An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels https://chat.whatsapp.com/DoFR3n8lLtI1RB5Zd2z2IT 💔RAYUWAR UMMAH💔 BY NARNAH ƘANWAR SOJA (Sayeedan Addah). 08101235739 💫 ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION 💫 16/11/2024. Happy birthday sister Najnurr ( Br barkama) Ubangiji Allah ya ƙara year’s masu albarka 💖 Page 1 & 2 "Yaushe zake dawo typing! We miss you! To ga new update!". Finally Narnah ƙanwar soja is back "Yes am back tare da zazzaffan labari mai ciki da darrusa da tsaƙwarar soyayya duk a cikin RAYUWAR UMMAH...... ADAMAWA YOLA A dai dai wane siririn lungu motar taxi ke shirrin tsayawa, cikin zafin nama aka bankaɗo ƙofar tamkar daga sama aka jifota cikin sassarffa batare da rufe kofar motar ba taye gaba .. Burinta kawai ta shiga izuwa cikin mutanen da sukaye cincirindon a ƙaramin kofar gidan duk juyawa sukaye suna kallon ta baki a buɗe bata bi ta kansu ba ta kutsa kai. Ganin Mubarak da gajeren wando da shabgigiyar bulala a hannun sa inda ya saita ƙarfin sa zai kai wane bugun charaf ta kama bullalar ciki da bakin ciki da takaicin da bai da misali ganin hakan ya joyo cikin tangalili. " UMMAH" abinda ya furta Kinan da sauri yarinyar da bazata haura shikkara Goma sha shida ba dake durƙushe a gaban sa yana jibgarta da ɗaure hannun ta da ƙafafuwan ta jin an ambaci sunan UMMAH da ko a mafarki bataye tsammanin wannan sunan ba a tsanaki ta kurma uban ihu da cewa “UMMAHHHH“.... Tana ƙoƙarin matsowa bahagun mari UMMAH ta zabga masa wanda yayi sanadiyar zubewar sa ƙasa yana tangalili , bata jira maganganun mutanen gidan ba ta kunce Munira da ke ta zubar hawaye nan ta tallafa ta suka bar cikin gidan ganin Ameera a motar tana sharar hawaye ta rungume ta tsafff UMMAH ta rufe kofar Kinan yayi dai dai da zuwan Farooq " mujee driver ye sauri taka mota mubar unguwar nan " Cewar UMMAH. Kai tsaye Farooq ya shiga cikin gidan ganin Mubarak tsaye yana tangalili sai huccen masifan da yake ta zubawa dogon tsaki yaja " Aikin banza ka sha giyar ka ka jibga matar ka ko ko kunyar hakan bakaje " . Sanin cewa baya cikin hayachin sa ya juya tare da shiga motar sa kai tsaye sai Unguwar Runde a ƙarshen kwalta ya tsaya cikin kadarra da ƙasaita ya nufe wane sirririn lungu a dai dai wane zauren gida ya tsaya da aka rufe da mayafin buhu kasancewar babo ƙofa a ruɓaɓen gidan sai wane ya motse fuska yakiye yana ganin gidan up and down...... " Idan ba don yarinyar nan akwai kaya ga daɗin harka da zubin kyau na yarinyar nan ba uban wa zai sa nazo wanan ƙazamin wurin har wata banzan Yarinya tace zata gayyamin magana wai Ummah shegiyar yarinya ko matsayin mai wanke min toilet bata kai ba wanan shine Ƙaddara ta"............... Karamin yaro ya aika cikin gidan sai dai masifan da zagin da Ummah take ye ne yasa kai tsaye ya kutsa kai domin nuna mata true colour sa....... WAYE FAROOQ? To be continued.......... 💔RAYUWAR UMMAH💔 BY NARNAH ƘANWAR SOJA (Sayeedan Addah). 16/11/2024. 💫 ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION 💫 "Yaushe zake dawo typing! We miss you! Muna son new update!". Finally Narnah ƙanwar soja is back "Yes am back tare da zazzaffan labari mai ciki da darrusa da tsaƙwarar soyayya duk a cikin RAYUWAR UMMAH. Page 3&4 WAYE FAROOQ? Umar Farooq Tambuwal Yaro mai taƙama da kyau da kuɗi ɗaya tilo a gidan Alhaji Farooq Tambuwal ya taso cikin gata da sakalchi daga primary school Nasa har ya kamalla karatu a matakin professor a kasar Amurka kasancewar sa yana son kasar sa Nigeria yasa ya dawo anan kuma ya samu gurbin zama lecturer a makarantar nan ta Abti University Yola jihar Adamawa state, duk da cewa bai cika zama anan ba but yana zuwa a time da yake so ya kuma time da yake so hausawa sukace komai na kuɗi ne . Umar Farooq yana da shekaru 28 izuwa yanzu da yake kan matakin 29 bashi da wane halli a rayuwar sa sama da neman manta duk inda macce take da zarar ya kai idon sa kanta tofa sai ya lashe zumar jikin ta ko ta wacce hanya ce. Farooq bashi da wane abokin a rayuwar sa sama da Mubarak ka tsaye yafe karfin sa nisa ba kusa ba sai dai wane babban ƙaddara ya haɗasu guri daya har suka ƙulla abota kasancewar Mubarak yaron talakawa ne sai dai bai taɓa damun Farooq domin bashi da wane banzan hali na ƙyamar talaka a rayuwar sa shi dai babban burin sa ya su macce a lokacin da ya kiso Mubarak Ali Saurayi mai kyau da nagarta ga basira sai dai kash ya kasance babban tantiri a unguwar su ta Runde inda kowa yasan wanan bak'ar halin nasa na sata da kuma shaye shaye babban abun mamaki a tare dashe a duk lokacin da faɗa ya taso ko i gidan ubanwa to zai shiga domin kare martabar unguwar su hakan yasa duk abinda yace a cikin wannan unguwar ake tsoron sa dole kuma a be wanan umarnin nasa domin a takaice idan ka nuna bazaka biba to iyalan gidan ka sun shiga ukku hatta ƴan sandan unguwar su sun kasa masa komai akai domin dai sun gaji da kama sa har ta kaiga ya kafa wata banzar ƙunƙiya ta masu shaye shaye a bayan makarantar primary na govnatii. Mubarak na samun kudin kashewa ta hanyar sata ko damfara da yasa ba ye sai kuma wasu ƴan siyasa suka fara ɗaukar nauyin sa izuwa ga aikin dabanci anan Mubarak ya shahara a kasanshi duk abinda yake aikata a zahiri Mubarak hankalin sa baya kan mata burinshi shaye shaye da kuma dabanci mutum ne mai ƙarfe da basira haduwar Farooq da Mubarak ta haifar da babban fitina da matsala kasancewar idan Farooq yazo Nigeria Mubarak she yasan lungu da saƙon nemo ƴan mata she kuma yana bashi manyan kuɗaɗi a hakan suka ƙolla babban abota da ta zama sillar jifa rayuwar UMMAH cikin masifa da fitina wanan itace ƙaddara ta riga fata.. a wannan lokacin ne kuma idon sa yakai ga Ameera ɗiyar Ummah Kinan Back to story.. Karamin yaro ya aika cikin gidan sai dai masifan da zagin da Ummah take ye ne yasa kai tsaye ya kutsa kai domin nuna mata true colour sa....... TO BE CONTINUED........ 💔RAYUWAR UMMAH💔 BY NARNAH ƘANWAR SOJA (Sayeedan Addah). 16/11/2024. 💫 ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION 💫 Barka d ranar juma'a Allah ya amsa mana bukatar mu Share domin Allah da Manzonsa S A W 🥰 "Yaushe zake dawo typing! We miss you! Muna son new update!". Finally Narnah ƙanwar soja is back "Yes am back tare da zazzaffan labari mai ciki da darrusa da tsaƙwarar soyayya duk a cikin RAYUWAR UMMAH. Page 3&4 Karamin yaro ya aika cikin gidan sai dai masifan da zagin da Ummah take ye ne yasa kai tsaye ya kutsa kai domin nuna mata true colour sa. " Na rantse da Allah Mama babo wacce zata kuma gidan mijin ta don uban mutum suzo su sake su don ban haifa ba kuma ban raina wa mazan banza yara ba shegu ƴan isk....." Katse ta yayi da magana cikin harƙuwa " ƙarya ne na rantse na sake matata akan ke ke har kin isa ke raba ne da matata Ummah ke bine a hankali tun kafin na sa a rufe ke a ƙasar nan har karshen rayuwar ke bazake sake kallon ko idon rana ba " "A'a Farooq gani kar ka ɓoye ne a duniya kashe ne fitsararre mara kunya kashe ne ka kaine lahira yarinya dai nace bazata kuma ba idan kuma sake ne ka rigi takardar har ƙarshen rayuwar ka ɗan iska mazinaci ne zaka kwaso cuta ka sawa yarinya na mahaukachin banza tsinewar Allah ya tabbata akan ka " Cigaba da musayar magana sukaye har takaiga ya ɗaga hannu zai tsinka mata mari shigowar mai unguwan su ne yasa duk suka dakata umarni aka bayar nan aka fitar da Farooq sukaye waje mata biyu ne a gidan sai wata tsohuwar mata wacce ake kira da Mama .. kai tsaye Ummah ta shiga cikin dakinta da gudu Amira da Da Munira suka faɗa cikin ta suna taya ta kuka hannu bibbiyu tasa ta ƙara rungume su sai ga wasu zaffafan sirarar hawaye akan kyakkyawar chocolate fuskar ta dake dauke da O face sai dogon hancin ta da yayi dai dai da zabin buɗaɗen bakin ta saurin bude dara daran idon ta taye domin ba ta don yaran ta suga kazawarta har suka hawaye a wanan kyakkyawar fuskar na ta katse su taye da cewa " Amira ke daura mana ruwan zafi bare nayi sallah daga nan sai muyi mata wanka na sayo mata maganin da zai rage mata zafin dukan nan kuyi hakuri yara na tabads laife na ne da ba aurar da ku ga mazajen da Basu san muhimmancin ku ba ku gafar tamin Amira ce t adube ta da kumburin fuskar ta da cewa " Ummah har kina tunanin wanan laifin na ke ne laife na ne da nace ina son shi Domin a wanan rayuwar duk abinda muke so she kike mana to wanan dalilin yasa kika amince da auren mu kuma wanan shine (AUREN ƘADARRA my next book ). Kallon su taye cikin so da ƙauna ta nufe kofar fita juyuwa taye ta dube su da cewa " Kuban wayar hannun ku " Ameera ce ta miko mata bata tsaya masa dogon ajiya ba ta ajiye a kan ƙaramar akwatin ta , ta fita waje bayan sallah sunce taliyar da Ameera ta dafa har sun gyara jikin Munira ta samu tasha magani sai Bachin wahala da takiye .. Kai tsaye Ummah ta shiga dakin Mama ta sameta kwance ganin ta yasa ta miƙe " ƴar albarka kice daren nan"? faɗa wa jikin ta taye ta fashe da matsanancin kuka " A'a Khadijah kice yau da kuka ke tuna wacce ce ke ke tuna jajircewar ke da jarumtar da Allah ya bake, ke tuna karfin guiwar da kike dashi kifa Uwa ce wacce Allah ya bata rayuwar yara biyu alhali bata kai matsayin Uwa ba , ke Uba ne wanda Allah ya bake amanar rayuwar mata biyu cikin hukuncin sa da hikimar sa ya bake ilimi da basira da fasaha wajen ganin tarbiyyar su , shin kin manta duk duniya kicce Allah ya basu matsayin ƴar uwa ,kuma Uwa da Uba duka to me zai raunata tunanin ke har ke zubar da hawayen ke akan mutanen banza tsinannanu m Maganar tane ya katse lokacin da suka tsinkayo matar gidan na shewa da sauri suka fito abinda ya gani ne yayi mugun bata mamaki yanda numfashi ta ke kokarin ƙwacewa gangar jikin ta idon ta ne ya tsaya chakk akan Ameerah Mu haɗu a gaba domin jin yanda zata kasance meke faruwa a dai dai wannan lokacin? Menene asalin labarin Ummah da Ameera tare da Munira .... Kuna ƙorafi typing yayi kaɗan na ƙara kaɗan yawan comments naku yawan typing. Barka da Juma'a https://chat.whatsapp.com/DoFR3n8lLtI1RB5Zd2z2IT 💔RAYUWAR UMMAH💔 BY NARNAH ƘANWAR SOJA (Sayeedan Addah). 16/11/2024. 💫 ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION 💫 PAGE 7 @ 8 "Yaushe zake dawo typing! We miss you! Muna son new update!". Finally Narnah ƙanwar soja is back "Yes am back tare da zazzaffan labari mai ciki da darrusa da tsaƙwarar soyayya duk a cikin RAYUWAR UMMAH. Maganar tane ya katse lokacin da suka tsinkayo matar gidan na shewa da sauri suka fito abinda ta gani ne yayi mugun bata mamaki yanda numfashi ta ke kokarin ƙwacewa gangar jikin ta idon ta ne ya tsaya chakk akan Ameera dake tsaye da Farooq suna riqe da hannun junan su ɗayan hannun kuma yana cikin himmar nata yana wasa ganin Ummah sai da ta razana matuƙa itama Ummah ganin ikon Allah takiye "Mata ta zo mu bar gidan nan kin san a hannu nake " yana faɗa yana ƙarawa mannewa a jikin ta ja taye kaɗan ta baya zataye magana Ummah ta katse ta da cewa "A'a Amira basai kin min magana ba Indai akan namiji ne bazan mike mugun baki ba amma ke juya kawai ke fita ido na bana son sake ganin ke a rayuwa ta gaki ga duniya ga kuma mijin ke Farooq a kusa dake ke yafimin na tuba laife na ne da na nuna zan rabaki da masoyin ke kiye hakuri Allah baku zaman lafiya " Cikin sauri ta juya ta ɗaga idon ta sama nan taga Munira a Kofar ta fito duk abinda ke faruwa akan idon ta wasu sirararan hawaye ne yake biyo kumatun ta Umma ce ta juya kanta " kima ga Mubarak nan tare suka zo bazan hanna ku bin mazajen kuba " saurin dakatar da ita taye a ƙofar shigar ɗakin.... " Babo wane hallita irin na da zai zalunci rayuwa ta ko ya kyautata min kice bake son zama na dashi na juya miki baya a matsayin na na yarinyar ke kuma ƴar uwa ta ke sani rayuwa ta fansa ne a gari ke Umma ke yafe mana Amman bazan iya miki butulci ba Umma". nan ta zube akan guiwar ta dake mata radadin zafi sakamakon duka da Mubarak ya sharara mata ganin haka Umma ta shiga ɗaki tana cewa " Allah ya mike Albarka ". Maganar Mubarak ne ya dakatar da ita sai dai kuma bata juya ganin su ba " wacce ce za'a ci ta bine Allah ya kiyaye idan ban kashe matsiyaciya ba shima Farooq ai don yana da kuɗi ne itta Umma taki ta gama asirce shi dole tace Ameera ta bishi anga idon Naira " takarda saki ya watsa mata a inda ta ke durqushe " na sake ke saki Biyu wawiya shegiyar yarinya mara sa uba k ". Baiye tunanin cewa zai sake kallo a rayuwar sabba sakamakon wane azazzabibin abinda ya sauka a kan fuskar sa yunƙurawa taye zata sake buga masa dutsen hannun ta Umma ce ta janye ta " Kul banson rigima barshi da duniya gidan kashe aho tana jiran wanda ba'a haifa ba balle wanda yake cikin ta yake yawo ".sakamakon mutanen dake zagaye a gidan ne yasa suka kwantar da tarzoma tare da jansa wacce ... Duk fitta gidan sukaye inda Ameera ta bi mijin ta suka shiga Mota suka ƙara wuta sai a wanan lokacin ne UMMAH ta fashe da wane matsanancin kuka" shikkinan na rasa Ameera meyasa Amira why menene dalilin hakan " Munira da Mama ne suka rarrashi ta cikin dare tagama haɗa akwati biyu nata sai na Munira guda ɗaya dakin Mama ta shiga duk da cikin dare nan suka rungume juna ta fara rarrashi ta sanan ta haɗa da nasiha . "Ba komai Mama zan ɗauke Munira gobe zan kuma jahar Kano da zama duk da nasan cewa banda kowa kuma banda komai anmman Kano jahar ta ce watakila na haɗu da dangina bazan iya zama a garin nan ba gwada na ja Munira daga wanan shaiɗanin yaron kuma in Sha Allah na mike alƙawarin watarana zan dawo garike idan da nisan kwana , nasan cewa watarana Ameera zata zo gunke watakila ma ta tambaye ke ina muka kuma ke gayyama ta gaskiya cewa muna zama a Kano sai dai babo wane hujja ko dalili da zai sa tasan inda muke da zama domin ne kaina Bansan inda zamuje ba ga wanan takardar duk lokacin da tazo mike da wanan maganar ke bata shi mallakin ta ne na fita daga hakkin ta domin bata dauke ne da wane muhimmanci a cikin rayuwar ta ba......." Asubar fari Ummah da Munira suka shiga tasha a inda suka shiga motar Kano sai dai mucce Allah ya bada Sa'a tafiya Shin abunda Amira taye ta kyauta ? Menene asalin alaƙar dake tsakanin su Ya zata kaya Umma a Kano Suwaye dangin Ummah A hankali zamu kai labarin.. Narnah ƙanwar soja ✔️ https://chat.whatsapp.com/DoFR3n8lLtI1RB5Zd2z2IT 💔RAYUWAR UMMAH💔 BY NARNAH ƘANWAR SOJA (Sayeedan Addah). 16/11/2024. 💫 ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION 💫 PAGE 9&10 "Yaushe zake dawo typing! We miss you! Muna son new update!". Finally Narnah ƙanwar soja is back "Yes am back tare da zazzaffan labari mai ciki da darrusa da tsaƙwarar soyayya duk a cikin RAYUWAR UMMAH. **************************************** RAYUWAR UMMAH Tunda suka sauƙa a tasha da mangriba sukaye sallah chan ƙasar wani bishiya addu'a suka shafa nan suka zubawa juna ido cikin tausayawa da ƙaunar juna duk da cewa yau su biyu ne a maimakon su kasance su Ukku sirararan hawaye ne ya biyo takan fuskar Munira Umma ce taye saurin da Katar da ita da cewa " ajiye hawayen nan zai miki amfani wani lokacin yanzu mu fara tunanin ta inda zamu kwana da safe mu shiga gari mu nema gidan haya mu fara sana'a muga abinda Allah zaiye da rayuwar mu " girgiza kai Munira taye kai Umma na bare to yanzu ya zamuyi kwana a tasha nan fa da akwai hatsari" banda abunke yau muka fara kwana a tasha ai tun kuna yara anan nagama kwana daku sai tsoro bayan nan ba'a bunda kika iya " To Ummah zaki fara maganar ke ko ai dai kinsan Ameera " shiru taye tunawa da kar ran mahaifiyar nata ya ɓaci Murmushi Ummah taye ta jawo ta jikin ta suka rungume juna anan suka kwanta asubar fari hayaniyar tasha ne ya fara musu busa akan kunnen su...... Duk inda ya kamata su samu matsakaicin gida a unguwanni talakawa hakan baiye ba har sungaji da neman mafaka gashi yamma ya kawo kai chan kan babban kwalbiti suka zauna duk a gajiye suke ƙafar nan maso buzu buzu kamar an fisgosu daga daji ajiyar zuciya Ummah ta sauke don duk gajiyar ta tafi tausayawa Munira tunda ba wani lafiya gari ta ba jiki duk ciwo chan wani tsoho ya ƙarasu inda suke da sallama amsa wa Sukaye chan ya dube su " Shin da akwai taimakon da kuke nema nan hanyar gida nane tun ɗazon na hange kamar kuna da matsalar muhalli "?! Charraf Umma ta fisgo zancen kamar damar jira takiye ya kawo karshen zancen " ehh baba gidan hanya muke nema ɗaki ɗaya ne da yarinya na bamu samu ba don Allah ka taimaka mana " murmushi yayi sanan ya dube su da mamaki da maganar ta na cewa Munira yarinyar ta alhali kamar kanwa ce da yayarta " ka taimaka bana " cewar Munira da ta katse masa tunanin sa , ba komai cewar sa ko zo mujee gida na Amman sai kuyi hakuri da yanayin gidan tabbas akwai ɗaki biyu ma Amman dai kuna da kuɗin biya ko dubu ashirin ne a shekara " murmushi Ummah taye " Alhamdullah baba komai mun amince mujee kawai "...... Tsayawa chakk sukaye lokacin da suka tunkaro shiga gidan gaban Umma ne ya yanke ya faɗi ganin gidan kamar gidan karuwai ga ɗakuna daban daban a jire sunkai goma sha biyar ga kuma wasu ɗakunan na matasa maza daga farkon shiga gidan sai madafar girke chan ta hango mata ukku a bakin wane ƙaramin lungu da gidan ko da ta hangu su da buta ta tattabatar da cewa nan nin Bayan gida ne ( toilet kinan). Kulu ce ta tsaya daga jawo ruwan da takiye daga rijiya ajiye gugar taye ta gyara kallabin ta tana hango Mallam Jauro da ƴan mata kyakkyawa tamkar daga ƙasar larabawa don ma ita Ummah chocolate ce ba kamar Munira da hasken ta yayi fat ba , jin shiru Kulu da a take masifar ta tana jan ruwa taye shiru yasa duk suka zuba mata ido nan suka hango abunda take kallo ..... Gyaran muryar sa Mallam Jauro yayi da cewa " Ga abokiyar zama nan na kawo muku sauran ko koya mata wanan banzan halin naku kinga kawo kuɗin ga ɗakin da zaku zauna yana nuna mata wane ɗakin dake nisa dasu yayi " Nagode sosai Baba Allah ya saka da alheri buɗe jakarta taye nan ta fito da dubu goma ta bashi akan cewa kuɗin rabin shekara ta biya nan ya amsa har yana tuntuɓe, da saure Lantana ta matso bai ankara ba ta bangaje sa tana ƙoƙarin fisqo kuɗin nan suka fara kokuwa abin ba karamin razana Munira da Ummah sukaye ba ganin abinda ke faruwa ........ To be continued… 💔RAYUWAR UMMAH💔 BY NARNAH ƘANWAR SOJA (Sayeedan Addah). 08101235739 16/4/2025 💫 ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION 💫 Ga mai bukatar group wattsp kai tsaye kiye magana da Admin ta wanan number na sama ... Chapter 11 : Gidan Duhu Ruwan sama yana tsiyaya kamar ana zubar da kukan da zuciya ke ɓoyewa. gidan ba gini ba ne – tamkar mafarki ne da aka yi masa hijira, tsakar gidan cike da laka, bango mai ƙyalli da datti, ƙofar da bata jin murya sai da ƙarfi. a nan ne aka sauke su – ita da diyarta, bazawarar da bata da komai sai tarihin da ba kowa ke son saurare ba. Bazawara ce amma ba ta rasa komai ba idan ba angayamu ku Munira tayi aure ba bani wanda zai kawo hakan a ransa , domin tana da rauni mai kama da ƙarfi. Zuciyarta na ɓoye ɓarna, amma idanunta na nuna ƙudurinta: zata fara sabuwar rayuwa, ko da kuwa cikin barikanci da cakuɗaɗɗen mafarki." “Ummah kin ce zaki dawo?” Inji yarinyar da ke tsaye da wata ratattar jaka a hannu, idanunta cike da damuwa. Munira ta juya tana kallon ƙofar gidan ba ta da amsa, sai zuciyarta da ke shawagi da tambayoyi: Shin wannan ne mafita? ko kuwa kawai wata sabuwar ramin kunci ne.. Umma ce taga halin da Munira ke ciki duk da cewa ta fita shiga cikin matsanancin damuwa kawar da abin tayi a ranta ta janyo ta da cewa "Kwana biyu mukaye a gidan nan duk muna tsoraci bazamu dawwama a nan ba ya kamata na fita waje domin ganin abinda ya kamata muyi gashi ba wani isasshen kuɗi a hannun mu idan ba na abincin daren yau ba zan dawo Munira ke kasance a ɗaki kinga gidan yanzu ba kowa ana ruwan sama wasu kuma sun fita neman kuɗin su matan na ɗakin su ke tabbatar baki fita ko'ina ba sai na dawo Allah miki albarka " Ajiyar wani sihitirchin numfashi taye badon ta saurare maganar duka ba ta amsa don tasan lallai Ummah sai ta fita daga gidan yanzu " amin Ummah ke kula da kanki da ruwan sama nan ke dawo da wuri ina tsoro sosai" In Sha Allah " abinda ta furta kinan taye saurin fita gudun kar ruwan ya dawo da ƙarfi tun safiya ana ruwan sama har yamma ai dole ne kawai na fita na nemo mana mafita ta faɗa cikin zuciyar ta tana ficewa .. John dake zaune a cikin rumfar dake fuskantar gidan nasu ya hango fitar Ummah sai sauri takiye cikin ƙaramin lokaci hankalin sa ya kuma akan wanan budurwar da suka zo tare sai da ya tabbatar ta ɓace wa ganin sa ya shigo cikin gidan a sanɗa sanɗa kamar ɓarawo yana shafa gini yana tafiya har ya iso ƙofar daƙin akiye gyaran murya ta bayan sa a tsoraci ya juyo ganin Lantana da buta a hannun ta ya fara sosa kansa ya juya baya baya yayi hanyar fita girgiza kanta kawai tayi don yanzu farkawar ta daga bachi kinan take fitsari nan ta shiga ɗakin ta Bakin sa ya cizah" kash wanan matar ta ɓata min plan nan ya shiga ɗaki yana cizon yatsa, ana sallah mangariba sai ga Ummah ta dawo a gajiye da ƙaramin leader a hannun ta hankalin ta gaba-daya yana kan tillon ƴar ta da tabarta cikin wannan gidan ganin ta taye akan sallaya murmushi taye da sallama cikin kwanciyar hankali ta cire hijabi ta ta ajiye kasancewar ba sallah zata ye ba tayi hanyar bayangida don kar dare yayi a yanayin tsoro sosai take a gidan ..... Bayan kwana biyu --- Chapter 12: Gidan Duhu Munira na zaune a tsakar ɗakin tana kallon ruwan sama da ke kwaranya daga saman rufin da ke amai da ƙarfi, kamar yana bugu da bugun zuciyarta. Bayan sallar magariba, iska ta ƙara sanyi, ƙamshin danshin laka yana cakud'a da wari daga band'akin baya. Cikin dare, babu motsi a gidan sai kukan jariri daga wani d'aki da ba a san inda yake ba. Munira ta matse jikinta da bango, lallai yunwa na neman sa ta kai hannunta ga katifa, duk da ba ta jin kamar tana da ƙarfin tashi. > “Ummah,” ta kirawo da murya mai sanyi, “ki tashi mu fita daga gidan nan… wallahi ni tsoro nake ji, babu komai da za a ci, kuma ba kowa ke kallonmu sai kamar zamu fara sata ko shashanci.” Ummah ta juya daga kwancen ta, idanunta sun kumbura saboda rashin bacci da damuwa. Sai ta share hawaye cikin duhu, tace da ƙasa: > “Munira... mu fita ina? Wannan ba gidan arziki bane, amma barin sa babu shiri zai iya kai mu ga halaka, amma... wallahi ban san yau yanda zan shiga kasuwa gobe ba. jiya na nemo abu har zuwa kofar tashar, babu wanda ya saurare ni...” Nan take sai suka ji ƙaran fashewar roba daga waje, sai wata kara mai ban tsoro daga ɗayan d'akuna. Munira ta kwanta da sauri cikin hijabin ta, zuciyarta na dukan kamar za ta fito. A hankali sai ƙamshi ya shiga ɗakin, wani ƙamshi mai ɗaci da yake ɗaukar numfashi—ƙamshin shan giya da tabar wiwi. tana sanin hakan na nufin John Jibril ne—mutumin da ba ya san iyaka da dare. > “Ummah…” ta kuma kirawo da murya mai sanyi, “ki yarda da ni, mu bar gidan nan gobe. Ko da kuwa yawo ne za mu fara a titi, wallahi ya fi zaman cikin bariki da tsoro da yunwa.” Ummah ta jinjina kai, zuciyarta ta faɗi sosai. a wannan dare, ba ta iya tashi ba—amma kalmomin Munira sun haƙikance a ranta. ta san lokaci ya yi da za su nemi mafita. ko da kuwa hakan na nufin komawa titin rayuwa ba tare da tabbas ba. — 08101235739 08101235739 💔RAYUWAR UMMAH💔 BY NARNAH ƘANWAR SOJA (Sayeedan Addah). 08101235739 16/4/2025 💫 ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION 💫 Ga mai bukatar group wattsp kai tsaye kiye magana da Admin ta wanan number na sama ... Chapter 15 ... Gidan duhu... Bayan wata ukku Tabbas sun samu ƙalube daban daban daga wanan gidan na bariki wanda yayi sillar tarwatsewar dukkan wani farin ciki ko murmushi a fuskar su duk sun fita hankalin su duk wata sana'a Ummah na ƙoƙarin yinsa domin tsira da yunwa da mutunci tana kulla da Munira wacce gaba daya duniyar ta sauya mata inda Ummah ke bada ajiyar ta a gun Lantana kasancewar kullum tana gida sai dai Lantana mayar kuɗi ne na gaske anan Ummah ke baya ɗari biyar a kowani mako don kula da Munira idan Ummah ta fita kasancewar John yasha kawo mata hari amman Allah na kuɓutar da ita A yanzu wanki Ummah takiye a gidan wani ɗan sanda tana musu wanke wanke suna bata abinci sai tasa a leader ta dawo da dare suci da Munira sai kuma goben ta sake fita ba anan ta tsaya ba har ƙosai tana soya wa wani zubin domin tsira daga Bara ko mazan banza . BAƘIN DARE A RAYUWAR UMMAH Kamar kullum tagama dukkan aikace aikace ta mangariba ta kawo kai nan sa jiki ta shigo ɗakin da sallama ta zube "Hajiya na kamalla aiki na sai gobe da yardar Allah zan dawo " Wani dogon tsaki taja nan tace wannan kuma ubanki ne zaimin nace ubanki ne zaimin mara kunya ai kinsani yau Sunday Alhaji zai dawo naggayami ke tun Friday ke shiga ke gyara masa ɗakin sa sanan ke ƙara gogge min ɗakin nan shashasha kawai " ta faɗa tana jin tsaki ta juya nan tasa guntun mayafin ta tabar gidan ... Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyin gaske ta share sirarran hawayenta da suka zuba Miƙiwa taye cikin sauri ta fara aikin duk da ba wani dutty hakan bai hana ta dawo perlour da ta gyrah da safe ba ta sake goggewa har ƙarfe tara yayi nan ta kuma ta sa turare charraf take an zagaye hips nata da wani hannun da bataye tsammanin hakan ba ko a mafarki ihu take shirin tsalawa charass ya rufe mata bakin ta da hannunsa Faɗa suka fara yi tana juyuwa sunaye ido huɗu da Alhaji Isa gabanta ne ya faɗi man ta fara janyo addu'a a zuciya ta suna faɗa yana ta kokarin ganin yayi nasara akan ta Tabbas ƙarfin namiji daban da na macce domin kuwa yayi nasarar kifar da ita akan gado haka ya yaga mata rigar jikinta iya ƙarfin ta tana kare ƙirjinta da ya bayyana Amman kaman maye haka ya fara romance nashi suna dambe hankalin sa ne ya fara fotta sabi da annushuwa da yafara wanda wanda tun ransa ya fara ganin Ummah yada sha'awar ta hakan yasa ya cire hannun sa daga bakin ta ya fara yunkurin cire mata skirt cizo ta sauke masa a kunne sa wanda taja da karfin da batasan tana dashi ba take ya ɗinauce jini ya fara fitowa ta fizgo fatan da gaske a haukace ya tashe akanta ya janyo bindigar sa dake maƙale a wando sa ya saita kanta dashi a take duk da cewa ta tsorata matuƙa banda rawa da jikinta yakiye bata iya komai ba Hanun a zabure ta miƙe yana cewa " kwanta don Ubanke ko na kashe ke kwanta" kasko ta jawo dake manne da soket bai an kara ba domin zafi da raɗaɗin da kunnen sa ke masa buga masa tayi a kansa man ya zube warrr a ƙasa yana juye juye sai jini dake fitowa a sassan kansa cikin tsananin tsoro ta dauke rigar sa dake rataye ta sa a jikin ta da gudu ta fita tana hakki.......... A firgici ta shigo gidan ko sallama bank kai tsaye ɗakin su ta nufa tana "Munira! Munira !!Munira !!! cikin tashin hankali da fargaba cewa tayi kissan kai tashi mubar gidan nan Munira jini jini jini Munira".. ita dake zaune tana tunanin me ya faru har yanzu Ummah bata dawo ba gashi dare yayi karfe 10 saura wani jagarta kawai ta ɗauka taka Munira sunaye hanyar waje wanda mutanen gidan suka sun fito ganin yanda ta shigo ba takalmi ba mayafi ga gashin kanta ya zubu duk ya rufe mata fuska suna fitowa ƙofar gidan sai ga mutane a kofar ganin ko lafiya kasancewar kowa yana Ummah baruwan ta ga tarbiyya bazata wucce a hanya bata gaishe da mutum ba a haukace suka fara gudu basu tsaya a ko'ina ba sai tashar domin baren garin Kano Banda hakki da jiniya ba'a bunda yake tashi sai yanzu suka samu nitsuwa suka nemo ruwa kusa da masallacin nan tasha sosai har cikin ta yayi ƙara Munira ce ta dafa ta " Umma ke kwantar da hankali ke ba komai in Sha Allah ko Bansan me ya faru dake ba nasan kinga jinini tun muna yara munsan kina tsoron jini bamu san dalili ba Amman yanzu ina muka dosa ina zamuje dare yayi ".. Dafa kafadaar ta taye" Munira dole naji ta tsoron jini rayuwata ta zama kalar jini tun lokacin danasan wacce ce ni jini masifa ne a garine jini masifa ne a guna bala'e ne sosai", nan ta fashe da kuka sosai ta rungume ta nan bachi ya kwashe su asuba ta gari a bakin masallaci ........ Chapter 16 Kwadayin Zuciya “Tun da kike son zaman hankali, da zaman lafiya to ki zauna a ɗakin baƙi wannan gidan ba naki bane, bana gidan uwar ke Umma bane ba kuma na uban ke ba wanda ma baki san sa ba shegiyar yarinya kawai ".... Ya fita ya barta a inda ya gama mata dukan tafiya sanan ya sadu da ita bisa dole dole ... Ta kwana cikin ruwan hawaye da sanyin dare. Abinci kuwa? Idan bata nemi kanta ba, sai ya bata tsaki ya ce “Ki kai kanki gurin abinci, ko sai na kira ki na ciyar da ke da kululu?” Ameerah ta fara kulle cikin zuciyarta. akwai darare da bata iya kwana ba saboda ƙunci. daga cikin duhun ɗakin baƙi , sai ta fara kiran sunan Munira da Ummah, amma kukan nata ba wanda ya saurara. Yanzu ta gane, duka na fake-faken duniya ne—kayan alatu, dakunan more rayuwa, hotunan Instagram—amma a ciki, babu farin ciki, babu mutunci. Kuma kamar da gaske, Farooq ya fara shirin ficewa daga rayuwarta. yana kawo ƴan mata daban daban Yau da gobe, ya daina kwana a gida. Ameerah kuwa, sai take jin kamar rayuwarta na cin tuwo a ƙasa, abubuwan dake sun juya baya ba komai sai tsananin ƙiyayya dake wanzuwa a cikin zuciya kamar ba Farooq da Ameerah ba soyayyar su da sha'awar da yake nuna mata duk ya zama babu yanzu a hankali damuwa yasa ya fara shaye shaye yabi sahun abokansa ga Mubarak lalacewa sa yakai an rufe sa a ɗaki sakamakon taɓin hankali yasha ƙwayar da yafi ƙarfin brain nasa banda kira sunan Munira ba'a bunda yakiye ga talauci da yasasu a gaba abokin shi Farooq ma ya daina kula sa kai rayuwa kinan Allah ya kyauta ..... 💔RAYUWAR UMMAH💔💔RAYUWAR UMMAH💔 BY NARNAH ƘANWAR SOJA (Sayeedan Addah). 08101235739 16/4/2025 💫 ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION 💫 Ga mai bukatar group wattsp kai tsaye kiye magana da Admin ta wanan number na sama ... Chapter 17 .... GUDUN RAI Madallah! Wannan salo na ƙara tsananta darasi da kawo sauyi—yana nuna cewa koda rayuwa ta rikice, har yanzu akwai wani haske a ƙarshen duhu. --- Kano ta yi cike da hayaniya—idan aka kunna rediyo a gari, ko a mota, sai a ji: > “Wata yarinya mai suna Ummah tare da ƴar’uwarta Munira, ake nema ruwa a jallo dangane da yunkurin kisan wani babban jami’in tsaro Alhaji Isa. duk wanda ya ga su ko ya san inda suke, a tuntubi ofishin 'yan sanda mafi kusa ko ya kira wannan lamba...” Hoto ya yadu—katunan neman su a jikin duk wata bango, cikin kasuwa, tashoshi, har ofisoshin gwamnati. Gari ya zama masifa garesu. su kuwa, rayuwa ta canza. kwana a waje, yunwa, zufa, tsoro, da rashin kwanciyar hankali ya zame musu abokai. Wurin da suka kwana a jiya—gidan bene ne da bai kammalu ba. duhu ne, cizo da sauro, ga rana da baƙin ciki. Ummah na kokarin ƙarfafa Munira, ita kanta ƙarfinta na ƙarewa. Sannu a hankali, suka koyi yadda ake tafiya da dare, su ɓuya da safe. wani lokaci sai su ɗauki ganyayyaki ko kayan shara su yi kamar mahaukata, domin kada a gane su. A wannan yanayin suka bar garin Kano da zama har suka iso cikin garin Kaduna a galabaice duk da sun samu taimakon abun hawa cikin tsakiyar dare ne ba kowa a kan titin sai wasu sirarran motoci dake zirga-zirga Ummah ce kwance akan hanyar traffic lights akan ƙafar Munira sai kakkarwa takiye sakamakon rashin lafiya ga yunwa ga baƙin cikin rayuwar ita kanta Munira fama takiye banbanci Ummah ta kamu da tsananin cewo ne wanda yasa tafara fita hayyacinta Duk kirar duniya Munira na mata Amman ina Ummah kam bata cikin hayyacinta chan numfashin ta ya ɗauke gaba daya wani razannanen ihu Munira ta buga wanda har motocin dake jire suka tsaya chakk sukaja birke Siririn glass nashi ya sauke "what happened u know Kaduna to Abuja akwai kidnappers ga dare yayi me yasa kuka tsaya" k bai ƙarasa ba ya hango Munira da gudu tana buga glass na motar" Yallaɓai ko taimaka min Mama na zata mutu don Allah ku taimaka min banda kowa sai ita yallaɓai sai roqon su takiye da daure yace driver taka mota mubar nan is part of planing a take ya tada motar duk suka bar gurin tana ihu tana kururuwa chakkk suka dawo baya baya da saure ya fito yaga matar dake kwance a tashe ga kumfa a bakinta security sa ne suka taimaka aka sata a ɗayar motar nan Munira ma ta shiga s Motar sa ya kuma basu tsaya a ko'ina ba Sai Khadma hospital Abuja Cikin gaggawa aka kawo gadon mara sa lafiya emercengy room aka nufa da ita wanda Munira sai kuma takiye tana korar sunan ta ganin an shigar da ita ne ta juya da baya baya ta zube rufff "Innallilahi waina illaihin rajiuon" a take ita ma akaye kanta domin bata agajin gaggawa Cikin nitsuwa ya wanke hannu sa sai yanzu hankali sa ya kwanta ganin ƙwararun doctor's guda biyu akanta wanda tun yana hanya ya kira doctor Nazif da ya shigo asibiti kasancewar doctor Khalid ne a kan duty .. Mu haɗu a gaba domin jin ya rayuwar Ummah Shin akwai rai ko kuma zata kuma ga Ubangiji ta Ya rayuwar Munira zata kasance idan babu Ummah Waye ne wanan mutumin da ya tabbatar ya taimaka wa Munira. Wacece Ummah? Menene dangantaka dake tsakanin Ummah da Munira da Ameerah?💔RAYUWAR UMMAH💔 BY NARNAH ƘANWAR SOJA (Sayeedan Addah). 08101235739 16/4/2025 💫 ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION 💫 Chapter 18... GUDUN TSIRA Wannan chapter ɗin ya ɗauki siffar sakamakon kwaɗayi da satar rayuwa > “Tun da kike son zaman hankali da zaman lafiya, to ki zauna a ɗakin baƙi. Wannan gidan ba naki bane, bana gidan uwar ki Umma ba, ba kuma na uban ki ba—wanda ma baki san sa ba. Shegiyar yarinya kawai.” Wannan kalmomi sun bugu da karfi a kunnen Ameerah fiye da dukkan dukan da ya rika yi mata. Amma yau... ya zarce. ya sadu da ita cikin karfi da ƙarfi, ba tare da izini ba. Da kyar ta iya tashi daga gadon inda ya bar ta kamar buhun kaya, jikinta ciwo, zuciyarta cike da ɓarna. > “Ya isa haka… ya isa… amma ina zan fara? Ina zan tsira?” ina zanje ?!!!.. Waiyoo Ummah na tuba Ummah ke taimakamin Ummah kizo ga ƴarki na neman taimakon ke " Ruwan hawaye ya haɗe da zufa. a ɗakin baƙi, sanyi da ƙunci sun mamaye ta. Wani lokacin ta rika jin kamar ma Allah ya manta da ita. Idan ta nemi abinci, sai tsaki ya biyo baya: > “Ki kai kanki gurin abinci, ko sai na kira ki na ciyar da ke da kululu?” Yanzu ta fara gane gaskiyar rayuwa. dukan kayan alatu da soyayyar bogi da take bugawa a Instagram—duk ƙarya ne. gaskiyar rayuwa tana cikin girmamawa, cikar mutum, da daraja—not kayan zinariya, a kowanne dare, tana kira: > “Ummah… Munira… Allah… ku taimake ni" Farooq kuwa, yana kara zurfafa cikin mugunta. Shaye-shaye sun zama jinin sa, zina ta zama saba. Ya daina kwana gida gaba ɗaya. Yana kai ƙawayen sa gidansu, yana sheƙa rayuwa a kan cin mutuncin Ameerah. Idan ya dawo, to duka da zagin da cin zarafi kawai ke jiranta. Mubarak kuwa—wanda Ameerah ta saba gani a matsayin “sabon zamani”—ya faɗa cikin wani hali. Shaye-shaye sun kama kwakwalwarsa gaba ɗaya, har aka rufe shi a ɗaki saboda yana haɗa magungunan da ke zautar da shi. *****Daren Fita***** Duk tsanani yana tare da sauki dukkan bawan da ya tuba ya nema taimakon Allah lallai Ubangiji zai gafarta masa kuma ya taimaka masa don shi Ubangiji Mai rahama ne mai jin ƙai ... Wata rana, bayan wata rana mai tsananin dare, Ameerah ta kai ƙarshe. jikinta a fashe, fuskarta a kumbure. ta san idan ta zauna, ba zata fito da rai ba. Sai ta soma ƙoƙarin fita. ɗakin baƙi yana da taga mai tsohon labule. a daren nan, sai ta share jini a bakin ta, ta ɗaure gwiwa. taga ya zama ƙofa gareta. tana hawa kujerar karfe, ta soka hannunta ta cire tulle. tana shirin fitowa kenan sai kukan ƙafa ya sa ta dakata—amma ta danne tsoron ta. Ta fito da ƙyar—sannan ta ratsa bayan gidaje, ta bi har ƙasan titi. bata duba baya ba, bata yi tsayawa ba. da ƙafa, cikin haɗari da duhu, Ameerah ta kama hanyar tasha safiya nayi ta shiga motar Yola domin zuwa gun Ummah da Munira ta Yola. A cikin zuciyarta tana kuka: > “Allah! na gane! na gane rayuwa bata gaɗa ba ce... Ina nadama.” Kai tsaye ta tsaya bakin ƙofar ta jinkiri shigowa tana tuna yanda Ummah da Munira zasu amince da ita maganar Ummah ce ta tuna na ƙarshe da sunaye share hawayenta yaye yau shekara guda rabuwa na da ƴan uwan na nazama butulu maciya amana na kasa banbanci tsakanin soyayyar miji da soyayyar Uwa kaico kaina ne Ameerah.. " Malama daga ina " a hankali ta kai idon ta sama nan taga Mallam Shehu ne mai gidan sam bai gani ta ba duk rauni a fuskar ta ga mugun rama da ya wanzu a jikin ta a hankali tace " Mallam Ameerah ce ɗiyar Ummah ". Innallilahi waina illaihin rajiuon abinda ya faɗa kinan yana korar matan gidan da Mama duk fitowa sukaye sai kirata sukiye banda kuka ba'a bunda takiye tana tambaya Ummah da Munira sai dai ba wanda ya bata amsar har bayan kwana biyu raye sauki sosai sannan Mama ta ajiye ta a ɗaki ta fara da cewa ga wanan leader naki ne Ranar da kikabar gidan nan washe gari ta sanar da cewa zata tafe Kano a gayyamki amman itama batasan inda zata rayu ba Kallon abubuwan ciki yaye nan ta sake fashewa da kuka mai ɗacin gaske sabuwar nadama ya lullubeta Mama wacce ce Ummah don Allah kiban labarin ta " Zan baki labarin komai Ameerah domin har abada Ummah bazata gayyamu ku komai ba ya kamata DUHU CIKIN HASKE ya bayyana a wannan lokacin. Gyara zama taye nan Mama ta fara da cewa " Sunan ta Ummul Khadijah tana da shekara bakwai ta rabu da iyayye ta badon tana so ko suna so ba a'a sai dai don Ubangiji ya sa ta zama uwa a shekarar ta na goma Ta samu rauni sosai wani mutum ya tsinci ta a bakin rafin nan ya kyauta wani ƙauyen kusa dashi kusa da matar sa tana da shekaru goma ta fita tallar Mangoro nan ta biyo ta daji anan ta haɗu da wata mana tana naƙudar haihuwa duk da cewa batasan komai ba Amman tasan da cewa tana neman taimako ga nisa tsakanin gun da ƙauye nan matar ta nema Ummah da taimakon ta da ikon Allah ta haife yara mata kyakkyawar sanan matar tace mata ta batasu kyauta ita mutuwa zataye tana wasiyya tana cewa ke gudu jihar garin nan don Allah zasu kashe ne su kashe min yara don Allah ke rige su tamkar Uwa ke ƙauna ce su tamkar su jinin ki ne ga wannan zinari ne mai yawa ke raba muku ke basu na baki amanar yara na ke tausaya musu ke musu adalci rayuwar su tana cikin hatsari ke gudu zasu kamaki ".. "Wannan shine karshen maganar mahaifiyar ku Ummah ya samu asali ne saboda ku kasa mata maimakon Ummul kukace mata Ummah", Chapter 19.. Ƙundin Tarihi Ameerah ta zauna a cikin ɗakin ƙananan, tana taƙawa a hankali, tana jin ƙarar hawayen da suka kasance cikin zuciyarta. Mama ta tsaya a gaban ta, tana kallon ta da idanuwanta cike da tausayi. "Ameerah," ta fara da muryar da ba ta cika ba, "na san cewa yanzu kana cikin wani yanayi na nadama, amma duk wannan yana faruwa saboda kowane ɗayanmu yana da matsaloli. Ummah tana da labarinta na wahala da kuka, amma wannan yana daga cikin shahararrun labarai na waɗanda suke zaune cikin cikin duniya na son zuciya da ƙoƙari." ---Mama ta ci gaba da labarin, "Ummul Khadijah. Wannan suna ya zo daga wani tsattsauran yanayi na rayuwa. A shekara ta bakwai, ta rabu da iyayenta saboda wata babbar ƙalubale da ta fuskanta, wadda ba ta dace da ƙarancin shekaru ba. Amma duk da haka, ta samu kwarin gwiwa daga wajen wata matar da ta haɗu da ita a lokacin da take kan hanya mai wuya." Ta ci gaba, "A lokacin tana kan tafiya daga ƙauye guda zuwa wani, ta haɗu da wata mata mai suna Amina. Ta kasance mai ƙarfin zuciya, kuma tana da iyali mai yawa. Wannan matar tana ba Ummah damar jin daɗin rayuwa mai kyau, har ta kawo ta a matsayin mai kula da yara mata daga wasu matsalolin da aka same su a cikin garin." Ameerah ta kalli Mama da tambayar idan wannan yana da alaƙa da yadda Ummah ta zama uwa ga Munira da ita. "To, akwai wani abu da ba ni sanin, ko? Na fahimci cewa daga yanzu akwai wani tarihi na taɓarɓarewa cikin rayuwarmu." Mama ta gyara zama sannan ta fadi, "Akwai wani abu da ke cikinsu, Ameerah. Bayan wasu shekaru, lokacin da duniya ta ba ta wahala fiye da yadda take tunani, ta yanke shawarar neman taimako daga Allah. Ummah ta sauka daga cikin wannan ɗakin mai wahala, sannan ta zama uwa ga dukan yaran da aka sami rauni ko kuma wanda aka rasa." Ta sosa gashinta, tana mai ci gaba, "Duk wannan yana nuni ga cewa rayuwa ba ta sauƙi. Amma kodayake, Allah yana bayar da hanya ga waɗanda suka nemi hakan." Ameerah ta tsaya a cikin wani yanayi na sha'awa da rikice-rikice, tana tunanin labarin Mama. Tana son yin tunani sosai game da matakan da take fuskanta a cikin wannan zamanin, amma tana ganin wannan ba shi ne mafi muhimmanci ba. Zuciyarta cike da tambayoyi masu yawa game da rayuwar Ummah da irin wahalar da ta sha. "To, menene ya sa, Mama? Menene ya sa Ummah ta zama wannan uwa ga kowane yaro?" Ameerah ta tambayi Mama. Mama ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta amsa, "Ameerah, a wannan duniyar tana nuni da yadda iyaye ke ɗaukar nauyin tarbiyyar yara. A matsayin uwa, Ummah ta zamo shugaba ga waɗannan yaran saboda tana da ƙwarin gwiwa da kuma kyakkyawar fata. Wannan yana tabbatar da yadda rayuwar mutum zata iya zama mai kyau da kyan hali da al'amura masu kyau." Ameerah ta ɗan kalli Mama, tana jin cike da abubuwan da ta koya, yana shiga cikin zuciyarta da kuma tunanin yadda rayuwarta ta kasance a wannan lokaci. Tana jin kamar wani nauyi yana ratsa zuciyarta. Duk da haka, ta kuma san cewa akwai hanyoyi da dama da za ta bi domin ta zama mai ƙarfi da kyau. Duk da cewa ta yi kuskure a baya, tana ganin akwai damar farawa daga sabon tushe. "Zan nemi su, Mama," Ameerah ta furta da ƙarfi. "Zan tafi Kano, na tafi neman Ummah da Munira. Zan ba su sanar da ni komai da ta shafi iyalina." Mama ta kalli ta da tausayi, tana kallon yadda Ameerah ta fara shirin tashi daga wannan halin, tana ɗaukar sabuwar hanya a rayuwarta. "Ki tafi da lafiya, Ameerah," Mama ta ce, "amma kafin ki tafi, ki tuna cewa zaki haɗu da wata hanya mai kyau don tsira. Cikin haske." --- Ameerah ta duba cikin zuciyarta da kammala nadamarta, sannan ta tashi da kafafunta cike da ƙauna da fata, ta shige cikin duhun dare, tana tunkarar sabon mataki na rayuwarta..... A sauka lafiya Ameerah Kano tana maraba dake .. 💔RAYUWAR UMMAH💔 BY NARNAH ƘANWAR SOJA (Sayeedan Addah). 08101235739 16/4/2025 💫 ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION 💫 Chapter 20 KOMAI LOKACI NE Wata ƙamshi mai laushi da sanyi ne ya dinga cika ɗakin. Wani ɗaki ne mai launin farin da blue , da fitilu masu laushi. gadon da Ummah ke kwance a kai yana cikin ɗakin asibiti na musamman, wanda ba a yarda da hayaniya ko shiga ba tare da izini ba. Kyamarorin tsaro na labe a kowanne kusurwa suna kallon komai. Doctors suna shige da fice cikin nutsuwa, kowa yana aiki da kwarewa. Amma ita Ummah… ba ta cikin hayyaci. Cikin bacci mai nauyi take, ba tare da sanin me ke gudana ba. Numfashinta yana fita da ƙyar, zuciyarta na bugawa da jinkiri, kamar zuciyar da ke ta fama da nauyin rayuwa. Munira kuwa, tana zaune kusa da gado, fuskar ta kumbura da kuka, hannayenta sanye da rigar sallah ta yara, sai ta na ɗaukar alwala tana jan addu’a, tana roƙon Ubangiji: "Ya Allah, idan akwai rai, ka rayar da ita. Idan kuwa ka fi so, ka karɓi rayuwarta cikin rahamarka..." --- A gefe guda kuma, a wani ofishin ginin asibitin, wani matashi ne tsaye a gaban tagar gilashi yana kallon fitilun dare da hasken titi. Wani kama da hoton da ba a saba gani ba. Kyakkyawa ne—fuskarsa siririya, dogon h 08101235739 💔RAYUWAR UMMAH💔 BY NARNAH ƘANWAR SOJA (Sayeedan Addah). 08101235739 16/4/2025 💫 ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION 💫 Chapter 20 KOMAI LOKACI NE Wata ƙamshi mai laushi da sanyi ne ya dinga cika ɗakin. Wani ɗaki ne mai launin farin da blue , da fitilu masu laushi. gadon da Ummah ke kwance a kai yana cikin ɗakin asibiti na musamman, wanda ba a yarda da hayaniya ko shiga ba tare da izini ba. Kyamarorin tsaro na labe a kowanne kusurwa suna kallon komai. Doctors suna shige da fice cikin nutsuwa, kowa yana aiki da kwarewa. Amma ita Ummah… ba ta cikin hayyaci. Cikin bacci mai nauyi take, ba tare da sanin me ke gudana ba. Numfashinta yana fita da ƙyar, zuciyarta na bugawa da jinkiri, kamar zuciyar da ke ta fama da nauyin rayuwa. Munira kuwa, tana zaune kusa da gado, fuskar ta kumbura da kuka, hannayenta sanye da rigar sallah ta yara, sai ta na ɗaukar alwala tana jan addu’a, tana roƙon Ubangiji: "Ya Allah, idan akwai rai, ka rayar da ita. Idan kuwa ka fi so, ka karɓi rayuwarta cikin rahamarka..." --- A gefe guda kuma, a wani ofishin ginin asibitin, wani matashi ne tsaye a gaban tagar gilashi yana kallon fitilun dare da hasken titi. Wani kama da hoton da ba a saba gani ba. Kyakkyawa ne—fuskarsa siririya, dogon hanci mai kyau, idanu masu zurfi kamar ruwan tabo, dogon gemu da aka gyara da kyau, fuskar sa cike da nutsuwa da kamewa. Shi ne Nashrudeen Khalid Ummar, ɗan babban attajiri a Najeriya, kuma wani hamshaƙin mai gida a fannin gine-gine da asibitoci. A dalilin ƙanin baban sa , aka gina asibitin nan da ake kira Ummukhadma Specialist Hospital — Shi ba wai kawai attajiri bane. Nashrudeen mutum ne mai hankali, mai tsananin tausayi, marar ƙyashi ko nuna isa. Yana da tsawo, kyakkyawan fata mai tsantsar haske da ƙamshi, kullum cikin suits masu tsada na turai. Wannan dare yana sanye da suit ɗin navy blue, farar riga da necktie mai kauri. Agogon Rolex ya cika wuyansa, amma duk wannan bai fi nutsuwarsa da kamunkai ɗaukar hankali ba. Tunda ya ga halin da Ummah ke ciki a titi, ya san cewa ba za a bar wannan matar ta bace ba. Sai ya ce da kansa: “Bari na kula da ita. Zata warke, insha Allah.” Har yanzu bai san cewar ita Ummah ɗin jininsa ba ce ba. Bai san cewar ita ce ‘yar wadda mahaifinsa ya rasa shekaru da suka wuce—wanda yanzu ke shan nadama yana rayuwa a kasashen waje ba tare da sanin ta rayu ba. A shekara sai daya yake zuwa Nigeria domin tunawa da haihuwar ɗiyar sa --- Yanzu dai lokaci ya tafi. Likitoci sun fito daga ɗakin. Nashrudeen ya mike da sauri ya karasa. “Doctor Nazif... any update?” Doctor Nazif ya jinjina kai, yana murmushi. “Masha Allah, tana dawowa hankali, amma tana buƙatar hutu. Zuciyarta da jikin ta sha wahala sosai. sai a saka mai kula da lafiyar kwakwalwa tazo dasu ta nutsar da ita, tunda alamun tsoro da trauma sun yi yawa.” Nashrudeen ya jinjina. “Komai ku buƙata, kuyi. ku ce da HR su tanadar musu ɗaki guda biyu na musamman, ita da yarinyar nan Munira. Na karɓi alhakin rayuwar su gaba ɗaya.” --- Washegari, Ummah ta fara motsi. A hankali, ta buɗe idonta kamar sabuwar rana ta fara haske a cikin duhu. sai ta sauke ajiyar zuciya. Ba zato, ta hango fuskar Nashrudeen da gilashin idanunsa, yana tsaye a gefe, yana murmushi cikin kulawa. “Ki yi ƙoƙarin hutawa, ba wani hatsari a nan. kina cikin aminci,” ya faɗa a sanyi. Kallon fuskar sa kawai ya ishe ta gane cewa akwai wani sabon salo na rayuwa da zai iya zuwa. Duk da bata san shi ba, zuciyarta ta karɓe shi kamar ɗan wani abu mai mahimmanci... --- Chapter 21 SIRRIN ZUCIYA Inda rayuwar Ummah ke dawowa sannu a hankali, kuma Nashrudeen ya fara gano gaskiyar dangantakar su: --- Kwana biyu kenan da Ummah ta dawo daga baccin da ya kusa zama na har abada. duk da jikin ta ya soma farfaɗowa, har yanzu cikin rudu take. kowanne lokaci da ta buɗe ido, sai ta yi ta kallon ɗakin, kamar tana tambayar kanta: Ina nake? waɗanne ne waɗannan mutane masu kyautatawa fiye da iyaye? Munira ta kasance kusa da ita, kullum cikin tsoron kada Ummah ta sake fita hayyacinta. Sai dai yanzu ta soma murmushi, har ta fara cin abinci kadan-kadan. Wata rana da safe, Nashrudeen ya shigo ɗakin yana sanye da shadda mai launin royal blue, hula a kai, da kamshi mai laushi. fuskar sa cike da kulawa, sai ya zauna kusa da gado, yana kallon ta da nutsuwa. "Ummul Khadijah," ya furta da sautin tausayi, "kina jin sauƙi?" Ta lumshe ido sannan ta gyara zama kadan. da mamaki yanda yasan wanan sunan nata "Ina jin sauƙi... amma har yanzu ba na gane komai sosai..." "Ki kwantar da hankali. wannan wurin lafiya ne. kuma ki sani, ba zan bar ku ba." Kallon da ta masa ya cika da tambaya da kuma godiya. sai ta ce da ƙasa-ƙasa, "Na gode... kai wanene a gaskiya?" Yayi shiru na lokaci, yana nazarin amsar da zai bayar. bai san dalilin da yasa zuciyarsa ke ja da ita ba, kamar akwai wani sirri da Allah Ya ɓoye har zuwa lokacin da ya dace. --- Watarana ya shiga binciken tsofaffin hotunan family su nan ya tabbatar da abinda idon sa ya Allah da sauri ya ɗauke waya ya kira Alhaji Umar da ya kasance a Nigeria chan ya kashe wayar ya shiga mota ya nufi asibiti ya koma ɗakin asibiti da zuciya mai nauyi. Yana shiga, sai ya tsaya yana kallonta. Kamar yadda aka ce "duk macen da zaka so da gaskiya, akwai alaƙa tsakaninku kafin duniya." ynzu ya fara fahimta: wannan yarinyar jininsa ce… ‘yar yayar mahaifinsa ce. Ma’ana, ‘yar Baffan sa cousin ɗinsa. Hawaye suka cika idonsa. Sai ya zauna, ya riƙe hannunta, ya ce a hankali: "Ummah... ba kawai ina so in taimake ki bane. Na fi haka kusanci da ke. Mun rabu da juna shekaru, amma yanzu Allah Ya haɗa mu." "Ni... jinina ne ki, amma ba haka kawai ba. In Allah Ya yarda, zan zama farin cikin rayuwarki har abada." Ummah ta tsaya kallon sa, zuciyarta na tafarfasa da sabbin abubuwa. Kamar mafarki, amma ba mafarki bane. Rayuwa ke sauyawa, kuma wata kyakkyawar rana tana haskowa. --- Munira na zaune kusa da Ummah a ɗakin asibiti lokacin da Nashrudeen ya dawo da wata tsohuwar jakar leather mai ɗauke da takardu da hotuna. Cikin nutsuwa da tausayi ya kalle su sannan ya ce: "Zan kai ku gida gobe... akwai wani abu mai muhimmanci da nake so ku sani." Washegari, sun tafi wani gida mai kyau a cikin Maitama, Abuja. Gidan ya sha kyau, ganyaye da furanni a ko’ina, iska mai daɗi na yawo. Kafin su sauka daga mota, Nashrudeen ya tsaya ya ce: "Wannan gida… shine gidan mahaifiyarki, Ummah. Kuma mahaifinki yana ciki." Ummah ta kalle shi da girgiza kai. “Ni? Gidan mahaifiyata?” Ta kama ƙirjinta, zuciyarta na bugawa kamar za ta fasa ƙirji. Yana riƙe da hannunta har suka shiga falon. Cikin falon, wata mata ce zaune, ta tsufa kadan, amma kyakkyawar kamanni da nutsuwa a fuskarta. tana cikin karanta Al-Qur'ani. da suka shigo, ta kalle su, sannan ta kafe ido akan Ummah. Qur’anin ta ajiye a hankali “Ya Allah... Khadeeja?!” ta furta da ƙara, hawaye na bin fuskarta. Ummah ta tsaya cak, zuciyarta na wani irin bugawa. ganin matar nan… kamar ta gane fuskar. Tana kama da fuskar da take gani cikin mafarki, fuskar da take fuskantar cikin dare-dare a mafarkinta. “Mommy …” ta furta da murya mai rauni. Hajiya Zarah, ta tashi da gudu ta rungume ta cikin kuka. "Ke ce! Ke ce fa 'yata! Na rasa ke shekaru da suka wuce... muna tunanin kin mutu, mun yi juyayi har aka yi jana'iza ba tare da gawarki ba!" Sai wani dattijo mai haiba ya fito daga ɗaki, yana kallon su da mamaki. ya tsaya, ya dube ta sosai, sannan a hankali ya furta: "Khadeeja… rayuwa ce ta dawo gare mu..." Sannu a hankali, suka zauna, Nashrudeen ya basu lokaci. Hajiya Zarah ta soma basu labarin abin da ya faru: > “Shekara goma sha biyar da suka wuce, muna tafiya daga Yola zuwa Kaduna lokacin da wani hatsari ya faru. Motar mu ta fashe, mun farka a asibiti. ke na rasa ke—duk da bincike, ko’ina muka kai labari, ba a gan ki ba. muka yanke shawarar cewa kin mutu. amma wallahi, tun daga ranar, rayuwata ta tsaya. Kullum ina mafarkin ki.” Idanun Ummah cike da hawaye suka ce, “Ni ma ban taɓa mantawa da mafarki na fuskar wata mata mai launin fata irin tawa ba...” Dattijon nan ya riƙe hannunta ya ce, “Ni ne mahaifinki, Dr. Umar wannan asibitin da aka kawo ki—Ummukhadma Hospital—sunanki na yi amfani da shi wajen ginawa. sunan ki—Ummul Khadeeja, amaryar zuciyata.” Ta fashe da kuka mai raɗa, Munira ma da Nashrudeen suka kalli juna cikin karyewar zuciya. A wannan rana, aka tabbatar da soyayya ta gaske: soyayyar iyaye, soyayyar zumunci, soyayyar Allah da ya ƙaddara haɗuwa bayan rabuwar shekaru. Sannu a hankali rayuwa ta soma haske ga Ummah. Munira ta zauna da su cikin jin daɗin sake haɗuwa da mutanen kirki. Ummah kuwa, bayan ta warke gaba ɗaya, sai ta cigaba da ganin Nashrudeen da zuciya mai kyau. Duk safiya yana zuwa, yana ɗauke da furanni ko littafi, yana dariya, yana jan hankali da nutsuwa. Yana cikin masu kuɗi, yana da kamfani guda biyu, yana zaune a Gwarimpa. Amma ba dukiya ce ta fara burge Ummah ba—halayen sa, ladabinsa, da yadda yake girmama iyaye da ilimi ne suka birgeta. 💔RAYUWAR UMMAH💔 BY NARNAH ƘANWAR SOJA (Sayeedan Addah). 08101235739 16/4/2025 💫 ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION 💫 . CHAPTER 22 LABARI CIKIN ZUCIYA Wata biyu kenan da Ameerah ta iso Kano cikin ɗoki da fata tana bin titi da titi, layi da unguwa, tana tambaya—amma duk inda ta shiga, babu wanda ya san su Munira ko Ummah. gajiya da tsadar rayuwa ya fara rinjayar ta. ta daina kwana lafiya, ta daina ci da ƙoshi. sai kawai ta kwanta tana kiran Allah a zuciya. Wata rana sai ƙawarta Rukayya ta ce, "Ameerah, akwai wata dilalliya tana nemo aiki. Akwai gidajen masu kuɗi a Abuja da ke bukatar masu aiki masu gaskiya. Me kike tunani?" Tana jin sunan Abuja, jikinta yayi sanyi. kamar zuciyarta na ce mata akwai wani abu a can. > "Nima na gaji da jiran banza," Ameerah ta ce. "Kaina zan tafi... komai na Allah ne." Aka kai ta cikin wata motar haya, aka kwasheta da wasu 'yan mata zuwa Abuja. Akwai damuwa a zuciyarta amma ba ta da zabi. Bayan kwana biyu da sauka a unguwar Maitama, aka tura ta cikin katafaren gida mai tsari da kyau. gidan kamar aljanna. daga ƙofar shiga ta san cewa ba talakawa ke zaune a nan ba. Ta shiga da tunani da buguwar zuciya, tana jiran mai gidan. Bata sani ba cewa rayuwarta na dab da canzawa. Yana cikin sharaɗin aikin, dole sai ta gaishe da yarinyar gidan da matar gidan kafin ta fara aiki. Ameerah ta nufi falo, tana ganin wata kyakkyawar budurwa tana kallo, sai wani ƙwallo ya zubo da sauri daga idonta. “Munira!!!” Munira ta waiwayo da sauri, ta tsaya cak. Idanuwanta suka buɗe. Ta ce, > “Ameerah?! Subhanallah Ameerah!!” Suka ruga suka rungume juna. Kukan su ya cika falon. tuni Ummah ta fito daga ɗakin sama tana jin motsi. Ganin su tare yasa jikinta yayi sanyi. > “Ummah... na tuba... na dawo... Wallahi na tuba! Ku gafarce ni!” Ta faɗi haka tana rushewa da kuka. Ummah ta matso a hankali, idonta cike da hawaye. Ta ce, > “Ameerah... na haɓɓaka, na raina ku... ban manta da ku ba.”sai suka rungume juna cikin hawaye da rawar murya Ameerah ta zauna a ƙasa, ta zayyano irin wahalar da ta sha. yanda Farooq ya ci zarafinta. yanda ta guje shi da jini a jikinta. yanda ta nemi su Kano har tsawon wata biyu. yanda ta shiga motar aiki domin nema mafita, ba tare da ta san Allah zai kai ta hannun 'yar uwarta ba. Munira da Ummah sun zauna suna kukan tausayinta. bayan dogon lokacin shiru, Ummah ta ce: > “Tuba ki kayi, Ameerah. Kuma Allah ya karɓa. Kuma mu... mun yafe. Domin ke ƴar mu ce. Ina jin ki tamkar jinin jikina.” Toh bismillah! Ga Epilogue / Chapter Na Ƙarshe na Hausa novel ɗinki mai taken Rayuwar Ameerah, Ummah da Munira: --- Chapter Ƙarshe 23 ƘARSHE MAI ƘARFI BAYAN WANI LOKACI Ranar da Ummah ta d'aura auren ta da Nushardaeen Khalid, ƙasar Abuja ta sha kwalliya. Gidan Ummul khadijah ya cika da farin ciki da zumudi. duk wanda ya san tarihin rayuwar Ummah yasan cewa wannan ranar ta fi kowacce muhimmanci a rayuwar ta. Munira ta zuba idanu cikin hawaye masu cike da murna. tana kallon yayar ta da ta raine ta kamar uwa, tana tafiya cikin farin sallah, kamar wata amarya daga aljanna. A gefe, mahaifinta Dr. Khalid yana zaune da farin ciki da kwanciyar hankali. a wannan rana ne ya ce a gaban duniya cewa: > “Na rasa ƴata shekaru goma sha uku, yau Allah ya dawo min da ita. kuma a ranar da take aure, ni ne nake daurin aurenta. sanan bata da wani laife da ake zargin ta dashi domin hukuma ta tabbatar da laifin Alhaji Isa na neman kitta mata haddi kuma hukumar ƴan sanda zata hukunta tashi bisa mataki mai kyau —na tabbatar da hakan a bainar jama’a.” An wanke Ummah a kafafen yaɗa labarai, kafafen sada zumunta, da gidan talabijin na ƙasa. An samu halartar manyan manyan sarakuna da attajirai gun ɗauren auren Ummah wanda aka ye ƙayattachin walima Umma ta samu kyaututtuka da dama Bayan an fito da amarya gaban jama'a da ƴan mata kyakkyawar a hannun dama da hagu sai wani kyau suke fitar wa na musamman Ameera wacce ta samu takardar saki daga Farooq don anyi da gaske kafin ya bata sai da akaje gaban manyan alƙalai Sai murmushi takiye ko zama samu wani bazawarin hhhhhhh lolz bance komai ba Sarkin Bauchi ya ƙara kunnu kai bai damu da Camera ko sarautar sa ba a lokacin da ya hango Ameerah da Munira, zuciyarsa ta girgiza. ya tuna da tsohuwar matarsa da aka yi garkuwa da ita da cikin ciki. Bayan dogon bincike da shaidar DNA, sai aka tabbatar da cewa lallai Munira da Ameerah ’ya’yansa ne na jini. Nan ya miƙa zinariya, kuɗi, da tarin kyaututtuka ga Ummah da Khalifa. Ya ce: > “Wannan yarinya Ummulkhadijah... ta rayu da halin da ko sarki bazai jurewa ba. amma ta tsira da addini, da mutunci, da imani. ni a matsayina na sarki, zan tallafa mata da duk abinda take bukata. wannan ita ce jaruma.” Nan Ummah ta fashe da kuka ta ƙara rungumar su " ashe duk muna da iyayye a wannan duniya muna da gata amman muka jure ruwan sama da yunwa da fargaba da tsoro lallai al Kur'ani gaskiya ne da yace mana bayan wahala akwai sauki Allah na gode ma "..... ƘARSHE MAI DADI Bayan shekara guda da auren su, Ummah da Nashrudden sun shirya tafiya kasa mai tsarki—Umrah. Sun tafi da Munira da mijinta likita, da Ameerah, wanda yanzu ta kuma karatun boko da na addini kuma tana addu'a samun miji nagari mai kirki kamar dai Munira alamar sabon rayuwa. Wani safiya mai cike da kwanciyar hankali, jirgin sama ya ɗauke su zuwa ƙasa mai tsarki. Ummah, Munira, Ameerah da Nashrudden. ga mijin Munira sai Dr Umar da Hajiya Zahrah da Sarkin Bauchi domin godiya ga Allah da ya dawo masa da zuriyar sa wanda aka ye kidnappeing maman su da tsohon ciki duk da an biya kudin fansa amman ba labarin ta .. suna cikin jirgin, hannunsu cikin juna, zuciyarsu cike da godiya. Tare da taimakon Allah mai rahama, suka tsaya gaban dakin Ka’aba, hawaye na zuba. Ummah ta ɗago hannunta tana faɗin: > “Ya Allah, na gode. Na gode da ka tseratar da ni. Na gode da ka dawo min da mutuncina. Na gode da ka hada ni da iyalina. Na gode da ka bani amana... kuma na rike ta.” Ameerah ta kifa kai cikin sujada, tana kuka kamar ruwan sama. Munira ta rungume ta, tana cewa: > “Mun sami gafara, mun sami gata, kuma Allah ya ɗaukaka rayuwar Ummah.”....... Kamar yadda ruwa ke tsarkake ƙasa, haka rayuwar su ta zama sabuwa.... Gabatarwa daga Marubuciya Narnah ƙanwar soja Rayuwar Ummah ba kawai labari ba ne, wata hanya ce ta rayuwa, cike da darussa, jarabawa da tausayi. Littafin ya ɗauki zuciya daga ƙuruciya zuwa girma, ya karantar da yadda nasara ke zuwa ta hanyar jajircewa, adalci da amana. Wannan labari yana bayyana yadda mace za ta iya tsira daga ƙalubale na rayuwa, ta tsaya da ƙafa biyu, ta zama haske ga wasu. Ummah, jarumar wannan littafi, ta fuskanci wutar rayuwa, ta sha wahala, ta rasa iyaye, ta rasa kai, amma a ƙarshe ta dawo da martabar rayuwarta. Labarinta na cike da kukan tausayi da murmushin nasara. Munira, Ameerah da sauran jaruman cikin wannan littafi sun taka muhimmiyar rawa da ke ƙara ɗaukar zuciyar mai karatu. Muna addu'ar ga Allah ya gyara mana ƙasar mu Nigeria wanda kidnappeing ya zama ruwan dare , fyade da rashin tausayi ya mamaye ta Allah ya bamu zaman lafiya Allah ya bamu ikon rigi amana Allah biya mana bukatar mu na alheri Bisslm fatan alheri An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels