An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe *NI DA GIDANA* *BY* _Zainab ilyas mazawaje_ _Best brilliant enterlligent writter_....🖋️ _Marubuciyar_ Mubarak ko mujahid? Adalilin zumunci Ni da gidana Cobara daga kogi Jarabtar ubangiji Gobara daga kogi Rashin Dangana Zarge (mugun kulli) Budurwar zuciya 'Ya'yan mijina Nadamar aurena Umma khulsum Sabanin Zato Ina bakin zaren? Tayi Dace Abdallah So halitta Kayan aro Bazata _Baa yarda a juya wannan littafiba ta kowacce irin siga ba tare da izinin marubuciyar ba_ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 *Page 1* 🗻 Labarin rayuwa ta d'auke yake da amsoshin tambayoyin wasu mataye,haka zalika d'auke yake da warwarar matsalolin wasu mataye. Kuma yana d'auke da mafita ga dubban matayen aure da suka shiga takun kumin Ina mafita ga damuwar su. Sumayyya, duk ke wad'an nan furutai ga manyan a minan'ta biyu Laila da Aliya da suka sata a gaba, suka zuba mata idanu, game da tambayoyin da suke ta yi mata a kan rayuwar'ta. Ta dubesu tayi murmushi. ”Ni ba 'yar kowa bace, ni 'yar talaka ce lis. Kuma ni ba kyakykyawa bace, amma na auri mijin da ko a mafarki, ban tab'a zaton zan aureshi ba. Na Shiga daula ta arzik'i nayi ninkaya a ciki da Sai d'ai, d'ai kun mata a duniya ke rabautar irin sa. Na mallaki kadarori da dukiya da ni kaina bazan zayyano su cikin sauk'i ba. Kuma shaida ne, da zaku labarta kowa wacece sumayya. Taja dogon numfashi ta d'ora. Duk da wannan jin dad'in duniyar da daula da sa'ar miji na kerewa sa'a da na rabauta, Ina tare da wani tabo na mikin ciwo a zuciya ta da ya kasa warke wa da a ka jarrabeni da shi, da Sai Jifa Jifa yake motsamin yayi ta d'an zugi idan na tuno jarraba ta, a rayuwa. Babu kuma Wanda yake fahimtar wannan damuwa tawa, sai Mijina da muka zama han'ta da jini.wannan ita ce mummunar kaddarata da nafi jin ciwonta fiye da kowacce. Laila ta dafa kafad'ar sumayya Sannan tace. "Sumy, yanzu nan har kina da Wata damuwa ko matsala a rayuwa da bata kau ba?. Zato na ai kin gama shan kwana." Aliya ta karb'a. "Wallahi yarda kika zama a bar Sha'awa ga mata a ko'Ina babu wanda zai yarda kina da Wata damuwa ko yaya a rayuwa sumayya. "Idan kuka fad'i haka, kun jahilci sanin ita kan'ta rayuwar. Babu yarda za'a yi a ce wai mutum burin sa a rayuwa ya cika d'ari bisa d'ari, ko bashi da matsala ko d'aya, dole ubangiji yatab'a shi, ta wani b'angaren ko a hanashi ta wani fannin. Cikakken musulmi, zai ce yayi imani, Sannan a ce wai ubangijin'sa bazai jarrabi imanin sa ba? impossible." "Gaskiya ne, dole ne Kam." A cewar Aliya. Laila ta muskuta, ta k'ara matsawa dab da Sumayya, tayi d'an duba kad'an cikin katafaren falon da samun irin sa zai wahalar a zamanin nan. "Sumayya, don Allah ki daure ki bamu labarin rayuwar nan taki domin na tabbatar a Kwai a bubuwa da yawa da mata zasu amfana da shi, domin ke d'in nasan bata wasa bace, Sai dai a d'au co's a wurin'ki a komai, tun da ga mai gida ma duk kin mallake, kullum tunanin'sa yana gareki." "Tabbas, tun da daga zaman mu a nan, ya kiraki a waya ya kai sau biyar." Inji Aliya. Sumayya tayi 'yar dariya tace. "Bazan ce ba haka ba ne a minai na, sai dai nayi k'ok'arin mai da tunanin Ku can baya, domin Kusan gwagwar mayar da sumayya tasha kafin ta samu wannan matsayin wurin Mijinta da wurin dangin'sa, har ma da ku da duk wad'an da nake burgesu da basu Sha'awa. Duk Wacce zata iya kwaikwayo na wurin juriya da Hak'uri da dangin sa da dogaro ga Allah, da iya tafiyar da miji da juriyar irin d'abi'un sa duk hutsancin'sa, to tabbas zata iya dace da irin rayuwar Sumayya ko ba duka ba. Sai dai matsalar dole idan Ina baku labarin za'a zo wurin da zan yi ta kuka, k'arshe ma na sare na kasa ci gaba. Saboda haka domin komai yazo min da sauk'i zan rubuta muku a rubuce kawai. Ta dan ja fasali, kafin tace. Na yarda Ku yad'a shi ma, ko ya zama littafi, domin na tabbatar 'yan uwa na mata zasu k'a ru da yawa ma. Ku bani Sati biyu, saboda kunsan Mijina yanzu bai fiye yin nisa ba sosai, kuma yana d'an jimawa bai yi tafiya ba ynz.,kunga kuwa Sai ya fita zan samu dama ko?. "Wallahi da gaskiyar'ki . Mu dai godiya muke sosai, muna jira ." Cike da zumud'i Laila ta fad'a.ita ma Aliya jinjina tayi mata. "Allah yaja da ran gimbiyar mata, Allah ya k'aro twin's biyu bayan su Abalkhair. " Murmushi Kawai tayi. Saboda sun jima suna yi mata nacin labarin rayuwar'ta saboda ta zamewa kowa kamar abar shaawa da kwatance. Amma fa ga Wanda ya San'ta ko ya gan'ta ko labarin'ta da ya shahara ya riski Mutum. Bayan Sati biyu kuwa Sumayya ta cika alk'awari ta basu rubutaccen labarin'ta. _______________________ _jigon al'amarin kaddara_ Had'uwa ta da Fa'iz Bukar, daga nan k'addarar ta soma. __ Ajin ya kaure da hayaniya saboda rashin malami,dama kuma al'adar 'yan a jin na mune surutun, koma da malamin, saboda sunci sunan mun gagara. Ni da nake monita na tashi na duba time table, domin naga wani malamine da mu a lokacin,naga English teachear ne, wato malamin turanci. Na nik'e na nufi taff room in da mu kaci karo da malam Abba class teacher d'in mu. Na rusuna nace. "Sir, babu malami a ajin, Sai hayaniya kuma suke sunk'i yin shiru." "Wani malami ne daku bai shigo ba?". Yace. Nace "English teachear ne sir, kuma anyi masa transfer,sabon malamin da a kace yau zai soma zuwa kuma bai zo ba." Da sauri yace. "Ai kuwa yazo. Malam Fa'iz sunan sa, yana ma staff room suna ganawa da princepal na baro su.muje na nuna miki shi, ki fad'a masa period d'in sa ta Shiga, bai Sani ba ne." Ban da shi malamai uku ne a staff room d'in biyu maza, Sai malama wasila dake aikin sa hannu a test a gefe guda. Yana gefe d'aya shi kad'ai a zaune yana duba wani text book. Dole da ka Shiga, shi zai fara d'auke maka idanu, saboda farar fatar'sa irin ta shuwa a rab. Matashin saurayi ne da duk cikin malaman babu mai k'asa da shekarun sa, sai dai sama. Ni dai Ina yin tozali da shi, na Shiga mamakin sake had'uwa ta da shi a karo na biyu a rayuwa ta, kuma zai zomin a matsayin malami. Ko da yake had'uwa ta da shi d'in ma ta farko, ba wani a bu ya Shiga tsakani na da shi ba, face wayata da na tab'a yarwa ya tsinta ya kawo min. Tsawon Wata tara Kenan. Amma a bin mamaki nunawa yayi kamar bai tab'a gane ni ba, da ya d'ago kai muka had'a idanu. Sai da ya wani ja a ji, cikin jin kai, Sannan yace da k'yar. "Kece monita"Yace. Na gyad'a kai. "Yes, sir". Har ya mik'e nayi ni kuma gaba, ya kirani yace. "O K. Jeki, gani nan zuwa.'" Ya koma yayi Zaman'sa kuma bansan dalili ba. Ban jima kuma da Shiga ba, Sai gashi ya shigo. Duk da an ga shigowar'sa ba'a saurara da hayaniya ba, kuma duk kuma da jarabar kallon da a ka bishi da shi, kamar bak'on halitta. A haka ya soma gabatar da kan'sa cikin harshen turanci. Ya dakataYace "Keep Quiet. I said keep Quiet. "Amma ba'a rage Surutu ba. Ai sai ya daka Mana Wata irin tsawa da dank'ara mana zagi, ya zarce da. "Ku wad'an ne irin jakai ne ku, a na cewa Kuyi shiru baza Ku yi ba?" Ai kuwa sai tsit ka ke ji , saboda dalilai biyu. Farko tsorata, na biyu babu wani malami da ya tab'a zagin mu, saboda ji da mu da malamai suke, koma me muka yi. Amma shi wannan daga zuwa har ya fara yi Mana lugude? Saboda Surutu Kawai ma?. Tabbas da a lamu zai fita zakka. Domin da jin kai da tsare gida ma ya shigo class d'in. Shiru yayi kuma yana ta harare harare da nufin yaga wata tayi ko uhum! yaci zarafin'ta, haka na karance shi. Babu Wacce kuwa ta kuma yin ko tari. Yayi sanyi kad'an ya soma magana cikin harshen Hausa kuma. "My name is fa'iz Bukar. Ba wasa ne ya kawo ni nan ba. Kuma bazan d'auki ko wani irin iskanci na d'aliba ba. Kuyi k'ok'arin Sani na kafin ku fad'a tarko na, shine maslaha a gareku. Bana son wasa, ko kusa cikin darasina. Bana kuma shiri da dak'ik'ai da jakai da basu San me ya kawo su makaran ta ba. Dole ne ni a iya darasina in dai na karantar. Idan yarinya bata fahimta ba, to ta tambaya,bayan wannan bata da uzuri kuma na cewa bata iya ba.Duk wacce tayi sake ta fad'o tarko na, to ta Shiga uku, ni bansan kalmar hakuri ba, ballantana tayi ceton ta. Ba wasa ne ya kawoni ba, na sake jaddadawa." Ya nuna ni da pen. "Ke monita lallai ki kula da hak'k'in aikin ki, ko kuma ki kwana a ciki. Duk mai Surutu Ina writing ki rubutamin sunan'ta. Kuma kiyi copy na time table ki kawo min anjima. "Sit down" . Yace, batare da ya kalleni ba, cikin jin isa. Na zauna. Note yayi mana muka kwafa. Yayi dogon bayani da turanci, yace duk wacce bata gane ba, tayi tambaya. Amma shiru kake ji. Iya tsiya da fad'in rai yasa wad'an da basu gane ba ma suka yi shiru. Ko a jikin'sa. Yace Kowacce taje tayi bita kafin ya dawo. Yana fita a ka rud'e da sowa. Yasha zagi, a d'abi'ar cin mutunci da ya soma da shi. Ya kuma Sha zuga da yabawa a b'angaren halitta. Ba'atab'a Samun malami mai kyau da a ji irin sa ba, bama iya cikin makaranta ba. Da ganin sa kaga half cast. Wato ruwa biyu. Yabar a bin fad'a Kam da k'orafi. Saboda baki d'ayan makarantar, babu a jin da malamai ke tarairaya kuma a ke ji da su irin mu. Bawai ga k'ok'ari ba, Sai dalilai biyu. ''ya'yan masu kud'i su suka cike fiye da rabin a jin. Sannan babu a jin da ya kai shi tsula tsula kuma kyawawan 'yan mata gagara gasa, daga kan farare zuwa bak'ake. Idan Mutum ya zagaye a jujuwan d'alibai ko'ina Mutum zai rantse tsince kyawawan 'yan mata a kayi na makarantar a ka zube a a jin mu. Shi yasa yawancin malamai suna da wad'anda suke so cikin class d'in mu, dalilin da yasa kenan saisuyi ta tsiya ba'a yin komai na hukunci. Amma duk da haka a Kwai d'alibai tsirari a cikin a jin 'ya'yan talakawa, kuma wad'an da baza'a ce musu kyawawa ba, kuma baza'a kushe ba. Wato irin mu, har dani. Ni kad'aice ban tofa komai ba, a kan sabon teachear d'in namu. Wato Fa'izu Bukar. Takun'sa ni ya burgeni sosai, saboda ta hakan na tabbatar zai yi maganin tsagerun d'alibai masu kuma nuna isar sunfi k'arfin komai. Kuma dole Zai kawo gyara da zakkarar da shagalallun d'alibai da dak'ik'ai. Saboda babu Wata alama ma da ya nuna na wata yarinya ta isheshi kallo ballantana a ce ya k'yasa da har zata samu damar kawo masa lalata. Fari ne sosai, da ganin Sama kasan cikin iyayen'sa a Kwai sirki. Bayan farin fatar sa a goge take, irin gogewar da ba'a cika samu ba cikin Hausa Fulani. A gefunan fuskar sa a Kwai k'asumba da ta d'an feso, dake nunin yana da baiwarta askewa yake. Idanuwan'sa madaidaita ne, masu launin shud'i, irin idanun nan da idan haske yayi haske yake dan ba da launin shudi. Yana da dogon hanci sosai, da madaidaiciyar hab'a da k'asumbar sa ta zagayo ta kewaye ta, tayi masa wani irin kyau da ta dace da tsari da ita kanta siffar halittar tasa. Babu a binda yafi komai yi masa kyau, irin turuwar girar sa bak'a da gashin kan'sa da suka d'ai sun isa bada shaidar irin jinsin da ya cakud'u da shi, ga Wanda yayi musu farin Sani. Wato (Shuwa). Madaidai cine a tsawo. Yana da diri irin Wanda mata suka fiso.mai cikar b'araza da gab'b'ai ,da fad'in k'irji. Bashi da rama Sam. Kuma bashi da k'iba sosai. Idanuwa bazasu tab'a k'osawa ba da kallon'sa, musamman mace. Kome take nema ga namiji, na dai surar kyau, to dole ta taka burki, idan tazo kan Fa'izu Bukar. Sai dai fa idan tana k'yamatar namiji mara sakin fuska, mai jin kai da wulak'anci, tofa baza ta iya da shi ba Sai dai hak'uri. Cinnaka ba Sani babu sabo, ko kuma mai kyawun dan maciji. Kirarin da naji d'alibai ke yi masa kenan, wasu lokatan. Amma Sai da ya d'an jima a makarantar yaci wadan nan kirarin sunayen. domin lokacin ne kowace d'aliba tasan wanene Fa'izu Bukar, domin halayen sa sun bayyana a sarari sosai. Alkalamin...... ✍️ _Zainab mazawaje_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe *NI DA GIDANA* *BY* _Zainab mazawaje_ _Best brilliant interlligent writer_.... 🖋️ Page *2* __Aharkar jajircewa da karatu, da rashin sakin fuskar jawo wasa a karatu, sosai Fa'iz ya burgeni, saboda malamai da dama wasa suke shigarwa cikin karatun,su . Amma daga baya nima sai na rink'a k'yamar wasu halayan Fa'iz Bukar. Bayan rashin sakin fuska kokad'an, a Kwai kuma iya cin zarafi ainun idan an b'a ta masa, akwai shi kuma da d'agawa da jin kai, kamar d'an sarki. Na kan had'u da shi a harabar makaran'ta, nayi niyyar gaishe shi, ko nuna sanayya, amma Sai ya wani d'auke kai ya kuma tsare gida,wato kar ma na samu kafa. Jinkai dai wurin fa'iz ya shaddade. Wasu mata suna dagawa idan sun san sun mallaki wani abu kamar kyau ko kudi ko sarauta, amma namiji yawanci bai fiye yi ba gaskiya, ballantana malam Faiz da iya abu daya nake jin zai iya jin kai, shine kyau, don ba dan wani attajiri bane da gani, ko mulki ko wani gawurtaccen ilimi da ya kai ya kawo, don da bazai zo koyarwa secondry ba, a fahimtata. Shi yasa nake jin haushin yarda yake wani dagawa, da wulakanci. Wannan dalilai yasa naja baya. Idan na ganshi a gabas, to sai nayi yamma ni. Washe gari, period d'in sa tana shiga, sai gashi ya shigo. Ya ninka jiya a kyau kam. Kayan da yasa, bayan haska ka shi da suka k'ara, sun yi masa kyau sosai. Ba kuma wasu Kaya bane na musamman ba. Kayan sanyi ne. Rigar sanyi ce mai duhu ruwan k'asa mai kwala, Sai wani gida gida a gaban rigar mai launin fari fari. Jin's d'in wandon daya sa, Shima ruwan k'asa ne, amma mai haske. Sai safar hannu, ruwan k'asa, safar k'afa ma haka. Komai dai to mach. Duk dai sanadin sanyin da a ke yi, yayi wannan shigar. Sanyin ranar yafi na kullum ma. Kayan da yasa jiya ma sun yi masa kyau, Amma na yau kam ba'a magana. ko daya ke, dole Kaya suyiwa Fa'izu kyau, ko wani iri. Amma fa ba kowa ne zai yarda ba, Sai Wanda ya ganshi. Ya tsaya gaban a ji, ya dafa tebur d'in teacher, yana kallon d'alibai d'ai d'ai cikin jin kai da isa. "Ina a ka kwana game da topic d'in da na karantar jiya, Kowacce ta fahimta?" Shiru babu Wacce tayi magana. "Wata ta tashi tayi min bayani ko in brief." Nan ma shiru. "A kwai tambaya? " Nan ma babu Wacce ta d'aga hannu. Ya gyad'a kai. "Cab'? Lallai yau jiki zai yi tsami. Kuna nufin wahalar banza nayi Kenan?" Ga rashin sanin Fa'iz, yawanci an gane aikin sa. Kawai shiryawa a kayi a nuna masa bai isa ba. Saboda yaci mutuncin d'alibai shalelen makaranta daga zuwa. Kuma ya nuna musu iyakar'su. Kuma intisar da ita ce zak'ak'uwa wa ta ma rasa kunya, ita ta tsara a nuna masa mun gagara, sunan da malam Abba ya Sama na. Ni dama bana cikin had'in kan. Shiru nayi naga na samu 'Yar uwa, Mu zama Mu biyu. ganin zai yi zaniya, nayi saurin d'aga hannu. Daya ganni ya fara da yi min kallon kufula. "Da kema kin iya kika saje da su? duk zan iya daku don k'aniyar'ku. Naku wasa ne Wallahi." Da sauri na soma yi masa bayani cikin turanci, saboda banason a binda zai tab'a min lafiyar jiki. Ina tsoron duka sosai, tun ina k'arama. Tambayoyi ya Shiga jeromin da turanci, uwa da 'ya'ya har da jikoki, duk domin na gaza amsa d'aya nima na fad'a tarkon'sa. Haka na fassara shi. Allah ya taimakeni na bashi amsa,saboda duk cikin class d'in babu Sama dani a kaifin basira, da haddace a bu. Ni nake d'aukar lambar farko duk jarrabawa ma.k'oK'arina ya haskakani, har na samu muk'ami. Yace cikin watsomin kallon raini. "Kinyi sa'a kin haye, kin tsallake hukunci na. Da kin gaza amsa tambaya d'aya da bazaki tsallake hukunci irin nasu ba. Amma zaki fad'o tarko na wataran, domin ban huce da ke ba.Saboda na kula ku duka taron tsintsiya ne babu Shara,ba kusan ma me yakawo ku makaranta ba. Shashashan Kawai, dak'ik'ai." Yau mun gamu da gamon mu. Haka na rink'a fad'i a zuci Kowa ya k'ara fusata da raina kan'sa fa ga wannan tahaliki. Bai d'auke mu ma a bakin komai ba, face Shara, tun da aibata mun ma da yake shaida ne. "Je ki kisamomin bulala babba a staff room, kuma ban yarda da babu ba." Yace dani. Na tashi zan fita mata ta d'aga hannu wai zata yi bayani. Yasakar mata kallon banza, Sannan yace "Is too late" Ta koma ta zauna ragwaf. Nayi sa'ar samo k'atuwar bulalar malam tukur. Nasan da ban samo ba, nima tawa ta sameni. "Ten, Ten, lashes ta tabbata ga kowace yarinya. Ku fito one by one Kowacce ta k'arb'i tata. Na baku damar da zan baku kun wofuntar, saboda baku da kirki, ban San me kuka d'auki kan, Ku ba. Ni kuma nasan kaina da darajar lokaci. Bazai yiyu na rink'a zuwa Ina aikin banza ba. Kullum Sai kun daku Wallahi, in dai baku canza ba. Zanga ni da bam bamci ku da jaki ko babu. Tun da shine kullum cikin duka, amma baya canzawa". Wata matsoraciyar duka irina farida ta soma bashi hak'uri tana hawaye. Ai kuwa da sauri ya d'aga mata hannu. "Yi min shiru ko bulalarki ta k'aru. Banace muku ni bansan kalmar hak'uri ba?" Wai yau 'yan class d'in Mu za'a daka.? Ko tsawa bamu Sani ba. Kuma Wai bulala goma goma. Na tabbata yarda a jin ke cike da 'ya'yan gata'ya'yan so, wasu ko yatsa ba a'tab'a sa musu ba da sunan hukunci. Intisar Ina kallon'ta taunar cingam take ma a binta, tana tab'e baki, Tana kallon fa'izu k'asa k'asa, saboda gani take tafi k'arfin nan. Duk cikin a jin babu kamarta a kyau, kuma babu Wanda ya kai Uban'ta kud'I. Malaman dake son'ta da yawa, shi yasa take tsula tsiyarta. Bata da kok'ari ko kusa, Amma Sai muga taci jarrabawa. Bata kallon kowa da gashi. Ta gasawa malami bak'ar magana kuma ta kwana lafiya. Ita ta fara fitowa, kamar zuwa tayi a fara dukan takanta, Amma Sai ta tsaya daga d'an nesa ta dubi Malam Fa'iz tace. "Sir, gaskiya bamu can can ci duka ba. K'aidar koyarwa, duka shine mataki na k'arshe. Kamata yayi kayi ta mai mai ta Mana karatun, ko na Sati guda ne, har Mu fahimta. Kuma fa mu senior ne kar ka manta, duka ai Sai jenior." Ina lura da kallon mamakin da yayi mata, tare da jin jina k'arfin zuciyar'ta da ta iya fad'a masa hakan. Rashin sanin intisar yasa yake mamakin. Bata da shayi, ga isa da alfaharin dukiyar uba da kanta. Shi yasa take ganin babu namijin da bazata taka ba, ta Sha ko da yake naga ta sassauta ma rashin kunyar tata a kan'sa ga yarda takewa malamai. Yace da ita. "Come here ". Ta isa gareshi yarda ya umarceta. Yace"Me kika ce?" Ta sake mai maita masa kuwa, har ma da 'yar dariya. Ya fusata yace "Why are you laughing.? Mai makon ta bashi amsar dalilin dariyar, Sai ta sake yi ma. Wani irin mari ya kai mata, ba domin tayi saurin kaucewa ba, ranar da taga taurari. Cikin harzuk'a yace. "Koni bawan ubanki ne, nake yi masa bautar koyar dake, baki isa ki dubi idona ki fad'amin wad'annan kalaman ba ki tsira. Saboda kin rainamin hankali zaki fad'amin wad'an nan lafuzan? Saboda jaka ce ke ko? Kuma a Ina kika zama senior? Kan ki fanko ne fa babu komi Sai tarin rubish. Simple topic irin wannan kika sa understanding? Ballagaza dak'ik'iya irin ki Zaman gida, shi yafi dacewa dake. Mai makon dai kizo a yi biyu babu. Ki wahalar da malami, ki kuma wahalar da kan ki, tun da k'wak'walwarki ta kifi ce ,ba fahimta za kiyi ba ma." Intisar Kam ta muzanta a lokacin, Wai ita aka tozarta gaban wad'an da take ganin ta fisu. Za'ace ba'a tab'a ci mata mutunci ba a rayuwarta ma Sai ranar. Kuma namijin da take takawa. Kasa cewa komai tayi, saboda yarda ta karanci zafin sa, idan ta sake tagawa, Sai a binda ta gani kuma. To bata tsaya nan ba, babban a binda ba'a tab'a yi mata ba, ranar an yi mata. Zafafan bulalai yayi mata da tafi ta kowa. A hannu yake bulalar sa, da tak'i tsayawa ne, ya k'arashe mata a jiki. Tasha kuka, Sai gata magiyar Hak'uri take bashi. Bai kuma saurara ba. Na yarda Fa'izu baisan kalmar hak'uri ba.Kowa bulala Sai da ya fito ya karb'a Kam. Amma biyar biyar, Sai dai ko Wacce d'aya Sai ka fad'awa mutan garin Ku. Yarda yake da zafi, haka ma bulalar'sa. Ni Amma na tsira, Sai d ai na k'ara tsorata da lamarin malam Fa'izu. Ai tun daga ranar kowa ya Shiga taitayin'sa da shi. Karatu babu wasa. Nutsuwar fahimta, kowa Sai da ya lalubo, idan ma baka da shi, to Sai ka aro. Tuni ya gyarawa marasa kunya zama da kuma dak'ik'ai , da yayi tambaya kuwa rige rigen bashi amsa ake yi. 'Yan a jin mu da malamai ke masifar ji damu, to fa'izu yafi tsanar mu shi. Yafi kuma takura mana ma. Amma yana da hujja gareshi. A Kwai ranar da yace. "Na fahimci kun d'auki kan Ku Wata tsiya, shi yasa kuka d'auki girman kai kuka d'orawa kan Ku. To zan saukar muku da shi kuwa." Gaba d'aya makaran ta ta d'auka da Fa'izu Bukar,ko'Ina ka zaga Zancen sa. Makaranta tuni ta soma gyaruwa, saboda matsayin displine master a ka bashi, saboda jajircewar sa wurin kawo gyara a makarantar. Ya gyara makaranta Kam, ko ga tsafta da tarwatsa Zaman da malamai suke na hira a k'i Shiga a ji koyarwa. Meeting na dole yasa a kayi harda prince pal aka kawo sauye sauye. Ko a makararru ma an samu sauk'i sosai. Domin Sai a jima ma ba'asamu wad'anda za'a tare ba da sunan makara. Saboda malam Fa'iz ke hukuntawa. Kuma babu sauk'i ko a fuwa a lamarin sa, ko wacece ke zaneki zai yi tas kuwa. Kuma idan zaki d'ige kina bashi hak'uri bazai hak'ure ba. Bada Hak'urin ma shi fusata shi yake yi naga. Tofa!. watan'sa na biyar nima na fad'a komar sa. Dama yayi min baki. Garin tsautsayi rannan Sai gani cikin makararru guda biyar. Zance tsautsayi, tun da ban tab'a makara ba. Abinka da matsoraciya. Jiki har rawa yake Ina bashi hak'uri da yazo kaina ya rik'e baki. "Cab' , monita kina shugabar d'alibai amma kika makara? Muk'amin ki bashi da wani amfani, tun da ke shugaba mai gyara kin gaza wazai gyaru kuma?" "Wallahi sir ban tab'a makara ba, yau ma akasi a kasamu na tuba, bazan k'araba." Yace"Kome zaki ce ba zaki tsira ba Wallahi. Kuma bulalarki Sai ta ninka tun da shugabanci aka baki ga 'yan baya, dole muna so ki ki yaye. Zafafan bulalai goma yayi min da naji kamar na shid'e domin zafi. hak'uri da nake bashi naga kamar tunzurashi ma nake, shi yasa na hak'ure. Hannaye na har tara jini suka yi bayan kumbura. Na yarda Fa'iz mugu ne na k'arshe. Da gayya ma nasan yayi min irin wannan bulalar mai ratsa k'ashi. Tabbas Sai a lokacin na yarda da zafin bulalar sa da d'alibai ke fad'a suna tsoro. Tun daga ranar naji na tsaneshi. Tun da uwata ta kawoni Duniya Kam ba'a tab'ayi min bulala ba nima ballantana mai zafi irin wannan. K'udirewa nayi a raina na daina yi masa magana ko a aji.Amma daga baya dole na saddak'ar, saboda malam Fa'zu yafi gaban nan. Tambaya ma baka amsa masa ba, hukunci ne mai zafi. Domin kuwa ko zagin'sa na tsamar nama yayi maka ma bainan nasi, ya cuceka. Ga dai intisar nan duk tayi laushi ta horu. Duk rashin kunyar nan da felek'e ta dire. Muddin ya shigo class wata nutsuwa ma take yi. Amma a jita jita naji wai son sa take kuma. Bama ita ba ya kwashi Jama'a masoya mata jingim, amma na b'oye. Tun da dai kota Ina babu Wata alama da ta nuna Fa'zu Bukar Zai karb'I tayin k'ok'on barar Soyayyar wata mace a makarantar, face ma Sai dai yayi fatali da k'ok'on barar. Ni Kam duk Wacce zata so ma Fa'iz wahalalliya na d'auketa, Wacce kuma aka yankawa kazar wahala a kace Sai ta fige.wahala bata ishe suba ne da wulak'anci suke neman k'ari. Haka nake cewa duk Wacce aka cemin ta Mato a kan son Fa'iz. Ban kuma yarda ta had'oni da malam Fa'izu ba, gudun inda zan ganshi ma nake yi idan ba 'ajin mu ya shigo ba. Duk domin kar ya kamani da laifin da zai ci zalina, saboda na daku, jikina bai manta ba. Kuma kumburin hannu n'a bai gama Sab'ewa ba. Amma duk guduna da shi, Sai da rannan ta sake had'oni da shi. Rannan na Shiga staff room Kiran malam labahani saboda period d'in sa ta shiga bai zoba. Ina Shiga staff room bisa tsautsayi idanu na da malam Fa'izu suka fara kicib'is. Suna zaune shida malam Abba da na fuskanci tasu tafi zuwa d'aya suna cin gyad'a. Malam Abba yana kan desk d'in da suka zube gad'ar, shi kuma malam Fa'izu yana kan kujera, suna hira har suna 'yar dariya ma. A raina nace. Dama malam Fa'izu yana dariya? Zatona ko murmushi bai iya ba. Da wuya ma naje staff room na ganshi Sai Jifa Jifa idan bashi da class, saboda a Kwai himma a wurin sa wurin kula da karantar da d'alibai. Muna had'a idanu da shi kuwa, ya wani d'aure fuska, ya kuma sakar min wani uban muzurai. "Zonan ke monita" Jiki ya na rawa na isa garesu. "Gidan'ku ba'a koyar da tarbiyya ne?" Yace , bayan ya jefa gyad'ar da ya murje bakin sa. Na Shiga dawurwura saboda bansan laifin da nayi ba, Sai da malam Abba yace min. "Tsuguna Mana Sumayya. Ya kiraki kuma kin zo kin tsaya Mana a ka. "Nan na fahimci Laifina, amma ni shi duk ya gigitani. Ganin Fa'izu Kawai tsorata nake yi. Malam Fa'izu batare da ya ko kalleni ba yace. "Sintirin me kike damun Mu da shi a staff room? Kullum kina kan hanyar zuwa nan? Uban me yake kawoki matattarar malamai?" Na sunkuyar da kai sannan nace. "Malami nake kira idan period d'in sa ta Shiga bai shigo ba". Ya tsaya da cin gyad'ar cikin d'aga murya da fusata yace. "Wayace Miki aikin ki na monita yana cikin haka? Hak'k'in ki ne Kiran malami, ko Hak'k'in malami ne yazo teaching da kan'sa?" Ba suna da time table ba ma?" Nayi tsuru tsuru da ni nak'i magana, gudun nayi laifin da zai casani. Tuni duk kallon malaman dake staff room yayi yo kan Mu, saboda yawancin malaman suna hallare. Da k'arfi Fa'izu yake magana, kuma nasan domin sujine, domin babu Wanda yake shakka, Sai ma su da suke shakkarsa, har ma da prince pal, da vice prince pal.saboda bayan zafin sa,ya tab'a cewa a kunne na da suna hira da malam Abba bayan staff room da zan wuce ta window, cewa yaja kunne a meeting domin kowa yayi hattara, na yana da hanyar da zai kai k'ara ma'aikatar ilimi ga shugaban kula da matafiyar ilimi na k'asa, in dai shugaba da malamai suka ci gaba da cin albashi a b'agas babu kula da hak'k'okin aikin su. Malam Fa'izu ya dubeni cikin fushi. "Kar ki sake na k'ara ganin k'afarki a staff room da niyyar Kiran wani malami. Wallahi na sake ganin ki? zaki fuskanci hukunci na ban Mamaki. Ihope you get it?". Na jinjina kai. "Kin fahimta nace? Talk to me." Na gyad'a kai da sauri. "Na fahimta, sorry sir." Yaci gaba da kallo ga malamai da suka kafa Mana idanu. "Albashi a na biyan kowa duk month mai nauyi kowa ya lamushe cikin jin dad'i amma ace wai Mutum baisan time d'in aikin sa bama Sai an kirashi? Why? Is not fair gaskiya. Menene amfanin time table da agogo Kenan? zamu sake zama da prince pal da teachers dole a yi gyara." Babu wanda ya iya cewa kanzil kuwa, saboda gaskiya ya fad'i da ba kowa zai iya bugar k'irji ba ya fad'I, Sai irin sa Mara tsoro mai dakakkiyar zuciya kuma. "Tashi Kije".Yace dani da nayi sunk'ui da kai. Tun daga ranar, ban sake yarda naje staff room ba, saboda gargad'in malam Fa'iz. Domin nasan makomata ma idan ya kamani. Ba'ajima ba kuwa na fahimci anyi gyara. Domin da lokaci ya Shiga malami Zai shigo da kan'sa. Ba kuma Zai fita ba, Sai lokacin'sa ya fita. Kuma karatu ya k'ara zafi. Malamai sun daina shigo da hira da wasanni cikin karatu, Wanda nafi kyauta ta zaton malam Fa'izu ya fahimci duk matsalolin dake cikin harkar koyarwa yasa aka kawo gyararraki. Ko Mak'iyin malam Fa'izu tabbas ya yarda sanadin zuwan sa, makaranta ta gyaru. Sauye sauyen ci gaba da ya kawo da yawa na ci gaba. K'orafin da a ke yi da shine bai kau ba wato na tsanani da cin zarafin studen't fiye da k'ima idan sun yi laifi. To ni fahimtata da hakan , Kawai na fahimci Fa'iz Mutum ne mai fushi da zafin zuciya. Shi yasa ma Sam baya d'aukar raini. A binda ya shige min duhu da shi, na yarda baya karb'an uzuri. Kuma baisan kalmar Hak'uri ba. Watanni uku suka rage muyi jarrabawar kammala makaranta. Saboda haka rannan Bayan malam Abba ya gama yi Mana subject d'in sa na mathematic, ya zauna yana bamu shawarwari domin mu kara zage damtse da karatu mu samu sakamakon jarrabawa mai kyau. *Zainab mazawaje* [6/20, 7:58 AM] Zainab Mazawaje: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe *NI DA GIDANA* *By* Zainab mazawaje _Best brilliant intrlligent writer_..... 🖋️ *page 3* Malam Abba, ya gyara tsayuwa, ya fuskanto mu yace. "Ko da yake yanzu kuna birgeni, naga ma ai duk kun canza kunyi laushi. Da idan an shigo a jin nan kamar kasuwar trade fair, amma yanzu kamar gidan makoki. Ko babu malami zanga Kowacce ta d'auko littafi tana bitar karatu. Wai yaya a bin yakene.? Ko walwalar ku ma bana gani." Ya karashe furucin cikin wani murmushi mai nunin da wata manufa a cikin maganganun sa. Fati d'alha tace "Sir, gaskiya ya kamata kayiwa aminin ka nasiha, ya fiye tsanani. laifi da k'arami da babba duk hukunci d'aya. Zagin da yake mana, ko iyayenmu basa yi mana. Wallahi matar'sa ta Shiga uku." Intisar tace. "Addu'a zaku yi masa kawai, domin ya gyara halin sa, amma mutum ko aljani ba za su iya sauya malam fa'izu ba wallahi". Kowa Sai da ya dubeta na Mamaki. Shi kuwa malam Abba murmushi yayi. "Yauwa 'yar gari, Kunji in da ake kalamai na nutsatstsu. Kuma idan b'era da Sata ai daddawa ma da wari. Kuma k'iriniyarku tayi yawa, dole Sai irin malam Fa'izu ne zai yi dai dai daku. Malam Fa'izu idan ba'ace Sam barka ba, baza'a kushe ba. Gyaran da ya kawo cikin makarantar nan ai ya yawaita. Ko prince pal da vice sun Sara masa. Ai addu'a ya dace Kuyi masa ta alkhairi. Ya dan yi shiru kafin ya numfasa yace. Bayan tarbiyyar da ya kimsa muku ya gyara muku harkar karatu sosai. Kuma ku zakuci amfanin sa a gaba. Shi ba ma mazauni bane jiddin. A Kwai a binda yasa a gaba, da ya samu zai bar harkar koyarwa, Kawai ya Shiga harkar da ba itace burin'sa ba, sabod kishin kasarsa. Zan iya rantse muku albashi ma shi baya gaban'sa. Burin sa a samu sauyi da ci gaba. Saboda haka kuskure ne d'alibi ya zauna yana aibata malami ko da dalili, tun da kullum cikin cin amfanin sa yake. Kuma ba'a iya biyan malami kun sani sai ubangiji ne kawai zai iya biyansa". Jikin kowa yayi sanyi. A ka rasa me iya cewa komai. Ni kuwa dama nasan kuka suka kawo gidan mutuwa. Malam Abba na hannun Daman malam Fa'izu ne, bazai tab'a yarda a ai bata shi ba ya k'yale, duk da dai gaskiya ya fad'I. Alkhairan da malam Fa'izu ya kawo, a makaranta, bai kamata a aibatashi ba, koda yayi laifin. Kowa ma yaji ba domin kud'i yake koyarwa ba, Sai domin kishin k'asar'sa. Wannan kad'ai ya isa yasa ya karb'i lambar yabo. Tunani na kenan da na wasu d'alibai da muka zanta daga baya. Daga baya ga mamakin mu, malam Fa'iz ya sassauta tsananin nan da tsaurara hukunci garemu. Kuma na lura canzawar da yaga munyi ne, Shima yayi d'an laushi. Sannan ya fito da wata hanya ta taimakon mu, don mu haye a jarrabawar mu ta gama makaranta ta gaba to. Lesson ya tsara duk yamma cikin makaranta ga duk wacce ke ra'ayi amma. Shi ya d'auki nauyin komai.hud'u da rabi an Shiga a tashi k'arfe shida na yamma. Duk d'alibai kuwa a ka yi ta tururuwar zuwa, saboda kowa so take taci jarrabawa. Ba kuma iya darasin turanci yake koyawa ba, har ma da sauran darussa. Kuma yawancin a binda yake koya mana wanda yake tunanin zai fito mana ne a jarrabawa. Baki d'aya muka ga ya canza ma. Ya rage zagi da fad'an nan da tsare gida. Amma duk da haka fa babu fuskar da za'a kawo masa raini ko wasa. Har hira ma yake damu amma fa a kan karatu, da bamu shawarwari masu kyau, duk a kan harkar karatu, saboda jarrabawar dake dosomu. Da jarrabawar tazo kuwa mun taki babbar sa'a. Domin kuwa yawancin a bubuwan da malam Fa'iz ya koyar damu shi ya fito. Har zargi ma muka rink'ayi anya bai samu tambayoyin jarrabawar ba a boye, domin komai ya fito da ya koyar damu. Ai sai yayi kuma farin jini wurin mu. Domin yayi mana k'ok'arin da babu malamin da yayi mana irin sa. Mun kammala jarrabawar cikin sa'a da kyauta ta zato, domin duk wacce ta sare, sai dakikiyar da kwakwalwarta ba ta aiki. Ranar da muka kammala jarrabawa da yamma, aka sha hotuna, har da malamai a kayi hotuna. Amma fa banda malam Fa'izu. Kuma anfi kwad'ayin ayi hoton da shi, saboda tarihi. Kuma abin alfaharine ga d'alibai, amma mirsisi yak'i. Ko da yake tsoron tun karar'sa ma a ke yi, malam Abba a ka tura. Ya dawo yace. "Kuyi hak'uri fa. Abokina yak'i yace yana da mata, kuma zatayi kishin haka. Duk d'alibai sun yarda, nice dai kunne na bai karb'a ba. Lambobin waya ma na malamai da ake karb'a malam Fa'izu hanawa yayi. A ka koma takan malam Abba ya bada lambar wayar malam fa'iz yace shi bashi da ita. Ta yiyu shi ya hana shi ya bayar, nafi kyautata zaton hakan. Intisar tafi kowa damuwa da lambar Fa'iz, saboda son da take yi masa ma ya fito fili. Amma ko giyar wake tasha bazata iya tambayar sa ba. Tun daga Sanda tayi masa rashin kunyar nan suke takun sak'a da shi. Ta gasu a hannun'sa. Tsakanin sa da ita hararace. Duk Sanda ya shigo class Sai ya tasheta yayi mata tambayoyin abinda ya koyar. Ta fad'i wanda ta d'an fahimta, tana yi yana jefa mata kallon wulakanci, da ta kakare kuwa zai ta gasa mata maganganun tozarci da gwara dukan ma dasu gaban dalili bai, to ya fuskanci tafi jin ciwon bakaken kalmomi, shi yasa baya dukanta ma sai dai ya tozarta ta gaban jamaa, ta hanyar cin zarafi da furuci. Gaskiya Ancle Fa'iz yasan takan iya tsiya, da ka fada tarkon sa, gwara a jefa ka gidan yari iya na waadin laifin ka. A cewar zuciyata . Tsawon wata guda, tun da na gama secondry, babu in da nake zuwa bayan islamiyya. Sam kuma fitar bata dameni ba ma saboda ni dama ba ma'abociyar son yawo bace. Sannan soyayya da tarairayar da nake sha wurin kawuna sulaiman ta isar min daga damuwa da wani a bu a rayuwa da zai sa na rinka yin tunane tunane. Kulawa gata, sangarta so da k'auna duk Kawu sulaiman ya tattare su a kaina. Haka ma kakana Laminu mai turare. Sai 'yar korar su mai taya su, matar kakana Baba Talatu da ya auro bayan rasuwar Inna Hajara kakata. Duk da baza'a had'ata da kakata ba inna Hajara, amma tana kamantawa sosai. Ni d'in marainiyace ta sosai, tun da ban bud'i idanu da iyaye na ba duk sun rasu Ina yarinya sosai. Bayan nan kuma nazo na rasa kakata Hajara ita ma data rungumi maraicina da kyau, take nunamin k'auna muraran. Sai da ta shekara da rasuwa kakana yayi aure, kuma saboda ni. Saboda babu yarda za'ayi ya zauna dani babu mace. Naga mutuwa a rayuwa ta Kam. Amma Sai a tara masu iyaye Sama da d'ari ba'a samu mai Samun kulawa da tattalin k'auna iri naba. Shi yasa bayan rasuwar kakata Soyayyar ta dawo kaina. Haka ma kawuna Sulaiman Soyayyar dake tsakanin sa da yayarsa mamana Khadija da bazata fad'uba, kaina ya tattarota bayan rasuwarta. Su biyu ne tal wurin iyayen su, kuma a Kwai k'auna da fahimta mai zurfi tsakanin su. Wannan dalili yasa Kawu yake mugun Sona da tausayina. Motsi kad'an yana bibiyar me nake ciki. Kome ya samu ni zai kawowa. Tun da ya gama digree babu aiki ya Shiga buge bugen aikin Samun k'ud'i na k'arfi, daga wannan zuwa wannan, duk saboda ni. Ma'abocin son K'wallon k'afa ne sosai. Suna da Club babba ma na matasa irin sa. Suna buga mach kurfa kurfa na state state bayan na garin su idan an gayyace su. Yama fi Samun kud'i tanan babu laifi. Amma lokacin daya ke bawa boll dabam, lokacin buge bugen sana'oin sa ma na kafi zuru da bam. Yayi rini, yayi Aikin gini, yayi aikin electric, har aikin fenti ya iya, idan an kirashi zai b'adda bami yasa Kayan aikin yaje yayi ya karb'i kud'in'sa. Mai k'wazon neman na kaine Kawu Sulaiman, bashi da girman kai Sam. Kuma duk sana'ar da yaji ana Samun kud'i zai koya, ba tare da raina taba. Shi yasa baya rabo da'yan kud'ad'e. Bamu da shi sai dai na rufin a sirin rayuwa, kakana ma a zaune yake ba kullum yake fita ba, da harkar Sai da turare ta karye masa. Da kanti ne da shi guda na saida turarurruka, yanayin rayuwa komai yaja baya. Kawu sulaiman ne ke k'ok'arin a bubuwa da yawa. kuma rayuwar mu babu fallasa, komai a Siri a rufe ruf.'Yan kayan k'walam na motsa baki ma Kawu na kan sayo lokaci lokaci. Ban rasa kuma 'yan Kayan ado irin na 'yammata ba, Kawu sulaiman yana fito dani kunya, ko ban furta ba zai sayo dai dai ikon sa. Ya kuma ban k'ud'i ko zan buk'aci wani a bu. Wani lokaci zaice na samo takarda da biro na rubuta duk abinda nake bukata na 'yan mata, nakan rubuta na bashi, shi kuma duk sanda ya samu iko ya kan sayo su a hankali a hankali. Kuma da an dauki lokaci zai sake cewa na rubuta abinda nake bukata, sannan ya kan bani 'yan kudi na kashewa ma jifa jifa, kuma ya danganta da nauyin aljihunsa na daga a binda zai bani. Ya wanke min duk wani hawayen maraici, saboda ubana talaka ne sosai, bai barmin komai na gado bama. Ko gidan da suke zaune da mahaifiyata ma na hayane, kuma biya masa ake yi. Tun mahaifiyata tana raye Kawu na yake nunamin Wata irin kulawa da soyayya, da Ina yarinya naji daga kakata, bawai sai data rasu ba. Domin da ta rasun ninkawa kuma yayi. Ya kusa zautuwa ma kawu da mamana ta rasu saboda kusancin sa da ita da k'auna. Kakana ma da matar sa kulawa da k'auna suna bani iyayin'su, saboda maraici hawan hawa da na samu kaina a ciki. Ina da ra'ayin son ci gaba da karatu, shi yasa ma aure baya gabana, ko kula kula da shaannin samari ba nayi, kuma kawu ya goyamin baya. Ina da samari, tun kafin na kammala secondry. Duk da haka dai i na da samari biyu da nake sauraren su sama sama. A Kwai Alhaji Rabi'u magidanci mai mata da yara. Yana da sukunin sa kuma yanayi min 'yan hidindimu. Yana da mota da yake zuwa wurina ma. Sai usman shi kuma saurayi ne, tela ne na aikin surfani. Hankalina ya d'an fi kwanciya da Usman saboda shi saurayi ne dai dai dani. Ina tsoron fad'awa tsakiyar ma'aurata. A nawa ra'ayin gwara tazo ta sameni. Amma shi Alhaji Rabi'u kullum zancen'sa na bashi dama ya fito, amma bana bashi had'in kai. Shima Usman ya damu da azo a yi wani a bu, Shima d'in ma ni nake bashi matsala. Ina son na samu ilimi sosai nayi aiki na rink'a tallafawa Kawu da kakannina. Wannan shine burin sumayya a b'oye. Kwanci tashi jarrabawar mu ta fito na samu sakamako mai kyau k'warai. Shi yasa direct jami'a,suka amsheni. Kawu yayi ta samin albarka. Sosai yayi farin ciki, har kyauta yace zai min. K'awaye nama duk sunci da kan mu yake a had'e. Saboda halayyar mu guda ce ta son karatu. Amma nafi su kyawun sakamako dai. Kawu sulaiman yayi min nasiha sosai da shawarwari, wurin tafiyar da rayuwata ta jami'a. Yaja kunne na sosai a kan kar nayi mu' a mala da k'awayen banza da samari. K'arshe yace. "Na baki dama, don Allah kar ki bani kunya Sumayya, kija mutuncin ki, kiyi a binda ya kai ki Kawai, wato karatu." Nace" Kar kaji komai, Ancle, zan kiyaye, ka ta yani da addu'a." To ban bashi kunyar ba kuwa. A shekarata ta biyu a jami'a ya dad'a sakin ransa sosai saboda yarda yaga komai nawa yana tafiya dai dai, Sai ma k'arin ci gaba. Na k'ara nutsuwa wurin kula da tattalin kaina. Na k'ara sanin darajar kaina sanadin k'yamatar wasu a bubuwa da nake gani. Na k'ara kyau na gogewa da wayewa kuma, amma wayewa ta sanin mutuncin kai da darajar kai, da iya muamala da mutane, da kiyaye abinda zai rusamin rayuwa. Ba fara bace ni, amma za'a iya sani a layin farare idan sunyi k'aranci. Saboda kulawa da kaina da nake sosai, fatata Sai ta k'ara gogewa ta haskaka sanadin gyara. Kawu lokacin Samun'sa ya k'aru, ya kuma Saki Samun'sa sosai a kaina ma a lokacin. Burin sa Kawai Sumayya ta zama a bar kwatance da alfahari. Alkalamin...... 🖋️ Zainab mazawaje [6/20, 8:19 AM] Zainab Mazawaje: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe *NI DA GIDANA* *By* _Zainab mazawaje_ _Best brilliant interlligent writer_..... 🖋️ *page 4* A tsukin kuma wanda nake kira da dan fodiyo wato (usman), ya matsa lamba. Sai ya nuna ala tilas sai na barshi ya turo manyan sa shi ya gaji da jirana. Ga a binda yace da nak'i yarda. "Sumayya, don Allah ki rufamin a siri nasan Matsayina. A farga ba nake tsindim na zaki iya kub'cemin. A komai kin canza kin samu haskakar da za'a k'yalla idanu a kan'ki a kawo miki hari. Babban a binda nafi kwad'ayi a kan'ki shine kamun kan'ki da nutsuwa da tarbiyya. A ina kike tunanin zan lalubo irin'ki idan na rasa ki? Tabbas zan shiga tasku idan na rasa ki. Ina sonki Sumayya fiye da tunaninki, don Allah kar kiyi min wasa da hankali. Ni dai na fito a San dani nasa rai ma. Aure zan jiraki zuwa lokacin da kika shirya." Sam aure baya raina a lokacin, ko fidda ma gwani. Tausayin Usman shi yayi rinjaye a raina, bawai son'sa ko son auren'sa ba. Saboda nacin sa da magiya na a mince amma nace ya bani kwana ki biyu nayi magana da Kawu na. Yayi ta murna kuwa. Ranar da mukayi zan fad'awa Kawu Sulaiman, Usman zai zo yaji inda a ka kwana, ranar Kawu na ya tashi da gyare gyaren d'akin'sa, saboda ranar lahadice baya fita Sai yamma, ni kuma bani da lacture. Na shiga taya shi, saboda gyaran da yawa. Kusan yayi d'ai d'ai da komai na cikin d'akin. gyare gyare da goge gogen da yawa. Na kafe Sai ya barmin nayi ni kad'ai. Ya saduda ya tafi ya barmin. Da yake Ina da saurin aiki, sai gashi na gama, ina mai da komai muhallin'sa naci karo da wata farar ambulan 'yar babba. Ko Ancle Sulaiman ya sanni da lafiyar bincIke. kamar nawa na Shiga k'ok'arin bud'ewa, domin naga menene a ciki. Amma a tsorace nake kar ya shigo ya ganni, yace mai hali kin soma ko? Domin na saba da wannan kalma tun Ina yarinya. Tuni na fahimci hotuna ne, da sauri na shiga zaro su, duk zatona hotunan budurwar sace da ban tab'aji da gani ba. A bin takaici a gareni, hotunan maza na gani, saye da kayan 'yan boll har dashi. Wani Mutum uku wani mutum biyu wani shida. A Kwai kuma wanda suka had'u su duka suka sa boll d'in a tsakiya shida 'yan club d'in nasu. Amma menene yaja hankalina na kasa a jiye hotunan kamar yarda naso da fari, da naga ba hoton mace bane? Mutumin da na yanke zaton zan sake gani a rayuwata, Mutumin da nasan babu wani dalili na sake had'uwata da shi, shine a cikin hotunan 'yan club d'in su Kawu Sulaiman.wanene? Faiz Bukar. Na sake kai ganina ga hoton, amma bisa ga wanda ya d'au hankalina da ganin'sa wato Fa'iz. Gaba d'aya ya haske hotunan. Kowanne da ka kalla, shi zai fara janye kallonka. Muryar Kawu Sulaiman naji a tsakar kaina. "Me hali baya fasa hali dai. Bincike kike min ko gyara sumayya?" . Nace. "Yi hak'uri my Ancle. Wani malamin mu na secondry na gani shi yasa na tsaya dubawa ma, dama kasan shi kawu?". Na nuna masa shi. Ya duba yace. "Au, Yarima kike nufi?". Na sake nuna masa shi, ga zatona bai kulaba. "Ka ganshi fa, wannan farin na cikin ku, malam Fa'izu fa." Yace. "Shi d'in nima nake nufi ai , sunan'sa Fa'izu, amma mu a bokan'sa Yarima muke ce masa. Mu kance masa kuma Gimba, wato d'an sarki, a hausance kenan. Amma mun fi Kiran'sa, da Yarima, a yaren barbarci ne, saboda usulin mahaifin'sa babarbare ne, mahaifiyarsa kuma k'abilar shuwa a rab ce. Na dubi Kawu saroro. "Me yasa kuke ce masa Yarima Ancle.?". Murmushi yayi ya karb'i hoton."Abokai suka sa masa kuma ya bishi. Baki ga takunsa yayi kama da na masu wannan sunan ba kema?". Nayi gajeriyar dariya. "Tabbas na harbo jirgin Kam, sunan ya dace da shi sosai, kun iya sa sunan a muhallin'sa. Ai ya yiwa dalibai horo sosai a school d'in mu. Bana zaton a kwai d'alibar da zata mance dashi. Sunayen ma da za'a kirashi da shi suna da yawa. Dama d'an club d'inku ne Ancle?". "Sosai, a harkar boll kuma muka had'u muka saba. Shekara shida Kenan da ya shigo club d'in mu na Kaduna united. Ya iya boll fiye da zaton mai zato, da shi muke ji a club. Ko jiya na had"u da shi da yamma a club, mun Sha hira a kan gasar wata boll da muka je. A Kwai mutunci tsakani na dashi, duk da babu wata a bota dai sosai tsakanin mu, Sai mutunci sanadin club tare da buga k'wallo. Hirar ta datse ne saboda baba Talatu da ta kirani. Usman dan fodiyo da yazo hak'uri na bashi, nace ya k'ara min kwana biyu dai. Mantawa nayi ban yi Maganar da kawuna bama. Kwana biyu tsakani da yamma Lis, ina zaune tsakar gida, Kawu sulaiman ya shigo, nayi masa sannu da zuwa, haka ma baba Talatu. Yayi mata sannu da gida. Ya dubeni yace. "Sumayya yau ina tare da Yarima, yace a gaisheki." Nace"Ina amsawa." Ya wuce yana yin wani murmushi da bansan musabbabin'sa ba. Ni dai nasan babu yarda za'ayi wallahi Fa'izu yace a gaisheni. Mutumin dake bala'in jida kan,sa. Ta ina ma ya tuna da sumayya, a rayuwa? Shekaru biyu fa Kenan rabona da gama makaranta. Kawai bazan iya k'aryata kawuna bane. Washe garima da Kawu zai fita sai yace min. "Sumayya yau ma zamu had'u da Yarima da k'arfe uku na rana a club, me zance wa Yarima?". Nace"Bani da a binda zance masa Kawu." Yace. "Kikayi haka baki kyauta ba, amma shi yace a gaisheki? amma zan ari bakinki na cimiki albasa kawai. Ni dai ban tofa ba. A yar tambaya ce ta soma tsayamin a rai name kawuna yake nufi da son had'a a lak'ata da malam Fa'izu? anya babu wani b'oyayyan al'amari a zuciyar'sa? . Ture komai gefe kawai nayi na shiga dakon jiran'sa ma na ya dawo nayi masa zancen d'an fodiyo, domin ya matsamin da sai ya turo iyayen'sa Usman yazo zance wurina, gaisawa Kawai mu kayi, kafin ma muyi nisa da magana, Sai ga Kawu Sulaiman ya dawo. Yana shigowa farfajiyar gidan, Usman ya rusuna ya gaisheshi, cikin tsantsar ladabi. Ni kuma nayi masa sannu da zuwa. Yace. "Sumayya zo na ganki na 'yan mintina". Nace"To, gami da Mik'ewa. Ya kuma waiwayi Usman yace. "Usman, kad'anyi hak'uri na katse muku hira, yanzu zata dawo." Ya nuna har a fuska babu komai. Hanyar fita waje yayi, na bishi. Kafin mu isa ga k'ofar fita yace."Sumayya, Yarima na kawo miki Ku gaisa. Daga meeting muke na wasan k'wallo da zamu buga da k'ungiyar 'yan boll ta Dolfin, very soon. Shi ya kawoni gida ma a babur dinsa, kinsan nawa ya samu matsala. Sai nace to why not bazaku gaisa ba, ko kuwa?" Murmushi nayi nace "To, Ancle." Kawai Samun kaina nayi da fargabar had'uwata da Fa'izu. Gabana ya rink'a fad'uwa ma, Yayin da na tuno d'abiun'sa na cin zarafi da fushi ko yaya aka kuskuroshi. Ban manta komai ba. Shi yasa nake ganin komai ma kamar lokacin da yana koyar damu, kamar zan yi masa kuskure yaci zarafina. A k'ofar gidan Mak'ocin mu Alhaji Bilyanu muka sameshi ya jingina jikin sabon Jan babur daya kasance nasa. Hasken fitilar k'erarren gidan mai haske komai ya haskemin shi sosai. Saye yake da Kayan 'yan boll koraye, Amma wandon dogone mai taushi. Ban tab'a ganin Mutumin da kayan 'yan boll suka yi masifar yi masa kyau ba, irin Fa'izu. Domin sun k'ara haskaka shi ma. Wani kyau naga ya k'ara da haske da 'yar k'iba ma kad'an, da ta k'ara yi masa kyau fiye da da. Ko har yanzu yana koyarwar?. Kaina na tambaya. Na yarda lallai ya samu dan cigaba na rayuwa, don ada bashi da babur sanda yake koyar da mu a makaranta. Na rusuna na gaisheshi. Ya k'ara d'aga idanu ya dubeni sosai bayan ya janye daga jingina jikin'sa da yayi jikin babur. ya dubi kuma Kawu sulaiman. Kawu Sulaiman kuwa tsare mu yayi da kallo ni da fa'izu ya kalleni ya kalleshi hak'oran sa waje cike da nishad'i da bansan dalili ba. Fa'iz ya dubi Kawu na. "Kasan Sai yanzu na ganeta Sulaiman? ai da ban fahimci wacce kake ta kwatantamin ba, saboda d'aliban da yawa ,ko na santa, ko sunan'ta iyanzu mantawa zan yi, an fa jima da yawa. Na manta sunan ta dai, amma na ganeta a ido. Sanin monita nayi mata na Class 6 B ko?.fitinan nun school ai dole na rike wannan class, duk da na gyara musu tsari". Tabbas baka da mantuwa Malam Fa'izu. Zuciya ta ta kimsamin. Na gyad'a kai, Sannan na kai dubana ga Kawu Sulaiman, na kuma dire kan Yariman nasa . Carab Sai muka had'a idanu kuwa. Sai yayi dan murmushi kafin ya maida kallon'sa ga Kawu Sulaiman ganin mun hada idanu. Zan iya cewa shine farko da nata b'a ganin murmushin Fa'izu gareni, a iya sanin da nayi masa. Cikin tausasa murya yace. "Sumayya, ai ban tab'a sanin ke Jinin Sulaiman bace. Da nasan hakan, Atleast ai da kinsamu kulawa irin wacce ta dace. A Kwai a minci da girmamawa tsakanina da kawun naki, he mean so much to me. Ina ganin k'imar'sa da shi kan'sa baisan iya ganin kimarsa ba da nake ji game ni. Nima yanzu Ancle d'inki ne Sumayya kinji ko?". Na sunne kai k'as cikin murmushi nace"To". Ya maida hankalin'sa kan Kawu Sulaiman kuma. "My man, Ina cikin mamaki fa yarda k'addara take ta had'ani da wannan Daughter taka, bayan mun rabu. Sau uku Kenan fa. Three times Sulaiman. Ya nuna yatsun'sa uku yana nuni da shi. Ni Kam sak'e sak'ena nake, Ina ganin kamar a majigi komai ke faruwa. Malam Fa'iz ke tausasa harshe yana fad'amin wad'annan kalaman? Dama ya iya tausasan kalamai a she? Kawu Sulaiman ya duba yana mai cewa. "Farko ta yarda wayar'ta na tsinta, ta kira layin mu kayi magana ta kwatan'ta min gidan nan na kawo mata. Kasan ban tab'a zuwa gidan nan ba Sai yau ai da tun a ranar na d'au haske, domin Sai yanzu komai ya dawo min,nan gidan nazo na kawo mata waya. Bayan watanni mun sake had'uwa da Sumayya a makaranta nayi teaching d'inta, Kenan a malamin ta nazo. Yanzu kuma Bayan shekaru biyu mun sake had'uwa da ita ta dalilin ka. Me hakan ke nufi Sulaiman, da sanadi ke ta had'ani da 'yarka?". Murmushi Ancle d'ina yayi yace. "Da walakin goro a miya. Kuma ruwa baya tsami banza. Idan kaji gudu kuma to da magana. Fa'izu baice wa kawuna komai ba, game da furucin da yayi, don wasa ma naga ya dau zancen. Ya sake dubana cikin dan jin kan nan nasa kamar bazaice komai ba ya dan juyar da kai sannan ya dawo da shi kaina yace. " Karatu kike yi ne Sumayya?". Nace"Eh". "Da kyau, kin birgeni. Ki daure ki zurfafa karatu, kici moriyar sa tun da kIna da k'wak'walwar fahimta. Ina yi miki fatan alkhairi da nasara." "Na gode Ancle." Na fad'a cikin wani nishad'i da naji ya bak'unci zuciya tashi guda. Gani nake tamkar ba Fa'izun da na Sani bane. Wannan yafi wancan kyawun Siffa ma da ake ta kwaroroto, da dan jiki kadan da ya kara, duk sanadin dan hutu da na fahimci ya samu, kuma sai naga yafi kyau a hakan, kuma halinsa ya canza wurin sanyi da sauk'in kai, amma nasan da dalili. Amma dai tabbas shine, tun da gashi mun tuna baya ma. Sai dai nasan komai yanayine sanadin kawu Sulaiman ne wanda ya nuna yana da muhimmanci a gareshi. _Ku biyo ni dai labari ba a soma ba ma tukun_. _Taku Zainab mazawaje_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe *NI DA GIDANA* *By* *Zainab Mazawaje* _Best brilliant interlligent writer_........🖋️ *Page 5* Nasan albarkacin kawu sulaiman naci na daga fuskar da na samu wurin malam Faiz. Zuciyata ce ta fad'amin. Fa'izu ya dubi kawu yace da Kawu na. "Zan tafi Sulaiman dare ya soma, don Allah goben ka fito da wuri, a yi training, kasan wannan wasan na farko ne sai mun nuna k'wazo fa." Cikin 'yar dariya Kawu na yace. " Babu ji Yarima. ai bamu da fargaba, tun da muna da champion irin'ka." "Kaji ka da wani zance. ni kad'ai ne zanji da komai? wato dani kuka dogara a nasarar ku ko?to kuwa wallahi zan kayar daku Ina sane." "Tuba muke Yarima, mun tuba mun bika, ayi afuwa". Yarda Kawu Sulaiman ke kwantar da kai, shi kuma Fa'izu ya sha mur serious babu kafar zai sauko, Sai dariya taso ta subcemin na kanne. Yana nan dai bai canza ba. Nace a raina. Nan dai na bar'su ni na koma wurin Usman. "Dan fodiyo, na jima ko? A yi hak'uri." Nace. Yace. "Gimbiya ai bata laifi. Yaya kuka yi da Yaya Sulaiman don Allah. Ina cikin fargaba." Nace"Karka damu, yace nan da Jibi zai yi magana da kakanni na zai yi maka magana" . Dad'i ya kasheshi a ranar, gani yake kamar yayi nasara. Ni kuwa tuni na fahimci Kawu na kamar bayason magana ta da Usman. Kai ban ma fahimci alk'iblar sa ba ma. Kamar bayason nayi aure a kusa ma, Sai nayi ilimi mai zurfi, amma fa zato nane. Koma hakan ne, nima burina ne dai. Amma Usman ne yake ban tausayi haka nan. Da daddare an kawo wuta, na d'auko caza ta zan saka wayata a caji, inda kawai Sai Ancle Fa'izu ya fad'omin a rai. Saboda shi ya had'omin da cazar, Sanda ya kawo min wayata da ya tsinta. gashi kuma a ranar yazo gidan namu. Zuciyata keta haskomin duk wasu a bubuwa na Fa'izu da suka wanzu tsakanina da shi. Na rasa kuma dalilin da hakan ya zauna min kuma a rai. Murmushin da yayi min da muka had'a idanu a bisa tsautsayi , yak'i sharewa daga cikin k'wak'walwa ta, duk da na tabbatar babu Wata manufa a zuciyar'sa game da hakan. Nayi kwance al'amarin farkon had'uwata da shi ya dawomin a hankali. Ga yarda a bin ya faru a tak'aice. Gidan k'anwar kakata naje wata Hajiya mariya, Wacce ita ta fara rainona bayan mutuwar mahaifiyata, kafin baba na ya rasu Shima. Bansan na yarda wayata bama, Sai da nazo gida, Ina kici kicin zaro canjin kud'ina zan yi aike, ga yaron aiken kuwa tsaye a gabana. To babu kud'I kuma babu wayar a babban zip d'in jakar, da bansan lokacin da suka zube bama. Dama jakar ta d'an farke Sai gani nayi ta yage ma sosai a she ban Sani ba. Nan nasan na rasa wayata a karo na biyu, domin ko wata biyu batayi da saye ba da kawuna ya sayamun Sabuwa bayan an sace waccan. Kuma mai tsada ce a kan waccan. Damuwa ta tayi nisa, a raina a ranar, saboda kar Kawu Sulaiman yace Ina da sakaci da rashin kulawa a kan abinda yasa k'ud'i ya saimin. Waccan an sace, wannan kuma nayar? ai bazai ji mutuwar sarki a bakina ba kuma. Ba kina naja na tsuke. Amma fa kullum a farga ba nake, kar ya ne mini a waya ya fahimci komai. Kwanaki hud'u tsakani Sai ga wata a miniyata mai suna Nuriyya.Muna hira nake fad'a mata b'atan wayata. Ta jajanta min. Nace. "Bani a ron wayarki ma na kira layin, duk da ban saka rai bama. Duniyar yanzu ba gaskiya. Masu tsoron cin haram ko rik'e haram, sun yi K'aranci. Da kud'i a wayar taki?". Tace. "Kinfi kowa sanin waya ta kullum cikin credit take, bata zama fanko, saboda Ina da masu yi mata hidima." Na warce wayar Ina cewa. "Allah ya shiryeki Nuriyya. Kullum baki da aiki Sai tatse samari, kuma ba auran su zakiyi ba, Wallahi kiyi hattara". "Na nawa kuma, wai ance da kuturu ka gama lafiya. Namiji ai yaso yaudarata, amma na nuna masa ni 'yar zamanice ai ni naci dubu Sai ceto, nafi gaban a washeni, domin murucin ni kan dutse ce ban fito ba Sai dana shirya. Ke dai ki jarraba Kiran ko kya dace, idan kina da rabo. A kwai na kirki a duniya." A ringin na uku, a ka d'auki wayar kuwa, bayan na k'agu da a d'aga. Muryar namiji a hankali naji tayi min sallama. Muryar bata da d'agawa irin ta maza. "Dawa nake magana?". Nace. "Sunana Sumayya..... Bai bari na k'arasa ba yace. "Ko zaki taimakeni Sumayya ki had'ani da mai layin wannan wayar da kika kira? Tsintar ta nayi a hanya zan wuce kwana ki hudu da suka wuce. Naji sanyin dad'i a raina nace"Wayar tawa ce wallahi yanzu ma kira nayi ko zan dace. Yace "Kin kuwa dace 'yammata. Zaman wayar ma a hannu na duk ya dameni, so nake na mik'ata ga mai ita Kawai. Don da na tsinta caji ma babu, Sai da na Sai mata caza Sabuwa na caza ko mai ita zai bugo, sai yau a kayi dace a ka bugo. Yaya za'ayi ki karb'a?". Nace. "Fad'amin in da zan sameka Sai nazo na amsa." Yace" Ba haka za'ayi ba, ke zaki kwatanta min in da kike nazo na kawo miki, dama fita zan yi. A wace unguwa kike?". Nace" Ina unguwar Doka". Yace. "Anya na tab'a Shiga unguwar nan?". "Kai ba d'an garin zariya bane?". Nace da shi. "Haifaffe ma kuwa. Yace da hanzari. Domin kana d'an gari ai baza'ace ko'ina kaje ba. Amma dai zan zo, idan na shigo unguwar Sai na tab'aki a layin da kika kira kiyi min jagora, kar na manta. Tare da a bokina suhail zamu zo, tun da shi idon gari ne. Amma ki tanadi ladan tsuntuwafa. Kinsan yanzu ba'ayin aikin da babu in come". "Ga zatona da gaske yake. Nace"Babu damuwa, zan bada idan babu yawa." Yace"Babu yawa ai. 'yar dubu goma ce kawai'. Fa'izu yace da Kawu na."Zan tafi Sulaiman dare ya soma, don Allah goben ka fito da wuri, a yi training, kasan wannan wasan na farko ne sai mun nuna k'wazo fa." Cikin 'yar dariya Kawu na yace" Babu ji Yarima. ai bamu da fargaba, tun da muna da champion irin'ka." "Kaji ka da wani zance. Ni kad'ai ne zanji da komai? Wato dani kuka dogara a nasarar Ku ko?to kuwa Wallahi zan kayar daku Ina sane." "Tuba muke Yarima, mun tuba mun bika, ayi afuwa. Yarda Kawu Sulaiman ke kwantar da kai, shi kuma Fa'izu ya Sha mur serious babu kafar Zai sauko, Sai dariya taso ta subcemin na kanne. Yana nan dai bai canza ba. Nace a raina. Nan dai na bar'su ni na koma wurin Usman. "Dan fodiyo, na jima ko? A yi hak'uri." Nace Yace"Gimbiya ai bata laifi. Yaya kuka yi da Yaya Sulaiman don Allah. Ina cikin fargaba." Nace"Karka damu, yace nan zai yi magana da kakanni na a sa lokacin da zaka turo, sai na fada maka. Dad'i ya kasheshi a ranar, gani yake kamar yayi nasara. Ni kuwa tuni na fahimci Kawu na kamar bayason magana ta da Usman. Kai ban ma fahimci alk'iblar sa ba ma. Kamar bayason nayi aure a kusa ma, Sai nayi ilimi mai zurfi, amma fa zato nane. Koma hakan ne, nima burina ne dai. Amma Usman ne yake ban tausayi haka nan. Da daddare an kawo wuta, na d'auko caza ta zan saka wayata a caji, inda Kawai Sai Ancle Fa'izu ya fad'omin a rai. Saboda shi ya had'omin da cazar, Sanda ya kawo min wayata da ya tsinta. gashi kuma a ranar yazo gidan namu. Zuciyata keta haskomin duk wasu a bubuwa na Fa'izu da suka wanzu tsakanina da shi. Na rasa kuma dalilin da hakan ya zauna min kuma a rai. Murmushin da yayi min da muka had'a idanu, yak'i sharewa daga cikin k'wak'walwa ta, duk da na tabbatar babu Wata manufa a zuciyar'sa game da hakan. Nayi kwance al'amarin farkon had'uwata da shi ya dawomin a hankali. Unguwa naje na yarda wayata bansani ba, a she kasan jakar ya yage. Na kasa fadawa kowa musamman kawuna da ya sai min kuma bata dade ba, nasan bazai ji dadi ba. Rannan kamar wasa Nuriyya kawata tazo nake fada mata, sai tace na kira a wayarta ko za a dace, tun da tana da lambata. Na kira babu musu amma bansa ka rai ba gaskiya, domin takai sati biyu da yarwa. A kira na farko a ka daga. Nayi sallama muryar namiji ce ta daga kiran, muryar ba ta da dagawa irin ta maza, ga dadin saurare. "Sunana Sumayya, .... Da sauri ya katseni. Ko zaki taimakeni Sumayya ki hadani da mai wayar nan, ta jima a wurina tsinta nayi z hanya". Nace " Ai tawa ce wayar, bugowa nayi ma ko zan dace na samu". Yace "Kin kuwa dace 'yammata, yaya zaayi ki karba". Nace " Ka kwatanta min in da kake sai nazo na karba". Yace "Ba haka ya dace ba, ni ya kamata nazo na kawo miki, a wace unguwa kike". Nace " Unguwar Doka". Yace "Anya na taba shiga unguwar nan". " kai ba dan garin zariya ba ne". Yace da sauri. "Haifaffe ma kuwa, domin kana dan gari ai ba dole bane a ce koina ka shiga, amma zanzo tare da abokina Suhail, dama zamu unguwa a babur din sa, shi idon garine nasan yasan unguwar, idan na shigo sai na kiraki a layin da kika kirani ki kwatanta min gidan, amma ki tanadi ladan tsuntuwa, domin ba a aikin da babu income yanzu". Nace"idan babu yawa baifi karfina ba zan bayar". "Ba yawa dubu goma sha biyarce kacal". Da sauri cikin mamaki nace " Dubu sha biyar? to daga nan na bar maka wayar mana, tunda ko sai da ita zaayi ba zatafi haka ba yanzu, tun da anyi amfani da ita". Ya sake yin wata 'yar gajeriyar dariya da ta k'ayatar da ni, banganshi ba, amma dai zuciyata sai haskomin hoton sa take, saboda tsadaddiyar muryace mai wani irin amon sanyi da dadi, da take kamancece niya da irin cikar surar mai ita. Kawai Ina jin a lokacin a cikin salo na raha yake sosai, domin barkwanci da raha basa cikin halayyar Fa'izu a sanina. "Bari nazo dai sai mu kashe maganar".Abinda yace kenan ya datse kiran kafin ma nayi. Nuriyya da tayi sararo tana jin mu ni da fa'izu, saboda hand's free nasa . Bayan na kashe wayar tace. " Kiji mu da Mutum. da har ina yabon'sa a zuci, ina kaga na Allah mutanen arziki, ta fad'a hannun Mutumin kirki,a she duk gayyar tsiyar ce . A bashi dubu goma kamar tasa ce zai bamu mu Saya?". Nace. "Ke dai rabu da shi, yazo tukun, muga gudun ruwan'sa. Nace a hankali domin tausarta. Cikin a binda baiga gaza a wa guda ba, Sai gasu sun kafe babur a kusa da k'ofar gidan mu da taimakon kwatancen da nayi musu a waya da suka shigo unguwar. Muna tsaye dama a k'ofar gida ni da Nuriyya. Samarin d'aya fari ne sosai, d'aya bak'i. Bak'in yafi sakin fuska da fara'a a garemu shima black beauty ne gaskiya. Bayan musayar gaisuwa, farin saurayin ya zura hannu cikin aljihu ya zaro waya gami da sabuwar caza ya mik'o mana. Ni na karb"a cike da godiya. Yace. "Sai ki kula, karki sake yarwa, domin ba lallaine ta dawo ba." Nayi mamakin canzawar sa kamar ba shine mai barkwanci a waya ba. Nuriyya tace da sauri. "Gaskiyane kam, domin ba domin mun yi dace da mutanen kirki irin ku ba, ai da tarasa kenan. Kuna da kirki da karimci gaskiya, don Allah yaya Sunayen Ku?" . Ni Kam naga Zak'ewarta, shi yasa nayi kasak'e ina kallon'ta. Wannan saurayin bak'in ,shi ya bata amsa. "Sunana Suhail labaran. Shi kuma sunan sa Fa'izu Bukar". "Kai Amma Sunayenku suna da dad'i, kamar na larabawa? a wace unguwa kuke ne? ". Nan naga mai suna Fa'iz d'in ya jefeta da wani irin kallo a sakarce, dake nunin ta isheshi da Surutu. Ni kuwa dama tuni ta k'ular dani na irin wannan shishshigi. Su ya dace su nememu da hakan, ba suyi ba, Sai mu mata? domin kawai ta zubar mana da daraja?. Tuni dama na fuskanci wannan Fa'izun d'an ji da kaine da fad'in rai. Tun daga Maganar farko bai sake cewa komai ba. Ko kallon mu bai sake yi ba, Sai da Nuriyya ta Shiga k'wak'ulen tambaya ga a bokin'sa ya waigeta sau d'aya, kallo ma na raini. "Zo nu tafi Suhail, kasan sauri muke yi, kuma ba jiran mu zasu yi ba". Inji Fa'izun. Inda ya ce masa "To" . Amma bai motsaba, saboda Nuriyya da ya soma yiwa kwatancen in da suke dalla, dalla. Bai yi nisan ma da zata gane sosai ba Fa'izun ya sake cewa. "Idan ba zaka zo mu tafi ba, ni kaga tafiyata. Bazan jiraka ba wallahi idan ka tsaya, ka taho daga baya." Faiz Ya dubeni yace. "Sai anjima." Nace. "Na gode, Allah ya saka da khairan." "Amin.". Yace bayan ya soma tafiya. Ganin haka Shima Suhail d'in yayi gaggawar binsa saboda ya fuskanci tafiya zai yi ya barshi, bayan babur guda suka zo kuma. Bai k'arasa yiwa Nuriyya kwatance ba dai ya tafi. "Gayun nan sunyi a rayuwa. Musamman ma farin, Fa"iz.Sai dai naga d'an girman kaine da nuna isa , d'an hana ruwa kuma gudu, abokin'sa ya fishi kirki. Yanason a k'ulla zumunci ya hana.Ya bani haushi fa!". Nace".Naji dad'in a binda yayi Miki, haka Kawai daga had'uwar k'addara Sai ki Zak'alk'ale? Wannan halin zub da ajine Nuriyya. Nayi mata tatas, tayi lub. Amma fa an d'auki lokaci in dai mun had'u Sai tatada Zancen wai taji ciwon rabuwar mu da su babu a direshi. Rannan kuma muna hira tacemin. "Kinsan me Zuciyata ta ayyanomin yanzu?" "Ta ina zan Sani,baki fad'iba.". Nace da ita. Tace"Zuciyata ke sak'amin, Ina ma ina cikin tafiya, na had'u da miskilin gayen nan, ai ko bai kulani ba naci riba." Nace. "Kin Shiga uku Nuriyya." Tace"A wani dalilin zaki kiramin musifa". Nace "Ai kuwa kin shiga cikin ta yanzu, tayaya za ki kwallafa rai da mutumin da ko kallo baki ishe shiba? dama daya hand some din guy bakin kike so, sai ince dan dama dama, don zai iya sauraronki ko baya sonki, saboda naga yana da saukin kai shi gaskiya. Ke ruwa ma ba saan kwando bane gaskiya daga yanayin ganin samarin nan kinsan ma ba saan nin yi ki ba ne, sun kuma kama dahir, kawai kisa hakuri". Ta harareni kawai taja tsaki. Nayi zaton za ta kuma tankawa na kare mata tanadi, sai tayi shiru. Domin gaskiya haushin yarda take zubar da aji nake, gashi sun nuna mata a aikace na ba ma gabansu, amma ta rufe ido ta kulle tunani, wai bata dau haske ba, saboda son zuciya kawai. Kunji wannan. Daga bakin alkalamin....🖋️ Zainab mazawaje muje zuwa Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe *NI DA GIDANA* *By* _Zainab mazawaje_ _Best brilliant interlligent writer_..... 🖋️ *page 6* Tun daga lokacin na fahimci Nuriyya kamar tayi fushi da furucin da nayi, don naga bata kuma dauko min zancen ba, a raina nace ya dai fiye miki hakan, kisan ciwon kan ki da mutuncin kan ki gaskiya. Daga lokacin, na samu lafiya ta dai na yi min Zancen, amma bansan cikin Zuciyarta ba ko tana sak'awa. A daren ranar dai Alhaji Rabi'u yazo ya matsamin lamba na sai na bashi dama ya turo iyayen'sa Yasan matsayin'sa. Sayayya fal yayi min kuma. Yace ya kuma gaji, ko yin ko bari yana son sani. Nace ya bari, zanyi magana da kawuna. Kafin ma na fad'awa Kawu Sulaiman, da Nuriyya k'awata tazo, ta rikirkita min lissafi. "Wallahi ni nafi miki Sha'awar Alhaji Rabi'u domin yafi Usman kud'i . Alhaji Rabi'u yafi Usman shekaru da gwagwarmayar sanin wahalar aure da juriya da sanin darajar iyali. Kefa kika ce zaune yake da matarsa lafiya, gashi kince yana yabon matar Sama. Mai wannan ai Sai namiji na gari. Shi kuwa Usman baki da misali a kansa da zaki samu tabbas, Sai kin Shiga zaki gani. Kuma kin tab'a cemin kin tsani kiyi aure ki fito a rayuwarki, ba kyason zawarci ko aure sau biyu. Tun da haka ne, dole kiyi taka tsantsan wurin aure, kar Kibi son zuciya. Tun da su duka sun yarda da karatunki da aiki da zakiyi to kar kibar Alhaji Rabi'u, shi ya dace dake. Kinsan maza irin su manya suka auri budurwa, ba k'aramin tarairayarta suke ba da nuna mata soyayya." Na Shiga rud"ani, domin cikin maganganun'ta a Kwai a bin dubawa ko ba du ba. Bata gushe da yi min hud'uba ba, Sai da ta cusamin auren Alhaji Rabi'u, naji shid'in kawai zan aura. Shi yasa banji fargabar sake tunkarar Kawu Sulaiman da Zancen ba, duk da nafa kai masa zancen Usman yace na saurare shi. Idona ya rufe. dubana yayi cikin 'yar fusata. "Wai ke Sumayya me kike nufine? Maza biyu za ki aura, ko menene k'udurin'ki?" Na duk'ar da kai zan soma magana ya katse. "Fad'amin wakike so da Gaskiya,Alhaji Rabi'u ko Usmanu?". "Alhaji Rabi'u." Nace. Jinayi gaba d'aya ya k'aryatani. "K'arya kike yi, Shima ba son'sa kike yi ba." Ni kuwa nace me zanyi, idan ba kallon'sa ba. "Tun da kika tsaya ruwan idanu tsakanin Alhaji Rabi'u da usman, ya nuna su duka ba wani so na hak'ika kike musu ba. So guda d'aya ne tak! Kuma ba'a yin ruwan ido a cikin'sa. Da kina son Usman, ba zaki dawo daga baya kice Alhaji Rabi'u kike so ba. Kuma da Alhaji Rabi'u kike so, tun farko shi zaki zab'a. Nafi zargin cusa miki ra'ayin'sa a kayi. Ya sauke numfashi a hankali, ya dubeni. "Bazaki auri d'aya daga cikin'suba, domin duk basu dace dake ba. Wanda ya dace dake a dabi'ance zai zo nan kurkusa in Sha'Allah. Zaizo, kuma kafin yazo zaki ga alama ta sanarwa ko nuni na hannunka mai sanda kam idanu na zuba masa kawai. Cike da Mamaki na dubi Kawu, amma kaina ya d'aure ban fassaro komai ba, a fuskarsa ko a kalamun'sa. "Zan sallami Usman da Alhaji Rabi'u da kaina. Babu ke babu su, ko a hanya, kinji na fad'a Miki. Na sake jadda da Miki, ko ki yarda ko karki yarda basu dace dake ba. Bayan ba son'su kike ba, kuma bani da garanti a kan'su. A ido kawai nake ganin'su, tunda babu wata huld'a da take Shiga tsakanina da su. Ina so ki darje Miji Sumayya ko domin maraicinki kinji." Sam banji dad'in hukuncin da Kawu ya zartar ba, don dai yafi gaban nayi jayayya da shine, matsayin sa ya wuci nan nesa. Amma na k'alubalanci tunanin'sa. Usman da Alhaji Rabi'u duk babu na yadawa wurin yabo. Sun Sha d'awainiya dani da Zaman jirana na shekaru, amma tashi d'aya a koresu? da wani ido zan kallesu? Wani zargi zasu yi min? ta ina zan maida irin'su? Wani lokaci kuma zan d'auka Zaman jiran wanda zai dace dani a d'abiance, bayan shi hali ba'a goshi yake ba da za'a gani a tabbatar. Abin a lullub'e yake. Addu'a ce kawai na tabbatar za tayi jagora Ta ina zan lalubo wanda ya dace dani, amma ba hasashe, ko zato ba. Na Shiga damuwa har wayewar gari, amma ban bari kawu ya fahimta ba, saboda ina jin nauyi da kunyar yasan hakan. Domin bani da kamar sa a duniya. Bana iya had'a kaunar'sa da ta kowa. Abinda yayi min a rayuwa, cikin family d'ina kaf babu Wanda yayi min rabi rabin'sa. Ya cancanta da nayi masa biyayya a komai da bai wuce k'a'ida ba, wato haramun. Da wannan dalili nayi ta jinyar damuwar Zuciyata a b'oye Ina had'awa da addu'a har komai ya sassauta a raina. Ban sake fita zance wurin Usman ko Alhaji Rabi'u ba. Sun dai daina zuwa, bayan d'ayansu kowan ne da yazo sau d'aya Kawuna Sulaiman yaje ya gana dashi. Bansan yaya suka k'arke ba. Ni dai nasan, duk Sanda tsautsayi ya had'oni da su a hanya, zan sha kunya, kamar na nutse. Bana fatan zuwan wannan rana ni Sumayya. Bayan watanni har biyar da korar Usman da Alhaji Rabi'u, hak'urina ya soma gazawa saboda Wata uku da suka wuce a ka soma gwab'amin da Zancen aure. Wai naki aure, duk sa'oina suna d'aki da yara d'aya ko biyu . Wai na fake da karatu. a Kawu na a ke jefa k'orafin, Wai shi ya huremin kunne na tsiri karatu domin kar nayi aure nayi nisa da shi. Saboda kowa ya lura da irin k'aunar da yake nunamin. Kuma a binda ya jawo matsalar, duk cikin dangin iyayena na kusa babu mai karatun jami'a mace. Kakana ma Sai da ya gwab'amin magana cikin hirar wasa yace, Wai na kusayin kwantai, saboda na tsaya ruwan ido da buri. Kakata Hajiya Mariya ita kullum naje k'orafin Kenan na aure. Itama kan Kawu Sulaiman ta d'ora laifin. Wani lokacin Hajiya Mariya fushi take yi sosai har takance. "To ya jik'aki ya shanye mana, tun da bayason kiyi aure. Na kan sake kunnata nace" Tsohuwar nan kin fiye rigima. Kinci zamani irin naki, ki barmu muma muci irin namu Mana, kai fa ya waye yanzu, karatu a ke fara zurfafawa kafin aure. To nan fa Sai ta balbaleni da fad'a har korata ma take yi tace kar na k'ara zuwa mata gida. Amma Sai na koma. Baza'a rabu ba Sai mun kuma yin fad'an. Sai dai idan bata matsamin da zancen aure ba. To ban san me zasu ce ba ko zasu yi kuma, idan suka San ya kori masu zuwa neman aure na. Duk da hukuncin nasa Sam bai min dad'i ba nima, bazan iya suka ko tona komai na Kawuna saboda bana so aga laifinsa. . Ina tsananin k'aunar sa, bazan iya b'ata masa ba Ina sane. Maganganun sun dameni lokacin da Usman ya aikomin da wasik'a a ciki yace wai naci a manar sa Ina sane, nasan wani za'a bani amma nayi masa alk'awarin aure. Ban ko bashi amsa ba na rabu da shi, saboda nasan kome zan fad'a masa bazai yarda ba. Alhaji Rabi'u kuwa, ban sake jin d'uriyar'sa ba shi. Rannan Ina zaune a tsakar gida, Baba Talatu ta tafi unguwa. Ranar bani da karatu, a hutu muke. Komai ni nake yi dama in dai Ina gida, kuma ni nake sa kaina, bawai Baba Talatu ke cewa nayi ba. In dai ta ita ne wanke wanke Kawai zanyi da sharar tsakar gida. Na gama komai, Ina zaune, Kawu Sulaiman ya shigo, ya sameni zaune nayi shiru . Ya jawo kujerar k'arfe da Baban'sa yake zama, ya zauna gabana d'an daura dani. "Sumayya a Kwai wani a bu da zakiyi yanzu?" Nace"Babu Ancle. Sai girkin dare, kuma Sai yamma sosai zan d'ora,tun da mai sauk'ine.Wannan damar nake jira da baki komai, kuma babu kowa Mu tattauna Wata magana dake. Kisa Nutsuwar nan taki da nasan ki da ita ki saurareni, ki kuma fahimceni 'yata". Kafin nan zan baki wani d'an labari da zai zama shine sharar fage,na a binda zamu tattauna." "Kinsan ai Yarima ko? . Na dubeshi da hanzari, Sai ya zarce da cewa. Ko daya ke, Kinfi ganeshi da Fa'izu. Zan baki labarin'sa a tak'aice, bazan b'oye Miki komai ba, saboda gaskiya da gaskiya ce za'suyi aiki. Yarima haifaffen garin nan ne, amma a salin'su 'yan maiduguri ne. Mahaifiyarsa sunan'ta Suwaida. Kuma k'abilar shuwa Arab ce . Baban'sa kuma babarbare ne, sunan'sa Alhaji Bukar, amma asalin'sa bafulatani ne na sokoto. K'annen Fa'izu uku, biyu mata Sai namiji dake bi masa Khalifa. Tsiran'sa da Khalifa,shekaru uku yace min. Bad'an masu kud'i bane Yarima, ba kuma talakawa bane can. Sai sa Sai sa. Amma dai yawancin d'awainiyar gidan Yarima keyi, musamman na kannensa mata Yarima d'an boll ne sosai, domin kuwa makarantar school a cadamic yayi dake cikin k'asar Ghana kuma cikin birnin Ghana ACCRA. Suna koyar da boll ne da karatu. Tun tashin Fa'izu da son buga k'wallo ya taso, tun yana k'arami, har girman'sa. Ya kuma samu sa'a a cikin harkar, ko nace yana kan samu. Iya boll d'insa yasa wani a gent dake hayowa 'Yan club a turai k'wararrun 'yan boll, yace zai kai shi spen wurin 'yan club d'in bacelona, ko real Madrid dake k'asar turan ta spen su sayeshi. Saboda ya iya boll sosai Sumayya. Duk fita Sai yaci mana cup. Lamba sha d'aya yake bugawa, Kinsan sune 'yan gaba, amfi ji dasu. Da yawa ma club Sukan gayyaceshi ya buga musu boll idan za'su gasa. To sai yasa kan'sa dai yake zuwa, Kinsan halin Mutumin. Yayi harkar teaching na wani lokaci da yasa kan'sa. Amma fa ya watsar yanzu, saboda harkar boll tasha masa kai, kullum Samun ci gaba yake yi a cikin'ta. Burin Fa'izu tafiya spen kawai, amma har hanzu egent d'in dai bai nemeshi ba." Ni kuwa na kada baki nace. Ancle, mai yasa sai yaje wata k'asa?". Yayi a garin'su mana." Yayi 'Yar dariya. "Sumayya ai fitar sa k'asar turai shine ribar wahalar buga boll d'insa. Domin kuwa can ne ake Samun kud'i na fitar hankali. Kinsan idan ya taki wannan sa'a ya tsallake tudun mun tsira kuwa? Ko kinsan a kwai d'an boll d'in da yake d'aukar miliyan talatin duk Sati a k'asar turai?" Nace cikin rik'e baki a rud'e. "Duk Sati Ancle?". "Sosai kuwa. A Kwai mai d'aukar Sama da haka Sumayya. Nan ma a na Samun k'ud'in musamman idan club ya shahara, amma ko kusa baza'a had'a shi da k'asar turai ba Kinsan yawancin kud'in ma daga wurin 'yan kallo a ke Samun yawan kud'in, to can turai, Mutum d'aya kika ji kud'in da zai biya ya Shiga kallon gasar k'wallo Sai ki rik'e baki. To Mutum miliyan nawa, ko Mutum d'ari nawa zasu Shiga kallon gasar boll na wata wata na kasa kasa, na cub club ke karawa da juna. Bari dai mubar Maganar boll, muyi wacce a kanta za muyi magana. Yarima yana da Wata budurwa da suke matuk'ar son juna mai suna Salima. Tana da kyau wai ainun, a fad'in a bokin Yarima na hannun dama mai suna Hashim. Ni dai ban tab"a ganin'ta ba, Sai jin labari. Mak'otan mune, suna zaune a Kaduna, cikin unguwar sarki. Mahaifiyar Salima attajira ce, domin business take na saro furnitures daga k'asashen waje. Sun rabu da Mahaifin Salima, ta sake wani auren wani attajiri a unguwar malali. Amma Salima tana gaban'ta. Ita kad'aice 'yarta a duniya, tana son'ta kamar rai. Salima tana da tarin masoya da yawa 'ya'yan attajiran gaske, amma Yarima take so kadai, kuma tasan wanene shi.Sun had'u da fa'izu a heal's and Bally da sallah. Shekarar su biyar Kenan suna soyayya.Wannan Shekarar Salima ta soma bautar k'asa. Maganar auren'ta ta taso, tace bata son kowa Sai Yarima. Mahaifiyar'ta ta nemi ganawa da Yarima. Bayan gaisuwa tace masa me yayi tanadi, game da auren 'yarta tun da yasan 'yarta ba gama garin 'yammata ba ce. Bai b'oye mata komai ba na matsayin'sa da kuma a binda yake yi, amma yace yana da wani buri da yake so ya cimma. Kuma in dai ya cimmasa to komai da take so zai yiyu, amma yanzu haka bashi da wani shiri irin Wanda take nufi. Yace yana da dai dai arzik'insa Wanda zai iya rik'e mace. Sannan gini yake yi ma yanzu ko rabi bai kaiba. Nan Sai ce masa tayi. "Haba Fa'izu! yaushe zamu saka rai da a binda bashi da tabbas? Wayasan San'da wannan buri naka ma zai cika. K'arshe Salima tayi aure har tayi haife haife burin bai cika ba. Nama tabbatar Sai ta rigaka aure. Kai da kan'ka kasan Salima ba matar talaka bace, ko a talaucin ta taso, ballan'ta na ta taso, gidan iko. K'warya ai 'yar uwarta take bi, domin idan tabi a kushi kunya zata sha." Yarima baya barin ta kwana, da anyi masa zai mai da raddi. Yace "Mama, ai ita k'waryar tasan da 'yar uwarta, amma Sai ta zab'i bin a kushi. Kenan ita taso taji kunyar. Salima ita ta fara nuna muradin'ta a kaina, duk da tasan wanene ni, me nake dashi. Daga k'ulla a bota da mutunci farkon had'uwa ta mai dashi soyayya. Bazan b'oye ba, wallahI, tun da na had'u da 'yarki mama ta Shiga raina sosai. Amma banyi a zarbabin nuna mata ba, Sai da ta fara. Kinga kuwa 'yarki ta rakito miki ni. Kuma burin mutum, ubangiji ke cika masa a Sanda duk yaso. Babu kusa kuma babu nesa. Saboda haka a kowani lokaci, ban fitar da ran cikar burina ba. Kuma bana gaggawa, na barwa mahalicci na ikon'sa a kaina. Salima kuma Ina mai tabbatar miki bazata rigani aure ba, saboda nasan duk runtsi bazata iya auren Wanda ba ta so ba. Duk tsayin shekaru nasan Sai ta jirani, da ta auri wanda bata so. Kinfi ni iko da 'yarki, amma nafiki kusanci da sirrikan dake zuciyarta. Babu a binda take b'oyemin. Ba kuma zan iya jiran Salima ba, saboda burin da aka ci mata. Zan yi aure a kurkusa, saboda addini mata hud''u ya halattamin. Zan auro dai dai dani a arzik'I. Ban kuma bar Salima ba,zan aure ta idan damar hakan ta samu a gareni duk jimawa. Bata da laifi, kuma nasan tana Sona. Wannan shine uzurin da yasa zan aure ta. Ba domin haka ba, to Wallahi da na barta Kenan har a bada. Domin bana waiwaye idan nayi gaba in dai aka nunamin iyaka ta, a kan komeye." Daga haka sallama yayi mata yayi gaba. Bai jira ma me zata ce ba. Amma ya lura maganganun'sa sun kad'ata." Kawu Sulaiman bai dad'a ba, bai raga ba, Sai ga kakana ya shigo, wato Mahaifin'sa. Da sauri Kawu Sulaiman ya karb'i jakar da take hannun'sa, ni kuma na karb'a daga hannun Ancle. Ya dubemu yace. "Hira kuke kai da 'yar taka?". Yace"Eh! Baba. Wata magana muke tattaunawa". Yace. "Zan kuwa katse muku hanzari kwa k'arasa daga baya. Wata unguwa nake so ka kaini Sulaiman ta gaida mara lafiya. Dan babban a Minina a ka kwantar a asibiti saurayi babu yarda yake. Ai baburin'ka lafiya yake ko?" Kawu yace. "Ai na gyarashi Baba. Dama matsalar kafireto ne". Yace" To, Muje ka ka kaini. Nan hirar tamu ta datse. Ni kuwa na k'agu naji yarda al'amarin ya Kaya. Da kuma Maganar da Kawu Sulaiman yace za muyi ta musamman. Kwana biyu ne rak tsakani , muka sake Samun sakewar ci gaba da hirar Yarima, wato Fa'izu Bukar. Baba Talatu tana d'akin Baba, wato kakana bayan kai masa bincin dare suna tasu hirar suma. Kawu Sulaiman Yaci gaba da cemin. "Sumayya Yarima yana buk'atar aure a kurkusa, domin yace Sai ya d'au fansa. Sai ya maida martani. Yaci alwashin, Sai maman Salima tazo tana rok'on'sa ya auri Salima, kuma Sai ya garata sosai. Yace Sai ta aza kwandon dana Sani a kan'ta tayi yawo dashi ta gaji." "Idan na fahimci dai dai, auren huce takaici Ancle Fa'iz yake so yayi?". Injini "Haka ne, Sumayya". Na sake cewa. "Ancle har Yaushe zai samu Wacce yake so cikin gaggawa yayi auren." "Kawu yace"Maganar a ce Sai ya samu wacce yake so bata taso ba Sumayya . Karki manta fa Yarima wato Fa'izu a cikin soyayya yake bai fita ba. Bai daina son Salima bafa, suna tare har yanzu. Amma bai fad'a mata a binda maman'ta tayi masa ba. Yasan kuma bata Sani ba. Yace ko Salimar bazata San zai yi aure ba, Sai ya basu katin gayyata". Nace. "Amma dai zai tashi hankalin Salima Gaskiya.Zai kid'imata ainun. Daga Sama fa zataji komai, bayan yasan suna son juna." Kawu na yayi murmushi. "Ai hakan shine muradin'sa. Mahaifiyar Salima tana mugun son'ta kamar rai. Idan kuwa hankalin Salima ya tashi, ta Shiga tashin hankalin da bata tab'a zato ba, to fa neman a gaji maman nata zata tafi na ceton 'yarta. Kuma dole Sai wurin Yarima". Kawu Sulaiman yasa Wata siririyar dariya. "Yarima yasan takan tsiya". Ni kuwa jagale nayi Ina kallon'sa. Yaci gaba da cewa. "Satin da ya wuce, na sameshi wurin training. Bayan ya gama nace masa me a ke cikine yanzu.yace min har yau bai nutsu wurin Samun wacce zai aura ba. Yace yanason yarinya mai hak'uri da hankali da addini ba Ballagaza ba. Domin Sai da mai irin wannan kyawun halin zai cimma manufar'sa ta a binda ya himmata cikin nasara. Amma wai a bokan'sa suna ta kawo masa tayin mata da suke ganin sun isa a sosu, bai je ya gan'su ba. Kuma ana ta kawo masa hotunan 'yammata kyawawa a cewar'su. Hotunan yace baisan a dadi ba, tun da ko bud'awa ma bai yi ya gaggan'suba. Na tambaye shi me yasa. Yace shi ganin hoton mace bazai gamsar da shi da komai ba. Ya ganta a zahiri, yayi kuma hira da ita, tanan zai san ta can can'ta. Nace masa, yanzu idan aka kawo maka ita kaga tayi zaka aura? Yace min. Maganar wai a ce tayi min ma, baya cikin tsarina, kuma bana kwad'ayin hakan, saboda nasan ba za ta tab'a yi min d'in ba ne. Sai dai Kawai na aureta saboda wad'ancan halayya idan na tabbatar tana da su. Kawu Sulaiman ya dubeni sosai yace. "Sumayya kin yarda dani?" . N'a gyad'a kai, cike da mamakin furutan'sa. "Na yarda da kai fiye da kowa Ancle." "Akwai Abinda zan umarceki kika sayi min Sumayya?" Nace"Sai Sab'on mahalicci dai?". Yace"To, Sumayya Ina so ki auri Fa'izu, wato Yarima." Na kad'u k'warai da jin furutan'sa, na kuma gaza cewa komai Sai sunkuyar da kai. "Yarima ya bani zab'in na samo masa irin Wacce yake nema in dai Ina da iko. Ni kuma ke Zuciyata ta halarto min, kina da irin wad'annan d'abi'u, kuma ke kad'aice a bar iko na a du,cniyar nan. Kina da irin wad'an nan d'abi'u da Yarima ya zayyano, har ma da k'arin wasu kyawawan da bai Sani ba. Ke kika dace da auren Irina Yarima, Amma ke da shi baku Sani ba. Kuma nasan ko kun Sani, bazaku yarda cewa kun dace da juna ba a d'abian'ce tun da kowa a bai bai yake kallon d'an uwan'sa. Kiyimin alfarma Sumayya ki a mince da auren Yarima. A Kwai dalilai da yawa da fa'idodin hakan, amma sai kin fara amincewa za kiji su daga baya". _Tofa_! Muje dai zuwa... *Daga alkalamin*...... 🖋️ Zainab mazawaje Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe *NI DA GIDANA* _Zainab Mazawaje_ _Best brilliaant interlligent write_..... 🖋️ *page 7* Jikina yayi sanyi, na lalubo k'arfin hali nace. "Ancle bani da Uban da ya fika yanzu. Zaka iya zartar ma da hukunci a kaina a duk san'da kaso, ko bansa ni ba. Amma idan kafiso kaji daga bakina ne, to na amince". Sai da na daure iya dauriya domin farantawa wanda ya fikowa so'na da son farin ciki na, amma ba domin raina na yana son auren Yarima ba. Auren da na tabbatar bazan tsinci ribar komai a cikin'sa ba, face k'ask'anci, bayan rashin rabauta da soyayya irin wacce nake buri a aure, nasan Fa'izu da murd'ad'd'en halin'sa,mai iyawa da shi bazance babu ba, amma sai wacce taci hak'uri ta tada kai dashi, har tayi guzuri. Ma'ana mai hak'urin gaske. Kawu ya cika da farin ciki mara misaltuwa game da a mincewa ta. Albarka kuwa nashata kwando kwando. Na kasa danne amma tambayoyin da suke tayi min zallo a zuciya ta nace. "Kawu, Ancle Fa'iz fa ya sanni tsayin zamani, bai nuna yana da muradin irina bafa". Yace"Na fiki sanin haka." Ganin bai d'ora ba kan haka na sake cewa. "Na Sani, kuma kai ma ka Sani Ancle Fa'izu baya sona, kuma nasan bazai tab'a Sona ba." A cewar Ancle. "Na yarda yanzu kam baya son'ki.Saboda bashi ya nuna ma muradi a kan'ki ba. Bai kuma halarto kima cikin macen da zai yi auren huce takaici ba. Amma hakan bashi yake nunin bazai tab'a sonki ba. Ko bai soki yanzu ba , zai iya son'ki nan gaba. Idan kuma bai so kin'ba to bazai wulak'antaki ba Sumayya. Saboda kina da d'abi'u irin na mata na gari. Kuma irin'su basa tozar'ta a gidan aure. Yaja dogon numfashi. Ki kwantar hankalinki. auren'ki da shi ba lallai bane. Jarraba sa'a ta zanyi na k'oK'arin had'a auren ki da shi, saboda Sha'awar hakan, da ganin dacewar hakan. Yarima kaifi d'aya ne. bashi da shayi, ko jin nauyi na b'oye a binda ke cikin zuciyar'sa. zai iya cewa ya amince da aurenki, zai kuma iya cewa Sam bai a mince ba. Saboda haka ki tsaya a k'ila wa k'ala." Jin haka na d'an samu nutsuwa. Dabara ta fad'omin. Daren Ranar ko bacci ban samu ba ko na awa d'aya. Addu'oi nayi tayi da nafilfili kan aure na da Ancle Fa'izu kar yayiyu. Rashin yiyuwar dai yace baya ra'ayin Sumayya a aure. Da wannsn niyyar nayi ta addu'a. Nasan cewa Anle Fa'izu yafi gaban a ce ba'a son'sa. Amma Ina! nasan ko kusa ba zamu dai dai ta bane. Saboda irin sanin halin'sa da nayi lokacin da yana koyar damu, ko yana son mace ba za ta iya da baudadden halin sa ba, ballantana ba ya sonta. Ni burina nayi auren soyayya mai dad'i da kwanciyar hankali, kuma d'orarre. Ta ya ya kuwa zuciyata zata so irin wannan aure? ai daraja kan daraja irin ta Kawu Sulaiman Kawai zan yarda na aureshi, duk da nasan makomar bazata yi min kyau ba. Amma duk da haka bazan iya bad'awa kawuna k'asa a idanu ba. Bazan iya ba. Na had'a Kayan miya ina sauri zan markad'a a blender, saboda kar su d'auke wutar. Kawu Sulaiman na gani ya shigo kichean, da ba sabon'sa ba ne.shi yasa na cika da mamaki na sararo ina kallonsa kafin nace. "Sannu da zuwa my Ancle." Cike da wani farin ciki da bansan musabbabin'sa ba yace. "Sannunki da aiki shalelen Ancle. Kin ganni har tsakar kichean ko?". Kafin na samu amsar bashi ya zarce. "Sumayya Yarima ya amince da auren'ki. Abinda bani da tabbas d'in yiyuwar'sa, Yarima ya tabbatar min." Gabana ne nidai ya bada ras! addu'ar da nayi bata Shiga ba kenan? Sai na soma istigfari a zuci, saboda addu'a ai bata fad'uwa k'asa banza, nasan sai dai in kaddara tace ta dole tasai na auri ya tozarta ni ba yarda zan yi, sai dai daga baya Allah ya kawo min sassauci da mafita kawai. Cikin uku kuma na abinda mutum ya roka a addua za'a rabauta da abu d'aya dole cikin ni'imomin Uban giji. Tayi yu ni Allah ta wani gefen ya bani. Jikina sanyaye na dubi kawuna da bakin'sa yak'i rufo saboda farin ciki. A karo na farko naji farin cikin daya nuna ya sosa min ma rai. Sai kace Wacce zata auri wani Mutum na musamman da ya zama abin wasoso wurin kirki? amma basarwa nayi, na d'an kau da kai nuna alamun kunya, kar ya fahimci halin da nake ciki. K'arshe yace "Yarima yana Kano, ma a waya mu kayi magana. Ya tafi buga boll da club d'in heart land da suka gayyace shi. Amma nan da kwana uku zai dawo.zai zo wurin'ki ku tattauna". Har ya Fice ban iya cewa da shi komai ba. Tun daga ranar na soma yiwa kaina jaje, tun da babu mai min. Tawa ta sameni. Auren Ancle Fa'izu ni wurina jarraba ce mai Zaman kan'ta. 'Yan mata da yawan gaske nasan za'su so auran Yariman kawuna, ko da kuwa a shirin wasa ne. Amma ni koda wasan ba na fata. Ban tab'a zaton zai a mince da aure na ba, duk da auren son zuciya zai yi. Wato babu niyya har zuci, Sai domin ya cimma wata manufa. Ko shakka, Ancle Fa'iz a minin Kawu na bashi da tabbas. Nasa rai kacokam da bazai yarda da aure na ba,Sai gashi ya a mince babu musu.kuma yarda nayi imani zan mutu haka nayi imanin babu ko digon sona a zuciyarsa, kawai domin ya cimma manufarsa ne. Suna tare da kawu Sulaiman a d'akin sa da daddare, ranar da ya soma zuwa zance wurina ban Sani ba, Sai da Kawu Sulaiman ya shigo gida yace na kimtsa nazo ga Yarima yazo yana d'akin'sa. Ba wani wahalallen shiri nayi ba, kadaran kadahan, saboda nasan kome nayi ba burgeshi zan yi ba. Na Shiga d'akin Kawu Sulaiman da yake bude da sallama, Ancle Fa'iz ya amsa, gami da cire kai sau guda ya dubeni, ya sunkuyar. Na ajiye tire dake d'auke da drink's mai sanyi da snack's da Kawu yace na kai masa. Na gaisheshi a mutunce, da girmamawa, na nemi kujerar dake fuskantar tasa na zauna. K'amshin turaren'sa mai sanya zuciya shauk'I, Sai tashi yake sannu sannu, shi yasa banajin nawa ma. Kallo guda nayi masa nima na kasa k'ara na biyu. Baki d'aya Sai na raina kaina. Shadda yasa pink colour mai duhu, da tayi masa kyau iyaka. Abinka da fari. Ancle Fa'izu mai nak'altar iya kwatance yayi tsararo ya iya misaltamaka cikar surar kyawun'sa cikin sauk'i, ko yayin to sai ya rage. Sai ka ganshi zaka tabbatar da hakan. "Sumayya, kinji komai daga bakin Sulaiman ko?". Da sauri ya furta . Nace "Eh!". Ya zarce"Sulaiman ba komai ya fad'a Miki ba, saboda ba komai na fad'a masa ba. Dalili, ni dake komai ya shafa da za muyi auren. Yace min, ya nemi yardar ki, kin amince zaki aure ni,shi yasa nima na amince nan da nan.. Bazan b'oye miki komai ba Sumayya. Ni ban iya boye boye ba, ko rufa rufa ko b'oye gaskiyar a binda ke zuciya ta. Ina so gaskiya da a Mana suyi Mana jagora sumayya. Nasan kuma kinyi niyyar taimakamin, tun da Kinsan me ya tursasani yin auren gaggawa irin wannan. Sumayya! Yace cikin kafeni da idanun nasa ma'abota kyau da fari masu launin shud'i shud'i. Kasa iya had'a idanu nayi dashi,sai amsawa. "Kiyi hak'uri da jin a binda zai fito daga bakina. Dole na tsage miki Gaskiya. Aure na dake na wucin gadi ne. Kinga ne ai". yace cikin d'aga bak'ar girar sa. A razane na dubeshi, batare da na niyyata ba. Auren wucin gadi, na nufin aure na zai yi na wani d'an lokaci ya rabu dani. Zuciyata ta tunasar min. Na jinjina kai a hankali, cikin jinjina kalaman'sa. Duk da na zargi auren da zai yi da auren manufa, ban kawo wannan niyyata sa ba. Amma ta yaya ma zan jefa kaina cikin wannsn rigimar da Zai iya janyo min zargin mutane, domin biyan bukatar kan sa shi kadai? Sam bazai yiyu ba, da sake. Ya d'aga kai yana mai kallon idanu na, da nak'i yarda mu had'a ido tun da nazo. Ko kallon'sa zan yi a sace ne. "Salima, ita kad'aice d'iya macen, da na tab'aso a rayuwa ta. Kuma har gobe, ita nakeso. Kuma a k'ok'arina na na sameta ne, ta hanyar rama a binda a kayi min na shirya wannan auren bakatatan. Ta yiyu kema kina da wanda kike so ko?". Ya zama lazim, nace masa Ina da wanda nake so, kar ya d'aukeni, wata kara zube, tun da gashi Shima Sai zuzuta son wata yake a gabana, tamkar gabansa take, saboda cin fuska, ni haka na fassarashi. Nace. "Ina da wan'da nake so". Sam banga wani sauyi a tare da shiba, Sai ma d'an murmushi, da yayi yace. "Shi Kenan, Kinga Sai ki fad'a masa irin auren da zaki yi ba d'orarre ba ne, face na wani lokaci, da zai k'are, na taimakona domin cimma manufata. Idan da fahimta da k'auna ta gaskiya zai fahimceki, ya jira . Yarda na d'aukeki sumul, haka zan dawo masa dake, ko k'warzane, bazaki yi ba. Zan kula masa dake. jin abin nayi wani bam bara kwai wai namiji da suna hajara, wani wawan namiji zai yarda muyi yarjejeniyar auren wucin gadi na dawo masa ya aure ni? gaskiya Ancle Faiz son zuciyarka ya zarme yarda ka manta da damuwar wani ko mafitarsa face taka. Zuciyata ce ta shaidamin. Ya gyara zama, cikin hard'e k'afafun'sa. "Hak'ik'a naga a lamomin hankali, da nutsuwa da addini a tare dake Sumayya. Shi yasa Sulaiman, yana cemin ke ya zab'amin na a mince, musamman da naji yace ma kin yarda da aure na. Amma dai Ina jimamin, yin auren wucin gadi, da d'iyar wanda nake ganin k'imar'sa da darajarsa a idanuna. Amma na kasa juya baya. I think, some thing is wrong with me." Nace. "Kaji da shi." A zuciya ta. "Amma fa wannan magana da mukayi, ina so ta zama sirrin mu, bana so taje kunnen kowa, saboda mu ta shafa." Nan kuma cewa nayi, a cikin zuciya ta. "Ka makaro". Yace. "Idan kina da a binda za'kice kema, kina iya fad'amin." Abinda na iya cewa Kawai shine. "UM!. Saboda naga al'amarin nasa, ya gagari cewa ta. Ya daga kai a hankali cikin kasalallen kallo ya dubeni da yaji shirun yayi yawa, ya dan tabe baki irin na jin haushi, ya maida kansa kan waya, naga yana ta danne danne, ashe flashing yake tayiwa kawuna, kuma shigowar da kawu yayi shi ya tabbatar min shi ya kira. "Lafiya dai Yarima?".inji kawu na. Yarima ya ce " Tafiya zan yi Sulaiman, shine na kira muyi sallama". "Haba dai, daga zuwa, ko minti goma ba kayi ba?". Yace a dan fusace. "Idan na zauna, ciwon zuciya sai ya karni ai, wannan bagidajiyar 'yar taka taki cewa da ni komai, sai kauyanci take ta dokamin, ina zan iya, gwara na ware kawai". Kafin kawu yayi magana, na dan dago kai muka hada idanu bazata, sai kuwa ya jefomin wani kallo da jefamin wata irin harara, da sauri na sunkuyar da kai. *lallai abin na yi ne inji mai tsoron wanka*. _mu dai je zuwa_ Alkalamin*....... 🖋️ _Zainab ilyas mazawaje_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe _NI DA GIDANA_ _Zainab Mazawaje_ _Best brilliant interlligent writer_..... 🖋️ *Page 8* Kawu Sulaiman, banga ya nuna komai ba illa yace. "Karkayi saurin rik'on'ta Yarima, had'uwar kuce fa ta farko". Yayi saurin d'aga masa hannu. "Kaga, kar ka bata wata kariya saboda tana 'yarka. Tana sane. Yanzu da cikin k'awayen'ta ne, da tuni ka soma jiyo shewarta, wai sunan ita 'yar jami'a ce, kyau a maidota primary, kuma ma a ji d'aya." Raina kam, naji ya sosu da furutan Ancle Fa'izu nacin fuska a gareni. Tabbas, halin'sa yana nan nacin zarafi, bai ragu ba ma, Sai k'aruwa ni a ganina. A gaban fa Kawu Sulaiman, Wanda zai nemi aure na a wurin'sa yake min irin wannan wulak'ancin. Gaskiya Ancle Fa'iz baisan wata aba wai ka ra ba, ko kawaici, ballantana kunya. Kawu Sulaiman ya dubi komai da aka kawo masa bai tab'a ba, yace. "Yaya baka Sha ko d'an lemon bama. Me yasa?". Yace. "Ta banine? a jiyewa fa Kawai tayi. Wai look at her, batasan ma yaya zata tarbi bak'o ba? to Sai yaushe? Wannan 'yar taka Sulaiman da gyararraki, ba gyara ba. Ya juyoyo gareni ya sake watso min wani kallo mai kama da harara. "Kinzo kinyi min wani dimkim dake. Sai a bin ya bashi 'yar dariya ya dara kad'an. Sunan fa wani ganye wai Shima dinkim. Sai ya sake sakin 'yar dariya da ban tab'a ganin yayi irinta ba. "Ya kuma fa isheka haka haka, Yarima. Kai wani irin siriki ne wai, gaba na sai aibatamin d'iya kake.Ko mutuwa ance tana alkunyar idanun iyaye.Wai kai bakasan Kawai ci ba, ko kunya?". Bud'ar bakin'sa yace. "San'da a kayi rabon su bana nan, ko zaka sammin taka?". Ancle Sulaiman ya bishi da kallo kawai, kamar bazai taga ba, sai yace. "Ank'i a sammakan, kasan darajar su ne." Murmushi Ancle Fa'iz yayi. "To, rik'e Kayan'ka, ka kuma mai da wuk'ar. Ka Sani, ko nace Sumayya tayi zuciya ta daina gidadanci kawai, shine zai sa na sarara mata Wallahi, ba Sai ka tada komad'a bama." Ni dai daganan, Sulalewa nayi na barsu, suna sa insa basu sani ba. Nace, sun fi kusa. Ga duk kan alamu suna irin wannan karawar, mai kama da wasa, a zahiri idan ka gansu. Wannan nasan somin tab'ine a kan matsalolin da zan fuskan'ta idan nayi saken auren Ancle Fa'izu. Duk yarda zanyi kuwa zanyi, domin yakice auren.Sam! ban shiryawa cin fuska ba, da tozarci da wulak'ancin Ancle Fa'izu. wato Yariman kawuna. Bazan yarda burina ya rushe ba. Tuni zuciya ta ta tsaramin, yarda nake son rayuwar aure na ta kasance. Rayuwa nake so, sosai ta soyayya da nishad'i da walwala, da farin ciki, da fahimta. Na tabbatar na auri Ancle Fa'izu duk sun rushe. Ballantana ma Wai auren wucin gadi, yake so nayi,wanda zai k'are kusa ne, nesa ne ban Sani ba, shi ya Sani. Abinda na sani, ni zai cuta kawai. Domin na tabbatar ko wani abu bai ratsa tsakanina na aure da shi ba, tilas ya sakeni kallon bazawara za'ayi min. Ban isa na goge tambarin zawarci a goshi na ba a idon mutane. Ga zato mummuna da za'ayi min a ce bani da hali ne. Dad'i ma samarina na baya suyi min dariya, da Allah ya k'ara, tun da ga zaton'su ni mayaudariya ce. Mak'iya na su sami hakoran yi mini dariya. Bani da abokin fad'a Sam. Amma duk Mutum nasan baya rasa masoya da mak'iya. Nasan kuma Kawu Sulaiman bashi da masaniyar nufin Yariman'sa. Nasan ko giyar wake yasha, bazai so nayi irin wannan auren ba. Dad'i ma naji daga baya, da yake bani da hak'k'in Yarima, gashi ya fad'a min k'udirin'sa kafin aure. Kenan na sake Samun hujjar ya kice auren cikin ruwan sanyi. Sai dai idan Kawu Sulaiman bai ji ba. Dole kuwa yajin. A d'akin Kawu Sulaiman, Ina rakab'e bakin k'ofa, shi ya fara magana kafin na fara,kamar yarda naso. "Abinda kika yi, dole ya b'ataran Yarima, saboda shifa wayayye ne sosai, mai son harka ta wayewa. Ballan,tana shi da ya sabayin hira da wayayya gogaggiya mai babban a ji irin Salima, dole ki sik'eshi.Bai kamata ki rikid'e masa ga siffar da nima nasan ba taki bace Sumayya .wani daliline a ranki, kika yi masa haka ko? Sannan domin k'arin kwab'a kika yi tafiyar'ki baku ko yi sallama ba. Menene damuwarki Sumayya?". Wannan damar nake jira. Kawu, ni wallahi halin'sa bazan iya da shi ba. Ko a makaran'ta tsoron karo da shi nake. Abu k'arami, Sai ya tozarta Mutum. Ka gani ma da idanun ka Kawu, gaban'ka ya rink'a yab'amin maganganu, ko nauyin'ka bai jiba." Ya katseni da hannu. "Da Kinsan Yarima sosai, da fahimtar'sa baza ki yi wannan k'orafi ba." Na fahimci kamar kariya kawuna Sulaiman yake bashi ma, shi yasa na fito masa da da Zancen da idan yaji, Sai ya zargeshi. "Ancle Fa'izu fa cewa yayi aure na zai yi na wani lokaci ya sakeni Kawu, saboda cikar burin'sa. Wallahi ya fad"a kaji na rantse." Ga mamakina wai Kawu nan ma bai damu da furucin Yariman'sa ba, da manufar'sa. "Karki damu da abinda ya fad'a. Ikon komai da tabbatar komai yana hannun ubangiji. Zukatan bayi, suna hannun ubangiji, shi yake sarrafasu yarda yaso. Saboda haka karki damu da komai. Ke ki nufi auren ku, da kyakykyawan zato,da niyya mai kyau, da kuma kyakykywar addu'a zaki dace.za kuma ki amintu daga a binda kike fargaba Sumayya. Ba kya gani, ko Mutum ne, ya nufeka da mugun nufi, kai kuma ka nufeshi da zuciyar alkhairi, sharrin'sa bayayin tasiri a gareka? Karki turje, kan wasu a bubuwa marasa tabbas d'in d'orewa, ki yasar da a binda yafi alkhairi a gareki, baki Sani ba. Ki dubama yarda k'addara take ta had'aki da Yarima, Ku had'u ku rabu, Ku sake had'uwa.Sannan ni da nafi kowa son'ki a yanzu, ubangiji ya jarrabi Zuciyata da son ki auri Yarima. Kuma Sam, bana k'aunar a binda zai kawo cikas a auren. Gani nake, Yarima shine kad'ai ni ya dace da rayuwarki a duniya kaf Sumayya. Shine kuma Wanda nake jin zai rik'emin a manarki ko bayan raina. Jikina ke fad'amin haka Sumayya. Sai auren ya gabato, zan fad'amiki dalilan da yasa na nace da aurenki da Yarima. Ban kuma damu da yana son'ki ko baya son'ki ba. Ke da kan'ki baki Sha Mamaki da ya amince da auren'ki ba? Aikin k'addara Kenan.Hakan na nufin fa, ke k'addarar cikin rayuwarsa ce ko yana so ko baya so. Wannan bai i sheki ishara ba? In da na barki, kema auren rashin soyayya zaki yi da d'aya daga cikin masu son aurenki, domin na tabbatar su suke sonki ke ba kyason su tun da kika tsaya ruwan ido. Tun da haka ne, ki jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya mana. Ki auri Yarima domin dalilai da zan fad'a miki su a gaba. Kuma ki yarda shi k'addarar rayuwarki ne, da bakisan me Allah ya shirya muku ba, ki aure shi saboda wannan. Ni dai ya fiyemin tarkacen samarin ki sau d'ari. Domin nasan komai a kan'sa, usuli da halayan'sa. Na gani, kuma naji a majiya ta gaskiya.Amma nasan ba lallai ki yarda da shi ba har zuci yanzu, saboda kallon wasu halaye na zahiri da kike yi masa. Amma a Kwai na bad'ini da bakisan da su ba. Shi yasa kike gani baza ki iya da shi ba. Tabbas zaki iya zama da Yarima, matuk'ar kika fahimceshi, kuma kika kiyaye a binda ya keso da wan"da baya so. Nasan ko baki gwanance ba, zaki iya koyawa zuciyarki, ki jure kiyi, Saboda kina da hak'uri da biyayya. Kuma ki sani, idan ma kink'i auren'sa ba damuwa zai yi ba, ba kuma hak'ura zai yi ba da auren cimma wata manufa ba. Wata zai samu ya aura. To ita Watan kina zaton irinki ce mai kyawun zuciya da zata ceto shi daga yin kuskuren da yake son aikatawa, nayin auren wucin gadi? Ke kuwa nasan ko baki taimakeshi da komai ba, zaki taimakeshi, da nasiha da addu'a. Sanin kan'kine yin aure da niyyar Saki daga baya saboda wata manufa, haramun ne. Kika yi kandagarkin hana afkuwar hakan bakiyi babban aikin Lada ba Sumayya? . Naji jikina yayi sanyi Lis, da furutan Kawu. Tabbas Gaskiya ya fad'i , a binda nake shakkar yiyuwar, na yarda Ancle Fa'izu zai karb'i nasiha daga gareni, ko shawara. A yarda yake ji da kan'sa, ni kuma yake ganina a raine. Kawu yace. "Kuma ki rink'a nuna kulawarki wurin mahaifiyar'sa, domin yana tsananin son'ta. Zan iya ce miki nan ne sirrin farin cikin'sa. Ki soma d'ana tarkon'ki tanan. Ki kula. _Nan farin cikin sa yake_ ni na sake jaddada wannan a raina, har sau uku ma. Da wad'an nan kalamai Kawu Sulaiman ya sake farauto Zuciyata ta a minta da auren Ancle Fa'izu. Amma fa ban daina farga ba ba, da zullumin auren. Tabbas ba domin na yarda da irin K'aunar da kawuna kemin ba, cewa zanyi farin cikin rayuwata ne baya so, shi yasa yace na auri Ancle Fa'izu. Amma duk da haka ni fatana ke dai kar ya dawo, fushin da tafi da shi na nayi masa kaiyanci ya hanashi dawowa. Amma idan kaddara ta sa ya dawo bazan bujire ba, ba dai haka na so ba. Babbar fargaba ta kar na kamu da son sa ma, nafi shan wahalarsa, saboda siradi ne mai wuyar gaske mace mai sunan mace ta dora idanu a kansa ta dauke ba tare da ya zabaro zuciyarta ta kamu da soyayyarsa ba. Shi yasa ban fiye son na hada idanu da shi ba, domin a kwai sakonnin da kallon ke aikewa zuciya ta da ni kadai na sani, in da shi kuma yake jin haushin hakan, ya kuma daukeshi a matsayin kauyanci na ko kallonsa ba na iyawa. Allah gani gareka, baiwarka marainiya, ka kawo mata dauki. Na fadi a hakan a zuciya ta ni kadai ina zaune cikin tagumi. _Taku har kullum_ _Zainab mazawaje_ Alkalami yafi takobi... 🖋️ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe *NI DA GIDANA* *NA* _Zainab mazawaje_ _Best brilliant interlligent writer...... 🖋️ *Page* *9* Nayi sauri na fito daga d'aki, na karb'e tsintsiyar da Baba talatu, ta soma Shara da ita. Bata Musa ba, ta sakar min. Sai da na share ko Ina na cikin gidan tas!. Na had'o Kayan wanke wanke zan'yi Sannan tace. "Ke dai Sumayya bakison kiga nayi komai, in dai kina gidan nan." Nace. "To, Baba Talatu, kina da kamata kiyi aiki? aiko tsari babu. Kiyi kwanciyarki, nayi aiki nayi kuma girki, Sai dai Kawai na kawo miki kici. In dai ina gidan nan baza kiyi aiki ba." Tace "Koda a Kwai d'iya irin'ki mai kyawun hali, gaskiya k'alline. Kina da kyawun d'abi,a Sumayya, ga biyayya, ga tausayi. Ta Yaya kuwa bakina zai gajiya da sa miki albarka? da Fata na gari. In Sha'Allah Sai kin haifi masu binki, kuma Sai kin gwangwaje Miji na alfahari. Saboda kowa ya bud'i baki a kan'ki fata na gari ne. Addu'ar iyaye da 'yan uwa kullum bibiyarki za tayi tayi." Tuni na saba da lafazan Baba Talatu da d'ad'a, kullum ne bata gajiya. Tsawon kwana tara, ban sake ganin ko inuwar Ancle Fa'izu ba, ga wawtata farin ciki na Shiga sosai, a zatona ai ba zai iya dani d'in ba ne, kamar yarda yace, shi yasa ya janye. A tsukin aka sake gayyatar k'ungiyar su Kawu sulaiman Kaduna united zuwa ga buga boll, cikin k'asar Enugu, za'su kara da club din Ranger's. Nan ma su Kawu na ne suka cinye. Ya bugo min waya, cike da farin ciki yana mai shaidamin, dama sau biyu muna waya da shi, bayan tafiyar'su. Nasan da Ancle Fa'izu suka tafi, amma ko zancen'sa bai yi ba, nima banyi ba. Na fiddaran hakan, Sai ji nayi Ancle d'ina yace.o "Ga Ancle Fa'izu zan kai masa ku gaisa, kuma kiyi masa murna, domin shi yaci mana k'wallon nasarar guda biyu. Yana dakin hutu amma na barshi yana shan mutuniyar tasa multina, bari na kai masa. Da sauri nace. "Don Allah Kawu ka rabu da shi, basai munyi magana ba, kace Ina yi masa murna Kawai". Yace. "Zai fi kyau ki kira wayar'sa ki fad'i masa. Idan baki da ita zan turo miki. Nayi d'an Jim, daga bisani nace. "Ina jin nauyin hakan, Ancle. Naga shi ya kamata a ce yama nemi sanin lambata, ya kirani, amma bai yi ba. Shi yasa nake ganin kamar zan karyar da kaina idan na fara. Amma idan kace na kirashi, zan kirashin". Yace. "A'a. Rabu da shi kawai, na fad'a masa. Kinsan dai komai a kan'sa. Kinga kuwa komai ba zai shige miki duhun menene dalili ba. Kinsan dole zaki rink'a had'uwa da irin haka, amma kiyi hak'uri wataran Sai labari kinji shalelen. Ni da shi mukayi 'yar dariya. "Gaskiya Ina son Kawu Sulaiman, har bansan adadi ba, ko misali. Kwanan'su d'aya tal da dawowa kawuna yace min. "Sumayya, yau Yarima zai zo. Don Allah, ki kula a komai, kar ki bani kunya kuma. Ki canza". Nace. "To, Kawu zan yi bakin iyawa ta" yaji dadi. Na samu kaina da tsala kwalliya da ado fiye da farkon zuwan'sa sosai. Less nasa kalar marun mai adon duwatsu da filawoyi ,mai kyau, da nasan sunai mini kyau, saboda kawaye na ma ko dani suke idan nayi ado dashi. Mayafi da takalmi to mach, daurin nan ya kafu a kaina kamar nike koyar da dauri ga 'yammata, bansa sarka ba tun da ba gani zai yi ba, sai fasion da bangles. Sai turare mai sanyin kamshi da humra da nasa. Nasan dai duk a banza wai talaka ya girmi sarki a wurinsa, nayi ne kawai domin jin hakan ya dace, kamar yarda na cewa kawuna zan yi a binda ya dace da duk zan iya. Har bakin k'ofar waje da yake tsaye na isa na tarboshi, saboda Kawu Sulaiman Baba ya aikeshi ya tafi, kafin fitowata wurin Yarima. Saboda haka kujeru na roba na Kawu na fito dasu harabar cikin wajen gidan kusa da dakin Kawu dake kusa da k'ofar fita waje, da yake a katange yake ba'a hangen na ciki. Kamar had'in baki, Yarima Shima Man less yasa na maza, kalar pink mai cizawa. Sun yi masa wani irin kyau Kam. Duk da naje har bakin k'ofa na tarboshi cikin sakin fuska sosai, da sakin jiki da girmamawa, Sam banga ya sakarmin fuska ba. Ya dai dubeni, a dak'ile ya kau da kai. Abin a hali ne. Nace a hankali cikin dan tabe baki, duk da nasan ba sona yake ba, amma na dan ji ciwon kallon saurin da yayi min yayi saurin dauke kai kamar yaga abin kazanta. Tare muka jeru zuwa mazaunin Zaman, hannun'sa cikin aljihu, yana tafiyar nan tasa ta isa da jin kai. Naga Sai wani shan k'amshi ma yake, kamar wanda aka tilasta Sai yazo wurina. Kujerun da zamu zauna, suna fuskantar juna, kuma ni na a jiyesu ina sane a hakan. Zuciyata ce naji ta soma k'ek'ashewa, daga fargabar da nake ciki ma na auran Ancle Fa'izu, saboda na hanga gabas da kudu da arewa, ban hango matsera ba, na tserewa auran. Shi yasa Kawai na mik'a wuya, tare da nemo hanyoyin da zanbi, na k'ubuta daga tozarcin'sa da ya zama lazim. Nasan idan na ci gaba da nuna d'ari d'ari da shi, da Jan jiki, da alkunyar nan, to kullum gumamin takaici zai ci gaba da yi, shi ko a jikin'sa, ni zai bari da ciwon zuciya. Tare ma muka zauna. Bayan na gaishe shi nace. "Yaya momi, da fatan tana lafiya " Sai da ya fara da yi min wani irin salon kallo da Idanuwan nan nasa masu farauce zuciya. Amma na tabbata, babu manufar komai cikin'su. Baki d'aya Sai naji yanayin komai nawa ya canza tashi guda. Wani irin feeling naji, da bantab'aji ba kan wani namiji ba. Gashi na jawa kaina, muna fuskantar juna bare na kub'uce, gaskiya macen da za ta iya kubuta daga tarkon shauki ko kaunar Ancle faiz ba ace babu ba, amma zai wahalar, sai dai wacce ba a halitta da shaawar son da namiji ba. "She is doing fine. Yace cikin dan sakin fuska. Na barota lafiya Lau. Amma yaya kikasan Momi?". Nace. "Tun da nasan'ka ai dole na San'ta" Yace"A'a ni kad'ai kika sani. Ita dai kinji sunan'ta wurin Sulaiman. Any way, naji dadi da kulawar ki a gareta." Sai naga ya dan kara sakin fuska kadan. Karo na farko kenan da na tab'aji ya nuna jin dad'i a a binda a kayi masa a sanina. Gudun kar na kuma laifi, nayi saurin cika cup da lemon maltina mai sanyi na mik'a masa. Kafin ya karb'a yace. "Lady Kinyi karatun ta nutsu Kenan!. Ban tanka ba. Ya Mik'a hannu ya karb'a, Amma bai shaba, ya Shiga juya d'aya kwalbar lemon da ban bud'e ba. "Yaya a kayi, kika San Ina son lemon malt?. aikin Sulaiman ne dai na sani". Idanun'sa na kan lemon yake surutan. Ya shanye, ya sake cika cup ya shanye. Ya bud'e d'aya kwalbar ya cika cup ya Sha, ya a jiye ragowar a gefe. "Da k'ishirwa na iso, Sai kika samu ladana kika yi a binda ya dace. Ina son maltina sosai a rayuwata. Na kansha kwalba uku ko hudu wurin training ko gasar boll." Nace. "Lallai kana son"ta da yawa." "Ke baki son'ta?" . Yace. Nace. "Kadai d'arsa min son'ta, ga yarda ka damu da ita." Yace cikin wani lumshe idanu kan kwalbar lemon. "Look, ki fad'i opinion d'inki Kawai, ba ruwan'ki da zab'ina ok? ". Naji rashin jin dad'in gwaliyar da yayi min, amma Sai na danne. "Domin na tayaka son a binda kake so laifine.?" Yace. "Kuskure ne dai, saboda ra a yina da bam naki dabam, banga dalilin da zai sa ki tayani son wani a bu ba, don ni bazan tayaki ba anan zance na fisabilillah, iya nawa zan tsaya, kinga kuwa bai kyautu kiyi min kara ba, gaskiya ni kullum ba na boyanta bayyana ta nake, ko da kuwa kowa zai tsane ni, i don't care". Kafin na wartsake daga wannan ya jefomin wani. "Sumayya wai addu'a kika yi min ne?". Na waro idanu waje. "Wace addu'a zan yi maka ni kuwa Ancle Fa'iz?". Yayi harr da idanu ya sake kafeni da irin kallon d'azu, jin furucina "Wallahi da da na tafi, naci alwashin bazaki sake gani na ba, saboda gidadancin da kika nunamin. Amma bayan few days, Kawai Sai samun kaina naji Ina son waiwayarki kuma, kuma zuciyata ta nuna min fin karfin sani sai da nazo ba domin na niyyaci zuwan ba, naga kin canza yau, kina d'an tab'uka abu. Kenan komai da kika yimin rannan kina sane Kenan.?". Bani da amsa, idan ma a Kwai bazai jiba. shi yasa na zab'i yin shiru. "Kin a mince zaki jure irin Zaman aure N'a? ". Samun kaina nayi da juya idanu na rausayar "Zan jure man, tun da na iya jure zafafan bulalanka goma, masu ratsa k'ashi da tsoka." Sai ya d'an d'aga idanun'sa Sama, mai nuna a lamun ya tuno komai. Sai yayi dan murmushi da banyi zato ba. "A shefa kin tab'a fad'owa tarko na ko? amma wannan shafar mai ne, idan kika yi saken da kika sake fad'owa tarko na. Kinsan yanzu matsayi uku zan had'a a wurinki da an shafa fatiha. Malaminki nake, Sannan Ancle,Sai na gaba mijinki.". Da hannun'sa yake nuni, ta hanyar lank'wasasu. "Haka ne?". 'Yar dariya na saka. Yace. "Zakiyi ta gasken ne" Ya tattaro, Nutsuwar'sa. "Ina so ki fad'amin nawa zaki buk'ata na shirin auren'mu na biki, domin na tanadeki , banason auren nan ya wuce Wata guda fa. " Da hanzari, na dubeshi. Duk nasan saboda manufar sa ne,da yake so ya cimma. Wani zafi, naji a k'irjina. Eh, ga 'yar tsana ka samu, dole ka gaggauta. A raina na fadi, saboda nasan ban isa na fadi a fili ba mu kwashe lafiya. "Barshi, na yafe. Ni babu shagalin da zan'yi." Ya jefa min kallon hadarin kaji. "Kija Mani zargi ko? to bazai yiyu ba. Bazaki tozarta min aure ba, ko ba kya Sona , kuma ko banason'ki za'ayi shagali irin Wanda ya dace. Kije kiyi nazarin adadin kud'in da zakiyi amfani da shi. Idan na dawo naji. Dole ne , kima saddak'ar." Shiru nayi, jin zai soma hawa dokin zuciyar'sa da nake tsoro. Bayan sa'oi kamar mai wani tunani sai kuma ya dago kai gareni da nayi shiru cikin kafeni da idanun'nan nasa masu narkar da zuciya. "Kiyi min magana ko?" Nace. "Zan fad'awa Kawu Sulaiman, idan na lissafa." Ya kwaikwayi salon yarda na furta. "Zan fad'awa Kawu Sulaiman idan na lissafa. To Wai meyasa zaki nuna bam bamci tsakanin ni dashi? Nima ba kawun bane?". Da nayi shiru, ya tafa hannun'sa a hankali, ya kuma dunk'ule. Shikenan 'yar gidan Kawu Sulaiman, Sai naji daga gareki." Ya ci gaba da lissafomin irin shirin da ya soma na auren. Lefema da Sadaki, da kud'in aure yace rana guda zai kawo. Kenan Ranar d'aurin aure Kawai za'asa . Yarda yake nuna a fuwa da komai, Sai a zaci, wani auren soyayya za muyi da shi, na an matsu da juna. Bayan nan bana gaban'sa na Sani, ko na sakan na a gogo. Manufar'sa ya d'anawa k'ahon zuk'a. Fargaba d'aya nidai ta ragemin, shine kar a zal ta fad'amin Ancle Fa'iz ya samu damar yi min cuta ta k'arshe. Shine burin'sa Yana cika ya sakenj, nazo na bud'e faifan Zaman zawarci. A binda nafi tsana Kenan a rayuwata, zawarci.. Jinake yi, har gabana na yankewa ya fad'i idan na tuno. Nina shirya had'uwata da Nuriyya domin taji labarin da zai kid'imata. Wato na aure na da Ancle Fa'izu. Mutumin da ta k'wallafarai a kan'sa kamar ta zautu, wai yau shi yake shirin aure na. Inda a ke neman'sa yayi b'atan dabo.. Ko da yake batasan waye Ancle Faiz ba dangane da halayya, da ko daura mata a kayi sai ta kwance, duk son da take masa ba za ta iya da halayen sa ba, saboda ita ba ta da hakuri, ga tsiwa. Ai a guje za ta raina kanta, ta ce ba da ni ba. _Taku a kullum_ _Zainab ilyas mawaje_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe *NI DA GIDANA* _Zainab mazawaje_ _Best brilliant interlligent writer_...... 🖋️ *Page 10* Nuriyya kuwa ta girgiza da jin komai. Nasan baza taji dad'iba, tun da ta nunamin irin son da take yi masa a baya. Sai dai bani da zab'i face dole na fad'a mata, tun da babbar a miniyata ce dole taji. Ban sanar da ita sirrin komai ba, na dai ce Kawu Sulaiman ya had'a auran, amma ni a fargaba nake.idanunta naga yayi rau rau. Tace"Sumayya al'amarin ubangiji ya shallake tunanin bayi. Tsakanina dake a wannan lamari addu'a Kawai, to yaya zanyi? bani da yarda zanyi Sumayya." To nima d'in dabara ta kubce, bani da yarda zanyin da na barmata, toma idan zan iya barmatan uban gayyar karba zai yi? Dani da itan da take azabar son sa duk rukuni guda muke. Babu Wacce ta rabauta da Soyayyar'sa, Sai ni da k'addarar auran'sa ta sauka a kaina. "Ni haushi kike bani da kike Kiran wai kina zullumin auren'sa. Kamar wannan zuk'ek'en saurayin za'a nok'ewa auran'sa? Wallahi da motsi a cikin kan'ki, ba kalau kike ba koma ba na gari bane, ke dai ko baki tashi da ribar komai ba, kika tashi da ribar kyawawan fararen yara, ai kin gama da shi. Kasuwa ta tashima ai d'an koli yaci riba". Ni kam haushi furucin'ta ya bani. Ana ga yak'i tana ga k'ura. "Inaji ganin jarabarki ta son kyau da fari, Sai kin auri maye, nasan ko kinsan mayen nema auren'sa za ki yi ". Tayi 'Yar dariya. "Tabbas!. Ko zai rink'a lasar kurwata kullum Ina suma na farfad'o zan aureshi in dai irin Ancle Fa'izu ne." Na jinjina furutanta. "Al'amarinki Sai dai neman sauk'i Nuriyya, amma ba waraka ba." "Bani buk'atar warakar Dama". Tace, ni kuwa binta nayi da kallon mamaki kawai. Akwatu Shida set da kit d'aya Ancle Fa'iz ya had'o min na lefe. Ya zuba abubuwa kuma gaskiya masu tsada fiye da zaton kowa. A tamfofi Holand manya guda goma ne. Bayan masu matsakaitan kud'i goma. Lesuna masu daraja guda goma ne. Shaddodi da material ma sunyi . Hakanan Takalma da jakunkuna babu masu rangwamen kud'i. Sai a jakar Kayan sarkoki' za'a sha kallo. Duk da babu gold, Sai da aka zab'a a ka darje wurin zab'o k'ayatattun sark'oki na cinyewa, launi launi. Tilas a ce isashshiyar mace da tasan kan sirrin iya ado da kwalliya ta zab'o. Ni dai Abin yayi matuk'ar d'auremin kai, na yarda ya narkar da kud'i irin haka a auren da yafi kowa sanin manufar'sa da makomar'sa a gaba. Hajiya Mariya tafi kowa, murnar zuwan aure na, inda tayi ta kod"a lefen tana labartawa ga wad'anda basu gani ba, tamkar kaina farau, kuma k'arau. Haka ma 'yan uwan uwa da ubana kowa Sai Sam barka da Fatan alkhairi. Sati hud'u a kasa d'aurin auren. An tasheni tsaye an kuma tashi Kawu Sulaiman tsaye da kakana. Domin duk basu shirya ba suma, saboda basu zaci zuwan aurena a tsukin ba. Amma Kawu Sulaiman naga ko a jikin'sa. Murna yake sosai da zumud'in zuwan auren . Kuma dama komai Ancle Fa'izu yace ga yarda yake so a yi a kan aurena da shi, to ta zauna. Shi yayi ta nacin kar a d'aga bikin ma kamar yarda kakana yaso, saboda yasan Yariman nasa, bazai so ba Sam!. Ashe kawu Sulaiman yayi tanadin'sa na aure na. Duk da yace min, suna Samun kud'I, shi da Ancle Fa'izu yanzu sosai a kan da a harkar boll, musamman ma Ancle Fa'izu da ya zama shine champion d'in su, duk yafi su Samun kud'i Amma na jinjina komai sosai da yayi min. Hidimar Kayan d'aki da komai shine mai kaso saba'in cikin d'ari a cikin 'yan uwa. Cikin hukuncin Allah komai anyi min na fita kunya. Ko saboda maraicina ne hagu da dama yasa kowa ya k'ure kan'sa wurin hidimtamin?. Bayan d'aurin aure na da Ancle Fa'izu da safe naji komai ya fice a raina. Jikina yayi sanyi, domin na tabbatar na Shiga hannu, Sai yadda ta kaya dani kuma. A cikin wannan yanayin, Ina cikin k'awayena uku, da 'yan uwa Ancle Sulaiman ya turo yana kirana. Na Shiga d'akin'sa da sallama, yana zaune gefen katifa, ya nunamin kusa da shi daga gefe yace. "Zauna, Sumayya, magana nake so muyi." Na zauna, na juyar da kaina gefen k'ofa da mutane suke wucewa 'yan uwa, Jifa Jifa, daga zuwa cikin gidan, ko daga ciki zuwa waje, saboda k'ofar d'akin bud'e take, ana hangen Mu. "Yaya naga baki da walwala ne? Kina da Wata damuwa ne, Sumayya.?". Nace muryata tana rawa. "Allah Ancle banason nayi nesa da kai. Wallahi auren ya ficemin daga rai. Bazan iya jurar na wayi garin Allah banganka ba, kawuna. Don Allah ka taimaka a sahalcemin auren nan." Yayi murmushi, ba tare da ya nuna damuwa da furutaina na sokonci, da kuskure gami da wawtaba. "Sumayya, hak'uri zakiyi. Ko ba jima ko ba dad'e dole Mu rabu Sumayya. Babu yarda za'ayi Mu dawwama tare.Aure shine cikar darajar mace, shi yasa nafi kowa farin ciki da auren'ki. A yau zan cika alk'awari na fad'a Miki dalilan da yasa na aura Miki Ancle Fa'izu, ko kya rage damun kan'ki, kafin kiga zahir kema da idanun ki ki tabbatar.. Yarima Mutum ne mai gaskiya kuma kaifi d'aya ne a magana, bashi da fargaba ko tsoro wurin tsage gaskiya, ko kad'an. Kinga mai irin wannan hali, za'ki sameshi da rik'on a Mana. Babu mai rik'on a Mana kuma Sai Mutumin kirki. Babbar d'abi'arsa da tafi burgeni, shine bashi da ZARA.! Wato kule kulen 'yammata, daga wannan a koma wannan, yarda yawancin a bokan'sa naga wasu suna da irin wannan hali. Zan iya rantse Miki, Sai kyawawan mata guda goma su wuce ta gabansa bai kulaba, saboda ba mai ra'ayin kule kulen 'yammatan bane. Macen da yake so, shi ita kad'aice a gaban'sa. Duk namiji mai zara, za'ki sameshi da d'auka da a jiyewa. Kome kike Tak'ama da shi, da yaga Wacce ta fiki, tauraruwarki zata dushe, yayi k'ok'arin barinki ya kai mata hari. Kuma namiji mai zara, kullum cikin hange hange zai kasance, ko aure yayi matarsa ba za ta tab'a gama gamsar da shi ba.Kenan daga nan, k'ofar matsaloli sun bud'e. A yi hattara mata. Namiji mara zara kuwa zaki sameshi da tsayawa ka'in da na'in a kan guda d'ayan nan da ya keso, Wata ba za ta yi ta d'auke masa hankali ba. Kuma ko k'addarar aure ya ratsa zai yi, to bazai rink'a auri Saki ba. Yau ayi gobe a Saki. Kuma namiji Mara zara, zaki sameshi da son matar'sa da kulawa da ita sosai da kishin'ta. Ki Sani suffofin Yarima fa nake wassafamiki, cikin rukunin namiji mara Zara. Mutane da yawa fassara d'aya suke yiwa Yarima, shi yasa har Sukan manta da wasu d'abiun'sa kyawawa masu wuyar samu a zamanin nan. Kuma nafi kowa sanin Yarima da fahimtar'sa cikin a bokan Mu. Shi yasa muka shak'u tamu tazo d'aya. Tuni na fahimci cikin halittarsa ne wannan d'agawar da jin kan da za'kiga yanayi. Amma a zuciyar'sa babu wani nufin yanayin hakan ne da nunin d'agawa na yafi kowa wani a bu haka nan d'abi'arsa take. Amma idan kika fahimceshi sosai, kika fuskanceshi, kika samu kan'sa Kuna Mu'amala ta d'asawa, to za'kisan Yarima a wasu juyin Mutum ne a bin so. Yana da kirki Sumayya, amma fa Sai Kinsan makamar iya zama da shi za'kisan hakan, har ki yarda. Nasan ke damuwar ki babba, babu soyayya tsakanin Ku. To ki Sani, anayin aure babu soyayya kuma a sameta daga baya. Kuma a na yin aure da soyayya daga baya ta gushe. Kinsan in'da matsalar take?". Na girgiza kai a hankali. "A cikin d'abi'a matsalar take Sumayya." Nace "Ancle Yaya a bin yake ban fahimta ba." Da sauri yace "Yauwa 'yar albarka, wato kowan ne da Wanda ya dace dashi ya aura wurin d'abi'a, shi ake kira da Sab'awar halaye. Kinga kamar a kan'ki keda Yarima. Babban a binda yasa nake ta jaddawa ma Kenan a raina na cewa KE DA SHI KUN DACE. Farko Kinga Yarima yana da zuciya sosai. Ke kuma kina da hak'uri. Ba komai ne ma yake b'ata Miki rai ba ke. Yarima yana da d'an rik'o da rashin saurin yafiya. Ke kuma kina da saurin yafiya, da mai da komai ba komai ba. Kafin ma a nemi a fuwa kin yafe, tun da take kin ma manta an b'ata miki ma. Yarima yana da d'an zafi, a wasu Mu'amalolin. Ke kuma kina da sanyi sosai. Sau tari Yarima bashi da son magana, Sai ki bashi sunan miskili ma kai tsaye. Amma a wani tsukin Sai kiga kamar bashi ba, har hira Sai kusha. Amma dai rashin son hayaniyarsa yafi yawa. Na fuskanci ke kuma kin iya zama da mai irin wannan halin. Kin iya da halayen mutane wurin zama. Kuma nasan za'ki iya da wannan halin nasa mai kama da miskilanci Shi yasa nace. KUN DACE. Wannan shine Sab'awar halayen da ake so tsakanin ma'aurata, domin Muddin Mutum ya had'u da mai irin d'abiar sa a komai, to alamarin ba zai yi kyau ba, ko kad'an, tamkar BOM a ka dasa, dake buk'atar lokacin tashin'sa yayi, yayi bindiga. Kema ki auna a bu d'aya rak!.ace mai zuciya, ya had'u da mai zuciya, Yaya kike zaton makomar?". Nace "Ai Sai a binda aka gani Kawai na rigima my Ancle." Yace k'arshen furutan'sa. "Ai Sumayya, wurin Sab'awar d'abi'u a ke sanin an dace, amma ba'a wurin Samun mai mai kudi irin kaba, komai kyau irinka ba, ko ilimi da sauran a bubuwa da akayi tarayya a cikin'sa. Wata soyayyar ma a waje iskace wani lokacin, Sai anzo an zauna, 'yar manuniya ta nuna na halayya da za'ayiwa juna dai dai, Sannan soyayya ta gaskiya zata maye gurbi. Shine an dace da juna, da kuma Soyayyar. Me yasa kike ganin, anyi shaharar riyar soyayya da anzo zaman auren Sai yak'i dad'i kuma?" Kawu Sulaiman yayi gaskiya. Na fahimci komai Kam, daki daki. Ya kamata kuwa ma'aurata kafin suyi aure, su fahimci irin d'abi'un wanda za'su aura, koda da bin cike ne, domin a San an dace da juna kar Sai an Shiga a fad'a cikin matsaloli. Dole naso Kawu Sulaiman, sosai ya hanamin kuka lokacin da zan yi. Ya kuma sharemin hawaye lokacin zubar'su. Na fad'i hakan ne, saboda dangin babana da su ya dace Sufi tsayamin a aure, cogewa suka yi, kuma babu a binda suka yi min, Sai k'afafuwa suka kawo a kayi biki da su, maza kuma d'aurin aure. Ko ganin k'asa ta rufewa Mahaifina idanu ne, suka watsar dani? tun da ko nemana ba sayi. Da babu Kawu Sulaiman a Sha'anin aurena, da bansan irin tozartar da zanyi ba. Har sark'ar gold Kawu ya bani a ranar k'irar dubai yari da sarkarta karama bayan shine jigo na yimin kayan daki. Ko bai tatike aljihunsa ba a kaina, nasan 'yan sulalla suka rage masa. Da daren da za a mikani na rinka kuka kamar wacce za a kai gidan yankan kai, har sai da murya ta ta dashe. Kawu Sulaiman da kyar ya lallasheni sai na koma kukan na zuci na bar na fili saboda farin cikin sa, domin na lura ya shiga damuwar rabuwar mu sosai shima domin kamar kwalla ma naga ya na gogewa a sace. Karfe tara dai dai motocin da Yarima ya turo a dauke ni suka iso, dama an gama shiryani da komai da zaa yi min, ni suke jira da 'yan rakiyar a marya na tsaya kuka. Cikin mintina a shirin an gama duruwa cikin motocin harda ta kai amarya, in da aminin Yarima Hashim shine ya dauke ni a atasa motar da kawayena uku. *Alkalamin zee taku*🖋️ Muje zuwa.Yanzu ne za a soma labarin.... ✍️ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe *NI DA GIDANA* _Zainab mazawaje_ _Best brilliant interlligent writer......🖋️ _Page 11_ A cikin motar kai amarya Hashim yana ta hirar barkwanci da kawayena, yaso ya tsomani a hirar, amma ya fahimci bazan tanka musu ba, a raina baisan harshi kanshi haushinsa nake ji ba, domin nasan shima yasan kullin da suka shirya game da auran, tun da babban aminin Ancle Fa'iz ne, na hannun da ma. _TUSHEN KOMAI_ Unguwar magajiya cikin garin zariya, cikin wannan unguwa gidan'su Ancle Fa'izu yake. Nan kuma zan zauna cikin gidan'su, tun da ginin'sa bai hattama ba, da saura sosai, saboda babban gini ya kamfatowa kan'sa da zai jima bai kammala ba, tun da bashi da samu na sosai da sosai da zai kammala da wuri. Gidan na su, babban gidane sosai, amma irin fasalin ginin dane dashi, kamar shekara talatin baya. Fentin da a kayiwa kafatanin gidan yayi kyau, duk da ba k'erarren bane. Babbar k'ofa d'aya ce ta bak'in k'arfe ta Shiga gidan. Khalifa, shi yake bima Ancle Fa'izu, d'akin'sa za'a fara tararwa da an shigo harabar makeken cikin gidan. Muhibbat, ita ke bima khalifa, d'akin ta na can gaba da nasa.A kwai kuma wani falo madaidaici da ya shiga tsakanin'su a rufe yake amma ruf, da alamun babu kowa. Khairat, ita ke bima Muhibbat, d'akin'ta yana jikin na 'yar uwarta. Wanda ke gaba da na khairat, falona ne babba mai d'akuna biyu. Kuma da usuli, anan khairat da Muhibbat suke a tare, sanadin zuwa na ne suka barmin wurin, saboda yafi yalwa, shi zai dace da a marya Irina. A kwai kuma wani fallen d'akin gaba da nawa, nan Ancle Fa'izu yake, amma da usuli Shima d'akin'sa kusa da na Khalifa yake. Duk daga baya suka canza tsarin komai, saboda auran. Bangaren hannun daman hagun d'akunan dake zagaye da farfajiyar gidan benene gajere da zai kai ka b'angaren iyayen Fa"izu, nan suke gaba d'aya. Gaba da benen kichean ne babba na Momi. Gaba dashi store ne madai daici, shi ya zama kichean d'ina, bai ma cinye komai ba, tun da Deep freezer ta bata samu Shiga ba, Sai Friedge da yake shi k'aramine. Daga bayan benen band'aki ne, gaba dashi ma wani ban d'akin ne. Gaskiya, komai nasu ya birgeni duk da ba masu arzik'in bane, amma na lura a Kwai soyayya da rayuwa mai ban Sha'awa a wurin iyalan gidan, kamar yarda sukan su iyalan gidan suke kyawawan gaske. Duk mahaifiyar"su suka d'auko, Amma Khalifa shi ya baud'e. Bayan sun wawashe kyan na gado sun barshi da kad'an, Sai ya fito kuma bak'i. Amma daga baya da naga Mahaifin"su, Sai naga a she shi ya biyo sak"! Kamar ni kenan.'Yan uwan mahaifiyata sun cemin wai Mahaifina na biyo, Wai da na biyo mamata khadija, da sai nafi haka kyau, domin kyakykyawa ce sosai kamar kawu Sulaiman, domin ta fishi ma a kace. Toni godiya na kewa mahaliccin halittar, domin nasan nafi wasu. Kuma babu mai dubana yace min mummuna. Ina nan a tsakiya. Idan ba'a yaba ba, to kuwa baza'a kushe ba. Idan Mutum yana duban na k'asa da shi, to bazai yi butulci ba ga mahaliccin sa, domin duniya kafi, a fika ne. Idan Mutum kullum kallon na Sama dashi zai rink'a dubawa, to ba zai zama mai godiya da tawakkali ga ubangiji ba. Kuma ni ban yarda a Kwai mummuna ba. Sai mace taso zata zama mummuna, in dai tana la'akari da wasu da suka fita tana sarewa, tana k'ask'anta kan"ta, to baya zatayi tayi. idan mace ta yarda ita mai kyauce Itama, to kullum k'ara kyawun zatayi, domin zata kasance ne ko yaushe cikin yin a binda zai k'ara mata kyau. Ra'ayin Sumayya ne. Ni dai, tun da aka kawoni d'akina a ka watse, banyi tunanin komai ba Sai bacci. Kukan da na Sha, yasa b'arin kaina ya matsamin da ciwo, nasan babban maganin'sa irin na Kwan'ta nayi bacci. Sam banyi tunanin wai na jira Ancle Fa'iz ba, ban sa rai da zan saka shi a idona ba ma a ranar. Bani da bashin salla, har shafa'i da wuturi na sauke kayana. Tun da na Kwan'ta ban tashi farkawa ba, hudu da rabi na dare . Da Saura sallar a suba. Na jero addu'oi na fito rik'e da torch light mai haske, domin na kasa bacci kamar kullum. Fargaba da rashin sabo na sabuwar rayuwa. Kona koma bazan iya ba sosai saboda kar na makara a sallah. Na fito domin duba a gogon falo.Falon babu kowa wayam. Amma naga an rufe k'ofar falon da na sayo kad'an, an rufe sosai. Wannan shi ya bani tabbacin Ancle Fa'izu ya shigo, bayan nayi bacci. Daga kishingida sai bayan sallar a suba na farka, gari ya soma haske. Na mike na fito domin sallar sallah , wato naje nayi alwala Sararo nayi, saboda ganin kuma Ancle Fa'iz kwance kan kujerata kamar mai bacci a falo. Singlet ce a jikin'sa, ya rataye rigar kayan' jikin hannun' kujerar. Na tabbatar bayan na koma na dan kwanta ne ya shigo. Hannun'sa da yasa ya rufe fuskar'sa shi yasa na kasa tantance bacci yayi, ko idanun'sa biyu. Sai dai da nazo zan wuce na fita, Sai Jinayi yace "Ina zaki?" Idanun' nasa , dai a rufe yake da na juyo na kalleshi. "Alwala zanje nayi" Nace. Shiru yayi. Bayan naje nayi alwala na dawo, na tarar kuma bayanan. Al'amarin' nasa Kam da d'aure kai. Ya sake shigowa bayan gari, yayi haske sosai. Yana saye da rigar wandon shaddar da yasa d'azu, milk colour. Dama Ina zaune a falon nayi zugum. Tunani kala kala sun lullub'eni. Yace dani "Ranki ya dad'e". Da ya shigo mukayi arba. Ban tab'a ganin'sa cikin nishad'i ba da walwala irin na ranar ba. Nayi murmushi nace. "Ancle ai Sai ku wannan." Daga nan na rusuna na gaisheshi a ladabce. Ya d'an nade rigar'sa ya zauna a kujerar dake gefen tawa, ya juyo yana kallona yace. "Sumayya aike kika kika can,can'ta da a baki kambun sarauta guda. Irin wannan harkar hutu haka? Tun jiya kika yi kwanciyarki da wuri, har na shigo baki Sani ba. Da a suba ma na shigo na k'wank'wasa jikin gadon'ki domin kiyi sallah, bakisan a nayi ba. Ni kuwa Ina na samu wannan hutun jin dad'in?". "Kai d'in dai kai ka dace da rik'e kambun sarauta Ancle. Ko a sunan da a ke kiranka da shi, ai an yarda anbi. Yarima fa kake". Murmushi yayi, da ya k'ara masa wani sihirtaccen kyau, ya saki zancen, domin yaga nayi baki, har na fishi hujja. "Kije Ku gaisa da Momi, domin muna gaisawa take tambayata ke, Wai yaya kika kwana, nace k'alau, amma Kije taga zahir dai." Naji sanyin dad'I da momin'sa ta soma damuwa da al'amarina. Nace. "Yanzu dama nake tunanin naje na gaishesu, ita da Abba, to ban Sani bane, ko sun tashi daga bacci, ko basu tashi ba." Yace. "Ai mu nan gidan, in dai muka tashi da a suba mukayi salla, to bama komawa bacci. Idan ma a kwai mai komawa baccin, to nine, kuma ba kullum ba nima, Sai San'da bani da uzurori da yawa. Amma Kije Ku gaisa da momin, shi Abba ya fita yau da wuri, amma an jima zai dawo. Na dubeshi, cikin rausaya idanu. "Ancle, muje kayi min jagora, kaji?". Yace cikin bud'e min idanuwa. "Kina da larurar makan'ta?". Nace. "Ko d'aya". Then, why kike so na jagoranceki?". "Kunyar Momi, nake ji Allah." Ya gyad'a kai "Kina da aiki a gaban'ki Yarinya. amma fa bazamu jera ba gaskiya, Sai dai ki bari nayi gaba, ki biyoni a baya." Duk da bansan k'asadin'sa ba game da haka ba na hak'ura da hakan, saboda tuni na soma fahimtar'sa, Ancle Fa'iz, mutum ne shi da bashi karb'ar uzurin magiya ko roko, shi yasa ma ban soma ba. Sai da na bada sa'oi tukun na bi bayan'sa. A harabar tsakar gida na had'u da Muhibbat tana Shara, muka gaisa, amma dai banga sakin fuska sosai a wurinta ba. Ita kuwa Khairat, tana kichean tana had'in Karin kumallo, domin k'amshin soye soyen'ta ma ya kauraye gidan. Da yake, Ina d'an hangen'ta, duk da bata hangoni ba, na k"arasa bakin k'ofar kichean d'in muka gaisa, nayi mata sannu da aiki cike da fara'a saboda naga fuska a wurinta. Da fara'a sosai ta amsa tace. "Yauwa Anti." Yarinyar tashi d'aya ta shigemin zuciya. Da alamu zatafi Muhibbat kyakykyawar Mu'amala. Idan kuwa haka ne, Sai nace ta gama tako sa'a a matsayinta na 'ya mace. Domin kuwa ba k'aramar kyakykyawa bace Khairat. Kyau da hali, kuwa ai sai mai sa'a kan sa'a, d'ai d'ai Ku ke had'a duka. A zaune dirshan na samu Ancle Fa'iz a falon Momi, kuma a gaban momi, yana shan tea. Duk da jin shigowa ta, bai cira kai ya dubeni ba, face momin da ta zubamin idanu, Tana k'aremin kallo a hankali. Ban kuma yi Mamaki ba, saboda jiya da a ka kawoni wurinta da daddare fusKata a lullub'e take har muka baro wurinta. Yanzu ne kenan zata k"aremin kallo sosai. Bayan na zube na gaisheta tace . "Sumayya, yau kin wayi gari, a sabon wuri, yaya a kaji da kewa?". Kaina sunkuye cikin ladab nace . "Momi ai bani jin sauyin komai, tunda Ina tare daku, kamar Ina gida ne.Ku iyayena ne, su khairat kuma 'yan uwa nane". Na lura furucina ya faranta mata, a fuskarta na Karan'ta. Momi da Ancle Fa'iz suna kama sosai, har kalar fatar fara tas, mai sofanen jajaja, da kuma k'wayar idanun mai haske da yawa, da yalwar bakar gira mai duhu.Hasken cikin idanun suma da har yake bada launin shud'I shud'I iri gudane. Duk da shekaru, sun d'an hauta kasan ta zuba kyau na lokacin k'uruciya, domin kuwa har yanzun yana nan, sauyin kad'an ne, na turawar shekaru. Tabbas barewa bazata tab'ayin gudu ba, d'anta yayi rarrafe. Momi ta kalli Ancle Fa'iz da yake karyawa a nutse, tace. "Sumayya ga karin kumallonku can Khairat zata kai muku, kuma ga mijinki yazo ya dirarwa nawa, ai Sai ki matso Ku cinye Kawai tare, Khairat ta k'aro muku" . Kunya naji ta kamani, domin bazan iya wannan aiki ba gaban Momi. gashi kuma bazan iya bijirewa umarnin'ta ba. Ancle Fa'izu kub'utar dani yayi da yace da sauri. "A'a Momi, wannan ai yama k'are, ko bai k'are ba, gwara a kawo mata nata. Ni yau girkin ma na khairat, maleji nake yi da shi, duk ta cika magi. Can yana cikin ci yayi saurun furzar da wainar k'wai. "Magi, na tauna Momi, me ya samu Khairat haka?". Momi ta dubeni tayi 'yar dariya. "Sai kinyi kamar kina yi Sumayya, domin kin had'u da Miji mai tsirfa da k'orafi, ko yaya aka kuskure. Ni na faraci kafin shi amma banji wani magi ba. Gishiri ne ya fito d'an kad'an. Kuma baiyi yawan da za'a yi k'orafi ba ko kad'an." Nan ne naga ya d'aga idanu ya dubeni da sababben kallonsa mara manufar komai yace. "Sumayya, karfa Zancen Momi yafa kid'imaki, duk da gaskiya ta fad'I, amma nasan baza'ki iya dani ba kema. Shi yasa girki iya cikinki za'ki rink'ayi idan kin soma girki. Ya dubi Momi kuma "Momi, kwanon a bincina fa yana nan a wurinki kamar da, saboda Kinfi kowa sanin yarda nakeson d'and'anon a binci ko yaushe.Khairat ke kamanta irin girkinki, to naga Itama ta soma shiriricewar yin girki irin na Muhibbat, yau a bu yayi kad"an gobe yayi yawa, to Itama na yafe ta, randa duk ba kya gida baki samu damar yimin girki ba Momi, waje zanje na samu wanda yayi min na saya wallahi." Banga wani sauyi ba Sam, a fuskar Momi, game da furucin d'anta, duk da tace. "Kadai biyo hanyar da bazata b'illemaka ba Fa'iz. Kayi aure, amma baka da kwanon a binci? Kana dai da aiki a gabanka". Yace. "jama kuwa momi, kuma nasan zan iya ne". Nan nasan ko a jikinsa game da furucin momin sa, kuma hakan ya tabbatar min, suna hirar wasa da momi, kuma tana sake musu yarda basajin kunyar fadin abu a gabanta. Wani irin kallo da kulawa, naga momi tana yiwa Faiz na tsurar kauna irin ta uwa da danta. Nan tasan dan gaban goshin momi ne. Kaina yana sunkuye Momi da Ancle a na ta hira a nutse yayin da yake shan tea, abin gwanin shaawa. Can Ancle ya waiwayeni da nake can gefen Momi. "Sumayya kije ki karya rana tana yi, naga daren jiyan bakici komai ba, tun da banga kin bude kayan ma da na shigo da shi ba, daren jiya". Momi tace " Haka tayi bacci bata ci a binci ba, garin Yaya kai kuma ka barta, me yasa za kayi haka, bayan kasan amare basa iya cin abinci a ranar baki daya". Ya dan waro idanu ga Momi kadan. "Momi bafa laifina ba ne, sanda na dawo na tarar tayi bacci, da alamu ma bata samu bacci ba kwana biyu yarda na fahimta, domin baccin mai nauyi naga ta nayi, shi yasa na barta kar na tasheta ta samu ciwon kai, ko ta kasa komawa, wai ni tausayawa nayi ai". " Eh da gaskiyarka, bari na kira khairat ta kawo mata nan kawai". "Aa Momi bafa zata iya karyawa a falonki ba, nasan halinta, ta kai mata komai falonta dai". Ni dai ban tsinka ba, sai ya sake kallo na bayan ya dire cup din tea da ya gama sha. " Sumayya ko zaki karya nan din? ". Murmushi kawai nayi, don bazan iya cewa A'a ba, ko eh. Kiransa a kayi a waya kafin ya kuma magana, in da naga ya mike da nufin fita, bayan yace. " Momi ina zuwa Salima ke kirana". Jinayi ni dai kamar an daureni da da bai bayi, zuciya ta kuma ta soma wani dan kidan kalangu. Yayin da na fahimci momi jikinta yayi lakwas ita ma, ko na menene oho. _Taku_ Zainab ilyas mazawaje.. ✍️ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe *NI DA GIDANA* _Zainab mazawaje_ _Best brilliant inteligent_ Writer ....✍️ *Page 12* Bayan na sauko daga saman Momi na kuwa tarar tuni khairat ta kawo min karin kumallona, tea a fulas na shayi da madara da bornvita da kwalin cube na suger a gefe sai soyayyan kwai da dankali ga kuma bread a gefe dai. Sai da na waiwaya gefe na kula da wata poly bag mai kyau da Ancle Faiz ya shigo da ita daren jiya. Na bude in da na tarar da gasassun kaji biyu manya lullube cikin rolling silk paper, anyi musu gashi na kwararru sosai da ko kwana biyu suka yi baza suyi komai ba, sun sha cabbage fried onion da tomatoes da kayan kamshi mai tsinkar da yawu. Tuni kuwa yawun nawa ya tsinke, naji cikina ya soma kugin yunwa, domin gaskiyar Momi jiyan yini guda ban iya cin komai ba, saboda fargabar sabuwar rayuwar da zan fada. Amma nasan Ancle tun da bai taba ba har yanzu, wata kil nasa dabam ya dauka, na dauke robar babbar yagort da har lokacin da ragowar sanyin sa, cikin wata karamar poly bag shima, na a jiye gefe, dole sai anjima na dada dumama kazar, tun da ta kwana. Na zauna ina karyawa zuciyata tana ta sake saken yarda al'a mura zasu kasancemin a gidan, gashi na shiga tsakanin tsofaffun masoya biyu masu masifar son junansu, wato Ancle da Salima, kaddarar aure ta cillo ni auren gun wanda zuciyar sa ta na ga wata har gobe, tare burin ya mallaketa, amma kaddara ta riga fata, nice kaddararriyar matarsa ta farko da Allah ya hukunta tun fil azal. A gurin Ancle auren wata manufa yayi, amma ni a zuciyata sam ba na halarto hakan yanzu tunda igiyar aure ta sarkemu. A haka dai kamar bazan fuskanci wata matsala ba a gidan ga yarda na lura, harshi kanshi Ancle Faiz banga ya nunamin wata halayya mara dadi ba, sauyi ma na gani a kan kafin muyi aure. To fatana tafiyar ta ci gaba a haka ko bazai rinka shiga cikin sabgogina ba yarda na ke so, zan dai samu nutsuwar da zan soma janyo raayinsa a hankali, daga alkiblar da yake fuskanta, duk da gashi ya soma da cewa ma Momi ce zata ci gaba da yi masa girki duk da yayi aure. Ire iren wadan nan basu soma damuna ba saboda nasan manufar auren da mukayi da shi a zuciyarsa . Amma ni a Zuciyata, aure ne nake ji munyi mai manufa kyakykyawa, irin wanda a keso. Shi yasa ni a binda zan maida hankali a kai, shine ta yaya zan janyo ra'ayin'sa gareni kawai na kuma fahimtar da shi kuskuren da yake kokarin aikatawa, wanda nake ganin zai yi wuya ya fahimce ni, ko ya ma saurare ni a yarda nasan waye Ancle Faiz tun tuni. Bayan na karya na hau sama na gaishe da Abban su Ancle da naji shigowarsa, mutum mai halin karimci da kirki da ka ganshi, yayi ta samin albarka, tare da adduoi cikin auren mu, duk a gaban momi, domin suna tare. Zuciyata naji ta washe da samun nutsuwa da farin ciki da halin karimci da adduoi da Abban yayi min. A hanyar saukowa daga bene mukayi kicib'is da Khalifa, in da ya dakatamin yaja baya, domin na wuce. Shine farkon ganina da shi, Shima haka. Ta yiyu wannan dalili naga yana yimin wani mayataccen kallo Sama da k'asa nasha mur, saboda duk namiji mai wannan hali na kallon k'urilla, haushi yake bani.Amma duk da haka, bai sauya da k'uramin idanu ba, sai fara'a da ya sake sakima yana washe hak'ora, a haka muka gaisa, ya haye saman Momi. Ni kuma na sauko, na nufi d'akina, in da naga Muhibbat tana wanke wuri da tsintsiya. Nayi mata sannu da aiki, ta amsa cikin wani salo na i sa. Araina nace, wannan miskilanci ta d'orawa kan'ta, ko kuwa haka yanayinta yake?. Bani da mai bani amsa, shi yasa dole sai munyi nisan zama da ita zan canki amsa. A kan kujerar da Ancle Fa'uzu ya tashi ta falona na kula da wata tsadaddiyar wayar sa a kife. Mantawa yayi, ko a jiyewa yayi yana sane bansani ba domin dazu ai Salimar ta kirashi a waya a saman Momi ya sauko, kenan a falona ya zauna. Halin nawa nayi, na d'auka, domin a ganina yanzu ina da hurumin tab'a abin Ancle Fa'izu, tun da Mijina ne. Numfashina Sai da ya tsaya cak! na wucin gadi, ganin wacce ke kan fuskar wayar Ancle. Duk da ban tab'a ganin ta ba, nasan ita ce. SALIMA. Kyawunta da a ka kod'a to zarta ma da na ganta, a hoto gaskiya. Wani irin kishi naji ya ziyarci zuciyata mai rad'ad'i. Shine shaidar farko da yake nunamin na tsundima tsindim a kogin son Ancle Fa'izu wanda da nake yaudarar kaina da da cewa bana son'sa. Duk da nasan Salima yake so, ni auransa kawai na rabauta da shi, babu zuciyarsa kuma sanadin dai salimar. Hakan baisa na daina jin ciwon kishin sa ba. Salima tafi kama da irin larabawan Lebanon d'in nan, da basu cika haske ba da yawa, Sai tsagwaron kyau. Bata kai hasken fatar Ancle ba ko kusa, illa dai cikar halitta ta koina. English wear's tasa, wacce ta matsemata jiki, surar halittar ta ta d'iya mace, ta bayyana a sarari, domin rigar daga sama kamar 'yar shimi bata da hannu a jiki, gata mai nuna surar jiki daga ciki, domin shef din unders dinta har launin kalar a na hangowa, rigar banzar mai shara shara bata boye komai nata daga ciki ba, don da ita rigar saman da baasa ba, ni banga bam bamci ba, kanta kuma babu d'an kwali ta Saki yalolon gashinta ya zubo gadon baya,wani kad'an ta gefe ya zararo kan k'irjinta. Ni dai nasan tana sane kawai tayi wannan shigar ta iskanci, bawai rashin wayo ko rashin sanin kuskuren haka ba, duk wanda yaga hoton dole ya karar kai tsaye akwai manufarta. sai dai meye manufarta ga hakan, ubangiji masani. Na sake kallon ta a hoton na zumburi baki, na jin haushi. Sam shigar zub da darajar da tayi ta bawa namiji har ya zame masa mudubin dubawa a waya kullum ya sik"eni, bawai iya Kishi bane. Saboda kayan da gani masu tsadar gaskene, sai dai sun tashi a banza, tun da masu nuna tsiraicine gaskiya. Shi kuma Ancle soyayyace ta rufe masa idanu ya biye mata ya iya ajiye hoton a fuskar wayar sama, bansani ba, ko ita ta bashi damar a jiyewar, a fuskar waya ya biyewa soyayya ya ajiye din, duk zai iya yiyuwa. Sau tari wasu matan, suna ganin tallata surar jiki ga namiji wayewa ce, da k'arin janyo soyayya. To wallahi karyane. Na karya ta ni Sumayya. Bayan janyowa kai zunubi, ragewa kai daraja da k'ima ne matuk'ar babu aure gibi kuma sukewa kan'su sosai. Ko namiji bai nuna ba, ko bai hango aibi ba a lokacin to a gaba kuwa za'a karb'i raddi wallahi. To ni Ancle Fa'izu ya fita laifi a wurina, da ya kasa hango kuskuren ballantana yayi mata gyara, kuma wai nan aurenta yake so yayi, sai gashi har ya a jiye hoton ya zauna a fuskar wayarsa, ko yaushe kenan da shi zai fara tozali, idan ya d'auki waya. Tabbas giyar soyayya ta bugeshi yayi yana sane, bawai a ce bai hango illar hakan ba. Irin haka ne, idan namiji soyayyar banza yake yiwa mace, to ya samu kofa, tun da kalar tarko ne a ka da na na kama mutum da shi, ko da ba ma namiji bashi da mummunar manufa kan lace hadari ne, tunda akwai shaidan zuga zugi a gefe. To al'amarin soyayyar Ancle da Salima, bazan iya sharhi ba, tun da bansan ciki da wajenta ba, amma a zato da kallon da nake yiwa Ancle Faiz, ba mutumin banza ba ne, amma sanin mutum na badini, sai ubangijin dai da ya halicce shi. Sai dai nasan ko meye a keyi a boye na rashin gaskiya, wataran zai bayyana. Bansan sanda nayi Jifa da wayar ba jikin bango saboda kishi da haushi. Jikake tus! na d'auka naga glass d'in ya fashe. Na d'ora jikin TV stand. nasan masifa ce kawai zan sha. Iya ka kenan. Duk da Khairat ta kawomin break fast , ban karya ba, Sai da nayi wanka na shirya cikin kwalliya da ado sosai. Na zauna na karya. Har lokacin Ancle Fa'iz banjiyo motsinsa ba, ko yana dakinsa ne, domin da na baro saman momi yanzu bayanan. A shiryen sa ya shigo min, Shima yayi wanka yasa shadda ruwan goro, hartin d'in gajera ce iya gwiwa, gaban rigar anyi masa aiki na kwala mai kyau. Sunfi yi masa fiye da wacce ya cire. Duk da sirrin kyawun ba'a kaya yake ba,a halittar ne, sai baza wani sassanyan kamshi yake yi mai tashi a hankali, da shiga ruhi. Yana shigowa na dake, saboda laifin da nayi masa, amma jikina na soma jin ya soma rawa rawa kadan na tsoro kuma, saboda nasan waye Ancle idan ransa ya baci. Wayar tasa kuwa ya Shiga nema . "Ba nan na bar wayata bane?". Mik'ewa nayi tsam naje na d'auko inda na a jiye. Har na mik'a masa naga yanayi min wani salon kallo, da alamu na tuhuma ne, kafin daga bisani ya d'ora idanu a kan wayar yayi tozali da ta'asar da nayi. Ya sake dubana. "Garin yaya kika fasa min waya?". Na sunkuyar da kai nace. Garin tsautsayi ne kayi hak'uri Ancle." Na koma na zauna a bina. Ransa b'ace yace. "Garin ganganci dai kika fasa min waya Sumayya. Me ya kaiki d'aukar wayar da take a jiye? Lek'en a Siri ko meye?". Naji shigar furucin'sa amma na dake, saboda nina jawa kaina. Kawu Sulaiman ya Sha yi min nasiha na daina tab'a a binda banawa ba, musamman na sirri, nace sai na gani, gudun fad'awa rigima, saboda binciken da nake yi masa a d'aki. Na k'ara bashi hak'uri. "Ancle kayi hakuri nayi laifi, amma bazan kuma ba please". Nayi masa tayi da tea da na Sha saboda ko rabi na kasa sha, bansan dalili ba, ga kuma yunwar ban cike gurbinta ba, duk da nasan yasha tea saman momi, duk domin kau da zancen ya wuce. Kuma babu dad'i, daga auren mu a ce mun soma samun Sab'ani. Ancle ya iso gareni, ya zauna gabana, kamar tea d'in zai sha, amma Sai naji yace a hankali cikin wata galabaitacciyar murya. "Sumayya, me yasa kike kishi a kaina?". K'warai gaskiya ya fad'i, kishin yafi kaini ga hakan, amma bazan so ya yarda ba, duk da ya d'ago, shi yasa nace. "Wajibine mace tayi kishin mijinta". Ya sake jefomin tambayar da ta hargitsani. "To, Kina so na ne?". Nayi kokarin sarrafa kaina. "Ai ko da so ko babu so, mace zatayi kishi a kan mijinta". Da sauri yace. "That's not true. Sai da da so ake yin kishi. Nayi mamaki da a d'an tsukin nan da zuciyarki ta iya So na. ke kinga na can canta kuwa?". Na kasa iya cewa komai, saboda sani a gaba da yayi, ya tsareni da idanun nan nasa masu sace zuciya farat d'aya. "Idan za kiyi shawara dani tabbas zance kiyiwa zuciyarki shamaki da soyayyata, domin bata da amfani a gareki Sumayya Sam ,Sam, kuma ko a gaba bazata amfane ki ba, kece mace ta farko da bazan so, ki kamu da soyayyata ba. Kamar yarda nake kallon su Khairat, haka nake kallonki Sumayya. Zan iya bugar k'irji nace miki k'anwata, zan iya ce miki kuma my Daughter duk dalilin Sulaiman. Really, ke matata ce, amma a furuci ne kawai, misalin auren mu kamar shirin wasan kwaikwayone da mutane su ke gani, su rinka zaton gaskiya ne, idan suna gani, amma a badini ai duk shiri ne, sabanin tunanin su. To a wurina, haka ne. Shi yasa bazan yarda na d'ora miki wani nauyi nawa ba. Kema nasan bazaki so ba, ko zaki so, ni bazan so ba. Shi yasa tun farko ban b'oye miki komai ba, ballantana ki Shiga duhuwa, idan kika ga ba yarda kika zataba. Ko da yake Ancle sulaiman yace WAI NI DA KE MUN DACE. To ni ban kai hangen dacewar da yake nufi ba. Ko matakin benen soyayya bamu hau ba, yace MUN DACE? Bazan yi miki k'arya ba, nace Ina sonki, saboda kiji dad'i, kuma bayan k'aryar ma kuma ai da yaudara. Shawara ta, ki daure ki rink'a kallona a matsayin Kawu Sulaiman ba miji ba, hakan zai kawar miki da damuwar da zaki iya samun kan ki a ciki, ko takura. Zai sa ki Samun sakewa da farin ciki a zaman mu, idan kika da sawa zuciyarki hakan. Ki jarraba Sumayya, zaki tarar da a binda na fad'a miki,zaki gasgatani." Ni dai har ya fice, kamar gawa, na gaza yin motsi. Nasan shi ko a jikinsa, game da furucin da ya furta min, saboda babu d'igon kunya ko kawaici a tare dashi, wurin fad'in a bu, ko yin abun da yasa kan'sa. Tun da gashi bai b'oyemin komai ba, tun farko. Amma a bu da nafi jinjinawa. Farko yace na rink'a kallon'sa a matsayin kawuna Sulaiman. Wurina kamar haramta halas ne. Shi Mijina ne, to don me zaice na rink'a kallonsa a matsayin Kawu na,da aure ya haramta a tsakanina da shi. Sannan ya dubi cikin idanuna yace yana k'yamatar wai na soshi. Kuma wai aure na dashi iya furuci ne, ban da a aikace. Banyi zaton za'ta kai mu da nisa haka ba, domin zatona duk wata d'awainiyar aure zai bani damar nayi masa, iyakaci ya k'aurace min, tun da baya Sona. Komai kenan bazan yi ba, hoto zan zama. Gaskiya da sake. Na dad'e a daren ranar ban iya samun bacci ba, ina tsara salo salon yarda zan fitowa Yariman kawu na, mai wuyar Sha'ani da tsadadden samuwa. Idan yasan wata ai baisan wata ba. Nayi wayewar sanin komai, da iya komai. Zan fito masa duk ta inda bai zata ba. Kuma cewar da yayi na rink'a kallon'sa a matsayin Kawu Sulaiman zan kuwa fitine shi, duk shagwab'a da tab'arar da nake yiwa Kawu Sulaiman tun ina yarinya, har girmana zai shata salo salo, bashi da k'orafi ko sababi, idan yayi zance ai shi yace na rinka kallonsa a matsayin kawu na, zan ce shi yaja, tun da shi ya ban damar hakan, sai duk a binda zai faru ya faru. Da ace ban riga na aure shi ba, ya furta min kalaman nan, to tabbas zan yi zuciya na barshi. Amma tun da yayi saken da igiyar aure ta sark'emu, to wallahi bazan hak'ura da shi ba, Sai inda k'arfina ya gaza. Bani ba, ko wacece ma a binda zatayi kenan, in dai ta samu nasarar mallakar miji irin Ancle Fa'iz. Baza ta yarda ta canza shi da wani ba sai dai tayi k'ok'arin canza shi zuwa ga yarda takeso, idan zata iya, Ko taci layar hak'uri ta zauna da shi da halinsa. A ranar dai nayi ta bak'i amma yawanci k'awayena na jami'a saboda su na gayyata a yinin biki na, saboda bana son tsofaffin k'awayena na secondry su san na auri malam Fa'izu, terere za'ayi tayi, ana kwazawa. Daren ranar Ancle Fa'izu ya shigo falona, amma ba muyi hira ba doguwa. Duk yarda naso ya saki jiki ya jima yak'i, ya kawomin uzurin wai a gajiye yake, na kuma karb'a. Ko minti biyar bai yi ba, yayi min sai da safe ya wuce d'akin sa. Da safe na a jiye bak'unci gefe d'aya, tun da nayi sallar a suba ban koma ba. Ancle Fa'iz nema ya tasheni sallar a suba bai san nima gwanar tashi bace k'arshen dare nayi nafilfili har zuwa a suba, to Sai yazo ya tarar dani zaune Ina lazumi, Sai ya juya. Tare muka Shiga hada hadar girkin safe da su Khairat, duk da Khairat tayi tayi na bar aikin sayi nak'i. Ta hak'ure, Sai gashi muna aikin tare cikin armashi, har 'yar hira mu keyi. Ita kuwa Muhibbat baya ga gaisuwa bata sake cemin komai ba. Bayan miskilanci, ma da naga tana fama dashi da jin kai ainun, ko irin yanayin yayan tane da ita ban Sani ba. Amma shi Ancle sanadin aure ya d'an sauya,tun da har yana 'yar hira dani. Ta yiyu ita ma ta sauya idan an Kwan biyu, amma fa a zatona. Muhibbat dai tafiyar ta tayi ta barmu da aikin, kuma na lura sanadin zuwa na ne. Khalifa ne ya lek'o kichean d'in ya soma yiwa Khairat Maganar ta dafa masa ruwan wanka idan ta gama.Sai kuma yayi Jim, da ya ganni, in da ya sake bina da mayataccen kallo, Sannan ya miko gaisuwarsa gareni. Na amsa da sauri na kau da kai na ci gaba da a binda na keyi. Zuciyata bata sak'amin komai ba, game da Khalifa, Kawai banajin dad'in kallon da yake yi min ne, ko santaran nake babu aure. Ban Sani ba, ko shi kuma tasa d'abi'ar Kenan, ko kuma wani k'uduri ne a ransa. Amma yaya zanyi, tun da k'addara ta cilloni gidan'su. Bayan ya tafi, Khairat tace . "Yaya Khalifa ya cika matsawa mutane idan yaga a na aiki. Da da wutar nefa ma Sai na jona masa a Heater ko electric cooker. Amma tunda yaya Fa'izu ma zaice na dafa masa ruwan wanka, Sai kawai na had'a musu wuri guda." Nan nasan itace ke yi musu hidimar komai shi da khalifa, nasan zuwana kuma bazai Ancle Faiz ba zai sauya hakan ba. _This is just the begining👌🏻_ _Taku_ _Zainab ilyas mazawaje_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe *NI DA GIDANA* _Zainab ilyas mazawaje_ _Best brilliant interlligent writer_... 🖋️ *page 13* Nace da Khairat, bayan tafiyar khalifa. "Bari na d'ora musu a gas cooker d'ina, idan yaso sai ki d'ebarwa khalifa nasa, kin san yanzu ruwan sanyi ba zai zububa a jiki, dole sai an d'an dafa, tun da da ragowar sanyi, tun da kuma safiya ce, kije kiyi shirin makaranta, kar ki makara, naji kina tambayar lokaci, na k'arasa soya dankalin." Tace "Gaskiya kam. Kin hutashsheni ma, na gode Anti Sumayya. Dama na kusa latti wallahi, wannan yaya Khalifan zai sake b'atamin lokaci. Na gode." Nace. "Kai Khairat, ina a bin godiyar, ai an zama d'aya." Cikin mintina kafin ta shirya, na dafa ruwa, ta mik'awa Khalifa nasa. Ban bata na Ancle Fa'izu ba, nace na a jiye masa, duk da na fahimci ita ke yi masa wannan aiki, ba kuma fasa bata zai yi ba na sani saboda baya son na yi masa hidima kowacce. Ni kuma na Hak'k'ak'e aikin ya dawo hannu na duk runtsi. Da na gama na zuba komai a mazubin da ya dace. Daga Sama na jiyo muryar Momi, nan nasan ta tashi Kenan. Na nufi benen domin na gaishe su har Abban. Amma gyaran muryar Abban da naji yana saukowa daga benen na dakata. Saye yake da babbar riga babu ta ciki. Nan nasan iya k'ofar gida zai fita. Na tsuguna na gaisheshi. Cike da farin ciki sosai ya amsa, ya tambayi lafiyata da yarda na kwana. Ya sake jero adduoi masu kyau gareni kamar rannan. "Allah ya shi albarka, ya baku zaman lafiya 'yata." Ba kad'an ba naji dad'in addu'ar nan tasa. Ko ba 'ace ba,kana ganin sa kaga mutumin k'warai mai karimci. Fara'a Kam a fuskar sa kamar gonar auduga. Nasa kai da nufin d'aga labulen mai kauri da ba'a ganin na ciki, na tsinkayi maganganun, kuma farko Sunana naji an kira, shine dalilin da gabana ya fad'i na kasa shiga, in da maganganun suka yi ta tururuwar shiga kunne na. Muryoyin Khalifa ne da momi. "Sumayyan ai babu laifi Itama Khalifa.Tana da hankali da nutsuwa ga alamu ga ladabi. Gashi tana karatu, amma banga alamun wayewar banza a tare da ita ba kamar wasu." Yace. "Momi, bafa a saurin yabon d'an kuturu, Sai ya mutu da yatsu." Ta karb'eshi. "Haka ne Khalifa sai ya mutu da yatsu." Ya sake cewa. Momi, ni fa tun kafin ma na ganta na tsaneta. Da na ganta Sai nafi tsanarta. Kallon k'urillama nayi tayi mata, domin naga me Yaya Fa'izu ya gani, a jikinta har ya zab"i auren'ta, amma bangani ba, ba kalar auren sa bace ma ko da a kaddarar aure. Momi kuma naga mai kafirin wayoce fa yarinyar nan, da iya kissa, daga zuwa har ta zama 'yar gida?anya bazata d'auke miki hankalin d'aba a gaba?". Da bata ce komai ba ya zarce. "Momi amma fa Yaya Fa'iz ya kwafsa, kan a bu kad'an yayi wani auren huce haushi, kodai k'arawa kai haushi, tun da na tabbatar Salima kad'ai yake so a duniya. Laifin mominta ai bai kamata ya shafeta bako?". Nan momin tace. "Shima ai ba Salimar yayi nufin b'atawa ba, nufin sa na kan mamanta, amma dole ita zata fi kowa jin ciwon hukuncin da ya zartar na yin aure.Nasan labarin bai same ta ba, tun da kaji shiru.Amma dai ya aikewa da iyayenta katin d'aurin aure, ta yiyu bata ji ba.Nima banji dad'in a binda yayi ba na zartar da hukuncin yin aure, a matsayin ramuwa. Nafi son sa da Salimar sau dubu. Babu yarda banyi ba, na hanashi auren nan, amma ya dameni da magiya da lallami, kullum har Sai da na saduda. Ni kunyar had'a ido nake da Salimar ma wallahi. Yarinyar da take mutuwar son'sa, duk in da d'an uwan sa yake, Sai da ta nemi Sani. Bata gajiya da yi mana d'awainiya, jikinta bai huta ba, haka ma kud'inta. Amma a ce sakayyarta kenan? Gaskiya Sai yanzu nake jin ciwon auren ma, bayan anyi. Ko a waya kunyar mu gaisa nake ji. Kasan kusan kullum tana bugowa ta gaisheni." Khalifa yaja dogon tsaki. "Dole ma yarinyar nan tabar gidan nan Momi, dole ya sallameta, ko bai shirya ba." Momin tace"Wani irin furuci kake yi Khalifa? Kai kake auranta, ko kana da wani k'arfin iko ne a kan mai auranta? ai babu maganar dole, tun da Shima ba sonta yake yi ba, yarda na fuskanta , kama hutar da kanka. Idan d'an koli yaci kasuwa, ai gida yake komawa ko?". Khalifa yace. "Haka ne Momi. Ni dama babbar damuwata, kar ta ritsa dani. Saboda Salima tace za'ta samomin babban aiki na acounter a kamfanin babanta. Kinga idan auren ta da Yaya Fa'izu bai yiyu ba, taji yayi auren nan, yaya kike zaton makomata Momi? ni za'ayiwa buk'ulu fa. Ai dole na shirya Munak'isar da zai saki yarinyar nan momi, idan naga bashi da niyyar sallamarta da wuri." Ban tsaya naji me momin zata ce ba, na juya a hankali na sauko, saboda idan na Shiga za'su tsargu. Idan kuma na ci gaba da tsayuwa, za'su iya fitowa su ganni. Nayi zaune a d'aki, damuwa duk ta baibayeni. Maganganun Khalifa su sukafi zafafa k'wak'walwa ta. Bansan zan fuskanci Wata matsala ba kuma a gidan, bayan ta b'angaren Mijina da nake tunanin ita kad'aice da zan ji da ita. To A she bayan matsalar da nake da ita ta Mijina, duk gidan ma Ina da matsala da su, babu mai yi dani a she duk sun fison Mijina da Salima. Gaskiya naga Muhibbat Sai wani fizga fizga take min. Momi farin cikin Ancle, Fa'iz tace ta fison Salima sau dubu dani. To ko iya nan matsala ta ta tsaya, ai da aiki gagarimi a gabana. Ancle baya had'a kaunar momin sa da ta kowa. To ni kuwa da wanne zan soma? ta Ina zan fara? da yaya zan soma warware matsalolin da suka yi min k"awanya hagu da dama?. Duk da wad'annan matsaloli dake gabana, amma domin k'arfin hali wai b'arawo da sallama, Zuciyata Sai rad'amin take da cewa. Sumayya karki kaya, ba"a sanin maci tuwo, Sai miya ta k'are, kuma mai zabarin nema, yana tare da nasara, wataran, musamman mai nagarta. Ni dai nasan, bawai nacin son Ancle Fa'iz ko ya soni, shine babbar matsalata ba. A ra'ayina, a tsarina, babu a binda nak'i jini irin a ce nayi aure ya mutu, Sannan a ce ma ban dad'e ba. Sam! ban shiryawa Zaman zawarci ba, ban kuma shiryawa amsa sunan bazawara ba. Domin Muddin wa'adin aure na da Ancle Fa'izu ya cika ya sallameni, ban isa na goge tambarin sunan bazawara a goshina ba. Nasan samarina ma zasu samu labari, suyi min dariya, musamman Usman, da ya tab'a yab'amin magana da karin magana, yace wai k'arshen a lewa dai kasa ce, suna nan suna zuba ido kuma, suga k'arshen'ta. Shi zaton'sa wani mai iko sosai na samu na barshi. Bayan wani lokaci, na koma na gaishe da Momi. Sam banga wani sauyi a tare da ita ba, sai ma bangajiya, da tayi min, da cewa, wai taji nice jigon aikin komai, na karin kumallon ranar. Khairat dama ita ta kwashe komai, ta kaiwa kowa. Nima har d'aki ta biyo ni dashi. Tace min. "Anti Sumayya, na tafi makaranta. Fuska ta cike da fara'a nace "To, a dawo lafiya, K'anwata. "Khairat, ita ce na tabbatar tana k'aunata da zuciya guda. Kuma nima ta shiga raina, tashi d'aya. Har lokacin, banga Ancle Fa'iz ba, ya fito daga d'akin'sa ba. Bacci yake ko menene, ban Sani ba. Kamar na Shiga na gaisheshi, na kasa. Na had'a ruwan wanka mai zafi dai dai dai, nasa turarrurukan wanka, na rufe da murfin babban bokitin wankan,mai kyau. Sai da na gama shiryawa, na zauna a falo, Ina karyawa, Sannan na jiyo muryar Ancle Fa'iz shida Khalifa a tsakar gida suna magana. Nan nasan a she Khalifa, ba fita yayi ba. Kafin na farga naji sallamar Ancle Fa'iz. Amma daga bakin K'ofa ya coge, muka gaisa. Nace. "Ancle ga ruwan wankan ka can na kai maka toilet. Nan naga yayi dan jim, kamar bazai ce komai ba. Ni kuwa nasan shammatar'sa nayi, shi yasa na sashi a kwanar nazarin yarda zai yi da katsalandan d'in da nayi, na binda bayaso nayi. Wato yi masa d'awainiya ko Wacce iri. Nace. "Ancle, Fa'iz kajini kuwa?". Yanayin sa kamar amsar rashin bukatar hakan zai nunamin, amma sai ya canza niyya, ta yiyu nauyin ya wofuntar da kyautatawar yayi, ko kuma wani dalilin ne. Ya shafi, kyakykywar bak'ar sumar'sa da take a kwance ta soma fesowa, daga askin da yayi mai suna SKIN, da yay masa kyau kuwa sosai. Yace. "Naji ki Sumayya." Daga haka bai sake cewa komai ba, ya tafi. Nasan da bai a mince ba, zai fad'amin ba ya so, tun da bashi da rufi, ko alkunya. Naji dadi kuwa sosai da bai gwasaleni ba. Ranar nayi bak'i sosai. Baba Talatu da Hajiya mariya suka fara bud'e fage. Da Tsokanar wasa na tarbesu nace. "Ku kuma tsofaffun nan Sai yau za ku gamo kai, Ku ringid'o kuzo? Ko ku lek'oni jiya? Kuma naga duk mazajen nan ku ai naga duk sun tsofe, babu sabon jini, sun zama jagwal, ballantana kuce tarairayar'su tasa kuka kasa lekoni jiya kuka shantake". Baba talatu tayi jagale tana kallona na shegantakar da nayi musu, nasan kulla kalmomin daukar fansa ta tsaya yi. Taku a kullum_ _Zainab mazawaje_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe *NI DA GIDANA* _Zainab mazawaje_ _Best brilliant interlligent writer...✍️_ *Page 14* Hajiya Mariya tayi 'yar dariya tace. "Shak'iyyar wofi. Kwana biyu dai munji kunne, da kika yi gaba, yanzu kyayiwa mijinki kuma." Baba Talatu, tace"Sa'a ma kika yi muka zo yau. Dama idan dad'i yayi wa Mutum yawa, Sai yace Allah kasheni na huta. Da Kawunki Sulaiman cewa yayi, kar muzo, a bari an d'ebi lokaci tukun. Kakan kine, ma yace sai munzo mun duba masa ke lallai, duk da dai bake kad'ai bace ma a gidan, ko menene ai da wasu, amma shine za kiyi mana godiyar mayu ko?". Naji nauyi, na saddakai k'as nace kuma. "Yaya Kawuna yake?". Baba talatu, tace. "Dama nasan shine a layin farko. To Lfy Lau yace a gaisheki da kyau." Na yi murmushi kuma nace. "Allah sarki tsoho mai ran k'arfe, yaya yake, kina kulamin da shi kuwa? (kakana). Tace "Tace.Ko ke albarka.Lfy Lau yake, yace na gaisheki." Hira sosai muka yi, daga bisani, na kaisu wurin Momi. Momi ta karb'esu da daraja kam, suka yi tama hira, har Hajiya Mariya tace da Momi. Ina Angon yayi, bamu ganshi ba?". Momi, tace. "Sun tafi ziyarce ziyarce, shida Khalifa, d'azu. Tace"Ai nayi zaton jin za muzo ne, ya waske, gudun kar muzo muyi masa d'iban Karan mahaukaciya,saboda ya Samu, Sabuwa, ya ya damu gefe." A kasa dariya, a tare.momi tace cikin dariya. "Ina zai ya daku, ai da tsohuwar zuma ake magani, kuma da sabon gini gwara yabe". Hirar barkwanci tsoffin nan sun Shashi da Momi. Hakan yay min dad'i kam, sosai. Nuriyya tazo a ranar, kuma da ita muka yi ta tarben bak'i har girke girke, duk da momi ta aiko da nata daron tace a bawa bak'i. A Sati na na d'aya a gidan, Ina zaune gaban mudubi Ina taje kaina, Wanda yasha washing da retourching, yana ta shining ya kwanta lamb'am. Ba kuma wani tsawo ne da shi ba can, iya saman kafad'ata yake tsayawa. Ina kuma alfahari da a bina a hakan. Half vase ce a jikina, da under wear na siket iya gwiwa, domin kwalliya na gama nasa turarurruka na jiki, zan saka kaya na kenan, naji an banko k'ofa da sauri, an shigo. razana nayi, bawai ga yanayin under wear kawai dake jikina ba ma, saboda nasan babu mai iya shigomin d'aki kai tsaye haka ba, domin ko Ancle Fa'iz mijina iya kacin'sa falo, bai tab'a Shiga cikin d'akina ba. Wanda na yanke tsammanin zai shigo, shid'in ne ya shigo. Ancle. Sau d'aya ya dubeni, sai naga ya yi saurin juyar da kai, ta yiyu yanayin da ya ganni ne bayaso idanunsa su sake sauka a kai. Da ya shigo ya wuceni ya isa kan gado, ya zauna. Na Samu sauk'in razana, ganin shine. Naja dogon Hijab na sallata nasa da sauri domin bansan me yake faruwa ba, na sake kai duba gareshi, cike da Mamaki. Da ganin'sa kasan daga wanka ya fito. Silk d'in sumarsa da bata taru da yawa ba, jik'e take da ruwa. Zulaika ce gajera a jikin'sa, da towel fari, sol, da ya sak'ala a kafad'a. Nace. "Lafiya kuwa, Ancle?" . Kafin yace komai, k'ofar d'akin da take a bud'e ya tashi ya jawo ya rufe. Sannan Yace. "Mutum, domin ya shigo d'akin matar'sa laifine?". Na girgiza kai. "Ko kusa, my Ancle. Gani nayi baka tab'a shigowar bane" Yace. "To, yau na shigo, then so what?". Nayi shiru, Ina kallon'sa. Ya sake zama kan gadona, ya cire towel d'in da ya sagala a kafad'a ya ajiye gefe. "Sumayya, wani a bune ya faru, nake so, Kije falo ki zauna, ko da Momi ta aiko kirana, kice bananan". Toh! wata Sabuwa Inji 'yan caca. Kallon da nayi masa galala, yasan tambayace zan masa na dalili, ya katseni. "Karki tambayeni dalili. Just ki aiwatar, kyaji komai daga baya. Yanzu babu lokaci, kiyi sauri Kije" . Na ja zani zan d'aura, kasan Hijab yace. "Kisa kayanki mana, tun da kin d'ebo. Kiyi sauri amma". Bani da zab'i face bin umarnin'sa da nasan zai iya jefani a matsala babba, idan a kasamu kuskure a ka gane gaskiya. Amma k'arya kuma ba'halin Ancle Fa'iz bace, ko mai amfani ce. Tun da yau yayi kuwa, nasan da akwai babban dalili, ba kuma k'arami ba. Na Shiga kici kicin cire Hijab domin saka Kayan da sauri, duk da nauyin'sa da yake zaune a d'akin yasa nake komai a sanyaye kuma.Ko Fahimtar hakan da yayi Sai naga ma juyar da kan'sa gefe ya jawo wani littafi irin na ma'aurata zalla da Nuriyya ta sayomin yana dubawa, kamar na warce littafin, don bazan so ya karanta ba, amma bazan iya ba, sai na rabu da shi na mai da kai ga abin da ya kawo min farmaki yanzu, da ana samun a kasi tawa ta sameni. Ban gama d'aura d'an kwali bama na fito, na jawo k'ofar d'akin na barshi a ciki. Na fara da kunna kallo, domin Samun Nutsuwar yin basaja.Amma, zuciya ta cike da tararrabi take, na me yake faruwa. Fatana dai ko maye, kar ya ritsa da ni, wurin yiwa Ancle Fa!iz Mijina biyayya. Ko minti biyar kuwa, ban cika da zama ba, Sai ga Muhibbat ta d'aga labulen k'ofata tana daga tsaye k'erere, da jin isar nan da fad"in rai tace. "Yayan yana nan?". Nace. "A'a bai shigo ba ai ." Ta tsuke fuska. "To, Ina zai Shiga Kenan?". Nayi tsai, Ina kallon'ta Sai kuma nace. "Kin duba, d'akinsa baya nan?". Bata amsamin ba, illa tsaki da taja, ta saki labulena ta tafi. Na d'an ji ciwon hakan. A binda na kasa tantancewa, ni take yiwa tsakin, ko kuwa rashin ganin yayan nata. Bayan mintuna da fitarta na Shiga d'akin na sameshi, a kwance ma yake a binsa. Ya ajiye littafina can gefe, da alamu ba karantawa yayi ba, ya dan dudduba ne sama sama kawai. Nace".Muhibbat tazo nace mata baka nan, wai don Allah me ya faru ne?". Yace. "Zan fad'a Miki, Jeki d'akina ki d'auko min Kaya marasa nauyi, shirt da jins, ko T. Shirt da troser da takalmi, da under's, a Kwai sababbi da ban bud'e ba under's, su za'ki d'ebo." Nace" Tom." Da na fito a d'arare, nayi sa'a duk suna saman Momi, Ina jiyo hayaniya kuma. Na Shiga d'akin Ancle, a karo na farko. Gado ne Kawai da kwabar zuba Kaya,set, da kujerar zama guda daya. Na bud'e kwabar, duk na d'auko Kayan da ya sa na d'ebo. Wasu Kayan duk a hargitse, bayan da gogaggu a ciki. Nafi zaton wurin neman wani abu ya hargitsa. Da na kawo masa, na d'ebo mayuka da turarurruka na jiki da na Kaya, da comb nawa. Domin ban d'auko nasa ba. Yace"Sumayya kwashe turaren nan, banasa turare mai k'arfi, Sai mai sent, cool, irin nawa. Nace. "To" . na kwashe. Na fito na barshi yana shiryawa. Da na fuskanci ya gama na kai masa Karin kumallo d'akin. Tea da soyayyan plantain ne da k'wai da Khairat ta kawomin. Ya juyo yana mai gyara botton d'in riga yace. "Ke me zaki ci, da kika kwaso Break fast d'inki kika kawomin?". Nace. "Ancle, ai yayi min yawa dama, na Mutum biyu Khairat ta kawo." Yace "Duk da haka, Kije ki karya, idan yayi Miki yawa kikai kichean a ba mabuk'aci. Ni a waje zan karya ma." Ba haka na so ba, na maze amma, saboda na soma karantarsa, idan yace Bazai yi a buba, to fa a rabu da shi kawai. Na kwashe kayan da ya cire da nufin wankewa ko ba a lokacin ba. Na zauna a falo. Ya fito yace. "Zan fita, ki rufemin d'akina an jima, mukullan suna kan tebur d'in ward robe." "Nace"To, Ancle". Sai da ya lek'a tsakar gidan, yaga babu kowa Sannan yay wuf ya arce. Nayi masa a dawo Lfy, Bayan ya Fice, bai amsa ba, shi yasa nasan bai ji bane. Bansan me yake faruwa ba, amma Ina ta jiyo hayaniya a Saman Momi, da a lamu bak'ine. K'arfe takwas na dare, Ancle Fa'iz ya dawo. Dama yakan lek'oni, kafin ya wuce wurin Momi, idan ya dawo. Karfe takwas na dare Ancle , ya shigo falona da sallama na amsa, nayi masa sannu da zuwa. Yace. "Bari naje wurin Momi naga yarda za mu kwashe da ita Sai nazo na fad'a Miki kome ya faru, nasan kin zak'u. " Yafi a wa d'ya, kafin ya dawo. Na d'ebo turare cikin show glass ya shigo. Kan kujera two seater ya zauna. Nima Sai nazo kusa da shi dab, na zauna. Nace. "Nayi zaton kamanta fa" Yace. "Yaya zan manta, bayan ninace zan fad'a Miki. Ya kwantar da kan'sa jikin tudun kujera ta baya, cikin galabaitacciyar murya yace. "Don Allah Sumayya ki daina saka wannan turaren d'akin mai k'arfi. Wanda kike sawa ma na jiki sent d'insa is high. Turare mai k'arfi har kaina yake hawa." Na danne, ba dad'in da naji nace. "To my Ancle, zan daina sawa na samu air freshner Kawai mai sanyin k'amshi na d'aki. Na jiki kuma zan saka iya body spray mai sanyi, sansanya". Yace. "Koma wani iri kiyi amfani da shi, amma d'an kad'an zaki sa. Yayi a jiyar zuciya ya zarce. Dazun Salima ce tazo gidan nan. Ina wanka naji sallamarta. Shi yasa Ina jin ta hau benen Momi, ni kuma da na fito daga wanka shine nayi sauri na shigo d'akinki. Saboda nasan Momi zata tilastani da cewa,na bita Muje wurin mamanta, saboda ta turo kirana har sau uku nak'i zuwa. Tayi laushi tayi nadama sosai, ni take ta zabarin nema nazo ta bani hakuri na auri 'yarta, batasan ta makaro ba. In dai nine to Wallahi ba ta ma soma nadama ba. Sai jiyan Salima da yamma ta samu labarin aure na dake, domin mamanta b'oye mata tayi a she a son samunta Sai an nemoni an dai daita komai, Sai Salima ta Sani, saboda tasan taga katin auren ma ba k'aramin hauka zata yi musu ba. To jiya ta samu labari, ta tashi hankalin su. Ta nemeni a waya na fad'a mata a binda mamanta tayi min. Kuka ta rink'ayi min sosai, Wai banyi mata a dalci ba da tun farko na rufeta. Wai ai babanta yana raye ai shi Sai ya d'aura mana aure. Amma Yaya zanyi aure? Ina nake ta tsoma rayuwarta. Ko ina zaton zata iya rayuwa babu ni. Ke surutai kala kala. Jiya ma cikin dare ta kirani a waya tana kuka da surutai. Gaba d'aya daren jiya ban samu bacci ba fa. Kiran waya, babu hutu. Lallashin duniya nayi domin ta fahimci bawai na barta Kenan ba, Ina sonta, kuma Ina da burin auren ta, amma da sauran lokaci. Kuma auren da nayi duk Saboda ita ne, domin idan ban tauna tsakuwa a ya taji tsoro ba, al'amari Bazai gyaru ba. Amma Salima fafur ta kasa fahimtata. Da na gaji na kashe waya ta, naki kunnata kuma har yau. Shine fa kika ga tazo da safen nan, Wai mamanta tace tazo ta tafi dani, saboda ta gigita nutsuwar su." Duk da fargaba ta rufeni da jin a binda ya faru, da nima zance ya shafeni dole. Cikin taushin murya nace. "Ancle, Kayi hakuri mana kai ma. Tayi nadama fa maman nata. Kuma naga burinka kenan." Ai gani nayi, ya mik'e zaune sosai ya dubeni. "What? Nayi me? Wai nayu hakuri yanzu? Lallai yarinya baki sanni ba, labarina kike ji." A raina nace. Ban dai gama sanin ka ba. "Wa'adin da na yankar mata wallahi Sai ya cika. Ina son Salima. Ina son 'yarta fiye da zaton su. Amma wallahi ban shirya auren'ta yanzu ba, ko da kuwa za'a tattaromin kud'in masu arzik'in k'asan nan a bani a matsayin gudun mawar aurenta. Wallahi bazan aure ta ba sai wa'adin da na d'ibar musu ya cika". Nan nasan lallai Ancle Fa'iz ya wuce sanina da karatuna. Zuciyar da Kawu Sulaiman yace yana da ita, ta wuce zatona. Amma a hakan kullum zuciyta k'ara zarmewa take a son sa, duk da zahirin halayan'sa masu wuyar Sha'ani da juriya, suna dad'a tallata kan su da kan su. Wannan bai hana Soyayyarsa k'araci gaba da hab'aka a raina ba. Wuyarta mu kwana Mu tashi, nayi ido hud'u da shi, naji muryarsa kuma. Zan iya cewa, tun da daga ranar nan, gaba d'aya naga gidan sun sauyamin fuska, idan a ka cire Khairat, da Ancle Fa'iz. Amma Khairat ta d'an ja baya dani kad'an a kan da. Ta yiyu kashedi a kayi mata, saboda ko magana zata yi min zan ga bata da nutsuwa. A kan matsalar Ancle fa da Salima na zurma wannan rigima. Saboda Momi tayi iya yinta Ancle yak'i saukowa a yi sulhu shida maman Salima. Domin burinta Kawai yazo ta bashi hak'uri ya auri Salima. Shi kuma yace ba yanzu ba, bashi da ra'ayi Sai lokacin da yayi ra'ayi. Momi da kan'ta tasan halin d'an ta, idan ya kafe a hak'ura, idan ba haka ba, to lamari b'aci zai yi. K'arshe ma a yi uwar watsi, yace auren ma baza'ayi ba ya hak'ura da ita. Da wannan dalili Momi ta danne zuciya tasa masa na mujiya. Wato ido. Amma a damuwa take game da lamarin, saboda a wurinta a ke kamun k'afa, ita kuma ta kasa yin yadda suke so ga Ancle. Shi yasa Sai a Kayi haushin kaza huce kan dami, ni fushin a ka juyeshi a kaina, saboda su so suka yi ya sakeni ya auri Salima a lokacin, tun da sun zo neman sulhu. Shi kuma Ancle sun ga bashi da niyyar, hakan. Sun fahimci baya nunamin wata kulawa,ko ta aure. Domin kowa ya Sani, baya zaman minti biyar a d'akina, ballanta na wai ya kwana ciki, bayacin a binci na ko da wasa. Amma kuma babu wani fitintunu na rikici tsakani na da shi, duk da borar da na zama. Ina girmamashi, da yi masa biyayya dai dai gwargwado. K'alau muke zaune ba'ajin ko tari na na wai muna ko da da musu. Wannan shi ya zamo k'arin umda da ya had'u da na bijurewar sa ga auran sa da a ke so yanzu da Salima, a kace Ina wuta a jefani. Alhakin komai kamar gani suke a wuya na yake, nice sila. A tunani na inda a dalci basa yi min haka ba. Matsalar Auren Salima da Ancle tun kafin a San Ancle zai aure nine. Ya kuma fad'i hujjar bijirewar sa ga Momi. To don me zan zama a bar juyewa haushi? nima a barni naji da kashe wutar gabana Mana, da suma sun San da ruruwar ta. Zaman aure na da Ancle ko a suna ma bashi da takwara, ko mahad'i. Ban ware girki na ba, har lokacin tare muke yi da Khairat na gidan duka. Wani zubun ni keyi, amma Ancle bayaci momi ke yi masa nasa shi kad'ai kullum. Momi ta kirani har saman ta, naje na gurfana cikin sababben ladabi da nake mata, ko uwata albarka, domin jiki na har rawa yake, saboda tsabar biyayyar da nakewa Momi idan ta Sani a bu. Idan nasan tana son a bu ma, bana jira, Sai ta sani, yi nake. Cikin d'aure fuska Momi ta dubeni."Sumayya daga yau, bana son ki sake saka hannunki cikin girkin gidan nan, ki rink'ayin naki.Dama Fa'iz nike yi masa, Kinga iya cikinki zaki dafa. Na fad'awa Fa'iz ma zaki soma girkin ki." Nace"To, Momi". Naci gaba da tsuguno, koda sauran umarni, da naga tayi banza dani, na mik'e na janyo sanyayyun k'afafuna nayi waje. Ancle bai min zancen girki ba, momin ce ta sake kirana tace"Nayi magana da Fa'iz ya ce. Ko me kike so, ki tambaye ni, na baki, kudin girkin cefane da abin da kike so ki dafa". Abinda na fahimta, so a ke a kara nisantani da shi, yarda komai babu ruwansa dani, sai dai na tambayi momi, kuma dama ce da za a rinka samu da za a rinka gasa mini magana, son rai. Tun yanzu kenan na soma haduwa da matsaloli, kafin ma na soma samun kofar da zan dana tarko na ga Ancle Fa'iz yarda zan soma janyo raayin sa gareni ya ma soma saurarata ko a hira ne, wanda wannan aiki ne na sani ja mai zaman kansa, to ban kzi ga wannan ba ma ga wata gwaramar ta tunkaro ni, ta mutan gidan, idan a ka cire khairat kowa ma ba kauna ta da son zama na yake a gidan ba, musamman khalifa da kallon kiyayyarsa gareni yafi na kowa, to ta ina zan fara, abinda yawa wai kura ta shiga kasuwa, kwace goriba kuma hannun kuturu ai bazai yi wuya ba. Abin nufi banje koina a zuciyar Ancle ba, ballantana a sha wuya wurin rabani da shi. _Taku_ _Zainab ilyas mazawaje_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe *NI DA GIDANA* _Zainab ilyas mazawaje_ _Best brilliant interlligent writer_.... 🖋️ _Page 15_ Saboda Momi ta kula ban fiye zuwa wurinta na karbi abun bukatar da tace ba, ta sake kirana washe gari. Na durkushe a gabanta kamar mai neman gafara. Sai da ta shari lokaci kafin ta waiwayeni tana kallon wayarta, da latse latse kamar ba ita ta kirani ba, kamar yarda ta saba yimin, sai can a dakile ta waigeni. "Um, kina sane da cewa nace kome kike bukata ki na girki da bukatun yau da kullum kizo wurina, domin Faiz ni yake ba kudi duk sati na bukatun gidan nan, har kayan a binci da komai". Nace. "Momi, ai ba sai na karb'a ba, tun da ina da kayan garata da aka kawo ni ita, da komai na girki." Ta zabgomin wani kallo na baki isa ba. "Na Sani d'iyar tajiri, 'yar na gada. To, hak'k'in mune ciyar dake. Babu ruwan mu, da wanda aka kawo daga gidan tsoho. namu za'kiyi amfani dashi." Ni kam mamaki ya kamani ma, na menene a bin zafin a ciki. Ai duk domin a amfana dashi aka kawo garar. Na sanyaya murya nace. "Allah ya huci zuciya, Momi, ayi a fuwa, tuba nake. Zan rink'a karb'a.Duk da haka komai na aikin gidan nike yi. Wanke wanke Shara, wanke band'akuna da kayan k"amshi. Amma fa banyi fari ba, bata hanani ba dai. Khairat girki ne nata. Muhibbat Sai taga dama take sa mata hannu, kuma Momi bata yi musu gyara ba. Daga nan damuwa ta soma samun gurbi a Zuciyata. Gani da yalwar kud'i, ga Kayan binci a store, da a ka kawomin komai a kwai, amma wai kullum Sai naje wurin Momi karb'ar komai, kuma idan naje, Sai an min wulak'anci kafin a bani, musamman idan Khalifa da Muhibbat, suna wurin. Habaici, da zambo da tsaki, nafi shansu ma. Gaba d'aya Momi ta canza min. K'iyayya muraran ta fito min da ita. Ko kirana tayi, ban ji ba, ko na kuskure wani a bu, to zagine. Banza ,shashasha, sauna, d'iyar matsiyata, wannan sunaye nane,da Momi ta rad'amin daga baya. Sam bata Kiran Sunana ma. Kullum a mai laifi nake,da nayi da banyi ba, Sai an k'irk'irar min. Khalifa da Muhibbat sun fi takuramin. Bani da 'yancin fitowa tsakar gida Sai habaici, harara da tsaki. Amma Khalifa idan shi kad'ai ne, kulani ne kawai bayayi, sai harara da tsaki, sai dai idan Muhibbat tana kusa, ya samu 'yar uwa Sai suyi min taron gayya. Khairat idan tana kusa, a fuska zanga ta nuna damuwa sosai a kan a binda suke min. To sai dai bata da yarda zata yi da su, sun girmeta. A Kwai Sanda tayi magana a kan bai dace ba a binda suke, suka hayayyak'o mata. Khalifa ma saura k'iris ya kai mata duka Muhibbat ta Kare. Yace mata a gabana. "Wallahi, kika sake yi mana shishshigi jikinki Sai ya fad'a Miki. Kuma Sai na fad'awa Momi, zagon k'asa kike mana." Tun daga lokacin, Sai take jan jiki, da taga sun soma yi min iya shege. Sunan da suke kirana da shi, wai 'Yar jiran k'ofa. A bin nufi, ni Salima nake yiwa gadon wuri, kafin tazo. Wato bani da wani amfani face kula da muhalli suke nufi. Jin sunan ya zamemin jiki, domin suma shi suka rad'amin ko kirana za'suyi, bayan na Momi da nake ji da shi kuma. Duk da naga gabar suke dani ta sosai, ni har gaishesu nake, idan basu kulani ba, amma babu sauk'i wai ciwon Arne. Ko sallama nayi musu basa amsawa ma. Rannan Khalifa ya biyo Muhibbat a guje suna wasan banza, ni kuma zan wuce rik'e da fulas da kofunan tea biyu na glass, na fito daga kichean zanje na wanke su, Muhibbat da gayya ta bangajeni da k'arfi na kife, fulas ya fashe da kofuna, ni kuma bakina ya d'an fashe na k'ume da garu, kafin na kife amma Muhibbat ko ta d'aga kai ta dubeni ballantana tace sannu. A gaban Momi, aka yi, domin ta lek'o ta Sama tana yiwa Khalifa magana, amma bata yi magana ba, kuma ko sannu. Hak'urin dai da nayi ban tanka saboda naga kullum k'ara d'aukar zafi a ke yi dani. Ta yiyu, so a ke na tanka a yi b'atacciya. Domin ko washe gari da naje gaishe da Momi, bayan ta amsa da k'yar, na mik'e Sai Muhibbat da take kusa da ita taja tsaki tace. "Aikin banza, isar ba'a isa ba. Mace Sai nacin jarraba, ba'a sonki, amma kin manne." Ban d'aga kai na dubeta ba, na fito. Momi naji. Sati na biyu Kenan da aure na da Ancle Fa'iz. Ji nayi komai yayi min zafi. Baki d'aya naji gwara nayi komawa ta makaranta, duk da hutun da na dauka da saura kwana biyar ya cika. Babu wani a bu da yake d'ebemin kewa a gidan. Ga kuma damuwar wulak'ancin da a ke yimin. Ni kuma bazan iya fad'awa kowa ba nawa, ballantana Ancle Fa'iz da dangin sa ne kemin. Nasan bai Sani ba, tun da komai Sai bayanan a ke min, duk da ba wani sona yake ba, ballantana nace suna shakkar ya Sani ya d'au mataki, Sai dai kawai sun San shi mai zafi ne da baya d'aukar wargi ko wani iri, ko yaga anyi wani a bu da bai da ce ba, batare da ya taka zazzafan burki ba. Sam hutun ma da na d'auka na aure ma nayi da na Sani, domin bai min rana ba, Sam. Sannan babbar damuwa ta kawu Sulaiman yak'i zuwa ballantana naji sanyi. Domin ganin sa da hirar sa mai kwantar min da hankali, kan mantar dani damuwa ta, da maraici na. Ancle Fa'iz ya kasa bani lokaci, ko yaya da zan jarraba salo ma na soma jan hankalin sa gareni, ko da daga hira ma gajeriya a bin ya faskara. Kullum cikin uzuri yake, idan na nemi hakan. Banyi zaton zai yi tsaurin samuwa haka ba gareni. Amma kuma duk Sanda zai fita, ya kan ce me nake so ya sayo min, nace babu komai.Abinda nake son ya gaza.Komai ya sayo d'aurina dabam. Kuma komai ya sayowa su Khairat sai ya sayo min. Wannan ya, tabbatar min rukuni guda ya a jiye mu. Randa na hak'k'ak'e zan fad'a masa komawata makaranta, ranar ya shigo da robar madarar roba biyu a hannunsa, ya mik'omin d'aya. Daga tsaye bai zauna ba, Sai yace. "Bari naje na nemi Ado coach d'in mu, naji ance yanzu yazo bana nan, ba domin shiba kwanciya zan yi na gaji". Ban yi mamakin gajiyar da yake yawan cewa yayi ba, saboda nasan Boll ya buga, ko training. Amma uzurin sa na kullum da baya yankewa, shi yafi ban mamaki. Har ya juya, Sai ya dawo yace min. "Ki rink'a rufe k'ofarki da daddare Sumayya. Naga har na kwanta a bud'e take, me yasa?". Nayi masa wani salon kallo nace. "Bacci ne, yake kwasheni ban Sani ba." Yace"Yace "Saboda me?". Nace. "Saboda bani da a bokin hira" Ya gyad'a kai."Kin raina a bokan hirar takine. Gaki da book's na gani, ga kayan kallo ai sun isheki." Nasan jahiltar manufata yayi, yana sane. Nace cikin narai narai da ido. "Wad'an nan ba'a bokan hira bane face d'ebe kewa. My Ancle kaifa kace na rink'a kallonka kamar Ancle Sulaiman, amma Sam baka bani lokaci irin nasa. Baka hira dani irin sa. Anya za'ka maye gurbinsa? Kullum Sai kace kana da uzuri. Na Shiga d'an Kukan shagwab'a kamar na gaske. Ni Wallahi bazan iya wannan rayuwar ba. Kullum ni kad'ai kamar mayya.Karabani da Ancle d'in dake yi min hira yana sani dariya da wasan nishad'i, kai kuma kak'i hira dani. Ni gida zan tafi yau ma". Yarda nayi zaton zai d'an lallasheni ko yaya, ai sai ya bud'emin wuta. "Maza maza tashi, ki tafi, karki bari k'uda ma ya rigaki. Ni zaki fad'awa wai damuwar sulaiman gareki? to duk Soyayyar da yake miki ai bazai iya aurenki ba, Kenan no reason da zaki rink'ayin wani prouding a kan'sa har da wata tutiya. Kuma tun da haka ne me yasa baki zauna can ba, yayi ta sangartaki yana shagwab'aki da soyayya, karki auri kowa, tun da, Soyayyarsa da kulawarsa ita kad'ai ke gamsar dake." Na yarda Ancle Fa'iz ya iya yanka maganganun ramuwa na cusa haushi, idan aka yi masa kan kara shi kuma na itace yake yi. Raina kam ya b'aci da jin furutan'sa. Kenan babu inda zanji San yi a gidan. Da sauri na mik'e na Shiga d'aki na janyo gyale na da takalmi da jaka. Na fito. bada niyyar fita na fito ba, jarrabawa zan yi naga zai barnin na tafi, kuma idan ya barnin ficewar zanyi, domin zuciyata wani irin suya kawai takeyi. Yana nan zaune in da na barshi. Ya bini da kallo, Yayin da na yafa gyalen, nasa takalmi, nayi kamar banganshi ba, nazo zan fita. Wata tsawa ya dakamin har Sai da jikina ya d'au rawa. Bana ko kokwanto su momi sunji, kuma nasan ransu zai yi fari tas. Ya nunani da yatsa. "Wallahi, kika tsallake tudun k'ofar nan kika fice Sai kin raina kanki." Nayi tsuru tsuru dani, kamar wacce ta yiwa sarki k'arya. Sai kuma na dawo turus na zube kan kujera na Shiga rera kuka na rufe fuskata da gyale Ina ta sheshsheka, a zahiri rantsewa za'ayi na gaskiya ne, amma a bad'ini na k'arya ne. Ina k'yallaro shi, dai jijjiga kai yake, yana Jan kwafa da ina Kukan, tabbas naga 'Yar damuwa a tare da shi, naji yace. "Haka siddan Ina zaman zamana na jawa kaina d'aukakkiya. Jin furucinsa, Sai na k'ara sautin Kukan sosai. Ya dubeni yaja tsaki, tsam Sai naga ya mik'e yace. "Kyayi ke kad'ai ." Yasa kai ya fice. Yana fita na tashi na Shiga d'aki nasa kayan bacci. Kyakykyawar riga ce silk mai k'aramin hannu doguwa, nasa da hular bacci mai kyau. Na kishingid'a bada niyyar bacci ba tukun. Damuwar da naga Ancle ya d'an Shiga sanadin Kukan da nake yi da yake zaton gaskene ta farantamin. Da wannan na soma fahimtar wani sirri nasa da zan iya cin nasara a kan sa wani lokacin. Sam bayason a na yi masa kuka musamman na wata damuwa haka na fuskanta. Ban sa rai da zai sake waiwayata ba a daren, Sai jin sallamarsa nayi a falo yana Kiran Sunana. "Sumayya! Sumayya!!. Naki amsawa ku ma nak'i fitowa, domin so nake ya shigo d'akin. Kuka ma naci gaba dayi kamar dama can aikin kukan nake yi. Babu shiri ya fad'o d'akin. Da alamu shirin baccin yayi Shima. Riga ce ta bacci yasa da dogon wando pure cotton mai taushi, irin kayan. Sunyi masa kyau ainun. gaskiya Sai da ya tsaya a kaina na sakanni yana kallona Kawai, Sannan ya tsuguna a gabana, murya k'asa k'asa yace. "Wai Sumayya menene damuwarki? haka kawai kina neman ki d'agamin hankali. Me kike so ne?". Cikin shagwab'abb'iyar murya nace. "Bakaine kace bazan tafi gida ba." Ya kuwa sake k'uluwa yace. "Bazakije gidan ba na hana,kuma ko me za'kiyi. Ke ko kunyama ba kyaji k'atuwar budurwa kamarki ki rink'a acting irin na yara, k'anana, har kina kuka saboda sangarta ko? Ko da yake goyon kakace dole kiyi. Ga Sulaiman kuma ya sangartaki. To Any way ni bazan d'auki sakarci ba wallahi, tun wuri ki Shiga taitayinki." Nayi dib! Ko uhum ban sake cewa ba, face mitsitstsike idanu. Shiru ya ratsa wurin na mintoci, Sai Iskar sama dake motsi tana wulwulawa tana bada iska madaidaiciya mai dad'I, sakamakon d'an yanayin zafi da ya shigo a tsukin. Ko tausayina yaji, Sai kuma ya tausasa murya Maimakon kausasawa da fari. "Sumayya, ni banga a binda zai sa ki rink'a damun kanki ba. Da a ce tun farko na munafunceki, to shine za'ki damu kanki, idan kika ga wani sauyi. Amma haka siddan ki rink'ayimin tuhumar da gangan? Me na yi miki? Kullum fa Sai na tambayi me kike so, menene damuwarki, amma duk ban fita ba. Kinsan manufar auren mu, kin a mince, to me yasa zaki rink'ayi min bore bayan anyi?. Naga shiru ba mafita bace, gwara na fad'amasa burina ko zanyi sa'a ya a min ce daga nan k'ofar farko ta bud'e. "Ancle nifa buk'atata ka rink'a yagar min lokaci, muna hira ko yaya, na samu mai debemin kewa. Su khairat da kake cewa muyi hira basu da lokaci kullum suna kan hanyar makaranta, Boko da islamiyya. Dare kuma Kowacce d'akinta take Shiga, saurin bacci ne dasu. Momi kuma kunyarta nake ji, bana iya sakin jiki muyi hira sosai." Nayi dace yace. "To, zan jarraba yarda kike so, amma fa ni ba ko yaushe nake son hira ba, karki zamemin BBC, uwar watso kanun labarai". Dariya furucinsa ya bani, har nayi ta fito fili a hankali, saboda yanayin da ya furta. Shima sai naga yayi 'yar dariyar. "Ke dai 'yar tawaye ce rigimammiya, mai fuska biyu kuma. Kin rikita mutane da kuka, kuma kin dawo kina yimin dariya ko? Warki ne ni dai dai k'ugun kowa." Yanayin da muke ciki, da yanayin lokacin, ya sanyayamin zuciya sosai. Naso mukasance daren ranar da faranta ran juna irin na ma'aurata, koda iya hira, amma Ina!.Mikewa Ancle yayi. Nikuma na tuno da a binda nake son ce masa. Nace"Am, Ancle" Ya juyo a hankali. "Ina jinki Sumayya." Nace. "Gobe nakeson komawa makaranta. Yace"Sai yanzu za'ki fad'amin?" Nace"To, na bari, Sai Jibi? ". Yace. "No, kije goben, tunda kin niyyaci hakan. Daga nan yayi min Sai da safe ya fita. Inajinsa ya b'amemin k'ofar sosai. Na kuwa kasa bacci. Da nayi juyi, Sai na hango Ancle Sanda ya tsuguna gabana, ya zubamin kyawawan Idanuwan nan nasa masu hasken blue masu kashe gab'b'ai, yanamin surutai a hankali. Gaba d'aya kasa dai daita nutsuwata nayi a lokacin. Komai nasa mai ruruta wutar k'auna ce, ga ma'abocin kallonsa. Nasan shi a lokacin babu komai a ransa, burinsa ya shawo kaina Kawai. _Wasa farin girki_ _Muje zuwa_ _Zainab ilyas mazawaje_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe *NI DA GIDANA* Zainab ilyas mazawaje _Best brilliant interlligent writer...... 🖋️ *Page 16* Ranar wata alhamis, Ancle Fa'iz ya shigo da daddare ya sameni ni kad'ai a falo zaune nayi shiru. Mutan gidan duk suna saman Momi ana ta shan hira, da kallon TV. Ya shigo ya zauna, bayan nayi masa sannu da zuwa yace. " Sumayya wai zaman kad'aici menene ribar sa? sai kiyi ta jan jikinki da mutane, kina ware kan'ki why?". Na d'aga idanu na dubeshi bansan me zance ba. Shi duk zaton sa nike jan jiki da mutan gidan, saboda baisan komai da yake faruwa ba. Na yarda a je a hakan, gwara ya zargenin da na zama nice ta farko da zan soma kai masa k'orafi a kan Maman sa da 'yan uwan sa. Musamman Momin sa da yake ji da ita matuk'a. Na daure nace. "Kasan fa ni kunyar Momi nake ji." Yace da sauri cikin dan fushi. "Kinga don Allah ki dai na irin wannan gida dancin. Kunyar lafiya? Shike nan sai kice lalllai sai dani za'kiyi sabo, ni da ba mazaunin gida ba? ki gyara wannan hali naki please, in dai kina so mu shirya". Nace "To". Laifin da ba nawa ba na amsa. Naci sa'a ranar ya zauna wurina, ya d'an d'ebemin kewa, nafi zaton tausayi na bashi, na kad'aicin da nake ciki babu kowa. Amma dai hira ce jifa jifa, me kama da tambaya, kuma yawanci a kan karatu na. Duk da haka yafi babu, domin ko babu komai, muryar Ancle sanyaya zuciyata take, tamkar kaskon da yasha wuta, a ka tsoma a ruwa, duk da kunyar kallon sa nake yi, musamman idan ya sani a gaba. A hankali, a hankali kusanci da jituwa ya soma shiga tsakanina da Ancle Fa'iz. mukan jima muna 'yar hira, musamman da daddare, Saboda lokacin yafi zama a gida. Ya kan jima a falona, amma kallo yafi yawa a kan hira. Ancle Fa'iz baya son kowani film Sama da kallon boll , Sai film d'in china. Dole na koyawa Zuciyata son,su duk da bana k'aunar ganin su, basu dameni ba. Amma har kud'i nake sawa na sa a turomin a memory da yawa saboda shi. Duk da Shima d'in yana da wasu da yafi gani a waya. Duk wani a bu da na san ya naso, tanadar'sa nake yi na tarbeshi da shi, saboda sa'ar da na samu yana shigowa falona ya zauna. A bin dai da bayaso nake yi, shine narka da shagwab'a. Narka da shagwab'a nake yi masa muraran cikin mu'a mala ta da shi, musamman idan ina son yayi a bu yak'i. To shi kuma wannan ce ba ya so, domin bayan k'orafi har hantarata yake yace yi. Yace. "Ke tafi can ki bani wuri, bani son tab'ara. Wani lokaci ya cuno baki yace. Duk Sulaiman ne, ya sangartaki ya shagwab'aki saboda mugunta, domin yasan gidan wani za kije bashi zaki k'warzaba ba.Rannan na kada baki nace " Ancle kaifa kace na rinka kallon ka a matsayin Kawu Sulaiman, kuma shine na maisheka hakan wurin muamalar da nake da shi, amma sai kuma kayi tayi mun fada kuma? ". Na karasa furucin cikin 'yar shagwaba. Abinda dariya sai yayi shiru mukus bayan da yayi min kallo daya kawai. Mikewa kawai yayi ya fice, nasan rasa amsar bani yayi. Wani zubin kuma idan ina zuba masa salon shagwaba a hira ya kan kasa yin shiru ya kance "Bari dai na baki wuri ba dani ba wannan tab'arar, wanda ya sangarta ki, shi zai iya d'auka. To nan na kaishi gargara Kenan, domin ficewa yake ya barni. Wani zubin kamar cikin 'yar tsawa zai ce min. " Za ki soma shashancin ko? Ki shiga hankalinki Allah, ko ranki ya baci, da girmanki ba yarinya ba, ki rinka irin wannan sokwanci, ki kiyayeni fa". Bani yin fushi, sai nayi murmushi kadan na sunkuyar da kai na rabu da shi, sai wani jikon, saboda idan naci gaba, tabbas nasan ran nawa zai baci. Kuma yafi daukar zafi idan bashi da walwala na fahimta, shi yasa na karanci yarda zan tafi da shi a komai, game da yanayin da yake ciki. Duk da bayaso, ni kuma ban daina ba, domin ni kuma ta haka nake so na Shiga jikinsa da zuciyarsa mu shak'u. To daga baya ma sam daina k'orafin yayi da ya gaji. Sai dai yayi banza da ni baya yin magana, idan na kai shi kuma bango ya mik'e kawai ya Fice, Sai yak'i shigomin kuma Sai yayi min ban iska na wani lokaci, ranar da na kai shi gargara Kenan. Ban ja baya da komai ba, saboda damar da na samu daga gareshi, nayi ta shigo masa da abubuwa iri iri,duk da ina shan kyara, wani zubin, banayin zuciya, domin kuwa ni mai ne mace kuma wataran bazai yi ba, musamman idan shakuwa ta soma shiga tsakanina da shi. Wata sa'ra dana d'auka, idan zai yiwa kan'sa a bu, Sai nace Sai yayi min, ko munyi tare. Yana da wani a bin yanke farce mai kyau, duk ranar juma'a yake yanke farce da shi. Na kance ya kawo nayi masa Sai yak'i. Ni kuma Sai na takuramasa nace Sai yayi min ban iya ba da kaina. Farkon randa na soma damun sa da magiya, ya jefomin kallon tara saura kwata yace. "Wai da can wa yake miki? Ko domin Samun wuri?. Nace"Baba Talatu ce. Yanzu kuma bani da kowa Sai kai Ancle, ka taimaka." . A ranar fafur yak'i yi min. Amma daga baya ya soma yi min, saboda bak'in naci. Ni bana zuciya, Sannan ga binbinin magiya da kwantar da kai, ta haka naci nasara kan Ancle da murd'ad'd'en halin'sa. Randa zai soma yanke min farcen ma, sai da yaja tsaki har sau uku, irin na na takura masa, kafin ma na kara sa mika hannu ya fizgo hannun nawa ya soma da sauri da sauri, ni kuma wani sanyin dadi naji mai sanyaya zuci har ya gama, idanu na na kansa, banki mu dawwama a haka ba, fuskar sa a daure duk bai san abinda nake ba. Yana gamawa yace. "Tashi ki bani sarari, tun da bukatar ki ta biya". Na narke murya, ina yi masa wani salon kallo nace ." Ancle baka yi min fa na kafa ba". Ya zabgamin wani kallo, kawai bai tanka ba, ni nasan amsar, shi yasa nayi gum ban kara tofawa ba, na kunshe dariya ta a ciki na mike don ficewa daga falon nasa, na fahimci kamar ya fahimci dariyar da nake dannewa, shi yasa naga ya cira kai ya dan bini da kallo, daga bisani ya girgiza kai a hankali irin na na buwayeshin nan, ya mai da kai ga karasa yankan farcen sa. Babbar nasarar da na samu ta ya soma gajiya da naci na ya na dan yi min a bu, yasa na k'ara k'aimi. wani lokaci ni da shi a falona, na tsiri tsifa saboda ganin arhar damar ga Ancle Fa'iz. Da. na soma nace "Ancle don Allah tayani tsifar kai." Ko kallona bai yi ba, a fusace yace. "Sumayya kina nema fa ki raina ni da yawa. Nine ma zan yi miki tsifa?." hakuri na bashi a nan, saboda naga ya d'auka da zafi. Ban daddaraba wani lokaci muna tare muna kallo na sake tsirar tsifa. Ina cikin yi nace. "Wash!. Ya waiwaye ni. "Me ya faru?" . Nace"Wani ciwo ne a yatsana da naji, garin tsifa gashi ya yanki wurin". Yace"Garin Yaya kika ji ciwo?". Nace "Jiya ne ina yanka nama". Yace" Sannu, cikin dan tausayawa, zaton sa gaskiyane, yace "Ya kamata ki rink'a kula." Na faki idon'sa nayi murmushi. Nace "Ancle don Allah ka tayani, kaga gobe mai kitsona zata zo, kuma ciwon hannu na bazai barni na Karasa tsifar ba. Please za'ka tayani my Ancle?". Ga mamakina mai makon ya fara da fusata yarda ya bayi min, sai naji ya ce. "Sai dai nayi miki aski, ni shi na iya Kawai." "Haba dai aski. Yaya zan yi aski ina mace dani." Naci gaba da marairaicewa. Yace"Sumayya wai ni bawan kine kome?". Na fik'e murya irin ta d'a,a nace" Haba! Haba!!. ai ko a shirin wasan kwaikwayo, dole a ce da mijin iya Baba. Darajojinka sun girmi haka tuni, mijina, ba domin na isa ba, sai don larurar nan, kuma nasan kai mai tausayine fa". Ya sassauto, domin naga ma ya d'an Saki fuska. "To, nawa za'ki bani na Lada?". Na marairaice. "Haba, my Ancle. Ina Daughter guda sukutum Sai na biya" Yace "Idan baza'ki biya ba, to kisa hak'uri kuwa." Na Shiga magiya da naci da shagwab'a duk dai, babu shirI ya fizgi kibiyar dake nake mik'a masa cikin fusata. "Wannan Yarinyar wallahi da ace kina da maita, kika kama kurwa ba zaki saki ba, daya zan miki, daga shi babu k'ari". Banyi fushi ko kusa face 'yar dariya ma. "Na yarda wallahi, mai shirin zuwa sama ko takarda ya taka ai ya rage". " inji wa babu in da yaje, kawai zance ne". Yace cikin bani amsa cikin kosawa, don har da 'yar harara ma, ya fizgi kibiyar daga hannu na cikin fusata ya soma. Yana kan kujera ina gabansa a kasa. Daga d'aya Sai da a ka tafi uku, kuwa, saboda naci na. Amma yanayi yana dunguremin kai. A raina fad'i nake, aje a hakan, naci nasara, tun da ka samu, kazo hannu, hakan yake kuwa tayani tsifar ya zame masa k'ara'i, ko ba yawa, ina shan dai sababi, amma Sai na jure. Wani lokacin littattafan makaranta na na kan kwaso nace ya koyamin wasu a bubuwan. Zai koyamin na gane, amma Sai nace bangane ba, domin mu ja lokaci. Sai Nasha fad'a kafin ya sake. Duk Ina yin haka ne domin na Shiga jikinsa, da rayuwar sa, mu k'ara shak'uwa. Kuma bana yarda na zauna nesa da shi, ko tazara kad'an bana bari, jikin sa dab nake rakab'uwa kamar 'yar kyanwa kullum in dai ya zauna. Farko randa na soma yi masa hakan, matsawa yayi. A wayance muna hira na kuma matsowa jikin sa. Ya sake dan matsawa, a na uku Sai yace min. "Wai duk wadatar wurin nan Sai kin matsamin Sumayya?" . Murmushi nayi, nayi masa Farr da ido nace"To, ya kake so nayi? bani da kowa yanzu da yafi kusanci dani Sama da kai. Idan ban rab'u da kai ba, Ina kake so naje?". Bai tsinkamin ba, ya maida kallon sa ga mutuniyar tasa, wato boll. Wannan damar tasa na sake shigar da wata. Sai muna zaunen, Sai na rink'ayin layin baccin k'arya, Sai nayi luuu! na zubo jikin, sa, har sau uku Ina yi, yana d'an tureni. Nan ma da fari yayi k'orafi yace. "Wai menene haka ne Sumayya?" Nayi firgigit Ina mitstsike idanu. "Me ya faru? Menene Ancle.?" . Kamar bansan komai ba nayi. Mik'ewa yayi yace "Na lura kora da hali kikemin. Bari na tarkata na barmiki wurinki kafin kiyi min kora da kara." Dariya ta cikamin ciki fal! amma ina bari ta fito zai d'ago komai, shi yasa na gintse a bata. Nan ma tun yana mita har ya zame masa jiki, ya rabu dani, ko nayin baya tankamin, kuma baya janye jikinsa, Sai ya mai da idon sa kan kallo Kawai, domin kallon ke sawa ya jima sosai ma a falona. Domin ni nake samo irin film d'in da yake so, har na boll masu tashe. Duk domin na ja hankalin sa ya rink'a jimawa sosai. Shi yasa har k'arfe d'ayan dare yana kaiwa. Wani lokacin ma bacci zan yi, shi zai tasheni idan ya gama kallon. Wani zubin shi zai yi bacci, ni zan tashe shi. randa ya gaji kenan idan ya buga boll. Kuma duk dare, Sai ya koma d'akin sa, bai tab'a kwana a wurina ba. Tun daga ranar da nayi wa Ancle Fa'iz gyaran d'aki ya zame min jiki. Kullum Sai na Shiga nayi masa gyara,domin bai karb'i mukullin d'akin ba da na cira, yana wurina. A bu d'aya yafi damuna, nake gwagwagwar juriya. Shine na yarda Ancle yake yawan yin waya da Salima, kuma a gabana. Sautari ita ke bugo masa, kuma ya amsa ya biye mata a falona suyi ta hira. Ko Ancle baisan ina son,sa ba, bai kamata yayi min haka ba a zatona, tun da yasan aure mu kayi, dole zanji babu dad'i. A binda Zuciyata ta bani kawai, Ancle Fa'uz bai d'auki auren mu a bakin komai ba, face aure ne kawai na wata manufa, mai wa'adin k'arewa. Sai dai na lura, Salima tana cikin damuwa ainun na aure na da Ancle Fa'izu. Domin Kusan kullum idan suna waya, a lallashi da ban hakuri yake k'arewa. Sababbun kalmomin da yake fad'a mata har na haddace sune. "Kinfi kowa sanin matsayinki a zuciya ta Salima. Wallahi sonki da k'aunarki babu a binda ya gutsiresu, suna nan. Kiyi hakuri lokacin zai zo, kamar yanzu ne. Aure na dake babu fashi, za'ayi in Sha'Allah. Ki soma kiran kanki ma matar Fa'iz." Idan hirar tayi tsayi tashi yake ya fice da wayar suna hirar soyayya, bazan sake ganin sa ba, Sai safiya. Kishi sosai nake ji, amma danne zuciya ta nake yi, kar nayi wa kaina gurun gund'uma. Domin sautari, nuna matsanancin Kishi, kan sa mace, tayi a sarar wanda take kishi a kan'sa. Ina ga ni kuma da har yau ban mallaki zuciyar sa ba?. Ancle Fa'iz, har yau bai je Kiran da maman Salima ke aiko masa ba da sak'on yaje ba. Na lura kuma bashi da niyyar zuwan ma a kusa Sam. Tayi aike har ta gaji. Nasan kuma ko da kanta tazo bazai saurare ta ba. Kuma ko kunya bai ji ba, ga 'yarta suna tare kullum a na shek'a soyayya a waya. Ancle Fa'iz da bam yake. Na gama shirina tsab na makaranta. Na rufo k'ofa, na nufi d'akin Ancle Fa'iz a karo na uku yana ciki tun da na aure shi. Da safen da na Shiga d'akin Ancle Fa'iz, haka kwance yake kamar mai bacci, amma da nayi sallama Sai naji ya amsa. Na zauna kan wardrobe gajera dake jikin gadon, na, fara da gaisheshi. Nace kuma."Ancle, zan tafi makaranta." Ya bud'e idanu a hankali, ya mik'e ya tashi. Ya nufi sib,ya bud'e ya k'irgo kud'i jikin kyauro sabbi fil, ya zara ciki ya mik'omin. "Ga kud'in mota dana kashewa." Nace"Wallahi, kabarshi Ina da kud'i da yawa." Zan masa gaddama, a karo na farko, ya lalubi tafin hannu na, ya mannamin kud'in ciki, ya dunk'ule. Yace. "Ungo nan malama, hak'k'inki wuyana yake, I don't care, a bout, you have money or not." "Na gode, Ancle. " Na fad'a a ladafce. Lokacin na kula da irin iskar da ya sakarwa kan'sa. Ga fankar tsaye, kusa da kan'sa ga fankar Sama, Sai kad'awa take. Kuma ya saki k'arfin'ta. Nace"Ancle Fa'iz iskar nan fa tayi maka yawa." Bayan ya koma kwance ya bani amsa da cewa. "Tayi min kad'an ma." Nayi dariya a hankali nace. "Shikenan,Kawai Sai a huda bango a k'ara Maka da A C." Ya rungume fulon da yake kwance sosai kafin yace. "Wannan a bune sassauk'a tun da Ina da Hajiya kamarki, Sai kisa a yimin a kusurwoyi hud'u ko?." Murmushi nayi, cike da jin dad'in zolayar da yayi min, ban taga ba kuma saboda sauri nace. "Na tafi Ancle." Yace. "A dawo lafiya." Momi kuwa da nayi mata sallamar zan tafi makaranta bayan gaisheta, bata cemin ko cikan ki ba. khairat ce tayi min a dawo lafiya, a tsakar gida. Muhibbat tsarabar harara na samu. Khalifa baya nan shi. Abban su Fa'iz ma a waje na sameshi na gaisheshi har k'as nace na tafi makaranta Abba. Addu'a mai kyau yayi min.Mutum ne mai kirki da kyautatawa na lura. Ga shi da sanyin zuciya sam ban tab'ajin ya d'aga hak'ark'ari ga kowa ba, Sai dai na jiyo muryar Momi. Ina yawan jin hargowar fad'anta ga Muhibbat. Ita ma Kenan. Komawata makaranta, na samu sauk'in damuwa. K'awayena suka yi ta murna dayi min shak'iyanci kuma. Abubuwan da suka wuceni tuni na mai dasu, saboda a minai, gashi ni kuma akwai himma da fikira wacce baiwace daga ubangiji. _Tabbas Sumayya ta soma samo bakin zaren sakarta, amma bamu sani ba, zai tsinke ko zai tafi dodar ga irin sakar da take so tayi_ *Taku* _Zainab mazawaje_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe. *NI DA GIDANA* *Zainab ilyas mazawaje* __Best brilliant interlligent writer_ ........ ✍️ *Page 17* Ranar litinin sai yamma Lis ni da gida. Sai naji na sarara a raina a kanda. Sanda na dawo daga makaranta, Kichean nake shiga na dafa a binda ya samu, nayi shigewata d'aki, idan ba alwala ba bana sake fitowa. Amma duk a binda na dafa, ina kaiwa Momi. Bata tsinkamin, amma sai na a jiye gefe. Bansan yaya take da shi ba. A lokacin babbar damuwata na samu kulawa koyaya daga Mijina, kar abin yayi min yawa wai shege da hauka. Cikin nasara na soma samun kuwa. Domin Ancle yana d'an zama a falo na fiye da da, muyi 'yar hira kad'an, da sai dai mu zauna kawai muyi jugum jugum, ko shi naga yana ta chat a waya, kuma nasan da Salima ne, sai yayi kamar ma ya manta da ni a wurin. Da abin yana da muna daga baya sai na dai na sawa kaina damuwar, domin naga ba mafita bace. Ancle baya jimawa dai sosai ma a falona idan ba wani kallo na kunna da yake so ba. Kuma bai fiya yi min hira ba, Sai dai ni. idan kuma na cika jan shi da hira, Sai yayi min shiru, nayi ta zuba kamar kun nan niyar rediyo baya tagamin. Idan hirar ma tayi tsayi, Sai kawai naga ya tashi ya fice. Hakan na nufin na dameshi da Surutu kenan. Da na fuskanceshi, sai nake binsa da salon halinsa. Da naga yayi shiru ya daina tayani, ko bani amsa, Sai nima nayi shiru. A hankali a hankali na soma sanin Ancle Fa'iz. Me yake so, menene bayaso. Kuma hakuri da kwantar da kai yasa na soma fahimtar. Ancle yana da wani irin hali da raayoyi da ya bam bamta da na wasu mazan, baison turare mai tashi, sai mai sanyi can kasa, baison turaren wuta na daki sam, ko za asa sai dan kadan sosai da baaji sai sama sama, haka ma air freshner nunawa yayi baiso ta yi yawa sai kadan. Sannan baya son k'unshin zamani da ake yayi, yanzun. Bansani ba, Sai bayan nasa an zo har gida an rangad'amin.hannu da k'afa, marun da bak'i na fulawoyi, yayi kyau ya zanu. Amma yana arba dashi yace. "Wannan ai b'ata jiki ne,menene a bin Sha'awa game da wannan shirmen." Nace"Kwalliya cefa ta mata Ancle." Yace"b'ata kwalliya dai, Ina a bin burgewa a ciki?". To kwalliyar fuska ma ta mata, baya so Ancle Fa'iz. Ranar wata lahadi banje makaranta ba, bayan kwalliya ta situru nasha make up.powder eye liner, da eye shadow ,lipstic da white lips da jagira tsararriya, da tasha shape. Wallahi kuma nayi kyau har ga Allah. Amma Ancle yana shigowa da ya kalli fuskata ai sai naga ya kwashe da dariya. Dariya sosai da ban tab'a ganin yayi ba. Zatona daga can wurin su Momi ya taho da a bar'sa, ai sai na ta yashi, ina yi ina tambayar ba'asi. Abin gwanin bandariya wai yaro ya tsinci hak'ori. Yace"Kema dariyar kikewa yi wa kan ki?". Nayi harr da ido, Nace. "Kamar yayafa?'". Ya sake duban fuskata, ya tintsire da dariya. "Kinga fuskarki kuwa? Sai kace wata sabuwar aljana?". Tabbas furucin'sa ya sosa min rai, amma na daure zuciya ban nuna ba, ko furtawa ba. Cikin salo ma na kamar shagwab'a nace. "Kai Ancle, me fuskata tayi?". Yace"Kin cikata da shafe shafe da yawa. Ga na fuska, gana ido gana leb'e gana gira, gana zagayen ido. Is too much, Sumayya. Don Allah karki sake yi." Tun daga lokacin kuwa ban sake yi ba. Iya kacina powder kad'an, kwalli. Sai white lips idan tayi hali. Domin ragowar basa burgeshi, baya so. A bubuwa da yawa basa burge Ancle Fa'iz. Lokacin da ka Tak'ark'are Sai kayi masa bajinta, to lokacin zai kushe. Shi yasa daga baya na sanyawa Zuciyata salama, bana fushi sam idan nayi abu ya kushe bana fushi, sai dai nayi k'ok'arin gyarawa irin yadda ya nuna yana so, ko bana so kuwa. A cikin 'yar hira dana ke Samun albarkacin ta a tsukin, nake bincikar sa irin ra'ayoyin sa da a binda yake so da wanda baya so. Ya kan fad'a min, wani zubin. Wani lokacin kuma ya bijire yace wai menene dalilin da nake damunsa da tambayoyi da bincike?. Nan saduda na rabu jdashi, na tara gaba kuma. Har lokacin babu ka lamun somi somin Sona dana fuskanta daga gareshi. Har lokacin girkin Momi kawai yake cI. Cikin hikima nake yi masa magiya nace ya rink'a ragomin, nima ina Sha'awar girkin Momi. To wani zubin ma nan falona yakan zo da shi yaci, saboda naci na. Nima daga nan Sai na turo masa nawa da magiya nace yasa albarka. To dai nawan ma kushewa yake a gabana. Ya kance gishiri ya zarta. Ko kuma magi. Ya dai ficewa na cika attaruhu. To Sai na rage sa attaruhu, na rage magin ma da gishiri, nayi iya iya wata wurin kyautata komai. To amma me.? ya daina k'orafin, amma ba yabo. Na lura girkin Momi kawai ya fiso. Kuma naci, na yaba Kam. Yabon gwani tilas. Momi ta iya girki sosai kuwa. nafi zaton fannin girki ma ta karanta. Na dai zamewa Ancle Faiz dan kadafi, na manne na nace, cikin shiga al'a muransa, duk furucin da zai jefamin mara dadi ba na yin fushi ko zuciya, zuciyar tuni ta horu da haka har ta bushe. Ni keyin zaraf cikin al'amuran sa, kafin ya buk'aci a bu nayi. Sam. baya so na yi masa d'awainiyar komai. Rufe dakin sa yake yi da mukulli idan zai fita. Idan yana ciki, kuma bayaso nace zan Shiga ballantana nayi masa gyara ko Shara kamar yarda na k'wallafa rai, Sai ya hanani fir!. Baisani ba rannan na zari d'aya daga cikin 'ya'yan mukullin sa da yake jikin key holder na b'oye. Da yamma Lis, na taso daga makaranta da wuri saboda lacture ta ranar gajeriya ce na bud'e d'akin nasa. Gaban su Muhibbat da Khairat suna hira, suka bini da kallo. Gyara nayi masa sosai. Dakin a share yake tas, amma a kwai 'yar k'ura jikin sib da wardrobe. Na k'alk'ale komai . Na cire zanin gadon nasa masa sabo gau, nawa duk da nasan ma baiyi wani datti ba, saboda ba laifi Ancle yana da tsafta. Haka ma labule na cire nasa masa nawa sabbi masu kyau, domin biyu aka yi min. Nasan ma mai kyau ne, amma nawa sabone ful, domin kala biyu ne dani masu tsada. Zanin gado kuma kala uku. Na tsara masa Kayan cikin kwabar sa, na jera, saboda yana yawan hautsinawa ya barsu garin binciken kaya. Nayi masa gyaran da bazai rinka hautsina komai ba, komai dalla dalla. Na ware under's d'insa da singlet da gajerun wanduna, har da Kayan boll da babu wanki na kai d'akina na a jiye da niyyar gobe na wanke. Na fesa masa air freshner Sama Sama, kar yayi min k'orafin turare ya hau masa kai. Shi yasa ma ban k'ara da turaren wuta ba. Dakin nasa yayi kyau sosai kamar ba shi ba. Da yake falon ma babu tarkace, kujera guda ce sai TV dake jikin bango da risiba. Wata laptop d'in Ancle na gani madaidaiciya ta d'au hankalina na bud'e. Tabbas da nasan me zan yi tozali da shi, da ban bud'e ba. Hoton Salima ne da Ancle Fa'iz ya cika fuskar laptop d'in. Suna jikin juna, Salima ta kwanto a jikinsa ya tallafota da hannayensa ya mannata gam a jikinsa. Tamkar mata da Miji. Abin ya d'aure min kai, dama Ancle Fa'iz zai iya haka? Ko kuwa soyayyarce duk ta zautar da shi, ya biyewa hud'ubar shaid'an?. Sai da na daure zuciya na sake kallon hoton. Su duka murmushi suke yi a hoton. Sai da nayi tasbihi ga mahaliccin surorin'su. Ita da shi d'in babu kanwar lasa wurin kyau. Sun dace da juna Kam in dai wurin duba ne.idan kuwa suka tashi haihuwa,wad'anne irin kyawawan yara za'su haifa. Za'a Sha kallo. Ko shakka Ancle Fa'iz yana son Salima sosai. Kusan duk wani abu nasa mai muhimmanci hotonta ne a kai. Wayoyin sa biyu ne banason gani ma, Saboda duk hoton Salima ne. Da dai da key holder dinsa na d'aki hoton Salima ne, k'arami a ciki anyi masa siffar zuciya. Lallai Ina da gagarimin aiki a gabana, tun da ko makami na yak'i daya ban mallakaba, na satar zuciyar mijin da muka kusa tarayya da Salima. Ko ince ni zaman wucin gadi nake yi a wurin Ancle, waadi nake jira. Tayi min fintin kau Salima na k'wace Miji tuni. Tun da familyn sa ma duk mayak'anta ne na fagen daga. Gashi kullum kuma k'ara zarmewa nake cikin Soyayyar Ancle Fa'iz. Shi yasa kullum kishin sa ma k'aruwa yake a raina, duk da bai a jiyeni a rukunin mata ba ma. Ba domin na tabbatar Sai mun d'ebi 'yan kallo da shi ba, da Sai na rotsa laptop d'in nan. To laifi kan laifi ma zanyi. Na shigo masa muhalli bai Sani ba, kuma nayi masa tsadadden ta'adi. Nan ma cewa zai yi lek'en a Siri ya kaini. Wannan hoton, ko ba'ace ba, nasan yana ji dashi. Da na fito daga d'akin Ina rufe komai, Momi da Muhibbat na gani daga saman bene sun kafa min idanu, nayi kamar bangan su ba. Nasan Muhibbat ta kai mata tsurku. Fuskar'sa d'auke da alamomin Mamaki ya shigomin. Hannun sa ya dafe kujera yana daga tsaye ya ce. "Wa ki ka ga ya shigar min d'akina?" Kamar da gaske na dake "Anya an Shiga d'akinka kuwa yau Ancle? Wani a bune ya faru?". Yaja dogon numfashi. "Tabbas an Shiga an jima, domin komai na d'akin ya canza. An canzamin tsarin komai na wurin. Wanene mai wannan aiki, ko nace wacece?". Na kanne cikin b'oye dariyar dake son k'wacemin. "Ta'adi a kayi maka Ancle?". Yace. "Gyara a kayi, tun da wurin ya k'ara haskaka yayi kyau". Naji dad'i sosai na yabon da yayi. Ancle Fa'iz kafin ya yaba abu a ya'ra. Saboda Jan zare, na zolayeshi da cewa. "Ancle, Ina Jifa aljanun cikin d'akinka ke sonka, suka yi maka gyara." Yayi min k'uri da idanu, har Sai da naji wani abu mai hargitsa yanayi kafin ya nisa tukun yace. "In dai haka ne, to kece shugabar aljanun, ke kika jagorance su." Dariya nasa ta burgewa. Wato ya fahimci ni nayi masa dai gyaran. "Ina kika samu mukullin d'akina? Yace. Nace. "Jikin mukullayenka na cira." Nayi zaton zai min fad'a, amma Sai naji yayi shiru.Na fahimci yaji dad'in gyaran da nayi masa a fuska. Duk da kullum nunawa yake yi baya so nayi. Tamkar kaska haka na Mak'alewa Ancle Fa'iz, saboda ya rage kyarata da yawan yi min fada,a kan da. Domin takai ko bai shigo d'akina ba, ni zan bishi nasa d'akin, bana kuma shayi, ko fargabar mutanen gidan. Tuni na soma yin sabo da shan zagi, harara, habaici da zund'e. Shi yasa idan ma anyi min, bana d'aukar'su a bak'on al'amari da zai yi ta damuna. Wannan yasa zuciya ta ma ta kangare ta bushe, domin idanuna sun rufe da Soyayyar Ancle da bin hanyoyin da zan janyo ra'ayin'sa gareni. Duk da Shima Ancle Fa'iz d'in ina shan wuyar sarrafashi wurin shishshige masan da nake yi. Yakan nunamin ma k'arara cewa na ta kuramasa, wani lokacin, amma Sai na shanye. Bayan Ancle Fa'iz ya sauko daga saman Momi, ya sameni zaune a d'akin'sa Ina dakon'sa. Ya samu wuri ya zauna, ya fara da cire hular kan'sa. Nayi zaraf na d'auka, nasa a kaina na dubeshi nace. "Ancle tayi min kyau?". Ya jefeni da kallo d'aya na gefen ido yace. "Ke namiji ce da hula za'ta yi miki kyau?". Sai na cire daga kaina nasa masa a kan'sa. Ya cire ya ajiye. Na sake d'auka na rik'e nace. "Wallahi hula ba k'aramin kyau take yi Maka ba, my Ancle." Yace. "Ko?". Na sake saka masa a kan'sa, ya kuwa cire da sauri yace. "Wai yaya haka ne, ina cirewa kina samin?". Nace. "To, ni nafi son ganin ka da hular, kafi kyau Allah". Wannan Karon wani murmushi naga yayi Maimakon hasala da nafi zato, yace. "Sumayya, kina fa takuramin, kina fa sani surutun da ban shirya ba, Allah kina ma cin darajar maraicinki ne nake sassauta miki, domin ina tausayinki wani lokacin, amma a kiyayi dai zuwa rafi kullum, wataran sai an fasa tulu". "Nayi murmushi. "In dai bukatar da a kaje na debo ruwan ya samu to ai ba damuwa, Ancle kasan ranar biyan bukata rai ma ba a bakin komai yake ba". Ya dan daga min bakar girar sa gami da dan fito da ido. "I see". Iya a binda yace kenan, da alamu ya dan shiga duhu da furucina, ko kuma ya fahimta ya maze, saboda na fahimci yana da saurin karantar mutum sosai, amma sai ya waske yayi kamar baisan me kake ciki ba, ni kuwa da gayya na furta. Kwana biyu na sake samun Ancle a daki ya na bubbude sababbin wasu unders da ya sayo daga leda ya na dubawa, bai dago kai ba gareni duk da ya amsa sallama ta. Na zauna gefen sa kan kafet din dakin, shi kuma yana gefen gado. "Sannu da aiki my Ancle". Nace ina murmushi. Yace " Yauwa sannunki". Na mika hannu zan amshi singilet din dake hannun sa, ya janye. "Ancle gani fa zanyi". Yace "Ahaka ba kina gani ba, look karfa kizo ki matsamin, bana son takura". Na sake yin murmushi. "Ni ba takura maka zanyi ba Ancle, kawo to na ninnin ke nasa maka a ward robe". " Barshi nayi". Nace "Kai my Ancle bai kyau tu ba ina zaune kayi aiki ba gaskiya kawo please". Yace " Hmmm!! " Kawai. Kamar bazai bani ba sai ya miko min kayan duka ya mike yana mai fadin. Yarinyar nan duk kin bi, kin hanani sakat? nasan idan ban baki ba baza ki barni ba, bansan wa kika gada ba wurin kafiya a dangi". Nayi 'yar dariya nace. "A dai laluba za a samu, domin ruwa baya tsami banza" "Bulala kawai Allah zan a jiye kusa dani. Surutun da ki ke Sani banyi niyya ba, yayi yawa fa". Nace "Barewa fa a dawa ance da d'anta take wasa Ancle Fa'iz. Kaman ta bani da kowa Sai kai? Kaine uwa, kaine uba, kaine Kawu, kaine Yayana kaine....." Ya da katar dani da hannu. "Ya isa !. Ke kin fiye Surutu, Sai kace aku kuturu." In da sabo na saba da irin wad'an nan lafazai nasa. Kuma a hakan muke ci gaba da hirar bana fushi kamar kullum. Ranar dai na ganshi cikin walwala dai, Bansan dalilin ba. Ya nutsu ya soma cemin. "Ki ta yani murna, na samu shigowar wasu kud'ad'e masu yawa na wasu wasanni da muka yi a state uku, Sai jiya aka turomin nawa cikin a count. Ban tab'a Samun kud'i masu yawa a wasa ba irin wannan. Nayi kasafin su ma. Na wari wanda zan ba Momi da Baba, na wari Wanda zan Sai mota, da wanda zan sake jefawa a harkar ginina da yake taci min kudi, da na samu da ya handame". Naji dad'i sosai da na samu matsayin da ya fad'amin sirrin ci gaban'sa. Na kuma yi ta surfamasa godiya da addu'a na kyautar kud'in da zai ba iyayen'sa, Sai a zaci nawa iyayen zai bawa. "Wallahi ka kyauta Ancle Fa'iz, musamman alkhairi na kyautatawa ga iyaye yafi kowanne. Allah ya saka da alkhairi, ya k'ara bud'i" Ya gyara zama daga kishin gid'ar da yayi gefena da nake ninke masa kaya. "Kema za'a baki Lada na ganin ido, kamar 'yar dubu goma, tayi?". Nayi masa murmushi "Wanda za'a ba kyauta har yana da zab'i? aiko naira goma ka bani godiya zan yi tayi, ballantana har dubu goma Ancle?". Ya kanne ido guda cikin dubana yace. "Na lura, kina da Yakanah! Saboda haka bari a k'ara miki dubu goma su zama twenty thausand. Godiya nayi ta surfawa da addu'a." Yace. "Ya isa haka Sumayya, Sai kace kyautar rai na baki?". "Ancle wai kuwa wacece Anti Husna da naji su Khairat suna yawan fad'e?". Yace"k'Anwar Momi ce, ita ce autar su. "To, Ancle Jamil fa?". Yace. "Yayan Momi ne" Na sake cewa "Maman fahad fa?" Cikin nuna 'yar k'osawa yace. "K'anwar Babar Momi ce, Kenan uwa take a wurin Momi. Na gaji Sumayya, tashi Kije ki kwanta, bacci zanyi karfe goma na dare ta gota, ina son yin sammako". Nace"Abin har da kora my Ancle?". Yace"Wanzami dama ba yason jarfa, ni me yasa jiya kika koroni daga d'akinki?". Cikin 'yar dariya nace. "Au, daga kayi bacci na tasheka nace kaje ka Mik'e a gado?". Yayi doguwar hamma kafin yace. "Wannan a bu duk mai sauki ne, idan baki son tafiya, nan d'akin yayi miki, Sai na kawo miki guzurin filo, ba Shike nan ba?" Na kuwa ce "Kawo min". Sai kuwa naga ya tashi, ya na kokarin jawo filon, nan nasan da gaske yake. Kafin ya dauko kuwa na mike da sauri na fice, in da nace masa " Sai da safe Ancle". A tsukin cikin wata hudu da aure na da Ancle Fa'iz, a bubuwa sun soma zuwa min yarda nake so. A lokacin ne kuma na sake shiga tsangwama da takura da fitintunu a cikin gidan, saboda sun fuskanci muna d'an d'asawa da Mijina, yana nunamin kulawa fiye da da. Kwana ne kawai Ancle bayayi a d'akina, amma har a binci tare muke ci, idan ya shigo d'akina. Kuma ni na gadar masa da hakan, domin ko shi kad'ai ya soma ci, Sai na zo na sashi a gaba,nima na soma ci, muci gaba da ci tare. Ko a bincin Momi ne kuwa, domin naci na yasa kullum Sai yaci nawa. Shi yasa baya cika cikin'sa ma da a bincin Momi, saboda yasan nawa d'an k'a'ida yana jiran'sa. Wulak'anci da cin mutunci muraran a ka Shiga yi min a gidan, da kare ma ba zai ci ba. Duk wani laifi idan a kayi a gidan, Momi ni take cewa. Babban a bin takaici har Sata a ka kallafamin. A zatona babu wani abu da ake sacewa, domin a d'oramin laifin sata ne kawai. sai Momi yau tace an sace mata a bu kaza, gobe ma haka, kuma tace nice ware, nice lallai zan d'auka, domin cikin 'ya'yan ta babu b'arawo. Momi ta kirani cikin 'ya,'yan ta, ban da Ancle, taci min mutunci a matsayin ni b'arauniya nayi mata Sata. Khalifa ma da Muhibbat su zageni son ran'su. Khairat ce Kawai bata tofawa, zanga ta b'ata rai sosai. Na lura bayan kirkinta, hak'uri ne da ita ainun. Muhibbat ta matsamin lamba sosai a tsukin. Idan nayi wanki, nayi shanya ta zubar a k'as. Da yake Ina wanke ma na Ancle marasa nauyi, amma bata zubar da na yayan'ta. Kunji son zuciya. Ni ke sharar gidan, amma randa Muhibbat ta so tsiya, Sai ta fizge tsintsiyar daga hannu na, ta share ko'Ina. Sharar idan ta kwashe Sai ta watso falona. Na rink'a dauriya, Saboda Kawai bana so K'orafi ya fara b'ulla daga bakina wurin Ancle ko wani nawa. Sannan Zuciyata tayi nisa a son Ancle Fa'iz, banason a binda zai haifar da sa'in sa tsakanina da kowa nasa . Zaman aure na mutu ka raba na k'uduri yi da shi, iya yina. Komai nawa na Kayan kichean, ni da Muhibbat muke amfana, musamman idan tayi bak'in k'awayen'ta, komai na kichean d'ina za'tayi facaka da shi. Filet filet da kofuna na k'arau ta yi amfani da su, ta zubemin a waje babu wankewa, ta kuma fasa na fasawa da gayya, duk dai Sai an cuzgunamin nayi magana, an zagi ubana. To, ni kuma Sai nayi lub, kamar banji ciwo ba. Kayan kichean d'ina duk ta farfashe k'arau d'in, ban dai tanka ba, na k'yale. Sun Sani a kwana sosai Muhibbat da Khalifa. Wulak'anci salo salo, zagi da Habaici. Hannune kawai basa sawa su dakeni. Sau d'aya nayi wa muhibbat magana da ta fasamun fulas d'in shayi, da shi kad'ai ya ragemin, ta kuma kwashemin drink's na Friedge da nake tanada saboda Ancle.da tayi bak'i. A binda ya fito daga bakin'ta shine. "Ai naga, ba' daga gidan uba, akazo da drink's ba, yayan mu ya saya, aikin banza shishshigi babu kwarjini, diyar matsiyata ke har wani kaya ne ma dake na kichean da zakiyi fariya a kai, kuma komai na ci ko sha ai yayan mu ke sayowa ba daga gidan tsoho a ka kawo ba". Raina ya sosu, tamkar na fallamata mari, amma na daure zuciya, saboda ubana da baya raye da ta tsomo a ciki". Tabbas yayanta na sayo komai, amma wanda duk ta kwashe ni na Saya. Kawu Sulaiman yana aiko min da kud'i a kai a kai, kuma yawanci, wurin yiwa Yayan su d'awainiyar sa kai na, suke tafiya. Sauk'inta bana yini a gidan,saboda makaranta, ba domin haka ba, a bin yawa zai min, wai shege da hauka. Ranar a sabar bani da lacture, banje school ba. A kayi dace nayi bak'i kuma.'yan uwan ummata da suke uba d'aya, baba Maryam, da baba Hasana. Tare na had'a mana a binci mukaci, Sai yaran su, dana ware musu a faranti guda. Ancle Fa'iz ne ya shigo da a zahar da ba sabon'sa ba. Ina hangen sa ta taga, saman Momi ya haye rik'e da poly bag k'arama, irin ta take a way. Muna hira da bak'ina ya shigo falon da sallama, baisan da bak'in ba, Sai da ya shigo. Bayan sun gaisa, na gabatar masa da su suka gaisa a mutunce kuwa. Sai yace nazo yana son ganina dama tsintsiya ce a hannuna, zan share a bincin da yaran suka watsar, sai baba Maryam tace naje Kiran mijina ta share. Nabi bayan Ancle Yana tsaye a d'akin nasa ya rungume hannu a k'irji, ya jingina da bango, kamar wani a bu yana damunsa na fuskanta. Nace "Ancle yau ka dawo da wuri Amma " Fuskar'sa babu walwala yace "Eh!" Yayi shiru. Sai daga baya Yaci gaba. "Momi ta dawo dani,saboda waya tayi min wai na taho mata da take a way yunwa take ji. Nace mata yanzu Momi a binci Sai ya gagareki a gidan bayan da a kwai komai? Saboda bana son dawowa, Ina kan wani a bu mai muhimmanci, amma Sai da na barshi, saboda tace min su Khairat dama ke dafa binci su bata, kuma duk sun tafi unguwa tun safe . Kuma gashi likita yace lallai Sai taci a binci sosai kafin tasha magungunan ta, na larurar rashin lafiyar da take ciki." Nan na dubeshi nace, Dama Momi bata da lafiya?". Ya dubeni galala. "Wace irin tambaya kike min? Waye baisan MomI bata da lafiya ba, kwana biyu? duk da tace kikan jima bakije kin gaisheta bama, amma ai za'kiga ta fad'a kwana biyu". Wannan abu ya Sosa min rai, shi yasa kika ga na kasa juriyar a jiyewa zuwa wani lokaci. Domin da nace Momi tayi miki magana ki bata a binci, tun da kina gida, Sai tace bata buk'atar a bincin ki, tun da baki damu da ita ba. Tunda ta kwanta jiyya baki tab'a yi mata sannu da jiki ba, ba kya gaishe ta ma. Kuma da kina bata a binci, kika daina, Sai dai kiba almajiri. A binda ciwo a ce Momina ta rasa a binci a gidan nan Sai da na dawo, amma ga bak'inan su sunci, har sun zubar". Tun da nazo gidan raina baitab'a b'aci ba irin ranar. Duk a binda suke yi min, ni banyi k'orafi ba Sai Sai su? Kuma gashi ya Shiga cikin su, ya yarda tun da yake tuhumata. Na had'iyi yawu da k'yar . "Nifa ban fahimci zargin nan da ake so a lik'amin ba. Sam ni bansan Momi bata da lafiya ba. Waya fad'amin? Kuma Ina gaisheta, ni banga alamun wani rashin lafiya ba. A binci Ina bata ta dai naci tace bataso, to yaya zan yi. Na sake daukar zafi saboda na fuskanci Ancle yana bayan su, yarda ya daure fuska yana yimin wani kallo a sangarce. Kuma a binci ma ai cewa a kayi nayi iya cikina, nifa a ka ware. Kuma ai ba'a bani umarnin ma bawa Momi a binci ba, iya kaina a kace na dinga dafawa, ina dalilin da zaa dawo a na zargina kuma. Ni fa nasa kaina nake bawa Momi a binci". Take naga ya fusata ga rashin zato na. "Har wani alfahari kike na wai ke kika sa kanki kika ga damar bawa Momi a binci? Sai da kika ga dama? to kiga kuma hagu. Kar ki sake bawa Momina a binci, umarni na baki Shima. Ki dafa iya cikin ki na sake fad'a. Ki Sani, ko zan iya hak'uri a kan wani a bu, banda a tab'amin uwa. ko wanene bai isa ba wallahi." Take zuciya tazo min iya wuya. A fusace nace. "Girkin ma ai ba dole bane. Domin iya cikina zan wahala? nama daina dafa komai, kome na samu ya fad'o bakina ya wadatar. Kuma Allah shine Sha'hidi a kan kome nene gaskiya. K'arya ta shekara k'arya. Gaskiya na makwafinta". Ina fad'in haka na mik'e nayi ficewata. Na fusatashi sosai na gani kan fuskar sa, amma Sai naga ya gaza cemin komai, face bina da kallon Mamaki, har na fice.Tun daga ranar na rufe kichean ruf, ko ruwan tea bana dafawa. Sam bana karyawa da safe, ko ina gida. Abinci Sai a bu mai ruwa ruwa,Sai ciye ciye Sama Sama. Amma banacin gaskiya a bincin kirki a cikina. Ga damuwa da na d'orawa zuciyata. Kuma na d'au fushi da Ancle Fa'iz ko falonsa bana zuwa. Da safe yana shigowa wurina Bayan sallar a suba. Bayan na gaisheshi, bana sake ko kallon sa ballantana na tsinka masa. Shima ganin babu fuska, Sai ya ajiyemin kud'in da yake bani, batare da sake kulani ba. To dai banga ya d'au fushi kamar ni ba, yarda na fuskanta. Komai ya sayo zai kawomin nawa d'aki ya a jiye. baya cewa komai, Sai ya fita. Ni kaina banyi zaton Ina da zuciya ba, Sai da aka kaini bango. Dama wasu sunce, mai hak'uri bai iya fushi ba. Ba iya Ancle Fa'iz ba na d'au fushi da shi ba, duk gidan ne. Ji nayi an kai ni gargarar da bazan kuma d'aukar raini da wulak'anci ba. Momi Kawai zan iya d'agawa k'afa, albarkacin Ancle Fa'iz da kuma darajar haihuwa, tun da ta haifeni. Amma ita kan'ta Momi taga canji a wurina. Kullum zan je na gaisheta, Amma fuskata babu walwala, da rawar jiki na biyayya da nake yi mata. Domin da kullum naje gaishe ta, Sai na tambayi ko da wani aiki da zan yi mata. Bayan fa Kusan aikin gidan gaba d'aya da na kallafawa kaina, kamar mai aikatau. Momi ta ban Mamaki da tace wai bana zuwa gaishe ta, da bata a binci, da dubiyar rashin lafiyar da ban San da ita ba. Gaba d'aya zuciya ta ta karkata wurin yarda da cewa Momi yak'i take yiwa Salima bayan idonta. Domin Khairat ce ta sameni rannan da babu kowa a gidan bayan sallar magariba, tazo d'akina tace min. "Matar Yaya, wallahI ki k'ara rik'e mijinki da kyau, domin Kusan kullum Sai Salima ta yiwa Momi waya. Rannan hands free Momi ta manta tasa, naji Salima tana yiwa Momi magiya kamar zata yi kuka, Wai tana bala'in Son Yayan mu, shi yasa baza ta iya zama da kishiya ba, Wai Momi ta taimaka mata. Saboda Salimar ta cewa Yaya, ya sakeki tun da saboda ya sameta ya aureki, kuma tun da Momin ta ta sauko ma tace ko yaushe yazo a yi aure. Amma Sai Yaya yace mata babu ruwanta da zancen auren sa dake, tayi gefe da shi. Kawai tasa himma a kan tsara musu zaman farin ciki da Soyayyar da za'su shimfid'a, kafin isowar auren. Ita burin Salima fa Kawai Yaya ya sakeki kafin auren ta da shi. Shi kuma yak'i bata amsar yiyuwar hakan. Momi hak'uri ta bata dai, tace tabar komai a hannun'ta zatasan yarda za'ta b'ullowa komai, saboda yanzu binsa take yi a sannu, saboda har yau bai gama hucewa ba, da a binda maman'ta tayi masa. Kuma Khairat ta ce min, taji Momi tana fad'awa Ancle Fa'iz wai ya d'auki matakin plannig, wato tsarin iyali a auren ku, saboda batason ya haihu da ke kafin zuwan Salima. In so samu ne ma ya sallameki yanzu, tun da kwalliya ta biya kud'in sabulu. Amma Sai cewa Momi yayi. Momi nasan a binda nake yi nima name ya kamata nayi a lokacin kuma da ya dace, kusamin ido". Momi bataja musu da shi ba, duk da bata fahimce shi sosai ba. Haka za'lika nima ban fahimta ba. Amma fatana kar burin su ya cika a kanki Anti Sumayya. Wallahi ni nafisonki da Anti Salima." Wani irin k'aunar Khairat ya k'ara mamayeni. Rungumeta Kawai nayi, nace ."Khairat Ina k'aunarki, fiye da kowa a gidan nan. Allah ya ganar da su gaskiya, su san ni ba a bokiyar hamayya bace, face masoyiya ga Ancle, mai son sa da son ci gaban'sa, da su baki d'aya. Ta kuwa ce. "Amin". Murmushi nayi, da a ke gudun, na samu ciki na haihu da Ancle, to duk Ina tunanin su ya tafi? Ko jituwar da suka ga munayi da shi a tsukun, suna zaton komai yana tafiya na aure tsakanina da shi? da sun San komai nasan Momi bazata yi a sarar yawun bakin'ta ba. Tun da Khairat ta fad'amin maganganun nan, suke tayi min yawo a rai. Tabbas k'wace goriba hannun kuturu bazai yi wuya ba. Za'su iya iya rabani da Ancle Fa'iz nan da nan, tun da ko tubalin ginin dasa sabo da k'auna da shak'uwar da nake fad'i tashin yi kullum, bai yi nisa ba, ballantana yayi k'warin da Sai anyi gwagwagwa da shi, kafin a rushe. Shi yasa wata zuciyar ke min shelar cewa, Kawai na shafawa kaina lafiya da Ancle, na saddak'ar, nasa rai da isowar cikar wa'adin auren mu, na rungumi k'addarar shiryawa zaman zawarci, da tunkarar sabon wani auren da bazan tab'a so ba, Sai dai nayi a larura. Saboda manyan matsaloli ne masu wuyar warwaruwa ke ta tunkaro ni cikin aurena da Ancle Fa'iz. Ko ga na Momi Kawai ya isa na sare. Saboda naga k'iyayyar mai zafi ce, tunda har ba'ason had'a jini dani. Lallai Khairat, tana k'aunata sosai, tun da ta iya fad'amin sirrin mahaifiyarta. Na tara bokiti bakin fanfo zan debi ruwa zan Shiga band'aki nayi wanka, saboda wani zafi da ake surfawa, Muhibbat ta taho da sauri da nufin angijeni tayi saurin shigewa saboda neman fitina, bayan ta baro wani band'akin a bayanta. Batasan a yarda nake ji da tsiya ba, kowa ya tunkaroni a lokacin karawa za' muyi. Shi yasa banyi jinkirin angijeta ba,iya k'arfina, Sai gata a k'asa wanwar . Ta kuwa Mik'e da masifa za'ta soma aunamin zagi, yarda ta saba. Nace cikin d'aga murya. "Ahir. yarinya. Karki d'auki kawaicina a matsayin gazawa. Kuma karki d'auki hak'uri na a matsayin tsoro. Idan har ke kin cika d'iya ta halas, to ki kai ga jikina, domin fad'a na baki na matsorata ne." Sautin murya ta da yayi Sama, a she Momi taji yo, Sai ta fito, haka Khairat, suka zubo Mana idanu daga saman bene. Muhibbat tayi min wani matsiyacin kallo, cike da mamakin yarda na rikide tashi guda, don duk iskancin da take min sunkuyar da kai nake yi na wuce. Tace cikin tafa hannu. "Samun wuri, Wai d'an wake a hotel. ke bora, kuma 'yar tsaron k'ofa, har kina da bakin magana? har da fiffik'a? to ba za ta kaimu da nisa ba, zakisan matsayin ki idan kin manta. Bari yaya ya dawo." Na sake hada idanu da Momi sai kuwa na sake daga murya a fusace. "Yazo din, me ya isa yayi min, datse min numfashi, ko duka na zai yi, don bazan daku ba wallahi, iko daya ne dai cal zai iyayi kololuwa, shine ya sakeni, kuma na shirya tsab, tun da ba autan maza ba ne. Gari da yawa ai maye baya cin kansa". _wasa farin girki, har yanzu ba a shiga farfajiya na rigin gimu da manufofi da soyayya da dadin wannan littafi ba, duk maison ya kashe kwarkwatar idanun sa, to ya turo_500 kacal 👌🏻 Ta wannan a count no👇 8025527956, Opay. Zainab ilyas _Shaidar biya ta wannan number ta whattap_. O9096409711 _Zainab ilyas mazwaje_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe *NI DA GIDANA* _Zainab ilyas mazawaje_ _Best brilliant interlligent writer_.... 🖋️ *Page 18* Furutaina na fahimci sun tunzura Momi, saboda gabanta nake tijarar, kuma tasan na ganta. Kuma tasan idan 'yarta tayi sake muka dambata, Sai na lallasata sosai, saboda na fita siffar k'arfi ma a ido. Ita 'yar kyalan kyalan take. Bata da cikowar komai a jiki na cikar surar mace. Kyan iya fuska yake, Sai farar fatar abin alfahari, irin na 'yan uwanta, idan aka cire Khalifa. Momi tace cikin daga murya da fusata. "Karki kulata Muhibbat. Ai Kare baya yi Maka haushi ka rama, Sai Ku zama d'aya. Ko a usuli da nasaba kun bambamta, ba kya daka ta tata ba. Kinsan kuma harbi ga d'an kunama gado ne." Na d'aga kai na kalli Momi a zuciye, na kau da kai, Kenan ta ramawa 'yar ta. Darajar haihuwa taci, da tazarar shekarun da ta bani, gashi na samu tarbiyyar girmama manya, da ta gane ita ma shayi ruwa ne. Domin sun kaini k'urewar bango. "Momi, ni Mamaki take bani fa! wai bora kuma 'yar jiran k'ofa keda a bin cewa. A cewar Muhibbat. Na Doka mata kallon k'ask'anci. " Ke shashasha, ragowar yunwa, A littafin maganganun dake bakina wallahi , shafin farko ma ban bud'e ba. Zan kuma karance miki shi, in dai kika ci gaba da ja dani. Matsoraciyar Kawai, Wacce a fad'an baki tafi kauri". " Ina kai nan, Sai muka had'a idanu da Khairat. Murmushi tayi, dake nunin taji dad'in 'yancina da na karb'a.Dole idan ba'a kiyaye ni ba, za'a sassauta kuwa. Nan na wuce band'aki na bar Momi da Muhibbat suna ta yada maganganu. Na fahimci na had'a musu zafi, bayan mamakin da na basu. Basu tab'a zaton zan iya haka ba. A na Kiran sallar Isha'I na jiyo sallamar Ancle Fa'iz ya shigo. Nasan Kiran'sa a Kayi a waya, domin baya dawowa dai dai wannan lokaci. Nan ma saman Momi ya wuce kai tsaye. Ina zaune rik'e da kofin flastic, Ina shan corn flake's, domin shine ire iren kalar a bincin da na komawa, mai ruwa ruwa. Sati biyu kenan da k'untatawa kai na da nayi na k'in yin girki. Saboda b'acin ran da nake ciki, bayan rashin a bincin kirki, duk na soma rama, k'asusuwan kwarin wuya na sun soma yi min mirjani. Ga bak'i da na soma yi. Ancle ya shigo min da sallama a sanyaye jikin sa naga. Saye yake da rigar kakin jin's riga mai gajeran hannu da wandonta na jin's. Gaban rigar manyan mab'allaye ne, ya b'alle biyu na saman a na hango k'irjin sa kad'an.Kayan jajaye ne masu duhu, shi yasa sun k'ara haskaka kyawunsa da hasken fatarsa. Kyawun da suka yi masa bazai misaltuba. Tamkar d'an bak'on balarabe a k'asar Hausa. Bantab'a ganin yasa kayan ba. Ta yiyu, sababbine ko a jiyayyu. Ranar ko sannu da zuwa na kasa yi masa,saboda nauyin damuwa da ya rik'emin Mak'oshi. Tun da muka samu Sab'ani da shi, dama gaisuwa Kawai ke had'ani da shi, ko sannu da zuwa, idan ya dawo ya shigo ya a jiyemin nawa a binda ya sayo na mak'ulashe. Ancle Mutum ne mai sakin hannu sosai na sayo wannan sayo wancan na wasa baki, in dai yana da shi. In yayi kud'i za'aci dad'i kam ba kad'an ba. Ya zauna kusa dani kan kujera. Na basar na ci gaba da shan corn flakes d'ina kamar ban San da tsirar sa ba. K'iris Kawai nake jira, a yi b'atacciya. Yace "Sumayya!. Na amsa da k'yar. "Wai maye yake damunki ne? gaba d'a ya kin canza, kan d'an a binda bai kai ya kawo ba. Ban San ki Sam da halayyar fishi ba, ko rigima, ballantana fad'a. Ina kika a ro wad'an nan d'abi'u? " Duk a sanyaye naji yana furutan ma. Na fusata nace. "Ba'arowa nayi ba ma, Karb'owa nayi kyauta, domin na ceci kaina Ancle." Yayi d'an jinkirin magaba, domin jinjina furutaina. "O k, naji. Yanzu fad'amin a binda ya faru a yau". "Au, ba'a fad'a Maka ba?" Yace. "Ko an fad'amin a dalcine naji kuma daga b'angarenki ko?". Nayi yak'e na takaici. "Duk a binda akace Maka nayi gaskiya ne Ancle. Bani da kirki. Duk d'abiar da kasani ta banza, toni gwanace. Matsalolin duk da suke faruwa a gidan nan, nice sila, tuntuni fad'a Maka ne ba'ayi. Saboda haka babu wani bincike da zaka kumayi, na kuna kuma yanzu babu wani kauri ko hayaki da zai tsoratani, kazartar min da hukunci Kawai, shine magana". Kuka ne ya nunamin fin k'arfi, na aibata kaina da nayi, domin na yarda k'wallon mangwaro na huta da k'uda kawai. Nayi k'ok'arin Mik'ewa na shige d'aki, Sai Ancle ya rik'e hannu na, domin dakatar dani. Iya k'arfina da bansan ina da shi ba, nasa kuwa na fizge, saboda a tunzure nake sosai nace. "Ni ka rabu dani, Ancle ka zartar min kawai da hukunci, shi ya rage kawai". Na fad'a d'akin ina sheshshekar kuka. Baki bud'e na bar Ancle Fa'iz, domin furutaina sun girgiza shi ainun. Ina Shiga d'aki Sai gashi ya biyo ni. Na hau kan gado, Shima ya hawo. Ina ja da baya, yana biyoni. "Wai ka rabu da ni Mana. Bana fad'a Maka gaskiya ba? Ka k'yale ni Ancle" Cikin kuka nake fadi. Nama rasa a binda ya hanashi yin zuciya a lokacin ya rabu dani, domin mai zuciyar ne. Sai da na kai k'arshen gado, na hak'ure, saboda ya kureni yarda bazan iya zullewa ba kuma. Ga Mamaki na, sai yayi dan murmushi ya d'ago fuskata, da hannayen'sa ya shiga sharemin hawayen fuskata da wani tisue da ya fito dashi daga aljihunsa. A hankali kamar mai rada ya soma cemin. "Ban yarda ke mutuniyar banza bace, mai kuma mummunan halaye, banyarda ba Wallahi, duk da kinyi ik'irari da bakinki. Duk in da kika je kika b'ata kanki, zanje na k'arya taki nace karya kike yi. Zan baki Kariya sosai, na kuma wankeki, nace Sumayya yarinyace me ladabi, mai kirki, mai hak'uri, mai addini, tayi zarra wurin yakanah da kamun kai.". Furutan sa sun zo min a ba zata. Ban tab'a sanin shi d'in ya tsaya nazarin sanin halayena ba, har ya karance su tsab, a tsawon watanni Kusan biyar da auren mu. Jikina yayi sanyi, kuma yayi laushi lub'us. Har lokacin hannun sa yana rik'e da hab'ata fuskata na fuskantar tasa dab yace. "Bansan me ya hargitsaki ba, ya kuma tunzuraki, har kike k'agar halayyar banza kike danganta su, da kanki. Me zai sa kiyi haka? haba my Sumy." Baki d'aya lakar jikina ta mace. Sunan da ya k'irk'iran min lokaci d'aya, yayi matuk'ar karb'uwar jin dad'in sa da tasiri a Zuciyata, wurin hab'aka k'aunar Ancle a zuciya ta, da da nake k'oK'arin ya kicewa da k'arfi, saboda wuya, da fitintinu, wani irin yanayi na samu kaina a ciki da bazai misaltu ba, game da irin yanayin da muke ciki a lokacin da Ancle, domin numfashinsa ma inajin saukarsa kamar ni nakeyi, bai kuma saki hannuna ba, da habata da ka kaita dab da fuskarsa ba yana magana. Cikin sauk'i Ancle Fa'iz yajanyo ra'ayina na fad'a masa a binda ya faru, Amma banda na can baya. Ko sunan Momi ban kamaba,domin matsayinta gareshi, bazan iya cewa tayi min wani a bu ba. Fushi sosai na gani kan fuskarsa, yace. "Banyi Mamaki ba, Muhibbat zata iya fiye da haka. Dadai Khairat ce, shine zanyi ko kwanto, domin shigen halayyarku d'aya. Muhibbat kowa hak'uri yake yi da ita a gidan nan Sumayya. Ko iyayen mu, ni nake yi musu maganinta idan ta buwayesu, domin ni kad'ai take shakka. Nasan kuma ba iya a binda ta tab'a yi miki kenan ba, kin b'oye wasu. Kiyi hakuri domin, ni. Ki jure domin ni.ki kau da kai domin ni.Nasan kina Sona, domin a binda kike min, Wallahi soyayyace Kawai zata yi jagoranci ga haka.Don Allah komai ya wuce, kinji Sumy?". Bansan Sanda murmushi ya sub'uce kan leb'ena ba. "Wallahi komai ya wuce. Kuma zan k'ara d'amarar juriyar a binda zai sake biyo baya, my Ancle. Naji dad'i daka fahimceni, batare da tallafina ba. Da sauri yace. "Yauwa my daughter. Bazance da Momi ko Muhibbat komai ba, domin cewa za'ayi nabi bayanki. Sai kiga rigingimu sun kuma b'allewa. A Kwai wasu a bubuwa da nasani da kike zaton ni d'in bansa ni ba. Har jarrabaki nayi a wani a bu, amma Sai da kika lashe jarrabawata. Nayi miki jinjina Gaskiya." Ya k'arashe cikin wani tattausan murmushi, ya Mik'e a hankali, jikin sa Sam babu kuzari ya Fice. To ni d'in ma ya burgeni ainun, na yarda ya janyo hankalina, yasa nayi sanyi na hak'ure komai, sa'i d'aya. Ban tab'a zaton yana da taushi da sanyi na d'abiar iya tarairayar mace ba cikin salo na sace zuciya. Ni Kam ai sai na k'ara matowa a Soyayya. Faruwar rikicin nan, da aka so Ancle ya d'au mummunan hukunci a kaina, kamar k'ara ingiza alak'ata da Ancle Fa'iz tayi da k'arin shak'uwa. A binci tuni Ancle ya maido cin,sa falona. Ko Momi tayi masa girki, Sai ya d'auko ya shigo wurina. Dama ga nawa da ya zame masa k'ara'i, Sai yaci ko bayawa. Yanzu kuma yakan d'an yaba, sab'anin da da Sai ya kushe, ko yace na kuskure wani a bu, ko kuma yayi shiru bazai yaba ba, ko da yayi dad'in. To yanzu, nima na k'ara zage damtse ne sosai wurin kyautata girkin da jikina da kud'ina. Na sayi littattafai na koyon girki da Shiga group group kuma na internet na koyon girki, har da na practical. Duk domin na k'wato 'yancina a matsiyina na matar Fa'iz ya damu da girkina, ya rink'aci fiye da na kowa. Jiddin tare muke cin a binci da Ancle Fa'iz. Hira ma ya rage yawan yimin k'orafi, ko nuna damuwa irin da yace na dameshi. Amma dai duk da haka bai fiyason hira ba, Sai Sama Sama. Ana jimawa sosai kafin ayi hira da shi mai tsayi. Sannan zafin zuciyar'sa yana nan daram, Sai dai idan ba'a b'ata masa ba. Shi yasa nasan irin takun Zaman da nake yi da shi. Momi da Khalifa da Muhibbat ganin mun sake d'inkewa da Ancle fiye da da, ai Sai a ka sake yiyowa kaina da fitintinu iri iri, amma ba'a takani kamar da. Musamman Muhibbat da take zuwa gabana ta d'uramin ta maguzawa (zagi). Yanzu Sai baya baya, idan zata yi min tsiwa, saboda na nuna mata nima A' ce , tsab zan casa ta idan ta Shiga hannu na. Wannan yasa a kayi musaya, Khalifa ya karb'i ragamar, domin yasan bazan iya da shi ba. Sai yafi uzzuramin a tsukun. Zagi ta uwa ta uba. Lub! nayi , duk da nasan iya zagi zata tsaya, bai isa yace zai kai hannu jikina ba. Na mai da shi, tamkar Kare mai haushi, da Sai an kula zai samu tasiri. Saboda darajar Kawai Ancle da yace na jure domin shi." Cikin hutu muke a tsukin. Saboda haka, Ina zaune na rasa a binyi, ga babu wuta, babu a bokin hira, na fito tsakar gida fitina ta afku. Na rabka ta gumi. Ancle Fa'iz ya shigo da sauri, ya tsaya kaina yace. "Sumy zo Muje kiga motar da na Saya a k'ofar gida, Sati shida Kenan da na bada cigiyar a samomin irinta, Sai yanzu a kayi katarin samota." Cike da farin ciki nayi a zamar Mik'ewa."Wow! Ina murna my Ancle. Muje na ganta. Nasa mayafi nabi bayan Ancle Fa'iz. Motar Kam tayi kyau sosai. Pomatic, sunan ta, kuma Automatic ce. Dark green. zata dace da mai ita Kam. "Gobe tun da babu makaranta, Sai Muje na d'anaki Mu zaga gari ko?". Cike da zumud'i na gyad'a kai. "Sosai ma, a she nice farkon d'ani " Washe gari kuwa, a gaban Momi da Muhibbat muka Fice ni da Ancle. Mugun kallo Momi ta jefa min da nayi mata sallamar zamu fita da Ancle. Bata tsinka ba kuma. Amma nasan Ancle ya fad'a mata komai. Tafiya muke cikin 'yar kyakykyawar motar zuciyoyin Mu duka cike da nishad'i. Hatta Ancle na ganshi cikin walwala sosai, duk da ba Wata hira muke sosai ba, Sai Jifa Jifa, Sai Jan motar da yake, sannu sannu, ya Saki slow music na R. Kelly, cikin wak'ar sa ta I blieve I can fly. I blieve I can touch the sky. Ancle yayi 'yar dariyar nan tasa ta burgewa da Sai tayi hali za'aga yayi. Yace. "Sumayya kinji wani Mak'aryacin mawak'i a binda yake cewa kuwa?" Na saurara, naji nace "Ai da kansa yake Ancle. Tunda cewa yayi ya yarda zai iya tashi sama, kuma ya yarda zai iya tab'o saman gajimare, kaga mu 'yan jine da kunne, ba yarda muka yi ba." Ancle ya gyad'a kai. "That is true." Yace a Tak'aice. Na maida kaina wurin taga ina ta faman kallace kallace ta tagar mota, har na k'yallaro wata mata tana tuk'a mota, gwanin Sha'awa. Na waiwayo gefena nace wa Ancle Fa'iz. "Ancle wai kuwa tuk'in mota da wuya?". Yace "Babu wani wuya, nima nan da nan na koya. Kinga wannan Automatic tafi sauk'i sosai fiye da manual, domin Kinga Auto, ita take caccanza giya da kanta, kuma totur Kawai zaki taka, ki tafi, babu ruwanki da taka kuloci da caccanza giya." Nace"To ai ni bazan fahimta ba Ancle Fa'iz tun da ba koyon nayi ba" "Kina Sha'awar koyon tuk'in mota?" Yace bayan ya rage sautin music d'in da yake tashi da hannu guda, guda kuma yana kan sitiyari yana d'an jujjuyashi. Nace "Wallahi Ina Sha'awar driving." Yace "To kuwa kin samu. Bari Muje filin koyon tuk'i na soma nunamiki daga yau." . Nasha mamaki da nan da nan Ya juya kan mota, ya canza hanya Sannan ya k'ara speed, Sai gamu a babban wani fili babba, har da wata mata ma da mijinta, Itama tana koyo. Ancle ya nunamin komai a hankali, da yarda zan yi komai. Kamar wasa ya bani kan motar, ko tsoro bai jiba, yace na jarraba, amma yana kusa dani a gefena. Kafin na soma yace" Sai kin sa nutsuwa sosai fa, kuma ki cire tsoro, idan ba haka ba, zaki jima baki iya ba." Tiryan Tiryan da na bi shawarar Ancle na kuma bi yarda ya nunamin komai, Sai gashi ina tuk'in motar sannu a hankali, saboda nima nutsatstsiyar ce ga saurin daukar karatu. Sai da ya sani nayi round biyar na tafkeken filin wurin. K'arshe yace. "Sumayya, Stop the car." Da na tsaya cak, yace.Na tsaida mota a hankali. "Kin burgeni gaskiya. Nasan duk in da muka sake yin fita uku ko biyar zaki iya mota. Abinda ya rage Kawai zai rage miki, hawa titi da lunguna, kinsan Shima training d'insa, dabam yake da na filin wuri irin wannan. Yanzu ki mai damu gida." Na zaro idanu "Daga koyon farko? baka tsoron na tintsirar da kai a hanya. d'an Murmushi kawai yayi, bai tanka ba, ya karb'i kan motar. Tun daga ranar kullum Sai mun fita a mota nida Ancle Fa'iz saboda koyamin mota. Mu kanyi yawace yawace kuma sosai a mota, bayan mun gama da komai. Bantab'a Samun farin ciki ba, zuciya ta ta rink'a haske tun da na auri Ancle, ba kamar na lokacin. Domin mun sake da juna da hira da annashuwa fiye da ko Yaushe. Amma dai har lokacin bansan matsayi na ba wurin Ancle Fa'iz. Ko da wasa banga alamun wai sona a tare da shi ba, duk da kulawar da yake bani fiye da baya, da kuma hira ta nishad'in da mukan yi. A k'arshe dai nike Jan mota na fita damu na dawo da mu. Har takai ma yakan bani mukullin motar na fita, ni kad'ai a cewar sa, da haka zan k'warance. K'iyayya sosai kuma mai zafi, na ganta a wannan k'arni, tasu Momi da 'ya'yanta, amma nayi biris. Da muka koma makaranta, Ancle ni ya bawa mukullin motar nake zuwa makaranta da ita. Shi ba kullum yake hawa, bai fi a Sati sau biyu ko d'aya ba. Domin idan ba wuri mai nisa bane, ya gwarace ya hau babur. Shi yasa motar kamar tawa. Idan Zai hau Sai dai ya karb'i mukullin a hannu na. Nan ma, Ina wuta a jefani. K"iyayya ta ninka ta baya. To na lura Momi, kamar batason b'acin ran Ancle Fa'izu ma.Domin ran nan na gaji da fitintunin da suka yawaita Saboda hawa motar Ancle Fa'iz. Na Shiga d'akinsa nayi sauri na ajiye masa mukullin motar, na fito da niyyar na Shiga motar haya. Ashe Ancle ya ganni, Sanda na a jiye. Ya d'auko da sauri ya biyo ni, in da ya kira suna na na tsaya cak a tsakar gida. Yace "Banace kibar mukullin motar ko yaushe a hannunki ba? Me kike nufi da ajiyewa? Kina nufin motar haya zaki Shiga? Kuma idan zan hau, ai ina yi miki magana ko? banason fa kike min gaddama". Karab a kunnen Momi, dake shirin saukowa daga bene dama jin muryoyin mu, ya Sata saukowar. A fusace tace "Wai Fa'iz, motar nan kan ka ka sayawa ko Sumayya?" Nan naga fuskar Ancle ta d'an sauya, zuwa ga yanayin jin zafin furucin Momi, amma a tausashe yace. "Momi ko kaina na sayawa, ai kamar iyalina na saiwa. Guntun gatarinka kuma ai yafi sari, ka bani. Rufin a Siri ce motar gida, domin tafi Shiga motar haya sau dubu ni a wurina." Nan naga Momi tayi shiru ta kasa mayar masa da martani. Ya Mik'omin mukullin motar na amsa a tsorace. Domin kuwa Momi tana da k'arfin iko kan d'anta da zatashi, yayi duk a binda taga dama. Na lura, a Kwai dai a binda yake taka mata burki a yanzu. Kwana biyu rak da faruwar wannan, Ina zaune da yamma Lis, Ina karatun littafi, gefe a hannu na biscuit ne short bread, Ina ci a hankali. Saye nake da Kaya English wear masu kyau, masu a don fari da bak'i na nad'e kaina da bak'in yanki nayi rooling d'insa, gashin kaina da nayi parking ya fito tsakiyar rolling d'in da nayi ya bayyana saboda ya kara cika da yawa ma sanadin kulawar da nake bashi fiye da baya. Khalifa ne tsidim ya fad'omin falon, babu ko sallama. Bai tab'a shigowa ba Sai ranar "Ina mukullin mota?" Yace dani yana shigowa. Na dubeshi a hassale. "Wace motafa?" "'Kuji mu da 'yar rainin hankali, a kwai wata mota, bayan ta yaya Fa'iz?" NayI masa kallon tara saura kwata, na bawa banza a jiya, na ci gaba da karatun littafina. Ya kunnu sosai "Wani salon wulak'anci kika fito da shi na share mutane? wai kin samu rana har da baje shanya? . Na d"aga masa hannu "Kaga Khalifa, ja tsummar rayuwarka ka b'acemin da gani. Bazan bada mukullin ba, Sai naji shak'a na suma na farfad'o tukun. Baligi kamarka a ce bakasan hak'k'in Shari'a ba, ka shigo min d'aki kai tsaye babu ko sallama,Sai kace ba d'an musilmi ba." A harzuk'e kamar ya kaimin naushi yace. "Ank'i a yi sallamar, gidan ubanki ne.?" Yana fad'in haka Kawai naga ya fad'amin d'aki . Tuni nasan aikin gama ya gama, domin mukullin kuwa ya d'auko, saboda a kan teburin mudubi na a jiye. Ya fito rik'e da shi Yana karkad'awa cikin jin Isa . Ya. jamin tsaki ya Fice. Na dad'e zuciya ta tana ta tafarfasa saboda d'iban albarkar da Khalifa yayi min. Bayan gasa min magana, ya shigemin uwar d'aka sirrina yayi bincike saboda mukullin mota. Naci alwashin duk runtsi zan hak'ura da motar nan na zauna lafiya. Ancle Fa'iz yana shigo min, ko zama bai yi ba yace "Waye ya fita da mota, banganta ba a farfajiyar gida?". A tak'aice banja da tsayi ba, nace "Khalifa ne" Wani irin kallo Ancle yayi min kafin yace cikin fushi. "A wani dalilin zaki bashi mukullin motar? to karki sake bashi, na fad'a miki." Fargaba ta afkuwar rigimar da bansan iyakacin ta ba, da kuma ni zan zama a bar zargi, shi yasa na marairaice nace "Haba my Ancle, d'an uwanka nefa Khalifa, smma a ce bashi da isar amfanarta?". Yace "Domin yana d'an uwana Sai a kace wajibi Sai yayi iko da a bina? Kuma babu izinina? For what reason?. Zan ci gaba da lallashin sa, ya d'agamin hannu. "Sauraramin Sumayya, babu ruwanki. Ya numfasa Sannan can yace "Wannan yaron Khalifa bashi da mutunci da kike gani. Wai ni zai dubi tsabar idona yace Wai ba girma na bane a ce matata tana hawa motata. Kenan nine dai dai da shi, da zan hau mota ya hau mota? to Wallahi bai isa ba, zai zo ya sameni Sai na Sab'amasa." Duk yarda naso na lallashi Ancle gudun afkuwar rikici, bai ma tsaya ba, ballantana ya saurareni, domin ya hau taken nasa , Sai yarda hali yayi. (Zuciya). Na dafe kaina cike da fargabar a binda zai biyo baya kuma. A daren ranar dai Ancle Fa'iz yazo ya sake dank'amin mukullin motar. Baice komai ba, kuma naga ransa a b'ace . Gudun kar na k'ara masa damuwa yasa na jinkirta fad'a masa k'udirina na hak'ura da motar, Sai washe gari. Amma kafin nan, Momi ce ta katsemin hanzari. Shigowa tayi Itama kai tsaye falona tana huci. "Munafuka, algunguma, kara da kiyashi. Ungulu da kan zabo. Dama masu iya magana, sunce idan belbela ta samu dama Sai tace masar ne garin ubanta. To Wallahi ba ki isa kisa 'ya'yana gababa. Tun da suke ko musayar yawu basu tab'ayi ba, amna sanadinki Fa'iz yaci mutuncin Khalifa gaya, akan mukullin motar da ba daga gidan ubanki kika zo da ita ba. To bani mukullin motar,ni na k'wace, ki turoshi nima yaci zarafina ya karb'a. Idan bakiyi haka ba, to baki isa k'aramar shaid'aniya ba ma kanwa kuma uwar gami." Momi tak'i tsayawa taji mafarin komai saboda rashin a dalci. Iya cin zarafi tayi min a ranar, bayan ta karb'e mukullin motar. Bansan iya adadin zagin da a kayiwa ubana ba a gidan nan. Ubana da yake kwance cikin kabari baisan hawa da sauka ba. Wannan shi yafi komai soya min zuciya. Na kifa kai na Shiga razgar Kukan da bantab'ayin sa ba, tun da nazo gidan. Menayiwa Momi? ta Ina na kuskurota?.menene Laifina a kan mota kuma? Tambayoyin da najerowa kaina Kenan, bayan naci kuka na k'oshi. Kyautatawa da biyayya,ninninkawa nake a b'angaren Momi fiye da kowa, saboda son da nakewa d'anta. Hakan yasa take da Wata daraja ma mai tsada a Zuciyata. Amma gashi duk a binda nake, Momi bata k'aunata. Nina lallashi kaina, saboda bana so Ancle Fa'iz yazo ya tuhumi sanadin damuwa ta, kuma ni bazan iya duban cikin idanun'sa nace Momin sa ta b'ata min ba. Bazan iya ba. To takaicin bi da bi, ya rink'a zuwar min, kamar Wacce iyaye suka yiwa baki suka ce Jeki kin gani. Domin bayan fitar Momi da kamar awa d'aya, Sai ga Ancle Fa'iz ya shigo min Shima, ransa a b'ace. Na dad'e banganshi cikin b'acin rai ba, irin haka, ko nace ma ban tab'a gani ba. Kuma wuri ya zauna yayi shiru Kawai. Na lura bai kula da yanayin damuwar da nake ciki ba. Na daure nace "Ancle Fa'iz lafiya kuwa kake? Wani a bu yana damunka ne?" Ya d'aga idanu a hankali, ya dubeni. "Zuciya ta ce take ta kai kawo, tana ta jimamin yarda na rasa matsayi tashi guda a wurinki, da zan baki umarnin kiyi a bu, amma ki k'iyi. Ya numfasa tukun ya d'ora da. Nace kar ki sake bawa Khalifa mukullin mota, amma shine kika bashi. Yanzu na shigo na ganshi yana gyarawa mota parking, da alamu dawowar sa Kenan daga yawon da ya tafi da ita. Zamana kike Sumayya, amma kika fifita farin cikin wani da nawa. Kika zab'i biyayya da kyautatawa ga wanina,da bashi da gurbin da ya can can'ta kiyi masa haka Sama dani. Why?" . Ya k'arashe furucin cikin kasalalliyar murya. Na sake Shiga kam, sabon rud'ani. Ta yaya zan wanke kaina ga Ancle ba tare da kawo laifin Momi da na tabbatar ita ta sake bawa Khalifa mukullin motar da ta k'wace a hannu na ba. Tabbas, ko zan sanar da Ancle Sai ta hikima da tausasa kalamai, saboda kar na fito da laifin Momin sa a sarari, da ko bai nuna jin zafi ba, ni bazan ji dad'i ba. Sai dai ina bud'e baki zan soma magana, ya katseni a harzuk'e. "Look kar kice dani, komai,domin bazan yarda ma dake ba, adana yawun bakinki karki yi asarar sa a banza". Ya tashi ya fice a binsa,bai kuwa sake lek'oni ba a ranar. Hawayen da na tsayar, su na ci gaba da zubarwa. Da nawa zanji a cikin'su. Momi zargina take, Khalifa ma, haka, ga Uban gayyar ma, yazo min da tasa tuhumar. Kuma ta Ancle tafi tayar min ma da hankali. Ji nayi Sam,bazan iya juriyar da nake zato zan yi ba,na jure duk rigimar da zata tunkaro, saboda Soyayyar da nakewa Ancle Fa'iz da tasa nake nacin son zama da shi, duk da bai nuna a aikace, ni matar'sa bace, face 'yar tayin zama Kawai.idan so cutane,to hak'uri ance magani ne. to zan d'au hak'urin kawai,domin na zauna lafiya. Bazan yarda da k'uruciya ta ba, a gadar min da ciwon zuciya.Tak'i kad'an zan k'ara, idan naga a bin yaci tura, zan bar musu gidan'su Kawai. A she kuwa gab, yake da yaci turar. Wasa ma farin girki a she, matsala na gaba. Dai dai k'arfe uku na dare, Khalifa ya sad'ad'o ya shigo min d'aki, bisa ga tsautsayi na sabon da nayi na rashin rufe k'ofata da mukulli daga ciki, Sai dai na tura ta Kawai, ga kuma fahimtar da Khalifa yayi, Ancle Fa'iz baya kwana a wurina. Wannan shi yasa ya samu nasarar yin a binda ya k'udurta a sauk'ak'e. Fitila ya fara kunnawa da ya shigo, haske ya gauraye d'akin Sannan ya ta sheni, ta hankar bubbuga filon da na d'ora kaina a kai. A tsorace na tashi. Na sake tsorata sosai da ganin Khalifa a kaina ya zubomin idanu. Na bazama na jawo softcotton blanket da na a jiye gefena, saboda irin Kayan baccin dake jikina na shan iska ne, saboda zafin da ake yi, a tsukun. "Lafiya? Khalifa me ya kawoka d'akina cikin dare? Cikin hankalinka kuwa kake?". Ya zaro min idanu, irin na tsoratarwa. "Na fikima wadatar hankali Sumayya. Ramuwa ce Kawai ta kawoni d'akin nan, saboda wai saboda ke Yaya Fa'iz ya cimin mutunci, cin mutuncin da ba'bu mahaluk'in da yayi min irin'sa. Nasan kuma ke kika zugoshi, to Wallahi kinyi kuskure babba,domin ni ba a takani a Sha!." Wani irin tsoro ya kamani sosai, domin zatona Wata illar zai min, ko ya hallakani. Muryata na rawa nace. "Khalifa, amma Sai cikin dare za'ka yi ramuwar? idan gari ya waye Kayi min komenene, amma don Allah banda yanzu." Yace "Ina! ai Wallahi baki isa ba, yanzu zan rama. Ramuwar gayya tafi ta gayya ciwo. Ciwon da naji a zuciyata Sai na ninninka miki irin'sa. Ki bani had'in kai, na 'yan mintina ne zan idar da nufina na tafi, idan kuma ba haka ba, zan k'ulla miki sharrin da babu mahaluk'in da zai iya wankeki a duniya? sai kowa ya tsaneki, ni da yaya Fa'iz Kawai kika had'ani, ni kuma Sai na had'aki da kowa kin zama a bar k'ya mata.mintina gomz sun isa na ida nufina na tafi, don ba yi min kika yi ba, kawai domin na cuceki ne, na kuma sake nisantaki da Yayana". Tuni na d'au hasken me Khalifa yake nufi,na kuma girgiza da mummunar manufar'sa, da ya rik'a a matsayin ramuwa. Nace "Wallahi Khalifa bazan aikata aikin ashsha ba, ban aikata ma a baya ba, Sai yanzu da nake da nauyin hak'k'in aure a wuyana? ni ba halina bane. Na yarda kayi min kowani hukunci idan kalmar hak'uri bazata ceceni ba, amma banda wannan manufar taka" Yace "Ai ban baki zab'i ba. Kuma ramuwa fa nace zanyi, kuma ramuwar mugunta ai a binda Mutum kasan yafi k'i shi za'ka yi masa ka huce. Kuma nasan mijinki ma, duk da baya sonki, zai tsaneki ya sakeki take, idan ya sa ni." Yana fad'in haka naga ya nufoni, ya fado gefen gadon kusa da ni. Nayi zallo gefe a zabure. "Wallahi zan fasa K'ara na tara Maka jama'a". Yace "Haka na fiso ai ki tara Mana ma mutane." Ya nufoni gadan gadan, ya kai min wata mahaukaciyar cafka. Na zille cikin zafin nama Na kuwa daddage na fasa wata irin k'ara cikin kad'aitaccen daren. Na kuma fasa ta biyu da tafi ta farko sauti. Sai naga Khalifa ya tsaya cak. Ancle Fa'iz ne kuwa farkon shigowa, saboda d'akin'sa yana dab da nawa, dole yafi kowa ji. Da Khalifa bakin k'ofa yaje ya tare, domin kar na fita, Amma ganin shigowar Ancle, Sai yaja gefe guda, ni kuma jin Ancle ya kira Sunana yana shigowa falon da sauri, na antayo daga d'aki, bayan naja wani mayafina dake jikin hunger na lullub'e k'irjina. Yarda na taho karta na nufo Ancle Fa'iz Sai a zaci jikin'sa zan fad'a, Amma Ina zuwa Sai na tsugune k'as a gaban'sa Ina kuka. Ancle naga ya Shiga wani irin rud'u da yaga Khalifa, ya juyo da kan'sa ya dubeni. Ya zuba Mana idanu Kawai, ya dubeni, Sai ya dubi Khalifa kuma. Can yasa hannu ya d'agoni daga durk'uson. "Ihun me kike yi? Me ya faru? Me yasa naga Khalifa a d'akin'ki? Kafin na iya amsawa Sai ga Muhibbat,da khairat sun shigo, ai Sai na sake Shiga d'imuwar rasa ta Ina zan fara, saboda kunyar Jama'ar da suka soma taruwa, kuma duk Jinin Khalifa.lokaci guda naga idanun Ancle sun sauya kala, sun yi jawur, Sai a zaci ba'ainihin kalar su fari fat bane, masu bada launin shud'i shud'i.Khalifa kuma Kawai yake kallo cikin sauyayyen Jan idanun. Cikin tsawa yace masa. "Me ya kawoka d'akin Sumayya? giya kasha, ko wiwi, ko kuma hodar iblis, fad'amin." A dake ya amsa."Sumul nake. Kuma idan Ina shan d'ayan su, ai kaine shaidar farko, Yaya Fa'iz." "Karka fad'amin Maganar banza, idan ka tashi shan, Sani zanyi? Fad'amin a binda ya kawo ka d'akinta, ko nayi Maka illar da bazaka moruba Wallahi." Bud'ar bakin Khalifa. "Gayyatoni tayi da kanta. Kuma batun yau ta soma gayyatata ta ba, saboda tace wai baka sauraronta, baka bata lokacinta, irin na mace da Miji yau ma bore nayi mata, nace zan fallasa komai, shine tayi ihu, domin reshe ya juye da mujiya." Muhibbat ta d'au salati, amma wani sakaran kallo da Ancle ya jefa mata, Sai ta d'inke bakin. Khairat dai bata ce komai ba, illa tagumi na tsantsar damuwa. Da k'yar na samu wani k'ololon a bu ya fad'amin da ya tsayamin a k'ahon zuci, saboda Shiga firgicin jin sharrin da Khalifa ya kallafamin. "Wallahi Ancle K'arya yakemin. Ina kwance na ganshi a tsaye a kaina.... Khalifa ya katse da sauri. "Ta d'an a dam za'kiyi min? Saboda kina tsoron hukuncin da zaki fuskanta?" Na sake fashewa da kuka. "Kaji tsoron Allah Khalifa...." Ya sake katseni."To, tsoronki zanji idan banji tsoron Allah ba? ai tsoron Allan yasa na zab'i na Toni a Siri komai yazo k'arshe." Shigowar Momi dai dai nan yasa na sake firgicewa, domin nasan al'amari ma ya gama lalacewa. Ga Khalifa ya hanani nayi bayani sosai har Momi ta shigo.K'arin d'imaucewar tawa ma, da na kasa gane gaskiyar sirrin zuciyar Ancle Fa'iz na yarda ko rashin yarda, game da mummunan sharrin da Khalifa ya k'ullamin, domin har Momi ta shigo ta soma magana baice komai ba. Da alamu bayan rud'ani, kansa ya d'auki zafi, b'ararraka caji Kawai yake tayi. Momi ta dubemu Mu duka tace "Wai me yake faruwa a nan.? Ihu da surutai sun tsoratani da k'yar na iya fitowa, zatona ko b'arayi suka shigo ma, Sai da na tabbatar da muryoyi." Kafin ma ta rufe baki Muhibbat ta zayyano, Khalifa ya karb'a ya k'arashe har da k'ari. Mugun Kallon da Momi tayi min banyi zaton zan tsira daga shan maruka ba, hagu da dama, ko kuma saukar mahaukacin duka, irin na kawo wuk'a. "Biri yayi kama da Mutum, kuma alamu a lamun somin hauka zub da miyau.Tuni na tsinke da al'amarinki dama Sumayya, zaki iya fiye da haka. Wato bayan kin tarwatsamin Zaman lafiyar yara, yanzu kuma kinzo kin gurb'atamin tarbiyyar yarona da na d'ebi shekaru Ina tarbiyya. To Wallahi hukuncin da zan d'auka a kan'ki ba iya ke kad'ai zai tsaya ba, har iyayenki, ko da yake baki ma dasu Sai kakanni, to har tsufansu bazan tausaya ba." Cikin Kukan da da k'Yar yake fita saboda tashin hankali nace "Momi, Wallahi sharrin Khalifa ne, shine......" Ta dakamin tsawa."Rufemin baki Munafukar banza,mai bak'ar a niya, da mugun hali, da mugun usuli." Nan naga Ancle Fa'iz ya dubi Momi a har gitse, da alamun Furucinta ya Sosa masa rai sosai, Kawai ta tsira ne, saboda itan maman sa ce, bansan me yasa shi jin zafin furucin ba dai, tun da iya tunani na yanzu ni na gama tozarta, na gama bakin jinin da baza a tausaya min ba ko jin zafin duk kalar mummunan furucin da za a jefeni da shi. Babban tashin hankalina da har lokacin bansan cikin zuciyar Ancle Faiz ba, game da yarda ko rashin yarda game da sharrin da khalifa ya kullamin, har zuwa in da Momi tace. "Dole sai ka saki yarinyar nan Faiz, umarni ne ba shawara ba, in dai nina haifeka, na baka daga nan zuwa safiya kawai, ni na rasa uwar dalilin da yasa har yanzu ka kasa sallamar ta ta ka ma gabanta, daga taimako? to taimako mana domin ka samu sararin auren Salima, ne,kuma bukata ta biya, to jiran me ka keyi?". Dai dai nan cikin sheshshekar kuka na daga idanu na dubi Ancle, in da muka hada idanu, idanun nan nasa suna nan jazur, kawai sai naga ya lumshe su a hankali ya sunkuyar da kai kawai, da alamu yana cikin tsananin rudani, kuma kwakwalwarsa ta dauki mugun zafin shiga tashin hankalin da bai taba shiga ba. Ni kam babu abinda nafiso irin yace ya sakenin yafiye min komai, me zan tsinta a gidan, kuma da wani ido zan ci gaba da kallon kowa na gidan, musamman Ancle Faiz game wannan mummunan sharrin da a ka kullamin. *Bonanza* _Tabbas page din baya da wannan duk na tsawaita domin page biyu ne duka a matsayin daya kowanne, domin ni kaina na afu da kuzo kubawa idanunku a binci na hakika game da wannan labari da har yau ba ku shiga birnin sa ba_ _Ga duk mai son ayi da ita to ga dama ta garabasa, cikin sauki da rahusa, saboda abubuwan da mutum zai amfana da shi na karuwa da nishadi ya ninninka kimar abinda zai bayar babu ma hadi_ mai bukatar hakan ga a count no 8025527956 Opay _Zainab ilyas_ _Shaidar biya ta wannan number ta whatapp_ 09096409711 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels