzu zan tafi, idan naje duk abin da ake ciki sai mu riƙa waya" "Kin dage dai amma da kin bar ni naje da kaina" "A'a duk da nan Kano ne amma za a iya samun wani wanda ƙila an masa transfer daga can yazo nan, ko kuma wani wanda ya san case ɗin ka acan Yola gara dai naje" "Har tsawon wane lokaci kuke so na ɗauka ba tare da na sake ba?" "Ko iya haka ma ai ka sake tunda kana zuwa ko ina." "Ni fa yanzu babu komai a tare dani duk wani evidence da muke da shi yana gurin Nashwa kuma sun kashe ta sun karɓe komai to kina tunanin me zan iya yanzu, amma da ace ina da hujja a kansu ko ɗaya ce wallahi da sai na tona musu asiri" "Allah ya ji ƙan Nashwa" "Amin ya rabbi." Tare suka jera suka fito, suna shirin fita Mommy ta sauko daga sama. "Ina zuwa kuma?" Gabaɗaya suka jiyo suka kalleta. "Ni fa ban gane me kuke nufi ba anya babu abinda kuke ƙullawa kullum sai na ganku tare" Murmushi Affan ya yi sannan "Mommy ko mene za a ƙulla ai za ki sani" "To ina kuma zaku tafi?" "Lawisa ce za ta fita, ni ina gida babu inda zan je" "Sabon salo ne yasa zaka rakata mota?" Sai lokacin Lawisa ta ce "Kai Mommy" "Kin ga Lawisa sai kin dawo" Ya furta yana juyawa ita kuma ta yi murmushi. "Mommy an kirani emergency call daga asibiti so zan je na ji" "Okay sai kin dawo. Kai kuma ƙaraso dama ina son magana da kai" Suna zama ta kalleshi "Affan ka daina maganar aure ko?" Ɗan murmushi ya yi sannan ya ce "Mommy ba haka bane, kece gabaɗaya kin yi min takunkumi" "Affan kenan, yanzu dai ba wannan ba, ka ga dai tunda aka ɗauke Badriyya yau ku san wata huɗu kenan babu wanda ya sake kira, ko saki ma basu nema ba to shi ne na ce me zai hana mu nemesu ka sawwaƙe mata kawai" Mommy ya ƙurawa ido dan gani yake kamar ba ita ba, bai taɓa tunanin za ta faɗi wannan maganar ba, ta cigaba da cewa "Na yi magana da ɗayar ƙawar tawa anan Kano suke zaune akwai yaranta biyu, ina so ka je ka gansu sai ka zaɓi wadda ta yi maka a ciki, sannan na yi magana da wani director abokin mahaifinku ne tun yana raye mahaifinku ya hidimta masa har ya kai wannan matsayi na Director anan wata jami'a so ya ce akwai slot da aka ba shi ya kuma saka sunanka, so at anytime za a iya nemanka" Zama ya gyara sannan ya ce "Mommy amma mene fa'idar sakin Badriyya?" "Saboda haka suke buƙata" "Mommy dan Allah kiyi haƙuri mu ɗan ƙara masu lokaci, saboda ni na san Badriyya tana sona." "So na hauka dai, duk wannan bala'in ba ita ce ta jefamu a ciki ba" "Mommy duk da haka ina neman alfarma ki bani dama na kirasu na kuma yi magana da ita kafin yanke hukunci" Shiru ta ɗanyi rai ɓace. "Please Mommy" "Na ji ba damuwa na baka dama." "Thank you Mommy" "It's okay. Yanzu dai yaushe zaka je gidan Hajiya Bilkisu" "Mommy yaushe kike so na je?" "Ko zuwa weekend jibi asabar ko kuma lahadi" "Zan je ranar Sunday insha Allah" "To shi kenan Allah ya kaimu" "Amin ya rabbi." ******** ******* A hankali ta fara buɗe idanuwanta da suka mata nauyi, kallonsu ta fara yi ɗaya bayan ɗaya, Saddiqa da Surayya ne a kanta, sai Yazid. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Ta furta hankali sannan ta kai dubanta ga hannunta da aka sakawa drip. "Sadiya sannu" Saddiqa ta faɗa, sannan ta kalli Surayya, ki kira Dr kice ta farka. Ɗan lumshe ido ta yi ta ji kanta yana juyawa sosai, sai kuma ta buɗe ta fara ƙoƙarin tashi zaune, Saddiqa ce ta taimaka ta zauna sai kuma ta fashe da kuka, a daidai lokacin kuma Surayya ta shigo tare da Dr. "Kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki." "Aunty ina su Najma?" "Suna wurin Mameey" Kallon Dr ta yi ta ce "Dan Allah Dr ka sallame ni yau." Ta sake fashewa da kuka. A kan ta ya tsaya sannan ya ce "Kar ki damu zamu baki sallama idan muka ga yanayin jikinki amma dole sai kin kwantar da hankalinki." Goshinta ya sha bandeji ga kuma gefen bakinta da ciwo. Yana gama dubata ya ce "Kiyi haƙuri zamu saka miki drip idan ya ƙare sai a sallameki" Sai daya ɗauko ruwan ya saka mata sannan ya fita. "Yazid kayi haƙuri amma zan iya samun matsala da duk wanda ya yi wa 'yar uwata wannan abin" Surayya ta yi maganar rai a ɓace. "Surry kar na ƙara jin kin yi magana" "Haba Aunty Saddiqa ki duba ki ga abin da suka mata fa, wannan wane irin abu ne, tun da Aunty Sadiya ta aure shi ba ta ƙara samun kwanciyar hankali ba." "Surayya idan kika ƙara magana wallahi sai ranki ya ɓaci" Shiru ta yi tana ƙara ɓata rai, kawai ta juya ta fita. Saddiqa ta kalleshi ta ce "Ka yi haƙuri Yazid ka san Auta sai a hankali" Murmushin yaƙe kawai ya yi tare da cewa "Babu komai." Shiru ya ɗan biyo baya ƙafin ya ce "Aunty Saddiqa ina neman alfarma" "To ina jinka" "Dama game da Yakumbo da aka kama to sun ƙi sakinta dan a station ma ta kwana, sai yau ya ce sai ta ba shi haƙuri a bisa ɓata suna da ta masa sannan ta bawa Sadiya haƙuri. To kuma ga Sadiya a kwance a asibiti shi ne na ce ko zaki saka baki su saki Yakumbo wallahi tana da hawan jini, ta ba shi haƙurin ma ya ce lallai sai Sadiya ta haƙura zai ba da damar a saketa" "Subhanallahi, waye wannan?" "Wani ne wai Sadiya na kama da tsohuwar budurwarsa." "Kuma sai me? Kama da wane ai bata wane." "To haka dai ya ce, ni dai fatana a saki Yakumbo Bahijja." "A saketa dan Allah ni dama ban ji haushin abin da ta yi min ba" Sadiya ta furta a sanyaye tana kwance a gado. Saddiqa ta kalli Yazid ta ce "Ka kira a waya zan yi magana dasu." "Nagode" Ya faɗa sannan ya kira wayar. Lawisa ce ta ɗaga suka yi magana da shi sannan ya ba Saddiqa wayar ta sanar mata da Sadiya ba lafiya amma ita kanta ba zata so a riƙe wani a dangin mijinta ko wani makusancin shi, sannan da kanta ma ta faɗa a sake ta dan haka su yi haƙuri komai ya wuce" Sai da Lawisa ta kira Affan da ƙyar ta lallaɓa ya yarda aka saki Yakumbo. _Bayan Kwana Biyu_ Har zai fita daga gida Umma ta dakatar da shi, ya tsaya yana kallonta kafin ya sadda kai ƙasa. "Yazid ko dai ka fara shan wani abu?" "Umma babu abin da nake sha" "Yakumbon ka fa tana asibiti amma kuma ka ƙi ɗaukar mataki akan abin da matarka ta saka wani banza ya mata." "Umma wallahi ni a ruɗe nake a wannan lamarin, itama Sadiya har gida aka je aka mata duka, kuma 'yan uwanta na zargin Fatima da Maryam ne, ga ta a asibiti" "Ok so kake ka faɗa min cewa ba zaka iya rabuwa da karuwar yarinyar nan ba" Ɗan lumshe ido ya yi, dan har cikin ransa sai daya ji wani iri da aka kira Sadiya da wannan suna. "Umm...." "Dakata Yazid wallahi a wannan gaɓar zan iya yin fito na fito da kai idan baka rabu da wannan yarinyar ba." "Umma zan rabu da ita amma dan Allah ki bari sai ta samu sauƙi" "Shi kenan Allah ya kaimu." Da ƙyar ya iya cewa "Amin." Yana fita kai tsaye gidan wan mahaifinsa ya nufa, wanda shi ne waliyyinsa a lokacin bikinsa da Sadiya. Ko daya je a ƙofar gida ya same shi da almajiransa. Bayan sun gaisa ya ce masa ya shiga ya gaisa da 'yan gida. Tunda ya kalli yanayinsa ya san akwai matsala dan haka yana shiga ya miƙe ya bi bayansa. Suna zaune a zaure Yazid ya zayyana masa duk irin abubuwan da suke faruwa. "Assha! Garin ya duk haka ta faru amma ba ka zo ka sanar dani ba Yazid?" "Baffa na ɗauka zan iya kashe wutar amma abin ya ci tura" "Subhanalillahi, yanzu ya jikin nata?" "Da sauƙi tunda jiya ma har tana iya cin abinci da kanta" "To Allah ya bata lafiya yasa kaffara ne, kuma insha Allah da yamma zan je na samu mahaifiyar taka, daga nan kuma zan yi ƙoƙari naje asibiti na dubata" Kai Yazid ya gyaɗa. "Dan Allah irin haka ta faru a riƙa sanar mini da wuri" "To Baffa insha Allah" Baffa da yamma kuwa ya samu Umma kamar dai yadda ya alƙawaranta kuma ya zaunar dasu tare da Yazid da ƙannen nasa. Dukkansu babu wanda ke fara'a dan sun tabbatar zuwansa ba zai zama alheri ba. "Kenan ƙarana ka kai gurinsa?" Umma ta yi maganar rai a ɓace tana kallon Yazid. "Ai ya isa ya kawo ƙarar saboda ni mai faɗa ne aji a gidan nan tun da ni wan mijinki ne" "Hmmm!" Ta sauke numfashi tana ƙara haɗe rai. Kallon Fatima da Maryam ya yi ya ce "A cikinku wace ce taje ta daki matarsa." "Baffa ƙarya take saboda mu bamu zuwa gidan sa ba dan babu abin da zamu tsinta a gidan" Maryam tayi magana rai ɓace. Hannu ya watsa mata sannan ya ce "Kin ci gidanku, gidan ɗan uwanki kike cewa babu abinda za ki tsinta" Baki ta turo bata sake cewa komai ba. "Wannan ba daidai bane, duk irin abubuwan da kuke ina sane ƙyalewa kawai na yi amma lokaci ya yi da zan ɗauki mataki akan hakan" "Baffa abubuwan sun fara yawa ita...." "Idan kika sake magana sai ranki yayi mummunan ɓaci. Ku bar yaro ya samu nutsuwa da iyalinsa." Sai lokacin Umma ta sake cewa "Ba zai yuwu mu bar yarinya tana abin da take so, dan haka dole ne ya rabu da ita ko kuma ya ƙara aure." "Idan ya ƙara auren kina ganin wadda za a kawo muku alheri zata haifar ko kuwa idan ya saki matarsa kina ganin shi ne sauƙi ko kuma jindaɗinku, mene ribarki akan haka?" "Ni kaɗai na san irin abubuwan da nake fuskanta, dan haka ni dai na ba shi zaɓi." Duk yadda Baffa yaso ya nusar da su amma suka kasa fahimta haka ya haƙura ya tafi ya ƙyalesu da mummunan ƙudurinsu. *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._* *_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_* Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* lLITTAFAN SUNE: 1-WUTAR ƘAIƘAYI 2-WA'ADI. 3-A CIKIN IDO.. 4-TAZARAR SO #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah [6/19, 8:47 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@sanazty_ _Facebook@SaNaz Deeyah_ _Tiktok@Habibtyn Habibi👸💍🦋_ Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe Facebook page: https://www.facebook.com/share/16d2wDeqer/ *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ _Book 1_ ```🆓Page 10``` Cikin nutsuwa ya fito daga mota yana ƙarewa farfajiyar gidan kallo, ko ina ya ƙayatu da flowers, ga kuma wani guri gefe guda anyi rumfar shaƙatawa. "Barka da zuwa" Ya ji siririyar murya ta sauka a dodon kunnensa, da sauri ya juya ya kai dubansa gareta. Murmushi ta yi masa sannan ta ce "Sannu da zuwa" "Yawwa" Ya furta a taƙaice. "Bismilla ka shigo" Da ido ya bita sannan ya motsa, tana gaba yana biye da ita har suka ƙarasa katafaren falon da ya gaji da haɗuwa. Kujera ta nuna masa tare da faɗin "Bari a kira Anni ɗin" "Ok" Ya furta a taƙaice tare da zama, ita kuma ta bi wata slicing door ta wuce. Ta ɗan juma a ciki sai kuma ta fito hannunta ɗauke da ƙaton tray da drinks akai sai wasu bowls ɗauke da dambun nawa ɗayan kuma cin-cin ne. Kan center table ta ajiye sannan ta ja table ɗin gabansa. "Bismilla ka taɓa kafin a kawo abinci" "Thank you" "Never mind" Ta furta tana zama a kujerar dake gefe. "Kai ne Affan Ahmad Giwa?" Murmushi ya yi yana gyaɗa kansa alamar eh. "Tun jiya Anni take faɗa mana zuwanka, barka da zuwa." "Barka dai" "Amma your face looks familiar kamar na sanka somewhere" Fitowar Haj. Bilkisu ne ya dakatar da ita, ta miƙe tsaye, ganin haka ya saka Affan miƙewa shima. Kamar bata son taka ƙasa haka take tafiya har zuwa lokacin da ta samu kujera ta zauna, Affan ya kai gwiwoyinsa ƙasa tare da gaisheta. "Affan bismillah koma kan kujera ka zauna." Zama ya yi amma ya kasa ɗago kai, gabaɗaya ji ya yi tana masa kwarjini. "Ina Farhan ne?" "Tana ɗakinta" "Kirawo ta, kice ta fito ina son ganinta" Tana knocking ta murɗa handle bata jira an mata iso ba, Farhan na kwance a gado tana kallo a system Ayda ta rungumeta "He's cute kuma handsome ne, wallahi kun dace da juna sosai." Ayda ta faɗa cike da murna. "To don't break my legs kin ga ɗagani tukun." Murmushi ta yi sannan ta ɗagata ita kuma ta gyara zama. "Har ya ƙaraso kenan." "Yeah yana parlour, kin gan shi kuwa? Wallah top class ne." "Ki daina zaƙewa da yawa saboda kin san halin yaran masu kuɗi yanzu sai ya ce kece kika masa." "Haba dai, ni ai ina da Nasir ba zan ma Nasir butulci ba amma maganar gaskiya Affan ya haɗu kuma na san ke zai zaɓa ma, kin san yaran masu kuɗi akwai son farar fata" Ta ƙarasa faɗa tana dariya, sai kuma ta saka hannu ta dafa kafaɗarta tare da cewa "Be calm, ai tun kafin yazo na ce inya miki kawai ki amsa" "Ya yi min 100/100" Murmushi Ayda ta yi tare da cewa tun ma kafin ki gan shi?" "E mana, ai na san ki kin san high and low class tun da kika ce ya yi to yes na yarda, kin ga muje dai kar Anni ta fara faɗa." Miƙewa suka yi cikin fara'a suka fita, sai dai suna fita Farhan ta haɗe rai, "Anni barka da gida" Ta faɗa tare da zama. Farhan ita ce babba tana da shekaru 23 fara ce sol dan farin ta har ɗaukar ido yake, tana da kyau daidai misali, dan tana da sexy eyes ɗin da sune suke ƙara mata kyau, ta yi karatun ta har matakinn master a ƙasar china inda yanzu take aiki da wani company na sufuri. Yayinda Ayda ta kasance ruwan tarwaɗa, sai dai kuma fannin kyau Ayda ta fi Farhan kyau, saboda ita yanayinta ya yi kama da shuwa arab ga kuma ɗan duhun fata da take da shi, shi ne ya ƙara fito da kyawun na ta, tana da manyan idanu, dogon hanci da ƙaramin baki, itama a U.S ta yi karatunta har matakin degree, sai dai yanzu tana masters anan B.U.K tana da iyeyi sai dai bata da wulaƙanta mutum dan ko baƙi a gidan itace mai tarba. "Baki gaishe da Affan ba ko baki gan shi ba ne" Ɗan ɗago kai ta yi ta kalleshi a ranta ta furta _Wow_ a fili kuma a yatsine ta ce "Ina wuni" Kamar kar ya amsa haka ya ji, amma ya daure ya ce "Lafiya lau." Haj. Bilkisu ta yi murmushi tare da cewa "Affan wannan sune ƙannen naka, wannan ita ce Farida muna kiranda da Farhan ita kuma wannan ita ce Aisha muna kiranta da Ayda. Farhan ta gama karatu a yanzu haka aiki take, ita kuma Ayda tana kan karatun dan shekara ta ƙarshe take a masters, project take ta fama da shi a yanzu." Murmushi ya yi sannan ya kallesu "Allah ya taimaka." "Amin" Ayda ta amsa. Haj. Bilkisu ta ce "Shi kuma Affan dama na yi muku bayani akan sa ko? Kun san waye shi da komai na faɗa muku jiya" "E Anni mun sani." Cewar Ayda ita kuwa Farhan sai ƙara shan ƙamshi take. "Bari na barku da shi sai ku samu tattaunawa kuna 'yan uwa amma babu zumunci ko, Affan ai kamata ya yi ku taho da Lawisa" Murmushi ya sake yi sannan ya ce "Ta je aiki amma next time insha Allah" "To babu damuwa." Suna ta hira da Ayda yayinda Farhan tana ji amma ta yi pretending tana danna waya ita a dole sai ta ja ajinta. Anan ya bawa Ayda labarin Nashwa da dalilin ajiye aikinsa sai dai yanzu ya samu lecturing a northwest university. "I wish a B.U.K ne, ka ga na san zamu riƙa haɗuwa" "Yeah da a B.U.K so shi bai samu ba" "Eyyah! Ban ji daɗi ba." Sai lokacin Farhat ta ɗago suka haɗa ido da Ayda ta ɗan ƙyafta mata ido. "Farhan muna ta hira kin yi shiru" "Yeah am busy doing something, kuma it's very important so kin ga ba zan tsaya hira ba" Murmushi Affan ya yi dan ya san ɗagawa ne take wanda in jan aji ne da ɗaga kai bata kai shi ba, amma tun lokacin daya auri Badriyya ya watsar da makaman yaƙi, bala'i da baƙin kishinta sai da suka canja masa rayuwa. Da zai tafi kuwa tun a parlourn ya karɓi number Ayda, Farhan na jira ya ce mata ta bashi ta ta saboda ta ji ya ce zai karɓi number dan a ƙara sabawa da juna amma sai kawai gani ta yi ya miƙe, abin ya sosa mata rai. "Bari na kira Anni sai ku yi sallama" Cewar Ayda, da ta tafi sai kuma Farhan ta fara kallonsa a sace, yana gani ya basar, Haj. Bilkisu ta fito ta yi masa godiya sannan ya wuce Ayda ta masa rakiya har jikin mota. "Ke ban gane ba, wai naga yana ta wani nan-nan dake kuma ya karɓi numberki" Farhan ta yi maganar lokacin da Ayda ta dawo daga rakiyarsa. "To ai kece kika tsaya kina wani jan aji, shiyasa na ƙyaleki haba ai bai kamata ba, haka za ayi soyayya har ta kai ku ga aure?" "Ni fa ba jan aji na yi ba, gani na yi bai min magana ba shiyasa nima na basar" "Ni magana ya yi min, ai shi ne baƙonmu mu zamu fara masa magana sannan ya saki jiki damu" "To na ji na yi kuskure mene abin yi?" "Idan ya kirani zan haɗaku ku yi magana, kin ga daga nan sai na tura masa numberki shi kenan" "To babu damuwa." ******* ******* Sai da suka gama fita da kayan kaf sannan suka dawo, Sadiya ta sauka daga gadon, Saddiqa ta kama hannunta suka fita. Mota ƙirar Peugeot 206 ta gani baƙa Yazid na tsaye jikin motar. Suna ƙarasawa ya buɗe mata baya ta shiga ita da Saddiqa shi kuma tare da Surayya suna gaban mota. Ganin Yazid yana jan motar abin ya ƙara bata mamaki sai dai bata bar mamaki ba sai da ta gansu a wata unguwa da ban ƙofar wani gate ash, suna fitowa ta tsaya. "Sadiya muje mana" "Aunty ina ne nan?" "Gidanki ne." Kallon Yazid tayi sannan ta kalli Saddiqa. "Ban gane ba?" "Mu shiga ciki duk daga baya za ki ji komai. Shiga suka yi, madaidaicin tsakar gida ya sha tarazo sai flowers ƙananu daga gefe, sai ƙofar parlour, safe content mai ɗakuna biyu da dinning area sai kitchen da store, ko wane ɗaki akwai toilet a ciki sai kuma wani extra toilet a tsakar gidan. Kai tsaye ɗaya daga cikin ɗakunan suka shiga ta kwanta kan gado tare da lumshe ido. "Surayya ki shiga kitchen a dafa mata ruwan tea da ko indomie ce" Miƙewa Surayya tayi ta fita. Sadiya ta miƙe zaune tare da kallon Saddiqa "Aunty dan Allah ki faɗa min ina ne nan, na san dai gidanki yafi wannan girma bare na ce sabon gida kika koma." "Sadiya gidan ki ne wannan" "Gidana!" Ta furta da mamaki tana ƙara kallon ɗakin. "E, ki godewa Allah Sadiya, Allah ya muku arziƙi kuma zaku fantama, ko wannan motar da kika gani tashi ce, ai ku kam noma ta muka rana." "Wai har an sayar da attarhun?" "Hmmm! Ai Sadiya tarhu ya yi albarka, kina asibiti ya kirani ya faɗa min ya sayar da attarhunsa ya saya muku gida, ni da shi ne muka zaɓo furniture muka kuma kwaso kayanki saboda ya ce daga asibiti so yake ya yi surprising ɗinki da gidan nan" Murmushi ta yi tare da faɗin "Allah sarki Yazid, Allah ya ƙara masa buɗi na alkhairi" "Amin Sadiya." Sai da yamma lis sannan suka tafi lokacin kuma Yazid ya ɗauko yaran daga wurin Mameey. Suna zaune da yaran a parlour an kunna musu cartoon ita kuma tana kwance kan three seater sai ga shi ya dawo gidan. A hannun kujerar da take kwance ya tsaya tare da faɗin "Ya jikin naki?" Ɗan murmushi tayi sannan ta ce "Da sauƙi" Sai kuma ta miƙe zaune "Abban yara wannan gida har haka na yi mamaki sosai" "Ko dai bai miki ba?" "Ya yi min amma yanzu har abin ya kaimu ga wannan gida?" "Sadiya wannan ai ba wani babban gida bane rabin ploti ne kawai dai tsarin ginin ne ya yi kyau, a gine na saya na kuma sayi mota" "Alhamdulillah" Ta furta tana goge hawaye. "To mene na kuka? Kin ga ki kwantar da hankalinki, yanzu dai ki faɗa min me kike so a saya miki da dukiyar nan da muka samu" "Abban yara kenan, ai ni kam ba sai ka sayi komai ba, fatana kawai ka gina rayuwarmu kuma Allah ya baka ikon amfani da dukiyar ta hanyar halak" "Amin Mommyn yara kuma ina mai ƙara miki godiya domin arziƙin nan namu ne baki ɗaya, kin taimaka da harshenki wajen ƙarfafa min gwiwa da kuma ƙarfinki wurin bayar da gudunmawa wanda zan iya cewa wannan noman ku san rabin kuɗinki ne aka yi amfani da su." "Kai daina faɗar haka Abban yara, kuɗina ai naka ne" "Haka ne, Allah ya miki albarka" "Amin ya rabbi." Washe gari tare suka je suka kai Najma wata private school aka mata register, Sadiya mamaki kawai take ganin 100k ne school fees, Najma da take government school amma sai gata a private school mai kyau. A hanya suna dawowa Sadiya ta kallesa ta ce "Abban yara amma kana ganin zaka iya affording school fees ɗin nan, sai nake ga kamar ya yi yawa" "Bai yi ba, zan iya insha Allahu, kuma ai ba haka zan zauna ba zan fara kasuwanci ne baki san har na bayar ayi min cigiyar shago a kwari ba, ke kuma na kama miki shago anan zooroad" "Kwari da zooroad kuma? Ban gane ba" "Na bayar da order zan fara sayar da shaddoji da yadika, huluna na maza da dai sauransu, ke kuma shagon zan zuba miki shoes and bags ba dai ke zaki zauna ba zamu samu wanda za su zauna sai dai kuɗin dai asusunki zai riƙa zuwa, domin ke za ki riƙa controlling komai." Ɗan zaro ido ta yi sannan ta ce "Abban yara ni kam gaskiya a'a ban yarda da wannan ba, ka dai riƙe shago ka haɗa mana kuɗaɗe ka ƙara bunƙasamu, ni abu ɗaya nake buri a yanzu" "Me kenan?" "Karatu nake so na koma" "Karatu?" Ya maimaita. "E, dan Allah ka barni" Ta furta da shagwaɓa. "To shi kenan zan yi tunani akai." Ɗan turo baki ta yi. Ranar bai fita ko ina ba tun bayan fitar da sukayi sai ɗauko Najma da ya yi daga school tun bayan nan bai ƙara fita ba, dan sallah ma a gida ya yi azhar da la'asar, sai da magrib ya fito da shiri, tana kitchen tana kwashe tuwo da ta gama tuwon semovita miyar agushi, "Ashe kina nan" "E, kamar fita za kayi ko?" "Fita zan yi, maybe sai bayan isha'i zan dawo" "Abinci fa?" "E, idan na dawo zan ci, ki duba mirrow drawer na ajiye miki saƙo" "To shi kenan, a dawo lafiya" "Allah yasa" "Amin ya rabbi." Sai da ta shirya kayan a dinning area ta zubawa yaran abinci sannan ta shiga ta yi wanka, ta saka kayan bacci silk riga da wando, ta fesa turare sannan ta janyo drawer, tana ganin takarda gabanta ya faɗi, jiki a sanyaye ta ware, sentence na farko da ta karanta ya ɗaga mata hankali tana shirin miƙewa ta zame ta faɗi. Sai da ta ɗan saki ƙara sannan ta cije laɓɓanta, ta sake kallon takardar da take kallonta a matsayin baƙar takarda sannan ta sake fara karanto rubutun da aka yi da manya baƙi kamar haka. _NI YAZID USMAN NA SAKI MATATA SADIYA BELLO SAKI ƊAYA(1) IDAN TA SAMU MIJI TA YI AURE._ Ji tayi ko ina yana juya mata, sai kuma ta miƙe tsaye ta haɗe takardar. "Saki? To laifin me na yi dana cancanci saki?" Wani ƙarfi ta ji yazo mata, da sauri sannan ta janyo akwatin da ta gani ajiye wanda Saddiqa ta ce mata da shi suka kwaso kayanta. Kayan ta haɗa tare dana Najma da Ihsan sannan ta fita parlour, a lokacin Ihsan har ta yi bacci saboda tara na dare ta wuce, Najma ce dai tana zaune tana kallo da yake har solar ya saka musu. Zane ta ɗauko duk girman Ihsan shekara uku amma haka ta goyeta da zane ta ce Najma ta taso su tafi. Da ta rufe gidan kuwa key ɗin ta wulla ta saman get dan ta san yana da extra, sannan ta wuce tana jan akwati Najma na biye da ita har titi, basu daɗe a tsaye ba suka samu Napep kai tsaye ta ce a kaita Sultan Road, kwatance ta yi masa har ƙofar gidan Saddiqa basu yi ciniki ba shiyasa ya cajeta har ₦4000 haka ta ɗauka ta ba shi sannan ta doshi get ɗin gidan, tana knocking maigadi ya ce "Waye" "Sadiya ce" Ta furta a taƙaice, ya buɗe mata ƙaramar ƙofar tare da yi mata barka da zuwa, shi ya karɓi trolley ɗin ita kuma ta kama hannun Najma suka shiga cikin gidan. "Sadiya kuma?" Saddiqa ta faɗa lokacin da maigadi ya shigo da akwatin, sai dai kafin ya bayar da amsa kukan Sadiyar ne ya mata sallama, da sauri ta miƙe ta fita, a daidai lobby ta zauna tana kukan ga kuma Ihsan ta farka. "Sadiya lafiya?" Bata ba ta amsa ba sai kuka da ta cigaba da rerawa. Saddiqa ta kunce mata goyon sannan ta ɗauki Ihsan ta ja hannun Najma suka shiga ciki ta kwantar da Ihsan kan kujera ta kuma dawo taja hannun Sadiya. Tsawon awa guda ta yi tana kuka da babu tsayawa kafin daga bisani ta fara shashsheƙa. "Sadiya mene ke faruwa?" Miƙewa ta yi ta buɗe saman trolley ta janyo takardar ta miƙa mata, karɓa ta yi ta ware ta fara karantawa. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ta furta har sau uku sannan ta dafe goshi, ta daɗe bata sauke hannu ba, sai daga baya ta janye tare da kallon Sadiya har lokacin ta kan goge hawaye. "Sadiya mene ya faru har Yazid ya aikata ɗanyen aiki haka?" "Ban sani ba, lafiya lau muke da shi, kuma yau babu inda ya fita sai magrib da zai fita ya ce ya ajiye min saƙo ashe wannan baƙar wasiƙar ce" Sai kuma ta sake fashewa da kuka, da sauri Saddiqa ta sauka tana share mata "Ki daina zubar da hawayenki, bari na kira Yazid ɗin naji" Da sauri ta ɗauki wayarta ta yi dialing number ɗinsa, sai dai cikin rashin sa'a a kashe ta sameta. "Tabbas ya san za a kirasa shiyasa ya kashe waya." "Tun akan wannan case ɗin ne, dama Umman shi ai bata ƙaunata, kuma har 'yan uwansa sun ci alwashin rabamu, na san shi ne dalilin, na san Yazid ya sake ni ne ba a son ransa ba" "Sadiya ni ban ɗauki wannan a matsayin hujja ba, kin sadaukar da komai ciki har da farin cikinki dan kawai ki daɗaɗa masa amma shi ya kasa ɗauke damuwar 'yan uwan shi saboda ya faranta miki, sai lokacin da wahalarku ta yanke sannan zai ce ki tafi gida, ke da shan wahala wata banza da morar daɗin." Hannu Sadiya ta saka ta sake goge hawaye ta ce "Nima na yi wannan tunanin lokacin ina tahowa nan, amma a raina ina jin cewa ba laifinsa bane, cikin ƙannensa da mahaifiyarsa dole a samu wanda ya raba auren" "Ƙannensa ɗin banza, kima bar maganar nan, Sadiya ki share hawayenki kawai, amma dole ne Yazid ya faɗa min dalilinsa na sakin ki, kuma dole ya mayar dake dan ko Mameey ba zamu bari ta san kun rabu ba, ko bai ɗaga wayata ba zan bi shi gida ne, muje mu kwantar da yaran kema kiyi bacci." Ranar Sadiya da Saddiqa duk babu wanda ya runtsa, dan dai ba ɗaki ɗaya suka kwana ba, ita tana tare da mijinta, kuma bata faɗa masa gaskiyar abin da yake faruwa ba, kawai dai ta ce masa Yazid da Sadiya sun samu matsala shi ne Sadiya ta taho gidanta, kuma ita take son ta gyara komai basu so Mameey ta sani. "Kin yi daidai haka ake so babba ya kasance, amma mene ya haɗa Sadiya da Yazid har haka, gaskiya a bincika dan na san Sadiya macece mai kawaici" "Wallahi kuwa kai da ka san halin naku na maza, duk amincin da mace za ta muku sai kun kai ta maƙura" Murmushi ya yi tare da faɗin "Kullum burinki shi ne ki ɓata mu" "Gaskiya nake faɗa, saboda kai ma babu yadda ban yi muje asibiti ba amma kaƙi" "Inje asibiti su yi min me? Saddiqa na sha faɗa miki ki kwantar da hankalinki indai haihuwa ce akwai wanda suka fimu daɗewa kuma daga baya sun samu haihuwa muma mu haƙura mu gani, aurenmu fa ko shekara goma bai yi ba" "Amma a waɗan da suka fimu daɗewa ka samu labarin wanda suka zauna basu nema ba kawai suna jira, Allah ma fa cewa ya yi tashi in taimakeka." "To addu'a bata wadatar ba? Kin ga Saddiqa na kwaso gajiya dan Allah kar ki ɓata min rai, ni dai asibiti ba zanje ba ai yi ta min wasu gwaje-gwaje mararsa ma'ana" "Ai shi ke nan" Ta faɗa tana saka hannu a haɓa. ****** ****** Jiki a sanyaye ta karɓi wayar daga hannun Ammi tare da karawa a kunne. "Badriyya!" Jin muryar Affan ta dira a dodon kunnenta ya saka tayi saurin miƙewa ta bar ɗakin, hannu ta saka a baki tana son hana hawayenta zuba amma ta kasa. "Kina ji na kuwa?" "Affan dama za ka nemeni?" Ta yi maganar da muryar kuka kuma lokacin hawayen har sun zubo. "Dole na nemeki Badriyya saboda har yanzu akwai igiyar aurena a kanki" "Affan dan Allah ka yi haƙuri dani, duk wasu abubuwa dana aikata kishinka ne da tsananin soyayyarka suka ja min, amma dana ji labarin rasuwar Nashwa hankalina ya tashi kuma na ji a raina ban kyauta ba, musamman haɗuwarmu ta ƙarshe da ta kasance faɗa har da zage-zage, har yau ina dana sani." "Haka Allah ya shirya, karki damu, dama na kira ne dan na sanar miki saƙon da iyayenki suke so na baki" "Wane saƙo, Affan dan Allah kar kace zaka rabu dani" "Badriyya iyayenki sun matsa akan sai na sakeki, sun ce ko ban sake ki ba su da kansu za su kai ƙara kotu a raba aurenmu" Hannu ta saka ta rufe baki tana shashsheƙar kuka. "Kiyi haƙuri Badriyya na san iyayenki ba za su ƙara yarda na zauna dake ba." "Affan....." Sai kuma ta yi shiru tana shashsheƙa. "Am very sorry Badriyya, na sakeki saki ɗaya, amma ki sani har abada kina raina, kuma idan iyayenki sun amince zan mayar dake ko da kin gama idda zan shiga sahun manaimanki" Wayar ta saki tana shashsheƙa, a lokacin Ammi ta fito. "Badriyya mene haka" Kallon Ammi ta yi a take taji komai na juya mata, ta sume a gurin Ammi ta yi kanta tana kiran sunanta. Affan yana ji, sai dai kawai ya kashe wayarsa, gabansa ya ji yana faɗuwa, ƙafafunsa ya ji sun sage dan haka ya dafa bango sai kuma ya zube a ƙasa ya fara tuno rayuwarsa da Badriyya tun lokacin daya fara ganinta. *Waiwaye* Mu haɗu a next page, more comments more typing... *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._* *_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_* Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* lLITTAFAN SUNE: 1-WUTAR ƘAIƘAYI 2-WA'ADI. 3-A CIKIN IDO.. 4-TAZARAR SO #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah [6/20, 9:15 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@sanazty _Facebook@SaNaz Deeyah_ Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe Please likes my facebook page: https://www.facebook.com/share/16d2wDeqer/ *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ *_Wanda za su sa yi novels ɗinmu akwai details a ƙasan page ɗin nan ku biya ku cigaba da karatu, dan koda mutum 5 ne cigaba zamuyi, wutar ƙaiƙayi ma free pages ɗin shi na gab da ƙarewa so make your payment as soon as possible, muna maraba da ku a koda yaushe domin makarantanmu kune ƙwarin gwiwarmu🥰_* _Book 1_ ```🆓Page 11``` *Waiwaye* Driving yake da ɗan sauri yana so ya ƙarasa office kasancewar shi sabon ma'aikaci ne baya son ya yi latti, ga kuma yanayin hadarin daya taso alamu ne na ako wane lokaci za a iya sheƙewa da ruwa. Har ya wuce su a gefen titi, kuma titin babu yawaitar ababen hawa, sai kuma ya yi reverse a hankali ya dawo ya tsaya gabansu, ya sauke glass ƙasa tare da kallonsu. "Sannunku" Ya furta, ɗaya ta amsa ɗayar kuma ta ɗan kauda kai gefe hannunta na riƙe da wasu takardu ta rungume yayinda ta rataya school bag a bayanta. "Na ga kamar kuna neman abin hawa ga hadari?" "Wallahi kuwa, tun ɗazu duk wanda muka tara basu tsayawa ma" "Saboda hadarin dake garin so kowa burinsa ya samu mafaka" "Hakane!" "Ku shiga sai na rage muku tafiya ko zuwa bakin titi ne inda zaku samu yawaitar napep" "To shi kenan mun gode" Ta faɗa sannan ta juya ga ƙawar. "Muje ko" "Ni kam ba zan shiga ba because ban san waye shi ba kar ya cucemu" Bai ji abin da ta faɗa ba amma yanayinta ya nuna kamar bata son shiga ne ga shi yana ƙara makara. "Baiwar Allah ki shiga da zuciya ɗaya, nima office nake son zuwa ga shi time na ƙara tafiya" "Ka je babu damuwa zamu samu abin hawa." "Ni kam gaskiya sai dai na tafi na barki, kin san dai test ne damu ga kuma hadari idan ruwa ya ɓalle mana anan ya zamuyi?" "To ki tafi kawai ba matsala" Buɗe murfin motar ta yi ta shiga, shi kuma ya ɓalle murfin ya ƙarasa gabanta ta ƙara kauda kai. "Dan Allah ki zo mu tafi, wallahi da zuciya ɗaya zan ɗauke ku ni ba macuci bane" "Kar ka damu, ku je kawai" Ta furta tana jin hawaye na neman zubo mata" "Ni na ji a raina ba zan iya tafiya na barki haka ba" Sai lokacin ya ga fara'arta, ta yi murmushi sai kuma siririn hawayen ya zubo a ido ɗaya, ta saka hannu ta goge. "Kar ka damu ku je kawai" "In ci darajar manzo(SAW) ki shiga na saukeku please" Ya furta yana haɗe hannayensa. "SAW" Ta faɗa sannan ta sauka ta buɗe back seat ta shiga. Yana driving amma babu wanda yake magana, ya dai zuge glasses ya kunna musu AC. Suna isa bakin titi ta ce "Ya isa nan ma" Ko ƙarasa rufe baki batayi ba aka fara ruwa. Ya ɗan juya ya kalleta kin ga da ace na saukeku da yau wannan ruwan a kanku zai sauka" "Ina zan kaiku?" "B.U.K new site" Wadda ke gaban motar ta faɗa. "Ok" Ya furta yana taka motar. "Ku lecturers ne kenan" "Wane mu? Mu students ne, muna final year ɗinmu ɓangaren Business administration" "Wow ashe tare da masu kuɗi nake" "Hmm! Masu neman hanyar da za a samu kuɗi dai" "Duk ɗaya ko Hajiya" Ya faɗa yana kallon ta backseat ɗin. "Sunana Affan Ahmad Giwa, ni ƙaramin ma'aikaci ne a gidan tv" "Alhaji Ahmad Giwa dai da muka sani?" "Ba wannan ba, wane ni in san babban mutum kamar shi, suna ne kawai yazo ɗaya" "Ma sha Allah! Ni sunana Aisha Kabir ita kuma Badriyya Shehu" "No wonder take da kyau kin san masu sunanta kaɗan ne a duniya kuma kyawawa kaɗai ake sakawa sunan" "Ni kam a bakinka na fara jin wannan" "Ya kamata dai ki bincika za ki gane kema" Duk hirar da suke Badriyya bata saka baki ba, har ya isa school ba a gama ruwa ba, ko daya ƙarasa department ɗinsu bai bari sun fita ba ya ce a bari ruwan ya ɗan tsagaita. Hira sosai ta ɓalle tsakanin Affan da Aisha anan take ba shi labarin accounting taso ta yi amma mahaifinta ya ce ba zai bar mace ta yi aikin banki ba shi ne ta haƙura take business admin. Wayar Badriyya ta fara ringing, ta kalla ta ga class rep ne ya kira. "Hello 001 ya dai?" "Anyi cancelling test yau bamu da lectures na ga baki online na ce bari na sanar" "Ya salam ka ga shi har mun shigo school" "Ayya am very sorry ya kamata ace na sanar miki since" "Ba damuwa, nagode" "You're welcome" "It's my pleasure" Yana kashewa ta sauke ajiyar zuciya. "Badriyya lafiya?" "Anyi cancelling test da duk lectures ɗinmu na yau" "Kash! That's the reason na ce miki karmu shigo saboda hadarin dana gani" "Haka Allah ya ƙaddara" "Yanzu dai kawai mu koma gida ko?" "Ok. Bari ruwan ya ɗan tsagaita sai mu sauka mu samu napep" "Shi kuma drivern naku ku yi ya ya da shi?" "Haba ai kuma wahalar sai ta yi yawa" "Karku damu ai ba kune kuka tambaya ba ni ne na yi niyya" Gabaɗaya a gidan su Badriyya suka sauka, Aisha har ta rufe ƙofar yayinda Badriyya na faɗin "Nagode" ta yi gaba. Glass ya sauke tare da cewa "Idan ba damuwa ki bani number ki mana, kin ga sai na zama driver na dindindin ko?" Murmushi tayi tare da cewa "Ai ka fi ƙarfin driver" "A'a fa karki saka na riƙa jin kaina na girma" Karɓar wayar tayi ta saka masa number sannan suka yi sallama ya tafi. Aisha na ƙarasawa inda Badriyya take ta ɗan kai mata duka ita kuma ta goce. "Wallahi gayen can son ki yake Baddy" "Ni kuma haba sai dai ke, ki ga fa hirar da kuka sha" "Amma a hirar waye yafi ambata, sannan kuma kina gani yadda yake ta nan-nan dake, ni na tabbatar idan ya kira numberki zai buƙata" "Ni ban yarda ba, idan ni yake so meyasa bai karɓi numberta ba sai taki?" "Saboda kin nuna halin ko in kula, ga kuma miskilanci shiyasa ya yi tsoron tambaya kai tsaye" "To na ji idan ya buƙaci numberta ya kuma ce ni yake so, za ki goge numbersa daga wayarki kiyi blocking sannan kuma ko kun haɗu karki sakar masa fuska" "Sannu sarakan kishi, kina so ɗin kenan" "Idan har ya taya zan sayar ni fa na daɗe da saninsa hasalima ni fan ɗinsa ce, anyway ina so mu ƙulla wannan deal ɗin" "Na amince zan ga in zaki iya" "Deal" "Yeah deal" "Ok" Badriyya ta faɗa tana murmushi. _*Bayan Wani Lokaci*_ Aisha na zaune akan gadonta ta ga saƙo ya faɗo wayarta, ɗauka ta yi ta duba, abin ya matuƙar bata mamaki dan haka da sauri ta bi kiran. "Hello" "Kin ga saƙona kenan?" "Na gani Suhailat amma gaskiya bana jin Badriyyar dana sani ce, ko last week na je gidansu kin san idan ana cikin hutu ba a haɗuwa sosai kuma ta ce min an ƙara 3 weeks a bikin." "To ƙarya take miki bata so kowa ya sani ne, yau aka ɗaura aurenta, ki hau whatsapp a group ɗin class ma maganarku kawai ake, saboda kowa ya san kece ƙawarta kun ɓoye biki" "Na rantse da Allah zan iya buɗe data yanzu mu yi video call ki ganni, ina gida fa, a kwance nake ko kayan bacci ban cire ba ina ta kallo a system" "Ba sai mun yi ba na san ba za ki min ƙarya ba, amma meyasa ta ɓoye?" "Ina zan sani, na yi tunanin ko za ta ɓoyewa wani ban da ni, amma ina zuwa." Tana gama faɗa ta kashe, da sauri ta faɗa toilet ita kanta ta san wankan da ta yi yau kawai dai dan kar aƙi yi ne amma bata fita ba." Material ta saka dan sune marar nauyi ta ɗauki jaka da atm ta fita, kai tsaye ɗakin Mamansu ta nufa "Mama zan je gidansu Badriyya" "Meya faru?" "Idan na dawo zan baki labari" "Ke dakata ban son shirme ta ya zan barki ki fita a haka duk kin ruɗe" Numfashi ta sauke sannan ta ce "Mama yau ake ɗaura auren Badriyya" Kallon mamaki Mama take mata kafin ma ta yi magana Aisha ta riga ta "Mama ta ɓoye min ne, koma ince ta ɓoyewa kowa, 'yan class ɗinmu sai ganin laifina suke, shiyasa nake son zuwa na ji dalilin ta na yin haka" "Ko za ta ɓoyewa kowa bai kamata ta ɓoye miki ba, bata kyauta ba amma dai ki bi komai a hankali karkije kuyi hayaniya dan na ga a fusace kike, idan kuma kin san hayaniya za kije kuyi to gaskiya ki haƙura idan zuciyarki ta sauko sai kije" "Ba zan yi ba Mama amma dai ina so naje saboda na wanke kaina" "Allah ya kiyaye, ki kula" "Amin." Napep na tsayawa ta hango Badriyya tare da wasu 'yan mata biyu sai Affan da abokansa ana ta hotuna, har ta biya mai napep kuɗi basu lura da ita ba, sai da ta kusa ƙarasawa kawai Badriyya ta ganta, ta ɗan furgita sai kuma ta yi murmushin ƙarfin hali. "Aisha ki shigo mu yi hotuna" "Ba shi ya kawo ni ba" Ta furta rai ɓace, da sauri Badriyya ta ce "Ok mu shiga gida mu yi magana" Sai lokacin Affan ya ce "Aisha yaushe a gari, kin dawo kenan" Murmushin gefen leɓe tayi sannan ta ce "Haka ta faɗa maka?" "Baby dan Allah karka ƙara magana, kin ga Aisha muje ciki" Da sauri tayi gaba, ita kuma Aisha ta sake kallon Affan sannan ta wuce. Gidan kamar ba na biki ba dan babu mutane sosai, a gefe suka tsaya Aisha ta kalleta cikin ɓacin rai ta ce "Badriyya duk mene wannan? Dama za ki iya ɓoye min aurenki?" "Kiyi haƙuri Aisha gaskiya na ɓoyewa kowa ne saboda ina gudun snatchers kuma kin san ance a ɓoye nema a bayyana samu, dama na yi niyyar na faɗa miki daga baya, kuma kin san gidan nan dai gidan malamai ne ba a komai daga walima sai ɗaurin aure kawai aka yi" "Kina tunanin ni zan iya yi miki snatching?" "Babu wani abin yarda a wannan duniyar, kuma na ga kina ta ƙara shigewa Affan ni kuma gaskiya kishina ba zai barni na bari a raɓe shi ba koda ciki ɗaya muka fito bare ƙawa." "Badriyya bakin ki ne yake faɗar haka?" "Ƙwarai da gaske" "Shi kenan ya yi kyau, Allah ya baku zaman lafiya" Daga haka ta juya da sauri ta fita, ganin fitowarta ya saka Affan ƙoƙarin tareta amma ta wuce da sauri taƙi ta saurare shi. _Bayan Mako Guda_ Tana kwance kan doguwar kujera hannunta riƙe da waya tana game kira ya shigo mata. Kallon wayar take tana tunanin kamar ta san lambar amma ta kasa tunawa, kawai ta ɗaga tare da yin sallama, yana amsawa ta gane waye ta kuma tashi zaune. "Ina ƙofar gidanku" "Kofar gidanmu kuma?" "E, ki fito dan Allah idan babu damuwa" "Shi kenan gani nan zuwa" Yana yanke kiran ta ɗanyi shiru tana tunani, mene zai kawo Affan gidansu, miƙewa tayi da sauri ta nufi ɗaki ta ɗauki gyale ta yafa sannan ta leƙa ta cewa Mama za ta waje tana da baƙo. Jikin motarsa ta gan shi tsaye ya harɗe hannayensa, ta ƙarasa a sanyaye tare da yi masa sallama. "Ko zamu shiga mota?" "A'a sai dai ko mu shiga daga ciki" "Ok." Ya furta gami da rufe motar, kujerun roba ta saka musu a tsakar gidan, ya zauna ita kuma ta shiga ta kawo masa ruwa. "Sannu da ƙoƙari" Murmushi kawai ta yi. "Aisha dama.....na zo ne on behalf of Badriyya ina so na baki haƙuri a bisa abinda ya faru, tabbas bata kyauta ba kuma na nuna mata kuskurenta, so dan Allah kiyi haƙuri" "Ni ban riƙe ta ba, na manta da komai." "Na san ba za ki iya mantawa a ƙanƙanin lokacin nan" "Affan abin da Badriyya ta zaɓa kenan, dama tasha faɗa min ita idan ta fara soyayya za ta ja baya da duk wata ƙawa budurwa sannan idan ta yi aure matan aure za tayi abota da su ba 'yammata ba, a lokacin da take yi min irin maganganun nan da yadda take faɗa min zafin kishinta na ɗauka wasa ne amma da ta aikata hakan sai na tabbatar, sai dai na yi mamaki tun daga yarinta na fara ƙawance da Badriyya bani da wata ƙawa kamarta hasalima a secondary school ta samu matsala ta kwanta jinya sai aka mata repeating amma ban shiga jami'a ba sai dana jira muka zana jamb tare muka cike school da course ɗaya, kuma Allah ya taimakemu gabaɗaya muka ci jamb sannan muka samu gurbin karatu a jami'a, tare muke ko yaushe sai dai dama ita miskila ce shiyasa wasu lokutan idan mun samu saɓani sai ace nice da laifi kasantuwar bata da hayaniya ni kuma am free to everyone around me" Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce "Ba komai ta nuna min asalin kalarta a yanzu" "Na san bata kyauta ba kuma ban goyi bayanta ba, sannan na yi mata faɗa sosai, kuma itama ta ce na baki haƙuri kuma za ta kiraki a waya ta sake baki haƙuri" "Ta riƙe haƙurinta bana so, kuma insha Allah na rabu da ita har abada." Duk yadda Affan ya so ya shawo kan abin amma ya kasa, sai dai babban abin da ya ba shi mamaki shi ne ko a jikin Badriyya bata damu da rabuwarta da Aisha ba. Tun wata uku da aurensu ya fara fuskantar matsala daga gareta, kullum cikin zargi da tuhuma, babu damar yaje aiki ya dawo tun a ƙofa za ta fara shinshina rigarsa, tun abin baya ɓata masa rai har ya fara, wata ranar lahadi suna zaune suna hira ya ce da ita "Baby so nake ki ɗan rage kishin nan naki ya yi yawa" Ta haɗe fuska sosai tana kallonsa, kafin ta ce "Affan ni gani nake sam bana kishinka, wallahi da da yadda zan yi da sai na daƙile aikin nan naka, ni fa duk wani aiki da zai shigo da mata rayuwarka ba ƙaunarsa nake ba, tun ranar dana ziyarci gidan radionku naga ku san duk abokanan aikinka mata ne ranar ko runtsawa ban yi ba" Ɗan zaro ido ya yi, sannan ya yi murmushi, ki kwantar da hankalinki, kin manta a cikin dubban mata ke ɗin na gano na kuma aur" Murmushi ta yi sannan ta ce "Hakane Babe! Amma ni gaskiya....." Sai kuma ta turo baki. "To mene na ɓata rai, am sorry Baby kina ji?" Kai ta gyaɗa. "Ina so ki je ki bawa Aisha haƙuri." "To mene na yi mata da har zan bata haƙuri?" "Saboda ƙawarki ce, kuma tare na sanku, dan Allah Baby kiyi haƙuri ku daidaita" "Ni fa ba zan daidaita ba, saboda na lura Aisha sonka take, tun farko ma so ta yi kace ita kake so bani ba, dan haka ni gaskiya ka daina min maganarta" Tana gama faɗa ta miƙe tsaye, sai kuma aka turo ƙofar parlourn aka shigo. "Yaya ashe kana gidan" "Eh ina nan, ya dai?" Kai ta ɗan sosa sannan ta ce "Dama...dam..." "Kin ga ni ba sai kin faɗa min ba, bari na tashi na tafi gurin Mommy" Tana kallonsa har ya fice sannan ta zauna. "Lawisa ya kike?" "Lafiya lau Aunty Amarya, na zo na tayaki hira ashe ma Yaya yana nan" "Dama fita zai yi gara ma da kika zo" Murmushi kawai ta yi suka cigaba da hira. *Bayan Wata Biyar* A cikin asibitin ya yi parking sannan ya kalleta "Maman Baby mun zo" Murmushi ta yi sannan ta ce "Yauwa Babe amma dai za ka dawo ɗaukana?" "Insha Allah, ba dan akwai wasu baƙi da zamu gana dasu ba ai da sai na jira ki gama sannan na tafi" "Amma duk da haka ya kamata ka shiga dani ko?" "Ok babu damuwa mu je your majesty ai duk yadda kika dama haka za asha" Murmushi ta yi, ya sauka ya buɗe mata ƙofa ta fito sannan ya shigar da ita, har ƙofar ɗakin awo ya kaita sai daya tabbatar ta shiga sannan ya juya. Yana ƙoƙarin fita ita kuma ta shigo a kiɗime bata sani ba har ta ɗan buge shi, ta ɗago tare da faɗin "Yi haƙuri dan Allah" "No kar ki damu" Har zai wuce ta yi saurin cewa "Dan Allah ko za ka iya taimaka min?" "Dame fa?" Ya tambaya yana kallonta. "Na kawo wata mata ne, kuma wallahi a ruɗe nake na manta jakana a gida, ko zaka taimaka min sai na yi maka transfer daga baya?." "Tana ina" Ya furta. "E, tana nan waje" Ta faɗa tana nuna waje da hannu, duk da sauri yake amma ganin mace da tsohon ciki ya saka ya kasa tafiya har sai daya biya kuɗin komai, tare da budurwar suka yi ta yawo suna suyo kayan da ake buƙata kafin daga bisani aka shigar da ita. Yana duba agogo ya ga ƙarfe goma da mintuna sha takwas ya riga ya yi latti, "Am...ina fatan babu abin da za a buƙata ko? Na makara ina da meeting a office ne" "E babu, nagode Allah ya saka da alheri, in babu damuwa ko zan saka maka numberna sai ka kira wayar a kunne take idan naje sai na kira ka turo min account number" Murmushi ya yi tare da faɗin karki damu nima na bawa Mamanki gudunmawata ne ba sai an biyani ba" Yana faɗa ya ga ƙwalla ta cika maƙil a idanunta, maimakon farin ciki kawai sai ya ga ta fashe da kuka, "Lafiya?" Ya faɗa da mamaki amma kamar ƙara rura mata wuta ya yi, ta cigaba da kuka, yana ta rarrashinta saboda mutane har sun fara taruwa a wurin. Shiru ya yi ya lafe a bango yana kallon sarautar Allah, ɗaiɗaikun mutanen dake wucewa tambaya suke ko lafiya ko rasuwa akayi, sai ya ce musu a'a suke wucewa, ku san mintuna goma ta ɗauka tana kuka, shi kuma ya kasa tafiya har sai data gama kukan ta goge hawayen sai kuma ta miƙe ta kalleshi. "Ya kamata ka tafi kana ƙara makara" "Meyasa zan tafi na barki a wannan halin" Murmushi ta yi wanda da gani yaƙe ne "Babu damuwa fa" Shiru ya yi sai kuma a lokacin ya kalleta sosai. Matashiya ce da ba zata gaza shekaru ashirin zuwa ashirin da uku ba, ruwan tarwaɗa sai dai kuma kyakykyawar gaske ce, tana da ɓullar hanci wanda ta masa ado da dutse fari mai ƙyalli sai kuma fashin goshi da take da shi, doguwa ce sai dai ba can ba, bata da ƙiba kazalika bata da rama. "Am.....Kawai da ka yi maganar na tuno da mahaifiyata ne duk da ban santa ba ban kuma san kamanninta ba" "Oh so sorry, Allah ya jiƙanta da rahama ai ban sani ba da ban miki maganar da za ta sosa ranki ba" "Amin! Amma a zahirin gaskiya ban sani ba ko ta mutu ko kuma tana raye" Furucin na ta ya ƙara dulmiya shi a tunani, ya kalleta ya kuma kasa tambaya saboda gudun kar ta kuma faɗawa damuwa ko kuma ta sake yi masa kuka. "Ka yi mamaki ko? Ni marainiya ce a gidan marayu na tashi na tsinci kaina kafin daga bisani wata mata ta fanshe ni saboda bata haihuwa sai dai ban daɗe da ita ba Allah ya azurta ta da haihuwa, daga lokacin ta fara gana min azaba wannan matar dana kawo nan itace ke jana a jiki tana kuma taimaka min da abinci, labarina yana da tsayi kar in saka ka makara" "Zan so jin labarin naki gabaɗaya, ko zan iya samun numberki?" "Sosai ma" Ta faɗa tare da karɓar wayarshi ta saka masa number ɗinta ya yi saving sannan ya kira "Za ki ga 81 a ƙarshe" "To shi kenan nagode" "You're welcome." Yana fita ya ga Badriyya a gaban motar ta haɗe girar sama da ƙasa. *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._* *_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_* Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* lLITTAFAN SUNE: 1-WUTAR ƘAIƘAYI 2-WA'ADI. 3-A CIKIN IDO.. 4-TAZARAR SO #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah [7/9, 9:43 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@sanazty_ _Facebook@SaNaz Deeyah_ Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe Facebook: https://www.facebook.com/share/16d2wDeqer/ _Book 1_ _🆓Page 12_ Tattaro ɗan kuzarin daya rage masa ya yi sannan ya ƙarasa gabanta, sai ƙara haɗe rai take tana kaɗa ƙafa ɗaya. "Ba dai kin gama ba?" "Affan ina office ɗin?" "Faɗuwa ce tazo daidai da zama shiyasa na tsaya anan ɗin. Na samu wani rahoto ne shi ne na tsaya ɗauka." "Rahoto kuma na me?" "Kin ga mu shiga mota sai na ƙarasa baki labari kin san dai ba a son ku yawaita tsayuwa yanzu ƙafarki sai ta kumbura." "Ƙaramin ciki ne fa" "Koma dai mene ni kam ba zan bari ki wahalar min da Baby ba." "Oh babyn ma?" "Har da big Baby" Ya furta da dariya yana ƙoƙarin buɗe mota. Yana fara driving ta sake tambayarsa. "Wata mata ce aka kawo kin san wai shekarunta 60 a duniya amma ta sake haihuwa wai kawai saboda mijinta ya ƙara aure." Ya samu kansa da yi mata wannan ƙaryar. "Haihuwa fa Babe, to taya ta iya ɗaukar cikin?" "To kishin ku na mata ai babu abin da ba zakuyi ba akan kishi dai" "A'a Babe ita kam na ta ya yi yawa wace irin masifa ce wannan shekara sittin may be har jikoki ne da ita amma ta haihu" "Yanzu ko ni idan na ce zan miki kishiya kina shekaru 60 ba zaki iya ba?" Ɓata rai tayi yayi dariya, "Anzo wurin ko?" "Babe ka san bana son maganar kishiya" "Am sorry Babe misali ne fa" "Ni kam ban son wannan misalin, kuma koda ya kasance dani wallahi ba zan yi gasar haihuwa ba wanda na samu ma Allah ya raya, ni fa gani nake ɗa ko 'ya ɗaya sun wadatar ni kam ko iya laulayin nan aka barni da shi ma ya isa haka Allah ya raya" "Kin isa ma, ni da nake son 'ya'ya, ai a ƙalla sai kin haifa min ko 4 ne." "Haba Babe a wane cikin? Gaskiya ni kam ina haihuwa planning ma zanyi sai na yi shekaru biyar cif sannan zan kuma haihuwa" "Ban amince ba" Dariya ta yi shi kuma ya ƙara haɗe rai "Badriyya idan ma wasa kike nima bana son irin wasan nan, ina son yara dan haka ban yarda kiyi planning ba." "Gaskiya Babe rigima ne da kai, to akan me? Ka san kuwa wahalar? Kuma a wajen awo wasu ina ji suna cewa wannan so min taɓi ne wahala na gaba a lokacin da ciki zai girma ya fara rinjayata" "Baddy na faɗa miki bana son kiyi planning" "Gaskiya sai na yi" "Oh ina faɗa kina faɗa?" "Sorry" Ta furta rai ɓace. Har suka ƙarasa gida babu wanda ya kuma yi wa wani magana, yana sauketa ya juya yaja mota fuuu ya fita. "Ai wallahi duk fushin da zakayi ka yi ka gama amma planning kamar na yi na gama." _*Dare*_ Affan da Madam dai sun samu saɓani, dan gabaɗaya tun daya dawo da yamma ya ga babu fuska sai ya yi side ɗin Mommy, sai dare ya shigo kuma bai ganta a parlour ba ya san tabbas tana bedroom. Kai tsaye ya nufi can, a zaune ya ganta tana waya ya ɗan tsaya yana jira ta gama. "To duk abin da kuka ga dama ku yi, ina ruwanku? Ko ana dole? Mijina ne fa bana wani ba kuma ba dole sai na gayyaceta bikina ba, haba abu ɗaya yaƙi ci yaƙi cinyewa wata nawa ana abu ɗaya, ita abin ya dama ni ban ma san tana yi ba." Tsaki ta ja ta kashe wayar, ya san tabbas akan Aisha ake magana, dan shi kansa yana mamakin butulcin da tayiwa Aisha. "Madam" Shi ne sunan da yake kiranta da shi a duk lokacin da suka samu saɓani ya kuma fahimci tana ta haɗe fuska. "Na shigo ban ga abinci ba" Ɗan ƙara haɗe rai ta yi kamar ba za tayi magana ba sai kuma ta ce "Ban yi girki ba, na yi tunanin a gurin Mommy za ka ci" "Amma yanzu idan naci a wurin Mommy bayan kina gida me kike tunani?" "Babu, saboda ni bana kawo komai a raina" "Badriyya wai mene haka?" "Komai ma Affan" Ta furta a hasale. Kai ya ɗan girgiza sannan ya wuce ya bar ɗakin. Kai tsaye ɗakinsa ya wuce ya yi wanka ya shirya ya ɗauki key ɗin mota ya fita. Restaurant ya nufa ya yi order na tuwon semo miyar agushi duk da baya son cin abinci mai nauyi amma da aka kawo masa menu sai ya ji kawai yana sha'awa, ya saka aka kawo masa black tea. Har ya fara ci kawai yarinyar nan ta faɗo masa a rai ya janyo waya ya kirata, sai dai har ya mata 2 missed calls bata ɗaga ba, ya ajiye wayar ya cigaba da cin abincinsa. Yana gamawa kai tsaye gida ya koma. A parlour ya tarar da ita tsaye ta kama ƙugu, ya kalleta ya kuma kauda kai zai wuce ta ce "Affan daga ina kake?" Da mamaki ya juyo ya kalleta. "Daga ina nake?" Ya maimaita sannan ya yi murmushi "Ni ne zan miki wannan tambaya in kika fita ba tare dana sani ba amma ba ke ba, saboda ke a ƙarƙashin ikona kike" Yana gama faɗa ya wuce, ta bi shi da kallo tana faɗin "Nima ina da haƙƙi a kanka ai" Bai bi ta kan ta ba ya wuce, yana kuma shiga ɗaki ya saka masa key ya yi locking saboda ba zai iya da faɗanta ba. Akan gado ya kwanta ya fara tunani, mamaki yake yadda ta koma haka, farkon soyayyar shi da Badriyya ya san tana da kunya, haƙuri sannan mace ce da magana ma ba ta dameta ba, shiyasa har yake tunanin ita ɗin miskila ce amma kuma suna yin aure sai halayenta na gaskiya suka fara fitowa, rashin mutunci da rashin ganin darajarsa, zai wuya su rufa wata guda ba tare da sun samu matsala ba. "Why!" Ya furta a fili da juya kwanciyarsa. Kiran daya shigo wayarsa shi ne ya katse masa tunani, ya yi rejecting sannan ya bi kiran. "Assalamu alaikum!" Ya ji sassanyar muryarta ta doka sallama. "Wa alaikumussalam!" "Ina wuni" "Lafiya lau ya kike?" "Alhamdulillah, ka kira bana kusa da wayar" "Ayya ba damuwa, ya Auntyn ki fatan ta sauka lafiya?" Sai kawai ya ji ta fashe da kuka, zaune ya tashi hankali a tashe. "Lafiya mene ya faru?" Cikin kuka take faɗa masa Allah ya mata rasuwa bayan ta haihu ta samu ɗa namiji. "Kiyi haƙuri, Allah ya mata rahama" "Shi kenan yanzu na rasa gata, bani da wanda zai tallafeni" Ta furta tana sake sakin wani kukan. "Am..am so sorry insha Allah ba za ki rasa gata ba, kiyi shiru kiyi haƙuri kin ji, kin ga kina ɗaga min hankali ga shi dare ya yi bare na zo gareki dan Allah kiyi haƙuri" Ta cigaba da shashsheƙa, "Zan kiraki gobe sai na zo na sameki" Haka ya yi ta rarrashi for no reason sai bayan daya kashe waya yake tunanin meyasa ya yi hakan? Tausayinta kawai ne a ranshi kuma dama tun fil'azal shi mutum ne mai tausayi. ****** ****** Da ido yake ƙara bin unguwar da kallo very local area, motar shi gabaɗaya ta ɓaci da kwata saboda ita kawai yake bi, layin nasu ko ina kwata ne da datti a haka har ya ƙarasa ƙofar gidan kamar yadda aka kwatanta masa. Daga motar ya fito, yara duk sun fito sun yi cirko-cirko suna kallon motar. "Barka da zuwa" Ta faɗa tana jingina a jikin motar ta gefensa. "Barka dai ƙanwata da ban san sunanta ba" Murmushi ta yi "Ko dai rowar sunan ake min?" Kai ta girgiza tare da cewa "Sunana Nashwa" "Wow nice name, wannan suna kamar na larabawa" Murmushi ta sake yi "Nashwa kamar baki yi bacci ba ko? Na ga idanuwanki sun kumbura kuma ga shi sun yi ja" Hannu ta saka ta goge wani hawayen "A taƙaice dai na fahimci kina da arhar hawaye" Bata ba shi amsa ba, "Kin yi breakfast?" Kai ta girgiza alamar a'a. "To shi kenan in za a barki a gida kizo muje mu ci abinci" "Ai duk inda zani bata hanani, amma kuma zaka iya ɗaukana a motarka?" Kallonta ya yi da mamaki sannan ya ce "Meyasa ba zan iya ba?" "Saboda ka ganni fa, babu wata shiga mai kyau" "Karki ce haka dan Allah, baki da matsala muje kawai." Ya yi mamaki sosai yadda take cin abincin babu wata kunyarsa da ta ji, kana gani ka san tana tare da yunwa. "Nashwa!" Ya ambaci sunanta a hankali, ta kalleshi "Kin yi karatu?" "Tun dana gama secondary school har yanzu ban cigaba ba" Ya yi shiru ya kasa magana. "Ina so na tambayeka" Zama ya gyara "Ok ina jinki" "Meyasa ka taimaka min jiya, kuma a yanzu ma kazo gurina har ka bani abinci" Murmushi ya yi ya ce "Saboda kawai a labarinki akwai tausayi a ciki, kuma daga nan ma gurin Mamana zan kaiki, da ace uwar riƙonki za ta yarda da sai ta bar mana ke" Murmushi sosai ta yi sannan ta ce "Ai ba zata yarda ba, ka san duk ƙarshen shekara daga gidan marayu sai anzo ganinmu, so ka ga indai ba aure na yi ba to ba zata barni ba, kuma ni na ce aurena ko a ina zan yi to a kano za ayi biki, zan je can gurin shugabar gidan marayu." "Kenan kina da wayo aka kawo ki nan Yola?" "E, shekaruna goma a lokacin, kuma ina daga cikin yara masu ƙwazo a gidan marayu, lokacin da ta ce ni take so da ƙyar shugaba ta bata ni saboda tana sona, kuma ina renon yara jarirai da aka kai gidan, saboda tun tasowata nima a gidan na tashi, shugaba ta ce min a ƙofar gidan aka ajiyeni da safe maigadi ya fito ya gani an ajiyeni da kayana masu kyau kuma da wannan fashin goshi da ɓullar hanci, tun ranar da aka bani labari duk baƙin da aka yi sai naga kamar iyayena ne suka zo ɗaukata, sai ga shi har yau babu amo babu labari, babban abinda ke bani mamaki shi ne mene na yi da mahaifiyata ta yaddani sai dai zuciyata tafi tunanin ni ɗin shegiya ce" "Bar faɗa!" Ya furta yana ɗan runtse ido. "Na daina ka yi haƙuri Yayana da ban san sunan shi ba" Murmushi ya yi, itama ta mayar masa "Kin rama kenan" "E mana" "Sunana Affan" "Yaya Affan zan riƙa cewa" "Niɗan jarida ne ina aiki anan Alfahar Radio" "Oh kai celebrity ne ko?" Tana rufe baki wasu maza biyu suka zo gurin. "Yallaɓai barka dai" Hannu ya miƙa musu suka yi musabaha sannan suka yi hoto. Ƙura masa ido ta yi kafin ta ce "Yaya nima ina son zama 'yar jarida" "A'a" "Meyasa" "Saboda ba aikin mata bane" "Amma ai akwai mata da yawa 'yan jarida" "E amma ni ba zan bar ƙanwata ta yi ba, saboda aiki ne mai haɗarin gaske" Sun ɗan taɓa hira kafin daga bisani suka tafi gida kamar yadda ya faɗa. An karɓeta hannu bibbiyu domin Mommy da Lawisa da suka ji labarinta kamar su haɗiyeta, Mommy ta ba shi umarnin ya mayar da ita makaranta ya kuma cigaba da kula da rayuwarta har lokacin da Allah zai kawo mata mijin aure. Har aka yi wannan buduri aka gama Badriyya bata sani ba. Lokacin da zai mayar da ita gida sai kuma ya ga unguwa da ban, unguwa ta masu kuɗin, kallonshi ta yi sannan ta yi murmushi "Yaya na san kana mamakin nan ko?" "E sosai ma, nan kuma ina ne?" "Shi ne asalin gidan da ake riƙona can gidan daka gani gidan kakar Umma ne matar da ta rasu jiya, acan na kwana dana ji kace za kazo shiyasa ban koma gidan makoki ba" "Nashwa wai ba su kula da rayuwarki?" Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce "Babu kulawa, lokacin da ta ɗaukoni na faɗa maka da ƙyar aka bata ni, sai da ta saki kuɗi sosai sannan aka bata saboda ni mace ce mai farin jini a gidan marayu, so bayan tazo dani nan na ga gata ta nuna min shi sosai da ita da maigidanta wanda nake kira da Daddy kuma nake ganin ƙaunarsa a gareta, so daga baya lokacin ina aji biyar na secondary sai Allah ya bata haihuwa tun daga lokacin sai ta fara nuna bambanci yanzu kam abin ya yi worst, Yaya wallahi in zan kwana biyu ban kwana gida ba babu wanda zai nemeni kuma in na dawo babu wanda zai tuhumeni hakanan nake rayuwa a gidan, Daddy ma baya kulani, yaran yanzu shekararsu 6 a duniya." Shiru ya yi na wani lokaci kafin ya ce "Karki damu Nashwa kin samu wa, kuma wanda zai riƙa kula da komai na rayuwarki, ni dai addua nake Allah ya sa su yarda ki cigaba da karatu" "Za su yarda insha Allah, kuma a kano nake so na yi karatu Yaya" "Meyasa?" "Kawai dai na fi son na bar gidan nan na yi boarding" "To shi kenan ba damuwa." Haka rayuwa ta cigaba da tafiya yaje ya gaisa da mariƙiyar Nashwa kuma a iya ganin farko daya mata ya gane bata da mutunci kalar tarbar da tayi masa kamar an mata dole, kuma daya nemi yana son mayar da Nashwa makaranta ta ce masa ya yi ita ba zata hana ba amma da kanshi zai janye saboda Nashwa daƙiƙiya ce bata fahimtar komai, ya ji zafin abin amma sai ya danne. Ta fara karatu, kuma tana mayar da hankali sosai sun shaƙu da Affan da kuma ahalinsa har ta kai ta kawo sai tayi sati biyu a gidan su Affan, shekara biyu da haɗuwarsu Mommy ta bijiro masa da auren Nashwa wanda shi kansa akwai hakan a ransa amma ganin tana karatu ya saka bai mata maganar ba. Lokacin ɗan Badriyya mai suna Fu'ad har an yaye shi, ranar kuwa daya koma da niyyar faɗa mata an saka ranar bikinsa da Nashwa wata uku sai ya ji kunyarta ta kama shi da kuma tsoron abin da ka je ya dawo saboda ya san tana da kishi matuƙa. Yana wasa da Fu'ad ta fito daga kitchen, har za ta wuce ya kirata ta dawo. Zama ta yi tare da cewa "Affan ina jinka sauri nake naje na gyarawa Fu'ad shimfiɗa" Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "Amma Badriyya mene ya canja ki haka? Na ga sam baki bani kulawar daya dace" "To ai gani na yi ka samu mai yi maka shiyasa ni kuma nake bawa ɗana kulawa dan tunda kai akwai wadda take yi ai ba sai na yi ba" "Wace irin magana kike faɗa?" "Na san ka gane abinda nake faɗa ko ƙarya na yi ne?" "Look Badriyya ni ba tashin hankali nake son yi a daren nan ba, magana nake so mu yi akan haihuwa" "Affan wai mene damuwarka dan Allah?" Ta furta cikin ɗaga murya. "Damuwata shi ne bana so kiyi planning ina son haihuwa Badriyya" Shima cikin shouting ya yi magana. "Wallahi planning har na sha magani na yi kuma allura, ba zan haihu ba har sai ɗana ya yi wayo ko zan ƙara haihuwa to sai Fu'ad ya shekara biyar a duniya" "Saboda ke kike bayar da haihuwar?" "A'a saboda ni na san ɗaukar ciki, laulayi, girma da nauyin ciki, naƙuda, uwa uba gashi ina reno har yanzu" "Wannan ba hujja bace" "Ni kuma ita na riƙe a matsayin hujja" "To kada ki ga laifina idan na auro wadda za ta haifa min 'ya'ya koda ɗari nace ina so" Murmushin gefen leɓe tayi sai kuma ta kalleshi "Affan ka fito fili kawai kace min aure zaka ƙara ba sai ka tsaya kwana-kwana ba" "A lokacin dana aure ki bani da wannan ra'ayin amma ciwon kan da kike bani da kuma yadda kike son daƙile haihuwa bayan kin san ina so shi ne dalilina da zai saka na ƙara aure, duk da haka ban yi ba, sai da Mommy ta bani umarnin auren Nashwa kawai naga ya dace na yi aure, Nashwa marainiya ce kuma dama tana da burin hayayyafa domin ta tara zuri'ar da bata da shi, na san ko yara nawa nake so za ta haifa min. Dan haka ina so ki sani an saka min biki da Nashwa nan da wata uku, zakije umra kuma zan canja miki ɗaki shi ne goronki na faɗar kishiya ko ince abokiyar zama" Cikin tashin hankali Badriyya ta miƙe tsaye, dan jin furucin nasa ta yi kamar sukuwar doki a ƙirjinta. "Aure, kuma ka rasa wa zaka aura sai Nashwa da ta san komai nawa, ta rainani, Affan wallahi baka isa ba" "Kece baki isa ba, kuma kin san Nashwa tana da tarbiyya da biyayya, idan kin so za ta miki idan kuma kin zubar da mutunci kin ga sai ƙaramar yarinya ta rainaki" "To na rantse da Allah akan wannan ba zan raga maka ba daga kai har Mommyn....." Mari ya tsinka mata wanda ya saka ta yi shirun dole. *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._* *_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_* Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* lLITTAFAN SUNE: 1-WUTAR ƘAIƘAYI 2-WA'ADI. 3-A CIKIN IDO.. 4-TAZARAR SO #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah [7/9, 9:43 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@sanazty _Facebook@SaNaz Deeyah_ Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe Facebook Page: https://www.facebook.com/share/16d2wDeqer/ *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ _Book 1_ ```🆓Page 13``` Da yatsa ya nuna ta tare da cewa "Ki shiga hankalinki, rashin mutuncin na ki ya tsaya iya ni kada ki yarda ki sako mahaifiyata a ciki." Kallonsa take sai kuma cikin ɓacin rai ta fuzgi Fu'ad ta yi gaba. Tsawon sati ɗaya sam basu kula juna, har ya saba da cin abinci a waje kafin ya dawo gida, da dare kuma sai dai yaje side ɗin Mommy ya yi dinner dasu ko kuma ya saka Lawisa tayi masa abinda yake so, dan baya son cin abincin masu aiki. Yau bayan sun gama cin abinci Mommy ta dakatar da shi, "Affan lafiya dai?" "Mommy lafiya ƙalau" "A'a Affan karka ɓoye min, ni fa mahaifiyarka ce, naga kwana biyu anan kake dinner at times har da breakfast, sannan kuma ita kanta Badriyya ina kula da ita yau kwana biyu bata zo ta gaishe dani ba, hakan ya nuna bata ɗaukeni a matsayin uwa ba." Shiru ya ɗan biyo baya kafin ya ce, "Mommy kiyi haƙuri, kin san na fara bincike akan kisan yaron da aka yi, so ni kaina ba a nutse nake ba, ko baccin kirki bana yi, amma ban san cewa Badriyya bata shigowa ba, Mommy tun ranar dana sanar mata an saka ranar bikina da Nashwa ta fara wannan gabar dani, ni kuma aikin da nake ne ya saka ban biye mata ba." "Matar ka ba mace bace Affan, sam baka yi sa'ar mata ba, sai dai fatan Allah yasa wannan auren da zakayi ya zama alheri ya sa matarka ta so ka ta kuma kula da kai" Shiru ya yi bai iya cewa komai ba. "Ka je kawai, da safe kafin ka wuce kazo zamu ƙarasa magana" "To Mommy" Sallama ya yi musu sannan ya wuce. Yana kwance a gado ta banko ƙofar har sai daya furgita dan lokacin bacci ya fara ɗaukarsa. "Lafiya kuwa?" "Ba lafiya ba, Affan wallahi indai ina da rai ba zaka ƙara aure ba" Ƙafafuwan shi ya zuro ƙasa lokacin da take faɗin "Sai dai bayan ranka ko nawa ran." "Badriyya ko dai kin sha wani abin?" "Babu abin da na sha amma wallahi ba zan taɓa bari na haɗa miji da wata banza ba, saboda kar ka kusanci wata macen na rabu da duk ƙawayena, duk wata mace da na san ba muharramarka bace bana yarda tazo gidana, sai kuma kawai yanzu kace zaka ƙara aure to wallahi sai dai ayi mutuwar kasko, ni da ita mu rasa gabaɗaya" Sai lokacin ta ɗago hannunta ya ga wuƙa, dan bai lura da ita a hannunta ba. "Me kike ƙoƙarin aikatawa ne?" "Kisa, zan kasheka in kuma kashe kaina" Ta furta tare da fashewa da kuka kuma ta nufo shi da wuƙar a hannu, cikin zafin nama ya riƙo hannun suka fara kokawa har sai da ta yankeshi a hannun hagu da ƙyar ya samu ya ƙwace wuƙar daga hannunta tare da kifa mata mari. A gurin ta zube tana kuka, shi kuma da sauri ya fita saboda yadda hannun ke zubar jini da alamu a jijiya ta yanke shi, a haka ya ƙarasa side ɗin Mommy har sun kulle ya yi ta bugawa. A parlour Mommy da Lawisa suka yi kiciɓus, "Mommy waye haka a daren nan?" "Ina zan sani ni har na fara bacci bugun ƙofar ne ya tayar dani." "Mommy jira anan bari na ji ko waye" "Kar dai ki buɗe sai kin tabbatar da mai bugun ƙofar" Kai ta gyaɗa sannan ta ƙarasa jikin ƙofar. "Waye" "Affan ne buɗe Lawisa." Jin haka ya saka ta buɗe da sauri, kasancewar barandar da haske ya saka ta ga jinin a ƙasa yana ɗiga kafin taga hannunsa daya riƙe gam "Subhanalillahi" Ta furta tana zaro ido, lokacin kuma Mommy ta ƙaraso. "Yaya Affan lafiya? Mene haka" "Me kika tsaya tambaya kina gani yana zubar da jini, maza ɗauko box kiyi masa dressing" Mommy ta janyoshi ciki sannan ta mayar da ƙofar ta yi mata key. Lawisa na gama yi masa dressing ya jingina bayansa da kujera tare da lumshe ido. "Affan!" Mommy ta kira sunansa, a hankali ya buɗe ido ya kalleta. "Waye ya maka wannan? Gidan dai babu alamun 'yan fashi sun shigo" "Mommy ku kwanta kawai da safe sai mu yi maganar, ni zan kwana anan kan kujera" "Duk ɗakunan gidan nan ace ka kwana a kujera, ko babu extra room ai ka kwana a ɗakina bare ma akwai. Kuma ka san ba zan iya bacci ko kuma sa mun nutsuwa ba tare da ka faɗa min abinda ya faru ba." Bai ɓoye komai ba ya faɗa musu, Mommy ta hasala sosai ta kuma ce lallai sai taje part ɗinsu a daren, da ƙyar Lawisa ta hanata saboda time ɗin ɗaya har da mintuna shidda, ta ce mata dan Allah koma mene a barwa safiya. Ranar Mommy bata samu bacci ba, sai dai shi Affan ya yi bacci saboda allura da Lawisa ta masa, Mommy kuwa tausayinsa kawai take, a ɗakinta ya kwana, ta kuma kwana tana nafila tare da yiwa Affan fatan samun mace ta gari. _06:30am_ Kamar a mafarki ta riƙa jiyo bugu, a hankali ta buɗe ido, ganinta ta yi anan kwance dandan ƙasa, tunda Affan ya mareta ya fita tasha kuka, ta kuma raba dare tana kuka bata farka ba sai wannan bugun ƙofar ne ya tasheta, in da Allah ya taimaka ma tana cikin jinin al'ada da ta makara sallar asuba. Jiki babu ƙwari haka ta ƙarasa jikin ƙofar a buɗe ma take kawai dai an tura ne, tana buɗewa ta ji saukar mari har biyu a kumatu guda, aikuwa har sai da hawayen dole ya zubo saboda azabar marin, ji tayi an fuzgi hannunta an fita da ita sai lokacin ta ga Mommy ce, hankalinta ya tashi sosai. Mommy kuwa bata sake ta ba sai a ɗakinta inda Affan yake kwance. "Gashi nan ki kashe shi" Jin haka ya saka ta fashe da kuka mara sauti, ta saka hannu ta rufe baki lokacin da hawaye suke ambaliya a fuskarta. "Kin san kisa ko? Za ki iya kisa saboda za a miki kishiya ko? To ki sani Affan aurensa babu fashi in ya so ga shi nan ki kashe sa, idan baki iya zama ki tafi mana ko an miki dole ne?" Kan ta a ƙasa ta kasa cewa komai sai hawaye kawai. "Tun da Affan ya aureki bai huta ba, dubi yadda kika mayar min da ɗa, duk kin bi ki zabura shi, wannan wace irin masifa ce ya ɗauko mana, kara nake miki amma ba wai dan ban san abubuwan dake faruwa ba, ana aure dan a jidaɗi amma shi Affan yana aurenki jindaɗi ya yanke masa" Mommy faɗa kawai take ta in da take shiga ba ta nan take fita ba, sai da ta gama tas sannan ta ce,"Ki tashi ki ɓace min da gani, kuma ki kira wani a cikin masu aiki a goge duk inda jini ya ɗiga." Da sauri ta tashi ta fice "Shashasha." Tana haɗa kaya tana kuka a haka Lawisa ta sa me ta. "Wannan ba mafita bane Aunty Badriyya." Ɗagowa ta yi idanunta a jiƙe da hawaye ta ce, "Lawisa wallahi idan na zauna komai zai iya faruwa" "E ki dai zauna ɗin, amma kin san tafiyarki za ta iya ƙara tunzura Mommy tunda har yanzu cikin fushi take" Zama ta yi gefen gadon ta saka hannu ta rufe fuskarta, Lawisa a hankali ta ƙarasa gabanta tare da dafa kafaɗarta. "Aunty wallahi Yaya har yanzu yana ƙaunarki you're his favorite, koda Mommy ta saka ya auri Nashwa kawai tausayin maraicin ta ya saka ta yi haka ba wai dan ba ta sonki ba, dan Allah karki yi abinda za ki ja Mommy ta tsaneki" "Idan har Affan yana so na meyasa ya karɓi tayin auren Nashwa?" "Saboda ya farantawa Mommy, ita kanta Mommy ba dan ta ƙuntata miki ta yi hakan ba." Haka dai Lawisa ta yi ya rarrashi har Badriyya ta janye maganar zuwa gida, Lawisa da kanta ta mayar mata kayan cikin wardrobe. _*11:00am*_ Yana shigowa ta kafe shi da ido, ko amsa sallamarsa bata yi ba bare ya samu damar da zata kula shi, ya ƙarasa kujerar da take ya zauna a gefenta sai ta yi sauri ta miƙe tare da canja kujera. Murmushi ya yi sannan ya ce, "Ina so na yi magana da ke." Ba ta ba shi amsa ba, ya cigaba da cewa, "Badriyya ina sonki, wallahi da gaske ina son ki, kuma har yanzu ina son ki" Baki kawai ta taɓe tana jin ɓacin rai na ƙaruwa. "Na san kuma kema kina sona tun da har baki son kowa ya raɓeni, ki sani wallahi a abubuwan da kike min in wani ne da tuni ya ƙara aure ko kuma ya rabu dake, sai dai ni ina duba ƙaunar da kike min da ita nake miki uzuri. Badriyya, Nashwa ba ta da matsala ni na tabbatar zuwanta gidan nan ba....." "Hold on da Allah, ka ga Affan idan maganar waccan yarinyar za ka yi zan tashi ne in tafi karka sake yi min maganarta saboda na tsaneta kuma kome zaka faɗa ba zan taɓa ƙaunarta ba koda na second ɗaya ne." "Amma ki sani wannan abubuwan da kike yi jahilci ne." "Ka faɗa kanka tsaye Affan, ka ce ni jahila ce ba sai ka tsaya kana kwaskwarima ba." "Hmmm! Ban san haka kike ba, gabaɗaya gani nake kamar canjo min ke aka yi" "Ai fiye da haka ma zaka gani muddin baka janye maganar auren nan ba to wallahi kisa ne ƙarshen ta sai dai a shigo da gawarta gidan nan." Tana gama faɗa ya yi daidai da shigowar Mommy da Lawisa wanda a kunnensu suka ji furucinta na ƙarshe. "Gawa kuwa wataƙila taki za a fitar a nan gidan, ki sani zan ajiye surukuntaka in kashe ki a duk ranar dana shigo na iske kin kashe min ɗa, ba zan bari hukuma ta ɗauki mataki ba saboda na san za a barki ne ki cigaba da shaƙar iskar duniya saboda yanzu ba a kashe wanda ya kashe, to ni kuma a lokacin za a bugani a jarida da sunan na kashe matar ɗana." "Mommy..." "Ka rufa min baki Affan, ba zan zuba ido ana wannan shashancin a gabana ba, shiyasa tun jiya na ce ka sawwaƙe mata amma shegen baƙin na ci ya hanaka, to wallahi ba zan lamunta ba." Tana gama faɗa ta wuce, Lawisa da ido kawai take bin Badriyya da kallo, kenan duk irin nasihar da ta yi mata bata ratsata ba. ****** ****** Kallon ciwon ta yi wanda har ya warke. "Yaya ko dai zamu haƙura da juna?" Murmushi ya yi sannan ya ce "Saboda wannan ɗan ciwon?" "A'a ba dan shi ba, ka san nima Aunty Badriyya tana kirana tana kuma min gargaɗi a kanka" "Oh wai bata daina ba?" "E, amma ban faɗa ba dan ka mata faɗa dan Allah" "Ina ɗaga mata ƙafa ne kawai saboda wannan aikin da nake." Kallon takardun tayi sannan ta ɗauka. "Habu Labbo Bala" Ta furta a fili tare da zaro ido. "Wannan ba ɗan takarar senator bane?" "Shi ne" "To me ya yi?" Gyara zama ya yi sannan ya ce "Wata biyu da suka wuce akwai wani yaro ɗan tiktok da ya fito ya yi magana akan 'yan siyasa har ya ce zai tona asirin 'yan siyasa guda biyar ya kuma lissafo sunayensu, kwana biyu da yin abin aka nemi yaron aka rasa kuma har yau babu labarinsa, jami'an tsaro sun yi burus da lamarin kasancewar ɗan talaka ne ya yi ɓatan dabo, to mu kuma 'yan jarida mun ƙi mu haƙura shi ne muka shiga rigar 'yan sanda" "To amma meyasa sai Labbo Bala kaɗai?" "Ba fa abinda ya kamata ki sani bane, ki bari idan komai ya bayyana za ki ji, amma maganar gaskiya dukkansu mun yi bincike akai sai dai zarginmu yafi karkata a kan sa, yanzu ma da na saukeki a gida zan je in cigaba da aikin bincike ne." "Yaya yamma ta yi fa, ya kamata kaje gida ka huta" "Hutu ba nawa bane a yanzu Nashwa, yawwa ina son inji nawa zan baki na event ɗin?" Ya faɗa dan ya kawar da waccan maganar. "E to! Hall already an kama kuma ka bayar da kuɗin komai, sai na lalle da gyaran gashi" "Okay zan tura miki ta account" "Zuwa next week zan wuce kano, yaushe zaku shigo?" "E to ina tunanin ranar dinner" "Yanzu har sai na kai wannan lokacin ban gan ka ba?" "Kwantar da hankalinki, keda zan ɗauko ki na kawoki gidana ki riƙa gani na kullum" Hannu ta saka ta rufe fuska, ya yi murmushi tare da faɗin "Nashwa akwai kunya" Ɗan lumshe ido ta yi tare da janye hannun. "Yaya duk ranar dana haihu ace wannan ɗana ne, kuma wanda muka haifa ni da kai, to gaskiya ban san irin farin cikin da zan yi ba. Ji zan yi duk duniya na fi kowa sa'a da ina ganin kamar ranar ba zata zo ba" "Kamar yau ne Nashwa, insha Allah za ki ga yaranki" "Allah yasa" "Amin." A gida ya sauketa, sai dai yana wuce wa Allah ya kawo mata empty napep ta tara ta ce yabi bayan Affan amma karya bari ya sani. Ganin sun nufi bayan gari abin ya bata mamaki, ta fito da wayarta tana ɗaukar guraren da suke wucewa, sai da suka shiga wata doguwar hanyar da babu titi sannan taga ya parker mota, ta yi saurin fita ta ɗauki 10k ta miƙawa ɗan napep ta ce ya juya da sauri dan ta san Affan zai iya cewa a juya da ita, yana juyawa Affan ya juyo a tsorace, ganin Nashwa abin ya matuƙar ba shi mamaki" Da sauri ya ƙarasa gabanta "Meyasa kika biyoni?" "Saboda ba zan iya barinka a halin nan ba" "Wane hali? Zuwanki nan akwai risk, shiga mota muje" "Muje ina? Kawai mu ƙarasa zan iya tayaka aikin." "Su waye nan" Jin magana da ƙarfi ya saka suka ɗaga ido, han go bodyguards ɗin Labbo Bala suka yi, sun saito bindiga. "Na shiga uku" Nashwa ta faɗa tare da fashewa da kuka. "Ki shiga mota" Ya furta lokacin da bodyguards ɗin suka yo kansu su huɗu. "Bindiga ce Affan kawai mu miƙa kai." Ganin za ta ɓata masa lokaci ya saka ya fuzgeta yana buɗa motar aka harba bindiga. *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._* *_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_* Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* lLITTAFAN SUNE: 1-WUTAR ƘAIƘAYI 2-WA'ADI. 3-A CIKIN IDO.. 4-TAZARAR SO #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah [7/9, 9:43 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@sanazty _Facebook@SaNaz Deeyah_ Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ _Book 1_ ```🆓Page 14``` Cikin azama ya jefata mota shima ya shiga, kafin kace me tuni sun fito da mota sun biyo bayansu, da ƙyar Allah ya saka suka kauce musu dalilin traffic daya tsayar dasu kuma suna wucewa su kuma aka ƙara tsayar dasu. Kai tsaye gida ya wuce hankalinsa a matuƙar tashe, tunda ya shiga layinsu yake horn duk ya furgita 'yan unguwar a haka ya ƙarasa gaban gidan nasu maigadi ya buɗe masa gate shi kuma ya shiga da mota, yana fakawa Badriyya ta fito daga side ɗinta "Kam bala'i" Ta faɗa tare da ƙarasawa inda suke. "Ke uban me ya kawo ki gidana?" "Kamarya? Dama yau ta fara zuwa gidan nan? Ko kin ga ta shiga side ɗinki?" Affan ya yi maganar rai ɓace. "Hmm! Ai tsiyar auren tsintacciyar mage kenan, tun kafin aje gidan mijin har an san juna a titi, banza karuwa koma na ce shegiya" Mari Affan ya wanka mata, ita kuma ta riƙe gurin "Akan wannan matsiyaciyar yarinyar wadda bama asan asalinta ba ka mareni?" Sai lokacin Nashwa ta fashe da kuka tare da wucewa side ɗin Mommy. "Idan har baki iya bakinki ba wallahi zan mugun saɓa miki" Ya furta cikin ɓacin rai sannan ya wuce rai a ɓace. Sosai Mommy ta yiwa Nashwa faɗa saboda abinda ta yi ba ƙarami haɗari bane, shi kansa Affan ɗin ba dan tana so yake wannan aikin ba. Haka Affan ya yi ta fushi da ita ko wayarta baya ɗagawa sai dai su yi communicating da Lawisa. Ya rasa ma abinda ke masa daɗi, ga biki, ga rusa masa shiri da Nashwa ta yi ga masifar Badriyya da taƙi ta ƙare. Har Nashwa ta tafi Kano ba su magana da Affan, ranar dinner kuwa har ya ce ba zai je ba Mommy ta tilasta masa ta ce tunda har ya yi niyya ba zai fasa ba, kuma itama Nashwa ai za taji babu daɗi idan bai je, haka ya shirya tsaf Lawisa ita kam tuni ta yi gaba. Yana saka trolley a but sai ga Badriyya ta fito da na ta trolley" "Ke kuma ina zuwa?" "Kano mana, ka san dai ba zaka tafi ka barni har tsawon kwana uku ba. Lokacin da nake tafiya in bar ki baki ga haka ba sai yanzu?" "Affan ni ban ce zan je wajen bikinku ba, ina son zuwa kano na daɗe da wannan burin saboda ina son na yi yawo, akwai ƙanwar Ammi a gidanta zan sauka dani da Fu'ad idan kun gama bikinku sai ka ɗaukeni mu dawo" "Hmmm! Idan ma wata fitina kike ji wallahi kan ki zai ƙare" Bata tanka masa ba ta saka kaya a but ya koma ya yi sallama da Mommy ta yi masa fatan alheri sannan suka tafi. Tun a hanya ya lura kamar akwai motar da take bin su amma dai ya share, sai da har suka fita daga Kano sun ɗauki hanya babu tsammani suka kara musu, ya kasa controlling saboda waccan motar babba ce, haka ya yi ta tura shi har sai da suka wurgashi ƙaton rami. Da ƙyar aka fiddosu daga mota sai dai Fu'ad dama ba a fito da shi da rai ba. Affan da Badriyya kuwa sun shiga Coma dan ƙarshe ICU aka mayar da su, sai dai tun da aka fitar dasu aka ƙona motar dalili kenan daya saka aka ɓoye aka sanarwa da mutane cewa sun ƙone ƙurmus. Shugaban gidan radio ya bawa Mommy shawarar ayi haka dan ana ganin accident ɗin an san set-up ne. Badriyya bata ɗauki lokaci mai tsayi ba ta farfaɗo sai dai ta samu karaya biyu a ƙafa sai kuma gani da ta daina yi da ƙyar aka samu aka mata wankin ido shi ne ta fara gani da glasses amma idan babu wannan glasses ɗin ba ta iya gane mutum sai dai kawai ta ga shadow. Nashwa kuma tun ranar aka aiko musu da ta rasu, sun yi baƙin ciki kuma basu samu damar ganinta ba, an ce masu a Kano za ayi jana'iza ba sai an yi doguwar tafiya da gawa ba, Lawisa a lokacin tuni ta taho jin accident ɗin su Affan tana hanya kuma ta riski rasuwar Nashwa itama ta shiga tashin hankali sosai. Tattarawa suka yi suka koma ƙasar germany anan aka cigaba da jinyar Affan bayan ya warke suka sayi gida a Abuja sai dai ta hana Badriyya fita ko nan da can, daga bedroom sai parlour, shi kuma Affan har lokacin kwance yake ba lafiya yana ta ƙara ramewa yana bushewa, wannan dalilin ya saka Badriyya take ganin kamar Mommy so take ta kashe shi, ita kuma Mommy ta tsani Badriyya dan gani take kamar itace ƙashin bayan matsalarsu. _Cigaban Labari_ Jin ana knocking ya saka shi kai duba ga ƙofar "Come in" Ya furta a sanyaye. Lawisa ce ta turo ƙofar ta shigo. "Yaya lafiya kuwa?" Ta faɗa tana ƙarasawa gabansa. Ɗan lumshe ido ya yi ya ja dogon numfashi ya sauke sannan ya buɗe idon a hankali ya kalleta "Lawisa yau na rabu da Badriyya " "What!?" Ta furta a tsorace. "Yes na sawwaƙe mata, amma sai nake ji kamar na rabu da wani bangare na rayuwata ne, tabbas Badriyya tana sona kuma so ne ya saka take nuna zafin kishi a kaina, akwai matan da ba su iya controlling kishinsu dole sai an lallaɓasu haka ya kamata na yi tun farko, sannan Badriyya bata da laifi a accident ɗina da kuma kisan Nashwa hasalima bata ji ba bata gani ba ta rasa ɗanta da kuma ganinta, gani nake kamar na zalunceta" Iska mai zafi ya furzar, Lawisa ta ce "Yaya wallahi kai ma baka da laifi, ina ƙaunar Aunty Badriyya amma gaskiya kishinta ya wuce na hankali, tun Mommy na mata kawaici har ta daina, ina ganin tsanar Aunty Badriyya sosai a idanuwan Mommy, duk da haka Mommy bata saka ka rabu da ita ba, ta ce tunda bata son ka zauna da kowa to gata gaka babu inda za taje, a lokacin kamanninka ma tsoro suke bamu Yaya, gani muke kamar ba kai ba. Daga baya sai Mommy ta yi tunanin gara kawai a faɗawa iyayen Aunty Badriyya gaskiya, to shi ne fa tun da aka faɗa musu suke ta tijarar sai an sakar musu 'ya" "Ni sam ban ga laifinsu ba" "Ai dama kai haka kake" Ɗan murmushi ya yi wanda kana gani ka san ba daga zuci bane. "Shi kenan na rasa Nashwa yanzu kuma na rasa Badriyya" "Amma ai kana da Sadiya" Ta faɗa tana kauda kai gefe. "Wace Sadiya kenan? Macen da take da aure" "Yaya ni fa ina ganin saboda mu suka tashi daga wannan unguwar" "Hmm! Sadiya ai bata yi sa'ar miji ba, dan kwatakwata bai san darajar mace ba" "Ƙilan a banza ya sameta shiyasa yake wulaƙanta ta" "A banza kamarya?" "Ko auren haɗi ko kuma wani abu makamancin haka" "Ki daina faɗa wallahi har raina abin ya sosa" "Tofah." Sai kuma ta yi murmushi. ***** ***** Knocking ta ƙarayi a karo na uku sannan ta ɗan dakata tana tunanin ko dai ba a gida ya kwana ba, har ta juya ta ji yana faɗin waye. "Saddiqa ce." Ta furta tana kallon gate ɗin. Ƙofar ya buɗe sannan ya mata iso ta shiga sai dai a farfajiya ta tsaya shi kuma da alamu bai ma daɗe da tashi a bacci ba ko kuma bugun get ne ya tayar da shi. "Yazid nazo ne akan batun saki, ka san an ce zuwa da kai yafi saƙo, na kira wayarka tun jiya bata shiga maganar gaskiya ko bacci ban iya ba, shiyasa na ce gara na yi sauko na sameka kafin ka fita." Shiru ya yi ya kuma sauke kai ƙasa. "Yazid ina jinka, dan Sadiya a gidana ta kwana, ko Mameey bamu sanarwa ba na ce zan yi fixing matsalar ba sai ta sani ba." "Saddiqa ki bawa Sadiya haƙuri amma a yanzu ba zan iya dawo da ita ba, umarni ne daga manya ba laifina bane." Saddiqa ta kasa cewa komai, ta sandare a gurin idanunta cak akan Yazid. "Zan shiga ciki saboda ina son fita kasuwa da wuri, nagode ki gaida gida. Anan tsaye ya barta ta kusa mintuna goma kafin taja ƙafafuwanta da suka yi sanyi ta bar gidan. Da ƙyar ta iya driving kanta zuwa gida. A parlour ta tarar da Sadiya zaune kan kujera tana goge hawaye, Najma da Ihsan sun ɗora kansu a cinyarta, ji tayi kamar ta fashe da kuka. Ta ƙarasa gurin sannan ta ja yaran, muje in haɗaku da Dije ta muku wanka ko" "Maama! meyasa Mommy take kuka?" Najma da tafi hankali ita tayi tambayar. "Mommy bata da lafiya muje ayi wanka ayi break ko?" Haka taja yaran ta shigar dasu ta saka mai aikinta tayi musu wanka ita kuma ta koma gurin Sadiya. Jin an dafata ya saka ta ɗago rinannun idanuwanta ta sauke kan Saddiqa "Sadiya kiyi haƙuri babu wanda yafi ƙarfin ƙaddara" Jin haka ya tabbatar mata da ba a dace ba, a take ta saki kuka a fili, ita kaɗai ta san irin ɗaci da raɗaɗin da take ji. "Ban taɓa tunanin ko a mafarki Yazid zai iya rabuwa dani ba, na ɗauka cewa ko an sakawa Yazid wuƙa a wuya aka ce ya sakeni zai ƙi, sai ga shi salin alin ya sakeni, ya ruguza duk wata yarda dana yi masa" Ta ƙarasa tana sake rushewa da kuka. "Ni kaina na yi mamaki amma ba yanzu ne lokacin tattauna maganar nan ba, kiyi haƙuri, kin ga Habibi bai tashi ba bana so ya gane abinda ke faruwa dan ban faɗa masa komai ba, please tashi mu koma ɗaki, haka ta kama hannunta kamar ƙaramar yarinya suka nufi ɗakin, kan gado ta kwanta ta cigaba da kuka. _01:30pm_ Tana durƙushe kan abin sallah tana hawaye ga zazzaɓi da taji yana ƙoƙarin rufeta, idanuwa kuwa ƙarfin hali kawai take tana buɗesu saboda kanta da taji yana barazanar tarwatsewa, ko magana bata son ji saboda jin ta take har cikin ƙwaƙwalwa. Saddiqa da ta shigo da tray akan table ta ajiye sannan ta ƙaraso gabanta "Ki tashi kici abinci Sadiya, kar damuwar wanda bai damu dake ba ya saka ta miki illa" Ɗagowa tayi a hankali fuskarta jiƙe da hawaye ta kalli Saddiqa "Kina nufin Yazid bai damu dani ba?" "A'a ba haka nake nufi ba" "Aunty dan Allah ki tashi mu tafi gida, ina so naga Mameey ji nake kamar zan mutu Aunty" Rungumeta Saddiqa ta yi sai lokacin ta ji zafi zum jikinta. "Baki da lafiya ai, zazzaɓi ne a jikinki" Bata gama faɗa ba kawai taga idanuwan Sadiya na juyewa, ta ɗan fara jijjigata kawai taga baƙar ƙwayar tayi sama "Na shiga uku wayyo Allahna" Ta furta tare da miƙewa da gudu tayi ɗakin Ahmad. "Lafiya ya faɗa yana kallonta" "Habibi Sadiya ta mutu na shiga uku." "Wane irin magana kike faɗa haka" Ya furta tare da miƙewa da sauri suka yi ɗakin da Sadiya take. Yana taɓa kumatunta ya ɗauke hannu yadda yaji mugun zafin da jikinta ya yi. "Maza samo ruwa da towel" Da sauri tayi toilet ta ɗebo ruwan ta dawo ta miƙa masa, kallonta ya yi sannan ya ce "Ki nutsu ki shafa mata ko ina a jiki, tsugunnawa tayi gaban Sadiya shi kuma ya koma gefen gado ya zauna, ta cire mata hijabin sannan ta shafa mata sai da tayi second round sannan Sadiya ta sauke ajiyar zuciya ta dawo daidai sai kuma ta saki kuka. "Kin ga ku sameni a waje bari na fito da mota a kaita asibiti. ****** ****** "Saki?" Mameey ta faɗa tana kallon Saddiqa, ita kuwa tana durƙushe a ƙasan carpet ta kasa cewa komai tunda ta bawa Mameey takarda. "Saddiqa wai Yazid ɗin ne ya bawa Sadiya takardar nan?" "Mameey ni kaina ban gaskata ba, tun jiya abin ya faru amma na kasa sanar miki na ce in akwai yadda za ayi a gyara, da kaina naje gidan na sameshi amma ya gaskata min sakin ya kuma bani haƙuri" "Haƙurin banza haƙurin wofi me zamuyi da haƙurinsa wulaƙantacce irinsa, kin ga abinda nake gudu ai, kin ga tsiyar auren talaka, wancan gida da ɗan ƙaramin shago da wannan akurkin motar sune suka saka ya fara jin kansa wani shege ko, bayan da kuɗinta ya yi arziƙin, to bari komai ya lafa wallahi duk abinda ya san na ta ne ita ta ba shi sai ya dawo mana dasu har gadonta daya cinye" Mameey faɗa sosai tayi ta inda take hawa ba ta nan take sauka ba. Kwanan Sadiya biyu a asibiti aka sallamota, sai dai Mameey kullum cikin faɗa take bata tsayawa ta rarrasheta bata kula da damuwar da take ciki, yaran kuma ta rantse sai an mayar dasu gurin ubansu, dama bata wani shaƙu dasu ba, ba ta sakar musu fuska, haka ya ƙara jefa Sadiya cikin tashin hankali da kuma tunanin halin da zata shiga idan har aka rabata da yaranta. *Bayan Wani Lokaci* Sadiya tuni ta shiga sati na biyu da gama idda, sai dai bata fita ko ina, dama Najma ce take sintirin kaiwa school to ganin tana da damuwa sosai ya saka Saddiqa ɗauke su gabaɗaya, ga kuma Mommy da take nuna ba ta son yaran. Surayya data fito daga bedroom da waya a hannu ta ƙarasa parlour ta tarar Sadiya tana kwance kan three seater tana barci. "Faruq ka ga ma bacci take" Ta faɗa tana ɗan haska masa sannan ta ɗauke. "Ƙara haska min ita please" "Kai ban haskawa idan kana son ganinmu ka dawo mana, ka je kayi zamanka a ƙasar da ba taka ba" "Wallahi kin raina ni da yawa Surry amma zan yi maganinki" Dariya tayi tana zama kan kujera "Amma dai Yazid baya da mutunci wallahi" "Babu Uncle ɗin?" "Dama ai kara ce yanzu kuwa babu tunda bai san ta ba, kuma kun min laifi da kuka kasa sanar mini" "To ai ba abu bane mai daɗi bare a faɗa, ba ga shi yanzu ka ji ba" "Haba Surayya sai da har ta gama idda, nima fa ɗan uwanku ne damuwar nan har dani ya kamata ayi sharing" "Aunty Sady dai har yanzu taƙi barin damuwa" "Dole ta damu mutumin nan azzalumi ne, ai insha Allahu cikin satin nan zan dawo, dan Allah idan ta tashi ki kirani mu gaisa zan bar data kunne" "Ba ka da matsala" "Yawwa thank you" "You're welcome." **** Tana shafa addu'a Surayya ta ƙaraso tare da zama gefen gado. "Yau dai kin samu nutsuwa Aunty Sady dan na ga har bacci kika yi" "Ina so in fitar da komai ne a raina, a baya gani nake kamar ban rasa Yazid ba amma tun da na gama idda bai mayar dani ba na san shi kenan kuma" "Na ji daɗi da kika fara manta komai, Allah yasa haka shi ne mafi alkhairi" "Amin Surry" "Yawwa ɗazu kina bacci mun yi waya da Farouq shi ne ya ce dan Allah idan kin tashi na kira shi ku gaisa" "Ina fatan baki faɗa masa mun rabu da Yazid ba?" "Ya sani fa, amma Mameey ta sanar bani ba. Na kirashi?" "E, kira shi" Ta furta a sanyaye. Yana ɗagawa ya ce "Mara kunya yane?" "Kai fa dan ka fara tara saje kake ganin ka kai ko? Ko da ake ce maka age mate ɗina ai na baka watanni" "Baki da kunya wallahi, shiyasa tuntuni naso Mameey ta yi mini jumping amma babu komai ai yanzun ma na san an bigger than you" "Girman jiki ba, ka je ƙasar wasu kayi kane kane" "Ke kuma abin ya tsone miki ido ko?" "A'a a wane dalili" Sadiya dai tana jinsu suna ta shirmensu kafin daga bisani ta ce "Ni ka ga, ga Aunty Sady ɗin, shi ne dalilin kiran" "Oh wai dama tana nan kina min rashin kunya bata tsawatar miki ba" "Kai ka sani kuma" Ta faɗa tana miƙawa Sadiya waya. "Ga shi bari naje ɗakin Mameey kafin ku gama." Tana bata ta fita. Bai ce komai ba ya tsaya kawai yana kallonta har sai da ta ce "Yaro jira kake na gaidaka?" Ɗan lumshe ido ya yi, har cikin ransa yake jin muryarta tana masa daɗi. "Na yi tunanin zamu gaishe da juna ne" "Hmm ok to ina yini Faruq." Ta furta da gatse. "Lafiya lau ya yara?" "Kai!" Ta furta da mamaki, sannan ta sake yin dariya. "Aunty Sady ashe har kin gama idda ban sani ba, gaskiya ba a kyauta min ba" "To ai baka da lafiya, taya za a faɗa maka abinda ba na farin ciki ba" "Hakane Aunty amma kuma duk da haka ya kamata ace na sani, saboda yanzu inda wani ya min sakiyar da ba ruwa fa" Da sauri ta kalli ƙofa. Ya yi murmushi "Kina tsoron kar wani ya ji ne? To ai babu amfanin ɓoyewa tunda a yanzu zan iya shigowa cikin manemanki" "Faruq wai kana da hankali kuwa?" "Indai akan soyayyarki ne bani da shi SADIYA! INA SONKI kuma na shirya yin ko wane irin yaƙi dan ganin na mallakeki" "SADIYA!" Ta maimaita. "Ni ne a samanki saboda nan gaba kaɗan zaki cigaba da gaisheni kamar yadda kika yi yanzu, kuma abu ma in za ki bani sai kin rissina, zan zauna dake tare da yaranmu Najma da Ihsan dama wanda zamu haifa a gab....." "Ya isa haka" Ta furta tare da buga wayar akan tiles, a daidai lokacin Surayya ta shigo ɗakin. *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._* *_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_* Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* lLITTAFAN SUNE: 1-WUTAR ƘAIƘAYI 2-WA'ADI. 3-A CIKIN IDO.. 4-TAZARAR SO #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah [7/9, 9:43 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@sanazty _Facebook@SaNaz Deeyah_ Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ _Book 1_ ```🆓Page 15``` "Aunty Sady lafiya kuwa" Surayya ta faɗa tana ɗaukar wayarta, Allah ya taimaka bata fashe ba. "Mene ya faɗa miki wanda har ya ɗaga miki hankali haka?" "Surayya idan Faruq ya kira ko ya ce ki haɗa mu ka da ki kuma kawo min" "Wai lafiya kuwa?" " "Kin dai ji abinda na faɗa ai, ki fita ina so na kwanta" Kallonta Surayya ta yi sannan ta wuce. ****** ****** "Yaya Affan" Ta ambaci sunansa sannan taja kujerar dining tana facing ɗinsa. "Yaya nazo maka da wani albishir" "Na me?" "An saki Sadiya kuma har ta gama idda" "What?" "Wallahi dagaske ɗazu wannan ƙawar tawa take faɗa min" "Anya mijin yarinyar nan yana da hankali kuwa?" "Ya naga kamar baka ji daɗi ba, na ɗauka za kayi farin ciki" "Haba Lawisa, yanzu sai a saki mutum na yi farin ciki, to mene ribata?" "Gani na yi yanzu kana da damar zuwa gurin ta" "Ni dai duk da haka ban ji daɗi ba, kuma ina fatan Allah yasa bani ne sila ba, saboda naga soyayyar mijinta ƙarara a idanuwanta" "To ai kuma ka san aure rai ne da shi" "Hakane, Allah ya sa haka shi ne mafi alkhairi" "Amin ya Allah" "Zan samu na je kuma zan nemi aurenta insha Allah" "Allah ya sa a dace, amma dai da wuri za ka je ko?" "Ai ban san gidan ba, kuma gaskiya ko na je ba kai tsaye zan fito ba." "Kar fa ka tsaya jan aji ayi mana sakiyar da babu ruwa" "Hakan ma ba zai faru ba bi'iznillah amma kin san dole sai na ga kamun ludayinta" "Hakane, to Allah ya sa a dace" "Amin." _Bayan Sati Ɗaya_ Yana saka kaya a mota wayarsa ta fara ringing, ganin Ayda ce ya saka ya ɗaga tare da rufe motar sannan ya shiga driver seat lokacin ya furta "Hello" "Hi! Ya kake, hope you're in good condition" "Yeah, fatan kema haka" "Alhamdulillah, har yanzu dai mun ji ka shiru babu ziyara" "Wallahi ina taso na zo so lectures sun ɗan riƙeni." "Farhan ma tana taso ka zo ku yi hira, na ce tunda yau saturday let me call you na ji ko you are free" "Ayya, kin san yanzu haka bana gida but insha Allah ƙila na shigo gobe" "Haba why not ka zo yau?" "Ya yi late coz kin ga na ce miki na fita, ba zan gama abin da nake har na samu shigowa." "Allah ya kaimu goben" "Amin ya rabbi." Kai tsaye gidan su Sadiya ya nufa sai dai gaban shi na ta faɗuwa, adireshi ya bi har ya ƙarasa unguwar sai dai ya yi matuƙar mamaki da aka nuna masa gidan, _kenan da gatanta take auren wahala, lallai tana son mijinta._ Ya fito daga mota yana neman yaron da zai tura ya yi masa sallama. Mameey da Surayya ne zaune a parlour lokacin da yaron ya shigo "Wai ana kiran Sadiya" "Sadiya kuma?" Yaron ya gyaɗa kai. "Waye?" "Wani ne a mota" Jin haka ya saka Surayya taɓe baki "Yanzu haka Yazid ne dan na san shi ƙaɗai ne zai zo gurinta tunda ba fita take ba bare asan ta fito." "To mene ya kawo shi, ko zuwa ya yi ya ƙara ɗaga mata hankali?" "Wa ma ya san masa" "Jeki ki ji da wacce yazo." Da ɓacin rai Surayya ta fita sai dai ganin baƙon mutum ya saka ta yi turus. "Sannu da zuwa, ina wuni" Ta furta tana ƙara kallonsa a ranta tana yaba kyawunsa. "Lafiya lau, Sadiya ko tana nan?" "E tana nan, bismilla" Ta furta tare da juyawa. A farfajiyar gidan ta ɗauko kujeru biyu ta ajiye sannan ta ce "Bari na kirawo ta" "Okay thanks" Har ta juya sai kuma ta juyo "Wa za a ce mata?" Murmushi ya yi wanda suke ƙara masa kyawu ya ce "Baƙo ne" Juyawa ta yi ta shiga. "Mene ya kawo shi" Shi ne abinda Mameey ta faɗa. "Ba fa Yazid bane wani ne da ban" "Wani wa?" "Wallahi ban sani ba, na dai ce ya shigo wataƙila ita ta san da zuwansa" "Je ki kirawo ta" Da sauri ta wuce ɗakin Sadiya. A kwance ta tarar da ita ta ƙurawa guri ɗaya ido. "Ki fito kin yi baƙo" Jin haka ya saka ta miƙe tare da faɗin "Baƙo kuma?" "E, yana farfajiya" "Waye?" "Wallahi ban sani ba" "Baki sani ba kuma kika ba shi damar shigowa?" "Bai min kama da macuci ba, ki fito dai Mameey ma na kiranki" Tana gama faɗa ta fita. "Mameey ga ta nan zuwa, bari na kai masa ruwa" Yana danna waya ta ƙarasa tare da ajiye ruwa a gabansa. "Su Najma ba sa nan ne?" Ɗagowa ta yi ta kalleshi kafin ta ce "E, suna gidan Yayarmu." "Okay. Amma ban sanki ba, but naga kuna yanayi da Sadiya, mene sunanki?" "Sunana Surayya, kaima ban gane ka ba" Murmushi ya yi tare da faɗin "Za ki sanni soon" "Okay, ga ruwa bismilla, bari naje" "To nagode Surayya." "Ni ban yi da kowa yazo ba gaskiya" Ta faɗa tana ƙara tsuke fuska, lokacin da Surayya ta shiga. "Ai ba zuba ido zamuyi muna kallonki ba, kuma ba dole sai kin cewa mutum ya zo sannan zai zo ba" Zama Surayya ta yi tare da faɗin "Har Najma ya tambaya, amma kuma he's matured" "Tashi kije karki bar mutum tsaye shi kaɗai" Jiki babu ƙwari haka ta miƙe ta fita. Turus ta yi a lokacin da ta gan shi, ta ji gabanta ya yi mummunar faɗuwa. "Ki ƙaraso mana." Ya furta yana kallonta, bata musa ba ta ƙarasa tare da jan ɗayar kujerar ta zauna. "Na san kin yi mamakin ganina a gidanku ko?" "Sosai kuwa, dan ban yi tunanin ka sani ba" "Kin san bahaushe ya ce mai son ɗan tsuntsu shi yake bin sa da jifa" Shiru ba tayi magana ba. "Sadiya ban san kin fito daga gidan mijinki ba, sai yanzu ake faɗa min har kin gama idda." Ji tayi wasu hawaye masu zafi sun zubo mata babu shiri, ta saka hannu da sauri ta goge "Kiyi haƙuri ban san maganar za ta ɓata miki rai ba da ban yi ba" "Me kake buƙata?" "Dama nake so ki bani, Sadiya ina so na aureki" Murmushi ta yi wanda kana gani ka san na yaƙe ne. "Dan...." "Ka ga malam ɗan dakata" Ta furta tare da miƙewa tsaye. "Bana fidda ɗayan biyu shigowar ka rayuwata ya saka aka tilastawa mijina ya sakeni, bana sonka kuma har abada ba zaka taɓa mallakata ba" Tana gama faɗa ta juya, yana kiranta amma bata tsaya ba. Tana shiga suka kalleta, sai dai yadda ta wuce da sauri kuma tana hawaye ya saka suka gane lalle akwai matsala. "Surayya je ki duba ki ga lafiya" Da sauri ta fita, sai dai a tsaye ta gan shi kamar jiran fitowarta yake. "Am...dama Mameey ce ta ce na zo na ji ko lafiya, saboda mun ga Aunty Sady ta shiga da kuka." Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce "Surayya ban sani ba, amma....am...ko dan babu komai" Murmushi tayi tare da cewa "Karka damu, ka faɗa min koma mene" "Surayya!" "Na'am" "Maganar gaskiya na kamu da son yayarki, sai dai ita ba tani take ba, gani take kamar nine na zama silar fitarta daga gidan miji" Da mamaki ta ce "Dama kun san juna ne?" "E, amma ba can ba, na san ta gab da za ta samu matsala da maigidanta" "Amma ai hakan ba zai zama hujja ba" "A taki mahangar kenan amma ita yanzu haka take gani." "Kayi haƙuri, insha Allahu zan yi magana da ita, kuma idan har da gaske kake zamu shawo kan ta, zan yi magana da Mameey" "To shi kenan, zan iya samun number ɗinki dana Sadiya?" "E, bara na baka" Karɓar wayarshi ta yi ta saka masa numbers ɗinsu. "Akwai kayan dana tahowa da su Najma, ko zamu je mota sai ki karɓa" "To ba damuwa" Ƙatuwar baƙar leda ne bata ma san mene a ciki ba, ta karɓa tayi godiya. Bayan ta gama faɗar duk abubuwan da suka faru Mameey ta girgiza kai, "Har yanzu akwai ƙuruciya a tattare dake Sadiya, yanzu shi daya ƙwatar miki 'yanci shi kike kallo a matsayin maƙiyi" "Mameey da ace bai shigo rayuwata ba, da duk haka bata faru dani ba" Ta faɗa tana share hawaye. "Shi kenan, kina budurwa ma ban miki dole ba, bare yanzu da kike da damar zaɓen mijin aure" Miƙewa tayi ta bar ɗakin Surayya ta dafa Sadiya ta ce "Ki jarraba ki gani, wataƙila shi alheri ne a gareki, karkiyi gaggawa karɓarsa kuma karkiyi gaggawar korarsa, ki tsaya kiyi tunani sosai Aunty Sadiya" "To shi kenan, nagode sosai Surry" "Karki damu Aunty Sady, ga kayan daya kawo wa su Najma" "Ok, mun gode" Suna buɗewa suka ga kayan wasa na yara sai kuma chocolates da nau'ikan biscuits, dasu ice cream" "Lallai wannan da gaske yazo" "Hmmm! Kin ɗauka kashe kuɗi ne so?" "A'a amma ai suna daga cikin sunnonin soyayya" Murmushi kawai Sadiya ta yi dan a cikin damuwa take. ****** ****** Da sallama ya shiga bedroom ɗin Mommy. "Affan ka dawo kenan" "E Mommy" Ya furta tare da zama sannan ya gaisheta. "Dama magana nake son yi da kai akan yaran ƙawata dana ce kaje ka gani, kuma na ji baka ce komai ba" "Mommy ai bamu gama fahimtar juna ba." "Duk da haka ina son dai na san a cikinsu wacce ce tayi maka" Shiru ya yi, dan har ransa baya jin son ko wacce a cikinsu, shi a yanzu Sadiya ce kaɗai a gabansa. "Mommy akwai wata dana haɗu da itane, so gaskiya hankalina yafi karkata a kanta" "A cikin Kano? Yaushe muka zo bare har ka fara son wata, ko shekara bamu yi ba" Shiru ya yi tare da sauke kai ƙasa. "Affan!" "Na'am" "Ka faɗa min Farhan ko Ayda wace ce ta yi maka?" Shiru ya yi baice komai ba. "Kai nake sauraro" "Mommy na fi sabawa da Ayda" "To na baka sati biyu kaje ku fahimci juna da ita" Shiru ya sake yi har sai da ta ce "Je ka na sallameka" Miƙewa ya yi jiki babu ƙwari ya bar ɗakin. Yana shiga ɗakinsa ya faɗa kan gado, idanuwansa na kallon sama, ya rasa me zai yi. Tabbas yana son Sadiya amma baya so ya yi wa Mommy musu, wayarsa ya janyo ya kira Lawisa, tana ɗagawa bai jira ta ce komai ba ya ce "Lawisa kina ina ne?" "Ka san yau evening nake, ina asibiti" "Ina son ganinki ne, kaina ya ɗauki zafi" "To ko zaka zo?" "A'a, ban daɗe da dawowa gida ba, kuma a gajiye nake" "Okay to ko kawai mu yi magana a waya" "No kar ki damu, idan kin dawo gida sai mu yi magana." ****** ***** "Gaskiya Yaya kayan nan sun yi kyau sosai, kuma sun dace da Aunty Salma" Murmushi Umma ta yi sannan ta ce "Ai yanzu ne zai san ya yi aure, ba waccan sakaran mai farar ƙafa, yanzu ga shi ƙofofin arziƙi suna ta buɗe masa" Fatima ta yi murmushi, sai kuma ta juyar da kai ganin yana aika mata harara. "Shi fa Yaya Yazid har yanzu baya so a faɗi laifin Sadiya" Maryam ta faɗa tana taɓe baki. "Ke ki kiyaye ni, kar na sake jin kin furta wata kalma akan Sadiya" "An taɓo uwarka ba, ai dole ka nuna ɓacin rai. Ni Sadiyar nan ban san wane malami ke mata aiki ba data shanye ka" Shiru ta yi sannan ta kuma cewa "Kuma a cikin satin nan kaje ka karɓo yaranka ni zan riƙe kafin Allah yasa ayi auren su koma hannunka, dama ai yaran ne za su saka ka riƙa tunaninta ko ka samu damar zuwa gurinta to ka karɓo su" Ɗan lumshe ido ya yi, yana jin zafi a ransa. "Ko baka ji abinda na faɗa ba?" "Na ji." Ya furta sannan ya miƙe. "Zan wuce" "Allah ya taimaka" "Amin." Ya furta a sanyaye. Yana fita ya tarar da Lukman tsaye yana jiransa. "Ya naga ka fito rai ɓace?" Da jikin get ɗin gidan ya jingina sannan ya ce "Lukman ji nake kamar na cuci Sadiya" Murmushi Lukman ya yi tare da cewa "Oh kama ne ma? Ai ka cuceta, ni kaina kawai dole ta saka nake tare da kai" "Na san ba zaka taɓa fahimta ta ba, amma rabuwata da Sadiya shi ne maslaha" "A naka tunanin da hange mara tushe, shi kenan dai Allah yasa wadda za ka aura ta zame maka mace ta gari" "Amin, amma bana jin zan samu madadin Sadiya a wannan duniyar" "Kuma dai." _*Bayan Sati Ɗaya*_ Tana zaune taji shigowar motoci, haka nan taji gabanta ya tsananta faɗuwa. Shigowa da trolley da Surayya ta yi ya saka ta miƙe tsaye, kafin ma ta yi magana Faruq da Saddiqa sun shigo, yana ɗauke da Ihsan a kafaɗarsa. "Ke dai Allah ya shiryeki" Saddiqa ta faɗa tana harararta, Najma kuma da gudu ta rungumeta, a lokacin Mameey ta fito. "Baƙin Nigeria sannu da sauka" Murmushi ya yi yana sauke Ihsan, sannan ya ƙarasa gaban Mameey ya durƙusa har ƙasa ya gaisheta. "Ka tuno damu kenan" "Mameey a kullum kuna raina tun ranar dana samu kaina" "Kuma shi ne ka yi zamanka" "Karatuna naso in ƙarasa kuma kewarku ta hanani zama na ce bari nazo na ganku sai na koma" Sai da duk aka zauna sannan Sadiya ta ce "Yaro sannu da zuwa" Bai tanka mata ba, ya yi kamar ma bai san tana yi ba, sai da Surayya ta ce "Yaro ana magana fa" "Kin ga ki kiyayeni, karmu fara tun yanzu, sunana Faruq kuma ni bana cin miƙe, bata rakani ba sannan da zan dawo bata je taroni ba" "Gaskiya dai bata kyauta ba, nima yanzu na gama mata faɗa akan haka" Cewar Mameey, ita Sadiya bata ce komai ba dan tayi imani Faruq ya gama raina ta. Miƙewa ya yi tare da cewa "Mameey an gyara ɗakina?" "Tun jiya na saka aka gyara ma tas" "Bara naje na ɗan watsa ruwa na huta" "Ya kamata dai, abinci fa?" "Na ci a jirgi sai dai ko bayan magrib" "To shi kenan, amma fa karkayi bacci ka san ba a son baccin yamma" "Okay." Har ya fara tafiya ya ji Surayya na faɗin "Yau Affan zai zo gara da Allah yasa kina nan Aunty Saddiqa yana ta so ku gaisa" "Wai saurayin Sadiya?" Kai Surayya ta gyaɗa saboda haka Faruq bai ji tayi magana ba, lokaci guda ya ji zuciyarsa na ɗaci. "Sadiya wai yana da wani aibu ne?" "A'a Aunty amma ni bana so 'yan uwan Yazid da shi kansa ya ga kamar na kashe aurena ne saboda Affan." "To ya gani mana, mutumin daya sakeki babu wani dalili mene na yi masa kara?" Ɗan lumshe ido kawai tayi, wayarta data fara ringing ta kalla. "Ko shi ne?" "E, to tashi ki fita" "Haba kai tsaye haka babu wani jan aji" "Ma za ja ajin ya tsinke" Allah ya sa lokacin Mameey ta bar gurin. Miƙewa tayi tare da kara wayar tayi ɗakinta. "Lu'ulu'u" Shi ne sunan daya ke kiranta da shi duk da ta ce bata so amma yaƙi ya daina faɗa. "Sady kina jina kuwa?" "E, ina ji" "Oh shi ne kika ƙyaleni, ba dai zan yi zuciya ba" "Uhmm" Ta furta kawai. "Ina ƙofar gida" "To ka shigo mana" "Ban isa na shigo ba har sai kin min iso" "To na yi maka ka shigo" "Nagode lu'ulu'u" Bata ɓata lokaci ba ta shirya ta fita sai baza ƙamshi take. "Aunty da alama an faller ba" Juyowa tayi ta kalli Surayya lokacin za ta wuce tayi maganar. "Sorry" Ta furta tana rufe bakinta da hannu. "Ni dai ina jira yazo ya gaisheni" "Aunty ni fa har yanzu ba wani sakewa nayi da shi ba" "Za ki sake ai" Ta furta tana murmushi. Suna zaune akan kujeru suna taɓa hira sai dai har lokacin bata sake da shi ba, ko magana ya yi wani lokacin bata cewa komai. "Sady dama ina so naje na gaishe da Aunty Saddiqa so kuma tunda tana nan sai kawai na gaisheta anan" Kallon shi kawai tayi, ta tabbatar ya girmi Saddiqa amma saboda yana da respect baya iya kiran sunanta kai tsaye. "To babu damuwa" Ta furta a sanyaye. Cikin gida kuwa Faruq yana shiryawa ya fito. Saddiqa ta kalleshi ta ce "Na ɗauka zaka ɗan kwanta ka huta" "Ki bar hutun nan Aunty Saddiqa, gara in zo mu sha hira da ku" "Aikam gara ka zauna ka bamu labarin abroad, kaga mu ko ƙafar jirgi bamu taɓa takawa ba, har gara Aunty Saddiqa da Mameey sunje hajji sun je Umra amma ni da Aunty Sady ne bayin Allah" Murmushi ya yi tare da faɗin "Kuma zakuje insha Allah, ina Aunty Sady?" "Tana waje tayi baƙo" "Baƙo kuma?" "E, wanda zata aura, ka gan shi kuwa wallahi handsome ya fi Yazid komai" Cewar Surayya. "Bari naje na gan shi" "Kai dilla zauna zai shigo gaida Mameey ai" "Ba jira fa" Ya faɗa tare da wucewa. Saddiqa ta yi murmushi tare da cewa "Ke da kika san halinsa" Tun da ya tunkarosu Sadiya ta ƙura masa ido, dan ta ga ya haɗe ransa sosai. Yana ƙarasawa ya kalleta "Mameey ta ce ki sallamesa kizo" "Lafiya kuwa?" "Nima ban sani ba" Ji tayi gabanta ya faɗi. Affan kuma ya miƙawa Faruq hannu sai dai ga mamakinsu kawai suka ga ya juya, a daidai lokacin kuma aka turo ƙofa, shigowar Yazid ya saka Sadiya miƙewa tsaye shi kuma Faruq ya juyo. *SAURA 5 PAGES MU GAMA FREE PAGES* *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._* *_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_* Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* lLITTAFAN SUNE: 1-WUTAR ƘAIƘAYI 2-WA'ADI. 3-A CIKIN IDO.. 4-TAZARAR SO #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah [7/9, 9:43 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@sanazty _Facebook@SaNaz Deeyah_ Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ *Saura Pages 4 free pages sun ƙare, har na gama da group 1 grouo 2 yana jiran wanda basu biya ba, ku hanzarta a karanta tare daku* _Book 1_ ```🆓Page 16``` Kallon Affan ta yi ta ga ya haɗe rai, ta mayar da kallonta ga Yazid daya ke tunkarosu tare da Lukman abokinsa, sai dai tun kafin su ƙarasa Faruq ya tare su, Sadiya ta lumshe ido ta yi dan ta san zuwan Faruq ba zai haifar da ɗa mai ido ba. "Malam lafiya kuwa? Na yi tunanin babu abinda ya yi saura, mene ya kawo ka gidanmu?" Murmushi Yazid ya yi tare da faɗin "Akwai kuwa, idan ka manta zan tuna maka, akwai Najma da Ihsan kuma sune suka kawo ni gidan nan" "Su ma a yanzu baka da cikakken iko dasu, dan haka ka fice ka bar mana gida" "Kodai har yanzu baka warke daga ciwon son ba? To ka sani Sadiya ta maka zarra kuma tafi ƙarfinka, koda a mafarki kuwa" Jin haka ya saka Faruq cikin ɓacin rai ya ɗaga zai wanke Yazid da mari. "Faruq...." Sadiya tayi saurin furtawa, hakan ya saka shi tsayawa cikin ɓacin rai ya juya ya kalleta. Da sassarfa ta ƙaraso inda suke. "Baka da hankali ne? Abban su Najma ne fa" "Koma waye?" Ya furta cikin tsawa. Jin hayaniya ya saka Saddiqa da Surayya fitowa daga cikin gidan. "Yazid kuma a gidan nan" Saddiqa ta faɗa tana ƙarasawa. "Lafiya kuwa? Mene ke faruwa?" Ta furta lokacin data ƙarasa gabansu. "Kana kallo wannan zai aureta, saboda tafi ƙarfinka har abada." Ya nuna Affan da hannu. Hannu Sadiya ta saka ta dafe kai, ganin Yazid na neman tona sirrin da babu wanda ya sani. "Wai mene ke faruwa ne? Yazid dan Allah kar ka biyewa Faruq ku yi ta sa'in sa" Kallonsa Faruq ya yi sannan ya ce "To bari ka ji muna nan da kai zaka ji labarin aurena da Sadiya kai ni da kaina sai na kawo maka katin ɗaurin aure" Surayya baki ta saki, yayinda Saddiqa ta ɗauki maganar Faruq a matsayin shirme. "Faruq idan na isa to kar na kuma jin kayi magana" "Aunty Saddiqa ki ƙyaleni da shi yana kallona a matsayin wanda ba zai iya ba" "To ina iyawar bayan har kayi jinya ka tashi bata so ka ba, idan da zata so ka ai da tun kana jinya ta tausaya maka, ko ka ɗauka ban san komai ba, Sadiya ba matar yara bace" Sai lokacin Sadiya ta fashe da kuka, kawai ta durƙushe a ƙasa. "Faruq ka koma cikin gida ko na kira Mameey" "Babu inda zan koma sai dai idan tare da ita dan ba zan barta da wannan azzalumin ba" "Sadiya tashi ki koma ciki" Saddiqa ta faɗa tana kama hannunta. "To mene ya kawo shi, ya koma inda ya fito" "Ina ruwanka kai dai ka tafi kawai" Ta faɗa rai ɓace. Tana miƙewa ta janye hannunta daga na Faruq ta ƙarasa gurin Affan da sauri. "Affan dan Allah ina so ka turo magabatanka tare da sadaki a satin nan" "Am....Sadiya am very sorry ni ban san mene zan faɗa ba am speechless because shi wannan ɗan uwanki ne, wannan kuma tsohon mijinki kuma akwai yara tsakani" "Karka damu, ka tafi kawai zamuyi waya" Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "But dan Allah kar ki ɗaga hankalinki" Kai ta gyaɗa tana murmushin yaƙe. Suna zaune a falo kowa ya yi shiru, har lokacin Sadiya ta kan goge hawaye, shi kuwa Faruq ransa a ɓace yake sosai ganin Mameey ta bawa Yazid damar shigowa. "Dama nazo ne na karɓi yarana ne dan ina so riƙonsu ya dawo hannuna" Cikin tashin hankali Sadiya ta ɗago kai tare da faɗin "Wallahi baka isa ba, ba zan taɓa yarda in bayar da ƙananan yarana ba" "Kar na ƙara jin kinyi magana" Mameey ta faɗa rai ɓace "Dama ko bai zo ba na yi niyyar mayar masa, dan bana so ya riƙa mana sintiri gida, na fi so a yi rabuwa ta har abada" Da sauri ya ɗago ya kalli Mameey sai kuma ya sake sauke kai ƙasa. Faruq kuwa daɗi ya ji sai dai bai so Mameey tayi furucin zata mayar da su Najma ba. "Mameey gaskiya nima ban bayar da goyon bayan a ba shi yaran ba, saboda mata ne kuma baya da aure." Saddiqa ta furta rai ɓace. "Amma ai ina da iyaye, kuma ina da ƙanne mata" "To hakan me zai amfanar? Yazid wallahi ba zan iya baka yarana ba, sai dai duk abinda zakayi ka yi, saboda ban san wane hali za su shiga ba idan bana tare dasu" "Idan kuma mutuwa kika yi fa? Ba dole a wani wurin za su rayu ba, ni kuma wallahi sai kin ba shi yaransa, sai mu ga idan rantsuwarki tafi tawa." "Mameey a gaskiya nima ban bayar da goyon bayan a bawa wannan azzalumin yaran ba" Faruq ya furta yana haɗe rai. "Azzalumin ai ubansu ne idan ya ga dama ya kashe su ai jininsa ne" Da sauri ta miƙe cikin tashin hankali tayi bedroom ɗinta, Yazid da ido kawai ya bita yana jin zafi a ransa. "Surayya tashi ki haɗa sauran kayan yaran dama yanzu suka dawo ai, ya ɗauka ya tafi." "Mameey dan Allah kar ki raba Aunty Sady da yaranta" "Kiyi abin da na ce ko kuma ranki ya ɓaci" Da sauri itama ta miƙe ta bar parlourn. *Bayan Wasu Mintuna* Jin kukan Najma ya saka ta miƙe daga kan gadon, idanuwanta jajir ga kanta da yake sara mata haka ta fita falo taga Yazid ya ɗauki Najma sai zullo take, Ihsan ce bata ma yi kuka ba, za ta ƙarasa gurinsu Saddiqa ta riƙo hannunta, ta kalleta cikin tashin hankali sai ta ga ta girgiza mata kai saboda lokacin Mameey na tsaye. "Ba su ƙaunata wallahi na san ba za su riƙe min yarana ba, dan Allah kar ku rabani dasu" Kuka sosai take kuma a fili, Faruq ya ƙaraso gurin tare da kallonta "Ki bari su tafi amma na miki alƙawarin za su dawo" "Sai dai idan bayan raina" Mameey ta yi maganar da ɓacin, da sauri Yazid da Lukman suka bar parlourn, ita kuma Sadiya ta ƙarasa gaban Mameey "Mameey nice baki so? Idan har baki son su Najma saboda Yazid to nima baki sona, saboda idan da jinin Yazid a jikinsu nima akwai nawa, nina haifesu Mameey yadda kike jin son mu nima haka nake jin son yarana ak....." Bata ƙarasa ba taji saukar mari, ta riƙe kumatun sannan ta kalli Mameey "Ki dawo cikin hankalinki, da ina sonki ai kin ƙunsa min baƙin ciki kin auri wanda ba zaɓina ba, ƙasƙantattun mutane masu baƙar zuciya, to baƙin cikin da kika ƙunsa min rabinsa baki ji ba a yanzu" Doguwar ajiyar zuciya ta sauke sai kuma ta ɗiba da gudu kamar mahaukaciya ta fita, Faruq ya rufa mata baya. A gabansu Yazid ta ja tunga lokacin suna gab da get. "Yazid dan Allah ka mayar da aurenmu ko dan yarana, na san za su sha wahala idan ba su tare dani" "Kiyi haƙuri Sadiya, na miki alƙawarin yaran nan za su zauna ne kamar kina tare dasu" "Yazid wane zunubin na aikata maka da kake son rabani da rayuwata, ina son yarana dan Allah ka tausaya min" Ta furta tana kai gwiwoyinta ƙasa, Lukman wucewa kawai ya yi dan ji ya yi kamar zai zubar mata da hawaye. Faruq na ƙarasowa ya fuzgi hannunta har sai da ta miƙe tsaye, ta kalleshi rai a ɓace ta ce "Ka cika ni" "Ba zan cika ki ba, bai kai matsayin da zaki durƙusa masa ba saboda babu laifin da kika masa" Ɗayan hannu ta saka tana ƙoƙari fuzge hannunta daga riƙon da Faruq ya mata amma ta kasa. "Kiyi haƙuri Sadiya" Shi ne abinda Yazid ya furta sannan ya wuce. Hannu ta saka ta riƙe wuyanta saboda jin wani abu daya tokareta, bata san lokacin data ɗora kanta a ƙafaɗar Faruq ta fashe da kuka, shi kuma a lokacin ya ji wani abu ya tsikareshi tun daga babban yatsa har ƙwaƙwalwa, sai dai ba zai iya janyeta ba, kawai ya sauke ajiyar zuciya ne. _*Dare*_ Yana zama ya kallesu. "Ya naga fav bata fito ba?" "Waye kuma fav ɗinka?" "Ai kin san waye baya anan?" Ya mayarwa da Surayya amsa. Dan a yanzu da yake jin zai iya zama da ita a matsayin mata, ba zai iya kiranta da Aunty ba sannan ba zai iya faɗin sunanta gatse-gatse a gaban wasu, amma a gabanta yana iya faɗa. "Sau biyu ina zuwa amma taƙi fitowa kuka kawai take, ga Aunty Saddiqa ta tafi." Miƙewa ya yi Mameey ta kalleshi "Faruq ka zauna ka ci abinci kar ka biye mata, idan yunwar cikinta ta dameta za ta fito ta nema ai" "Ba zan iya ci ba idan har bata ci ba." Ya ɗebi abinci mai yawa a plate sannan ya ɗauki gorar ruwa ya wuce. Yana shiga ya ganta a kwance kan gado ko ɗankwali babu ta baza gashin kanta da yake a tsefe yake, bata ɗago ba duk da ta san an shigo, a gefen gadon ya zauna sannan ya ɗauki ɗankwalinta dake gefe. "Sady!" Jin muryar Faruq ya saka ta yi saurin ɗagowa ta kalleshi, miƙa mata ɗankwalin ya yi ta karɓa tare da ɗaure kanta sai dai gashin ya fito ta ƙasa kasancewar tana da yalwar gashi. Kallonta yake sai yake ganin kamar ta koma masa wata sabuwa fil a leda, ya ƙare mata kallo tun daga sama har ƙasa zuciyarshi na jin kamar ya janyota jikinshi ya rarrasheta. Ajiyar zuciya ta sauke ya dawo daga duniyar tunani daya faɗa, ba shi take kallo ba idanuwanta na kallon gefe. "Abinci na kawo mu ci, dan na ce idan baki ci ba nima ba zan ci ba" "Na ƙoshi" "Ni na san kina jin yunwa, dan Allah karki azabtar da kanki da yunwa." Kuka ta saki a fili ta kalleshi "Yaro me su Najma suka yiwa Mameey ta tsanesu, ko zata tsanesu saboda Yazid nima ya kamata ta sosu saboda ni, amma tun kafin na samu matsala da Yazid dama Mameey bata ƙaunar yarana" "Wallahi Mameey na ƙaunarsu, kawai dai Yazid ne take jin haushi" "Na san an rabani da yarana ne saboda a ƙuntata min" "Na miki alqawarin yaranki za su dawo gareko ko ba yanzu ba" "Idan har ba su dawo gareni a yanzu ba na san ba za su dawo ba, saboda bani da yadda zan yi" "Akwai" Kallonshi tayi da rinannun idanuwanta ta ce "Ta wace hanya?" Plate ɗin ya ajiye a side drawer sannan ya kalleta. "Idan kika aureni ni ne zan riƙe yaranki tamkar mahai...." "Ya isa Faruq" Ta furta sannan ta dafe kai. "Ka riƙa faɗin abin da zai yuwu" "Kina ganin kamar ba zai yuwu bane?" "E, saboda ni yayarka ce, kuma bazawara" "A hakan nake sonki" Murmushi takaici tayi tare da faɗin "Idan har ba so kake zuciyata ta buga ba to ka tashi ka fita ka bar min ɗaki" "Sadiya..." "Ka fita Faruq" Ta furta cikin tsawa. Miƙewa ya yi ya ce "Zan iya fita daga cikin ɗakinki amma ba zan iya fita daga rayuwarki ba, ina sonki kuma a wannan karon zan yi yaƙi ne har sai naga na mallakeki, kuma zan sanarwa da kowa cewar ke nake so ciki kuwa har da Baffa Umaru." "Idan kai mahaukaci ne ai su ba mahaukata bane." "Na haukace kam indai akan sonki ne ai na daɗe ina hauka" Yana gama faɗa ya fice. Ranar shima bai ci abinci ba haka ya kwanta ya kuma kasa bacci, yana ta tunanin ta ina zai ɓullowa lamarin, haka ɓangaren Sadiya kwana tayi tana kuka, idan ta gaji zata huta sai kuma ta ɗora daga inda ta tsaya. Tun asuba Mameey ta jiyo kakarin amai, dan haka da sauri ta nufi ɗakin nasu. Surayya ta riƙeta a toilet ita kuma sai amai take babu komai a aman face ruwa. Hannu biyu ta saka ta riƙe kanta saboda juya mata da taji yana yi. "Kin ga maza je ki kira Faruq" "Mameey gani, yanzu na dawo daga masallaci, waye ba lafiya?" Ya faɗa yana shigowa dan shima kakarin ne ya saka shi shigowa ɗakin. "Sadiya ce babu lafiya ka ɗauki key a ɗakina kan mirrow ka fito da mota mu kaita asibiti" Da sauri ya juya ya fita. ***** ***** Ba su katse mata magana ba har sai da ta gama tare da jaddada masu cewar suna son tsayar da ranar biki nan da wata uku. Ayda ta yi murmushi tare da faɗin "Kuma ni Affan bai sanar dani ba, amma Anni kece kika yanke hukunci ko kuma wa?" Kallonta Anni ta yi kafin ta ce "Ya miki yawa ne a rage?" "A'a Farhan batayi magana ba sai ni" "To ai na ga kece mara kunyar tunda maganar bikinki ake kike tsoma baki" Jin haka ya saka duk yanayin su ya canja, "Anni bikina ko dai na Farhan?" "Bikinki da Affan dan cewa ya yi kece zaɓinsa" Bata san lokacin da ta miƙe tsaye ba, Farhan kuwa ji tayi gabanta na bugu. "Anni hala kin manta ina tare da Nasir? Kuma ko da Affan yazo mun yi deciding Farhan, itama har ta aminta da shi" "Wane aminci ita da ko number juna basu, ta riƙa shan ƙamshi tana miskilanci na iskanci, to ai kuwa idan ma hange take ta daina, saboda ke ya zaɓa kuma babu abinda zai hana aurenku" Farhan da gudu ta yi ɗakinta, ita kuma Ayda ta dafe kai. "Anni dan Allah ki ƙara magana dasu wallahi ina son Nasir." "Kina son Nasir amma ƙaddara Affan ta zaɓa miki, Ayda shi fa Nasir ɗin nan bai shirya aure ba, saboda sau biyu ana cewa ya fito amma yaƙi, to mene amfanin soyayya da gaibu?" Duk yadda taso Anni ta fahimta amma ta ƙi, sai kawai ta juya ta yi bedroom, tana shiga Farhan ta ɗago ta kalleta. "Wallah ban ga wanda ya isa ya hanani auren Affan koda kuwa kece" Cike da mamaki take kallon Farhan, sai kuma ta goge hawaye tana murmushi. "Wai kina yiwa Affan wannan son amma kika kasa tsayawa ku fahimci juna?" "Ke Ayda ki shiga hankalinki, ni ba sa'arki bace" Murmushin yaƙe tayi sannan ta ce "Tun zuwansa ni ban ɗora raina a kan shi ba, saboda ina son Nasir kuma da shi nake son rayuwa." "Idan har haka ne meyasa Affan ya zaɓeki?" "Saboda shimfiɗar fuska tafi ta tabarma, zan faɗa miki gaskiya wannan jan ajin da kike yi babu abinda samari ke kallon shi face wulaƙanci, ko shi Affan tun ranar daya zo abinda kika riƙa yi naga bai ji daɗi ba kuma fuskarshi ta nuna, sai dai shi mutum ne mai zurfin ciki shiyasa ma bai taɓa faɗa min ba, kuma idan kin lura bai kuma dawowa ba. Sai dai ya faɗa min cewa zafin kishin matarsa ta farko shi ne abinda ya jawo mata baƙin jini a gurin family sannan kuma ya fara tunanin ƙara auren wannan yarinyar da aka kashe gab da bikinsu." Zama Farhan ta yi tare da faɗin "Nima da wasa nake, kin san bani da wannan kishin" "A yanzu ba zan gane ba, amma a shawarce ko kina da shi to ki rage. "Ayda wallahi na ji ina son shi, ta ina kike tunanin zan ɓullowa lamarin?" "Dole mu zauna mu nutsu sannan mu yi tunanin mafita." *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._* *_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_* Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* lLITTAFAN SUNE: 1-WUTAR ƘAIƘAYI 2-WA'ADI. 3-A CIKIN IDO.. 4-TAZARAR SO #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah [7/9, 9:43 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@sanazty _Facebook@SaNaz Deeyah_ Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe Facebook Page: https://www.facebook.com/share/16d2wDeqer/ *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ _Book 1_ ```🆓Page 17``` "Gaskiya jininta ya yi ƙasa sosai, dole sai an ƙara, zafin zazzaɓin ne ya jawo haka dan da baku kawo ta asibiti da wuri ba gaskiya da wata maganar ake ba wannan ba" Surayya ta kalli Mameey cikin tashin hankali. "Dr a rubuta sai aje a saya a saka mata" "Haba Mameey mene amfanin jini yazo iri ɗaya, a ɗebi nawa a saka mata, blood group ɗinmu ɗaya, dukkanmu A+ ne" "Faruq na manta ai saboda gabaɗaya a ruɗe nake, kuje a ɗiba ke kuma Surayya kije ki sayo masa malt da madara. Suna zaune jinin yana ɗiga a hankali, Surayya na riƙe da hannun da aka saka cannula, Mameey na zaune kan kujera shi kuma yana tsaye. "Jini na da Aunty Sady zai ƙara haɗuwa a yanzu, dama kuma ita ce favorite ɗina" Murmushi Surayya ta yi haka Mameey ma, dan duk basu kawo komai ba, bare gane abinda yake nufi. Shigowar Saddiqa ta saka duk suka kalli ƙofa. "Ya Allah, abin har ya kai haka?" Ta faɗa tana ƙarasawa jikin gadon. "Wallahi kuwa" "Har da ƙarin jini" Mameey ta gaida sannan ta ƙurawa Sadiya ido. "Mameey dan Allah ku dawo mata da yaranta." Ajiyar zuciya Mameey ta sauke kafin ta ce "Gani kuke kamar bana son Sadiya ko yaranta?" Shiru suka yi babu wanda ya iya cewa komai, ita kuma ta cigaba da cewa "To ba haka bane, ku sani daga ranar da muka nuna mun damu da yaran to daga ranar Yazid da iyayensa za su samu lagonmu, za su yi amfani da damar ne su riƙa ƙuntata mana kuma ba za su dawo da yaran ba, amma idan muka nuna musu bamu damu ba wallahi da kansu za su dawo dasu, kuma ko ba su dawo dasu ba a yanzu na tabbatar yaran nan in suka girma za su nemi uwarsu" "Allah ya sa haka ahi ne mafi alheri" Cewar Saddiqa. "Kin yi masa kwatancen?" "E, ya gane ma, ya ce yanzu zai zo ya dubata" Faruq ƙara haɗe rai ya yi, ya ji wani baƙin kishi ya turniƙe shi. Ya kalli Saddiqa ya ce "Ni fa bana son Affan ɗin nan ko kaɗan" "Aikuwa baya da matsala, kuma yana da kirki da jan mutane a jiki." "Ko ma dai mene bai dace da ita ba" Saddiqa za tayi magana aka turo ƙofa, Affan ne tare da Lawisa, dukkamsu da manyan ledoji biyu a hannu. Ƙarasawa ta yi ta ajiye a gefe. "Har da ɗawainiya haka?" "Babu komai Aunty Saddiqa ya mai jikin?" "Da sauƙi, ɗazu ma ta farka an yi hira da ita, bata daɗe da komawa bacci ba" "Allah ya bata lafiya" "Amin ya Allah" Itama Lawisa dubata ta yi sannan ta sanar musu Mommy ma ta ce a duba ta. Tun da Affan ya shigo Faruq ya ƙura masa ido har sai daya gane hakan amma dai ya basar. ******** Tun da aka kawo su gidan Najma take kuka, ta yi kuka har ta yi bacci amma tana tashi ta ɗora daga inda ta tsaya. Suna jin kukan na ta amma sun yi banza sun ƙyale babu wanda ya damu a cikinsu bare ya rarrasheta. Ɓangaren Yazid kuwa yana tare da Lukman ya kuma gama labarta masa duk irin abubuwan da suka faru sannan ya ƙara da cewa "Ka ga dai Umma ita ta dage in ɗauko yaran amma babu wanda ya yi maraba dasu har tsoron komawa nake kukansu har cikin raina haka nake ji" "Ba zan fasa faɗa maka cewa ka yi kuskure ba, raba yaran nan da mahaifiyarsu a yanzu kam dama akwai matsala, ita kan ta bana tunanin tana lafiya a yanzu, ina ganin me zai hana ka mayar mata da yaran kawai, idan ka yi aure sai ka kwashe su ka mayar hannun matarka." "Abu ne mai wuya mahaifiyarta ta karɓi yaran idan na mayar, a gabanka aka yi komai Lukman" "To shin su yara mene laifi nasu da suke fuskantar tsangwama ta ko wane ɓangare?" "Ni kaina abinda nake tambayar kaina kenan a kullum, amma dai na san na yi wauta, ina ji a jikina ban yiwa Sadiya adalci ba." "Hmmm! Ai ba yanzu ya kamata ka faɗi wannan ba. Yanzu dai kaje ka ga halin da suke kafin ka koma gida, sannan ka kwantar musu da hankali." Kai ya gyaɗa sannan suka yi sallama da Lukman. Tun daga zaure yake jin kukan Najma har tana kakarewa, sai dai ga mamakinsa yana sallama ya gansu su biyu rak a tsakar gidan ita Najma na kuka, Ihsan kuma tana zaune gabanta tana tsotsar hannu. Da sauri ya ƙarasa gabansu ya zauna ga uban sauro a tsakar gidan. "Waye nan?" Ya ji muryar Umma daga ɗaki. "Ni ne!" Ya furta a sanyaye. Maryam ce ta fara fitowa tana ɗan sosa kai. "Yanzu na ce bari na masu shimfiɗa" Shiru ya yi bai ce komai ba, Umma ta ce "Ai Fatima kamata ya yi ta musu shimfida kafin ta yi bacci, dan ni kam ai ba ni aka kawowa reno ba bare na yi jigilar yara." Nan ma bai ce komai ba, sai dai kawai tambaya da ya yi ko sun ci abinci. "Yaya babu yadda ban yi ba, amma suka ƙi ci" "Kawo min abincin" Kai ta ɗan sosa, "Amm....." Ta kasa magana. "Babu abinci fa, ya kike wani kame-kame ki faɗa masa gaskiya." Umma ta faɗa kai tsaye. "Umma yara ba su ci abinci ba kuma a kasa ajiye musu?" "To ya kake so a yi ne Yazid? Sun ƙi ci, har ɗure muka musu suka zubar, kuma ka san yanzu dai abinci a hannu a hannu yake, tunda ba za su ci ba ai akwai masu buƙata. Miƙewa ya yi, tare da faɗin "Ina zuwa" Da sauri ya fita. Ya ɗan juma bai dawo ba sai ga shi da ya dawo da takeaway na tuwon semovita miyar agushi da Bobo sai 'yan biscuits daya saya musu. Da kan shi ya basu abinci, ya lallaɓasu sosai suka ci, suna gamawa a jikinsa Ihsan ta yi bacci, itama Najma ta kwanta kan cinyarsa, yana ɗan musu fifita saboda sauro haka har sukayi bacci dukkansu. Yana zaune ya kwaɗawa Maryam kira, ta fito. "Kin musu shimfiɗa?" "E Yaya Yazid, na saka musu gidan sauro ma" "To muje na kwantar dasu" Sai daya kwantar dasu sannan ya kalleta ya ce "Maryam dan Allah ki kula dasu, yanzu suna tare da kewar mahaifiyarsu ne" Kai kawai ta gyaɗa, ya fiddo dubu ya bata. "Da safe sai a ƙara a break" "To Yaya sai da safe" "Allah ya kaimu" Yana kwance kan gado yana juyi ya rasa ya zai yi, Sadiya ce kawai ke faɗo masa a rai, lokacin da take kuka tana roƙonsa ya mayar da aurensu ko dan yaranta. "Anya na miki adalci Sadiya?" Ya faɗa a sanyaye, sannan ya ja numfashi da ƙarfi. "Mene ke faruwa dani? Meyasa na biyewa son zuciya na cutar da yarana da kuma Sadiya da ta sadaukar min da rayuwarta" Ya saka hannu ya damƙi fuskarsa. ****** ****** Kallonsa kawai take tana mamaki kafin ta ce "Ka ga ka tashi Affan, dan za ka roƙeni abu ba sai ka durƙusa min ba, ka da ka manta numfashi ma ina yi ne domin ku, kuma lokacin da mahaifinku zai rasu ya bani amanarku kuma ya ce kar in bari wani a cikinku ya yi kukan maraici, sannan kuma in baku tarbiyyar da har abada ba zaku ɗauko masa abin kunya ba. Na san kuma na baku tarbiyya kuma na gatanta ku, duk wani abu da kuke so na kan yi ƙoƙari na tayaku so, amma Affan a yanzu ni meyasa ba zaka so abin da nake so ba?" Lawisa ta ɗora hannunta kan cinyar Mommy tare da faɗin "Mommy kada ki manta irin son da Yaya Affan yake yiwa Nashwa, ni na san dama hakan sai ta faru" "Wannan ai ba Nashwa bace, kuma kama da wane bata wane" "Ina kallonta ne a matsayin Nashwa ta ce Allah ya dawo min da ita, Mommy dan Allah ki taimaka min ki ji tausayi na karki hanani kar ki bari na rasa Sadiya" Kan sa ta dafa tana murmushi ta ce "Na amince amma nima ina so ka auri Ayda kafin ko bayan ka auri Sadiya ka yi min alƙwari" "Shi kenan na amince Mommy" Lawisa ta sake yin murmushi. "Yaya da alama dai mata biyu zaka zauna da su a rayuwarka. "Zan yi magana da Uncle ɗinku acan Yola, in yaso sai su shirya zuwa next week su je, idan ta kama ma kawai a bayar da sadaki sai a tsayar da rana tunda bazawara ce, ba wani jan abin za a yi ba" "Duk yadda kika tsara ya yi" "Kana zuwa gurin Ayda?" "A'a tun last week ban koma ba, but muna waya" "Ka dai yi ƙoƙarin kwatanta adalci a tsakaninsu" "Insha Allahu" "Allah ya tabbatar da alheri" "Amin." Yana shiga ya faɗa kan gado tare da ɗauko waya ya kira number Sadiya, sai dai har ta gama ringing ta katse bata ɗaga ba. Ya kuma kira a karo na biyu, shima har ta kusa katsewa ta ɗaga. "Lu'ulu'u!" Ya furta lokacin da ta ɗaga, yana jiyo sautin murmushin ta. "Jiki ya ƙara sauƙi ko?" "E alhamdulillah, ai na fara cire komai a raina" "Ki cire gabaɗaya ma, Allah yana tare dake" "Hakane, fatan kana lafiya" "Lafiya lau, wani albishir zan miki amma dai sai na shigo gobe" "Kenan baka so na yi bacci yau?" "No ai albishir na ce kin ga kenan abin farin ciki ne" "Ni dai gaskiya a faɗa min" "Lu'ulu'u maganar ba ta waya bace" "To ai da sai ka ƙi faɗa in kazo kawai ayi ta" "Afuwan, zumuɗi ne ya saka na yi suɓul da baka" "To aikuwa ko hint ka bani" "Okay but kiyi min alƙawari za ki bani goron albishir" "An gama yallaɓai" "Yanzu muka gama magana da Mommy ta ce min ƙila next week za a turo gidanku tambaya kuma har da sadaki" Tana daga kwance ta miƙe zaune. "Joke aside" "Sadiya am not joking" "Alhamdulillah" "Finally dai za ki zama tawa Sadiya" Hannu ta saka ta rufe fuska kamar yana gabanta, sai kuma ta buɗe. "Allah ya tabbatar mana da alheri" "Amin" Ta furta a daidai lokacin kuma aka turo ƙofa aka shigo, ajiye wayar ta yi shi kuma da ido yake kallonta. "La...lafiya?" Ta tambaya tana kallon Faruq. Still bai magana ba har sai daya ƙarasa jikin wardrobe sannam ya jingina da ita. "Mene aibuna?" Ya furta a sanyaye, idanuwa ta lumshe sannan ta cije laɓɓanta. "Faruq dan Allah ka haƙura ka daina magana akan abinda ba zai yuwu ba" "Mene zai hana shi yuwuwa?" Kallon shi ta yi sai kuma ta miƙe a gigice. "Ka ga yadda ka koma kuwa? Faruq wai wane irin so ne wannan? Ka yi hauka ne? Ya kamata ka farka daga wannan mummunan mafarkin. "Kin san wani irin jinya na sha kafin in iya haƙura dake a wancan lokacin? Shine kike tunanin a wannan lokacin zan yi?" Murmushi ya yi tare da cewa "Ba zan iya haƙura ba a wannan karon, ba zan taɓa iya bari ki suɓuce min ba" Yana gama faɗa ya wuce da sauri. A parlour ya tarar da Mameey zaune kan kujera Surayya na mata yankan farce. "Mameey" Ya faɗa tare da zama a ƙasa gabanta. "Faruq lafiya kuwa?" "Mameey idan na roƙi alfarma za ki min?" "Idan har zan iya" "Mameey aure nake so." "Aure?" Ta maimaita da mamaki, Surayya ta saki baki tana kallonsa. "E Mameey" "To amma Faruq kana ganin Dadanka za ta amince ka yi aure at the age of 24" "E Mameey ai kece uwata, duk abin da kika ce ba za a musa ba" "Na ji, iyayen yarinyar fa?" "Idan har kun amince suma basu da matsala." "Wacece?" "Sadiya ce Mameey" "Wacce kenan?" Ta sake tambaya dan bata taɓa kowawa Sadiyarta yake nufi ba. "Mameey ta gidan nan, Maman Najma" Dafe kai Sadiya ta yi, dan ta fito kenan ta ji wannan ɗanyen aiki da Faruq ya yi, ita kuwa Surayya hannu ta saka ta rufe baki tare da zaro ido. *Saura Pages 3 mu gama free pages, ku biya in kuna so a cigaba da karatu daku.* *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._* *_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_* Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* lLITTAFAN SUNE: 1-WUTAR ƘAIƘAYI 2-WA'ADI. 3-A CIKIN IDO.. 4-TAZARAR SO #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah [7/9, 9:43 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@sanazty _Facebook@SaNaz Deeyah_ Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe Facebook Page: https://www.facebook.com/share/16d2wDeqer/ *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ _Book 1_ ```🆓Page 18``` Miƙewa Surayya ta yi, Mameey ta kalleta sannan ta yi mata umarni ta zauna, jiki babu ƙwari ta zauna tana kallon Faruq yayinda shi kuma yake kallon ƙasa. Sadiya kuwa da sauri ta juya tana hawaye. "Faruq ka faɗa min gaskiya, ko dai tsokanar mu kake?" Ɗago manyan idanuwansa ya yi wanda suka rine ya kalleta, sai kuma ya ɗauke, ita kanta Mameey ta tsorata da ganin yanayinsa. "Tuntuni nake da abin a raina, da farko na ɗauka shaƙuwa ce da kuma tausayi amma daga baya na gane ba haka bane, Mameey na yi ƙoƙarin na danne kar wanda ya sani amma na kasa fin ƙarfin zuciyata, ki tambayeta ki ji wallahi ciwon daya kwantar dani a asibiti kenan, ita kuma tana jin haka shi ne ta daina zuwa inda nake, Mameey duk da na san matar aure ce amma a lokacin ji nake kawai idan ba ita ba, ba zan iya kula ko wace mace ba, sai kuma ga shi yanzu ta rabu da mijinta kuma ana so a bata wani, Mameey dan Allah ki taimaka min kar na rasata" "This is serious, what!?" Surayya ta furta cike da mamaki. "Surayya ta shi ki bar nan" "Mam..." "Ki tashi na ce bana son musu" Jiki babu ƙwari haka ta miƙe ta wuce. Mameey ta mayar da kallonta ga Faruq ta ga yana goge hawaye. "Ka kwantar da hankalinka, ai ba a riga an ɗaura ba, ka ga dai ciwonka mun samu ka warke karka ƙara ɗago mana shi, tashi ka zauna nan mu yi magana" A sanyaye ya miƙe ya zauna gefenta. "Faruq" Bai amsa ba, bai kuma ɗago ya kalleta ba. "Ba zan hanaka Sadiya ba, amma bana so na tauye maka haƙƙi, na farko Sadiyar nan ta baka shekaru har 3, she's 26 you're 24 Faruq you're still young, sannan Sadiya a yanzu bazawara ce har da yara biyu dan ma ɗayar ta rasu da uku za a ce, kai kuma saurayi ne ɗanye yanzu ma ka fara tasowa, ka ji biyu ko, abu na uku koda ni na amince da aurenku da Sadiya bana tunanin dangin mamanka za su yarda hatta dangin babanka wasu gani za su yi na zalunceka, yau da ace Surayya kace wallahi zan baka ita koda ba ta so, amma ka zauna ka zurfafa tunani." "Mameey ni ban damu da duk abinda za a faɗa ba, saboda a yanzu idan har mutum zai biye faɗar mutane to ba zai taɓa yin abinda ya dace da shi ba. Mameey dan Allah ki taimaka min, dan Allah Mameey." Hannu ta saka ta shafa kansa "Ya isa, ka je zan yi tunani akai" ****** ****** Tana ƙarasawa gabansa ta juyar da kai tare da haɗe fuska. "Na yi laifi ko? Afuwan" "Ni kam ban karɓi wannan ba" "To ko dai na kama kunnuwana" Ya faɗa yana riƙe kunnen. "Ni na isa na ce haka, please a'a" Saukewa ya yi yana murmushi, "So ya kike, ya Anni and sister" "Duk lafiya lau, mu ƙarasa ciki mana" Har sun juya suka ji horn, amma ba su yi tunanin gidan za a shigo ba har sai da maigadi ya wangale gate. "Nasir ne!" Ta furta tana tsayawa. "Waye Nasir?" Ya tambaya, ita kuma ta ɗan saka hannu tana sosa kai cike da kunya. "Oh I understand, so ko dai na tafi?" "No ka jira ku gaisa sai mu shiga ciki, Farhan ma tana son ganinka" "Okay" Suna tsaye ya ƙaraso, fuskar nan ta ci mur, shima Nasir ba laifi black beauty ne. "Ke waye wannan?" Murmushi ta yi duk da a tsorace take da yanayinsa. "Shi ne Affan da nake faɗa maka cousin bro...." "Saurayinki dai" Ya furta da tsawa, kallonshi Affan ya yi cike da mamaki. "Dama an daɗe ana faɗa min kina cin amanata ban yarda ba, ga shi yanzu na gani da ido na" "Nasir wace irin magana kake haka" "Asirinki ne ya tonu munafuka babu wani daɗin baki da za ki min" "Karka sake ce mata munafuka" "Idan na sake me zaka iya?" "Zan saka a fitar da kai daga gidan nan" "To bari na dake ta naga abinda zaka iya" Affan bai gaskata ba sai daya ga ya kai hannu ya wanketa da mari. Ɗan runtse ido ya yi lokacin ya ji Nasir na faɗin "Ai bata da wani daya fini, saboda na riga na mata abinda ba zata iya rabuwa dani ba, dama ka haƙura dan babu abinda ban sani a jikinta ba, so ko ka aureta guntuna ce." Yana buɗe ido ya tsinkawa Nasir mari har biyu, sannan ya fuzgosa ya fara bugu, maigadi ya kwaɗa salati ita kuma tana kuka take roƙar Affan ya sake shi, da ƙyar ma'aikatan gidan suka raba lokacin har ya haɗa masa fuska da jini ya kuma ya ga rigarsa. "Kin ga Farhan je kiyi driving Nasir zuwa asibiti" "No need zan iya" Ya kalli Affan "Baka ci banza ba" Yana gama faɗa ya wuce ya shiga mota ya tayar cikin ɓacin rai. Affan sai lokacin ya gaishe da Anni. "Mu shiga ciki Affan" "A'a zan wuce ne" Ya furta da dakakkiyar murya. Sannan ya miƙe ya wuce kawai, Ayda kuka kawai take saboda duka biyu ga mari ga tsinka jaka. Kai tsaye gida ya nufa dan kan shi ya ji yana masa zafi tare da barazanar tarwatsewa, sai dai har ya ɗauki hanyar gida kawai ya juya akala ya nufi gidan su Sadiya. Tun a farkon layinsu ya kirata a waya ya ce ta fito. Ta fara son Affan shiyasa ba zata iya masa musu ba, amma da sai ta ce masa "Ba zata zo ba, dan tunda Faruq ya je ya baje ta gaban Mameey ta kasa fita, da rana tana ji aka zo kiranta cin abinci amma baccin ƙarya ta yi, sai kawo mata Surayya ta yi ta dire, gashi har yamma ta kasa fita bare ta haɗa ido da wani,. Saɗaf-Saɗaf haka ta fito kamar ɓarauniya, ta ji daɗi ganin babu kowa a parlour sai dai tana gaf da fita ta ji Mameey ta ce "Ina zuwa?" Sai da ta furgita, sai kuma ta runtse ido, bata juyo ba ta ce "Dama Affan ne yazo" "Shi ne kike sanɗa kamar mara gaskiya" "A'a" "To kije idan kin dawo ina son magana dake" A sanyaye ta wuce. Ƙofar motar ta buɗe ta shiga sannan ta kalleshi, ya kwantar da kujera sannan kuma bayanshi yana jikin kujerar. "Sadiya" Ya kira sunan da wata iriyar murya. Kallonshi ta yi sai kuma ta ce "Lafiya kuwa?" "Ina cikin damuwa" Sai kuma ya riƙo hannunta tare da buɗe idanunsa da suka yi jajir "I need you." Ya furta yana murza hannun, da ƙarfi ta fuzgi hannun cikin ɓacin rai ta buɗe motar sai ta ji taƙi buɗuwa, a rufe take ya yi locking ɗinta. "Affan mene haka? Ka buɗe min mota na fita" "Sadiya please..." Ya furta muryarsa na rawa. "Ba zan iya aikata abinda kake so ba kawai ka bar ni na tafi" Idanunsa ya buɗe ya dubeta "Wane abu nake so ki aikata?" Shiru ta yi saboda ta kama kanta. "Sadiya! Talk please" Kan ta ta ƙara saukewa ƙasa, shi kuma ya ce "Sadiya akwai wata wadda Mommyna take so na aura, yanzu haka daga gidansu nake, Sadiya a gabana wani banza yazo yana faɗin irin abubuwan da suke aikatawa tare, ban taɓa zina ba, ba zan iya auren mazinaciya ba, Sadiya ina sonki kuma bana so na rasaki, dan Allah ina so ki min alƙawarin kare kima da martabar iyayenki, kodan yaranmu" Hannu ta saka ta rufe baki lokacin da wasu zafafan hawaye suka zubo mata, haƙiƙa ta yi masa mummunar fahimta, ashe shi ba wannan yake nufi ba. "Ba zan taɓa aikata saɓo ba duk runtsi duk wuya, ko ba dan yarana da iyayena ba dan lahira zan kare mutuncina" Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke. "Tunda na fito daga gidan su Ayda sai yanzu na ji na samu relief" Kawai ji ta yi kishi ya turniƙeta. "Mu biyu za ka aura?" Ta jefe shi da tambayar. "Ke kaɗai ce Sadiya, naje ne kawai dan na bi umarnin Mommy kuma yanzu na samu hujjar da zan faɗa" "Dan Allah karka faɗawa Mommy, kar ma ka kuma ɗaga maganar da kowa, ka rufa mata asiri kaima sai Allah ya rufa maka" "Ke ta da ban ce Sadiya" Murmushi kawai tayi tana goge hawayen daya zuba. ****** ****** "Faruq anya baka fara shan wani abu ba?" Murmushi ya yi tare da faɗin "Idan ina sha ai zai nuna ni, Aunty Saddiqa kece last hope ɗina" Zama ta yi kan hannun kujera "Yanzu idan da Yazid bai saketa ba ya zakayi kenan?" "Ba zan taɓa dawowa Nigeria ba, kuma soyayyar ta ce za ta kasheni da sonta za a binneni" "Idan kana wannan maganar sai na ga kamar a film" "Hmmm! To shin mene laifina dan na ce ina sonta? Ni fa namiji ne" Dariya Saddiqa ta yi ta ce "Sadiya fa ta girmeka, har wanka ta yi maka, sannan kuma tana da yara, abu ne mai wuya ta yarda da kai" "Ni bana neman yardarta a yanzu, amma na san a gaba idan na kasance miji a gareta ai dole ta yarda dani" "Innalillahi Yaro wai dagaske kaine?" "Ni ne mana, Aunty Saddiqa dan Allah let's be serious" "Okay! To yanzu kai karatu kake fa, kana nufin Sadiya ta jira har ka gama school?" "Ni fa ko gobe a ɗaura, zan iya riƙe matata, ba dole sai da aikin gwamnati ba, zan fara ɗan business" Dariya ta sake yi tare da faɗin "Kamar almara" "Ba almara bace, yanzu dan Allah mene abin yi?" "Ina ga ka shirya kawai ka je gurin Baffa" "Kina ganin Baffa zai duba lamarin?" "To zai iya cewa kayi yaro a aure, kai kanka ba a gama riƙon ka ba bare ka riƙe wani." "Wallahi idan na auri Aunty Sadiya riƙon da zan yi mata ko Yazid bai yi shi ba, zan iya hana kaina idan har ita za ta ci ta ƙoshi." Ganin dagaske yake, ya saka Saddiqa ɗaukar ƙudirin taimaka masa, sai dai ta umarce shi da kar ya bari kowa ya san tana da hannu akan hakan. _*A Week Later*_ Shiru Mameey ta yi kuma kanta a ƙasa yake lokacin da Baffa ke mata bayani, bata katse shi ba har sai daya gama sannan ta ce "Baffa shi fa Faruq a yanzu haka karatu yake, kuma nan da wata biyu zai koma can Germany, idan har ya yi aure to waye zai riƙe matar?" "Ya ce zai iya, wanda ya ce zai haɗiyi gatari sai a sakar masa ƙota" "To da mene zai riƙeta, baya aikin komai, sannan uwa-uba Sadiyar nan ta girme shi fa" "Khadija!" "Na'am Baffa" "Ki sani dan Sadiya ta girmi Faruq hakan ba zai haramta aure a tsakaninsu ba, ka da ki manta manzon Allah (SAW) ya auri Nana Khadija (R.A) yana saurayi ita kuma bazawara, kin ga idan Faruq ya yi haka kamar ya yi koyi ne da manzo (SAW)" Sai dai ta numfasa sannan ta sake cewa "Dangin mahaifiyarsa za su ga kamar ni ce na saka ya auri Sadiya, sannan mutanen gari ma gani za su yi kamar na tauye musu" "Dangin Dada Rabi zan yi magana dasu, su kuma mutanen gari ai ba dole sai an burge su ba. Na yanke shawara kuma har na yi magana da Habu da Isma'il mun saka ɗaurin auren ranar juma'ar nan mai zuwa, hidimar biki kuma za a iya saka rana a yi daga baya. Ba akwai gidan sa na gado anan ba?" "Akwai amma ba a gyare yake ba" "To sai a haƙura da tarewar yanzu sai a samu a mata passport" Shiru Mameey ta yi bata sake cewa komai ba har ya gama tsare-tsarensa ya tafi. *Bayan Sati Ɗaya* A wajen adana motoci ya ajiye tashi, sannan ya fito jiki a sanyaye ya ƙarasa inda take. Tana ganin shi ta ƙara haɗe rai har ya samu guri ya zauna. "Yazid! Ka san maganganun da kake faɗa kuwa?" "Na sani saboda a cikin hayyacina na yi, kuma bana shaye-shaye" "Kana ganin mai yuwuwa ne?" Murmushin takaici ya yi tare da ɗora hannayensa akan table ɗin wurin. "Ni a wajena kamar ya yuwu ne, babu wata barazana da za ta dakatar dani daga abin da na yi niyya. Sai dana rabu da Sadiya na gane kuɗi ba sa taɓa sayen farin ciki, na ɗauka kuɗi sune maganin matsalata amma dana same su sai matsalolin suka ƙaru. Bani da nutsuwa, haka yarana, a lokacin da nake talauci ma na fi samun kwanciyar hankali da nutsuwa, ban sani ba ko dan kuɗin na same su ne da hanyar cin amana" Kallon shi kawai take tunda ya fara magana har zuwa lokacin daya kai aya. "Yazid amma idan kana tuya kamar kana mantawa da albasa, kai kana tunanin abu mai sauƙi ne Sadiya ta yarda da kai?" "Ni da Sadiya akwai yarda da kyakyawar fahimta." Kai ta girgiza tana murmushi tare da faɗin "A baya kenan, amma ina mai baka shawarar kada ka tunkari Sadiya da wannan maganar, wallahi ina mai tabbatar maka mutuwar kasko za ayi" "Ban fahimce ki ba?" "Kai ka rasa Yaya Affan ya rasa, har gara Yaya Affan shi bai ma san komai ba dalilin haka zai iya sakawa ta aure shi" "Haka kike gani?" "Haka ne ma." Miƙewa ya yi tare da ajiye mata mukullai a gabanta. "Wannan mukullan gidan da kika bani ne da kuma mota, dana shagon dana buɗe a kasuwa, takardunsu suna cikin motar ga ta can" Ya furta yana nuna mata motar da hannu. Juyawa ya yi tana kiran sunansa amma sam yaƙi ya saurareta. *Saura shafuka biyu mu gama free pages, ku garzayo ku saya domin cigaba da karatu* *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._* *_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_* Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* lLITTAFAN SUNE: 1-WUTAR ƘAIƘAYI 2-WA'ADI. 3-A CIKIN IDO.. 4-TAZARAR SO #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah [7/9, 9:43 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@sanazty _Facebook@SaNaz Deeyah_ Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe Facebook Page: https://www.facebook.com/share/16d2wDeqer/ *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ _Book 1_ ```🆓Page 19``` Suna zaune a dining area suna cin abinci, sai dai ya lura da Lawisa kawai juya spoon ɗin take a cikin abincin amma sam taƙi ci, baya so ya yi mata magana dan kar Mommy ta fahimta, sai dai haƙonsa bai cimma ruwa ba dan Mommy ce ta ce "Ya naga kina cakula abincin kin ƙi ci?" "Babu komai Mommy, kawai bana jin cin abincin" "To me kika ci? Ko kuma daga asibitin kin wuce restaurant ne?" "A'a Mommy akwai wata patient da aka kawo mana unconscious itane ta tsaya min a rai" Tana gama faɗa ta tashi ta wuce ɗakinta. Mommy ta kalli Affan ta ce "Ko ka san mene ke damunta?" "Tun ɗazu na lura da yanayinta amma sai na yi tunanin ko gajiya ce" "Kana asibiti ai dama babu abinda ba zaka gani ba." A zaune ya tarar da ita ta yi tagumi, ya ƙarasa bakin gadon tare da janye hannunta da ta ɗago kai ta kalleshi. "Na san abin da kika faɗawa Mommy ba gaskiya bane, ki faɗa min mene ke faruwa?" "Yaya gaskiya na faɗa, kai ma ka san idan akwai wani abu kaine wanda zan fara sanarwa." "Kin tabbata?" Kai ta gyaɗa alamar eh. Zama ya yi gefen gadon sannan ya ce "Mene ke damun ita patient ɗin wanda har ya hanaki sukuni?" "Am...am..." Sai kuma ta saka hannu a wuyanta tana shafawa sannan ta ce "Dama ɗane ya mutu a cikinta" Murmushi ya yi sannan ya ce "To ai ko ƙaramin yaro kika faɗawa haka ba zai yarda ba bare ni mai hankali." "Yaya am sorry!" Ta furta tana goge hawaye. "Sorry for what?" "Na san na tafka babban kuskure dan Allah ka yafe min" "Explain to me, ina jin ki what's goin on?" Idanuwa ta ƙura masa sannan ta ce "Yaya dama....dam...." Sai kuma ta sake yin shiru. "Idan har baki faɗa min ba, kenan bani da wannan matsayin da kike faɗa" Ji ta yi hawaye masu zafi sun zubo mata, ta danne zuciyarta sosai ta faɗa masa duk irin tuggun da ta haɗa har ya kai ga rabuwar auren Yazid da Sadiya. Miƙewa ya yi cike da mamaki yana kallonta, fuskarsa ta bayyana tashin hankali ƙarara. "Lawisa why?" "Yaya na ga ka damu ne shiyasa" Ta furta a lokacin wasu hawayen suka sake zubo mata. "Kina nufin da sanin Yazid lokacin da muka je har babarshi da ƙannensa suka zo, sannan zuwan da na yi na biyu wanda har na kai ƙanwar mahaifiyarsa station duk ya san da zuwanmu?" "Wallahi Yaya ya sani, tun kafin mu taho zan ce yanzu zamu zo shi kuma idan ya kintata lokaci sai kawai su zo, kuma duk mun yi haka ne dan a kawar da zarginta daga saki, ko sakin daya mata za ta ga ba laifinsa bane tunda dama danginsa ba su ƙaunarta." "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Lawisa duk ranar da Sadiya ta gano gaskiya ba za ta taɓa yarda babu hannuna ba, sannan kuma za ta tsaneni ne ba zan kuma yin wani abu da zai burgeta ba" "Ko za ta gane ma, insha Allah sai bayan bikinku" Ɗagowa ya yi a fusace ya kalleta, ita kuma da sauri ta sauke kai ƙasa. "Baki kyauta min, sannan kin cutar da Sadiya idan har bata yafe miki ba to tabbas sai Allah ya saka mata" "Na san na yi kuskure amma ni a lokacin bani da wani buri daya wuce na ga ka mallaketa saboda tsananin kamannin da suke da Nashwa." "Kama da wane ai bata wane, duk da Sadiya ma tana da hali mai kyau amma dai ban ji daɗin wannan lamari ba." Yana gama faɗa ya miƙe tare da mata sai da safe sannan ya wuce. Kwance yake ruf-da-ciki akan lafiyayyen gadonsa, ya rasa wane kalar tunani zai yi, mafita yake son samowa amma duk hanyoyin sun toshe. Idan ya ce zai faɗawa Sadiya gaskiya to ya tona asirin Yazid wanda za ta iya kallon abin a matsayin ya faɗa ne dan ya kare kansa kafin ta sani ta ɗauki mataki. Idan kuma ta sani da kanta za ta riƙa masa kallin maci amana kuma azzalumi. Wayarsa ya janyo ya tura mata text sannan ya lumshe ido yana jin faɗuwar gaba. Jin wayarsa na ƙara ya saka gabanshi faɗuwa, dan a tunaninsa Sadiya ce, sai da ta kusa katsewa ya buɗe ido, ganin Ayda ce ya saka bai ɗaga ba, daya ga ta dame shi da kira kawai ya kashe wayar gaɓaɗaya. ***** ***** Tana shafa addu'a ta ji ƙarar shigowar text, hannu ta saka ta ɗauki wayar sannan ta buɗe. _Sadiya! You should know that I love you, and my love is true. I did not come to you with the intention of deceiving you, and I was not part of any plan to deceive you, Allah is my witness to that. There is something that happened which I find difficult to explain to you, because you might think I was involved in a plan against you, but know that I truly love you, now and forever._ _Affan_ "Mene yake faruwa?" Ta furta a lokacin kuma ta yi dialing numbersa, sau uku tana bai ɗaga ba, sai dai hakan bai saka ta haƙura ba, ta kira ya kai sau biyar bai ɗaga ba dan haka itama saƙon ta tura masa. _Affan, what is going on? I hope this text isn't about a breakup. Affan, you have to know that your love now means everything to me, losing you would feel like losing a part of my life. You started loving me because I resemble Nashwa, but as for me, it was your beautiful character that made me fall in love with you._ Tana turawa ta sauke ajiyar zuciya tare da fatan Allah yasa lafiya. _Washe Gari_ Tun da ta farka take jin faɗuwar gaba, haka ta daure ta shiga wanka ta fito da niyyar ta shirya kawai ta tafi gidan Saddiqa dan gabaɗaya gidan nasu baya mata daɗi. Sai dai hayaniyar da ta jiyo ne ya saka ta yi sauri ta zura riga a gaggauce ta fita. Mameey, Dada(mahaifiyar Faruq), sai ƙanwar Faruq da suke uwa ɗaya sai Surayya da Faruq ɗin ne a parlour, Dada na ta faɗa. "Yanzu wannan za a aurawa ɗana?" Shi ne abinda ta faɗa lokacin da Sadiya ta fito. "To na rantse da Allah ki gaggauta bayar da umarnin a janye saboda a gidan Baffa na fara dira kuma ya ce aure babu fashi muddin ba daga nan aka janye ba. Mameey ta girgiza kai kawai sannan ta ce "Daga nan ɗinma mun so hanawa amma Baffa ya ce tunda Faruq ya ji ya gani babu yadda muka iya, idan har Faruq bai janye ba babu yadda zamuyi" "To idan ba asiri ba me Faruq zai yi da macen da take da har yara biyu, bazawarar da ta girme shi ma." Cikin ɓacin rai Mameey ta mayar mata da martani "Na ɗauka Sadiya 'ya ce a gareki, na yi tunanin za ki kare Sadiya a ko ina, na yi tunanin sai inda ƙarfinki ya ƙare idan aka yiwa Sadiya gori amma sai ga shi da kanki kike faɗar maganganu" "Dole ne na faɗa, da farko an ƙwace yaro an baki, yanzu kuma kuna son cutar da shi ta hanyar aura masa tsohuwa, saboda ku ci gadon shi" "Dada dan Allah ya isa haka, ni babu wanda ya tursasa ni akan na auri Sadiya, ita nake so kuma ita naga zan iya rayuwa da ita" Sai lokacin Faruq ya yi magana cikin ɓacin rai. Sadiya zama ta yi a ƙasa kawai ta fashe da kuka, dan bata da wani abu da za tayi daya wuce kukan. "Faruq kar na sake jin ka kuma yin wannan furucin, ko mene ta faɗa mahaifiyarka ce, kuma tana da iko da kai" "Ai bai sani ba, wataƙila yanzu ke yake tsammanin kece mahaifiyar" Ta kalleshi "Ka sani da ka auri wannan bazawarar gara na tsine maka na san duniya ka bi, akan zama da wannan" A fusace Sadiya ta taso, "To me zan yi da shi? Mene yake da shi, har yanzu bai ma san ciwon kanshi ba shiyasa yake faɗar wannan maganganun, nima ba auren shi zan yi ba, saboda ni bazawara ce ina da ikon zaɓar mijin aure da kaina" "Sadiya..." "Mameey ki bar ni na faɗa mata, duk Faruq shi ne ya ja min wannan wulaƙancin" "Kenan alfahari kike da kasancewa bazawara? Kuma ni kike kallo kina faɗawa maganganu?" "Ni....." "Idan kika sake magana ranki zai mummunan ɓaci Sadiya" Mameey ta furta a fusace. Dada ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Faruq "Yanzu a haka kake son ɗauko yarinyar da take tsayawa gabana tana faɗar magana. Faruq kai kaɗai ne ɗana namiji, burikan dana ci a kanka suna da yawa, amma ka rasa wa zaka ɗauko sai wannan?" Sadiya da sauri ta ƙarasa gaban Faruq "Wai Yaro duk kana ganin abinda ke faruwa? Ko dai ka fara shan wani abu? Yaro idan har baka so zumuncin mu ya ɓaci to ka janye maganar nan, Dada mahaifiyarmu ce, amma maganganunta sun fara tunzura ni, ka sani muddin aka tilastani na aureka a daren zan kashe ka." Tana gama faɗa ta juya da sauri ta koma ɗakinta, kan gado ta faɗa ta fashe da kuka a fili. Sai da ta yi mai yawa har muryarta ta dashe sannan ta miƙe zaune kanta ta ji yana wani irin sarawa. "Yazid me nayi maka? Wannan shi ne tukwuicin irin soyayyar dana nuna maka? Na rabu da komai ciki har da farin cikina duk dan na faranta maka amma kayi min sakayya da saki" Pillow ta damƙo ta kuwa ƙwalla wani gigitacce ƙara tare da kuka a lokaci ɗaya. Shigowar Saddiqa kenan tana rarrashin Mameey akan abinda ya faru suka ji ihun Sadiya da sauri suka yi ɗakinta. Mameey ta riƙota sosai lokacin tana ta ƙara ƙwalla ƙara kamar wadda bata hayyacinta. "Sadiya...!" Mameey ta furta tana jijjigata a lokacin taga idanunta a juye suke bata cikin hayyacinta. "Saddiqa muje ku kaita asibiti kamar bata cikin hayyacinta, Surayya ɗauko hijabi ki saka mata. Da sauri ta ɗauko Mameey ta ɗauketa ta kai motar Saddiqa. Suna zaune sun ƙura mata ido tana bacci lokacin an saka mata drip. Wayarta ta fara ringing, ta kalla "Affan ne ke kiranta" Cewar Surayya. "To ki ɗaga sai ki sanar masa bata da lafiya tana asibiti" Tana sanar masa ya kuwa ce ga shi nan zuwa. "Wai Dada wulaƙanci sosai ta yi?" Saddiqa ta tambaya tana kallo Surayya. "Wallahi mantawa da alaqa ta yi ta karta rashin mutunci, nima ganin Faruq a tsaye ne kaɗai ya saka ban mata rashin kunya ba. "Shima Faruq kafiya ya haƙura mana, wallahi Sadiya bama sa'ar auren shi ba ce" "Uhmm! Ni kaina haka na ce a lokacin da Aunty Sady na ƙoƙarin haɗamu na ce ai ni na fi ƙarfin Faruq, ashe shi ita yake kallo bama ni ba" "So dai bai masu halacci ba, yanzu ga shi ana neman lalata zumunci" "Wallahi kuwa." Ko mintuna talatin ba ayi ba sai ga Affan tare da Mommy da kuma Lawisa. Surayya ta bawa Mommy kujera ta zauna cike da mamakin kamanninta da Nashwa. "Ya jikin nata?" Affan ya tambaya. "Da sauƙi, ai bamu daɗe da zuwa ba, kuma ana saka mata drip ta samu bacci" "Amma me doctor ya ce?" "Kawai damuwa ce, ka san Aunty Sady akwai zurfin ciki, idan kuma abin ya yi yawa sai ya zamar mata damuwa" "Allah ya ƙara sauƙi" "Amin ya rabbi" Sun ɗan juma a asibitin kafin su tafi, da yamma kuwa Mameey tazo, sai dai duk budirin da ake yi Faruq bai san Sadiya na asibiti ba sai dare, kuma wurin 10:30 daya dawo Mameey ke sanar masa, a hakan ya dage sai yaje asibiti. A can ya kwana Mameey tausayinsa kawai take tana ganin son Sadiya kamar wata babbar ƙaddararsa ce tunda tare suka taso kuma bai taɓa faɗa ba sai a yanzu da har tayi aure ta hayayyafa. ********** "Gaskiya ban yi tunanin Sadiya bata so ba, a ƙa'ida babu yadda za ai mu aura mata wanda bata so, tana da 'yancin zaɓar mijin aure" Cewar Baffa, Faruq ya ji gabansa ya faɗi hanjin cikinsa sun kaɗa. Sadiya murmushi ta yi cikin jindaɗi ta ce "Baffa ina da wanda muka yi magana, idan ka bani dama zan ce su turo" "Malama sai ki bari ki gama warwarewa dududu jiya kika dawo daga asibiti" Ɗan zuɓurar baki tayi a lokacin da Mameey ke furucin. "Ki barta lafiya ai ta samu, Sadiya ki masa magana su turo zuwa jibi" "To Baffa" Ta furta tare da miƙewa, Faruq da ido kawai ya bita, Saddiqa kuwa sam bata ji daɗi ba amma ba zata iya cewa komai ba. Baffa ya gyara zama ya kalli Faruq "Ka yi haƙuri ka nemi wata, Sadiya ta fi ƙarfinka, ga Surayya ko kuma ka zaɓa a cikin 'ya'yan dangi" "Baffa ni ita nake so, kuma idan har kuka ce ba zaku bani ba zan kashe kaina ne" "Kisa? To shi kenan Allah yajiƙanka, ai mu bamu sangartaka ba, kuma ba zamu ɗauki rashin hankali ba" Cikin ɓacin rai Faruq ɗin ya tashi ya fita. ************ Kallon shi Umma take yana dire maganar ta ɗauke shi da mari, hannu ya saka ya kama kuncin, Maryam da Fatima kuwa dukkansu da mamaki suke kallon Umma. "Ashe kai mahaukaci ne ban sani ba? To ka gaggauta zuwa ka karɓo motar da ka mayar da duk wani abu idan ba haka ba wallahi sai na tsine maka" "Umma!" "Rufa min baki, ita matar da zaka aura kana tunanin ba zata riƙe yaranka ba? Ko kuma ni riƙon da nake musu bai maka ba?" Miƙewa ya yi tare da cewa "Umma duk riƙon da za ayi wa yaro ba kamar uwar data haife shi ba, Allah ya sani ina son Sadiya kuma ina ji a raina har abada ba zan samu madadinta ba" "Ni kuma na maka alqawarin duk ranar daka dawo da Sadiya to daga wannan rana sai dai ka canja wata uwar bani ba" Kallon Ihsan ya yi tana gefe ta yi shiru, duk yaran sun fita hayyacinsu, ga babu wata kula, kayanta sun yi datti sosai. "Maryam ki shirya su anjima zan kai su gurin Mamansu" "Babu inda za ka kaisu, idan ganinsu take son yi tazo nan ta gansu" Bai ƙara cewa komai ba ya saka kai ya fita. A ƙofar gidan ya zauna, ya rasa abinda ke masa daɗi, ya kuma rasa ta ina zai fara yiwa Sadiya bayani har ta fahimcesa, ga Lawisa ta addabeshi da kira, haka shago ma mutane sun dame shi duk da ya mayarwa duk wanda ya saka order kuɗinsa. Kai ya sunkuyar ƙasa, tare da riƙewa sosai. "Meyasa na aikata hakan a gareki?" Ya furta kamar zai yi kuka. Ya daɗe a zaune a gurin kafin ya janyo waya ya saka number Sadiya, sai dai har ta yi ringing ta katse bata ɗaga ba, ya sake kira a karo na biyu. Tana fitowa daga toilet ta ji wayar na ringing, da sauri ta ɗauka, tana ganin number gabanta ya faɗi, duk da ta goge amma lambar a kanta take, a sanyaye ta ɗaga tare da karawa a kunne. "Assalamu alaikum!" Yana jin muryarta ya sauke ajiyar zuciya. "Sadiya fatan kina lafiya" "Hmmm! Yazid lafiya kuwa?" Wani iri ya ji dan ya daɗe bai ji Sadiya ta kirashi da sunansa ba. "Lafiya lau, yaranki ne ke kewarki" "Uhm! Allah sarki, ina fatan suna lafiya?" Ta faɗa lokacin da ta ji wasu hawaye masu zafi sun zubo mata . "Lafiya lau sai dai ko yaushe sai sun tambayeki" "Meyasa ba zaka kawo min su na gansu ba?" Ta furta murya a karye. "Sadiya kuka kike?" Hannu ta saka ta rufe baki, "Dan Allah Sadiya ki daina" "Ina fatan yarana suna nan lafiya?" Ta sake maimaitawa. "Lafiya lau, amma yaushe za ki zo ki gansu? Ina so na kawo su amma Umma ta hana, kuma suna son ganinki" "Zan zo insha Allah, ka gaishe min dasu" Tana gama faɗa ta kashe tare da fashewa da kuka. *SAURA 1 PAGE MU GAMA FREE PAGES* *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._* *_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_* Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* lLITTAFAN SUNE: 1-WUTAR ƘAIƘAYI 2-WA'ADI. 3-A CIKIN IDO.. 4-TAZARAR SO #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah [7/9, 9:43 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@sanazty _Facebook@SaNaz Deeyah_ Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ _Book 1_ ```Last🆓 Page 20``` "Sadiya kina ji na kuwa?" Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa "E" "Sadiya idan babu damuwa ina son ganinki, akwai wata magana mai muhimmanci da nake so mu yi" "Gani na ba abu bane mai yuwuwa Yazid kawai ka yi haƙuri" Har za ta kashe ta ji ya ce "Ina so na faɗa miki dalilin daya saka na sake ki" Jin haka ya sa ta kalli wayar sannan ta ce "Idan har ka san ba wannan bane dalilin ganin kada ka saka na ɓata lokacina" "Wallahi shi ne Sadiya" "Shi kenan, zan yi tunanin inda zamu haɗu da yamma" "To babu damuwa Allah ya kaimu" "Amin." Tana ajiye wayar aka turo ƙofar. "Sarakan kuka, ke dai ba zaki bari ba" Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce "Na tuno su Najma ne" "Allah sarki, ni kaina kullum cikin tunanin su nake, last week ma naje na gano su, ban faɗa miki ba dan bana so na ɗaga miki hankali" "Surayya ya suke dan Allah?" "Alhamdulillah! Amma dai gaskiya suna cike da kewarki har yanzu basu manta ba" "Da raina amma an rabani da yarana" "Ki cire su a ranki dan Allah Aunty Sadiya" "Hakan ba mai yuwuwa bane, ba zan iya ba" "Za ki iya indai kika saka hakan a rai" Shiru babu wanda ya ƙara magana. "Aunty Sadiya yanzu nan da kwana huɗu kin zama mallakin Affan" "Kamar a mafarki ko?" "Sosai ma, ai na ɗauka Mameey za ta dage sai kin auri mai kuɗi, ko dan ashe Affan ɗinma masu kuɗi ne" Murmushi Sadiya ta yi. "Amma Faruq tausayi yake bani" "Tausayi kuma?" "E, baki ga ko zaman gidan baya yi" "Daga zarar na yi aure zai manta komai tunda zai koma karatu ma, Surry idan na auri Faruq ban masa adalci ba, a gaskiya so bai ma Faruq adalci ba daya saka masa ni a ransa" "To hakane, amma gaskiya yana bani tausayi wallahi ramar tsaye kawai yake" Murmushi Sadiya ta yi sannan ta ce "Ni kuma yarana kawai nake tausayi, ina so naje na gansu, amma bana son zuwa har sai bayan na yi aure" "Tabbas su Najma abin tausayi ne, amma still ba kamar Faruq ba" "Surayya kina son Faruq" "A baya ai ban fi ki son shi ba" "Har yanzu he's my number 1, amma ya kamata na taka masa burki dan ya san cewa ina gaba da shi." Shiru na ɗan wani lokaci ta yi kafin ta ce "Wallahi har yanzu mamaki nake sosai idan na tuna wai Faruq ya iya buɗe baki ya faɗawa Mameey yana sonki" "Ni kuma raina ne yake ɓaci, saboda Faruq nawa yake, nan fa nake fighting ma shi ke, ashe shi hangensa da ban ne" "Aikuwa dai da ban ne, shi Yayata ya gani" Murmushi ta yi sannan ta ce "Ina tunanin tausayina kawai yake, da kuma irin gwagwarmayar da nake fama da ita, amma kin san wani abu kuwa?" "Sai kin faɗa" "Idan har da gaske Faruq sona yake to lallai yana da matsala a ƙwaƙwalwa" Dariya Surayya tayi "Kai Aunty" "Allah dagaske nake?" "Yanzu ban ma sani ba, ko zai je wajen walima" "Bana jin zai je gaskiya, Faruq fa bacci kaɗai yake shigo da shi gidan nan" "Allah ya yaye masa" "Amin dai" "Anjima za ki rakani wani wuri" "Ina kenan?" "Ke dai zamu je" "To partyn fa?" "Ni fa babu wani party da zan yi yau, jibi in aka yi walima ta wadatar" "To Allah ya baku zaman lafiya Mrs Affan" Murmushi ta yi sannan ta cigaba da abinda take yi. ********** A ƙofar gidan napep ya sauke shi, jiki a sanyaye ya fita ya sallami mai napep yana ƙarewa gidan kallo. A haka dai ya ƙarasa bakin get ya ƙwanƙwasa. Maigadi ya fito ta ƙaramar ƙofa. "Sannu" "Yawwa, ko Affan yana ciki?" "E, bai daɗe da shigowa ba" "To in babu damuwa ka yi mini iso." "To ka ɗan shigo daga ciki, sai a kirawo shi" Bai musa ba ya shiga, ya kuma tsaya har maigadi yaje ya dawo. "Ya ce yana zuwa" "To nagode" "Haba karka damu" Yana nan tsaye Affan ya fito kuma tun daga nesa yake masa kallon mamaki har zuwa lokacin daya ƙaraso ya miƙa masa hannu duk da bai tunanin zai ba shi ba amma sai ya ba shi suka yi musabaha. "Mu ƙarasa ciki" "A'a nan ma ya isa" "Okay bara na ɗauko kujeru" maigadi ya saka ya kawo musu kujeru suka zauna. "Ina jinka, mene ke tafe da kai?" Shiru Faruq ya yi kafin ya ce "Alfarma na zo nema wajenka" "Alfarma?" "E" "To ina jinka?" Iska ya furzar sannan ya kalli Affan "Ina so ka yi min alfarma na auri Sadiya" Kallon mamaki yake bin sa da shi kafin ya ce "Ka san kuwa abinda kake faɗa?" "Na sani, dan Allah ka taimaka min, bana so Sadiya ta yi aure inda za ta wahala, ni kuma koda zan yi yawo da yagaggun kaya, ba zan bar Sadiya ta shiga wani yanayi ba" Hannu Affan ya saka ya dafa kafaɗar Faruq "Sadiya ba zata taɓa wulaƙanta ba, domin ina mata son da ko kai baka yi mata" "A'a, ka sani Sadiya jinina ce, kai kuma kana son ta ne kawai saboda kamar da take da tsohuwar budurwarka" "Wannan ba gaskiya bane" "Wallahi idan ban auri Sadiya ba ba zan taɓa samun sukuni ba, wallahi har mutuwa zan iya yi" "Nima haka nake ji a raina" Cije laɓɓa Faruq ya yi, sannan ya miƙe a fusace. ******** Tana zaune ta sake kallon Surayya da take shiri sannan ta kalli wayarta. "Surayya time yana ƙurewa dan Allah kiyi sauri, kin san idan 5 tayi ba lallai Mameey ta bari mu fita ba" "Yi haƙuri Aunty Sady, bari na ɗaura ɗankwalin" Ta faɗa tana ƙarasawa gaban madubi. Mameey da Umma Habiba da wasu baƙi biyu suna falo suna hira, tsakar gidan ma akwai tsirarrun mutane da suka fara zuwa saboda bikin. Faruq kai tsaye ya faɗo falon, Mameey ta kalleshi, dan gabaɗaya ya burkice. "Mameey Aunty Sadeey tana nan kuwa?" "E suna ciki amma suna shiryawa za su fita su karɓo ɗinki." Bai ce komai ba taga ya wuce kitchen, bai daɗe ba kuma ya fito ya yi ɗakin Sadiya da Surayya. Yana tura ƙofar suka juyo gabaɗaya, dan a tunaninsu Saddiqa ce saboda itace ta ce musu tana hanya. "Oh Faruq ka shigo kenan" Cewar Surayya. Ita kuma Sadiya tunda ta kalleshi sau ɗaya ta ɗauke kai. "Kin ce ba zaki aureni ba saboda na miki yaro? Kin kuma ce ni ba sa'an aurenki bane" Jin haka ya saka Sadiya ta kalleshi, sai data ɗan tsorata dan idanunsa sun zama jajir amma sai ta dake. "Kai Faruq ka shiga hankalinka, ni ba sa'arka bace, kodan ka ga babu wanda yake taka maka burki?" Murmushin yaƙe ya yi sannan ya ce "Mace bata taɓa fin ƙarfin namiji Aunty Sady, ki sani nana Khadija ta girmi manzon Allah amma kuma itace uwar 'ya'yanshi, sannan mu kuma muna koyi da shi dan haka ba zaki taɓa fin ƙarfina ba. Surayya ɗan lumshe ido ta yi sannan ta ce "Faruq ya kamata ka bar maganar nan tun da an riga an warware komai kum...." "Dalla malama rufa mini baki" Ya daka mata tsawa, kallon shi ta tsaya yi da mamaki. "Duk ba kune ke zuga ta ba, musamman ma ke sai na yi maganinki" "Ni kake yiwa tsawa?" "Na yi miki, ko haifa ta kikayi?" Za ta sake magana Sadiya ta yi saurin dakatar da ita. "Ki ƙyale shi kawai" Murmushin gefen leɓe ya yi sannan ya ce "Za ta ƙyaleni kam, kamar yadda na shirya ƙyaleku gabaɗaya" Yana gama faɗa ya ciro wuƙa, Surayya ta tsorata amma Sadiya ko a jikinta. "Zan kashe kaina ne, da naga aurenki da wani na, gara na bar duniya" "Ba zan hanaka ba, saboda ka san hukuncin wanda ya kashe kansa" "Faruq kada ka aikata haka dan Allah" Cewar Surayya. "Ki rabu da shi, tunda baya da hankali ya kashe kan nasa, ai da tuni sai ya kashe bama sai yazo gabana ba" "Hakan da kike ya ƙara tabbatar da baki sona, amma ki sani ni ina sonki har cikin raina, gara kawai na mutu dan ki samu kiyi rayuwa mai kyau" Yana gama faɗa da mamakinsu suka ga ya ɗaga wuƙar da ƙarfi ya sokawa cikinsa, Surayya ta ƙwalla mahaukacin ƙara yayinda Sadiya ta ƙame a tsaye idanuwanta gabaɗaya a waje. Cikin tashin hankali Mameey da Umma Habiba ke rige-rigen shigowa ɗakin, a lokacin kuma ya faɗi ƙasa Surayya taje gabansa shi kuma ya saka hannu yana ƙoƙarin zaro wuƙar Mameey ta riƙe hannun tare da fashewa da kuka, "Mene haka? Ya nake ganin wuƙa a cikin Faruq" Surayya kuka kawai take, lokacin idanunsa suna kanta amma da gani baya cikin hayyacinsa saboda jini kawai ke fita a cikinsa kafin daga bisani ya fara aman jinin. "Shi kenan mun shiga uku, Furuq duk wannan na mene?" Mameey ta furta tana kuka, Surayya ma kuka, Sadiya kuwa har lokacin ko motsayawa batayi ba daga inda take tsaye. Maƙocinsu da wasu samari biyu da sauri suka shigo aka fita da shi, duk cikin tashin hankali suke, sai da aka fita babar Rayyana ta kula da Sadiya a tsaye ƙiƙam ta zama shocked, ta ƙarasa gabanta . "Sadiya ki kwantar....." Ko gama faɗa batayi ba Sadiyar ta sume mata anan. _*Asibiti*_ Suna tsaye ƙofar emergency Surayya kuka kawai take, yayinda Saddiqa take zaune ta dafe kai, sun fi awa biyu a gurin kafin likita ya fito. "Dr ya jikin nasa?" Mameey ta tambaya cikin tsananin tashin hankali. "Ku kwantar da hankalinku, anyi nasarar fitar da wuƙar har an masa ɗinki, amma yanayinsa ya saka dole zamu tura shi ICU." "Shi kenan Faruq, innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Mameey ta furta tana fashewa da kuka. A hankali ta buɗe idanunta, sai kuma ta fara ganin abinda ya faru kamar mafarki ne ta yi. "Sannu" Jin haka ya saka ta yi saurin duban gurin, sai dai ganin maƙociyarsu ya saka ta miƙe zaune cikin tsananin tashin hankali ta ce "Kenan ba mafarki nake ba?" "Sad...." "Ina Mameey take, ina Faruq dan Allah kada ki ce min ya mutu" "Ki kwantar da hankalinki, Faruq sun tafi asibiti, kema tun ɗazu wayarki take ringing na ɗaga na faɗa baki da lafiya to mutumin ma har yazo" Ba ta ko kulata ba kawai ta miƙe da sauri taja mayafi ta fita. A ƙofar get ta ci karo da Affan. "Sadiya kin far...." "Affan na shiga uku, Faruq ya taɓawa kansa wuƙa wai saboda ni" Sai kuma ta fashe da kuka tare da jingina kanta jikin motarsa. Sai da tayi kuka sosai sannan ta ɗago jajayen idanunta ta kalleshi. "Sadiya kar mutane su gane halin da kike ciki dan Allah ki shiga mota." Bata musa ba, ta buɗe ta shiga tare da kwantawa jikin kujera, shima shiga ya yi, ya kunna motar tare da kunna AC. "Meyasa Faruq ya yi haka?" "Ni kaina har yanzu da kike faɗa mini ban gaskata ba." "Wai saboda zan aureka shi ne ya ce gara ya mutu ya bar mini duniya." "Yanzu yana ina?" "Asibiti, ban ma san a wane asibiti suke ba, dan Allah ka kira Surayya ta faɗa maka sai ka kaini." "Ok, amma ina so ki kwantar da hankalinki please." Surayya ya kira ta faɗa masa asibitin da suke ya ɗauki Sadiya suka tafi. A tsorace ta ƙarasa inda ta hango su Mameey zaune, sai dai tana zuwa Mameey ta miƙe tsaye tare da faɗin "Mene ya kawo ki nan?" "Mameey....." "Sadiya ko nan ma zuwa kika yi ki ƙarasa shi?" Kuka ta saki. "Ki tafi daga mu har Faruq babu mai buƙatar daganinki, dan Allah ki bar wajen nan." Babu wanda bai bawa Mameey haƙuri ba har Affan amma haka ta rufe ido gani take kamar ma Sadiya ce ta soka masa wuƙar. A mota kuka kawai take Affan dai ya zuge glasses ya kunna AC, shima shiru ya yi yana nazari, sai da tayi kuka mai yawan gaske sannan ta share hawayenta. "Affan...!" Ta ambaci sunanshi da dasasshiyar murya. "Sadiya karki ce komai a yanzu, kiyi haƙuri ki kuma kwantar da hankalinki insha Allah komai zai daidaita. Ajiyar zuciya ta sauke tare da riƙe ƙirjinta da taji ya mata nauyi sosai. "Ka mayar dani gida" Bai musa mata ba, yaja motar suka koma, sai dai bai ma ƙarasa ba Saddiqa ta kira shi ta ce masa kar ya bar gurin Sadiya har sai tazo dan gudun kar ta aikata wani abun. A ƙofar gidan ya parker mota ya kunna karatun al-qur'ani sannan ya kwantar da bayansa jikin kujera gami da lumshe ido. "Sadiya ki riƙa istigfari" Kai kawai ta gyaɗa masa, a haka har Saddiqa ta zo sannan tayi masa godiya taja Sadiya suka shiga ciki. "Aunty dan Allah kina ganin Faruq zai tashi? Bana so Faruq ya mutu Allah ya saka shi a wuta." "Muna saka rai insha Allah zai tashi, amma for now yana ICU" "Mameey ma ta kasa fahimtata, Aunty ba zan iya zaman aure da Faruq ba ganinsa nake a matsayin ƙani na, ban san ta ina zan fara yi masa biyayya a matsayin miji ba" "Sadiya ki kwantar da hankalinki, dukkanmu mun fahimceki, ita kanta Mameey ruɗewa ce ta saka tayi haka" Sosai Saddiqa ta rarrasheta, ranar ma tare suka kwana, su Mameey dai basu dawo daga asibiti ba duk da Faruq ɗin a ICU yake. _Ranar Juma'a_ *04:00pm* Tana kwance akan gado, idanuwanta suna kallon POP ɗin ɗakin, jin an turo ƙofa ne ya saka ta kai dubanta ga ƙofar ganin Saddiqa ya saka ta miƙe zaune a hankali. "Aunty ya jikin Faruq ɗin?" "Da sauƙi" "An fito da shi daga ICU ɗin?" "A'a amma dai yana ta samun sauƙi" "Aunty dan Allah ki bawa Mameey haƙuri ta bani damar naje na dubashi." "Za kije amma kafin nan dai taso muje Baffa na kira" "Baffa?" "E, ke amarya ce Sadiya" "Amaryar wa? Kenan ba a ɗaga bikin ba? Kuma ina ta kiran Affan tun safe wayarshi bata shiga" "Ki dai zo muje" Hannunta Saddiqa taja a lokacin kuma hawaye ya sake zubo mata. A parlour ta ga Baffa da ƙanensa sai wasu mutane biyu da bata sansu ba, zama tayi a ƙasa Saddiqa ta zauna kusa da ita. "Sadiya!" "Na'am" Ta amsa a sanyaye. "Karɓi wannan" Ɗagowa tayi ta kalli Baffa taga ya miƙo mata bandir biyu na kuɗi. "Wannan sadakin ki ne, dubu ɗari biyu, yanda aka saka bikinki ba'a ɗaga ranar ba, mun ɗaura aure kuma a yanzu girma ya ƙara hawa kanki, a yanzu ke matar aurece, matar...............! *Wa kuke tunanin Sadiya ta aura?* *Affan ko Faruq? Ko kuma wani ne da ban?* *Amsoshinku suna cikin Book2, ku biya ₦500 kacal domin cigaba da karanta littafin *WUTAR ƘAIƘAYI* *VIP ɗin littafin ₦1000 ne, sannan idan ya zama Complete a ₦1000 za a sayar da documents* _Mu kasance daku a fagen cigaba ga wanda suka biya kuɗaɗensu ta asusun dake ƙasa👇_ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels